huta ba, kin san duk
guda sai Allah ya dor
lokacin zaki a و
mutune n
"Halaka kamar ya y.
wannan yaro da rashin
nzu? ko a davyarinyar a kai
a son akai masa yarinyar ne
ki matarsa saki uku lokaci
ta, shi yasa wani
a"
"Halaka auren kisan w
jejeniyar daga ta shiga gidan a sakota
37
ruwa su sake maida auren su, sam tari hakan na faru. kuma
mutane masu kwadayi na amincewa suyi auren, wasu kuma
suna amincewa daga karshe su ki sakin matar rigima ta biy baya, wasu kuwa daga yin auran sai kauna ta shiga tsakanin
su, shi kuma mijin da ya biya aka daura auren nacan yana jiran
fitowar mata sai dai ya ganta zata awon ciki ko ya ganta goye
da da ba kuma damar yi mata magana tun da matar wani ce, ke dai kiga mutun.
"Allah ya kyauta"
Dan acaba ya caki birki dai-dai saitin Isma"il da Jamila
suna zaune bisa wani dan dakali suna hirarrakin soyayya irin ta bariki
"Har ka dawo?" Jamila ta tambaya
"Eh har na dawo" Ya bata amsa
"Wa ka ba wasikar?" Jamila ta kara tambaya "Mahaifiyar ta na ba" Ya bata amsa karo na biyu
"Good' Ta fada gami da dauko kudi ta kara masa.
"Isma"il abinda nake so da kai ka......"
"Ba sai kin fada ba anan zan tare ai" ya tari numfashin ta.
"A'a ba haka nake son cewa ba."
"Me ki ke son cewa?"
"Ina nufin ka bar min gida na"
"Ina bar miki gidan ki?"
"E, kwarai ko kana da gado na."
:
"Ko bani da gadon ki baki isa ki korcni ba banyi miki laifin komai ba"
"Nawa kake kashe min?"
"Ni bance ina kashe miki wani abu ba" ya fada muryar sa sanyaye
"Ko kana biya min kudin haya"
"Ba daya, amma kisa na saki matata mai min biyayya da
38
timako ki kuma ce in bar miki gida"
"Wannan kai ta shafa"
"Lalle mata tsinannune wajen sharri" ya fada ransa bace.
"Kai kai tsinanan namiji mara tunani, wanda karuwar da
bata da tabbas tasa ya saki matarsa"
gari"
"Allah ya isa tsakanina dake Jamila"
"Kanka akeji mahaukaci ya fada rijiya".
"Wallahi sai kin gane kurenki in dai kina yawo a sabon
"Malam ka hakura tunda tace bata sonka, ga mata nan a
gari kamar janfa ajos" wani mutun da ka geſa ya fada, tunda
suka fara sa in sa yana wajen ya zuba hajjar zomo don kama
bakin zaren
Басе.
"Me ye na ka a ciki?" Isma'il ya tambayi mutumin rai
"Gani nai kana neman zubar da ajin maza, tunda tace
bata sonka sai kasan nayi" mutumiya kara fada ga. dukkan
alamun yafi Isma"il rigima
"Malam rabu dashi wahala ce ba ta ishe ba" Jamila ta
fada gami da shigewa cikin gida. Ta rufo kofar da karfi Isma il
tsayawa ya yi ya zubawa kofar gidan ido kamar bazai tafi ba,
tunanin Hajara ya fado masa lokaci guda, yarinya mai sadaukar
da kai da biyayya lallai....."
"Allah wadaran naka ya lalace." Mutumin dake ba
Isma'il shawara ya fada gami da yin gaba yana wasu surutai da
Isma"il bai fahimci ko me yake cewa ba, koma dai me yake
cewa Isma'il bai damu ba lallai yau ya gam da sharrin mace.
tasa ya saki matarsa har saki uku lokaci guda, ita kuma ta ce ya
bar mata gidanta yanzu bai san inda zai sa kansa ba, ga talauci
ga rashin aikin yi, dama Hajara ke taimakonsa da abinci da dan
na kashewa cikin sana ar wankin da take yi, yanzu gashi wata
tsinanniya da bai san daga inda take ba ta sa ya saketa.
39
"Kai dana-sani ban aikata haka ba." Ya fada a fili
"Yanzu ya zan yi da raina?" Sumoli, abinda ya fado a ransa
kenan "Yanzu ya zan koma mata bayan ga yadda muka yi a
policc sitashin, gashi kuma yanzu bani da kudi." Kai rabu da
zaman dadiro in dai an yi shi sai an koma ai zaman masifa ne,
wata zuciyar ta ce dashi.
A bangaren Jamila kuwa tana kulle gida ta nufi daki
madubi shi ta fara dubawa kamar koda yaushe, madubin takan
dubashi kamar sau sittin a rana daya.
Ramar tata kullum ci gaba da take yi ta lura da haka..e ganin yadda kumatun da take yaudarar maza da shi duk sun
lotsa sun koma loko, kwarmin idonta ma ya fara fadawa,
awarwarayen dake shiga hannunta da kyar ta lura yanzu sai ta
dan wara "yan yatsunta yanzu suke zama, duwawukan da take
kaďawa da jan hankalin maza da su yanzu sun sakwarkwace
tamkar na tsohuwar da ta shekara sittin a kauye, nonuwan da
da take takama da su yanzu sun zama wasu irin tamkar irin
ruwan nan dan kwandala da ya yi gardamar dauruwa.
Hawaye suka kwaranyo kan ramammun kumatun ta
wayyo tana son duniya zata barta ruwa ya karewa dan kada tun
bai gama wanka ba, ta rasa meke mata dadi bata da da ko jika "yan uwanta ta guje su wanda suke kaunarta sun biyo ta don
maida ita gida ta yi musu wulakanci, ta kunna VCD dake ajiyс
saman katuwar talabijin, wani shahararren Nigerian Film ya fara bayyana, idanuwanta kafe kan talabijin din amma bata san
abinda ke ciki ba duk da tana sha awar fim din, zuciyar ta tuni
ta tafi wani tunani daban, kashe VCD ta yi gami da daukar "yar Karamar radio "world reciever" ta kunna.
"INNA LIL.LAΠ WA IΝΝA ILAIHIR RAJI”UN"
Abinda ya fara dukan kunnuwan Jamila kenan, sannan mai
adduar ya ci gaba "ALLAI YA YIWA HONARAВІІ JATAU BALA RASUWA YAU DA ASUBA BAYAN FAMA
40
DA GAJERIYAR RASHINLAFIYA, KAFIN YA MUTU SHI
NE KANSILAN KAUYEN KATSALLAWA YA MUTU YA
BAR MATA GUDA BIYU DA "YA'YA GOMA, ALLAH
YA JI KANSHI DA RAHAMA, SANARWA DA....."Kafin
ya fadi sanarwar Jamila ta kwalla uwar kara "Wayyo
honarabul ya tafi saura ni, wayyo Allah na shiga uku na
Jalace." Jamila ta ci gaba da kuka da fadar maganganu a fili, sai
dai duk maganganun da take ba na neman gafarar lai fu flukan
da ta yi a baya, sambatunc a ciki har da zage-zage, turkashi.
har yanzu bata gama saduda ba.
a Kullum ciwon Hajara sai ci gaba yake sai a kwantar
tayar abinci ma sai an dura mata wani ta yi amansa wani ya
shige da kyar, allura kuwa kullum sai ta sha guda uku amma ba
sauki ciwon arme.
Tuni su Hajiya Ladi suka fara ſidda rai da ita ganin
kullum magani ake ciwo kuma sai gaba yake yi, ba abinda ke
damun su kamar rashin iya magana da kuma rashin cin abinci,
ruwa ma kansa wani lokaci in an bata amansa take yi, fitsari da
bayan gida duk anan take yi sai dai in ta yi a dauketa daga
wajen a kwashe kazantar a canza mata kayan da ta bata, ban da
Hajiya ladi mai tsabta ce gidan ba zai shigu ba gaba daya, duk
wanda ya shigo gidan don dubata sai ya zubar da hawaye
musamman in ka santa lokacin da tana budurwa mai hankali da
ladabi, duk wacce ta shigo don dubata tana jin abinda take fada
sai dai amsawar ce ba za ta iya ba, sai dai ki ga ta juya ido
saitin da mutum yake, tarin da take yi cikin yake dan motsawa
yanzu cikin ya daina motsi, sai dai ki ga bakinta ya dan bude
kadan alamun larin kenan.
"Iallai yarinyar nan ta ji jiki." Alhaji Sadi abokin Alhaji
Isa mahailin Hajara ya fada yana dubanta kwalla cike da
idanuwansa.
41
"Tana ma kan jin jiki Alhaji." Ya bashi amsa muryarsa
sanyaye shima kallon Hajarar yake cikin tausayi.
"Wai an kai ta asibiti kuwa?" Ya tambaya.
"A gida ake dubata." Alhaji ya bashi amsa. "Gida fa ka ce?"
"Eh, ai wacce ke dubata kwararriyar likita cc."
"ina ba zai yiwu ba akai ta asibiti kawai a duba lafiyarta."
"Ai gani na yi ita ma ma"aikaciyar asibiti cc."
"Ta auna ta ne ta ga abinda ke damunta."
"Aa, ta dai dubata tana yi mata allura."
"Ina ba zai yiwu ba, wannan ai shaci fadi ne, in ba auna
jininta aka yi ba ba za a tabbatar da abinda ke damunta ba."
"Wanne asibitin kake ganin zamu kaita?"
"Ba wani asibiti da suka kware wajen duba irin
wadannan cututtukan kamar asibitin Zana."
"Hajiya." Alhaji Isa ya kwala kira, ta biyo bayan kiran da
sauri.
"Maza shirya mu kai yarinyar nan asibitin zana."
"To." Ta amsa gami da juyawa cikin daki da gaggawa.
"To Alhaji ni zan koma Allah ya sawwake, zan kuma
bullo asibitin ko da gobe ne in Allah ya yarda."
"To Alhaji Sadi sai na ganka na gode."
Cikin kankanin lokaci Hajiya Ladi ta hada komai da
komai da mai kwanciya zai bukata don ta tabbatar kwanciya za
a bata.
***
Kwana biyun da ya yi a dakin Sumoli rigima da masifa
suka sa Isma"il ya koma shagon gidansu ya tare, iyayensa sun
dan yi masa fada kadan don gudun bacin zuciyarsa akan
rabuwa da lajara da ya yi don sun yaba da hankalinta.
Bayan kwana biyun da tarewar Isma"il gudawa mai karli
gami da tsananin ciwon kai suka addabeshi wani lokacin har da
42
ciwon ciki, mahaifiyar sa da taimakon kawayenta sun hada
masa duk wani magani da ya kamata amma ina duk minti daya
Isma"il sake birkicewa yake, kwana biyun da ya yi da tasowar
ciwon zaka dauka shekaru biyar ya yi yana cutar.
"Hajiya wannan wace irin rashin lafiya ce ko dama bashi
da lafiya ne?"
"Lafiyar sa kalau wallahi Bilki, duka-duka kwanansa
biyu da farawa."
"To ai sai a gaggauta kaishi asibiti, don gudun halakarsa
kin san gudawa yadda take."
"Ai na dauka zan iya shawo kan cutar." To amma gashi
tana neman fin karfina."
"A gaskiya tafi karfin mu ma ba ke kaďai ba."
"Wane asibiti ya kamata in kaishi?"
"Ke ma kin san ba kamar asibitin zana."
"Haka yake, sun kware cikin minti goma sai su auna
mutum su fada mishi larurar da ke damunsa."
"Kwarai ma kuwa ai suna da wadatattun kayan aiki da
kwararrun likitoci."
"Bari in shirya in kai shi yanzu."
"Kin ga bari in baki dan notc akwai course mate dina a
wajen, kin ga kuna zuwa ba wani layi da zaki bi sai ki wuce
kawai."
"Da kin kyauta min."
"Ai zaman taren kenan." Ta fada daidai lokacin da ta
yagi wata farar takarda dake cikin wani dan karamin koren
littafi, ta dan yi wani gajeren watsattsale ta mikawa mahailiyar
Isma"il.
"Na gode." Ta fada yayin da ta karba.
"Ba komai Najeriya ce haka."
Suka yi sallama don rabuwa da juna, mahaifiyar Isma "il
la gaggauta hada kayan da mai kwanciya zai nema ta tabbatar
43
yadda yanayin Isma"il yake sai an ba su kwanciya.
Ramewar da Jamila ta yi lokaci guda ya sa karuwan da
ke Sabon Gari suka fahimci halin da take ciki, ta lura duk inda
ta siga yanzu kowa gudunta yake yi, kamar yadda aka saba yi
mata kirari haka aka juya yi mata habaici da shaguße gami da
dan kira, wani sabon suna da suke kiranta dashi wai LEDA ta
kasa ganc ma anar sunan, daga ta zo wuri sai kowa ya
tarwatse, abin yana bata mamaki ita da kowa ke rubibinta duk
da ta san kaya yanzu basa yi mata kyau saboda yawan da suka
yi mata bata yin munin da kowa zai rika gudunta ba.
Tuni ta sa gidajenta kwaya biyu a kasuwa, "yan
sarkokinta ma tuni ta karbi kudinta ta kulle, ta tabbatar zaman
garin na yanzu ya gagareta, don ta saba duk inda ta shiga a
dinga yi mata kirari tana wulakanta mutane, yanzu kuwa duk
inda ta shiga dan kira ake yi mata.
"Salamu alaikum." Malam Yakubu dillali ya fada gami
da lekawa cikin gidan, wata leda mai layi-layi a hannunsa.
"Salamu alaikum masu gida." Ya kara fada, sai dai
wannan karon ya daga murya fiye da sallamar farko.
"Shigo mana." Amsa sallamar Jamila kenan a koda
yaushe.
"To Hajiya." Malam Yakubu ya amsa, gami da shiga
cikin gidan, ya dan tsaya a kofar dakin.
"Shigo mana" Ta kara fada cikin isa, da alamun har
yanzu bata saduda ba.
"Yawwa." Malam Yakubu ya fada daidai lokacin da ya
zauna bisa lallausar kujera gami da kallon Jamila. Kallo daya
ya yi mata ya san cutar nan dake yawo cikin "yan bariki ita ta
kamata, shekaranjiya ma dan zuwan dare ya yi shi ya sa bai
gane ta ba, bulu-bulu kurajen da suka fito mata su suka
tabbatar masa da hakan don haka makocinsa y ayi, daga karshe
44
ya fara zagwanyewa.
"An sai da gidajen?" Jamila ta tambaya ganin irin kallon
da dillalin ke mata.
An sayar sai dai duka biyun dubu dari biyu da hamsin
muka karba da kyar." Ya fada gami da addu"ar Allah sa ta
amince a zuciyar sa, don gida daya ya sayar dubu dari uku da
hamsin dayan kuwa ya foyc takardunsa, dama tunda Jamila ta
sai gidajen sau daya ta taba zuwa ko kudin haya da sauran
aikace-aikace shi ke yi.
"Kai Malam Yakubu, nawa na sai gidajen?"
"Kin san yanzu Hajiya komai mutum ya saya yanzu in
dai zai sayar sai ya yi asara." Ya fada.gami da ci gaba da
addu ar Allah ya sa ta amince.
"Ammai kai ka ce min na sai gida ba a faduwa."
"E to abinda Allah ya kaddara ba yadda za a yi, sannan
ba kudi a hannun jama"a shi ya kawo haka."
"Amma ya kamata ace ko kudin dana saya a mayar min."
"Na yi kokarin hakan, kin san so ba samu ba, ko a mayar
musu da kudin?" Ya fada gami da tambayar karfin hali.
"Aa kawo su nan." Ta fada gami da mika ramammen
hannunta, awarwarayen da ke hannun suka biyo tsintsiyar
hannun zasu zube ta sa daya hannun ta dafe su gami da karbar
kudin lokaci guda.
Cikin kula ya mika mata kudin don gudun kar ya taba
hannun ta don ya ji wasu na cewa wai ana daukar cutar ta
musabiha, numfashi ma sama-sama ya ke ja a dakin.
A hankali Jamila ta kirga kudin dubu dari biyu da
hamsin ne cif cif.
"Sun cika." Ta fada bayan gama Kirga kudin.
"Ai dama sai da na bisu sosai." Ya fada yana kallon
kudin da alama yana son ta kara masa wanı abu, kun ji rashin
imani da rashin tausayi, irin na dillalai.
45
"Shi kenan ko?" Jamila ta tambaya ganin irin kallon da
Malam Yakubu ke wa kudin.
"Kin san dillalan da suka yi cinikin suna da yawa sun dai
wakiltani ne na karbo musu la"adarsu, kin san nafi kowa kusa
dake cikinsu."Ya fada yana murmushin farin ciki.
"Nawa nc la"adar?" Jamila ta ſada a kage, babban
burinta ta ga ta kama hanyar garinsu.
"Dubu hamsin ma kawai ya isa." Ya fada gami da yake
hakoran da goro ya yiwa illa.
Ba ta yi musu ba ta kirga dubu hamsin daga cikin kudin
ta mika masa, ya karba da sauri don gudun giftawar tsautsayi,
garin banza a farau-farau din banza yake karewa ga gida guda
ya samu ga kuma dubu dari da hamsin ya tashi da su, ban da
kudin hayar da ya dinga karba a baya da karin kudin hayar da
ya yi duk ya hada ya turmushe. Abinda Malam Yakubu dillali
ya manta akwai ranar sakamako ranar da kowa da kowa zai
gaban Rabbil Izzati talaka, mai kudi, basarake, mai mulki,
komai mulkinka sai ka yi wa Allah bayani, haka komai sarautar
ka sai ka fadi yadda mulkin ka ya tali. duk kwangilar da kayı
komai kankantar ta sai ka yi bayani, kuma ko Naira daya ka
ciwa 'yan tsangayar ka duka sai sun taru a gabanka don neman
hakkin su, tirkashi ni ban san kowa ba tambayoyin dake kan
kansilan tsangayar mu suna da yawa.
"Jeka mana ba na biya komai ba, ko akwai bashi ne?"
"Ba wani bashi na gode sai wani jikon"
Ba ta kara yin magana ba don abinda ya dame ta yana da
yawa, yana fita ta fara hada "yan kayan da ta ke tunanin suna
da mahimmanci.
Daya bayan daya ta dinga sa komatsanta a cikin but din
motar sai da ya cika dai-dai rufewa sannan ta rufe ta kulle but
din, sauran kayan da suka rage ta zubasu a bayan motar, bata
taba kafet da labulayen dakin ba, katon hoton marigayi
46
Honorabul ma nan ta barshi don bataga amfanin tafiya dashi
ba,
Cikin rashin karfin jiki ta bude motar bayan gama hada
kayan ta buda dash-bod na motar ta zuba kudin da mallan
yakubu dillali ya bata, duk inda magani yake sai ta nemo shi
abinda ta tabbatarwa kanta kenan farko ma batayi zaton ciwon
zai mata yankan kauna da wuri ba da tuni ta nemi maganin ko
aina yake, yadda ba tayiwa kowa sallama ba lokacin da tazo
haka yanzu bata gayawa kowa tafiyar ta ba, ta kalli gidan
kallon karshe kudin shekara biyar wani ciyaman ya biya mata
taci shekara daya da rabi sauran shekaru uku da rabi, ka na dai
shekaru nawa suka rage basu dami Jamila ba, ita dai ta dangana
da kyan su, duk da bata da lafiya ta san duk 'yan matan
kyawawa ne, ba mai arzikin ta ko suturar ta balle mota, abinda
Jamila ta manta shine zaman lafiya yafi zama dan sarki, sannu
a hankali ta tarar da motar kauye ta diba.
***
Sun iso asibitin da wuri amma cunkoso da layi na masu
cututtuka iri-ir shi ya hanasu ganin likita da wuri, Hajara zauna
take bisa bancin da aka tanada don zaman masu jinya, ta jin
gina da jikin bango, hannun ta na hagů tokance da bencin da
take zaune a kai duk tayi hakane saboda rashin karfin dake
jikin ta, lokacin da suka futo daga mota ma kama-kama aka yi
mata aka kawo ta nan inda take yanzu saboda kafafuwan ta
basu iya daukar ta.
Alhaji Isa mahaifin Hajara na zaune karkashin wata
bishiyar mangwaro dake farfajiyar asibitin, tagumi ya yi da
hannun hagun sa yana tunanin irin rashin lafiyar da hajara ke
fama da ita, wacce sun rasa kanta kullun sai ramewa takeyi, ga
magani anayi amma a banza kamar cutar ake dada izawa, shi
kan ya gama fidda rai da ita, kwana biyu kafin su ka wota
asibiti sau hudu tana suma a rana guda.
47
Karar tsohuwar tasin da ta shigo harabar asibitin ita ta
dawo da Alhaji isa daga duniyar tunanin da ya shiga.
Motar tayi fakin kusa dashi, itama dauke takc da wata
mata rike da wani saurayi kamar yadda Alhaji ya gani.
Bai gane taba sau lokacin da ta fito daga motar take
kokarin fito da saurayi.
Mahaifiyar Isma'il da ya auri 'yarsa ce.hakika, ganin
hakan ne yasa Alhaji isa ya sake maida hankalisa ga motar
yayin da ya lura saurayin da matar ke rike dashi Isma"il ne.
"Gakiya Hajiya da na san zaiyi min guduwa a motar
bazan dauke shiba" Dan tasin ya fada gamin an fito da Isma"il
da jikakken wando hakan ne ya sashi duba kujerar baya yaga
irin bamar da ta faru.
"Yi hakuri rashin lafiya nakan kowa" mahaifiyar isma"il
ta bashi amsa.
"Na san da haka nawa zaku biya ni? nawa zan
bada,wankin motar komai ai lissafi akc"
"To bari na kara maka nera dari akan tsadar da mukayi
da kai" ta fada gami da irgo dari biyar ta bashi dai-dai lokacin
da Alhaji isa ya karaso wajen.
"Sannu Hajiya." Alhaji Isa ya fada.
"Yawwa hajiya ta amsa gami da waigowa, Isma'il rike a
hannun ta.
"Au Alhaji ne" Ta fada lokacin da ta gare shi. gami da
jin kunyar abinda Isma'il ya tarka na sakin Hajara.
"Mc ke damun sa ne?" Alhaji ya tambayi yana kallon sa
cikin tansayi
"Wallahi kwana biyu gudawa mai karli da zazzafan
zazzabi gami da ciwon kai suka rufe shi"
"Ashsha Allah ya saukaka"
"Ameen na gode" Ta fada gami da kama kafadar Isma'il
ta yi ciki dashi,
48
Suna isa cikin suka iska dogon layi Hajiya ta jinginar da
Isma'il a gefe guda, ta laluba cikin jhakar ta ta dauko 'yar
guntuwar takardar da kawar tata bata, kai tsayi ta shi ga ofishin
da ake bada umarnin gwada mutum.
Tun lokacin da suka shigo wajen Isma'il ya lura da
Hajara, bai yi mamaki ba tunda ya san irin tarin da take dashi
wanda shima tarrin ya guda ya ce ta tafi gida. Bai kuma yi
mamakin gamin ramar da tayi ba don yasan ciwon tari dama
haka yake.
Hajara ce wacce ya ya kama ta a kira, amma "yan
guntuwar takardar da mahaifiyar isma"il ta shigo da ita da
kuma gamin cewa malamar asibiti ce ita ma, aka tsallake
Hajara aka shiga da isma"il wajen gwaji, dai-dai lokacin da
Alhaji isa ya shigo farfajiyar a gaban sa aka shiga da Isma'il.
Hajiya Ladi mahaifiyar Hajara ta gane Isma'il da
mahaifiyar sa amma ko kallon ba su isheta ba.
"Kin gane su kuwa?" Alhaji isa ya tambaye ta da ya lura
basu gaisa ba.
"Na gane ta mana menene?" Hajiya ta fada a zafafe.
"Ai ya kamata ku gaisa ki yi mata, Allah ya bada sauki
ko baki ga a hațin da Isma'il din yakc ba?"
"Gwara shi yana tashi, ita me ya hana ta yi min, Allah
sawake?"
"Ba mamaki ba ta gane ki ba"
"In bata ganeni ba, ba ta gane Hajara ba?"
"komai hakuri ake, abinda ya faru ya riga ya faru"
Banza kawai tayi dashi ta maida hankalin ta ga kallon
Hajara ita a gamin ta Alhajin bai damu da halin da yarinyar
take ciki ba.
An dauki tsawon minti arba in ana gweje-gweje kan
isma"il, Hajiya mahaifiyar sa na zaune a dan karamin dakin da
shi ake ftara shiga kafin wejen gwajin, suna hira da wasu ma"ai
49
kata.
Likitan ya dubi Isma'il bayan gane gwajin gami da yin
tsaki, ya fara rubuta a wata doguwar takarda cikin saurin hannu
da kwarewa.
"Me ke tsakamin ka da matar da ta kawoka?" likitan ya
tambayi Isma'il
"Mahaifiya ta ce" ya bashi amsa
"Hajiya bisimillah" daya likitan dake tsaye ya leka ya
kira mahaifiyar isma"il ganin likitan ya kara rubutan da yake.
"Kai fita daga waje"likitan ya umarci Isma'il mahaifiyar
Isma'il ta zauna a kujerar da Isma'il ya tashi.
"Hajiya" likitan ya kira sunan ta gami da mika mata rizol
din da suka samu na isma"il, kiran da yayi mata ne ya hanata
duba takardar.
"Na"am dakta"
"Nayi farin ciki da ya kasance ke ma aikaciyar lafiyace
saboda haka duk abinda ya kamata kiyiwa yaronki na dangane
da shawarwari da kuma magunguna.'
"Dokta ni bangane dogon bayanin da kake min ba" ta
fada a fusace gamin cewa ita ma aikinta kenan a turanin ta tun
kafin likitan yazo duniya take aikin.
"Danki na dauke da kwayoyin cutar AIDS. ku....."
"Me kake nufi daga fara gudawa kwana biyu ka cc yana
da AIDS" ta fada a fusacc.
"Abinda sakamakon ya nuna kenan"
Bata bashi amsa ba kallon takadar dakc hannunta
kama yi, sannan kuka mai karfi da kururuwa suka biyo baya.
"Haba Hajiya sai kace ba ma'aikaciyar lafiya ba.'?"
ta
"Wayyo Allah na shiga uku wannan da ya cuce ni ya
bata min suna wayyo" Ta yi waje da gudu, sukayi kicibis da
Isma'il don shima ya taso don jin kukan ta da ya yi, waje suka
yi tare tana kuka, yana fita waje ya fadi dai-dai kusa da bencin
50
dassu Hajara suke, mahaifin Hajara ya so rike shi amma kafiu
ya tare shi tuni ya kai kasa.
"Wayyo allah na shiga uku wannan da ya janyo mana
masifa" mahaifinyar sa ce tacigaba da kuka da maganganu.
"Lafiya Hajiya?" Mahaifin Hajara ya tambaya.
"Ina fa lafiya wayyo Allah na, wannan shegiyar cutar da
ba warkewa ya debo." Bata san lokacin da ta fada ba.
"Wacce irin cuta kuma?" Ya tambaya a firgice, lokacin
itama mahaifiyar Hajara ta maida hankalinta wajensu.
"Kanjamau." Ta kara bashi amsa ba cikin hayyacinta ba.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji"un." Alhaji Isa ya fada,
gumi ya rufe fuskarsa lokaci guda, don ya tabbatar "yar sa ma
ta kamu, tuni hawaye sun cika fuskar mahaifiyar Hajara, ita
kuwa Hajara bata san me ke faruwa ba. Mahaifyar Isma"il
kuwa kururuwa da birgima ta ci gaba da yi har mutane ke rike
ta kamar mahaukaciya.
"Hajiya." Alhaji Isa ya kira sunan Hajiya Ladi bayan
gama goge gumi da ya yi..
"Na"am." Ta amsa tana goge hawaye har yanzu idonta
kafe yake kan 'yar tata.
"Abin da za a yi mu koma da yarinyar nan ba sai an
gwada ta ba, mun sami amsar abinda ke damun ta tunda an
gwada mijinta."
"Haba Alhaji a bari a gwada ta mana ko..."
"Ke ban son maganar banza ki dauko ta kawai mu tafi."
"To." Ta amsa gami da kuka mai tsanani, ta mike ta
tattaro Hajara daidai lokacin da Isma'il ya fara wata gudawa
mai doyi da ta game wajen da wari gaa daya.
KASH!
MASU KARATU MU HADU A MAZA SAI SANNU
NA UKU DON JIN KARASHEN LABARIN.
SHIN
51
*HAJARA TA KAMU?
*ISMA'II ZAI SAMI SAUKIN CUTAR ALAKAKAI
DA YA KWASAА.
*YA RAYUWAR JAMILA KALA ZATA KASANCE
AARIN SU? KO TANA SAMUN SAUKI?
Taku
BEENTA WALEE
('Yar Autan Marubuta)
Daga MAZA SAI SANNU NA UKU
"Al'amin ka san caca?' Sani abokin Al'amin ya tambaya.
"Kwarai ma kuwa ba wacce ake sa kudi ba."Al'amin ya
amsa masa.
"To kai taka cacar tarai zaka yi."
"Ban fahimceka ba."
"Matar da aka ce AIDS ce ta kashe mijinta kai kuma ka
ke shirin komawa."
"Kana da yakinin ta dau cutar ne?"
"Kai ka tabbatar cewa bata dauka ba? Wannan ita ake
kira da shahadar kuda, in ban da ma rashin zuciya tun tana
budurwa ta ki ka ta so wani dan iska amma wai yanzu ka ce
wai zaka koma, kana saurayi tana bazawara mara lafiya."
"Ka san an ce da gwadawa jirgin sama ya tashi.
"Haka ka ce, to bari in fada maka wallahi idan cuta ta
kamaka kar ka yi tunanin zaka gan ni wajen dubiya."
Taku
Beenta Walee
Shi ma yans na firowa bs de dadews bs
GODIYA DA YABO NA MUSAMMAN
GA ALLAП (SWT) TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU
ТАВВАTA GA SHUGABAN HALITTA ANNABI
MUHAMMADU (SAW)
52
DANBORNO BOOKSHOP
RUMFA MAI LAMBA 145, LAYIN MABU LITIATRARAN HAUEA
LAY NÀ HUBU, KOFAR GADAH "YAN KURA, KABUWAR SYGARI, KANE
08028811674
Sai Wataranе
Ayuba Isycku Danzaki
TSARIN BANG0:
ANKA-G RAPHICS FAGGE
AUBINS PUBLISHERS, KURNA
OBOZ8611674
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau