Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GARARI VIBB PUBLISHERS GARARIHADIZA ADAMU SHITU (Matar Muhd.Nuhu Namarwa) Hadiza Ado Yalwa Garari 2 GARARI 2 NA HADIZA ADAMU SHITU (MATAR NUHU MUHAMMAD NAMARWA) 1 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Garari part 2 aba daya jikin Harira ya Ggama mutuwa hankalinta ya yi matukar tashi zuciyarta ta duguznuma, tunaninta ya rarraba akan wannan bakin albishir din da matan suka zo mata da shi, shin da gaske ne mutumin nan da zai auri Hansa'u yana da cutar Aids, ko kuwa makirci ne irin na mata ina zata sami wadannan tambayoyin wacce hanya za ta bi ta gano kan al'amarin to in ma da gaske suke ya zata yi ta raba wannan auren da Lawai ya dora burinsa kacokan a kai, suma ya zame musu wata madafa a rayuwa. Domin ban da wannan gidan da ya zama mallakar mutumin ne da suke ciki ya zama duk motsin da ta yi sai ta ga wani abun da ya zamo shi ya sai musu. 3 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Yanzu matsalar kayan abinci ta kau store dinsu cike yake da kayan abincin da ya sai musu banda kudaden da yake dankara musu, duk kwana biyu idan ya zo zance wajen Hansa'u. To amma wannan alkairin da yake musu zai iya sa zuciyarta ta danne wannan maganar da ta ji wadda barinta tamkar salwantar da rayuwar 'yarta ne, sam bata jin cikin zuciyarta zata iya wannan dauriyar. Tana son 'ya'yanta tana son inganta rayuwarsu da farin cikinsu. Wannan tunanin. ya hana idanuwanta rintsawa kafin wayewar gari zuciyarta ta Karfafa da shawarar da ta yanke na fara zuwa bincike. Washe gari ya kasance ranar Lahadi ne ta bi kwatancen da Lawai ya taba yi na gidan Alhaji Ahmad Ahuta. Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Unguwar shiru bata cika da yawan jama'a ba amma hakan bai hana ta gano gidan Alhaji Ahmad ba, saboda shahararshi, a unguwar. Gidane katon gaske fiye da zatonta ma aikata na ta fenti daga ciki ga katon get din gidan a rufe ta sauke ajiyar zuciya tana karantar makwabtan gidan da take ta tunanin shiga. Daya daga cikin gidajen ta yi tambaya game da shi, duk yawancinsu a rufe kofofinsu suke. Daga can ta hango kofar wani gida a bude wata budurwar yarinyar ta fito ta tsaya tana rike da kofar da alama wani take jira ta nufi gidan ta yiwa yarinyar sallama, ita kuwa ta amsa da fara'arta ta gaishe ta sannan ta bata hanyar shigewa a take ta samu karfin gwiwar shiga daga ainihin gidan zuciyarta cike da addu'ar 5 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 samun nasara a kan abin da ta shiga nema. Ta yi sallama matar gidan ta fito daga kiching da ga ni ba tambaya mahaifin budurwar yarinyarce saboda kamanin. Ita ma da fara'a ta karbeta sannan tai mata ta yin shigowa daga cikin falo, bata musu mata ba, ta bi bayanta zuwa cikin wani katafaen falo wanda yasha kayan alfarma sai kamshin turaren wuta dan maiduguri ke ta shi. Bayan sun gaisa shiru ya ratsa a tsakani ya yin da Harira ke ta tunani ta inda zata so ma magana har matar ta dan Kosa ta ce. "Baiwar Allah daga ina ban fa gane ki ba?' Harira ta yi murmushi. "Ba ma ki sanni ba, ni ma kuma ban san ki ba ai. A takaice ni ce mahaifiyar amayar da makocinku zai aura Alhaji Ahmad 6 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Ahuta, na zo ne nan ganin ku ne makotansa, kuma da na kowane, dan na yi bincike a kan wani abu da ya shige min duhu". Take ta zayyanewa matar zancan da aka sanar da ita a jiya da yamma, kuma.da abin da ya kawo su. Ta dora da cewa "Shine na shigo nan dan yin bincike tun da dai da na kowane, kuma za ku iya sanin wani abu game da shi, tunda ku makotansa ne kuma al'amarin ya hada har da mutuwar matarsa da kuma sakin wasu matan nasa Nan da nan fuskar matar ta juye zuwa kalar tausayi. Sai dai ta kasa maganar har zuwa 'yan dakiku sannan ta nisa. "Ni dai abinda na sani matarsa da ta mutu ta yi doguwar jinya, amma ban san wanne ciwo ta ke dauke da shi ba, 7 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 har zuwa lokacin da Allah ya yi ınata rasuwa, sauran matan da yake aure ban ma sansu ba, tunda ba shiga gidansa muke yi ba, saboda baya son a dinga zuwa masa gida". Harira ta sauke ajiyar zuciya tana godiya. Duk. da bata samu bayani sosai yanda ta ke so ba, amma shimfidar fuska tafi ta tabarma, inji Malam Bahaushe. Bayan ta fito daga gidan har ta fara nisa sai ta ji ana cewa "Hajiya tsaya". Sai ta waiwaya don ta ji mai maganar. Kamar da ita yake, sai ta ga wani saurayi ne, wanda tun shigowarta gidan ta kula da shi yana wanki a tsakar gida. don haka ta tsaya cak! Tana saurara karasowarsa. 8 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 "Hajiya na ji tattaunawar da ku kai da Maman Fati, ganin cewa ina da masaniya akan wasu abubuwan da ki ka tambaya yasa na biyo bayanki, amman mu fara barin layin nan tukun na". Batare da ta yi masa musu ba ta fara tafiya ya ce "Ni suna na Aminu yaron gidan Alhaji Ahuta ne ni, ina yi masa 'yan aikace aikace saboda na shigo ne nan gidan danna gyara musu injinsu daya lalace na ji hirarku tare da Maman Fati, ita kanta tsoro ne ya hana ta fada miki gaskiya, ni kuma na ga lamarin ba na 6oyewa ba ne, musamman tun da ya shafi lafiya da barazana da rayuwa tunda ki ka zo neman gaskiyar magana bai dace a 6oye miki ba, tabbas akwai mun san abubuwa a boye kamar yanda ki ka ji a kallah na zauna da matan Alhaji Uku kuma duk 9 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Kananun yara ne da basa wuce shekaru sha biya sha shida. Asma'u ya aura wadda bata fi shekara biyu ba ta fara matsananciyar cuta wanda har sai da aka kwantar da ita, a Asibiti kuma tana Asibiti ya dankara mata saki har uku tun daga ranar ban kuma jin doriyarta ba. Sannan ya kuma auro wata yarinyar Maimuna ita kuma shekararta daya ya sake ta ita ma bayan tasha fama da rashin lafiya, sannan ya auro Bahijja ita ce ta haura shekaru biyu Allah ya yi mata rasuwa bayan tasha fama da jinya wata rana ina aiki na ji yana hira da abokinsa a waya yana fada masa wai malaminsa ne ya gaya masa zai rabu da ciwon da yake da shi, ta dalilin auren wata yarinya me kananun shekaru, cutar zai samu maganinta gaba daya, amma sai ya yi aure auren mata a cikinsu zai 10 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 auri maganin cutarsa na ji ma ina tunanin wacce irin cuta ce wannan. Duk da ya taba yin wata jinya mai tsanani kamar ba zai rayuwa ba, amma a wancan lokaci cutar typot akace ke damunsa. Wata rana ina sharar dakinsa na tsinci wata takarda sakamakon cutar kanjamau da sunansa a jiki, kuma bata fi wata guda da yin wannan hirar ta su da likitan ba ya auro Amina, ganin kankantar yarinyar yasa na dinga tunanin Allah yasa shawarar likita ya bi ya aureta, ita ma batafi shekara ba ta kamu da matsanancin ciwo daga nan ya sake ta, sannnan ya auro wannan wadda ta mutu kwanan akanta ne na gane ciwon mutuwar yarinyar saboda tun farko bata son Alhaji kuma ta yi iya kokarinta ta bar shi amma iyayenta suka dage a kan 11 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 zamanta da shi wanda daga karshe ita ma abinda ya faru da suaran matan ya faru da ita. sai dai ita ta samu sassauci saboda bai saketa ba sai dai ta zauna a Asibiti tsawon wata uku har ajali ya sauka akanta sakamokon buguwar da zuciyarta ta yi Ai kafin ya gama bawa Harira labari gumi ya gama jika jikinta ya soma rawa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki Inna tunda Allah ya sa ki ka sa ni batare da an yi auren ba, amman duk hanyar da. za ki bi ki bita don ki hana yarki shgowa gidansa, don ceto rayuwarta. Harira ta share gumi "Na gode na gode dan nan Allah ya saka maka da alkairi ya sa ka gama da duniya lafiya”. Ya ce "Amin Umma ai yiwa wani yiwa kai ne domin ina da kanne ni ma. Sun rabu amma jikin Harira bai daina bari ba, saboda ta ga gaskiya a 12 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 tare da shi kuma ta yarda da abin da ya gaya mata, saboda yanda ta shigo cikin tashin hankali gaba daya su Asiya na tsakar gida, amma suka biyo ta aki, suna tambayar lafiya. Duk da ta ce musu ba komai hankalinsu ya kasa kwanciya musamman Asiya da ta zauna ta zuba tagumi sai Umaima ce ta ci gaba da lissafin kawayenta za su kaiwa katin gayyatar biki. Wanda dama daga ita sai Asiya suke ta shirya shiryen ita kam ko zama awajen bata yi ba, ta debo wankin kayanta ta na ji domin lamarin auren nata jinsa kawai take yi kamar tatsuniya. Yanayin da Ummansu ke ciki ya dami zuciyar Asiya ta kuma yi duk wata hikima da ta gane ko Umman zata gaya mata abin da ke damun zuciyarta amma sai Umman ta nuna mata ba komai 13 3 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 bayan ga komai din ta na gani a shimfide a kan fuskarta sai dai ta kasa bayyana mata. Tuntuni ta ke ta sake sake akan abin da zai iya zama sanadin damuwar Umma, babban tashin hankalinta ace wata matsala ce game da auren Kanwarta Hansa'u wanda alamu ya soma nuna hakan.. Tana gyara su Mahmud wajan kwanciya. Ummansu na tsakar gida tana dibar ruwa da za ta yi wanka wani yaro ya shigo da sallama "Wai ana kiran Hansa'u" Muryar Umma ta ji ta ana amsawa yaron "Je ka ce bata nan Ita kanta Umman bata san lokacin da wannan kalmar ta subuce mata ba ta fito daga bakinta ba. Asiya da ta tsaya cak cike da mamaki har Hansa'u da ke kwance a 14 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 kan tabarma sai da ta mike zaune sun hada ido da Asiya, amma babu wacce ta iya magana da 'yar uwarta. Bayan mamakin yanda ta iya sharara karya lokaci daya har da mamakin dalilin karyar. Ita kanta Umma jikinta ne ya dauki rawa ji take yi kamar ma ya shafawa Hansa'unta wannan ciwon sai gata ta zauna cikin tashin hankali sunan shi kawai da ta ji ya gama girgiza zuciyarta. Asiya dake hangota ta window ta fito da sauri "Ummana ya ya dai me ya ke faruwa?" "Dauki wannan ruwan ki samin a bandaki" Ta fada ba tare da ta bata amsar tambayar ta ba. ta yi yanda ta ce, amma ita ta sake tsinkewa zarginta yana son zama gaskiya koma me yake ta da 15 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 hankalin Umma yana da alka da auren Hansa'u, koma me Lawai zai yi yau za a yi ta ta kare, dan ba zan kai 'ya ta ga halaka ba. Saboda son duniya abin da Harira ke ta nanatawa kenan a zuciyarta. Har zuwa lokacin da Lawan ya dawo lokaci ne da ta ke tsammanin gaba daya yaran sun kwanta barci. "Yau na sha wahala wallahi.tunda na fita nake yaron rabon katin bikin nan manyan abokaina, ba ki ga yada suke yi min karaba". Ya fada ya yin da yake ajiye hularsa ta hango tudun kudi a aljihunsa yanda yake fara'a ta san cewa ba kanana kudi ya samo ba ba a wajen abokansa da kyar ta iya tattaro karfin gwiwar ta ta ce masa "Ka kuwa yi bincike akan mutumin nan?" "Wa ke nan tukunna?" 16 Hadiza Ado Yalwa ma. Garari 2 Ya mayar mata da tambayar shi "Alhaji Ahmad ahuta mana" Sai ya yi dariya "Ni na ga randa kauyenci zai barki Harira ke kin san waye Alhaji Ahmad Ahuta kuwa? То duk garin nan babu wanda bai san Alhaji Ahmad ba, to wani bincike zan yi a kan shi bayan kowa ya san shi ba 6oyayyen mutum ba ne". Harira ta sauke ajiyar zuciya. "Eh tabbas ba 6oyayyen mutum ba ne shi yasa ma al'amuransa kyawawa da munana ba za su boyu ba”. Daga nan ne ta so ma ba shi labarin matan da suka zo wajenta har zuwa binciken da ta yi a kai da cewa yana dauke da cutar kanjamau 17 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Nan da nan annurin fuskarsa ya dauke cikin tashin hankali da hargowa ya ce "Wato ke duk abin alkairin da zai same ni sai kinn yi kokarin kin haramta min shi, shi ne za ki bullo da maganar yana da aids to ba aids ba in ma Asibitin Zana ne a kansa sai anyi auren nan, kuma dai 'ya dai ta wa ce ni na ke da iko a kanta, in ma bakin ciki kike yi da samun arziki da rufin asirin da Allah ya yi min ta sanadinshi, to sai dai bakin ciki ya kashe ki, domin ko za a kaita yau gobe ta mutu sai an yi wannan auren babu fashi tunda Lawan ya soma daga murya da hargowa duk maganganun da yake yi daga Hansa'u har Asiya duk suna 18 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 jiyowa, domin babu wacce ta rintsa a cikinsu. Dukkaninsu suka mike zaune cikin tashin hankali Hansa'u har ta fara kuka tana cewa mutumin da ya ke da ciwo zai aura min yana cewa ko da za a kai ni yayo gobe na mutu sai an kai ni, wannan wane irin rashin adalci'ne. Asiya ta yi saurin rufe mata baki ita ma cikin muryar kuka ta ce "Ka da ki fadi munanan kalamai a kan mahaifinmu domin bai isa yin komai a kanmu ba, sai abin da ubangiji ya zartar a kanmu ki yi shiru mu yi addu'a daga nan ita ma kuka ya ci karfinta, har lokacin basu daina jin hayaniya a kan maganar ba. 19 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Kamar yanda Ummansu bata rintsa ba haka su ma su ka yi kwanan zaune ba tare da sun rintsa ba, domin sun san halin mahaifinsu, sun kuma yi alkashin daya dauka a kan maganar auren, na cewa ko gawata ce sai ya kai gidan Alhaji Ahmad ita kuma Harira in dai ta sake yi masa magana a kan auren to a bakin aurenta. Kwanaki shidan da suka rage Hansa'u ta tare a dakin mijinta sun zame musu tamkar zaman makoki babu wani me kuzari kowa ni me kakkafar maganar a cikinsu, hatta da rabon goron biki sun dakatar da yinsa. Ya ga gurin lawan kuwa ba abin da ya sanja kullum cikin hidimar raba katin daurin auren yake. 20 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Ana saura kwana uku daurin aure Alhaji Ahmad ya aiko a ai masa kiran Hansa'u Ummansu da take shara a tsakar gida ta ce "Ace bata nan ashe Lawan ya biyo bayan dan aiken kafar ya ji amsar da Harira ta baya, ya karasa shigowa afusace. Gabanta ya yi mummunar faduwa don bata taba tsammanin dawowarsa a wannan lokacin ba. Ya dubi Hansa u da take zaune ya daka mata tsawa "Ke ta shi ki fita". Cikin kankanin lokaci ta rame, idanuwanta duk sun kumbura sbaoda kuka, ya saka daga mata tsawa "Та shi ki je mutuniyar banza ni na ke da iko a kanki ko ita? kuma daga yau 21 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 idan ya kara kiranki ki ka ki zuwa ni da ke ne a gidan nan, saboda tsabar rikicewar da tsawar da ya buga mata ko takalmi bata saba bare mayafi, ta yi hanyar soro tana kuka, ya sake daka mata tsawa "A haka za ki fita sai kace hauka sabon kamu". Ya kalli kayan jikinta wani soshasshen lesi ne da wata kodaddiyar atamfa wadda ya manta tsawon tun kwanakin da yake ganinta a jikinta. "Maza ki je ki canza wadannan kayan ki wanko fuskarki" Ya juya ya dubi Harira wadda ke tsaye da tsintsiya a hannunta jikinta a sanyaye yanayinf uskarta kamar zata rushe da ihu. 22 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 "Ke kuma dama na dade da sanin ke ce ke nuna musu ni din ba komai ba ne a idonsu, har su ke yi min kallon raini, to ni din nan da ki ke gani ba irin mazajen da za'a dinga karyawa doka ba ne a zaune lafiya, ba kuma na cikin mutanan da za su dauki raini da tozarcin mace a idon duniya, in dan kina takamar ganinsu a gabanki, kina tare da su, to ki je na sake ki bana bukatar na sake ganin kafarki a gidan nan". Gaba dayan masu hankalin sai suka rushe da kuka. Ita kuma kalmar Innalillahi wa inna ilayyi raj'un da ta fada ta sa ta karfin zuciya. Ya daka musu tsawa mutuwa a k ayi da za ku sa mutane a gaban kuna 23 Hadiza Ado Yalwа Garari 2 kuka za ku taramin makota toh duk wadda na kuma jin bakinta sai jikinta ya ga ya mata kowa ya yi mai dalili. Ya shiga daki ya tuso Hansa'au a gaba, tana kuka har suka fita, sai a lokacin kuka ya zowa Harira ya yin da ta ke ta nanata wa Hansa'u Addu'ar kariya daga Ubangijin, sannan ta cewa su Asiya ku yi shiru dama ko da bai sake ni ba, zan bar gidan domin ba zan iya ganin ranar da za a fitar da Hansa'u a gidan nan ba,gwara bana gani, gwara ba na ckin gidan ku kwantar da hankalinku in dai da ragowar zamana zan dawo mu ci gaba da zama tare idan kuma babu ya zama dole mu yi hakuri zan yi ta binku da addu'a a duk in kuke na san 24 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 za ta same ku kuma Allah zai kareku". Ganin hankalinsu ya ki kwanciya yasa ta dinga nuna musu kamar ta fasa tafiyar, sannan ne fa bacci ya debe su ita kuma wannan ne ya bata damar yin shirin ta a nutse. Ana idar da sallar Asuba ta saci jiki ta tafi babu wanda ya ganta a cikinsu. Dukkaninsu sai wayar gari su ka yi suka ga Ummansu ta barsu barin da basu san lokacin dawowarta ba, sun shiga tashin hankali kamar wanda dayansu ne ya mutu, sun kasa aiwatar da komai a gidan sai kuka. Tun jiya Umaima ta ke ta saka wani abu a ranta ganin har wayewar yau da Ummansu ta tafi babu wanda 25 Hadiza Ado. Yalwa Garari 2 ya kawo mafita da za a raba ta da wannan auren ya bata karfn guiwar kawo tata shawara. Bayan da ta ji babansu ya fita yana cewa duk yarinyar da ba za ta bi umarnin sa ba to ta dauki haramar bar min gida donn ni ba zan dauki halin raini da Harira ta dora ku a kai ba, ta dubi yayarsu Asiya da ke ta sheshshka da ajiyar zuciya. "Yaya ni ina ganin yaya Hansa'u ta gudu ta bar gidan nan in ba yaga bata nan ba dole ya hakura da maganar auren. Asiya ta ce "Ni kuma ina ganin ni ya dace na fuskanci wannan rayuwar ni ya dace da shiga wannan ramin mutuwar domin bakin cikin da nake ciki a yanzu nafi zabar mutuwa 26 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 da rayuwa zan fadawa Baba ya mai da auren nan kaina, maimakon kanwata Hansa'u me Karancin shekaru. Hansa'u ta yi saurin rike Asiya ta ce, duk ba zai ai haka ba yaya ni baba ya fi sha'awa da na shiga wannan rayuwar kuma ni ma da na rayu batare da Ummata ba gwara mutuwa da rayuwa. duk abin da zamu yi yanzu harzuka zuciyar Baba zai yi in dai ba amince aurena da Alhaji ba harzuka zuciyar Baba kawai zai yi. Mu yi addu'ar Allah ya kawo mana dauki shine kawai abin da yafi. Kamar daga sama sai ji su kai an shigo hade da sallama Dan Baba suka gani a tsaye Baban wansu. Ba laifi yau yana tare da tsafta kuma babu 27 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 tsumman shaye shaye a hannunsa, da alama yana cikin nutsuwarsa. · Abin da ya fara cewa musu shi ne "Ina Umma?" Asiya ce ta yi saurin ba shi amsa "Ta tafi unguwa Sai a lokacin ya kula da fuskokinsu ya dubi Hansa'u "Ke kuma me ya sa ki kuka?" Ba wanda ya ba shi amsa. Ganin haka ya sa shi cewa "Na zo ne na yiwa Umma sallama zan je Lagas ku ce mata don Allah ta yafe min" Ya lalubi aljihunsa ya dauko dari biyu ya mikawa Asiya "Ungo wannan ku bawa Umma in ta dawo ku kuma ku raba wannan ku yi min addu'a. 28 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Dubu daya ya basu. Sai ya jin muryar Babansu su ka yi yana сеа "Zo ka fita rmin daga gida ban ce kar ka sake shigo min gida ba, daga yau karka sake shigo min gidan in ma dan uwarka ka ke zuwa gidan nan to yau ta fita ka je can ka neme ta" Kalmar ba karamin girgiza dan Baba ta yi ba, sannan ya dubi kannensa ya ga dukkansu kuka suke yi. Hankalinsa ya yi matukar ta shi yana so ya tambaye su me ke faruaw, amma babansu ya ki bari sai tura shi yake waje yake tare da cewa "Karya sake shigo masa gida. Shi kuwa Lawan a Gangarensa hadimar aure ma ta zame masa guda biyo domin tunda ya ga ya samu gida mai dan sararin dakuna ya karbi ta 29 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 yin tsohuwar bazawarsa da ke sayar da abinci a kasuwa da zummar zai toshe daki da rumfa ya zama daki da rumfa ya zame daki dai dai barin Harira gidan yasa ya je da bukatar a daura aure ta tare kafin bikin domin baya son a yi dauren aure batare da mace a gidan ba. Dama Asabe shi kawai take jira don haka bata yi wani musu ba ta amincewa bukatarsa. Ta fadawa yayanta da ta ke zaune a gidansa nan da nan shi ma ya amince a ka daura aure. A gobe dauren aure da daddare su Asiya sai jin mata suka yi nata shigowa suna rangwada guda sun shigo dakin Ummansu suna jin shewa da maganganu mata adakin. 30 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 A maganganun na su ne suka fahimci cewa amarya a ka kawo, amma sun kasa ganewa haya aka kawo ko kuma amaryar babansu ce. Basu gasgata abin da suke zargi ba sai da su ka ga babansu ya shigo da leda a hannunsa yana ta zabga kamshin turare sai bayan da ya yi kamar rabin awa a cikin dakin sannan ya kira wo ya ce "Kun ga wannan ita ce matar dana aura, ku dauketa kamar ita ta haife ku, dukkansu suka bi ta da kallo. Asabe gajeriya ce baka sol saboda mayukan da take shafawa akwai jabun hakoron makka a bakinta, ta na da kirki sosai ta dinga tambayar sunayensu, daya bayan daya sannan ta janyo ledar daya shigo 31 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 da ita gasasshen nama ne da Kabeji da tumatir ta raba shi biyu ta basu rabi. Sannan ya ce da Asiya dukw ani abu da kki ka san naku ne na amfaninku a nan dakin gobe ki zo ki daukar musu Asiya ta ce to. Daga nan suka koma nasu dakin cike da mamakin wannan aure na gaggawa na Babansu abin da ya ma fi basu yanda a ka yi idanun Babansu ya rufe ya iya auran wannan matar da suke ganin ko Ummansu ta girmewa in bata yi sa'arshi ba, to ko zai girme mata da kadan ne, sun dai ji dadin yanda take da fara'a. Daren ya zame musu daren bakin ciki domin washe gari ne aka 32 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 aura auren Hansa'u da Alhaji Ahmad Ahuta. Su na jin hayaniyar mutane Abbansu nata shiga da fita a tsakar gida, amma babu wacce ta fito tsakar gidan a cikinsu hatta Sayyada da take karama bata san abin da yake faruwa ba, ganin yayyanta na takore a daki yasa itama take fitowa. Asabe ce ta shigo da kwano a hannunta ta ajiye musu ta ci kwalliya sosai da koriyar atamfa ta ce "Wai ni 'yan mata me ku ke yi a daki har yanzu ba ku fito ba, ba ku yi wanka ba har da amaryar ma, ni ma da nake tsohuwar amarya ga shi na ta shi na shirya, to ku yi maza ku ta shi ku yi wanka ku shirya kafin mutane su fara shigowa, ga wannan kuma ku ci" 33 Hadiza Ado Yalwa Garari 2 Yanda su ka ga Asabe nata lallashinsu yasa' su ka ji baza su iya bata kunya ba haka suka ta shi kowacce ta yi wanka. Kuka na zahiri ya dauke daga idanuwansu sai dai na zuci. Gidan ya cika makil da jama'a ainun biki sosai ake yi amma duk cikar mutanen basu wuce na kawayen Asabe da danginta ba, sai daidaíku kawayen Umman su da suke shigowa daga makota. Asabe da yake wayayyiyar macece duk wanda ya shigo ta na karbarsa da fara'a ta kuma ce ai Harira ta dan fita ne wasu shirye shirye,

Chapter 1 of 4