Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
ranta zai fita, idan kuka kasheta mu mukai asara koshi wanda yayi mata cikin?" Ta6e baki Mami tayi tace"Hajiya wannan yarinyar fa micijin sari ka noqe ce, kidena goyon bayan ta,duk cikin jikokinki kinfi sonta, yanda kike sonta kike bata goyon baya ai yanzu ga irin ta nan, gashinan tajawo mana abin kunya a gari, yanzu duk wani dan cikin gidannan idan yafita an dinga nunashi kenan ana zundenmu a unguwa" Ran Mummy mahaifiyar Nadra ya 6aci saboda furucin Abu, ta share hawayen idonta ta kalli Nadra tace"kingani ko Nadra?, tun kafin ayi nisa acikin gidannan har an fara yi miki gori qanwar ubanki tana kiranki macijin sari ka noqe, maganin ki kenan" Jikin Nadra ya hau 6ari, gabanta ya tsananta fad'uwa, tanaso tafadi abinda yake ranta amma tana tsoron abinda zaije ya dawo acikin family, tana tsoron masifar da fad'ar tata zata kawo cikin family,amma yaya zatayi?, batada wata mafita data wuce hakan, ahankali ta d'ago kanta, gabanta na faduwa, cikin nauyin baki ta bude bakin nata da qyar tace"YAYA ARAF PILOT ne yamin ciki Mummy" (note: masu karatu kugane,akwai ARIF shine Dr. me innocent face, sannan Akwai ARAF shine Pilot, sunayensu kusan iri daya ne, banbancin harafi daya ne, shiyasa nake fadar kowanne suna da inkiyar aikinsa) Cikin sauri duk wani wanda yake zaune afalon yabita da wani irin razanannen kallo,Aunty Umaima tanajin ankira sunan qaninta qwalli daya tak a duniya amatsayin wanda yayi ciki ta gyara zamanta sosai tana kallon Nadra da kyau,shi kuwa Pilot da aka kama sunansa kansa yana qasa koda wasa bai dago ya kalli mutanan falon ba, kamar bashi akace yayi ciki ba, asalima tunda yagama karatun Alqur'ani awayar sa ya ajiyeta sai yanzu ne yadan sake danna wayar yana kallon time yana kuma taqaicin 6ata masa lokaci da akai a wannan zama. Mami Abu qanwar mahaifin Nadra, wadda ta gama yiwa Nadra gori ta saki wani irin ihu kamar me aljannu, sannan ta nuna Nadra da dan yatsanta tace"karya kike Nadra,kowa yasan Pilot dina nutsatstse ne wallahi, asali ma baya kulaki, amma shine yanzu tsabar kin rasa wanda zaki liqawa cikin shegen dake jikinki shine zaki kala masa sharri, to bari kiji nafada miki, gara tun wuri kinemi uban cikin ki, 'yar is'ka kawai" Alhaji Mahmoud wato Pumpy yanajin furucin qarshe da Abu qanwar sa ta jefi 'yarsa dashi cikin sauri ya runtse idonsa, gefen zuciyarsa yafara yi masa zafi kamar an zuba masa garwashi, tabbas Nadra tazo da magana me mutuqar rikitarwa, ba yan gidan kadai ba duk Jama'ar unguwa kowa yasan halin Araf Pilot uztaz ne, kullum yaqi yake akan tarbiyar yaran gidan, hankali bazai dauka cewa wai shine yayiwa Nadra ciki ba. Kalmar nan ta yar'iska da Mami Abu takira Nadra dashi shine yasa kowa yayi dif, yara sa'annin Nadra kuwa kansu yana qasa, basu taba ganin tashin hankali irin wannan ba tunda aka haifesu, Mami Abu taci gaba da fadin" lallai ma yarinyar nan, qiri-qiri kikeso ki maida abun yadawo kan dana,inda ace mijin ki Dr. ARIF yayi shiru ai shi zaki liqawa cikin, amma dayake shi din ba kanwar lasa bane shine kika dawo da abun kan dana ARAF,saboda kinga shiba me magana bane, to tun wuri ki nemi uban shegen ki, karuwa, 'yar'iska" Hajiya Kaka tayi wani kayataccen murmushi tace"yo dama ai 'yar iskar ce,fadi ki qara fada Abu Nadra 'yar'iska ce, koba karuwa kikace mataba?, to Nadra karuwa ce Abu,saikuma gashi karuwanci ya tare a gindinki, d'anki yayiwa 'yar yayanki ciki, saiki daina kumfar baki, kinga tuwo na mai na kenan, dan haka saikiyi shirin daukar jika ta kowane 6ari". Mami Abu ta fashe da wani irin kuka,"wato Hajiya kin yarda kenan?, kin yarda Pilot zai iya yiwa qanwarsa ciki?, Araf dako magana bata dameshi ba, yaron dako maganar budurwa beso ballantana aure, amma saboda Nadra ta masa sharri shine zaki yarda?" Hajiya Kaka tace"tabbas hakane, nagani kam, magana bata damu Araf ba amma kuma ya'iya lallaba yayiwa kanwarsa ciki ba, tunda tace shine yayi mata cikin ai bazatai qarya ba, cikin sane, dan haka dole a hukuntashi akan laifin daya aikata kuma a aura masa ita" Pumpy yayi ajiyar zuciya shida Daddy, Mummy kuwa quriii tayi itada Mama sai kallon kallo ake, Hajiya Kaka ta gyara zama tace"bame magana ne?" Daddy yace" Hajiya magana dayace kawai,wallahi, tallahi, idan har mun tabbatar Araf ne yayi mata wannan cikin wallahi saiya aureta dolen dole" "Baku isa ba" cewar Mami Abu, taci gaba da fadin"Dana bazai ta6a auran bazawara ba wallahi,wadda wani yataba using" Mama mahaifiyar Dr. ARIF tace" dolensa kuwa Abu, saboda shi ya 6atata kinga kuwa aure ba fashi, tayaya zai lalata yarinya sannan a barshi taci gaba da zama agidan dana?, shi wanda yayi cikin yaci bulus kenan?, dole Dr. ARIF zai sake ta shima kuma Pilot dolen sa ya aure ta" wata shewa Mami tayi tatafa hannayenta har suna bada sauti sannan tace"lallai ashe kuwa 'yarku zata mutu babu aure kenan" Cikin tsawa Hajiya Kaka ta dakatar dasu da wannan shirman, nan take palourn yayi shuru kowa da abinda yake sakawa a ransa. Abdul yayan Nadra, ya saki wata irin asirtacciyar ajiyar zuciya, sai yanzu yaji sanyin esin yana shigarsa, sai yanzu ne numfashinsa yafara daidaita yaji hankalin sa ya dan kwanta bayan yaji inda aka jingina maganar cikin. Abun mamaki duk wannan bala'in da'ake Araf pilot bai dago kansa ya kalli iyayen nasaba,haka koda wasa babu alamun damuwa ko tashin hankali a tattare dashi, yanajinsu, amma miskilanci yahana yace uffan, zallar mamaki nede akan fuskar sa wanda d'aurarriyar fuskar sa ta kullum-kullum takasa bayyana mamakin nasa. Hajiya Kaka ta kalli yaranta tace"Mamudu,Muhammad, dake Zainabu Abu dukkanku 'Ya'yana ne hakane?" gaba dayansu su ukun sukace"hakane Hajiya" Tace"to, matanku sun dade suna munafuntarku wallahi" Cikin sauri Mummy mahaifiyar Nadra matar Alhaji Mahmood wato Pumpy dakuma Indo wato Mama, mahaifiyar Arif mijin Nadra kuma matar Alhaji Muhammad, suka dago kansu su biyun suna kallon Hajiya Kaka saboda furucin munafurci dasukaji ta dangantasu dashi,kowaccen su ta bude ido alamun razana. Hajiya Kaka ta Kallesu sannan ta gyada kanta taci gaba"Araf da Nadra sun dade suna soyayya a 6oye batare da sanin kowaba, kuma iyayensu sun gane,shiyasa Sauda da Indo suka yi sauri suka hada auren dr. Arif da Nadra, dan kada ku farga kuce saita auri Pilot, kuma dr. Arif be sonta, itama Nadra bata sonshi,tilasta musu sukayi, sannan itama Abu data lura saita takawa Pilot birki don itama tanada wadda takeso ya aura, tunda sunso junansu abaya aiba abun mamaki bane dan yayi mata ciki" Hajiya Kaka tana gama wannan furucin Jikinsu yayi sanyi sosai. taci gaba da fadin"kunji yadda akayi, nikuma banfada muku ba dan banson tashin hankali, nasan Abu batada dadi kwata-kwata,ga Pilot nan azaune, bana mantawa nan yazo yasameni watarana yana kuka yana fadamin maganar soyaiyar tasu, nan nayita bashi hakuri, dan haka kada ku zargi kowa ku zargi kanku ku ukunnan, soyaiya tabbas yara sun so junansu, saide maganar cikin ne banida sani akanta, amma tunda kaji yarinya tafada da bakinta cewa shine yayi cikin to babu tantama shine yayi" Abdul yasake sakin ajiyar zuciya a6oye, ahankali yanajin nauyin dake zuciyar sa yana raguwa, Araf Pilot kuwa kallon Kaka yayi sau daya ya watsar, ji yake kamar yaje har inda take zaune ya shaqeta, wai ba tantama ciki na sane duk tabi ta tsaneshi kamar shi din ba jikanta ba. Mummy ta fashe da kuka idonta har yayi ja saboda tsabar tashin hankali, Pumpy ya kalleta yace"yimin shiru munafuka,kin bani mamaki Sauda, yanzu son zuciyar taku harya kai haka?, muna zaune agida kuna qulla abinda zaku iya?, okay wato kuna so ku sauya qaddarar da Allah ya tsara wa yaranku kenan?, dole sai wanda kukeso zasu aura ko?, yayi muku kyau, daidai kenan" Mami Abu tata6e baki tace" oho dai, nidai ciki bana dana Pilot bane wallahi, taje can ta yayimo wanda ya mata" Nadra ta dago kumburarran idonta ta kalleta tace"Mami kidena rantsewa, domin kuwa nasane, Yaya Pilot shine ya hadani da wannan qaddarar, idan nayi karya ya musa mana, ai gashinan azaune" Daddy ya kalli Mami da kuma Nadra yace"ya'isa haka kowa yayi shiru" ya juya kansa yana kallon Araf Pilot sannan yace"Araf" Cikin ajinsa dakuma nutsuwa da rashin damuwa ya dago kyakykyawar fuskar sa yace"Na'am Daddy" Daddy yasake cewa"Araf" wannan karon saida ya motsa dan qaramin lips dinsa sannan yace"Na'am Daddy" a karo na uku Daddy yace"Araf, sau nawa na kiraka?" fuskar sa kamar kullum babu fara'ah haka babu wasa bare rashin nutsuwa yace" Sau uku ne Daddy" Daddy yace"fine, tsakanin ka da Allah cikin ka ne ajikin Nadra koba naka bane?" Cikin rashin damuwa ya dago kansa sannan yadan saki murmushi wanda yasake qawata fuskar sa yace" Daddy ciki kuma?, gaskiya BA NAWA BANE!, ba ciki na bane, nayi tunanin ko bayan raina in bana duniya shine de lokacin danake cikin kabari bazan iya kare kaina ba zaku iya tsaya min ku zamemin sheda akan bazan iya aikata hakaba Daddy,yaushe zanyiwa Auta ciki Daddy?, tabbas nasamu Kaka akan maganar inason yarinyar, amma batun ciki, bansan shiba, bansan tushensa ba, haka kuma banda wata alaqa ta kusa kota nesa tsakanina da wannan cikin" "Karya kake munafuki, kaine wallahi, nawa Nadra take?, yarinya 'yar 18 years meta sani a rayuwar da har zaka nuna tayi ma sharri?, saide in tsoron uwarka Abu kake dole ka 6oye, amma tunda tace kaine kayi ciki na tabbatar cikin ka ne" cewar Hajiya Kaka Araf Pilot ya runtse idonsa cikeda 6acin rai, sosai kalaman Hajiya Kaka sukai bala'in qona masa rai, shi Dr. Arif daya ce banasa bane meyasa bata musanta ba?, sai shi?, nan take fuskar sa tasake dinkewa dama gata ga yanda take. Daddy ya saki ajiyar zuciya yace"Hajiya maganar gaskiya nima bana tunanin hakan gaskiya, inda nasa ne dole zai fada, domin kuwa Pilot yana tsoron ubangijinsa fiyeda mahaifiyar sa Abu, kowa yasan cewa atsaye yake akan ra'ayin sa, tsoron Abu bazaisa yakasa fadar gaskiya ba inda cikin nasa ne, nafi tunanin qarya take" ya juya ya kalli Nadra data zubawa Pilot ido takasa dauke wa,yace"Nadra, kinji abinda yayanku yace, ciki banasa bane,kifada mana gaskiya Nadra, kifada mana wanda ya miki cikin nan ninan nayi miki alqawarin sai inda qarfina yaqare akan qwato miki yanci" wani irin hawaye ne me zafi ya zubo mata, har yanzu bata janye idonta akan Yaya Pilot ba, bata damu ta share hawayen ba tace"Daddy cikinsa ne" Karon farko tunda aka fara meeting din Pilot ya daga kansa ya kalli Nadra fuskar sa a dinke, hannunsa harde a faffadan qirjinsa, sosai yake mamakin tsaurin ido irin na yarinyar. Pumpy ya girgiza kansa cikin damuwa yace"dukkanku ku tashi ku fita zamu gana da Hajiya" Ahankali Pilot ya saki ajiyar zuciya dan dama tun tuni zaman ya isheshi, cikin takunsa na izza dakuma tsayaiyen namiji ingarma yafice yabar falon ransa ba dadi. Abdul ya saki wata irin wawiyar ajiyar zuciya har dr. Arif dake kusa dashi saida ya kalleshi, ahankali suma suka fice,yaran yanmata sa'annin Nadra dakuma ita kanta Nadra suma simi-simi suka fita, ya rage daga Hajiya Kaka sai iyalinta dakuma matansu,Pumpy ya kalli qanwar su yace"Abu, abinda nakeso dake shine ki nutsu abar maganar nan har Nadra ta haihu, tunda tace ciki nasa ne shima yace banasa bane bamuda wata mafita data rage mu bari ta sauka lafiya aje ayi test a gani jininsa ne babyn ko ba nasa bane, idan har nasa ne wallahi saiya aureta sannan saiya karbi hukunci mai tsananin gaske akan wannan, idan kuma ba nasa bane qarya tayi masa shikkenan tayiwa kanta,dole saita fada mana ne sannan ne zamu dauki mataki, tunda taqi fadar gaskiya ai shikkenan, itace zata dinga yawo da tabo ajikinta, sannan idan mu ta6oye mana wanda yayi mata cikin ai bazata 6oyewa abinda zata haifa ba ko?, dole duk daren dadewa idan abinda ta haifa ya girma dole zata fada masa waye uban sa, babu maganar zubar da ciki, ba zamu zubar da ciki mu aikata laifi biyu ba, abari ta haihu ayi gwaji ai dole gaskiya zatayi halinta" nan take kowa yayi na'am da wannan hukunci, batare da 6ata lokaci ba, su Daddy suka fice. Sannan suma matan kowa takama gabanta. kai tsaye Mummy tana barin falon Kaka ta wuce dakinsu Nadra ta tarar da'ita tareda yan'uwanta mata zagaye da'ita suna bata hakuri. tsayawa tayi akansu tace"har mutuncin lallashi tasamu awajanku?, 'yar iska, uban waya aiketa?, ai kuka yanzu kika fara, wannan kukan dakike yi hawaye ne, babban kukan yana gaba, yana nan zuwa" wani sabon kuka ne ya qwacewa Nadra, ga wani irin amai daya taso mata, cikin sauri ta mike ta wuce toilet,baqin ciki yasake kama Mummy, tabita dawata irin harara kamar idonta zai fado. tana shiga toilet din ta dinga kwara amai, saida tayi tagama tsaf sannan ta wanke bakinta tareda wanke fuskar ta tadawo cikin dakin ta zauna, yanda ta wanke fuskar tata hakan yasa sumar kanta ta kwanta tagefen kunnuwanta tayi luff tareda sake qawata zallar kyawunta, Mummy ta kalleta cikeda qyama tace"Nady kin6ata wayonki a banza, na tabbatar Pilot bazai miki ciki ba, misali mu daukama shine yayi miki cikin ina tabbatar miki da cewa wallahi ko ya aureki bazaiga girmanki ba, bazai ta6a ganin qimarki ba, kalleki just 18 years, amma har kinsan ki kwanta da namiji kafin aure imagine mtseww" Mummy ta qare maganar cikin dacin zuciya. Nadra ta sunkuyar da kanta qasa tasake fashewa da wani irin kuka, sosai take kuka saide kokadan wannan kukan nata bai damun Mummy , hakan yasa saida tayi mata tass sannan ta fice daga dakin. ................................... 🍁 Acan part din Mami Abu kuwa, tunda ta koma sai faman sintiri take a daki,tunani ne fal ranta gaba daya tarasa inda zata tsoma ranta, magana take cikin zuciyar ta yaya zanyi da zancen cikin nan?, amma idan har Pilot ne yayiwa yarinyar nan ciki ya cuceni a duniyar nan. sallamar sa ce ta katse tunanin Mami, cikin sauri ta juyo tana qare masa kallo ganin kokadan babu alamun damuwa atare dashi, asalima wankan sa yayi yasake shirya wa cikin qananun kaya wanda suka karbi jikinsa sukai masa mutuqar kyau, zama yayi akan kujera yana qoqarin danna remote kamar baiga halin da Mamin nasa take ciki ba. Mami kuwa nazarinsa take sosai ko zata gano wani abu akan fuskar sa. "Araf" ta kirashi, cikin rashin damuwa ya dago ya kalleta da manyan idanuwansa batare daya amsa ba. tace"Kaine kayi cikinnan?????" Cikin gundira dajin zancen cikin nan ya saki ajiyar zuciya ya wurgar da remote din hannunsa sannan yadafe kansa da hannunsa batare dayace uffan ba, domin kuwa baqin ciki yama hanashi magana. Cikin qufula da wannan halin nasa tace"baka ji na ne?" Nan ma ba amsa shiru yamata,tsananin taqaici yakeji da quna aransa idan aka danganta shi da cikin nan. Jin yasake yin shiru yasa nan take Mami ta fusata sosai, cikin 6acin rai tace"nifa Araf shirunka na bani tsoro" runtse idonsa yasake yi, ba komai yake fad'a aransa ba face Allah ya'isa da yake jawa wannan matsiyaciyar yarinyar acikin zuciyar sa, gaba daya tasa ya muzanta a'idon family, mutuncinsa zai samu tawaya a'idon iyayen su maza, yanzu gashi mahaifiyar sa data yarda dashi sama da kowa a duniya itama gashi ansa mata shakku aranta har tana tunanin shine yayi ciki, shi kuwa me zai yiwa yarinyar nan domin ya huce?, wanne irin duka zai lakadawa Nadra idan suka ke6e? Nace ba, daga jiya zuwa yau har yanzu de babu wanda ya fada mana CIKIN WAYE NE acikin zaratan samarin wannan family ? Cikin waye littafin kudi ne, 500 ne kacal👌ki antayo kudi na antayaki cikin paid group azuba sharhi tare dake💃🏼 8033330504 Amina Muhammad Moniepoint tareda shaidar biya ta wannan number 08033300034 Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Yan Niger ku duba ArewaPen na dora👌🏻 Amnah El Yaqoub ✍️ 🍁CIKIN WAYE ?🍁 (A Confused Family Story) Writing By Amnah El Yaqoub page 5&6 *Wattpad*: AmnahElYaqoub *ArewaPen*: @amnahelyaqoub *Facebook username*: Amnah El Yaqoub *Subscribe to my YouTube channel domin sauraren CIKIN WAYE* 👇: https://youtube.com/@amnahelyaqoubnovels?si=-4w3XDkwjZA1hj0k *Whtsapp channel link:* https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45 *Like my page on Facebook👇* https://www.facebook.com/share/1a9oXkTpcy/ "Mami" yakira sunanta in gentle. Mami Abu ta zuba masa ido tana kallonsa batare data amsa ba, shima kallonta yake daga wannan kiran sunan bai ce komai ba yayi shiru. lokaci daya ranta ya6aci, afusace tace"kayimin magana mana,ko nima halin miskilancin naka zaka gwadamin?" Ahankali ya motsa lips dinsa yace"Mami ni fa bansan wannan zancen cikin ba,banda alaqa dashi,tabbas na nemi soyaiya da'ita abaya, amma banda masaniya akan cikin ta, Mami kuma nayi miki shiru ne saboda naga alama kina nema tunanin ki ya sauya akaina " Mami tazubawa fuskar sa ido tana sake nazarinsa,agefe guda na zuciyar ta kuma tana yarda da kalaman sa, domin kuwa kowa yasan wannan ba halin Araf bane bibiyar yanmata bare har akai ga yayi lalata dasu,tana alfahari a koda yaushe kasancewar sa ustaz qwalli daya jal a familynsu,ajiyar zuciya ta sauke tace"to daka nemeta da soyaiyar babu abinda yafaru de ko?" hannunsa yasa ya dafe goshinsa, sannan ya girgiza kan nasa cikin damuwa, yaga alama duk da wannan bayanin da yayi mata har yanzu kamar zuciyar ta bata yarda dashi ba,haqiqa Nadra ta cutar dashi, tagama dashi duniya da lahira. kallonta yayi yace"Mami nifa banyarda dr. Arif baiyi tarayya da ita ba, saide in yarinyar tsoron sa take ji kokuma wani kyakykyawan gargadi yayi mata akan cikin shiyasa ta danganta shi dani, babu wani namiji me lafiya da zai kasance da yarinyar nan agida daya har tsawon wata hudu yazuba mata ido batare daya kasance da'ita ba,ko kadan ban yarda da dr. Arif ba,because likitan Mata ne, zai iyayin dabarar su ta likitoci ya kasance da'ita batare data sani ba, kuma muddin nahadu da yarinyar nan kafin nabar gidannan sainayi mata dukan da bazata sake gigin yimin sharri ba, sai tayi dana sanin doramin wannan sharrin, saina kakkarya qasusuwanta in yaso daga ranar ta fadi ta mutu nikuma a koreni a Family" wani wawan mari Mami ta sakar masa, cikin sauri yad'ora hannunsa a kumatunsa yana kallonta da tsantsar mamaki, zai iya rantse wa da wayonsa da komai Mami bata ta6a dukansa hakaba, amma yau ta silar waccen matsiyaciyar an mareshi. Mami tace" Ashe bakada hankali Araf?, ni kake fadawa zaka daki 'yar yayana in yaso ta fadi ta mutu?, taurin zuciyar taka har yakai kayi tunanin dukan yarinyar datake dauke da juna biyu?, har wani cika baki kake kamar zakayi dambe da sa'ar ka?" wani irin abu me daci ya hadiye daqyar sannan yace"kiyi hakuri Mami ni ban iya 6oye abinda ke cikina ba" Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi sannan ta nemi waje ta zauna tareda fadin"dole zan nemi uwarta muje a zubar da cikin nan,bazai iyu muna zaune yarinya qanqanuwa ta janyo mana abun kunya agari ba,inma dr. Arif dinne yayi cikin bazai iyu daga kansu mu fara renon shege a familynmu ba, tun iyaye da kakanni babu wanda yata6a janyo mana abun kunya irin wannan acikin family" Araf ya kalleta da tsananin mamaki yace"Mami kisan kaifa kenan zakuyi, ai haramun ne hakan, ga laifin zina gana kisan kai, gaskiya Mami ki sauya shawara, ni ina ganin kuyiwa yarinyar qamshin mutuwa dole zata fada muku uban danta, danni harga Allah zuciyata bata gamsu da cewa ba dr. Arif ne yayi cikin nanba, dama baya sonta, zai iya zuba mata magani a abunsha tafita hayyacinta shikuma yabiya buqatar sa daga nan kinga babu wanda zai zargeshi tunda Dr. ne, yasan kan irin wannan dabarar, ku zaunar da yarinyar ku kama hancin ta ku toshe,ku daure mata hannayenta duka biyun, ku shaqe mata wuya idan taji qamshin mutuwa wallahi zatayi maganar gaskiya, sannan nima zata wanke ni daga cikin case din, amma maganar zubar da ciki gaskiya haram ne Mami, Allah ya haramta" cikin fishi ta kalle shi tace"ai da wannan abun kunyar yafuto acikin gidannan wallahi gara ace kisan kai mutum yayi" "A'uzubillah, haba Mami, yakike haka?, kefa musulmace, kuma kin yarda da kaddara, abunda kike kokarin aikata wa kisani ubangiji ya haramta" "To naji ubana, kada ka dameni kuma" Cikin 6acin rai yamiqe batare daya kalleta ba yace"zanwuce Lagos dan gobe inada tukin jirgi zuwa US" wani salati Mami tasaki "Araf kanada hankali kuwa?,wai meyake damunka ne? kwata-kwata kai Unserious ne akan komai, ana rigimar nan zakace zaka tafi?, in kanada hankali ko ance katafi ma ai bazaka tafi ba saboda gudun zargi" wani irin murmushi yayi yace"Haba Mami,kamar nine nayi mata cikin?, haka kawai saboda wata qanqanuwar yarinya ta kawo muku soki burutsu kunhau kai kun zauna nima saina watsar da aikina in zauna?, kinsan fa aikin company ne basu daukar excuse, maganar rigimar family kuma Mami kune kukaso hakan, nace kuyiwa yarinya qamshin mutuwa zata fadi gaskiya,tun afalon Kaka ya kamata ku karya qafarta ta hagu, sannan ku karya hannunta na dama,da tuni wani zancen ake, amma fisabililla kunata lalla6ata tayaya bazata rainawa mutane hankali ba?, ni ku barni da'ita mu biyu adaki, minti ashirin yayi yawa gaskiya zata futo" Mami tayi quriiiii da idonta tana kallon Araf, ta lura shidin da soja ne to sune na gaba-gaba wajan aikata kisan kai. to sauqin ta dajin dadinta shine shidin ba sojan bane,ta tabbatar kamar yanda yake fada idan aka barshi da yarinyar saide su dauko gawarta, zatayi magana taji sallamar Aunty Umaima, a dakile ta amsa mata. "sannu Mami" Aunty Umaima ta furta a hankali. wani wulakantaccen kallo mami ta watsa mata tace "uwar gulma sai yanzu kika dawo daga wajan kanwan uwar taki Nadra?, kuma kinsan kin bar danki jariri a daki yana kuka kintafi kanzagi ko?" Aunty Umaima ta kalleta tace"haba Mami, Nady fa kanwata ce,kuma qanina damuke ciki daya ake zargi da aika-aikar nan, kinga kuwa dole na damu" "ke gafaranan wawiya kawai marar hankali, ce miki akayi shine?" Aunty Umaima tace"Mami to waye?, yarinya ta furta da bakinta fa, sannan kice karyane haba mami Nadra fa jininki ce itama" wani wawan tsaki Mami tabuga "to naji, wuce daki ki shirya ki tafi gidanki" tajuya ta kalli Araf dayake bin yayar tasa da wani irin kallo baqin ciki fal ransa, wai shine Auntynsa guda daya tak a duniya take ikrarin shine zaiyi wa yarinya ciki,ko a mafarki bai ta6a tunanin haka ba, yayi tunanin ko baya raye itace ta farko wadda zata tsaya tsayin daka cewa ba shine ya aikata ba. Mamy ta dubi Araf tace"kaikuma wuce Allah ya kiyaye saura naji kaje sashensu" tun kafin ma ta qarasa magana shikam Araf ya fice cikin tsananin damuwa ko kallon Aunty Umaiman baiyi ba, daya futo compound harya juya ya kalli part dinsu Nadra wata zuciyar tana ce dashi yaje yayi mata rashin mutunci, sai kuma ya girgiza kansa kawai ya wuce yayi cikin motar sa, domin fada da ita ma ai kamar fada da 'yar cikinsa ne saboda tazarar shekarun dake tsakanin su. ...................................🍁 A can daki kuwa, Mama da Mummy sunata saqawa suna warwarewa suna tunanin hanyar da zasu samu mafita,Mama ta numfasa ta kalli Mummy tace"Sauda inaga zubar da cikinnan ne kadai mafita kokuwa?, tsakani da Allah yaushe zamu biyewa su Alhaji kawai saboda asan CIKIN WAYE sai mubar yarinya agaban mu ta haifa mana shege? " Mummy tace"to Aisha yanda kika gani, nifa I'm speechless wallahi" sallamar mami ce ta katse su da sallama a bakinta, mamaki karara a fuskokinsu suka amsa, suna mamakin ko menene ya kawo ta? Oho. Mama ce tayi mata sannu da kyar, ta nemi waje ta zauna tace"nazo ne akan maganar Nadra mu samu mafita, dan kuwa maganar nan ta shafemu duka, ba dana ne kadai ba, kowa da dansa a ciki, na matsa Araf dakyau domin in tabbatar cikin nan shine yayi ko kuwa, amma ya tabbatar min ba nasa bane, abinda yake nunamin ma shine shi bai yarda tsawon wata hudun da tayi agidan Arif shi Arif din bai nemeta ba,kuma nafadama masa cewa da ahaifi wannan cikin gara a zubar dashi, saiya nunamin aikata hakan haramun ne karma mu zubar mu sake aikata laifi, kunga inda ace shine yayi cikin to zai bani goyon baya wajan zubar da cikin kodan kada ahaifi cikin kuma asirinsa ya tonu" Ta maida dubanta zuwa ga Aisha sannan tace"Indo ni abinda nake gani shine idan fa muka bari harta haife wannan cikin akai gwaji kamar yanda su Yaya suka fada, kuma aka gano cikin nan na danki dr. Arif ne tofa mune acikin kunya gaba dayanmu bake kadai ba, haka idan muka bari Nadra ta haihu akai gwaji aka gano cikin nan na

Chapter 2 of 4