babu. Ta nan ta
gudu a tunaninsa.
Amma ba haka abin yake ba!Tun
daren da aka kulle ta aljanin ya dauke
ta, shi ya fasa silin din don ya bar wa
Malam Iro shaidar kulle ta da aka yi ba
shi ne mafitar hana ta yawon da ya
assasa mata ba.
A daren Fauziyya ta samu kanta
cikin gararamba ba tare da ta san inda
kanta yake ba, saboda a lokacin aljanin
ba ya tare da ita, shi da ma burinsa
kawai ya fito da ita ya sa ta yin yawo ba
madosa.
Tun da Fauziyya ta taso a
rayuwarta ba ta san wani abu wai jin
dadi ba, koyaushe cikin kuncin rayuwa
ta ke, wannan yana damunta matuka,
musamman yawan zamanta a gurin
73
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
najasa, tana takura ainun, don dai babu
yadda za ta yi ne.
Da ta samu lafiya na tsayin
shekara har kiba ta yi saboda kwanciyar
hankali, amma tun bayan dawowar
matsalarta ta fige, ta rame, ta kasance
cikin kuncin da ya fi na da muni.
Idan Fauziyya za ta zagaye fadin
garin Katsina tana yawo ba ta jin za ta
iya zama na minti biyar da sunan za ta
huta, saboda koyaushe tana jin sha'awar
ta yi ta tafiya, diddigenta a hanya suke,
kuma a cikin duhuwa.
Sai dai ta kan samu kanta cikin
raunin gajiya, amma zuciyarta ba ta ba
ta shawarar ta zauna ta hutan.
Na san za ka ce ba ta taba haduwa
da jami'an tsaro ba?
Sun sha ganinta, amma suna yi
mata kallon mahaukaciya tuburan,
74
SUNANMU DAYA-2 VAJNOOR
saboda yadda ta ke shiga duhuwaba
tarc da tana jin tsoron wani abu ba,
musamman kowa ya san yadda shukoki
suka yi yawa a gefen gari A King
paradisc hotel da ta biyo a duhuwar ma
ta ke bi, maimakon ta bi siririyar hanyar
da akc amfani da ita,mutanc masu
tafiyar Kasa, babura, ko motoci, amma
ita sai ta yanki daji ba ruwanta.
A wannanranaamummunan
al'amarin ya faru da Fauziyya, misalin karfe uku da mintocitna dare ta biyo
hanyar da akc amfani da ita,da yake
ranar ana ajon wwata kilaki sa Hirji,
wannan ya sa king paradisc ba ta yi
cikar dangon da aka saba yi ba, tun
kusan karfe daya ma sawu ya fara daukowa.
Fauziyya na tafe cikinrangajin tafiya, wani matashi da ya fito daga king
75
SUNANMU DAYA-2 VAJNOOR
paradisc cikin motarsa Toyota fara mai
lambar Mashi ya zo gurinta a tunaninsa
tana cikin karuwan da ke baza hajarsu a
gurin. Ya kashe motar bayan ya dallare
mata fuska da hasken fitilar motar.
Ya isa gurinta yana yi mata
magana, ta yi masa shiru ta ci gaba da
tafiya.
Bai yi wata-wata ba, kawai sai ya
rungumcta a kirjinsa, ita kuma ta wanka
masa mari dolc ya sake ta yana kallonta
galala. Yayin da ta ci gaba da tafiya ya
kasa jurcwa ya kai mata cafka a karo na
biyu. Nan ma ta wanka masa wani
marin, abin da ya sa ya kasa kai zuciya
ncsa kcnan, yana ganin a matsayinsa na
babban yaro ya za a yi karuwa kamar
wannan ficikar ta marc shi har sau biyu?
Wayc ubanta a kasar nan?
76
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
Kawai zuciya ta ja jagorance shi
sakarwa shaidan linzamin zuciyarsa ya
shige motarsa ya murjc ta.
Sanadin kenan, ko shurawa ba ta
kara yi a gurin ba, ajali ya riske ta ta
sanadin zafin zuciyarsa da ya biyc wa
ya aikata danyen hukuncin da ya zamo
tarin nadama".
Labiba na zuwa daidai nan a
labarinta sai ta rufe bakinta tana kallon
Abidu wanda tuni gumi ya gama jikc
shi sharkaf.
Та сс, "Duk wanda zai ba ka
wannan labarin, ai ka san ya wuce duk
inda ka kc tunani. Na san yanzu ka
fahimcc wacc ce Fauziyya, da wanda ya
kashe ta".
Shiru Abodu ya yi yana ambato.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
די
SUNANAM DYE VANOWOR
A cikin zuciyarsa, tabbas wannan
labari da Labiba ta ba shi ya kidima shi,
kuma ya yarda HAKKI NA BIBIYA!
Kafin ya yi magana Labiba ta ci
gaba da cewas
"Ba wasu ba ne bayin Allah da
suka tsayu da taimakkon Fauziyya ba face ni da Abid.
Mun kasance eikin tsananin
jimami yayin da muka samu labarin
mutuwar Fauziyya, to amma ba mu da
yadda za mu yi tunda Ubangiji ya fi mu
sonta, kuma Shi ya ara mana lokaci har muka taimake ta a baya.
Bayan mun dawo daga dogon
zangon da muka yi ne muka bibiyi sanadin mutuwar tata, duk abin da ya
faru tsakaninku ya bayyana a gare mu, Kuskure daya aka samu Abidu, lokacin da ka aikata wannan danyen aiki
khtESΓΠ
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
babu wanda ya ganka sai Ubangijin da
Ya chalicce ka, kamanta da Shiyana
ganinka, da ka tabbatar mutuwar tata sai
ka janye gawar tata yadda za ka samu
hanya ka tafi, abinka ba ruwanka baine
da yi mata gatancin sada ta da wadanda
za su suturce ta su kai ta makwancinta.
02.Amma saboda wannan shi ne karo
na farkó da ka taba yin kisan rai, sai
zuciyarka ta kasa zamaslafiya, daga
lokacin ne ka daima nyawon dare, ка
tuna?' m u olob ad sd sy sn
sl Nan ma ba ta jira cewarsa ba, ta ci
gaba.s Tewntiel sb silk 2 sd ide
"Damuwar da ka shiga ita ta sa ka
tuba daga rayuwar barikin da kakc yi a
boycomahaifanka ba su sáni rbat wanda
shi ma mahaifin naka yanadda tasa
matsalar sidansth. takaswrawasb wajen
rugujcwar rayuwaryalyansa. Wato ya
79
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
kasance mutum mai tsinuwa da cire
albarka ga wanda ya 6ata maimakon ya
yi masa addu'ar shiriya kamar yadda
Ma'aiki (S.A.W) ya fada mana a
ingantaccen hadisi, Ka fadi alkhairi ko
ka yi shiri.
Da yake ba labarin mahaifinka zan
ba ka ba, wannan matsalarsa ce, ina so
ka sani shi ma ya taka rawar da yanzu
yake nadamar duk 'ya'yansa babu na
gari, to in bacin abinsa, ka tsine wa
wanda ya 6ata ba dole shi ma ya batar
da naka ba idan ya samu sararin tunda
shi ba ka san illar da tsinuwar taka ta
janyo masa ba.
Bayan ka daina yawon darc wanda
kakc tunanin ka yi tsarkakkiyar tuba, ka
binnc abin da ka aikata ba tare da ka
sanar da kowa ba ballantana a je ga
maganar yanke maka hukunci.
80
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
Bari na kawo maka wata fatawa,
ko kuma na ce ingantaccen hadiso da ke
magana akan abin da ka aikata da hukuncinsa.
'An karbo daga Abi Bakar dan
Muhammadu, dan Umar, dan Hazami, daga babansa, daga kakansa Allah ya yarda da su, 'Hakika Annabi (S.A.W) ya
rubuta zuwa ga mutanen Yaman, sai ya ambaci hadisin a cikinsa cewa, 'Wanda
ya nemi mumini da kisa ga kuma hujja
za a rama, sai idan waliyansa suka yarda
wa wanda aka kashc, kuma hakika a
cikin rai akwai diyya, da rakuma dari, a
cikin hukuncin hanci, idan aka aibata halittarsa, akwai diyya a game da ido biyu, akwai diyya a game da zakari,
akwai diyya a game da fatar baki biyu,
akwai diyya a game da zakari, akwai diyya a game da gwaiwa biyu, akwai
81
SUNANMU DAYA-2 AJNOOR
diyya a gamc da tsatso, akwai sulusi
diyya a gamc da jaifa, akwai sulusin
diyya a game da munakkila, akwai
rakuma goma a game da hakora, akwa
rakuma biyar a game da mudiha, akwaj
rakuma biyar kuma ana kashe namiji
idan ya kashe macc. Amma game da
masu amfani da dinari akwai dinan
dubu". (Abu Dawuda ya ruwaito shi
cikin Mursal, kuma da Nisa'i da dan
Khuzaima da dan Jamd da dan Hibban
da Ahmad suka fitar da shi, kuma sun yi
sabani cikin ingancinsa).
Duba da wannan ingantaccen
hadisin ya sa muka ga dacewar shiga
cikin lamarinka don mu haska maka
idan ka zamo mai kwadayin
kyakkyawan sakamako, to ka yi
cikakkiyar tuba ta ba wa shari'a dama a
fidda hakkin rai da ka yi da kisan
82
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
ganganci kamar yadda wani ingantaccen
hadisin yake fada.
'Diyya ita ce hakika talatin da
kuma jaza'a talati, da kuma khalifa
arba'in, wacce a cikin cikinta akwai
'ya'yanta". (Hadisin Hasanun ne).
Abu na farko da muka fara duba a
tare da kai Abidu shi ne, ka kasance
masanin ilimin addini, amma saboda
kwadayin da kyallin zaman duniya ke
maka yawo a zuciya ya sa kana son 6ata
lahirarka, sai Abid ya kawo shawarar
yadda za mu dinga haska maka cewa,
abin nan fa da ka yi tuna ka binne, dole
akwai diyya a tare da kai.
Kun hadu da Abid a masallaci
kana tunanin ka taba ganinsa, sam ba ka
sanshi ba, hikimar dai jan hankalinka ya
sa aka yi maka wannan tsarin yadda za
ku hadu.
83
SUNANMU DAYA-2
NAJNOOR
1
1
1
A abin da ya yi na canko aya da
surar da kake karantawa a cikin
zuciyarka, da kuma kin fitowarsa yayin
da masu hidimtawa masallacin suka
shigo sun isa su tabbatar maka shi din
ba mutum ba ne.
A ranar ya sake bayyana a gare ka
a wajen gidan Amadi Kurfi yana shaye.
shaye, wai a nan ana nuna maka mutum
a fuska ba mutum ba ne, wato ka ga kai
duk wanda zai ganka a masallaci yana
kyautata maka zato, to a bayan idon
wasu kuma za ka iya kauce hanya
kamar yadda Abid ya nuna maka.
Maimakon ku yi haduwa ta uku
da Abid, sai muka hadu da kai a shagon
Shehu Boss, wanda tun fil'azal
cinikayya kan hada mu idan za mu yi
wa marayun Allah (Mutane) sadaka, na
ba ka labarin wata soyayya mai ban
84
-
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
al'ajabi a shagon. Kai da jin labarin
soyayyar ai ka san idan dai ba irin
labarun hikayoyin din nan ba da ake
kirkira to zai kasance a mafarki, don ko
mu a jinsinmu ba ma irin wannan
soyayyar ta sadaukar da rai har a fita
haddin addini, wato kadaituwa irin
lokacin da na ce maka Abid da
Sumayyah na yi.
Hikimar ba ka labarin nan ma a
kuma jan hankalinka, ka gane wani kulli
idan aka yi shi zai yi wahala a warware
shi cikin sassaukar hanjya.
Duk abin da muka yi a gare ka
babu zalunci, illa taimako da muka yi
maka, ka sauke nauyin hakkin da ke
tare da kai tun kafin guri ya kure maka,
ka rasa hanyar tuba.
Haduwar Abid da Salman
abokinka a Kaduna, ba ta nufin komai
85
ANOXA
1
1
SENANME DAYA-2
illa ana so Salman ya kawo ma
labarin da zai rikitar da kai, wata kila
iya tsinkaye da abin da ake so ka fasa
Amma haduwarsa da Nazeert
nufin kulla wani zaren da za a hask
maka wani abu na cewar, ba
SUNANKU DAYA ne kadai ab
mamaki ba, a'a dalil
KAMANNUNKU DAYA.
Na farko ba ka san sun hadu
har sun tattauna za su sake haduwa?
Luna Hotel don a tunatar da kai yawo
daren da ka yi har ka aikata laifin kisan
bayan kun gama wayar da Nazcer, Abi
ya bayyana a gare shi da nufin kai di
ne, ya kuma ba shi hakuri.
Kafin ka iso Luna din har sun rab
kowa ya kama gabansa, don haka da ka
zo ba ka tarar da Nazeer ba, shi kuma
tunda ya san kun hadu a darco shi ya s
86
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
da ka je washegari ya ga ka raina masa
hankali.
A washegarin ranar mun hadu da
kai gurin karbar dinki, haduwa ta biyu
ni da kai, tun a lokacin na so jan
hankalinka don na fara kyankyasa maka
abin da ka binne yana ta yaduwa da
mugunya a rayuwarka, amma sai ka
kawar da gabar da na kamo da nuna min
daukar zafinka, wanda da ma na san duk
abin da ka aikata can bayan dokin
zuciya ne, don ka kasance mara
sassaucin zuciya ta wajen sanyaya
lamuran da ga66an jikinka za su
aiwatar.
Saboda haka ni ma sai na
shashantar da lamarin muka yi hira
kawai muka rabu.
Kamar yadda ka sani kai din mai
laifi ne ta kowanne 6angarc, sai muka
87
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
1 ga yuwuwar gwara mu fidda wa
mahaifanka jin idan babu kai za su samu
nakasu ta bangaren soyayyar da suke
maka, saboda ko da hukuncin kisa zai 1
hau kanka abin ya zo musu da sauki ba
kamar yadda mahaifan naka suke
matukar girmama kaunarka har sukan
dauke ka da girman daraja fiye da
sauran yaransu.
Wannan ya sa Abid ya yi shigar
Alhaji Sani Kafinta ya je wa mahaifinka
da labarin ya ganka ka shawo barąsa!
Eh ai ka sha barasar, amma ka
dąina. Hakan ba yana nufin an zalunce
ka ba a wajenmu illa yadda na fada
maka za a cire maka tsammatar ci gaba
da rayuwa a gurin mahaifanka.
Koda yake daga baya akwai wasu
shehunan Malamai da suka kalubalance
mu a kan abin da muka yi ba taimako ba
88
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
nc, zalunci ne, sai dai duk da haka ya
zamo darasi ga shi mahaifin naka mai
aibata 'ya'yan al'umma.
"An karbo daga Aishatu Allah ya
yarda da ita ta ce, "Lallai Manzon Allah
(S.A.W) ya ce' 'Shin ana yin ceton
haddi, daga haddodin Allah?' Ya tashi
ya yi huduba ya ce, 'Ya ku mutane an
halaka wadanda suke kafin ku, domin
sun kasance idan wani daga cikinsu mai
daukaka ya yi sata sai su bar shi, idan
wani daga cikinsu mai rauni ya yi sata
sai su tsaida masa haddi". (Bukhari da
Muslim suka ruwaito shu).
Je ka a nan mun yi kuskure, ai mu
ma ababen halitta ne, dole a same mu da
kuskuren, kuma muna neman afuwarka
a wannan gabar!
Sai maganar dattijo mai 'ya, wadda
ake tuhumar ka yi mata ciki, shi ma an
89
1
1
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
kawo shi ne don a rikitar maka da tunam
ka tuna da wancan hakkin.
Bayan su kuma an kawo Naz
da Abdulmalik abokanka mам
tuhumarka da laifin kisan rai. Idan k
nutsu tsaf za ka gane, suna so ne ka
amsa laifin ka yi kisan kai cikin
ganganci, amma ka ki amsawa, wata
kila don kana ganin sun biyo maka da
kashe wasu mutanen ne maimakonr
daya tal da ka ke ganin bai kai daraja
ka yi asarar naka ran dominsa ba.
Da ka koma gida ka samu labaris
zuwan Nazeer, tun a nan ya kamata ka
gane wadancan da ka fara haduwa da
jinnu ne, tunda ga shi an sanar da kai
Nazeer din ya fi awa biyu a gidan yana
jiranka.
Sannan ka tarar da I.D card dinka
a inda ka ajiye shi a cikin dakinka
90
SUNANMU DAMA-2 NAJNOOR
amma duk wannan baiisa ka yi wani abu
a kai na abin da ake haska maka ba
Mu dawo fangare Rukayyah
wadda ka gansu da Abid, ka zo gidansu
ta fito kuka yi magana ta ce tas rabun da
kai a kan ka dauke ta kana neman 6ata:
mata rayuwa.
Ba asalim Rukayyan ka ba cс,.
saboda mun san darajar mutumei, kuma
mun karbi wancan gyaran da aka yi
mana na kuskurc, don haka muka guji
aibataka a gidan ko da kuwa ba ka da
rabon aurenta!
Sam Rukayyah ta asali ba ta da
masaniyar abin da ya faru daga
haduwarku a kofar Marusa zuwa
lokacin da ka aika kiranta.
Wannan shi ne abin da ya kawo ni
gare ka, na kuma sanar da kai abin da ka
binnc.
91
1
1
SUNANME DAYA-2 NAJNOOR
Muna neman afuwarka ka yafe
mana kuskuren da muka yi maka.
Sannan muna tunasar da kai, duk
abin da ya faru tsakaninmu da kai
fadakarwa ce ga al'umma, domin akwai
icri-irinka da sukan aikata laifin kisan
kai cikin ganganci, amma su binnc ba
tarc da sun bayyana ba, saboda kawai
kwadayin zaman duniya, ba sa ko
tunanin yanzu, anjima, gobe ko jibi za
su iya mutuwa.
Misali kamar kai in bacin mun san
lamarin Fauziyya wanda uwarta ta ja
mata da ba mu shiga lamarinka ba, wata
kila da haka za ka karc rayuwarka ba
tarc da ka bada damar fitar da hakkin rai
a garc ka ba.
Da wannan nakc maka fitan
alkhairi Abidu, ko ka kai kanka ga
hukuma a fitar da hakkin rai a jikinka,
SUNANMUDAYA-2 NAJNOOR
ko kuma ka zauna da hakkin. Sai dai ka sani, ko ba ka samu irinmu ba masu son
gyara al'umma ba, za ka iya haduwa da jafa'i kala-kala don ahkkin rai ba Karamar musiba ba ce ga wanda alhakin fitarsa ya rataya a kansa.
Wasu za ka riske su cikin kuncin
rayuwa koyaushe.
Wasu kuma duk zafin neman da suke ba ya amfana musu komai.
Wasu cuta ake jarabtarsu da ita, ka
ga dai sun kar wani don su su sake, amma ciwo ya hana sakewar.
To a irin wannan mcne ne riba? Ва gwanda mutum ya tsaya da gaskiyarsa
ba, don ya kwadaitu da kyakkyawan sakamako ba?"
Idanun Abidu sha6c-sha6c da
hawaye ya dago kai, murya a raunane
ya cc.
93
SUNANMU DAYA-2 AJNOOR
"Wallahi na gode da wannan
taimako da kuka yi min, na kuma yafe
muku duk abin da kuka yi min bisa
kuskure.
Tun daga yanzu ma ina mai yi
miki albishir zan kai kaina ga hukuma
cikin biyu a yi daya, ko dai na biya
diyyar rai da dukiya, ko kuma a kashe ni
duk yadda ya samu zan yi farin ciki,
muddin zan gyara kurena zuwa
lahirata".
Labiba ta yi murmushi, ta cc.
"Na ji dadi sosai Abidu: da ka
fahimci rayuwa. Ina kuma sanar da kai
zan yi kokarin hada ka da mahaifin
Fauziyya wanda har yanzu yake kukan
mutuwarta.
Saboda bayan ka barta a inda ka
murje ta da mota, hukumar 'yan sanda
suka tsinci gawarta suka yi sanarwa, har
94
a
At
a
Su
aj
a
Ka
Ka
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
shi Malam Iro ya samu labari ya je ya
karbi gawar tata yana mai kokawa da ta
mutu a cikin gurbatacciyar rayuwa.
Daga baya ne na yi shigar
bil'adama kamar yanzu, na je na yi masa
gamsasshen bayani game da lalurar
Fauziyya a matsayina na aminiyarta, na
nuna masa ma ai a gidanmu ta ke zuwa
duk lokacin da ba ta gidansa, sai ranar
da lalurin zai faru ne ma ciwon nata ya
taso ta fita.
Na yi masa kuma alkawarin zan
taya shi addu'ar Allah ya bayyana
wanda ya yi kisan, don na fada masa
akwai wanda nake zargin shi ya aikata
hakan a gare ta".
Abidu ya goge hawayen da ke
idanunsa, ya ce.
"Idan ba damuwa Labiba ki hada
ni da shi mahaifin Fauziyyan a yau din
95
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
nan don na yi alkawarin ba za a kwana
ba sai na kai kaina ga hukuma".
Labiba ta tsura masa idanu, lokaci
guda tsananin tausayinsa ya shige ta, ta
ce.
"Ba damuwa don wannan, sai dai
ka san me?"
Ya girgiza kai ba tare da ya yi
magana ba.
Ta ce, "Kafin ka damka kanka ga
hukuma, zan yi maka wani taimako na
gyara tsakaninka da mahaifinka, gudun
kada idan ya ji wannan labarin ya yanke
maka BAHAGON HUKUNCI, ma'ana
ka yi tuban da kake neman rahamar
Ubangiji, amma ka rabu da shi yana mai
tsananta fushi da kai, wanda mu ne
sanadi".
Ya ce, "Idan kin yi hakan ma kin
taimake ni, kuma zan ji dadi, ko da
96
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
hukuncin kisan ya tabbata a gare ni na
san zan samu addu'arsa".
Suka yi shiru su duka, kan Labiba
nakasa tausayin Abidu na kara shigarta,
shi kuma yana ji a ransa kamar ya fi
kowa sa'ar rayuwa, tunda har yau aka
tono masa abin da ya binne har aka nuna
masa hanyar tuba ta gaskiya ba irin
wadda ya yi ba.
Lallai wannan ya fi komai dadi a
gare shi, ba ya kaico don hukuncin kisa
ya hau kansa!
BAYAN SHEKARU SHA
SHIDA
Alhaji Abidu Nasir Barhim yana
zaune a katoton falonsa da ya gama
haduwa da kayan more rayuwa, Hajiya
Rukayyah tana daga gefensa dauke da
turtsetsen cikinta haihuwa yau ko gobc.
97
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
Muhammad dan shekaru goma ya
shigo falon rikc da hannun wani yaro
wanda shi ma ba zai wucc shekaru
goman ba. Sun taso ne daga makaranta.
Alhaji Abidu ya dubi Muhammad
da murmushi a fuskarsa ya ce.
"Muhammad ina ka samo aboki?"
Muhammad ya sake riko hannun
abokin nasa yana dariya ya ce.
"Daddy dan makarantarmu ne
wanda na ke fada maka SUNANMU
DAYA da shi".
Da sauri Alhaji Abidu ya dubi
Hajiya Rukayyah kamar yana son
tuhumarta wani abu, amma sai ya basar
ya maida duban nasa ga Muhammad ya
ce.
"Shi ma sunansa Muhammad
a
kenan?"
Muhammad ya kada kai, ya сc.
98
Sa
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
"Eh Daddy, sunansa Muhammad Abid Nasir!"
Gaban Alhaji Abidu ya sake faduwa, ya tsura wa yaron idanu, yana
tuna abubuwan da suka faru da shi can
baya, wato lokacin da ya 6oye laifin da
ya aikata. Wanda bayan ya kai kansa kotu, kuma Labiba ta gayyato Malam
Iro mahaifin Fauziyya, tun kafin a yi
zaman kotun ma Malam Iro ya ce shi
kam ya yafe wa Abidu abin da ya
aikata, yana fatan hakan ya zamo darasi
ga na 'yan baya.
A lokacin da kotun ta zauna kuma
aka yanke wa Abidu adadin abin da zai
biya diyya kamar yadda shari'a ta tanada, sannan aka umarce shi yin
azumi sittin na kaffara.
Tun daga lokacin ya samu
kwanciyar hankali, komai ya kwaranye,
99
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
har shi kansa mahaifin nasa sai da ya yi
sanyi lokacin da ya ji abin da ya faru da
Abidun, har ya huce da fushin da yake
da shi, mafarin kenan ya shiga cikin
lamarinsa har aka sanya ranar aurensa
da Rukayyah, lokaci kuma na yi aka yi
auren.
Yanzu shekarunsu goma sha biyar
kenan, suna da 'ya'ya hudu, Labiba ita
ce babba, wadda suka yi wa aljana
Labiba takwara, sannan aka haifi
Muhammad, sai Aliyu da Nafi'u. Yanzu
kuma ga cikin na biyar a jikin Hajiya
Rukayyah.
Alhaji Abidu ya sauke gwauron
numfashi, cikin kada kai ya mike tsaye
a cikin zuciyarsa yana maimaita kalmar.
"SUNANMU DAYA”.
MASHA ALLAH
100
AgV
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
Abin da muka yi kuskure Allah ya
yafe mana, wanda muka yi daidai Ya
hada mu a ladar.
IYAYEN YUSUF
Nura Sada Nasimat Kt
Da
Naja'atu Haruna Sale
Ke muku fatan alkhairi.
SAKO
Tabbas Ubangiji shi Ya sanya dan
Adam ya zamo khalifansa a ban kasa
don haka koyaushe bawa ya riki
gaskiya tare da kyakkyawar rayuwa.
Ka zama mai SADAUKARWA
wajen neman bautar Allah, kar ka sanya
wasu-wasi ballantana kayi tunanin INA
HUJJAR TA KE? Don kar ka shiga
WUTAR DAJ darrada karsheka
1011
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
BAHAGON HUKUNCI, amma fa
RASHIN JINI bai sa a gano
SUNANMU DAYA ba don rayuwa
yanzu ta zamo KAZA DA HATSI.
Daga alkalamin.
Aminu Malami Muhd
KADAN DAGA
WUYAR SABО
Та сс, "Wallahi Abba ne ya kori
Yaya Murtala".
Das! Na ji gabana ya fadi, gaskiya
ban so hukuncin da Abba ya yanke masa
ba, sai na ji da ma na ce eh a kan maganar
da ya fada.
Ban ankara ba na ji hawaye na bin
kumatuna, Asma'u ta се.
"Aunty kukan me kikc yi ne? Na
dauka abin da Abba ya yi daidai ne? Idan
102
SUNANMU DAYA-2 NAJNOOR
kika tuna cin mutumcin da ya yi miki... To
me ye naki na zubar da hawayenki a
banza?"
Na jawo hankici
Na sharc hawaycn da ke bin
kumatuna, na ce da ita.
"Kada ki damu Asma'u, ba wai na ji
zafin abin da Abba ya yi masa ba nc,
kawai na ji ya ba ni tausayi".
Daga nan hirar ta tsinkc, inda
Asma'u ta tashi ta bar ni a falon.
Darc ya yi shiru ban ji aikc na zo inji
Isma'il ba, har misalin tara na dare, saboda
haka hankalina ya matukar tashi, na sa hannu na janyo wayata na duba asusun, ko
Kwandala babu sai wasu kobbai.
Na ja dogon tsaki, ko me Isnar yake
nufi nc, ko ya yi fushi nc?
Ban san lokacin da bacci ya dauke ni
ba, misalin karfe sha biyu da rabi da minti
biyu sai ga wani yaro ya shigo gidan ya
103
SU NANMU DAYA-2 NAJNOOR
kawo takarda wai in ji wani ya ce a kawo
min. Na kara cikin zumudi, don na san ba
ta wuce ta Isma'il.
Na bude don na karanta, sai na ga
rubutun kamar ba nasa ba, amma haka nan
na daurc na soma karantawa.
Kin ga Fatima, ni fa ba karamin yaro
ba nc bare ki ba shi alcwa a baki, ko kin
dauka ban dauki haske a kan abin da ke
tsakaninki da Murtala ba? to ki sani ki
kuma dada sani, tuni na soma bincike a
kan al'amuranki.
MARYAM HASHIM. ALIYU WAMAKO
tul
Littattafan marubuciyar:-
RASHIN JINI
SADAUKARW
INA HUJJAR TAKE!
KAZADA HATSI
WUTAR DAJI.
SUNANMU DAYA
BAHAGON HUKNCI
DAJL.s
F
ancy Printing & Publishing Co
S/Unguwa, K/Dorawa, Katsina. 07027048439, 08131994808, 08095052216
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels