yarinyar
nan ba ma zai iya jurewa
wannan tsallen bataken ba, ya
zama dole ya hadata da ubanta
duk ma wacce za a yi a yi domin
hakurinsa ya kai bango.
Ya juya ya koma nasa dakin
Uzaifa yana kwance a dakinsa
ya lulluba da bargo mai taushi
yana chart da abokinsa a waya
ya dinga jin wani irin sauti
numfarfashi da shissheka ya
soma nazarin daga inda yake
jiyo wa wajan window sane na
waje sannan ya mike yana
82
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
nazarin to mutum ne a wajen ko
wata dabbarce.
Cikin wannan ruwan da
fargaba ya isa wajan sannan ya
kunna fitilar wayarsa wani
dogon tsaki yaja yayin da ya
haske fuskarta da fitilar wayarsa
duk da ta sa bayan hannuwanta
biyu ta rufe fuskarta saboda
kashewar da haske ya yi wa
idonta hakan bai hana shi gane
ko wacece ba saboda kayan taба
gani a jikinta yanzuma su ne a
jilkinta ga yanayin girmanta "Ke
me ki ke yi a nan?"
Ta sauke hanmnta da ba
muryar da ta yi tsammanin ba ce
83
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ita ma ta gane shi bakinta na
rawa ta ce "Uhm! Uhm koface
ta ki buduwa"
"Ba sai ki yi magana daga
ciki a bude miki ba".
"Na yi ba'a bude ba, mu je
bai saurareta ba ya yi gaba tana
binsa a baya har zuwa kofar
dakinsa.
Kofar da zata sadaka da falo
ya budemata sannan ya kirata Zo
ki shiga ta nan.
Ta dai bi zabin sane saboda
gigicewa da sanyin ya sa ta yi
badon ta san in da yake nufi ta
shiga ba, sai da ta shiga ne ma ta
gane a babban falon take sannan
84
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ta yi saurin shiga dakinta da ta
ga har lokacin dakin abude ma
yake.
A wannan rayuwar
sadaukarwa da Alhaji kai shi ne
kawai mafita a cikinta domin
yanzu ta gama saduda matukar
kadai take gani tafi dacewa da
ita.
Shine dalilin da yasa ta kasa
rufe kofarta ta kudunduna har
lokacin tana rawar sanyi kwallah
na zuba daga idonta nan da nan
zazzabi me zafi ya rufe ta
addu'arta Allah ya sa zazzabin
ya zamo ajalinta ta huta da
wannan zulumin rayuwa.
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
**
Lawan ya yi shirin fita tsaf
yana saka hula asabe ta tsaya a
bakin kofar dakin ganin yana
shirin fita ya sa tacewa "Na gaya
maka fa shinkafarmu ta kare,
kuma wannan kudin ma da ka
baya ba fa za su isa cefane ba".
"To ai shi yas ana baki dari
biyar din ki siyi duk abin da za
ki "
siya a ciki.
A cikin naira dari biyar din zan
sai shinkafa na sai kayan miya,
na sai magi da mai to wallahi da
sake domin sam ba zai isa ba."
86
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
"Wai ke wane irin rashin
hankali so ki yi ina ki ka kai
shinkafar buhu guda ko sati bata
yi ba, kun zo kina so ki mai da
niw ani marar hankali.
Asabe bata san lokacin da ta
lailayo wani ashar ta maka ba
"Mai kake nufi da abin da ka
fada, ka dai san ba daga gidan
tsiya na fito ba bare ka се
gidanmu na kai.
Shinkafar da ke kawo a ka yi
abincin wuni biki sannan muka ci
gaba da ci har kawo wannan
lokacin, in ba ka ce min sambarka
ba aikwa ba zaka kushe min ba"
87
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya ce "Sambarka cuta da
ha'inci".
Ya yi ficewarsa ya barta tana ta
sababi.
In bayan kar ace da ga yin
aurenta ta fara korafi da sai ta kai
kararsa gurin manya, domin dai
ita ba za ta laminci zargi da cin
mutumci ba.
Duk abin da yake faruwa a
kunne Asiya da Umaima ya yin
da suke shirin tafiya makaranta
domin duka duka karfe bakwai ne
na safe. Ta na ta wannan mitar a
tsakar ida suka gama shiri su kai
mata sallama sun fito suna
tattauna abinda yafi damunsu
88
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
rashin sanin halin da 'yar uwarsu
Hansa'u ta ke ciki sun damu
kwarai har suka nuńa sha'awarsu
ta son zuwa gidan. Su ka gayawa
Asabe amma daren jiya take gaya
musu abin da Babansu ya fada da
tai masa magana, wato gargadin
mijin Hansa'u a kan cewa to shi
fa baya son ana masa zirga zirga a
gida, idan ta kwana biyu da kansa
وو zai kawota gidan ta gansu".
Su dai wannan hukuncin bai
musu dadi ba.
Tun jiya suke tunanin yanda
za su bi a zancen da Asabe ta yi
musu suje gidan, suna kewar
Hansa'u matukar kewa
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Sun yanke shawarar idan sun
taso daga makaranta za su taka da
kafafuwansu su bi kwatance, har
gidan Hansa'un don su ganaota.
Hakan kuwace ta faru domin
suna ganin in har suka bari suka
koma gida toh basu da wani
lokaci na kansu da zasu iya fitowa
batare da Asabe ta sani ba, haka
su kaita tafiya har suka zo kofar
gidan sai dai da ganin tsarin gidan
ma kadai ya kada hantar cikinsu,
suka fara tunanin ta ina ya dace
su bi domin su samu su shiga.
Sun tura kofar gate din a rufe
take gam gam.
90
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Asiya ce ta dubi Umaima
"To ko mu kwankwasa?"
Ba ta ce mata komai ba, sai
ma ita din da ta soma kwankwasa
wa.
Maigadi ne ya leko ta wata
'yar kofa "Kai yaya what
99 happen".
"Da ganinsa ma ba bahaushe
ba ne suka kasa ba shi amsar
tambayarsa, har sake nanata musu
da gurbatacciyar hausarsa ya yi
"Me ku ke so?"
Su ka yi shiru suna kallon
juna. Asiyace tai karfin halin
cewa "Wajen Hansa'u muka zo".
"Waye Hansa'u anan?"
91
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Umaima ta ce "Amarya ta
nan gidan ta Alhaji".
Maigadi ya rufe 'yar karamar
kofarsa "Kai ku tafi Alhaji bai ce
wani zai shigo ba"
Sun ji rufe kofar tasa kamar
saukar aradu a tsakiyar kansu.
Ga koshi ga kwanan yunwa
basu sha wahala wajan gane
gidan ba amma shiga gidan ya
gagare su.
Haka suka zauna kan wani
tudu cike da sarewa ga yunwa ga
gajiya.
Daga karshe dole suka ta shi
suka koma gida.
92
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Duk yanda Lawai ya za ci
samun sauki daga Alhaji Ahuta
lamarin na neman canza
tunaninsa domin 'yar kyautar da
ya ke yi masa ta bajinta, tun da
Hansa'u ta tare ya make
hannunsa, ko haduwa suka yi da
shi gaisuwace kawai ke shiga
tsakaninsu.
A cikin kwanakin ma sai ya
bijiro masa da wani al'amari da
ya girgiza shi wai su ta shi daga
wannan gidan su sami wani su
kama, shi zai biya kudin shekara,
wannan gidan da suke ciki ya na
so ya gyara musu shi sosai ya
dora musu bene.
93
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Hankalin Lawai ya ta shi
kwarai domin ya shiga tunanin
cewa anya kuwa Alhaji ba
yaudararsu yake son ya yi ba ya
tashe su daga wannan gidan.
Sai dai dole ta sa ya amsa da
toh, tunda ba shi da hujjar
jayayya da shi a kan abinsa.
Tun dare yake tunanin
hanyar da ya kamata ya bi ya
fadawa Asabe maganar tashinsu
ya rasa, domin ya kula da Asabe
kwata kwata ba ta son babu, ba
kuma ta yarda da kaddara ba, ba
kuma ta da hakuri bare lamuni.
Tun da ya yi mata karyar
cewa gidansa ne bai san hukuncin
94
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
da za ta dauka ba, idan ta ji dama
gidan sirikin sane.
Yana tsaka da wannan
tunanin ya dinga jin ana buga
kofar gidan bam ban kamar za а
6allah.
A fusace ya mike ya na cewa
wai waye ne zai ballan kofa.
Asabe na ceaw Je ka dai ka
ga ni wannan irin bugun haka da
sassafe, sai kace name bin ba
shi".
Yana budewa ya yi tozali da
Alhaji Ahuta.
Gabansa ya yi wata irin
faduwa domin ganin yanda
fuskarsa ta nuna tsananin 6acin
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
rai, ya mika mas ahannu suka
gaisa.
"Karar yarinyar nan na kawo
Lawa don na ga ji da rashin da'a
da tarbiya da take nuna min, ka ga
dai kaunace tasa na tsallake mata
da yawa na zo na nemi auranta,
amman ace yarinyar nan na
guduna kamar kare, tunda na auri
yarinyar nan fa ko inuwa daya ba
mu taba zama ba, bare wata
magana ko wani biyayyar aure a
tsakaninmu"
"Subhanallahi" in ji Lawai
ya soma ba shi hakuri "Kuruciya
ke damunta alhaji amma ai ba ace
96
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
bata kaunarka ba bari na sa ko
hula ta na je gidan na same ta"
Alhaji na hucin bacin rai ya
ce "To in hakan zai yiwu da dai
yafi, domini ni shawarar da na
yanke da ba mai dadi bace"
Kalaman hakuri dai ya ci
gaba da ba shi ya shiga gidan da
sauri Asabe na tambayar abin da
ya faru.
"yar banzan yarinyar nan
mana Hansa'u ashe halin banz
atake gwada Alhaji aka kaita
gidan".
Asabe ta ce "Amma kamar
ba zata aikata ba sai dai ina zargin
'yan uwann na nata kamar suna
97
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
satar jiki suna zuwa gidanta dan
rannan daga zuwa makaranta basu
dawo ba sai la'asar".
Ya dora hularsa a kansa
"Koma me suke kullawa dai dai
na ke da su zan yi maganinsu bari
dai na dawo".
Duk abin da ake syi su Asiya
na ji sai dai jikinsu ya yi sanyi da
yanda aka yi Asabe ta gane sun je
wajen Hansa'u kuma babansu ya
ce zai dauki mataki a kansu, shin
wani mataki zai dauka?" kowani
mataki zai dauka ma sun san ba
wanda zai musu dadi ba ne,
domin sun fi kowa sanin halin
mahaifinsu bai furta ba ma yana
98
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
daukar mummunan mataki bare
ya furta".
Haka suka fito suka tafi
makaranta zuciyarsu cike da
wasuwasi da fargaba.
Zazzabi da ya hana Hansa'u
rintsawa tun cikin dare har yanzu
yana nan a jikinta musamman
kanda da yake tsananin ciwo
wanda da kyar take iya bude
idanuwanta ta na ji a ka turo
kofar aka shigo ta kasa bude
idonta sai jin muryar Babansu ta
yi a kanta ya na cewa.
"To mutuniyar banza kin
dauka wanda ki ka raina dinne shi
99
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
yasa kina jin ana yin sallama ki
ka yi wa mutane banza"
A firgice ta mike ta ja jikinta
zuwa jikin gado.
"Wato zuwa ki ka yi ki mike
kafa ki rashin mutuncin da ki ka
ga dama, wannan ba mijinki ba ne
da ba zai ce miki ki yi ki yi ba, ki
bari ki bari ba, har ki ke yi masa
wani guje gujen banza da wofi"
Ya dinga fada ta inda ya ke
shiga ba ta nan yake fita ba, har
ya soma kokarin dukanta Alhaji
ya rike shi yana ba shi hakuri ya
ce ai ma da laifinka da ba ka sa
igiya ka daure ta iyalinka ce fa,
kana iya yin duk yanda ka so da
100
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ita, lallashinta da ta ga kana yi ne
yas atake maka abin da taga
dama".
Ameenu da yake girki a
kitching duk hayaniyar da Lawai
ya ke yi yana ji don haka ya
fahimci duk abin da yake faruwa
ya kuma tabbatar da cewa
mahaifin Hansa'u ne. Kalamansa
na karshe ne suka girgiza shi har
ya kasa ci gaba da tsayuwar da
yake yi, ya zauna ya rike kansa da
hannu biyu.
Hatta Huzaifa da yake bacci
a dakinsa fadan Lawai ya farkar
da shi daga bacci domin shi
Lawai mutanne da bai iya magana
101
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
a hankali ba, gidan ya yi shiru
muryarsa kawai ake ji.
Hüzaifa ya ja dogon tsaki, ya
mike zaune a tsakiyar gadonsa
wai wane irin mutanene Alhaji ya
yayibo mana ne baccin safen ma
ace...
Kalaman Lawai na Karshe su
ka sa ya kasa karasa abin da yake
son fada. Ya mike tsaye zuciyarsa
ya ji tana son ganin wannan wane
irin uba ne.
Yana shiga kitchin din ya
tarar da Aminu dafe da kai
Kwallah na disa a idanuwansa.
A iya zaman da ya yi da
Aminu bai taba ganin hawayen
102
Hadiza Ado Yalwa Garari.2
saba irin yau, da hanzari ya
Karasa inda yake ya dafa
kafadarsa "Aminu me yasa ka
kuka haka?" me ya şame ka?"
Aminu ya dago tausayi ne
Oga, wallahi tausayin yarinyar
nan na ke ji”.
Huzaifa ya dauke hannunsa
daga kan kafadarsa yana 'yar
gajeriyar dariya "To wai Aminu
ko son yarinyar nan ka ke ne, ka
damu da yarinyar nan, damuwar
da ko danginta ba na jin sun damu
da ita"
Aminu ya dan yi murmushi
yana share kwalla "In so ta in yi
ya ya da ita oga tana matar aure
103
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kuma in ma ba haka ba, kai ka
san ina da wadda zan aura, kawai
dai tausayinta ne tausayin irin na
wanda ko wani mai kanwa ko 'ya
ko kuma duk ma wat anasaba ta
diya mace mai rauni zai ji shi a
ransa.
Daga nan ya dinga
zayyanewa Huzaifa abinda ya sa
ni game da ita tun daga zuwan
mahaifiyarta binciken aure kawo
yanzu zuwan mahaifinta.
Ko rakiyar da Alhaji ya so ya
yiwa Lawai dakatar da shi Lawai
din ya yi ya ce ya yi zamans a
dakin matar.
104
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya kuma ci gaba da ba shi
hakuri shi ma din tsayawa ya yi
Lawai yà fita ya rufe kofa bugun
rufewar kofar ya yi dai dai da
bugun zuciyar Hansa'u, duk dai ta
saddaka komai a yanzu dole ta
bawa Alhaji kanta ba zata iya yi
masa musu ba.
Yanda Lawai ya fito a fusace
ya na suratai yasa daga Uzaifa har
Aminu binsa da kallo ta tagar
kitchin din, har ya bace musu da
gani Uzaifa ya girgiza kai "Yanzu
kam ya fahimci irin abin da
Aminu ya ke ji game da yarinyar
lalle ne abar tausayi ce ya zama
kuma dole zuciyar imani ta
105
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tausaya mata domin bai taba ji ko
ganin Uba irin wannan ba.
Shi kam Da bai ji wani
abubuwan da kunnensa ba da zai
iya musantawa in fada masa a ka
yi.
Daga shi har Aminu sai da
suka razana suka kuma kalli juna
lokaci daya ya yin da suka ji
Karar buga kofar da Alhaji Ahuta
ya yiwa dakin Hansa'u sai dai
babu. wanda ya iya furta kowace
kalma a cikinsu kowannensu da
abin da yake ayyanawa a ransa.
Tunda Lawai ya shiga gidan
ya shiga zaynawa Asabe
abubuwan da yake faruwa.
106
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Sai da Asabe ta gama
sauraransa tsaf sannan ta се
"Amman Lawai da bari ka yi na
je na same ta na tambayeta ko
akwai wata matsalar na kuma
lallashe ta ka ga har yanzu fa ita
yarinyace".
A harzuke ya ce "Ita din wa
da za a lallasheta, ita ta haife ni
ko ni na haife ta, kuma ko da ta
ke yarinya ai ba dabba bace dole
ta san mai kyautata mata, cikin
yan kwanakin nan ba ki ga yanda
yarinyar ta canza ba ta yi bulbul
ta yi jawur da ita, idan borin nata
bana iskanci ba ne na kuruciyane
ta yaya zata iya mike kafa a
107
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
gidansa ta dinga cin mai kyau
tana shan mai kyau bata guje abin
hannunsa ba sai shi. ni na san
daga in da matsalar take kuma
zan yi maganinta, wannan
munafukar yayar ta su mai halin
uwarta Asiya ita take zugata, tun
da ki ka fada min tana zuwa
gidanta hankalina bai kwanta ba.
Ranar ko fita bai yi ba har sai
da su Asiya suka dawo, daga ita
har Umaima ba wadda ta cire
kayan makaranta, ya rufe gida, ya
fito da bulala, dukkansu sai da ya
zane su tsaf, sannan ya ce daga
yau sai yau kar ya kara ganin
wata ta fita daga gidan nan da
108
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Nufin zuwa wata makaranta wadda ake fakewa
da ita atafi yawon banza, hankalin Asiya
ya tashi wadda kwanaki yarage suyi jara bawar
Cikin muryar kuka tace baba dan Allah kayi
hakuri kwanaki yarage nagama karatuna, ya
ce tayi saurin shan gabansa tana rike bulalar
tana cewa dukan ya'isa haka, shikuwa
jikinsa har tsumo yake yake nizan fadi
magana kina mayar min da magana banda
rashin sanin ciwon kai yaushe dibga dibga
daku zaku dinga diban jiki kuna yawo a
gari, da sunan zuwa makaranta bakin jini ye
hana kowa yace jana sonku, yar uwar taku
data samu miyi kukeso kuje ku kasowa aure
dule ku zauna min agida ku zamemin yen
iskan gari,
toh ninan mahaifinku kada nasake ganin
wata tafita da niyyar zuwa makaranta, in
kuma allurai waddah takeson bujirewar
umernina kamar
yanda uwarku tomma a shirye
naknadauki matakin dana dauka akanta
akanku
109
Hadiza Ado Yałwa Garari 2
Ita kanta Asabe bata
tsammacin wannan hukunci mai
tsananin daga gare shi ba,ta dinga
ba shi hakuri ammah ina kamar
harzuka shi take yi fadi yake
wannan In ma ban hanata zuwa
gidan Hansa'u ba ai yawo bin
maza zata dinga yi kar ta janyo
min abun fada gwarama su su
zauńa a gidan, makarantar na
soke ta, kuma ban ce ki bawa
wats higiyar abincina yau ba,
gobe ma sa kara fita batare da sun
nemi izinina ba.
Sai da ya gama bambaminsa
da fadar munanan kalamansa
sannan ya ji sanyi har ya fita.
110
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Dukkansu kuka suke har da
shassheka shi ke nan yawargaza
burin mahaifiyarsu, da ta sha
wahala a kan karatunsu, ko dama
bai hana a basu abinci ba ba ma
jin. yunwa a cikinsusu domin
bakin ciki da takaici ya gama cika
musu ciki.
Asabe da kanta ta shigo
> dakinta da abincin da ta zubo
musu ta soma lallashinsu "Kun
san halin mahaifinku bai kamata
ku sawa kanku kunci haka ku
kwantar da hankalinku zan
lallashe shi da sannu har ya
hakura ya barku ku yi karatu".
111
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Asiya har ita din ma
haushinta ta soma ji ta san dai da
bata fada masa ba bata da
masaniya a kan dadewar da su ka
yi rannan basu dawo ba, sannan
in har ta san halinsa ta kuma yar
da su sun sanshi to h da bata furta
cewa zata lallashe shi ba, domin
Lawai mutumne da baya jin
lallashi ba kuma ya jin shawara
kuma ya jin shawara kuma ba shi
da hakuri sannan ya jima ya na
adawa da maganar makarantarsu.
**
Bayan Alhaji Ahuta ya rufe
kofar ya nufi Inda Hansa'u ke
tatakure tana makyarkyata ga
112
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
zafin zazzabi da zafin zuciya
kwalla kadai ke zuba a gefan
idanuwanta, duk da yanda
gabanta ke ta faduwa ganin
Alhaji ya nufota bai sa ta wani
yunkuri na gudu wa ba,
idanuwanta kawai ta mayar ta
rufe ko don ta samu saukin bugun
žuicya har ya kara so daf da ita,
ya zauna a gefanta, ya kai hannu
ya rike hannunta.
"Ki kwantar da hankalinki
mana Hansa'u ni ba jahili bane ba
zan yi miki abin da mahaifinki ya
umarce ni da na yi miki ba zan fi
so mu fahimci juna, ki mai da ni
cikakken mijinki amma kin sawa
113
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kanki tsoro da damuwa, ga shi har
ya haddasa miki zazzabi"
Ya kai hannun ya taba gefan
wuyanta.
"Kai wannan zafin jikin ya yi
yawa?"
Ya fada cikin damuwa bana
yanzu ba ne, tun yaushe ne baki
da lafiya haka?"
Bata ba shi amsa ba sai dai ta
bude idanunta da suke cike taf da
hawaye sannan bugun zuciyarta
da rawar jikin da take yi ya dan
ragu.
Hannunsa ya saka a aljihu ya
zaro wayarsa Likita ya kira ta na
ji yana yi masa bayanin zazzabi
114
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ne mai zafi bata san abin da
likitan ya ce ba ta dai ji yana
cewa ba damuwa.
Sannan ya fita ta sauke wata
nannauyar ajiyar zuciya tana
share ragowar kwallah.
A kichin ya samu Aminu da
Uzaifa ya ce da Amun ka sanarwa
yarinyar nan wani abinci da sauri
likita zai ganta, sannan ya dubi
Uzaifa da ya dauke kansa tun
daga shigowarsa kichin din.
Ya dai yarona ba wata
99
damuwa na ganka a nan"
"Babu"
Ya ba shi amsa a takaice ya
yi kamar ya sake yi masa wata
115
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tambayar ganin yanayinsa kamar
baya son magana yasa ya yi shiru
don ya san miskilancin Uzaifa ba
lallai ne ya ba shi amsa ba, tunda
ya fara da takaita masa.
Nan da nan Aminu ya hada
mata kayan tea a tray ya dura da
doyar da Uzaifa ke soyawa kansa.
Ya kwankwasa kofar sannan ya
murda ya shiga da sallama.
Ya hango ta can kurya a
kwance ya sauke ajiyar zuciya
"Kanwata ashe baki ji dadi ba,
shi yasa yau na ji ki shiru Allah
ya sauwake ya sa kaffara"
Duk yadda take jin jikinta
ganin Aminu yasa ta dan ji sanyi
116
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
har ta yi murmushi domin shi
mutum ne mai barkwance ko da
yaushe ba ya raba fuskarsa da
murmushi. Amin ta amsa cikin
sanyin murya ta shi ki ci abin da
ya samu, kanwata kada yunwa ta
illata ki".
juya.
Yana gama fadin hakan ya
وو
"Na gode yaya Aminu"
Ta yi furucin duk da bai ji
ma abin da ta ce ba ya yi
murmushi domin ya gama
fahimtar babu abin da ya faru a
tsakaninta da Alhaji.
Hadiza Ado Yalwa
Likita
Garari 2
dubata ya gama
sannan ya dauki jininta dan yi
mata gwajin MF dama JP.
Wunin ranar Alhaji bai fita
ba sai bayan sallar la'asar, tunda
ya shiga Hansa'u ta rufe idonta da
nufin barci take yi ya zauna a
gefanta ya zuba mata ido sosai ya
ji son yarinyar na shiga bargon da
jijiyar jikinsa ya tabbatar kalmar
rabuwa da ita ko da ya furta to
yaudarar kai ne domin ba žai taba
iyawa ba.
Duk abin da take so zai yi
iya iyawarsa na ganin ta amince
masa ya na jin a jikinsa kamar ita
ce maganin cutarsa.
118
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ba zai taba yarda da ya yi
wasa da rayuwarta ba, ba zai bari
lafiyarta ta tabu ba. ya shafa
gefan fuskarta me bayyana karar
da kuruciyarta sannan ya yi ajiyar
zuciya yana yabawa kansa sa'ar
da ya yi.
Ko lokacin da ya soma
ganinta bai ga kyau a tare d aita
ba kamar yanzu. Shi kuruciyarta
kadai ya hanga. Ya mike tsaye
akwai bukatar ya fita wajen da za
a dauke masa abin da ke
addabarsa saboda kasancewa da
yarinyar nasa ya shiga wani hali
shi kuma ya fi son binta a hankali.
119
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya mike ya gyara mata
bargon da ya dan zame mata
sannan ya kara mata karfin AC ya
ja mata kofa ya fita.ya kira
yarinyarsa Janifer ta tabbatar
masa da tana nan cikin Ni'ima
Hotel can ya nufa to amma me?"
Duk yanda yake ganin
kuruciyarta yau din ma sai yaga
ta yi masa tsufa hoton fuskar
Hansa'u kadai yake gani dama
wasu abubuwan natare da ita da
baima ganewa idanuwansa su ba,
suka kuma zamo burin ganinsa.
Sai ya kasance ba shi da
walwala har jenifa ta fahimci
hakan yace baya jin dadin jikinsa
120
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
komai ya ji ya fice masa daga
ransa dole ya bar hotel din da ya
so ya kwana a can. Ya tsaya a
wani Bekiry ya jido kayan snacks
da ice cream caculate da sauran
tarkacen kayan zaki yana rayawa
a ransa yara sai kayan zaki.
Haka ya tsaya a wani
boutique riguna da dogayen
wandona masu bayyanar da surar
jiki ya zaba kaloli masu daukar
hankali kayan da suka fi daukar
hankalinsa ke nan a jikin mace shi
yasa ya fi son hulda da yaran
kabilu ba hausa ba su matsalarsu
kawai duk yarinyar daka taba sai
121
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ka ga ta san maza shi yasa bai
taba sha'awar aurensu ba.
Lokacin da Hansa'u ta ji
fitarsa ta samu karfin jiki domin
babu żazzabi a jikinta tunda ta
sha magungunanta, saboda haka
ta shiga wanka ta shirya cikin
doguwar riga ta materiyal su ma
tun nata ne na gida, ta raba
gashinta gida biyu ta daure ta
zauna a bakin gado da carbi a
hannunta tana karanta addu'ar fita
daga cikin wani kunci. Ta dinga
karantawa.
Ta tabbatar da babu kowa a
gidan domin Aminu ma ya yi
mata sallama ya tafi gida Uzaifa
122
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ma ta na jin lokacin da ya fita a
motarsa, kasan zuciyarta da
tunanin mahaifiyar dana kannenta
ita kam tana cikin kewarsu tana
cikin kishirwa ganinsu. Ta dinga
tuna wasu abubuwan da suka yi
lokacin da suna tare wani lokacin
ta share kwalla wani lokacin
kuma ta yi murmushi.
Har bata san lokacin da
Alhaji ya shigo da mota ba sai jin
muryarsa ta yi ya shigo da
sallama ta amsa da sanyin murya
ya fadada fara'arsa "Yauwa Baby
na jiki ya fara warwarewa ki yi
hakuri na jima sai da na fita na
tuna ba waya a hannunki bare na
123
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kira ki na ji yaya jikin na ki,
hankalina ya kasa kwanciya ban
ma gama abin da na ke yi ba, na ji
ba zan iya tsayawa ba, ban san
halin da ki ke ciki ba".
Yana fada yana fito da
kayayyakin da ya siyo mata daga
leda.
Ice cream ya bude ya debo
cokali "Bude bakin"
Ya kai bakinta ta kau da kai
cike da tsananin 6acin rai. Ya
dora shi a kan ciyarta "To dauki
ki sha tunda kunya ki ke ji, ban da
abinki nawa ki ke da ba za a baki
a bu a baki ba, ki ke jin kunya".
124
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya dauki daya robar Ice
cream din da ragowar alwowin ya
nufi dan karamin firij da yake
gefan gadon ya zuba a ciki.
"Ga ragowar nan in sun kare
ki yi min magana asiyo wasu ki
66
rage jin kunyar nan
Haka ya zauna yana ta
Iallabata har sai da ya ga ta sha Ice
cream din sosai sannan ya kamo
hannunta "Ta so mu je mu yi kallo
a falo za ki ji dacin jikinki
kwanciyar nan ta ishe ki haka, ta
dinga jin kamar ta kurma ihu gaba
daya ya gama matsa mata sai dai
ta yiwa kanta alkawarin yi masa
biyayya ko da hakan zai zama
125
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ajalinta, ko don kada ya fadawa
babansu da take tsoro shi ma
tamkar ajali.
Lallai kallon da suke yi a
yanzu na debe mata kewa wani
lokacin har ta kan dan yi
murmushi film din tom and jerre
ne kala kala har Alhaji ya fahimci
jin dadinta da kallon yawancin
abubuwa shi ke fassara mata da
hausa kallo na yi mata dadi sosai.
Har ya soma hamma ya
dubeta "Mu je dakina ki ta ya ni
kwana, ko ba wata matsala za ki
iya kwanciya ke kadai".
"Zan kwanta a dakina"
{
126
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya sake yin hamma ,to " ba
damuwa, amma ko da akwai wata
matsala ka da ki rufe kofarki,ki barta a
bude ba wani abu fa."
Ta daga kai kawai.
Ya ja gefen kumatunta ya na
murmushi ba magana sai daga kai.
"Mu kwana lafiya." Ya kwashi
wayoyinsa da makullen motarsa ya shiga
dakinsa.
Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya
face mata da gani,ita kam duk wani abu
da zai kai shi ga fatar jikinta tsananta
shiga tashin hankali ya ke yi. Domin tana
ji kamar daidai yake da shiga kwayoyin
cutar da ke jikinsa cikin nata jikin, shi ya
sa ba ta samu kwanciyar hankali ba, sai
ta ga ba ya wajen, don ta fuskanci kamar
ma da gayya yake yawan taba ta, domin
ba ya iya shafe 'yan mintoci ba tare da ya
127
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
riko hannunta ko janyo wani sanadi dfa
zai hada jikinta da na sa ba.
Duk da ta sakankance ta mika
rayuwarta, amma tsoro da fargaba.
aya.
Kash! mai karatu,a nan zan dasa
Shin ina Harira ta nufa? Shin ina
labarin ESP Abdul da Jidda matarsa?
Duk mu hadu a littafi na uku.
Daga mai debe muku kewa Khadija
Ado Yalwa(Khadija Adamu Shitu) don
yabo ko ba da shawara 09065291030 sai
na ji dga gare ku.
128
3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya