sauki a dawo dake don
ni lafiyar ki na aura."
"Don Allah Isma'il ka rufa.... kuf...kuf...kuf min asiri
ka ji tausayina ka taimakeni wayyo Allah! Na shiga uku...."
Kuka mai karli gami da tari mai nauyi suka hanata karashe
21
rokon da take.
Isma"il ji ya yi kamar zugashi aka yi, wani sabon rashin
tausayi ya fado zuciyarsa, wani bakin faifan shaidan mai hana
mutum tunanin kyakkyawan abu da aka yi masa a baya ya
lullube kwakwalwar sa.
"Ke jimana ki tafi gidanku kawai." Ya umarceta bayan
tuna dadi da Jamila kala ke jiyar da shi.
"Yanzu Isma"il haka zaka yi min?" cikin Ta tambaya
kukan bakin cikin bijirewa mahaifanta da ta yi, maganganun
mahaifinta suka dinga karantowa a zuciyarta kamar yanzu ya
fadesu.
"Babu wani zabi da za ki kara yi Hajara?" Tambayar
mahailinta.
biyu.
"IHajara zabin da muka yi miki bai yi ba?" Tambaya ta
" Hajara." Ya ci gaba "Zamu amince da duk wanda kika
kawo min a matsayin mijin da za ki aura don gudun fadawarki
wani mawuyacin hali, sai dai abu guda da nake son tabbatar
miki shi ne duk halin da kika tsinci kanki a dangane da zaman
rayuwar aurenku da Isma'il kar ki zargi kowa sai kanki, ina
fatan kin fahimta?"
Lallai kam yanzu ba wanda zata zarga sai kanta, abin
kunya, yanzu in ta koma mai zata ce da iyayenta, da wanne
idon zasu kalleta ita da wanne idon zata kalle su? Tambayar da
ta yiwa kanta a zuci wacce ta san bata da amsar ta.
"Ki hada yanaki yanaki ki tafi sai na nemeki." Ya katse
dogon tunanin.
"Ban fahimce ka ba?" Ta tambaya.
"Abubuwan da kika san zaki nema a gida yayin jinyar
rashin laliyar taki." Ya fada da kakkausar murya, burinsa ta
hada yanata yanata ya huta da dawowa gida da safe, sai ya tare
a dakin Jamila kawai.
22
"To na ji." Ta fada ganin cewa da gaske yake. "Kuf....kuf.... kuf.....kuf." Tari mai karfi ya kara turnuke ta hawaye suka kwaranyo ta ramammun kumatunta.
"Fara harhadawa mana tun ina nan." Ya fadi haka don gudun kada ya fita ta ki hadawa.
Tashi ta yi ta fara hada abubuwan da ta san zata yi amfani da su kamar yadda ya shawarceta, shi kallo ne kawai na
sa cikin zakuwa da farin cikin zai rabu da kaya, mhm mai
karatu namiji kenan.
"Wai Isma"il da gaske kake?" Ta tambaya da gaggawa
don gudun kada tari ya hanata.
"Bari ki gani." Ya nufi kwabar kai tsaye ya bude gami da fara turo kayan sawarta tsakar dakin.
***
Jamila Kala zaune take ita kadai a dakinta, taba sigari
rike a hannunta na dama, ita kanta ta tabbatar yanzu ta fara
ramewa a yadda ta gani a madubi, hakan na da nasaba da
yawan gudawar da take, abin da ta kara la"akari da shi yawan
cututtuka marasa jin magani sai damunta suke kara yi, kuma
duk ciwon da ya kamata bai sakinta.
A zuciyarta ta gama yanke shawarar korar su Isma"il da
Alhaji Lawan ta tabbatar yanzu duk jininsu ya gama zagayewa da cutar alakakai, kuma ta tabbatar yanzu matansu da duk wanda suke muamala da su sun gama kamuwa, sai dai a
tunaninta ya kamata t'sanar da su don su yi fargaba ta tashin
hankali gami da kunan zuciyar da ke damunta kullum ko wane
minti ko wane kiftawar sakon din agogo suma ya dinga damunsu, sai dai inda gizo ke sakar ba ta san ta inda zata bullo
musu ba, ta saka wancan ta saka wannan wata dabara ta fado
mata ta d'an yake hakora abinda ta kira dariya duk da tunda aka
fada mata rizol dinta bata taba farin ciki ba daidai da rana daya.
23
***
"Shi ne ya ce ki taho gida?" Hajiya Ladi ta tambayi
Hajara dakc tsaye da kunshin kaya a hannunta. "Eh....kuf...kuf..." Ta fada gami da yin dan tari. "To kuma me ye na kukan?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
"Ya baki takardarki ko?" Hajiya ta tambaya.
"Cewa ya yi kawai na taho zai biyo baya na." Ta fada cikin sa ar da tari bai katseta ba.
"Wannan wacce irin magana ce ki taho gida ba takarda."
Shiru ta kara yi ta nufi wata "yar kujcra ta zauna saboda
rashin jin karfin jiki da take fama dashi.
"Bari Babanki ya dawo a san na yi, dubi yadda kika kara
lalacewa." Hajiya Ladi ta fada sannan ta ci gaba "Wai tarin me
kikc hakа?"
"Nima ban sani ba." Ta bata amsa a gajarce. Suna cikin
hirar Alhaji Isa ya shigo hannunsa rike da bakar leda.
"Lafiya." Ya tambaya gami da kallon Hajara irin duban
da ya yi mata dubana da uba kan yi wada yayin da aka hanashi
ya ki hanuwa, daga baya sakamako ya zama mummuna, la
wani bangaren kuma za ki iya lissafa shi a kallone na tausayi
da damuwa.
biyu.
"Ba tambayar ku nake yi ba?" Ya kara tambaya karo na
"Lafiya kalau cewa ya yi ta dawo gida." Hajiya Ladi ta
fada.
"Ko dai wani abun ta yi masa?" Ya tambaya don ya rasa
maganar yi shi kansa ya san ba wani abu ta yi masa ba.
"/an tura in ji." Ya fada a gajarce ganin Hajiya ta yi
masa shiru.
Hajiya Ladi ci gaba ta yi da ayyukan da tasa gaba ko
kallan Alhaji ba ta yi ba don haushi.
24
"Yanzu dan nan me ya sa baka son tsayawa ka ji
matsalolina kullum sai ka ce kana da uziri ko zaka shiga
mitin?" Mahaifiyar Alhaji Lawan ta tambayeshi cikin takaici
da bakin ciki.
"Ki dan jirani yanzu ma mitin din zani." Alhaji Lawan
ya fada ba tare da ya dubi sashin da mahaifiyarsa take ba.
"Kullum ai haka kake cewa dan nan." Mahaifiyar tasa ta
fa, gaba kawai ya yi bai bata amsa ba.
Ihaji yaron nan kyanda ke damunsa." Daya daga cikin
matansa tr fada daidai lokacin da ya zo kofar dakinta.
"Nemi ruwan kifi ki ba shi." Ya fada ba tare da ya kalli
yaron ba.
"Alhaji wannan kyandar tafi karfin ruwan kifi." Matar la
fada gami da dada nuna yaron Gangaren da Alhaji yake,
harshen yaron cабa-caba da kuraje kanana hakan yasa baya iya
cin abinci hancinsa cike yake da majina sai wani dan tari yake.
"In kika sa ya Gata min riga sai na yi bal daga ke har
shi." Ya fada gami da hararar yaron, yaron kamar ya san
abinda ke gudana ya fashe da kuka, kukan da murya bata fita,
zaka gane yana kuka ne in ka kalli yadda idonsa ke fidda
hawayc da yadda cikinsa yake sama yana kasa, haka Alhaji ya
wuce ko kallonsu bai kara yi ba.
"A dawo lafi a." Daya matar wacce daga ita sai kofar
fita ta fada.
"In dawo ir yaki." Alhaji ya maida mata da bakar
mila Kala ta amince da Alhaji ya tsani
ra sauraron ko daya daga cikin matan
ta daga ransa, hatta amaryar da ba ta fi
magana, tun rana
matansa tun rana
saba, ya yi du
sheka hudu da
kin min
sa a a ya isk
biyar ya sadashi da Burma Road, cikin
la ta yi kwalliya kamar shi take jira, sai
25
dai yanayin da ya ga fuskarta abin ba magana.
"Jamila lafiya na ganki cikin bacin rai?" Alhaji Lawan ya tambaya daidai lokacin da ya rufe kofar motarsa. "Lafiyar kenan." Ta bashi amsa agajarce.
"Ni kwanan nan na ga ramewa ki ke, me ke damunki."
"Kai ma taka na zuwa." T'a ſafa a ranta a fili kuma ta ce
"Ban jin dadin jiki na."
"To mu je asibiti mana." Ya bukata, tunanin dansa
Mustapha dake kyanda ya fado masa, nań da nan ya kauda
tunanin cikin sauri gami da cewa "Ko ba kya ji ne?"
"Ina jinka, na je asibiti tun watannin baya da suka wuce
sai dai in dauko maka takardar ka je a duba min abinda ke
damuna." Shawarar da ta yi kenan dazu don bata son gaya
masa da baki gara ya gani a takarda ko ya li tabbatarwa.
"Assha, assha, maza dauko min ko gidan ba zan shiga ba
sai na sayo magungunan, akwai likita na wajensa zani don
gudun sayo jabun magani," Ya fada lokaci guda tunanin
mahai fiyarsa ya fado masa "Mhn tsula sai hakuri." Ya fada a
fili gami da saurin kauda tunanin don yanzu Jamila ce a
gabansa.
Mintuna ųku ta sharc don binciko sakamakon da aka bata
a LAMCO LABORATORY, tana yin kicibis da takardar
gabanta ya ſadi irin faduwar da ya yi a farko, ta kalli takardar
sakon mutuwa gami da yin yake.
Har yanzu yana jingine jikin motar kamar yadda ta barshi.
"Yawwa kin samo takardar." Ya tambaya yana
murmushin zai kara samun fada a wurinta, lallai kwalli ya yi amfani.
"Na samo ta da kyau." Ta fada daidai lokacin da ta mika
masa takardar.
Bude mota ya yi yana karbar takardar zama ya yi gami
26
da tada motar lokaci guda ya sa giya lamba daya ya nufi
unguwar Bachirawa inda likitansa yake.
Bin sa kawai ta yi da kallo har ya bace mata da gani.
"Sai ki hakura haka." Isma"il dake bayanta ya fada a
kishance, tun dade wa yake wajen, ganin zuwan Alhaji Lawan
shi ya hanashi karasowa.
"Honey barka da zuwa." Ta fada tana murmushi, mage
kenan mai kwanciyar dfaukar rai.
"Ga honey dinki can yi tafi."
"Kai me yasa baka rabo da fushi, me zan yi da wancan
tsohon."
"Hausawa sun ce da tsohuwar zuma ake magani."
"Ni wannan ba tsohuwar zuma ne a wajena ba."
"Ke yanzu fa na kora matata gida:"
"Haba honey saki nawa ka yi mata."
"Ban saketa ba tukunna, ji na yi tana wani tari."
"To ai honey kamata ya yi ka sakcta ka zo nan mu tare
kawai."
"Allah Jamila?!"
"Allah kuwa honey." Ta fadi haka ne da zummar idan ya
saketa zata yi aure mijin da ta aura shima ta sa ta kare idan mai
mata ne ta aura an dada samun wasu gawarwakin kenan.
"Saki nawa ya kamata na yi mata?"
"Saki nawa ne kat?"
"Saki uku."
"Abinda ya kamata ka yi mata kenan, mu huta."
Isma"il ya dan yi jim yana tunanin Hajara da irin
hakurinta da sadaukar da kai ga miji da dauke kai a kan abin
hannunta.
"Mu je akwai takarda da biro a dakina." Ta katse tunanin
da yake.
Ta rike hannunsa na dama suka shiga gidan kai tsaya,
27
yana shiga dakin ya cire doguwar rigar dake jikinsa ya yar
gefen katifa, Jamila kuma ta bude wata "yar roba ta dauko
takarda da jan biro.
"Ka san da jan biro ake saki." Jamila ta fada daidai
lokacin da ta miko masa.
Bai yi magana ba cikin sanyin hannu kamar ba ya so ya
fara rubuta takardar..
"Yi maza mana sai ka ce rubutun dan koyo."
Ya dan kara sauri.
"Na gama." Ya fada gami da mikawa Jamila takardar
don karantawa.
"Yanzu ya za a yi takardar ta sameta?"
"Kin san yadda za a yi?"
"Sai ka fada."
"Dan acaba zamu samu a majalisar "yan acaba can da
suke zama gindin darbejiya na san ba za a rasa dan Gwammaja
ba, gidansu bashi da wahalar kwatance, sai a bashi takardar ya
mika gidan."
Hakan kuwa suka yi bai sha wahala wajen yiwa đan
acabar kwatance ba.
: "Na san yarinyar ba kanwar Ali ba." Dan acabar ya fada.
"Yawwa dan gari, ga wannan takardar ka kaiwa Hajara
ka ce in ji ni." Ya fada yana yake, Jamila tdauki naira dari ta
mikawa dan acafar don ya yi saurin kai takardar.
***
"Likita bokan turai." Alhaji Lawan ya fada daidai
lokacin da yake shirin zama kan kujera dake fuskantar Dokta
Umar Yahuza dan kimanin shekaru ashirin da tara sun dade da
Alhaji Lawan shi ke duba lafiyar sa da ta karuwan da yake
nema, abinda ke daurewa Dakta Umar kai Alhaji Lawan bai
taba kawo matarsa ko dansa ko wani dan uwansa ba duk waccе
Alhajin ke kawo wa a duba za ki ga matan banza ne kai har
28
"yan daudu ya sha kawowa a duba irin wadanda ke masu
kawalci.
"Alhaji kenan, kwana da yawa." Dokta Umar ya fada
bayan gama nazarin wata "yar guntuwar takarda.
"Lafiya kalau, in ka ga mutum a wajenka ai ba lafiya."
"Ina fatan dai ba kai bane?"
"Eh, bani bane wata yarinya ce."
Abinda Umar ya tabbatar zai ji kenan kullum wata
yarinya.
Ya dan yi murmushi daidai lokacin da Alhajin ya mika
masa takardar.
Ya ajiyc takardar gabansa suka ci gaba da hira.
"Kwanaki aka ce min ka tafi kwas?" Alhaji ya tambaya.
"Kwarai kuwa ai na wata uku ne."
"Ashe ka sami karin girma?"
"Ka san karin girma ya danganta da gatanka."
"Haka yake."
Kiran sallah da ladanin masallacin dake harabar kilinik
din ya yi shi ya katse Dokta Umar hirar da suke.
"Lokacin sallah ya yi." Dokta ya fada.
"Ka duba min takardar mana." Ya fada a zake.
"A"a sai na yi sallah tukunna, ko a debo maka ruwan
alwala?"
"Bar shi in naje gida na yi."
Amsar da ya saba bashi kenan kullum in sallah ta ritsa
dashi a wajensa, abinda ke daurewa Dokta kai.
Minti wajen arba"in suka dauka wajen yin sallar Azahar
hakan na da nasaba da limamin irin wadanda ke kiran kansu
Ahlussuna ne. kowa da yake sunfi kowa tsaida salla da yin
salla cikin nutsuwa
"Assalamu alaikum." Dakta ya fada lokacin da zai shiga
ofis bayan gama sallar, carbi a hannunsa na dama yana ja gami
29
da motsa baki.
"Amin." Alhaji Lawan ya amsa.
Ya fara duba takardar bayan shafa fatihar da ya yi ya cire
farin gilas din dake fuskarsa ya kara duba takardar.
"What?!" Dokta ya tambayi kansa gami da daga wa ya
kalli Alhajin.
"Kar ka damu da tsadar maganin." Alhaji Lawan ya fada
cikin isa.
"Ka san abinda ke rubuce a takardar nan kuwa?" Dokte
ya tambaya gami da mikawa Alhajin takardar.
"Ka san da da ajami aka rubuta ba sai na kawo maka ba.
boko ne rubuce a jiki, ka san bangaren rubutun boko ni da
makaho bambancin mu kadan ne."
Ya sake karfar takardar lokaci guda ya maida dan farin
gilas din da ya cire da farko.
Kurawa takardar ido ya sake yi ba ko kiftawa.
"Alhaji wa ke da takardar nan?" Ya tambaya gami da
addu"ar Allah ya sa ba karuwar Alhajin ke da ita ba don yana
samun kudi da Alhajin ba zai so mutuwarsa yanzu ba.
"Na gaya ma tun farko ta wata yarinya ce." Alhajin ya
fada a zake gami da jin haushin kwane-kwane da likitan ke
neman yi masa don bai yi karatun boko ba.
"Ko ciki ne da ita." Ya kara tambaya a gaggaucе.
"Ba daya." Dokta Umar ya bashi gajeriyar amsa ba tare
da ya dubeshi ba takardar kawai yake nazari.
"Shawara? ce don ba ta rabo da kayan maiko da zaki."
"Ba daya." Abinda ya kara fitowa daga bakin Dokta
kenan.
"Kai Dokta ka fada min, ban son juya-juyar da kake
min."
"Alhaji yarinyar dake da wannan takardar tana dauke da
kwayoyin cutar kanjamau, sama da wata biyu."
30
Tun da dakta ke aiki bai taba ganin wanda gurni ya fara
tsattsafowa daga kumatu ba sai Alhaji Lawan, hakan ne ya sa
ya kee zargin lallai yarinyar karuwar Alhaji Lawan cе.
"Me ka ke nufi da cutar kanjamau, yarinyar fa kalau
take, duk "yan matan Sabon Gari ba wacce ta kaita ta shiga mai
kyau."
"Ko ita cc sarauniyar kyau in dai. ita ce mai wannan
takardar to kwayoyin cutar na nan dankare a jikinta sama da
wata biyu." Dokta ya fada gami da nazarin yanayin da Alhajin
ke ciki, duk ya canza kamar ba shi ke tsawar a fada masa
abinda ke jikin takarda ba, ga mamakin Dokta sai ya ga hawaye
ya fara kwaranyowa Alhaji Lawan kamar a wasan kwaikwayo.
"Alhaji me ke faruwa?"
"Dokta na shiga uku na lalace, wayyo duniya."
"Alhaji kar ka damu in dai ba ka sadu da yarinyar ba a
"yan kwanakin nan."
"Jiya ma muna tare, shekaranjiya ma muna tare." Yanzu
ni ya zan yi da raina, ina ji ina gani zan mutu kwanana bai kare
ba wayyo." Kuka ya biyo bayan maganarsa.
"Akwai magunguna da za a baka in ka kiyaye, zaka dade
a duniya."
"Kayya Dokta, kawai tawa ta zo karshe, wannan yarinyar
Allah ya tsine mata, sai n ayi maganinta shegiya macuciya..."
"Alhaji zage-zage ba naka bane, ka kwantar da
hankalinka ba zaka mutu ba..."
"Haba Dokta ba wani dadin baki da zaka yi min akwai
abokaina da wannan tsinannen ciwo ya rutsa da su, ba su kai
labari ba."
"Abinda za ka yi ka je ofishin SWAAN dake INARoad akwai shawarwari da zasu baka, za su taimakeka,
matuka."
"Kayya Dokta, ba wata shawara, ni tawa ta kare duk
31
abinda na tara bani zan ci ba, ba sadaka ba zakka ba kyauta ko
alheri, "yan uwana, "ya"yana, makota na duk ba su ji dadina ba gashi yanzu Dakta zan tafi,"
"Ba zaka tafi ba Alhaji da dan saura." Ya fada a
zuciyarsa, a fili kuma ya ce "Ka yi hakuri Alhaji komai na duniya dan kaddara ne."
Shiru Alhajin ya yi masa sun dauki kusan dakika ashirin
ba wanda ya cc da wani kala, abinda Dakta ya lura dashi
hawaye da gumi sun yi саба-саба а fuskar Alhajin ba ka isa
ware gumi ko hawaye ba.
"Ban takardar." Alhajin ya fada.
Mika masa takardar ya yi ba tare da ya ce masa kala ba.
Ya karbi takardar da hannun hagu ya tura a aljihun babbar rigar da ke sanye jikinsa.
Tashi ya yi ba sallama ya fita, Dokta bai yi masa magana ba, don ya san abinda ke damunsa ya fi kartin a dameshi da
magana, kamar mutum ne a ce masa saura kwana kaza ka mutu
dole ya damu, masana ilimin yau da gobe sun ce ba abinda ya fi dadi dadi kamar rashin sanar da mutum ranar mutuwarsa.
Haka ya hau titi ba dubawa, motoci guda biyu dake kan
titin suka taka birki kadan ya rage su bugawa juna, wani dan
acaba dake gefe ya gangara kasa.
"Allah ya isa." Dan acaban ya ſada.
Alhaji Lawan bai damu ba wanda ya kuna baya tsoron
kauri, shi babban burinsa ya isa gidan Jamila ya hallakata,
tunda ya sai bindigarsa bai taba aiki da ita ba sai yau da-yake
shirin aika Jamila Kala lahira, gosulan da ya tarar a Kurna
Babban layi ya yi matukar bata masa rai, gumi kawai kc dada
kwarara a fuskarsa, ga hayakin motoci ga "yan acaba sun
dameshi da karar hon. haka kawai ya ji kansa ya fara wani
matsanancin ciwo lol i guda, ya dan sa hannu ya dafe kan, a
hankali gosuln ya fiya cikin sa a ya sami waje ya kutsa
2
yafita, sakin motar ya kara yi kamar kibiya, daidai tirafik din
bariki wajen mai bada hannu cikin tsautsayi yara biyu masu sai
da pure-water suka isallako da gudu don kira da wani mutum
dake kan acaba ya yi musu don sayen ruwa, Alhaji Lawan bai
yi aune ba sai ganin yara ya yi a gabansa, bai yi kokarin taka
birki ba bi kawai ya yi ta kansu, don ya san taka birkin bashi da
wani amfani.
Mutanen dake gefe kowa rike kai ya yi ganin yadda
Alhaji ya yi faca-faca da kananan yaran dake neman abin da
zasu ci su da iyayensu, wasu kuka suka kama yi gami da salati,
yayin da kabilu suka kama ihu.
Ko damuwa bai yi ba ya ci gaba da tafiya ido rufe diadai
rawul din da zai kai mutum iyafot (airport) wanda yake kusa da
ofishin Ambassadon Nijar, wata babbar mota irin wadanda ake
wa mahukacin lodi zuwa Nijar ta yi kwanciyar magirbi duk
lodin ya tarwatse bisa titi, Alhaji Lawan ya ja wani mahaukacin
birki, karar birkin ta firgita mutanen dake gefen titin, wani
mutum dake rike da kura ya saki kurar ya nufi wala
wangamemiyar kwata kai tsaye ya fada ciki da tunaninsa nan
ne wajen da ya fi masa tsira, Alhaji Lawan ya dauke kan motar
kadan ya ragę ya shiga karkashin motar, gefe motar ta yi tą
nufi wajen wasu kyauraye dakc gefe, nan ma Alhaji Lawan ya
shawo kanta da kyar ta dawo kan hanya Alhaji Lawan ya yi
ajiyar zuciya, duk da ya san kwanaki kalilan suke rage masa
dole gabansa ya fadi, ci gaba ya yi da mahaukacin gudun da
yake yi ya kudirar niyar zuwa ya dan ranJamila.
Zungeru Road ya nufa kamar kibiya ko ina ya gifta sai
kallonsa mutane sukc kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Alhaji Lawan bai yi aune ba ya ga mota kirar Toyota
dankare da lodin rodi mace a kan hanya, Alhaji Lawan ya
lalubi burki kamar yadda ya yi a baya, ya ji kamar totur din ya
kara takawa, ya yi kokarin dauke kan motar ya ji shi a kulle
33
kara ya kwalla daidai lokacin daya tabbatar da ba makawa sai
ya hadu da motar, motar ta kutsa kai Karkashin akiro kurar
kamar gareji da aka tanda domin ta, rodikan dake cikin motar
suka fasa gilasan motar Alhajin tun daga kansa har zuwa ruwan
cikinsa ba inda rodi bai shiga, rodin ya yi masa irin yadda akewa tsire, ta kasa kuma kafafuwansa suka yi raga-raga
saboda lotsawa da gaban motar ya yi, wani tsoho dake cikin
lambunsa yana ban ruwan salad ya rugo da gudu don ganin
abinda ya faru, yana zuwa ya ga yadda rodi ya yi wa Alhaji, ya
rike kai gami da zaunawa lokaci guda saboda juwa da ta fara dibansa, bai dade da zama ba motar ta kama wuta lokaci guda. Karshen mai wulakanta iyaye da iyali kenan.
***
"Salamu alaikum." Dan acabar ya yi sallama a gidansu Hajara.
"Wa"alaikas salam." Hajiya Ladi ta amsa. "Wai gashi Isma"il ne ya ce a ba Hajara." "To an gode ina ka bar Isma"il?"
"A Sabon Gari."
"To je ka Allah ya kiyaye."
Lokacin da dan acabar ya kawo takardar Hajara kwance
take ko tashi bata iya yi, sai dai a kwantar a tayar. "Hajara! Hajara!! Tashi Isma"il ya aiko da sakon takarda ban san ko mai ke rubuce ba." Ta fada gami da tallabo kan Hajara, ta dauki filon dake kusa da kan Hajara ta jingina shi jikin bango sannan a hankali ta jingina Hajarar a jiki. Hajara ta dan bude idonta a hankali ta kalli wasikar dake hannun mahaifiyarta, ta sake rufe idonta tsawon dakika biyu
sannan ta kara budewa a karo na biyu, ta miko hannu don karbar takardar hannun na rawa kamar wacce aka kadawa gangi, Hajiya Ladi ta mika mata takardar, ta karba ganin da budewa lokaci guda.
34
NI ISMA'IL NA SAKEKI SAKI UKU, KI KUMA
GAGGAUTA KWASHE RAGOWAR TARKACEN
KAYANKI. DALILIN BAN IYA ZAMA DAKE KI GOGA MIN
TARIN SHIKA KO TARIN FUKA ВА.
SAI AN JIMA
DAGA LAIYAYYE NA JAMILA KALA
Tana gama karantawa hawaye suka kwaranyo mata ga
cuta ga saki, ta ki maganar iyayenta ta bi son zuciyar ta ta auri
jahili wanda bai san hagunsa ba barc damar sa, yanzu ga halin
da ya jefata.
"Me ke rubuce jikin takardar?" Hajiya Ladi ta tambaya.
Bata iya bata amsa ba sai dai takardar da ta mika mata.
Hajiya ta fara dubawa.
"To kuma me ye na kukan don kin rabu da kangi. "Вa
kukan rabuwa dashi nake ba, ina kukan saba muku da nayi ne"
"Ki sha kurumunki inda wannan ne ba komai" "Hajiya
ku yafemin nasan bazan dade a duniya ba mutuwa zanyi don
Allah ku......" kuka da tari suka hanata karashe maganar.
"Ki daina kuka mun yafe miki itama hajiya kukan take
tana rarrashin ta.
Tunanin Al'amin ya fado mata lokaci guda ta tuna irin
nasi hohin da ya dinga yi mata lokacin da ta nuna bata kaunar
sa, hakika da zata ganshi yanzu da ta bashi hakurin wulakancin
da tayi masashima kafin rai yayi halinsa, don ga yadda take jin
kirjinta na uzzura mata gami da ciwon jiki ko ina ga tari wanda
shima uwa uba ta tabbatar to amma cutar tata bata tashi bace.
"Sala mu alaiku" fumi dake yiwa Hajara allura gami da
magunguna ta shigo, hannun ta rike da wata yar farar jakar
leda.
"Yawwa, sannu da zawa fumi" Hajiya ladi ta amsa.
"Kukan me kuma kikeyi?" fumi ta tambaya tana kallon
35
Hajara cikin tausayi, don tasan Hajara tun tana karama, kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa amma yanzu ga yadda
ta koma, don gamuwa da sharrin Namiji, duniya kenan "kiyi hakuri in Sha Allahu zaki warke ki koma kamar yadda kike da."
"Allah yasa Fumi" Hajiya ta amsa da gaggawa.
fumi ta buda yar jakar dake hannun ta gami da ďakko
wata kwalbar allura da sirinji sanye cikin leda, ta yage ledar
sirinjin ta soka allurar saitin lallausar jar robar da ta yi wa
ruwan allurar dake cikin kwalba hijabi, lokacin guda ta ze
ruwan gami da tsartar da kadan daga cikin ruwan gefe guada, a
hankali sai da ruwan allurar ta zo dai-dai kan wata lamba dake
da zanen gado-gado da Hajiya Ladi ba ta fahimci ko mene ne
tsira allurar Hajara jikin ta, ta dan jawo allurar ta dubi ruwan
sannan ta kara tsira allura.
Hajara ta dan ya motsa baki kadan 'yar kwalla kadan ta fito mata.
"Sai kuma an jima" Fumi ta fada"
"Yawwa Fumi mun gode" Hajiya Ladi ta bata amsa
"A ba komai wallahi" Ta fada dai-dai lokacin da take
hada yan komatsen ta.
Dai dai lokacin da gumi ke shirya lita Alhaji ya shigo
"Ya ya likita" Alhaji ya fada.
"An yi allurar sai kuma an jina"
"Wai ya naga har yanzu jikin nata baya yake ci"
"kasan Alhaji komai sai sannan, kuma haka ciwon tari
yake bai cika jin magani ba"
"To Allah ya kyauta"
"Amin" Hajiya ladi da gumi suka amsa tare.
"Wacce takarda nake gani a hannunki da rubutun janbiro
sai kace sakon mutuwa?"
"Ba sakon mutuwa bane, takardar saki ce"
36
"Subhanallah saki a ina kuma?"
"A nan gidan"
"Ke ni bangane ba"
"Isma'il ne ya saki yarinyar nan"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma yaron nan bai
kyaua ba"
"Wacce irin rashin kyautawa kuma, ai haka akeso ya
sallame ta din don ta rabd da kwallon mangwaro ta huta da
kuda"
"Haba Hajiya ya ki ke magana kamar jahila, Allah
madaukakin sarki ya halatta saki, amma bayan so, kar ki yi
farin ciki duk lokacin da ki ka ji an ambaci saki"
"To Alhaji wannan dai ai ta kare"
"Ko ma wanne irin bai kamata ki nuna farinciki ba"
"Da halin kome ne ko kuwa?"
Tun da sukea da Alhaji bata taßa hararar sa ba sai yau,
shi kanshi abin ya bashi mamaki.
"Ko me?. Ta tambaya har yanzu hararar sa take
"Kwarai ma kuwa in sakin bai wuce biyu ba"
"Saki uku ne amm sani ba ko kana da malaman da
za su gyara maka"
"Subhanallahi
hankali yake"
"Alhaji wai me
masane ya karasa ta a h
"Kar ki dauki zafi
a