dana ne pilot to fa nanma de gaba dayanmu ne zamuji kunya tunda gida daya muke,idan mun bari ta haihu angano me cikin me zasuyi?, me hakan zai amfanar?, saboda haka ni ina ganin kawai muyi magana azo a zubar da cikin nan kowa yahuta"
Mama mahaifiyar Dr. Arif tasaki ajiyar zuciya tace "aiko ba hakaba ma dole tashafe mu, tunda mutanan Unguwa zasu san an haifa mana cikin shege agida"
Mami tace"Alhamdulillah, to kunga yanzu abar tone-tone a hada karfi da karfe musamu mafita"
Mummy ta kalleta tace"hakane Abu,amma saidai mu binne maganar nan kada su Alhaji da Hajiya suji kokuwa? "
Mami da Mama suka hada baki sukace"kwarai kuwa, dan zasu iya kawo cikas"
Mami tace"mafita daya ce shine cire cikinnan kawai, inma wani ne daga waje yayi mata cikin ai asirin gidanmu bai tonu ba, amma ya za'ai mu bari munaji muna gani a haifi cikin shege, kuma muna raye ba mutuwa mukai ba, to menene amfanin mu kenan inde zamu bari a haifi cikin shege a wannan family"
kowaccen su ta gyada kai alamun gamsuwa.
Mama tace"bara nakira Dr. Jiddah tazo"
nan da nan ta kirata sukayi magana tace tana zuwa, bayan minti 30 Dr. tayi sallama aka gaggaisa sannan mami tamata bayani, Dr. Jiddah ta jinjina sannan tace"ku kira yarinyar naduba"
Cikin sauri Mama ta mike ta shigo da Nadra,Mummy ta bita da muguwar harara.
Mami kuwa da kallon tausayi tabita, tunda yanzu ta tabbatar ba danta ne yayi cikin ba sai kuma take tausayin ta, haqiqa ta tausaya mata a karon farko.
Dr. ta ruko Nadra sannan tace" kwanta kinji na duba ki"
A sabule ta kwanta, Dr. ta aunata tana girgiza kai alamun tausayi, tagama dube-dubenta tace "tashi kije abinki"
Bayan tatafi Dr. ta kallesu tace "Kuyi hakuri da cikinnan, dan idan mun ce zamu cire to tabbas zata iya mutuwa,kuma ku kalla dakyau cikin nata ya tasa ina tunanin kamar yafi 4 month dinma gaskiya"
Mummy tace" Dr. a cire kawai idan ta mutu sai me?, baqin cikin danake ji acikin zuciya ta rayuwarta bata da wani amfani a wajena.
Dr. ta girgiza kanta tace"Haba Hajiya Sauda, yarki cefa, idan rai yabaci hankali ne yake dawo dashi, hannunka baya ta6a ru6ewa ka yanke shi kayar"
Cikin sauri Mummy tace"tuni ma, tun yaushe? lokacin da zanje asbiti nabiya kudi a yanke mun shi waya sani?"
Ta mike tsaye taci gaba da fadin "bara muje wani Hospital din kawai su zubar dashi, dan nidai data haifemin shege gara ta mutu kowa ya huta"
taqarasa maganar tana daukar mayafinta, dagowar da zatayi ta nufi kofa taga Pumpy ya rungume hannu a kirji yana kallon su gaba dayan su.
__________________
to Jama'ah
Dr. Arif yace ciki banasa bane.
Araf Pilot yace ayi mata qamshin mutuwa zata fadi gaskiya kuma shi bai yarda Dr. Arif zai zauna gida daya da Nadra kuma yakasa nemanta ba saboda haka kawai ciki na Arif ne.
agefe guda ga Abdul yayanta yana hamdala saboda jifa yawuce kansa.
acikin su ukun nan Wai cikin nan na waye?
500 kacal
8033330504
Amina Muhammad
Moniepoint
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
tareda shaidar biya ta wannan number 08033300034
Mrs Usman ce✍️
🍁CIKIN WAYE ?🍁
(A Confused Family Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
page 7&8
*Wattpad*:
AmnahElYaqoub
*ArewaPen*:
@amnahelyaqoub
*Facebook username*:
Amnah El Yaqoub
*Subscribe* *to my YouTube channel domin sauraren CIKIN WAYE* 👇:
https://youtube.com/@amnahelyaqoubnovels?si=-4w3XDkwjZA1hj0k
*Whtsapp channel link:*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
*Like my page on Facebook👇*
https://www.facebook.com/share/1a9oXkTpcy/
Gaban Mummy yayi wata irin faduwa, hannunta yafara rawa saboda tsabar razana, cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa takasa hada ido dashi.
Dr. Jiddah kuwa sum-sum tamiqe ta silale tabar falon kanta aqasa cikin kunya.
Cikin 6acin rai Pumpy ya qarasa shigowa falon sannan ya kalli Mummy da kanta ke qasa har yanzu takasa hada ido dashi yace"koma ki zauna marar tawakkali da yarda da kaddara,tun shigowar Abu nake tsaye a window ina jinku kuma ina kallonku,wacce irin masifa ce wannan?, memakon ku taru ku rufa mata asiri kunemo mafita shine kuka shirya wannan gurguwar shawarar?, shikkenan ai, yanzu hankalinku saiya kwanta, kun kyauta dakuka tonawa 'yarku asiri, yanzu kunsan adadin mutanan da'ita wannan likitan zata fadawa cewa 'yarku tasamu ciki ta hanyar banza?, kun nuna baku yarda da abinda ya sameku ba kenan?"
gaba dayan su su ukun shiru sukai babu wacce tasamu zarrar kallonsa, duk cikin kalaman sa babu na qarya haqiqa yafisu gaskiya, saide haihuwar shege fa ba qaramin abu bane.
Cikin damuwa Mami ta dago ta kalle shi tace"Yaya dama saboda rufin asirinmu ne shiyasa muka yanke wannan shawarar, muda kanmu ba zamu cutar da Nadra ba, Yaya ka fahimcemu idan Allah ya temakemu cikin ya zube shikkenan asiri alekum"
Cikin 6acin rai ya daga mata hannu yace"dan Allah dakata Abu,banason jin shirmen banza da wofi,ke harkinada bakin cewar rufin asirinku ne?, ai nasan saboda danki kike fadar haka, ko karya nayi?,saboda yarinya ta ambaci sunan danki kina tsoro ayi gwaji aga ciki nasa ne shiyasa zakice a zubar dashi"
Cikin sauri Mami tayi qasa da kanta, ko shakka babu cikin manufofin ta harda hakan ma.
kallonsu yayi jikinsu a salube gaba dayan su, kana ganinsu kasan fadan dayake musu ya shige su, hannunsa ya nuna musu sannan yace" wallahi summa tallahi duk wadda ta kara tunanin kaimin yata asibiti domin a zubar mata da wannan cikin to kotu ce zata rabani da ita,mun riga mun yanke hukunci a bari ta haihu ayi gwaji a gani cikin waye, idan bana Pilot bane za'a gwada Dr. Arif, shima idan ba nasa bane za'a gwada Yayanta Abdul, su ukun nan de sune mazan gidan samari"
ya juya ya kalli matarsa yace"kekuma Sauda tabbas igiyar auranki na rawa, kinji na rantse, ke ko tsoro bakyaji wajan zubar da cikin yarinya ta fadi ta mutu?, koda yake ashe fa kince baki damuba kota mutu ko tai rai, saboda haka mu zuba ni dake"
yana fadar haka ya juya ya fice a zuciye.
kukan Mummy ne yadawo dasu hankalin su, domin kuwa kan kujera ta fada, ta fashe da kuka riris kamar wanda aka aiko mata da saqon mutuwa "wayyo Allah Nadra kin takaice ni a rayuwa, kin cuceni Nadra, kinci amanata, ina tarbiyar dana baki,yanzu dawanne ido zan kalli mutanen duniyar nan?, kin cuceni Nadra"
Mama ce tayi ajiyar zuciya ta dafata sannan tace"kinga, kiyi hakuri Sauda, mu manta da abunda yafaru, bamuda ikon dawo da hannun agogo baya bare mu gyara kuskuren mu, sannan bamuda ikon sauya qaddarar wannan yarinya,abinda yafaru yariga yafaru, saide muyi haquri mu kar6i qaddarar data samemu hannu bibbiyu, mu barta ta haihun kawai, ninayi alkawari zan karbi abinda aka haifa na rike, itakuma Nadra Allah ya bata miji nagari"
Mami kam da qyar ta bude baki tace"yanzu fisabilillah wanne irin hukunci ne wannan su Yaya suka yanke?, shikkenan sai muje asbiti da 'ya'yanmu na cikinmu ana musu gwaje-gwajen ciki wannan yashiga agwada,-wannan yashiga agwada saikace familyn ya'iska?"
tana fadar haka tajuya ta fice daga falon ,harga Allah jikinta yayi sanyi da wannan al'amarin, sauqin ta daya shine ba danta ne yayi cikin ba, bare ace bayan ta haihun za'a liqa masa.q
Kai tsaye part dinta ta wuce cikin taraddadin wannan al'amari, tana shiga falon taga Umaima bata nan tayi tsammanin ta wuce gidanta, hakan yasa ta shige dakinta, saide tana shiga dakin taganta zaune agefen gado ta rafka uban tagumi, zama tayi a kusa da'ita tace"Umaima baki tafi ba?"
Umaima ta saki ajiyar zuciya sannan ta janye tagumi tace"Eh wallahi Mami, ina nan, hankali nane atashe,ina ganin kamar Araf baida gaskiya fa Mami"
Hajiya Abu ta kalli babbar 'yar tata tace"Hmm Umaima kenan, abinda zuciyarki take saqa miki kenan?"
Umaima tace"Mami bahaka bane, gani nake kamar Nadra bazata mai qarya ba, wata zuciyar tana ce dani tabbas shima baida gaskiya"
Ajiyar zuciya Mami ta saki tace"Umaima kenan, har yanzu ke yarinya ce, nice nan na haifeku keda Araf, inda ace baida gaskiya tabbas dazan gane,kuma shima da tuni yace a zubar da cikin saboda karta haifa asirinsa ya tonu"
Aunty Umaima ta jinjina kanta alamun gamsuwa sannan tace"Eto saide hakan, kuma gaskiya hakane Mami inda ace baida gaskiya toda tuni shida yarinyar sunje sun zubar da cikin, ko basu zubar ba toda yanzu shine zai baki goyon baya akan a cire cikin saboda kar a gane shine yayi"
tasake sakin ajiyar zuciya sannan taci gaba da magana "wallahi sai yanzu naji sanyi araina Mami, hankali na harya kwanta,ko yaya ne bazakaso ace naka ake zargi ba"
Mami tace"hakane kam, nima abinda nagani kenan, shiyasa naje wajan Sauda nafada mata ko zamu zubar da cikin kawai,to muna cikin shawarar Yaya yazo ya hana"
Umaima ta numfasa tace"kai wannan masifa, wannan tashin hankali dame yayi kama?, wallahi Nady tazama abun tausayi, dan Allah Mami kubar Nadra ta koma bangaren Mama, dan wlh nakula ba alamun sassauci a idon Mummy"
Mami tace"Eh itama Aishan abinda tafada kenan dazu, tace idan ta haihun ma zata riqe abinda aka haifa,wajanta zata koma"
daga nan sukai shiru gaba dayan su kowacce na sakawa a ranta.
........................................🍁
Alhaji Muhammad ya juya ya kalli dan'uwan nasa yace"Mahmoud yanaga ranka kamar a 6ace? meyake faruwa?"
Pumpy yayi murmushin takaici tareda kallon dan'uwansa kuma twin brother dinsa yace"ba dole kaganni haka ba Muhammad, al'amarin yaran nan damuna yake wallahi, kuma ban qara shiga damuwa ba sai dazu, kaiii wato Muhammad mata basuda tunani da hankali, wai dazu ina shiga ciki naga Aisha taka, da me dakina saudat dakuma Abu sun kira wata likita wai sunaso a zubarwa da Nadra ciki"
Alhaji Muhammad yace"What!?, to ina hukuncin da muka yanke akan a bari ta haihu agani ko cikin waye?"
Pumpy ya girgiza kansa cikin taqaici, nan take ya labarta masa yanda akayi, sannan yaci gaba da fadin"sun gwammace suji kunyar lahira akan ta duniya"
Daddy yayi tsaki "Allah ya ganar dasu, amma kasan kuwa Dr. Arif yayi wauta acikin al'amarin nan?"
Pumpy"yace tame kuma?"
Daddy yace"Haba Alhaji, ai lokacin dayaga tanada cikin sai ya rufa mata asiri harta haihu, yanzu kenan dana na cikina bazai iya rufawa 'yar wajanka asiri ba?, aida yayi haquri idan ta haihu sai yasamu Pilot suyi magana, inyaso ko sakinta ne yayi, sai shikuma Pilot din ya aureta, kokuma yayi hakuri ya rungumi kaddara,sai a sake gyara musu auren kawai"
Alhaji Mahmoud yayi murmushi yace"Muhammad kenan,ko kaine haka zakayi wallahi, because abu ne mai matukar razanarwa, kuma Muhammad kai kayarda cikin Pilot ne?"
Daddy yace"why not?, of course na yarda because yarinyar bazata masa qarya ba,dan yana d'an qanwar mu hakan bazai sa mu bashi goyon baya akan kuskure ba, asali ma babu wanda yafi qarfin kuskure arayuwa"
Pumpy ya saki a jiyar zuciya yace"kwarai kuwa babu wanda yafi qarfin kuskure,amma gaskiya ni zuciyata tana fadamin cewa Nadra qarya take,zaiyi wahala ace Pilot ne yayi wannan danyen aikin inka duba duk zuri'armu bamuda wani ustaz kamarsa,sannan inda shine ai zakaga alamun rashin gaskiya akan fuskar sa kokuma yanayin sa, amma kaga shi tunda aka fara maganar ko a jikinsa,hankalinsa kokadan bai tashi ba, shikuma marar gaskiya ko Yaya yake saiya tona kansa, kuma kasan dazu na hangoshi driver yasaka masa trolley a booth inaga tafiya zaiyi ma"
Ran Daddy ya kara baci, ya gyara zama sannan ya girgiza kansa yace"kai wannan yaro akwai dan rainin hankali, ai bekamata yayi tafiya a wannan halin da'ake ciki ba, amma komai nisan kwana ai dole zai dawo, fatanmu Allah ya kaimu ta sauka lafiya dai agani,aiko cikin waye dole zamu gani, gaba dayansu su ukun za'a hadasu ayiwa kowa test agani"
Pumpy ya jinjina kansa zuciyar sa na yankewa,kansa har sarawa yake saboda damuwa, darura ce acikin zuciyar sa fal, musanman da dan'uwan nasa yasake tuna masa za'a hada samarin gidan duka su ukun ayi musu gwaji, kokadan zuciyar sa bata gamsu da Abdul babban dansa yayan nadra ba, Allah shine abun tsoro Abdul ma abun tsoro ne, saboda shidin manemin mata ne na gaske, cikin sanyin jiki yace "Aminnnn."
......................................🍁
Dr. Arif dake zaune agefen mahaifiyar sa yasaki ajiyar zuciya tareda wani huci numfashi bayan yagama sauraren labarin da mahaifiyar sa ta bashi akan shawarar zubar da ciki dasuka yanke,ya kalleta yace"Mama meyasa to dan zaku zubar da cikin sai kun kira wata likita daban?, da sai kimin waya in kawo muku magani saiku bata kawai, saboda zubar da cikin kawai shine mafita"
gaban mama ya yanke ya fadi,karfa ace shine yayi cikin nan shiyasa yace azubar, cikin tashin hankali tace"Arif, kafadamin gaskiya kayi tarayya da yarinyar nan ko bakayi?"
Cikin sauri ya kalleta yace"Mama wacce irin tarayya kuma?, itama tasan ban tabata ba, tunda gashinan tafada da bakinta"
Mama tace"to in hakane meyasa zakace azubar da cikin inba tsoro kake kar asirinka ya tonu ba?"
idonsa ya runtse sannan ya bude, cikin taqaici yace" kiyi haquri mama, abarta ta haihun, shikkenan?"
yana fadar haka yamiqe yabar falon, yayinda ta bishi da kallo gabanta yana faduwa.
...................................🍁
Nadra tana kwance abin duniya ya taru ya mata yawa,tunani take yanda rayuwa ta sauya mata zuwa qunci,ga azabar ciki,ga bakin cikin rayuwa, ga bala'in Mummy data ke mata,wani irin abu ne yatokare mata maqoshi,har batasan lokacin da hawaye yake zarya daga kan kumatunta zuwa saman qirjinta ba, sosai take hawaye amma koda wasa bata damu da share hawayen ba,cousin cousin sister ta Ummi ce ta shigo da sallama a bakinta ta zauna tareda kallon Nadra, duk gidan su biyun nan itada Ummi sunfi kowa shaquwa acikin yanmatan gidan, ahankali tasaki ajiyar zuciya "Nady" ta kirata.
Shiru Nadra tayi bata ko kalleta ba,Ummi tafara magana cikin tausayawa tace"kiyi hakuri kinji, nasan its painful amma ki daure kici jarabawarki kinji aminiyata"
Cikin rashin son magna Nadra ta daga mata hannu tace"Please Ummi, ki qyaleni dan Allah naji da kaina"
ta bude baki zatayi magana kenan wayar Ummi tayi kara, cikin nutsuwa ta dauki wayar, tana dubawa taga Yaya Pilot ne, cikin mamaki ta kalli Nadra tace"dauki wayar nan, inaga dake zaiyi magana"
wani wawan kallo tayiwa Ummi wanda yasa Ummin takasa magama.
Sake kira yayi akaro na biyu, kai tsaye Ummi ta dauka tace"Yaya barka da yamma"
a taqaice yace"Barka,ina wannan yarinyar?"
kai tsaye itama Ummi tamaida masa da tambaya tace"Nady?"
shiru taji bai bata amsa ba, ta kuma san halinsa bazai ta6a tankawa ba, hakan ya tabbatar mata da cewa itan yake nufi.
Cikin ladabi dakuma kwantar da harshe tace"gatanan a zaune yaya"
a taqaice yace "bata"
wayar ta miqawa Nadra,amma Nadra ko kallon wayar batayi ba bare Ummi tasa ran zata amsa.
Ajiyar zuciya ta sauke tace masa "Yaya nabata amma ko kallo ban ishetaba"
Dan qaramin lips dinsa ya motsa kamar ba zaice komai ba, har Ummi ta cire rai zaiyi mata magana sai can kuma yace"Ok, saka a hands free ki fita daga dakin"
Cikin ladabi Ummi tace"To Yaya"
Ahankali ta miqe tsaye sannan ta saka wayar a speaker tayi abinda ya umarceta tafice tabar musu dakin.
Cikin husky voice dinsa dake rikita Nadra a zamanin soyayyar su yace "Kina jina, please ki saurareni,inaso in miki gargadi na qarshe akan 6atamin suna da kikayi, wannan shine tukwicin soyaiyar dana nuna miki?,ni zakiyiwa sharri?,ki godewa Allah nabar gida kuma Mami na tamin kashedi akan bani-bake,amma banda haka, wallahi tallahi da sai na karya qasusuwanki na watsar,marar kunyar banza kawai, ki rasa wa zaki dorawa wannan sharrin sai ni?"
Wani irin kuka ta saki mai cikeda tsantsar nadama tace"karya kake Araf,mayaudari ne kai,ashe dama soyayyarka zata iya kassaramin rayuwata?, wallahi ka cuceni Araf, ka lalatamin rayuwa, amma kasani bakomai akwai Allah, kuma ka rubuta ka ajiye sai anyiwa 'yarka abinda kayimin"
wani irin baqin ciki ne yakama Araf, ada kam bai yarda Nadra ta rainashi ba, amma a yanzu haqiqa yayarda duk duniya babu wacce ta rainashi taga makwancin sa kamar ta,tabbas akwai alamun tasamu matsala a qwaqwalwarta, tsabar taqaici da baqin ciki daya kamashi gaba daya ma kasa magana yayi, batare da yace mata komai ba yayi qit ya kashe wayar.
Cikin waye littafin kudi ne, 500 ne kacal
8033330504
Amina Muhammad
Moniepoint
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
tareda shaidar biya ta wannan number 08033300034
Yan Niger kuduba ArewaPen na dorashi.
Amnah El Yaqoub ✍️
🍁CIKIN WAYE ?🍁
(A Confused Family Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
page 9&10
*Wattpad*:
AmnahElYaqoub
*ArewaPen*:
@amnahelyaqoub
*Facebook username*:
Amnah El Yaqoub
*Subscribe* *to my YouTube channel domin sauraren CIKIN WAYE* 👇:
https://youtube.com/@amnahelyaqoubnovels?si=-4w3XDkwjZA1hj0k
*Whtsapp channel link:*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
*Like my page on Facebook👇*
https://www.facebook.com/share/1a9oXkTpcy/
Cikin Nadra yakai wata takwas,gaba daya ta kumbara sosai, ga cikin nata ya girma dayawa, kowa ya kalleta sai ya tausaya mata.
zaune suke tareda yan'uwan nata gaba dayan su,harda su farida da Umaima, sunata firar su kadan-kadan, farida ta kalleta tace "Nady kina zuwa awo kuwa?"
kanta ta girgiza alamun a a bata zuwa
Umaima tace"amma ya kamata ki fara zuwa saboda next month zaki haihu"
shiru tayi ba tace komai ba, tana de binsu da kallo daya bayan daya,Umaima tasake cewa "sannan kuma ki dinga motsawa kina tattaki koda acikin gida ne kinji Nady?"
hawaye ne me zafi ya zubo daga idonta, kawai de tanajin Aunty Umaima ne, amma ita kadai tasan baqin cikin datake ji aranta, ganin tana wannan hawayen ne yasa jikinsu yayi sanyi domin kuwa duk surutu irin na Nady yanzu tazama kurman dole, duk cikin yan'uwan nata Ummi kadai take wa magana agidan.
Meena ce ta qaraso wajan su tace"Nady kije Hajiya tana kiranki"
ahankali ta miqe daqyar tana cije lips dinta ta nufi part din Hajiya, tana tafiya tahadu da Mummy, cikin rawar murya tace"sannu Mummy"
kallonta Mummy tayi, tasake kallon qaton cikin ta, ta watsa mata harara tayi gaba ta barta.
daqyar taja qafafun ta ta qarasa part din Hajiya, tana shiga ta hango Ummi, saikuma qamshin turaren dake sakata annashuwa awatannin baya,duk da tasan cewa ba yanda za'ai taji qamshin turaren Yaya Pilot inde ba zuwa yayi ba, hakan baisa tayi gigin juyawa inda yakeba bare su hada ido.
shima anasa 6angaren tunda tataho ya zuba mata ido yana kallonta, zuciyar sa cikeda tausayin halin datake ciki, saide Idan ya tuna qazafin da tayi masa sai yaji ransa yasake 6aci, tun ranar da balli yatashi akai family meeting ya tattara ya koma bakin aikinsa bai sake ganin ta ba sai yau,haka bai sakejin koda sautin muryarta ba tun ranar da sukai waya da'ita yayi mata kashedi.
Nady kam ko kallon inda yake batayi ba, ta qarasa ta zauna agaban Hajiya ta gaida ta.
Cikin dakiya da rashin wasa shima ya dauke kansa daga kallonta ya kalli Ummi yace"wannan yarinyar tana zuwa ganin dr. kuwa?"
Ummi ta kalleshi taga fuskar sa ahade babu alamun wasa tace"wallahi Yaya bata zuwa, munyi-munyi da'ita taje amma taqi zuwa"
kafadunsa yadaga alamun rashin damuwa, bai kalli inda takeba ya juya yadubi Hajiya yace"ku kaita asbiti, saboda kumburin nata yayi yawa,kana ganin ta kasan akwai matsala, kuma Hajiya kina zaune a gidan nan amma a rasa me kaita asbiti?"
Aunty Umaima data shigo falon yanzu ta kalleshi cikin harara tace"anqi akaita din, meyasa bakazo kakaita ba?"
Cikin sauri ya hade hannunsa waje daya yace"Maman Farouq please kiyi haquri,amma ku ajiye fishi ku kaita taje taga likita, gaba daya family kowa ya zuba ido akan wannan ciki amma ita yarinyar bakwa kula da lafiyar ta"
Nady ta dago kanta tace" anqi aje din kokuma ka daukeni ka kaini, banza dan'iska kawai, mugu,azzalumi, in Allah ya yarda a'idonka za'a wulakanta yarka kamar yanda kamin"
tana fadin haka ta rushe da kuka sosai kamar ranta zai fita,yanda take kukan kadai zaka kalla kasan cewa bata cikin hayyacinta.
lokaci daya ran Araf ya 6aci,yarasa awanne dalili zata dinga jifansa da munanan kalamai irin wannan, cikin sauri yatashi ya nufeta gadan-gadan babu alamun Rahma akan fuskar sa, a yanda ya taso din nan idan aka barshi tsaf zai iya yimata illa.
Hajiya data kasa magana tana kallon ikon Allah cikin sauri ta miqe tasha gabansa ta hanashi qarasawa wajan Nadra,jikinsa har rawa yake tsabar 6acin rai haka hannunsa ma sai karkarwa yake kana gani zaka tabbatar daya kamata bazai mata ta sauqi ba, Hajiya ta dafa kafadarsa tace"ku dinga haquri da qanwar ku Araf, zafi da qunci ne yasa tayi wannan furucin kuma ba'a hukunta mace da farucinta".
har yanzu idonsa yana kan Nadra yakasa daina kallonta,haka launin idanuwansa sun fara sauyawa zuwa ja, yaso ya wanke ta tas,amma saboda Hajiya ta tunatar dashi situation din datake ciki shiyasa baiyi mamakin masifar tata ba.
cikin sauri Anty Umaima ta janye ta suka shige dakin Hajiya.
saida yaga shigar su dakin sannan ya dauke idonsa akanta, ya janye hannun Hajiya daga kafadarsa, yace"amma Hajiya ya dace ta dinga yimin rashin kunya haka?, yaushe aka haifeta?, meyasa zata dinga bibiyata da sharri?"
Cikin lallashi Hajiya tace"Nasani, kayi haquri"
Kansa ya girgiza cikin damuwa sannan yanufi qofa zai fice daga falon tareda fadin "Allah ya sauke ta lafiya,gara ta haihun agani ko cikin uban waye a jikinta"
cikin sauri Hajiya ta bishi da kallo, kamar taji yace Allah ya sauke ta lafiya, anya Nadra ba qarya take musu ba?, Idan shine yayi mata cikin tayaya zai yi Addu'ah Allah ya sauke ta lafiya har yana ikrari agani ko cikin uban waye?
Bayan yabar part din Hajiya tafiya yake yana tunani, gaba daya ransa ba dadi.
................................🍁
Haka rayuwa taci gaba da juyawa Nadra, tako'ina babu sauqi, saitaje wajan Hajiya ne kadai take samun sassauci, hatta mahaifiyar ta kyararta take, yauma bayan tatashi kai tsaye tabar part dinsu tatafi wajan Hajiya, ahankali take takowa harta qaraso cikin falon, anan taga yayunsu maza su ukun suna zaune, Yaya Abdul, Araf Pilot, dakuma dr. Arif.
tunda tataho Yaya Pilot ya hangota cikin ajinsa ya dauke kansa, bai sake kallonta ba harta qaraso kusa dasu.
shikam dr. Arif kasa hada ido yayi da'ita saboda kunyar ta yakeji bayan ya gujeta yace bazai zauna da fasiqa ba, sosai yake tausayin ta amma babu halin nunawa,gaba dayansu basu iya yimata magana ba.
Abdul ya girgiza kansa cikin damuwa yace"Allah mai girma"
ita kam ko kallonsu batayi ba bare gaisuwa ta hadasu ,gaba dayansu su ukun haushin su take ji, jitake kamar ta rufe su da duka, tafiyar ta kawai take zuwa dakin Hajiya, a daidai qofar shiga dakin tayi tuntu6e saiji tayi timmm tafadi qasa.
kan kace me, ai gaba dayansu su ukun aguje sukai kanta musanman dr. Arif daya kasance likitan mata yariga yasan illar hakan,yana zuwa kanta baiyi wata-wata ba yasa hannu zai cicci6eta.
Cikin tsananin kishi da baqin ciki Pilot yasakar masa wata irin tsawa ya tureshi yana fadin"don't touch her"
Cikin sauri dr. Arif ya kalleshi da tsananin mamaki,a wannan halin datake ciki wanne kishi za'a nuna?, yanayin yanda Pilot yayi masa tsawar kamar har yanzu akwai soyaiyar Nadra aransa duk da awatannin baya iyaye sunyi masa shamaki da'ita, yayi tunanin Pilot din yariga ya cire Nadra aransa tunda akai musu aure.
ganin yanda dr. Arif din yake kallonsa yasa cikin masifa yace masa"kasan kana tausayin ta amma ka'iya daga hannu ka mareta kwanakin baya?, kodan kaga banyi ma magana ba akan haka?, alokacin igiyar aurenka tana kanta shiyasa ban daukar mata mataki akan hakaba"
Abdul yayi tsamo-tsamo jikinsa yana rawa, tun suna yara babu wanda yakejin kansu su ukun nan, sunada hadin kai sosai ta yanda basason 6acin ran dayansu, amma gashi akan mace har ana qullatan juna arai, ya tsorata sosai ganin yanda ran pilot ya 6aci har jijiyoyin wuyansa suna futowa,gabansa sai faduwa yake yarasa dalili.
fuskarta Pilot ya riqe da hannunsa biyu yace" Nadra!!, Nadra are you ok?"
ganin de shiru babu motsi atare da'ita hakan yasa cikin sauri ya dauke ta cak a hannunsa sai mota, dr. Arif da jikinsa yayi sanyi saboda maganganun da Pilot yafada masa haka de yabi bayan Pilot din yabude masa motar yasaka ta, sannan yayi sauri yajasu sai asbiti .
Abdul kuwa dama da yaga masu bala'in akanta sun gama kishin sun dauke ta shiyasa bai bisu ba kai tsaye yashiga yasanar da Hajiya, daga nan yafuto da gudu yayi part dinsu yafadawa Iyayensu gaba daya halin da'ake ciki.
kan kace me,kowa na gidan na asibitin, har masu auren,kowa yayi shiru ana cikin zulumi babu wanda yake magana, sai Abdul ne kadai yake bada labarin yanda akayi,duk wanda yazo asbitin sai Abdul ya tsara masa.
Iyayensu maza suna tsaye daga gefe kowa yanayi mata Addu'ah acikin ransa,suma iyayen mata gaba dayan su suna zazzaune kowacce da abinda take saqawa aranta.
Araf Pilot kuwa yana zaune agefen Hajiya yayi shiru.
Mamy kam bata zauna ba, tsaye take tana Addu'ah Allah ya sauke ta lafiya ayi wannan gwaji asirin uban kowa yafuto fili itade asamu a wanke danta daga zargi.
kusan awa daya aka