har dai ka ga ji da zaman
jiranta ka tafi.
34
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Su kuma har lokacin suna takure
waje daya suna kallon yanda ake shigowa da kulolin abinci da ruwa da
lemuka kala-kala, duk kuma abin da
aka kawo Asabe zata shio musu da
shi amman kananun kannensu ne
kadai ke iya ci, dominsu kowani
lokuta suna wuce wa ne ta shin
hankalinsu na daduwa saboda karfe
biyar da rabi ne dai dai a ka sa
lokacin da za a dauki amarya.
Kamar yanda Hansa'u bata iya
cin wani abu ba, haka Asiya da
Umaima.
Asiya ke ta kokarin tunasar da
Hansa'u yin addu'o'in tare da
zayyana mata wata hikima ta
musamman da ta gano wadda take
35
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ganin zata taimaka mata wajen
gujwar kamuwa da wannan cutar,
dukkaninsu zuciyarsu ta nutsu da
shawarar Asiya wannan su samun
'yar nutsuwa amma gabansu bai
dana dukamketoku ba, har zuwa
lokacin 'yan daukar amarya suka
zo, sun dunkule kansu waje guda
suka dinga wani irin kuka mai ban
tauşayi, da kyar aka banbare
Hansa'ų daga jikinsu, ji su ke yi
kamar wadda za a kai kabari ba
wadda ta samu karfin gwiwar
rakiyar amarya
Daga Asabe sai kawayenta da
suka yi ragowa suka tafi kai
amarya.
36
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Basu fi minti goma da tafiya
ba Lawan ya shigo ya taddasu a
daki.
"Au zama ku kai a daki ba za
ku fito ku gyara gidan ba".
Lokacin da uwarku tana nan
kuna barin ta yi cangal a cikin
gida wato yanzu kuna son ku nuna
ba ita ta haife ku ba shi yasa ku ka
makale a daki tun safe.
Haka suka ta shi duk jikinsu
ba kwari daya ta hada wanke
wanke tana yi daya kuma na
shara.
Nan da nan suka kammala
sallamar Asabe suka ji a lokacin
duk suna zaune a tsakar gida
kowacce ta yi tagumi Asabe ke
37
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
cewa "Kai masha Allah wannan ai
abin ku yi mata murna ne ba bakin
ciki ba, kun ga daular duniya
kuwa a gidan 'yar uwarku
Hansa'u. Ai duk wata 'ya mace ta
gidan miji ce kuma wata rana
'ya'yan gidan wasu ne Allah ya
baku ya tata kawai addu'ar da za
ku yi kenan"
Ta shiga daki tana ta kakkabin
zancen su kuwa Uzirin rashin sani
kawai su ke yi mata, amma ba
waddda ta ji wani sanyi a kan
daular duniya da ta ke ciki fada
domin rayuwar 'yar uwarsu yafiye
musu koma me za su samu tare da
ita.
38
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Lokacin da Aminu ke wanki a
kofar gidan ya dinga ganin jeran
gwanon motoci 'yan kawo amarya
nata shigowa cikin gidan ya tsaya
cak ya na zancen zuci kar dai
babar yarinyar bata yarda da
gaskiyar da na fada mata ba, ta
kawo 'yarta".
Uzaifa da.. yake zaune akan
farar kujerar yana karatun nes
magzine shima ya dago cike da
mamaki.
"Wai me ya ke faruwa a gidan
nan?"
Ya dubi Aminu.
"Ga shi nan kuwa kana gani
aure ya y1
وو.
39
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Uzaifa ya ce "To Allah ya
kyauta ya ci gaba da karatunsa
Karshe ma da ya ji hayaniyar mata
na damunsa sai ya nade kujrarsa
ya koma dakinsa, amma tunanin
ya hana zuciyarsa ci gaba da
karatu, to wannan bawan Allah
mantawa yake yi da lalurar da
yake tare da da ita,- shi ma yana
daga cikin jahilan mutanen da
basu yarda akwai kwayar cutar ba
ne, suna dauka talauci ne kadai
cutar tunda shi ga shi har yanzu
bata tagayyara shi ba, amma laifin
iyayen da suke ba shi 'ya'yansu ne
saboda kwadayin abin duniya yafi
yawa me rabon shan duka ai baya
jin bari.
40
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Da wannan ya rufe shafin
tunaninsa ya mike dan gabatr da
alwalar sallar magariba duk
jama'ar da suka yiwa Hansa'u
rakiya sun watse jin gidan take yi
shiru kamar ba wani mai numfashi
a cikinsa, sai kukan tsintsaye da
wani irin tausashen kamshi da
yake ta shiga hancinta.
Dama tuni ta zame jikinta daga
kan gadon da suka yi mata mai
sauki tun ma kafin su gama barin
gidan gani take yi zata iya daukar
ciwon ma a duk abin da ta taba a
gidan ta bude idanuwanta don
gabatar da kudirin da yake ranta.
Dakin ya hadu fiye da zatonta
kayan gado ne 'yan kasar turkeye
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
sai kyalli suke yi kamar madubi
dakin ya na da girman gaske an
ajiye komai bisa tsari gado da
wadrop madubi, sai dan karamin
firji abakin gadon paintin dakin da
tayels din farare ne, tas pantin
kayan gidon shi ma fari ne da
ruwan toka.
Zanen da yake shimfide a kan
gadon fari ne tas me adon furanne.
Standard A.C nata ba da sanyi
da wani irin ni'ima kamshi. A iya
rayuwar Hansa'u bata taba shiga
kayataccen wuri kamar wannan
ba, amma zamanta a gidansu ya
fiye mata: wannan zama na
mintinan a nan..
42
21
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Jakarta ta bude ta dauko
kwado me hde da 'yan makullaye
da Asiya ta bata ta nufi bakin kofa
ta duba kofar ta gogaggen katako
ne tana kyalli kamar madubi
gabanta da bayanta bata ga in da
zata sakala kwaďo ba,
gwiwowyinta suk ayi sanyi.
Hankalinta ya ta shi ya yin da
ta soma jin shigowar mota cikin
gidan ta tabbatar Alhaji Ahuta ne
ta soma zagaye dakin tana tunanin
in da ya dace ta shiga ta boye
kanta, kamar ance ga shi kawai sai
ta hango mukallin a kan window
dakin da sauri ta nufi wajan ta
dauko mukullin ya yin da ta ke jin
takun tafiyasa, na dada karatowa
43
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ta dinga gwada mukullayen can ta
ga daya ya ruf ta murda ta ji ta
rufo sosai a lokacin ya soma
kwankwasa kofar ta jingina
bayanta jikin kofar ta sauke
numfashi amma har lokacin
zuciyarta bata daina bugawa da
sauri ba,
"Hansa'u bude kofa ni ne
Alhaji bude".
Ya fada ganin ya nata bugu
shiru. Ya dan yi murmushi ya yin
da zuciyarsa ke tunsar da shi dama
irin wadannan yaran ba a rasa
tsoron namiji a ransu, me yiwuwa
ta rufe ne saboda tsoron daren
farko. Ya juya yana murmushi
"Lallai wannan karon ma 'yar
44
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
shela ya samu za a jima yana
amfanar kuruciyarta.
Ya ji yarinyar ta skae shiga
ransa ya na da tabbacin ko yunwa
ma zata fito da ita kafin wayewar
gari don haka ya koma falonsa ya
zauna ya kunna kallo ya cire
babbar rigarsa ya. dauko
gasasshiyar kaza daya da lemon
kwali ya soma ci cikin kvanciyar
hankali.
Yana zuba idon jin motsinta
amma shiru har dare ya yi nisa ya
gaji ya koma dakinsa ya kwantar
surar yarinyar na yi masa gezau
har cikin barcinsa.
Haka Hansa'u ta kasa rintsawa
saboda tsananin tsoro a iya tsahon
45
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
rayuwarta bata taba kwana ita
daya ba, a dakin ba tare da 'yan
uwanta ba, ga azababbiyar yunwa
da ta hana mata sukuni irin wadda
bata taba ji ba, gabanin sallar
asuba juriyarta ta kore ta yi
tunanin fitowa ta dudduba ko za ta
dace da abub da za ta saka a
cikinta.
Ta bude kofar a hankali
sannan ta leko ba alamar akwai
mutum a falon a hankali ta fito da
sanda tun kafin ta gama fitowa
kamshin naman ya cika mata
hanci tana fitowa kuwa ta samu
ldar a ajiye akan tebur ga wanda
ya ci ya rage a filet ledar ta dauka
cak ta juya dakin da sauri tasa
46
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
mukulli ta sake rufewa ta na
budewa ta na hamdala ga sarki
Allah Kazace guda da biredi da
lemon kwali a cikin ledar lallai
yunwa bata da hankali bare
Hansa'u da ta yi kusan wuni biyu
ba komai a cikinta sai ruwa.
Hannu baka hannu kwarya ta
soma cin naman.
Ba ta jima da soma ci ba kuma
a mai ya dinga ta so mata ta tafi
bandakin cikin dakin da gudun a
nan ta dinga amayo duk abin da ta
ci sannan ta yi alwala domin har
an fara kiraye kirayen sallar asuba,
ta na idar da sallah wani irin bacci
ya yi awon gaba da ita.
47
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Lokacin da Alhaji Ahuta ya
fito daga dakinsa bai yi mamakin
ganin ta dauki ledar Naman ba
domin ya san dole yunwa ta
addabeta ya yi murmushi sannan
ya nufi kofar dakinta ya dan
kwankwasa kusan sau uku bai ji ta
bude ba, a zahiri ma bata ko ji shi
ba, saboda baccinta da ya nisa.
Har ya game dukkan abin da
yake yi ya fita ya dai lekata ta
window ya kuma hangeta a kan
sallaya tana barci ya yi murmushi
"Haba 'yan mata haka ake yi eye
amma na san yanda zan bullo
miki"
Ya fada asarari ya yin da yake
kare mata kallo Aminu da ya tảho
+8
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
karbar jakarsa ya na jin furucin
nasa ya sunkuyar da kai yana
gaishe shi. ya amsa da murmushi
ya mika masa wani mukulli "Kа
wanke wancan farar motar".
"Yanzun nan dai Uzaifa da ita
zai fita yau kada ka 6ata masa
lokaci da safe nan zai fita"
Aminu ya karbe mukullin
"Yanzun nan z aa wanke Alhaji.
Ya kara shi har bakin motar ya
raka shi sannan ya dawo yana
wanke motar yana tunanin halin
rashin tausayi irin na Alhaji
Ahuta.
Shi dai ya ji dadin kawai ba
ruwansa da matsalar da yake saka
'ya'yan mutane a ciki. Hansa'u
49
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
bata farka ba har misalin karfe
daya da rabi na rana, ita kanta bata
san ta yi barci me tsayi haka ba,
yanda ta ji anata kiraye kirayen
sallar azahar abin ya bata mamaki
da sauri ta shiga bandaki wanka ta
soma yi sannan ta yi alwala duk
son ta sami karfin jikinta ne.
Ji- ta ke. yi kamar iska zata
dauke ta da kyar ta iya idar da
sallah ta gane abu mai dumi take
son sawa a cikinta to kuma kafin
ta ci wani abu in ba haka ba zata
iya amai. Ta murda kofar dakin a
hankali sai ta ji kamar ana motsi a
falo don haka ta tsaya tana
ssauraran abin da ke faruwa muryar
wani namiji ta ji yana rera wakar
50
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
jinin jikina ta bude a hankali ta
leka wani saurayi ta hango
wankan tarwada da mofar a
hannunsa ya na ta goge tayal yana
wakensa cikin kwanciyar hankali.
Sannan ta samu karfin gwiwar
bude kofar ta dai san ko Alhaji Na
wajan ba zai iya haike mata a
gaban wannan saurayin ba.
Aminu yana tsaka da aiki yaga
an bude kofa an fito cak ya tsaya
ya bita da kallo kamar yanda ya.
zata Faramar yarinyace sosai
kuma yar wannan matar domin
tsananin kama da suka yi.
Ganin ya tsaya yana kallonta
ya sa ta ce masa "Sannu da aiki"!
Yawwa
51
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya amsa mata da sauri har
muryarsa na sarkewa ya ci gaba
da binta da kallo kai jama'a yanzu Alhaji me zai diba a jikin wannan
baiwar Allah kankanuwar yarinya
wani irin tausayinta ji yana
shigarta hade da mamaki yanda a
ka yi mahaifiyarta ta yi watsi da
gaskiyar da ta zo nema ya kuma
gaya mata ta yarda ta kawo 'yarta
wannan gidan.
Hansa'u da ta wuce shi ta yi
sa'a kofar da ta nufa kichin ne ita
ma ta nufe ta ne don ganin ita ce
abude ita dai a jikin hoto ta taba
ganin irin wannan kichin din don
haka babu yanda z aa yi ta iya
dafa koda ruwan zafi a cikinsa duk
52
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kowa da kayan shaye manya
manyan gwangwanayen madara
da ta yi tozali da su a kichin din ta
tsaya cak tana kalle kalle har
Aminu ya shigo da moffer а
hannunsa da alama kiching din ma
goge shi zai yi.
Yanda ya ga tana tsaye ya san
tana da wata bukatar-ne ya. се
"Akwai abin da ki ke bukata ne?"
Ta dan yi murmushi "Ruwan
zafi na ke son dorawa amman ban
iya kunna wannan abin naku ba".
Shi ma sai ya yi murmushi
hade da sakin moper hannunsa ya
nufi gurin gas din "Zo ki ga ni".
53
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya murda ya kuna sannan ya
kuma murdawa ya kashe ya ce kin
66
gane yanda ake yi".
Sannan ta kunna ita ma ya
dauko kettle din dafa shayi, ya се
in ma ruwan zafi ki ke so idan ki
ka jona kettle din nan a socket
mintina kadan zai tafasa kin ga sai
ki yi abin da ki ke so ya nuna mata
wajen kayan abinci sannan ya ci
gaba da aikinsa.
Ta koma dakinta ta dauko
ragowar namannan ta zuba masa
maggi ta soya abinta domin ita
gashin bai mata dadi ba.
Lokacin da ta fita tuni Aminu
ya fiya gama aikinsa, ta raba
komai biyu ta hanyar da ta ya fita
54
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tana waiwaye in da zata ganshi
tana karewa gidan kallo. Fadar
kyawun harabar gidan ma kadai
bata baki ne, can ta hango shi
cikin rumfar da ake aje motoci ta
dinga daga masa hannu har ya
gane kiransa take yi. Sannan ta се
"Yaya ne mene sunanka".
Ya ce "Aminu" ta yi
murmushi "Ba zan iya çe maka
Aminu ba zan dai ce maka Yaya
Aminu".
"To na gode kanwata
Ya ji dadin karramashin da
ta yi sai yake jin kamar
kanwarsa ce ta jini".
Ta shiga dakinta ta kulle
kanta sannan tasha tea da bread
55
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
da naman da ta soya ta koshi har
ta rage na anjima, sai kuma
kewar gida da yan uwanta ta
dame ta.
Addu'ar ta Allah ya kawo
sanadin da zata bar gidan nan
batare da wani abu ya same ta
ba, lokaci lokaci tana sharar
kwalla ita kam bata san wani irin
uba ne da su ba, ta na kallon dan
Baba a cikin idanuwanta yana
kuka yana tambayar me ya faru?
Babansu na tura shi, ta rintse
idanuwanta wasu kwallah me
zafi ta zilalo ko za a kai Hansa'u
gobe ta mutu sai an kaita gidan
Alhaji Ahmad Ahuta. Lalatattun
56
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
'ya'yanki marasa tarbiya to me
mugun hali aniyarki ta biki".
Munanan kalaman babansu
ke nan akansu da mahaifiyarsu
suka dinga amsa kuwwa cikin
kunnuwanta, kwakwalwarta ta
daketa shigar da tsanarsa cikin
zuciyarta da ke dada tafasa ta
dinga daukar zafin da ya mika
sakonnin cikin hanyoyin
sadarwa jikinta, nan da nan
jikinta ya dauki zafi iskar da ta
ke kadawa tana shiga cikin
jikinta ta zame mai tsananin
sanyi wani irin yanayi ne ya
dinga shigarta me kama da
zazzabi ta takre waje guda
57
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
amma bata jin kasalar da zata
iya kwanciya.
Ta dinga jiyo motsi a falo a
kai a kai. Bata iya yunkurin tashi
ta boye kanta ba, to ko ta gudu
ta dogara ne da kulle dakin da ta
yi duk da hakan bai hana
gabanta ci gaba da faduwa ba.
Can ta ji ana kwankwasa
mata kofa zubawa kofar ido ta
yi kawai tana sake takure jikinta,
har mai bugun ya gaji ya daina.
Can kuma sai ta ji muryar
Aminu a bakin windo yana cewa
"Kanwata ga abinciki nan a
bakin kofa ni zan tafi gida sai
gobe in Allah ya kai mu".
58
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Muryarta a dashe ta ce "To
na gode yaya Allah ya tashe mu
lafiya ya ce ameen".
Tana jiyo takun tafiyarsa ya
na 'yan wake wakensa. Тa
tabbata ke nan ita kadai ce a
gidan nan. Ta sauke ajiyar
zuciya sannan ta mike ta bude
Kofa.
Foodflasks ta gani da plates
ta dauka ta bude jlollof din
taliya ce da ta sha busasshen kifi
sai kamshin species ne kadai ke
ta shi.
Cikin zuciyarta tana raya wai
Aminu ne ya yi wannan girkin
ko me.
59
Hadiza Adö Yalwa Garari 2
Kamar yanda Alhaji Ahuta
yai ta bugun kofar ta ji ya kama
yau har cikin talatainin dare
kuma duk Hansa'u na jin shi ta
yi shiru sai dai lamarin na yau ya
tunzura zuciyarsa ya fahimci
cewa yarinyar nan zata iya
zamowa me taurin kai don haka
ya dace ya dauki mataki a kanta
ya dinga jero tsaki lokaci zuwa
lokaci da haka har bacci ya
dauke shi.
Washe gari bai bi ta kanta ba
lokacin da ya shirya har ya tafi
daga gidan, ya dai kudurta a
ransa cewa da zarar ya dawo yau
60
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
din nan zai sauke mata duk abin
da yake kanta.
A yau Huzaifa baya fita da
wuri kuma ga al'adarsa in har
yana gida da kansa yake
shiryawa kansa break fast sai dai
Aminu ke ta ya shi wasu
abubuwa.
Lokata da dama tare suke
girki in har yana gida, domin
sun saba da zama su kadai a
gidan kuma baya son cin abincin
sayarwa.
A yau ma ya fito kitchin din
sanye da kayan bacci Amin ke
fearar dankali yana wake61
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
wakinsa shi kuma ya na wanke
kaza.
Hansa'u tunda ta ji motsin
Aminu a kitchin ta ji tana
sha'awar fitowa ita ma ko dan ta
dafa abin da za ta cі.
Ta na sanye da doguwar
rigar atamfa wadda aka hada
dinkinta da yadin satin wanda
tun sallar bara waccen
Ummansu ta yi musu tare da su
Umaima rigar har ta dan dage
mata bayan laushin da kodau din
da ta yi, duk yawan kayan da
Alhaji Ahuta ya zuba mata alefe
da wanda yake kawowa dinki
62
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
amma bata taba sha'awar saka
kayan ba.
Wadda aka kawota da itama
Asabace ta takura mata ta saka,
har kuka ta yi saboda takaicinsa
saka kayan.
Ta shiga kitchin din da
sallama ganin Huzaifa a tsaye
yasa ta tsaya cak ta kasa
karasowa ciki, ta kuma kasa
komawa, ba ta taba tsammanin
Aminu shi da wani ne a ktchin
din ba.
"Kanwata shigo mana mi ki
ke so?"
Ba ta ba shi amsa ba sai ta
soma gaishe shi ya amsa sannan
63
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ta gaida Uzaifa ba amsa ba ya
dai juyo ya yi mata wani irin
kallo sannan ya maida kansa ya
ja tsaki da ya bayyana asarari ya
ci gaba da abin da yake yi wai
dubi irin yaran da Alhaji yake
aurowa a cikin gidan nan irin
yaran da ko matsayin 'yan aiki
basu ishe mu
Ya fada a cikin zuciyarsa
sannan ya sake jan bayanannen
tsaki. Yadda Huzaifa ya yi mata
da yanda ta ga yanayinsa lallai ta
fahimci me matsayi ne a gidan.
Ba don ma ta san Alhaji Ahuta
bai taba haihuwa ba da sai ta ce
dansa ne sai ta ji ciwon abin da ya
yi mata.
64
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Aminu da ya ji rashin dadi har
'yar kunya ta kama shi sai ya ce
"Babban yaya kenan Uzaifa bai
fiya zama a gida ba".
Ta dan yi murmushi.
"Me zan ta ya ku da shi yaya
Aminu, ban saba da zama ba aiki
66
ba duk sai na ji wani iri
-Aminu ya yi dariyar yake yanasatar kallon Uzaifa yaga yanayin
da zai nuna domin ya san halinsa
da muguwar kyama ba kowa yake
yarda ya taba masa abin da zai ci
ba, ya kowayi sa'a yana aika masa
da harara ya ce "Ki je ki zauna
kanwata hutu ne ya zo miki kin ga
kuwa dole ki huta"
65
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Hansa'u ta yi murmushi kawai
don ta kula da irin amsar da
Uzaifa ke bawa Aminu da ido ta
juya zuwa nata dakin maimakon
yin abin da ta fito yi dafa ruwan
tea.
Bayan sun gama Aminu na
zuba na Hansa'u Uzaifa ya dube
shi "Baka dibi naka ba wannan
kuma na waye?"
وو" Na amarya mana"
"Wai kai ina ruwanka da.
yarinyar nan wanda ya ajiyeta
bai bata abincin ba sai mu ne za
mu dafa ta ci"
Aminu ya e "Sorry oga ga ni
na yi muntsare mata in da zata
66
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
dafa bai kamata kuma mu dafa
mu hanata ba".
Uzaifa ya ja dógon tsaki
"Kai dai mugun shisshige ne
wallahi da kai"
Ya fada ya yin da yake fita
daga kitchin zuwa na shi dakin.
Aminu ya ajiye mata a bakin
"Kofarta sannan ya koma kichin
ya dauki na shi ya wuce can kam
bancin a harabar gidan ya zauna
zuciyarsa cike da tausayin
Hansa'u yarinya kamila mai
sanyin hali tana gama yin break
fast ta shigo kitching din a nan
ta debo tukuwane da filet din da
aka bata duka ta wanke tana
67
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
share kitchin din Aminu ya
shigo ya tarar ma ta gama aikin
da ya zo yi ya ce "Na gode aiki
na ne ai".
Ya ce "Kin ga Uzaifa don
yau ka da ki dauke shi wani iri
yana da saukin hali sosai, shi
son girmansa ne matsalarsa".
T dan yi murmushi ta gane
Aminu yana gani kamar ta damu
ne da abin da ya yi mata ta се
"Ai dan manya ne yaya Aminu
dole ya so girma ba wata
damuwa".
Ya ace "Gaskiya ne
96
wannan.
68
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Shiru ya ratsa na wani lokaci
Aminu ya ce "Kwanaki wata
mata ta taбa zúwa makotan
gidan nan don binciken aure sai
na ke ganin kamar mahaifiyarki
ce saboda tsabar kamar da ku ke
yi.
Hansa'u ta dago kai cike da
mamaki nan da nan idanuwanta
suka kawo kwalla muryarta a
sarke ta ce "Eh Ummanmu ce
ashe kana nan lokacin da ta zo".
Ya yi murmushi ni ne ma
nan wanda ya fada. mata
gaskiyar al'amarin amma na yi
mamaki da na ga an kawo ki
gidan nan".
69
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ya gabatar mata da tambayar
da take cik ransa.
Idanuwanta suka ci gaba da
zubo da kwalla cikin rawar
murya ta ce "Ummanmu bata
nan ne"
Daga nan ta juya da sauri ta
koma dakinmta.
Ya bi ta da kallo har ta 6сасе
masa da ga ni
Ummanmu bata nan ne ya
nanata kalmar a sarari hade da,
bude hannuwansa na rashin
sanin fadar maganarta.
Haka kawai ya ji yana son
shiga al'amuran yarinyar yana
son taimaketa don yà kula da
70
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
matakin da ta dauka, ba abin
dogaro ba ne, to amma me ye
abin yi.
Tunanin da yai ta damunsa
ke nan har ya bijiro mata da
tambayar da ya san ta girgiza
zuciyarsa.
Ta dora kanta a kan
gwiwarta ta sakale hannuwanta
jikin kafafuwanta kuka ta ke mai
sauti har da shessheka.
Ba ta da juriyar duk lokacin
da ta tuno Ummansu da 'yan
uwanta tana jin ukuba a
rashinsu.
Sam ta manta ba ta rufo
kofar ba har ta ji diran motar
71
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Alhaji bata motsa daga in da
take ba ba zato sai ji ta yi an
murda kofa an shigo.
Af irgice ta dago sai kuma ta
mike a razane don ganin Alhaji
a tsaye a gabanta, ta fara tsalle
tana zagaye dakin tana cewa don
Alla don Allah".
Ya ce "Lafiya me ya faru?
Nutsu ki min magana me ya
firgita ki me ya faru?""
Ba ta tsaya saurarensa ba ta
fito da gudu ta samu dan wani
sako bayan kujera ta labe har ya
zo ya shige bai ganta ba ta na ji
yana waya yana cewa. "Ka da ku
bar yarinyar nan ta fita daga
72
Hadiza Ado Yaiwa Garari 2
gidan nan" da alama da masu
gadi ya ke dama abin da tai zato
ke nan shi ya sa bata yi yunkurin
fita ba.
Ta na ji ya yi mata nisa ta
mike da sauri ta nufi cikin dakin
ta rufe kofar da sauri, sannan ta
jingina bayanta da jikin kofa
tana mai da numfashi.
Daga Aminu har masu gadi
sun tabbatar masa cewa ba ta
fito daga falo ba sannan ya
tabbatar da cewa boyar masa ta
yi, ba karamin haushi ta ba shi
ba ya kum ayi alkawarin fita
daga sabgarta na zuwa wani dan
lokaci da yake ganin zata fada
73
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
tarkonsa wanda bata isa ta fita
daga ciki ba
Washe gari ya shiya tafiya
Abuja shi da Uzaifa wanda za ta
dauke su twason sati guda.
A bakin Aminu l hi labarin
tafiyar Alhaji. Ta yi farin ciki
sosai ta sake har ta kan iya
fitowa falo su yi kallo ita da
Aminu.
Ta ko yi girkuna irin na
zamani kala kala a wajen
Aminu, har tana mamakinsa
kamar ba namiji ba yanda ya
kware sosai ta sami rangwamin
damuwa matuka.
Σ
7+
४
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Ranar da Alhaji ya cika sati
daya cif ya kama ranar lahadi
ne. Tunda yamma ake tafka
ruwa kamar da bakin kwarya har
zuwa karfe tara na dare tun tana
tsaye a bakin window tana
kallon yanda ruwa ya ke sauka
har ta gaji da tsayiwa.
Misalin karfe takwas da 'yan
mintina ta yi sallarta ta isha'i
tana cikin karanta littafinta na
addu'o'i bacci barawo ya dauke
ta. Har bata ji diran motar Alhaji
ba wanda tun bayan sallar
la'asar ya sauka a garin amma
saboda a yanayin ruwan sama da
75
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ake yi basu samu karasowa ba
sai yanzu.
Ya shigo falon da sauri duk
yanda yake kaucewa dukan ruwa
sai da babbar rigarsa ta jika tun
daga bakin kofa ya cire ta har
lokacin ya na jin saukar ruwa
yana murmushi yana yi ne
wannan da duk haukan "da
yarinyar nan za ta yi ba wanda
zai ji ciki har da Uzaifa da yake
jin nauyinsa kamar dan cikinsa,
kuma shi ne da kansa mafi
kusanci da su wanda bayan
kofarsa ta waje akwai wata
kofar da zata iya sadaka da
dakinsa a cikin falon wanda ko
76
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
kiransa yake son yi ba sai ya
zagaya ba haka shi ma idan yana
son shigowa ba sai ya yi wahalar
zagayowa ba.
Sai dai ba kasafai Uzaifa ke
amfani da kofar ba, amma da an
yi wata kwarafniya me karfi
Uzaifa zai iya ji
Wannan danyar yarinyar
kuwa ya san zata iya yi masa
kwaroroto kafin ya samu ya
cimma manufarsa a kanta.
Jallabiya mai gajeran hannu
kawai ya saka ya fito daga
dakinsa hannunsa dauke da
mukullayen gidan gaba daya
wanda a ciki ya gama gane na
77
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
dakin Hansa'u dama nemansu
ya yi ya rasa tun farko.
Ya kuma so ya bita ta lallami
shi yasa bai matsa da binciken
su ba.
Yan da ya ga tsarinta shi ya
tilasta masa nemo su domin ya
yi gaggawar biyan bukatar ransa
ya ajiye mata taurin kai.
A hankali ya zura mukullin
ya bude kofar yanda ya hangota
tana barci ya kidima shi jikinsa
har rawa ya ke yi, ya dinga
tafiya ciki sanda har ya isa inda
ta ke a kasa kan darduma
akwance tana sanye da doguwar
riga mai santsin jiki ruwan hoda
78
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ta bayyana matukar kuruciyarta
dan kwalin ta ya zame kitsonta
shiku ya tattare a tsakiya kai ta
saka ba ta daure jelolin ba.
Ta yi haske fiye da sanda ya
santa fatar jikinta ta yi wani irin
laushi da bayyana hutu ya kasa
hakura yanda zuciyarsa ke
wassafo masa abubuwa a tare
da ita maganadison ya ci gaba
da tsarin figarshi gareta ya kai
hannunsa kan abin da yafi
daukar hankalinsa.
Kamar wadda wutar lantarki
ta ja haka ta farka a tsorace sai
dai rikon da ya yi mata ya zarce
wanda zata zille masa hankalinta
79
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
ya kai karshe wajen ta shi ĝi ta yi
kamar ya soma zuba mata cutar
jikinsa ne.
Ya so ma magana. cikin
muryar rada rada "Ki kwantar
da hankalinki ni fa mijinki ki ne
ki saki jiki da ni duk abin da ki
ke zan ba ki gida ne, ko mota ko
yawon...
Wani karfi ta ji ya zó mata
ya yin da shi kuma kasala ke
raunata karfinsa ta hankade shi
daga gare ta ta nufi kofar fita
tana budewa ta ga ta budexta fito
bata ma san in da takedje fa
Kafarta ba.
0א
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
Har sai da ta fito ta samu
wani sako da ba shi da yalwal
haske shukokin sun sa ya dan yi
duhu ta rakube a wajan ta na
hakin gajiya domin ta san in har
ta sake ta kai kanta bakin get din
gidan maigadi ba zai barta ta fita
ba, koma dole ya mika ta
wajansa.
Har yanzu ana yayyafi a
garin iskar ruwa ma sanyi na
kadawa ko ina, sanyi ne da ke
gigita mutum nan da nan ta
soma rawar sanyi har hakoranta
na hadawa da juna.
Alhaji Ahuta kuwa da ya fito
bai ganta ba ya ja tsaki ya koma
81
Hadiza Ado Yalwa Garari 2
dakinsa shi kam ya gama gajiya
da wannan lamarin na