An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
PIAZA SAI SANNGBINTAA WALI
(Mirs Auwal G. Danborno)
MAZA SAI SANNU 2
S
un share kusan awa guda suna tafka masha"a da
Jamila kala. Lallai dole masu kudi da "yan siyasa su likcwa Jamila kala. Tsawon shekaru sha biyu da fara neman
matan Isma"il, ma"ana tun lokacin da ya balaga bai taßa nema
da wacce ta kai Jamila kala ba.
"Isma"il " Jamila kira sunan sa a hankali ga dukkan
alamu itama ta jigata.
Jamila" shima ya kira sunan ta daga kwancc.
"Ya kamata ka shirya ka tafi dare ya-farayi"
"a nan nakc son kwana"
: "A'a bai dace ba saboda iyalanka" ta fadi haka ne don
burinta ya gogawa matarsa alakakai.
"ban sha"awar zuwa gidan nan wallahi"
"Haba sweetheat gobe ma rana ce, bari in zuba ma ruwa
kayi wanka.
Karfe tara dai-dai Isma"il yasa kayansa bayan gama
wanka da yayi.
"Bari in fesa ma turare" Jamila ta fada tana murmushin
farin ciki samun abokin tafiya.
"Na gode ya fada dai-dai lokacin da ta gama fesa masa
turaren.
"Gobe fa da wuri zaka shigo Isma"il"
"Kamar karfe nawa?" ya tambaya yana murmushin
banza ta fadi
"Kamat karfe goma"
"Lokacin ina kasuwa"
Ka zo ba komai zan dauke nauyin ka.
"Ba komai sweety Allah ya kaimu.
Har wajc ta rako shi, ba ta koma gida ba sai da taga
bacewar marigayin, kamar yadda ta kira shi.
8
ya isa gida cikin farin ciki da annushuwa, sai dai abinda
ke ba Isma"il mamakin lokaci guda sha"awar Hajara ta fada
masa duk da cewasun gajiyar da juna shida Jamila kala.
gidan bude yake, sauran abokan hayarsa zaunc a kofar
gidan suna hirar matan makota.
"Sannunkiü ya ſada a gajarcc.
"Yawwa barka da zuwa suka amsa baki daya..
"Yau ma a abuge yake" Malan Lawan mijin ta Salla ya
fada bayan shigewar Isma il gida.
"Gashi Allah ya bashi kyakkyawar mace mai biyayya,
"haba Malam Musa baka ganin yanzu duk ta jema
saboda wahala da takeyi.
"laka yake Malama Lawan a da in dai mutum ya kalle ta
dole ya kyasa amma yanzu duk ta kode kamar wacce ta haifi
"ya ya ashirin.
"duk da haka da sauranta don yanzu in ka....."
"ina wuninku wata mata dake rike da yaro a hannu ta
fada dai-dai lokacin da zata gifta ta kusa da su.
"lafiya" suka amsa gaba daya.
"Mhm masu layya suke da kayan nama" Malam Lawan
ya fada.
"Tanko dai yayi dacen mata" a cewar Malam Sani.
"don ma Hijabi ta sa, amma da dan gajeren mayali tasa
da kaga sura" Malam Iawan ya fadi yana dariyar shakiyanci.
Amma bata kai matar Alhaji Yahaya ba?.
"A wannan ai karshe ce na ji ma ance ya saki uwar
gidan"
"Kai kuwa ai dole ya sake ta irin wannan daula da ya
sannu"
"Ba wannan ne yasa ya sake ta ba". Malam Musa Tada.
"Me yasa?
"Yawwa Malam Lawan kayi tambaya a wajen dan gari.
9
to bar gamin Alhaji Yahaya nada kudi gidan sa ba wadatar
binci kuma...
"Kai Musa kamar Alhaji Yahaya ace gidan sa ba abinci
zabga-zabgan yan "yammatan dake gidan sa kai kace ci dasu"
"Gaskiyar ka Malam Sani, baka sani ba dama auri saki ke
gareshi, duk wayan nan "yammatan da kake gani gidan
kowacce da uwar ta"
"Mc yasa har yanzu ba"ayi masu aure bane"
"Wai karatu suke" a cewar Malam Sani.
"Yo karatun boko wani karatune"
"In banda iskaci me suke a makarantun"
laka suka yi ta gulma kamar yadda suke yi kullum har
dare ya raba, sannan suka shiga wajen kazaman matan su.
***
Zaune take gefen gado sanye da doguwar rigar fakistan
mai ado tun daga wuya har kasa, kanta tsefe yake ta daura wani
baki.dan kwali mai adon jar fulawa tayi tagumi da hannun ta na
hagu wanda zane yake tsab da kunshi irin na Sudan.
Ta fiyar da taji bata kawo a ranta cewa Isma il ne ba,
don tasan lokacin dawowar sa bai yi ba.ya shigo dakin kamar
wanda aka jeho, bata san lokacin da murmushi ya kubce mata
ba, ta saki hannun ta daga tagumin da take, kai tsaye ta tashi ta
taro Isma"il gami da rungume shi, dawowar sa da wuri tayi
matukar burgeta, kuma yau kwata-kwata ya canza mata kamar
ya kara kyau.
Isma"il naji dadin dawowarka da wuri.
"Ni ma naji dadin kwalliyar da kikayi don ni
"kana nufin kwalliyar ta burgeka?"
"Kwarai ma kunta"
har yanzu rungume suke da juna kamar yadda ya fada
kwalliyar ta bargeshi, yaji sha"awar ta ta kwaranyo zuciyar sa,
kamar ya hadiye ta.
10
"Wane irin kamshi nake ji a jikin ka?"
"Turare ne wani aboki na ya fesa min.
"Kamar turaren mata"
"A turare a kwai na mata a kwai na maza?"
"Kwarai makuwa Darling".
A hankali ta fara cire maballan rigar Isma"il cikin
nutsuwa, dai-dai ta circ masa kayan dake jikin sa ta barshin
daga shi ai gajcren wando, maballayc uku kadai ta cire a jikin
daguwar rigarta, rigar ta rabu da jikin ta cikin sauri ya rage
daga ita sai jar shimi, ta saki Isma"il ta nuli makunnin wutar
dakin, Isma"il ya kalli bayan ta ya hadiyi yawu gami da yin
tsaki cikin zuciya.
"Ina da irin wannan matar nake tafiya wurin wasu "yan
iska" ya fadi haka cikin zuciyarsa.
***
Yau kusan kimanin shekaru biyu kenan Alhaji lawan na
neman Jamila kala ya kashe mata kudin da ko zaa yankashi
baisan adadin su ba, sarkoki da yan kunna yen gwal bazai iya
misalta yawan wanda ya saya ba, shadda leshi atamla duk
masu tsada ba irin wanda baya sayowa Jamila reza yanki ba
kyauye, kudin da yake kashewa Jamila ko mahaifiyar da ta
tsugunna ta haife shi baya kashewa, amma abin bakin cikin ko
siket dinta bai taba gani ba,hana rantsuwa ya taba taradda ita
tana canza kaya, ya kuma taba yin rawa da ita ta mintin uku
fatin wani abokinsa, shima sai da yayi mata alkawarin
makudan kudi.
a
Tafe yake cikin motar kirar jeep chiroki mai ruwan gwal.
farar shadda da farar hula muhadu a baki gami da bakin
tabarau sanye a fuskar sa.
Yau ne bokan ya bashi rana don sauraron matsalar sa da
biya masa bukatun sa kamar yadda yayi alkawari.
Daidai kauyen BAGADAWA ya saki hanya, hanyar da
11
yabi hanya ce mara kyau hade da rairayi gami da busassun
itatuwa a gefen hanyar dajin.
Ya sami kusan mintina arba"in yana tafiya bisa wannan
mummunar hanyar a hankali ya fara hango "yar kewayayyiyar
bukkar bokan da shi ya kira malami, minti biyar da hango bukkar ya isa, ya tadda bokan zaune bisa wani yagalgalalallan
buzun da bai gane ko na wace irin dabba ba ne, sai dai abinda
ya ba Alhaji Lawan mamaki bokan magana ya ke ba tarc da
wani na kusa da shi ba, bil asalima kamar yadda ya lura ko a
cikin bukkar bai ga alamun motsin mutum ba.
"Eh ka gaya musu an samu" a cewar bokan.
"IH"a hahaha dariya, mai karfi ta biyo bayan maganar.
"Na riga na gaya muku wannan kashe shi za a yi" ya
fada bayan gama dariyar, gaban Alhaji Lawan ya fadi, wato
daman wannan bokan har kisa ya ke,
"To har an gama da shi madalla da ku bayina, na san ba
zaku bani kunya ba, nima har abada ba zani baku kunya ba.
salla dai ko? to na daina".
Yana gama magana wanı curarren hayakı ya fito daga
bakinsa ya nufi wata bishiyar kuka dake kusa da wajen.
"Me ke tafe da kai?" Boka ya tambaya har ya buda baki
zai fara zuba boka ya daga mai hannu.
"Na san matsalarka", ya fadi yana zare ido, Alhaji Lawan
shiru ya yi yana kallon bokan.
"Matsalar ka Jamila Kala" Bokan ya fadi kamar yadda
dan koren sa ya fada masa.
"Kwarai kuwa Malam", Alhaji Lawan ya fada a
mamakin ce.
"Kar ka kira ni malam nan gaba"
"To Ma...."
"Aa!" ya daka masa tsawa.
"To! To! na ji"
12
"Ka kira ni Boka kai tsayc"
"To" Alhaji Lawan ya fada a gajarce fuskarsa na
kwararar da gumi, kamar wanda kunama ta harba a kan
gyambonsa.
"Me kake son samu wajenta?" Bokan ya lambaya.
"Na dade ina yi mata hasara har yanzu shiru ba wani
bayani kamar an aika bawa garin su".
"Fadi bukatarka kai tsayc"
"Bukatata yadda na kashe kudi na samu makamako"
"Har yanzu baka fadi ba, ka sani mu nan ba wani boyeboye ko alkunya, ban kira kai na da malami ba, Boka fa na ce
ma ka kira ni, ni ba kura ba ce lulluße da fatar akuya, ban shi
ga rigar malanta ba bokanci na ke yi SAK! in kashe mutum ka
ke so mu yi fadi za ka yi in arzikinsa ka ke so mu karaya fadı
za kayi, in jini ka kake so mu sakar mata, ko mu sata cutar tusa
duk wanda ya zo wurinta daga buda baki zai yi magana sai tusa
ta barko mata, wane ne ka kě so ciki?t
"So nake na sadu da ita" ya fadi da gaggawa kamar
subuce masa maganar ta yi.
"An gama"
Ya dau tsawon minti goma yana hade-haden daga karshe
ya hada wani gari-gari kamar kwalli, ba za kice ga kalar abin
ba, ya cakuda ya daura cikin wata karamar kwalbar turare.
"Karbi wannan " ya fadi yana zazzare ido kamar
barawon da mata suka kama.
Alhaji Iawan ya miko hannu ya karba ya dan dubi tsakin
maganin dake cikin kwalbar, gaskiya ya rena shi a zuciyarsa,
ya zaa ce wannan dan garin shi zai biya masa bukata, duk da
irin kudin da ya kashe a banza.
"Kar ka rana garin maganin" Bokan ya fada kamar ya
shiga zuciyar Alhajin, hakan kuma shi ya ba Alhajin mamaki
da amincewa da Bokan, abin da Alhaji bai sani ba, Bokaye sau
13
tari kan karanci fuskar mutum su fadi yanayin da suka ganshi cikin farin ciki ko saßanin haka, kuma kowane mutun mai hankali na iya yin hakan.
"Nawa ne abin sadakar?" Alhaji Lawan ya tambaya.
"Nawa nc kudin zaka cc" Boka ya gyara masa. "To nawa ne kudin?"
"Dubu hamsin!" ya fadi da karfi gami da zarc ido kamar
beran da tarko ya kama wai shi kar a kawo wasa ko ai ragi.
Gogan naki cusa hannu kawai ya yi a aljihu ya debo
kudi. Bako irgawa ya dai tabbatar sun haura dubu hamasin.
Boka ya miko hannu ya karfe kudin dan kar wani sabanin
fasawa ya gifta
"Shi wannan kwalli shi ake kira da Kifil in ka sa, duk
macen da ta ganka sai ta yi sha"awa, yadda za ka yi amfani da
shi, in kajc kofar gidan yarinyar sai ka samu waje ko cikin
motarka ka shafa, da kun hada ido an gama, ko me ka ke so
zaka samu
"Na godc kwarai" ya fada gami da farin cikin kamar an
bashi tsaleliyar budurwa.
"Shegun masu kudi in banda haka ba zaka ci kudinsu ba"
Bokan ya fada bayan fitar Alhaji Lawan.
"Duk karya muke ba mu da wani magani, canki fadi ne
kawai, ni wannan kwallin ma ban san dame da me na hada ba,
ni dai na san akwai garin batir a ciki" ya tintsire da dariya gami
da buga kafa har da hawaye. Ya ci gaba da cewa aka yi su bada
zakka ko su yi sadaka, sai su dinga goce-goce yanzu idan Allah
ya sa maganin ya yi to ni kakata ta yanke saka.
Ya isa gida da gaggawa kamar wanda aka koro da ga
wajc.
"Dannan kaje rasuwar da na fadama" mahaifiyar Alhaji
Lawan ta tambaya dai-dai lokacin day a shiga gida.
"Banje ba" ya amsa a gajar ce
14
r 1
daidai lokacin ya fara taka
matattakalar benen da za ta sada shi da turakarsa.
"Me ya sa baka son zumunci ne dannan?" ta ſada cikin
kunan rai da bakin cikin wulakancin da ya ke yi mata, wannan
karon bai amsa ba, don tuni ya haye sama.
Shi kadai ne danta ta kuma sha matukar wahala da
fadinta bata baki ne, ta fi jin dadinsa kafin ya samu kudi,
amma kudi na zauna masa ya canja sabuwar rayuwa.
ya kwashi kusan minti arba"in yana kwalliya zuwa wajen
Jamila Kala, Hausawa sun ce in kana da kyau ka kara da
wanka, wannan dalilin ne ya sa Alhaji Lawan yin kwalliya da
yake ganin zata firgita Jamila, duk da ya san ta saba ganin "yan
birmi.
Kamar yadda ya shiga bai saurari kowa ba, haka ya fita
bai saurari kowa a gidan ba har mahaifiyarsa.
Kai tsaye ya wuce farfajiyar da yake ajiye motocinsa,
motoci jere birjik kamar a Akija ta Katsina road.
Mota ya dauka dunkulalliyä sabon yayin boksuwaja
wacce ba kowane Bello da Mudi ne ke shiga irin ta ba a birni.
ga
Tukin minti ashirin ya sada shi da Burma road inda gidan
Jamila kala yake ya kuma yi sa a kofar gidan bude yake
dukkan alamu ba wanda yazo, dan da wani na cikin da yaga
mota yasan duk masu zuwa gidan Jamila ba talaka.
Hannu ya sa a aljihun rigar sa ya dauko "yar kwalbar da
ke cike da kwallin da bai san dame akayi shiba.
Ya turmutsa dan tsinken da ya siya wajen wani dan koli
ya gwale idon sa na dama ya turmutsa tsinke, "wash" ya yi
"yar kara gami da yamutsa fuska saboda tsabar zafi da yaji, bai
hakura ba don karfin hali ya kara danna tsinken dan sawa daya
idan, ya kara gwale daya idon ya dankara masa kwalli da boka
yake zancen akwai garin batir a cikin "wash" wannan karon ma
kara, ya kara yi ya dade cikin motar kafin radadin ya huce ya
15
dubi dan madubin da a ka tana da don duba baya, idon yayi jawur kamar yadda ya gani yasa wani farin hankici ya goge hawayen daya Gata masa fuska, ya bude motar a han kali ya ziro kafarsa abinda ya ba Alhaji Lawan mamaki gaban sa yayi faduwar da bai taba yiba, faduwar gaban da sai da ya yi jim kafin ya tsallaka kwatar dake ga bansa, "Alhaji Lawan" yaji an kira sunan sa ya daga kai, wayyo Jamila kala ce sanye da riga da wando na jins baki kanta ya sha shamfo sai sheki yakeyi har yanzu kirar na nan kamar yadda take duk ba wannan ne ke burge Alhaji Lawan ba, murmushin da take shi ke burgeshi da kuma mamaki tunda yanke kashe
mata makudan kudade bata taba yi masa murmushi ba ko da
sau daya ya dada gwale idon sa wai don kwallin ya kara aiki kamar wasa murmushi Jamila kara fadada zuwa dariya.
A bangaren Jamila ita murmushi da take yi murmushi ne
na ta tabbatar yauma ta kara samun abokin tafiya a gida basai taje nema ba.
"Ya ka tsaya a nan?" Ta tamtaya gami da karasowa kusa da shi, hannun sa ta rike izuwa gidan kamar rakumi da akala binta kawai yayi yana da da zarc ido.
Har cikin daki ta kaishi suna shiga ta cire masa hula gami da babbar riga da yake sanye da ita.
Zaunar da shi tai bisa gado gami da sumbatar kumatunsa. Bari in kullo kofar gidan T'a fada gami da tashi tsaye ta nufi kofar dakin.
"Dole tsafi gaskiyar mai shi" Alhaji ya fada bayan fitarta. "T'suntsu daga sama gashasshe" ita ma ta fada dalidai lokacin da take kulle kofar gidan.
Rigar dake jikin ta ta fara cirewa daga ita sai yar Bez ta
zauna kusa da Alhaji Lawan.
Ilankalinsa yayi matukar tashi tashin da bai tabayi ba yaji dadi gami da yin godiya ga boka a zuciyarsa sai dai wata
16
faduwar gaba dake damunsa ca acikin zuciyarsa.
wasanni ta kama yi masa har hankalin sa ya gushe ta na
lura da gushewar hankalin ta fara ciremasa kaya daya bayan
daya cikin gaggawa da dauki gamin da zumudin samun abokin
tafiya.
***
A gidan su Hajara kuma gardama ce mai karfi ta turnike
tsakanin mahaifin IHajara da mahaifiyar ta Hajiya Ladi.
"Haba Alhaji yanzu na fada maka matsalar da "yar nan
ke ciki kace a rabu da ita
"me kike so ayi mata?"
"Aje a taho da ita" a cewar Hajiya
"Ke kinsan meyc aure kuwa?"
"Haba Alhaji ko mai sanin darajar aure ai ba ma kyaleta
yunwa da wahala su kashe ta ba"
"ita ta saya"
"Ni dai gaskiya zanje in taho da ita ko da karfi ne, don
ina ji ina gani ba zan bari "yata ta halaka ba"
"Ban amince miki ki fita ba in kuma ki ka fita karki
dawo min gida" Alhaji ya fada a fusace.
"Kar na dawo ma gida?" Ta tambaya a mamakince a
zaman su na sama da shekaru ashirin bai faba fada mata haka
ba.
"Haka na fada kuma haka nake mufi"
Zura masa ido kawai tayi cikin mamaki
Ki fita harka tsakanin miji da mata in ba so kike ki fada
cikin fushin Ubangiji ba"
To yanzu Alhaji ya za a yi?" Ta tambaya cikin sanyin
murya mai nuna alamun ta amince da gajeriyar nasihar da yayi
mata amincewar dole.
"Zubawa sarautar Allah ido don duk wanda ya sabawa
iyayen sa sai yaga sakamako"
17
tayi"
yanzu Alhaji baka yafe mata ba?"
"Na yafe mata amma dole taga sakamakon sabawar da
"Kai na shiga uku yanzu ni ya zanyi da raina wayyo.."
T'a ſada gami da yin kukan bakin cikin halin da yarta ke ciki.
Ai sai kiyi ni kinga fitata" ya fada gamida nufar kofar
gida abinda Hajiya Ladi bata sani ba dauriya ce yake irin ta
maza da zaa tsaga zuciyar sa yafi kowa bakin ciki da takaici.
***
Tun daga kwanan farko da Isma"il ya yi a dakin Jamila
kala wanda ta kora shi gida saboda iyalin sa kamar yadda tace
Isma il bai kara kwana a gida ba kullum da irin karyar da yake
shirga wa kwata-kwata bama ya san ganin ta, kullum sai karfe
goma na safe ya ke dawowa gida abinci da dan kudin kashewa
kullum Jamila ke bashi ba ruwan sa ya wanke goma ya tsoma
biyar ga dan tabi da yakeyi da dare :
"Wai yanzu Isma"il ina kake kwana ne?" Hajara ta
tambaya
"Ke ina ruwanki da in da nake kwana nafa gaji
wadannan tambayoyin naki na remin wayo"
"Amma ya kamata na tambayeka a matsayina na matar
ka" Ta fada muryar ta na rawa kamar zata yi kuka, shiru kawai
tayi tana kallo sa cikin mamaki kamar bashi ne Isma"il din nan
mai dadin zance da yake zuwa gidan su ba gwanin iya kwalliya
sarkin iya zance.
Can a tsakar gida su Tasalla sun sa hira kamar yadda
suka saba kullum.
"Oh ni Tasalla wannan yarinya tana ganin tasku sai kace
marainiyar dake hannun kishiya".
"Ke ma dai kya fada yanzu fa ya dai na dawowa da dare
sai iyanzu zaki ga shege ya shigo" a cewar Saude.
"Tun da a fara wankau ko kwanon shinkafa da ya bai
18
:
sayo mata ba" Larai dake gefe guda ta fada
"Kuma daga ganin yarinyar daga gidan gata ta fito in kika yi la"akarin da irin kayan dakinta da shegen ya cefanar" A
cewar Saude.
To ai baki sani ba tunda ta zo fa bai taba yi mata dinki ba
kuma walla..."
"Kc Larai karki rantsc." Ta salla ta tari numfashinta,.
sanna ta ci gaba "Mahaifiyar sa ta kawo mata super print irin
"yar dari uku da hamsin kwanaki."
amsa.
"Yaushe wacce super print?" Larai ta tambaya.
"Wata koriya mai alamar ganyen rogo." T'a salla ta bata
""T'o ai wannan sawar ta biyu." A cewar Saude.
"Kwarai ma kuwa ta sa ran wata alhamis ta kuma Kara
sawa ran wata talata, yau sati biyu kenan da kwana uku." Larai
ta fada daidai lokacin data kamo kwarkwata a kanta ta rabon sa
da wanke wa sama da wata biyu in ka dauke wankan tsarki da
take yi, wannan kuwa ba sabulu.
"Dama ni tun daga tsarin zaman nan nasan ana zaman
karya." Saude ta fada.
"Gaskiya ya za a ce namiji ya sai da kayan daki na kakaf
ina kallonsa."
"Ai yarinya ce bata san ILLAR MAZA ba, kuma ba ta
san MAZA SAI SANNU ba, har yanzu ba ta tabbatar da
MAZA BA SU DA TABBAS ba, kuma,a ta yi hankali ba sai
ranar da ta tabbatar da NAMIJI BA DAN GOYO bane..."
"Ahayye ayuuriri." Suka bushe da dariya jin irin
kalmomin da Tasalla ke fada kan maza kamar ba namiji ne ya haifeta ba.
"Allah da gaske nake Saude ba za ta yi hankali ba sai ta
tabbatar da NAMII TABARMAR KASHI ne ta kuma
hakkake da NAMIJI KWANDON ZAWO ne.."
19
"Suka kara bushewa da dariya karo na biyu, jin Tasalla
na sakin baki.
"Amma dai har da mazajen wajen Katsina ko?" Saude ta
tambaya tana dariya.
"Ke ban son iskanci kina nufin iyaycna."
"Ai namiji kika ce."
"Ban da iyayena."
"Mu da namu iyayen kenan?" suka kara bushe da dariya
ganin zare ido da Tasalla ta fara yi tun ba a je ko ina ba
maganganun na neman faddawa kan iyayenta.
A cikin dakin Hajara kuwa hirar da ta biyo baya "Yanzu
kana nufin a matsayina na matarka ba zan tambayeka ba?"
Hajara ta kara maimaita tambayar.
"Kina ban ci da sha ne?" Bai san-lokacin da kalmar ta
subuce daga bakinsa ba.
"Ina dai ciyar da kai na, wanda kai ya kamata ka ci da
ni." Ta fadi haka ganin Isma"il bai san kunya da kara ba, gori
na farko da ta fara yi masa kuma shi ya ja, duk da haka bata ji
dadi a zuciyarta ba.
"Na gode." ya fada a gajarce don bashi da abin cewa.
"Ai kai ka ja." Ta fada a nadamance.
Banza ya yi da ita, sai dai abinda ya kudurce a zuciyarsa
ba zai kara dawowa ya kwana a gida ba har lokacin da zata gaji
ta bar gidan don ya gaji da ita, inin ya so ya koma wajen Jamila
ya tare tunda tana son sa ga kuma kudi, ya yi godiya a
zuciyarsa rashin haihuwa dake tsakaninsu in suka rabu sun
rabu kenan, dama shi ya san aurc abu ne mai wahala gwara
zaman bariki in ka gaji ka gudu ko ku bata ba mai tuhumarka,
tunda baku tara shaidu ba, a hanya kuka tsinci juna a hanya
zaku yarda juna.
***
BAYAN WATA BIYU
20
Bakin cikin halin da Isma"il ya jefa Hajara ya fara sa ta
ramewa ga tari da Hajara ke yi, wanda bata san abinda ya
haddasa shi ba, magani ba irin wanda bata sha ba, amma tari
kullum kara gaba yake yi, kamar maganind a take sha na kara
tarin ne. Wankin da take ma dai nawa ta yi saboda tarin, kudin
da ta tara, shi take ci, da kuma magani, Isma"il kuwa ba
ruwansa, shi barikinsa ya sa gaba.
Kuma kullum kara tsananta yake уi.
"Kuf.... kuf.... kuf.." Tari ya turnuke lajara kamar yadda
ya saba kullum duk lokacin da ta bude baki don yin magana,
sannan ne lokacin da shi kuma tarin zai fara aikinsa.
Isma "il dake zaune gefen gado ya harareta ya matsa gefe
guda gami da toshe bakinsa da hannu da wani dan hankici mai
ruwan kasa da ke hannunsa, Hajara na son yi masa magana
amma tarin da take fama da shi ya hana.
"Isma.....kuf.....kuf... ""Tarin ya kara turmuketa. Ya karа
kallonta kallo irin na wulakanci.
"Wai Hajara wacce irin rashin lafiya ke damunki haka?
Ni fa gaskiya ba zan iya zama dake kina irin wannan tarin ba,
don tun muna firamare ake gaya mana irin wannan tarin
communicable disease"
"IHaba....kuf.... kuf.... Isma"il ai Allah...yake dorawa
mutum cuta shi kuma ke yaye masa, ka yi hakuri tund ina
shan maganiczan samu sauki in Allah ya yarda." Hajara ta yi
sa"ar fada, wannan karon tarin bai yi sa"a a kanta ba.
"Ba wanı sauki yau watanki nawa kina tarin gashi
kullum sai ramewa kike, in ba dama kawai ki tafi gidanku ni ba
zan iya zama dake haka ba, in kin sami