Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
dauka Nadra bata haihu ba, ga de ciwo nan tana jinsa gadan-gadan amma haihuwa shiru,kasancewar Arif likita ne shiyasa ya kasance adakin haihuwar, ganin yanda ta galabaita yasa suka yanke shawarar zasu yi mata c.s, Arif yafuto yana goge zufa ya kalli iyayensu maza yace "Pompy kayi signing za'a yi mata aiki because rayuwarta na cikin hatsari" Cikin tashin hankali iyayen suka kalleshi, Mama tace"Innalillahi meyake faruwa Arif?" kallon mahaifiyar tasa yayi yace"tabugu dayawa Mama, kuma bleeding take sosai dan sai ansamata jini ma" Araf Pilot ya dafe kansa cikin damuwa. Bayan pompy yayi sign aka futo da'ita za'a maida ta dakin tiyata, suna ganin an futo da'ita dukansu sukai kanta, saide bata cikin hayyacinta, amma duk da haka saida ta kalli mahaifiyar ta cikin kuka tace"Mummy ki yafemin mutuwa zanyi" wani irin kuka ya subucewa Mummy, tasa gefen mayafinta ta share hawayen sannan tace"kidinga yin salati Auta, nayafe miki, kuma koda kin mutu kisani shahada kikayi" Hajiya ta kalli Mummy da sauri, sosai tayi mamakin furucinta na qarshe akan yarinyar, cikin izza ta maida mata martani tace"bare ma lafiya kalau za'a mata aikin ta rayu kamar kowa saide dan baqin ciki ya mutu" Mummy ta kalli Hajiya Kaka tayi shiru tana cigaba da goge hawaye. Nadra na kuka Mummy nayi, aka shiga da'ita dakin tiyata, bayan awa uku cif dr. Arif yafuto da yara biyu a hannunsa, nan take kowa ya miqe tsaye, akafara kallon-kallo,shima kallon mutanan gidan nasu yayi yarasa wa zai tunkara da yaran tunda babu wanda yasan ubansu?, haka ya tsaya cak, bai bawa kowa yaran ba kawai de yace''ga Babies ta samu Boy and Girl, kuyi hakuri amma yaron yakoma. Pompy sunkuyar da kansa yayi qasa yakasa kallon yaran, haka Mummy ma kuka take sosai, wai yau jikokin tane shegu har guda biyu, Pompy dayake namiji ne haka ya daure ya goge hawayen idonsa Daddy yana bubbuga bayansa alamun lallashi, daqyar Pompy ya kalli dr. Arif yace"zamu iya ganin ta?" Arif yace"zaku iya ganin ta Pompy" daga nan cikin sanyin jiki Arif ya miqawa Hajiya Kaka yaran gaba dayan su,yakoma gefen Abdul ya tsaya, wanda har zuwa wannan lokacin kansa ke qasa baya kallon kowa. Hajiya Kaka tana karbar yara gabanta ya yanke yayi wata irin faduwa, tsananin tsoro ya kamata saboda yanda yaran suke tsananin kama da daya daga cikin samarin gidan jikokinta. Pompy yayi qasa da muryar sa, ya kalli matarsa cikin tsantsar damuwa yace"Sauda,muje dakin haihuwar nan ki lallashi Nadra tafada miki gaskiyar wanda ya mata wannan cikin tun kafin azo ana za'ai gwaje-gwaje mu sake tonawa kanmu asiri, tunda Allah ya sauke ta lafiya gara musan waye uban yaran nan" Cikin sauri Mummy ta kalleshi, kafin tayi magana yace"eh hakane mana,kije kisameta tafada miki gaskiya, domin ni har cikin zuciyata harga Allah ban yarda cewa Pilot zaiyi mata hakaba kamar yanda tafada" Fuskar Mummy ba annuri tace"Alhaji kabarta dan Allah,kota fada ko karta fada damuwar ta ce, ai me faruwa tariga tafaru, tunda tariga ta haifi shegu idan mu taqi fada mana wanda ya mata, ai bazata 6oyewa abinda ta haifa ba,dole wataran saita fada mata waye uban ta. Cikin damuwa Daddy yace"Ke dakata Sauda,banason jin sakarcin banza, ni hannuna bazai ru6e na yanke na yada ba, ba lalle tafadi komai agabana ba, amma ke ki tashi kije kiyi abinda na umarceki tun kafin raina ya6aci" Kai tsaye wajan da mama take zaune ta qarasa, tayi mata bayanin komai daga nan suka wuce dakin da Nadra take kwance, tana ganinsu tayi sauri ta sunkuyar da kanta qasa, kana ganin ta zakasan cewa ta galabaita, waje suka samu suka zauna suka sakata agaba, ganinsu yasa nan take tafara hawaye, Mama tafara lallashin ta, saide baqin cikin halin datake ciki yasa kukan nata yaqi tsayawa, Mummy ta fusata tace"dan ubanki kiyi mana shiru,wani ne ya aike ki?" Cikin sauri tasa hannu ta toshe bakinta tayi gum, Mama ta kalleta tace"Nadra, duk wata mace me ciki musanman wadda ta kusa sauka anayi mata fatan ta haihu lafiya ne, fatan mu shine ki sauka lafiya, kuma Allah yasa kin haihu lafiya Nadra, mace me ciki ana cewa qafar ta daya tana duniya ne daya kuma tana lahira,tokede gaki nan a duniya Allah yayi kin haihu lafiya, bakyason musan waye yayi miki ciki domin mu qwata miki yancin ki?, Nadra kifada mana gaskiya waye yayi miki ciki?, idan dana ne dr. Arif karki ji nauyi na kifadamin gaskiya, idan yayanku ne Abdul karki ji tsoro kifadamana kawai, sannan Idan Pilot ne kifada kawai babu abinda za'a iya yi miki muna tare dake, bare ma mude daga wajanmu munsan cewa Araf bazai miki ciki ba, idan har shine ya miki ciki tayaya zai bada dama aje ayi gwaji?, yanzu haka duka gidanmu kowa yana asbiti, kuma kisani ba zamu bar asbitin nan ba dole kowa zai so yaji halin da ake ciki dangane da yaran dakika haifa" babu musu Nadra ta goge hawayen idonta,tiryan tiryan tafara basu labari tace"Mama Allah shine shaida ta,in banda wannan qaddarar banta6a sanin wani da namiji ba a Rayuwata, kuma tunda nafara soyaiya da Yaya Pilot kullum cikin yimin nasiha da gyara yake, ko hannu nakai jikinsa nan da nan yake nunamin kuskure na, Nima qaddara ce ta fadamin banta6a tunanin zan girbi abinda na shukaba, banyi zaton zan fuskanci wannan matsalar ba, abinda yafaru shine, ana gobe daurin aurena....... " _____ Jama'ah nide Ta Rasulu nace CIKIN WAYE?๐Ÿค” Pilot yace garama tayi ta haihu agani ko CIKIN UBAN WAYE๐Ÿ˜‚ masu karatu nasan kuna cikin zaquwa akan son sanin CIKIN WAYE? toga Nadra nan zata bamu labarin wannan ciki na waye, nesa tazo kusa๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Yan comment section wasu sunce cikin Abdul ne, yayinda wasu suke cewa cikin Pilot ne,watama cewa tayi cikin Dr. ne kawai basaja yake, to sanin gaskiya sai Allah sai Nadra saikuma uban ciki๐Ÿ˜‡ Alhamdulillah anan nakawo qarshan free page dina na littafin CIKIN WAYE ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Hajiya ki biya 500 babu tsada ayi tafiyar dake, Asha comment dake,ki karanta da kanki yafi abaki labari ace ai cikin wanene๐Ÿ™ƒ 500 Amina Muhammad Moniepoint Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 tareda shaidar biya ta wannan number 08033300034 wanda basu siyaba nagode da bibiyar wannan labari, nasan anan zamu rabu, sbd haka saimun hadu a sabon littafi na nagaba ANTI HAYATY ma'ana KECE RAYUWATA.๐Ÿ˜˜ Amnah El Yaqoub โœ๏ธ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4