Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🍁CIKIN WAYE ?🍁 (A Confused Family Story) Writing By Amnah El Yaqoub page 1&2 *Wattpad*: AmnahElYaqoub *ArewaPen*: @amnahelyaqoub *Facebook username*: Amnah El Yaqoub *Subscribe* *to my YouTube channel domin sauraren CIKIN WAYE* 👇: https://youtube.com/@amnahelyaqoubnovels?si=-4w3XDkwjZA1hj0k *Whtsapp channel link:* https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45 *Like my page on Facebook👇* https://www.facebook.com/share/1a9oXkTpcy/ Sai kuka jini a littafin CIKIN WAYE ko?, a qarshan littafina MATAR ABBANA na sanar cewa qarshan wannan shekarar damuke ciki zaku jini acikin littafi na nagaba me suna Rayuwata,kuma sai kukaga sa6anin haka, maganar gaskiya labarin nan na Rayuwata yayi tsawo dayawa, bazai iyu nagama shi sannan inyi posting dinsa qarshan wannan shekarar ba kamar yanda nasaba kawo muku zafafan labarai na sau daya ko sau biyu a shekara,shiyasa na ajiyeshi agefe nakawo muku dan qaramin labarin CIKIN WAYE ku rage lokaci dashi, shikuma wancen zanyi qoqari in rubuta shi zaizo muku sabuwar shekarar da zamu shiga insha Allah, labarin Cikin waye labari ne na family wanda na tabbatar insha Allah zai nishadantar daku,sannan zai motsa muku tunanin ku wajan son gano waye asalin me wannan ciki?, inaso mu wasa qwaqwalwar mu da wannan labari,ku qaraso ayi nishadi,a dauki darasi, ayi tafiyar tare daku😍 _____ Kallo d'aya zakayiwa mutanen palourn kagane hankalin su a tsananin tashe yake, babban falo ne wanda aka qawatashi da hamshaqan kujeru masu mutuqar tsada dakuma kyawun kallo, kyakykyawan light blue din carpet ne malale a dukkanin falon, gefe guda ga wani tangamemen enlargement din photonsu a ajiye agefe, gaba daya mutanan gidan babu wanda babushi acikin photon, Hajiya Kaka ce atsakiya yayinda 'ya'yanta dakuma jikoki suka zagayeta,sosai esi take aiki afalon amma hakan bai hana duk jama'ar dake ciki yin zufa ba, duk wanda ka kalla nan take zaka hango tashin hankali a kwayar idonsa, banda mutum daya, wani hadadden gaye wanda yake zaune agefe kokadan babu damuwa atare dashi asalima karatun Alqur'ani yakeyi da IPhone 16 din dake hannunsa,matashi ne me jini ajika, aqallah zai kai shekaru ashirin da tara, shine kadai zaune agefe hankalinsa kwance babu alamun damuwa atare dashi. Alhaji Mahmoud dake tsaye fuskar sa sharkaf da gumi duk kuwa da tsananin esin dake aiki a rantsatstsen falon, banda ambaton sunayen Allah babu abinda yake,gaba daya yakasa zaune yakasa tsaye sai sintiri yake afalon,yayinda sautin kukan NADRA kadai ke tashi a falon, Hajiya Kaka dake sanye cikin wani dakakken leshi wanda kana gani zaka tabbatar cewa uwar masu gida ce ta dace da wannan shiga, ta kalli babban d'anta Alhaji Mahmoud cikin tsananin damuwa da baqin ciki sannan tace"Zauna Mamudu, wannan maganar bata tsaye bace" a salu6e ya zauna tareda zura hannu cikin aljihun babbar rigarsa ya dauko Handkerchief fari qal ya goge zufar data wanke masa fuska sannan yakallo matarsa Hajiya Saudat wato mahaifiyar NADRA, wadda ta buga uban tagumi da hannayenta biyu yayinda gefe guda jikinta yake rawa banda fad'uwa da gabanta yake faman yi duk lokaci daya. Hajiya Kaka ta qarewa kowa na palourn kallo tsaf, ta maida dubanta zuwa ga wani matashi wanda yake sanye cikin qananun kaya riga da wandon jeans,fari ne tas tamkar balarabe, kokadan babu digon baqi atare dashi, haka a shekaru aqalla zai kai 28 to 29 years, yanada innocent face ta yanda bazaka taba gane shine yayi laifi ba,shi dama can haka yake tun suna yara, koda yayi laifi idan ka kalli fuskar sa ta salihai bazaka ta6a cewa shine yayi laifin ba. Hajiya Kaka tasake kallonsa dakyau tareda sakin ajiyar zuciya tace"Dr. ARIF!" Ahankali ya dago kansa ya kalleta batare daya amsaba. ta muskuta ta sauko kasan carpet ta zauna dakyau sannan tace'' duk nan wajan ba bare ko?'' cikin gamsuwa da tambayar tata ya gyada kansa alamar eh, Hajiya Kaka ta jinjina kanta sannan tace"Alhamdulillah, kaga daga Babanka Muhammad,kawunka Mamudu, kanwar Babanka Abu,iyayenku mata, saikuma kannanka da yayyenka hakane?" Dr. Arif yace"Hakane Kaka" Hajiya Kaka tasake kallonsa ta numfasa cikin damuwa sannan tace"Dr. Arif kazo mana da rikitacciyar magana wadda ta girgiza zukatanmu, tasanyamu cikin damuwa,yau watanku hudu da aure kuma matarka Nadra tanada ciki wata 4 hakane?" cikin Sanyin jiki Arif yace"hakane Kaka" Hajiya Kaka tace"tom Arif, amma kace ba cikin ka bane, menene gaskiyar magana?, Inaso kadubi Allah Arif, kada kamata kazafi,kafada mana gaskiyar magana akan cikin dake jikin Nadra CIKIN WAYE?". Arif yasake dago kansa ya kalli kowa dake palour, sannan ya maida kansa qasa yace"wallahi Hajiya Kaka ba cikina bane, asali ma banyi tarayyar aure da Nadra ba wallahi tallahi!, kuma gatanan ku tambayeta kuj......" Tun kafin yaqarasa cewa ku tambayeta kuji Hajiya Saudat Mahaifiyar Nadra ta fusato cikin 6acin rai da masifa ta daga hannunta alamun dakatarwa sannan tace"kai dalla dakata!, kada ka raina mana hankali mana, ka nutsu kasan mekake fada,wacce irin magana ce wannan wai mu tambayeta muji?, me zamu ji?" "Kinga aakata Saude!!" cewar Mama, mahaifiyar dr. Arif. cikin bala'i da masifa taci gaba da fadin"wallahi baki isa ba,baki isa ina zaune kisamun yaro agaba kina nema ki liqa masa cikin daba nasaba, duk family kowa yasan dana dr. Arif nutsatstse ne,ai bazai mata qarya ba,yariga yafada cewa ciki ba nashi bane, dan haka a rabu dashi" Alh Muhammad Mahaifin dr. Arif ya saki ajiyar zuciya,tunda aka fara magana tashin hankali ya hanashi cewa uffan, ya kalli matarsa mahaifiyar dr. Arif yace"kinga ya'isa haka kiyi shiru Indo, ni tunda na zauna afalon nan na kalli idon Arif nasan cewa qarya yake ciki nasa ne, ban yarda da danki ba, ban yarda dashiba,tun suna yara idan yayi laifi haka za'a hukunta yan'uwansa azuwan sune sukai laifin ba shiba,fuskar salihai dayake da'ita yasa muke yarda dashi to wannan lokacin ba zamu dauki wannan sakarcin ba, duk da dana ne naciki na dole za'a hukunta shi amatsayin me laifi" Hajiya Aisha tace"Haba Alhaji, yaya yaro zaizo da wannan gagarumar matsalar kuma kace ciki nasane?, tunda yace ba nasa bane ai ya kamata ku bincika kugani, meyasa bazaku tahumi yarinyar akan maganar ba?" Cikin 6acin rai Hajiya Kaka ta nuna ta da hannu sannan tace" anqi a tambayeta din, idan ciki ba nashi bane tona waye?, banason jin komai, banason qananun magana tsawon wata hudu yana zaman aure da yarinya waye zai shiga gidansa yayi mata ciki?" Ta juya ta kalli dr. Arif tace"kai Arif dauki matarka ku koma gida" taqarasa maganar tanayi masa nuni da qofa. wani irin kukan baqin ciki ne yakama dr. Arif, wanne irin dangi ne wannan?, wacce irin rayuwa ce haka?, yazaizo da wannan maganar amma kaka tayi watsi da'ita?, hawayen baqin ciki ne ya zubo daga idonsa, yasaka bayan hannunsa ya goge hawayen yace"kiyi haquri Kaka, amma wallahi, tallahi, bazan iyaba,nafada muku niba ciki na bane,bazan iyaba kaka, amma nide daga yau nadaina zama da fasiqa" wani lafiyaiyen mari babansa yamiqe tsaye ya watsa masa yana huci yanajin kamar ya rufeshi da duka, jikinsa har rawa yake saboda tsabar 6acin rai, Alhaji Mahmoud yatashi yaruqo Alhaji Muhammad yana fadin"Haba Alhaji, ya zaka mareshi?, dr. Arif fa ba qaramin yaro bane" Wasu irin sabbin hawaye ne suka silalo daga idon dr. Arif, yayinda hannunsa na dama ya riqe kuncinsa dashi yana kallon mahaifin nasa cikeda tsananin mamaki, domin kuwa zai iya rantse wa tunda suke bai taba daukan hannu ya dakeshi ba sai yau akan Nadra, cikin baqin ciki yace"Daddy, ko kasheni zakayi wallahi tallahi bazan maida Nadra gidana ba,Annabi Muhammad S.A.W yayi mana umarni da mu zabawa 'ya'yanmu uwa ta gari,Daddy meyasa zataje tayi ciki awani waje sannan ku tilastamin zama da'ita?, bazan iyaba Daddy, koda naci gaba da zama da'ita zan dinga zarginta ne, bayan wutar tsanarta da zata dinga ruruwa ajikina". Jin wannan maganar ta dr. Arif itace tasa jikin kowa dake zaune afalon ya karayin sanyi. Mummy mahaifiyar Nadra cikin fusata tace"aikuwa yau za'a yita a gidannan,billahillazi in abunda na mallaka zai qare bazan taba yarda a dorawa 'yata laifin zina ba,ban bawa Nadra wannan tarbiyar ba,wallahi kabani mamaki dr. Arif, duk irin karramawar da mukayi ma amma karasa wadda zaka jefa da kalmar fasiqa sai Nadra, bakaiba har iyayenka sainayi shari'ah dasu akan haka" Cikin fusata mahaifiyar dr. Arif tamiqe tsaye tareda kallon Mummy tace"so what?, wallahi nima bazan zuba ido aliqawa dr. Arif cikin daba nasaba, ita yarinyar ai tasan inda taje ta yayimo cikinta" Hajiya Abu wadda yaran suke kira da Mami, qanwa daya tilo awajan Alhaji Muhammad mahaifin dr. Arif, dakuma Alhaji Mahmoud mahaifin Nadra,ta kalli matan yayun nata ganin yanda idonsu ya rufe akan 'ya'yansu har sun manta iyaye da 'ya'ya da jikoki ne afalon, ta numfasa tareda firfita da tafin hannayenta alamun zafi yadameta duk da sanyin dake falon tace"ku dakata,tun dazu kunata abu kamar qananun yara duka ku biyun nan, shin tinda aka fara maganar nan kun tambayi Nadra?, kunji ta bakinta?, kawai daga jin abinda dr. Arif yace baku tambayi ita Nadra ba, amma kun zauna sai 6a6atun banza kuke musammam ma ke Sauda" Ta qarasa maganar tana kallon Mummy, mahaifiyar Nadra. wata irin harara Mummy ta wurgawa Abu sannan tace"Ina ruwanki a maganar nan Malama?, nakasa dake ne?" Mami ta kalli cikin idon Mummy tace"da ruwana Sauda, tunda dr. Arif da Nadra nima yarana ne, yaran yayuna ai inada ikon magana akansu nima, saboda haka bakida hurumin dazaki hanani magana akai" Alhaji Mahmoud mahaifin Nadra ya goge gumin fuskar sa sannan ya kalli qanwar tasu yace" tabbas Abu bamu ji ta bakinta ba har yanzu, amma ai gatanan" ya juya ya kalli Nadra wadda kanta ke qasa, idonta banda d'igar hawaye babu abinda yake, tun tana goge hawayen harta gaji ta barshi yana sauka qasan kumatunta,yarinya ce qarama bazata wuce shekaru goma sha takwas ba, fara ce tas kamar ka latsa jikinta jini yafuto,tanada tsananin kyau wanda babu wani namiji da zai kalleta ya'iya dauke idonsa akanta, tanada kyakykyawan jiki babu alamun rama ko mahaukaciyar qiba atare da'ita, jikin nata dan dai-dai ne a murje take, yanayin zaman da tayi dakuma rashin mayafin kirki ajikinta hakan yasa qaton kwankwasonta yasake bajewa akan carpet din dake malale afalon, dogon gashin idonta yajiqe sharkaf da hawaye yayinda fatar saman idonta tayi luhu-luhu ta kumbura alamun tasha kuka harta qoshi, tanada manyan idanuwa masu bala'in daukar hankali farare tas, saide a yau wannan fararen idon nata yarine ya koma jajir dashi kamar gauta, dan qaramin pink lips dinta yabushe saide ruwan hawayen dayake gangarowa akan kumatunta shine yake sauka har zuws lips din nata, sanadin hakane lips din nata yadan jiqe. "Nadra" mahaifin nata yakira sunanta. lokaci daya kallo yakoma kanta,duk ilahirin mutanan falon kowa saiya zuro idonsa yana kallonta,wannan Hadadden Gayen dake zaune agefe kamar babu shi afalon yadan motsa lips dinsa sakamakon karatun Alqur'ani dayake acikin iPhone dinsa, yakai qarshen surar dayake karantawa tareda switching wayar ya dago kansa yana kallon mutanan falon, har yanzu babu alamun damuwa ko tashin hankali a tattare dashi asalima qafafun sa yasake hardewa yana kallon kowa, hadadden gaye ne naqin qarawa,yanada chocolate color fatarsa kamar ta kyawawan mazan Ethiopia, kana kallon fatar jikinsa zaka tabbatar hutu da jin dadi ya ratsashi,kalar idanuwansa sak irin na Nadra saide nasa yana dan lumshe su kamar me jin bacci,yanada dogon hanci tareda cikar gashin gira ta yanda idan yayi larabci tsaf zakace shidin balarabe ne, dan qaramin baki gareshi mai ban sha'awa yayinda yakeda cikar sumar kai mai laushi kana gani kasan iya sumar kansa kadaima tana lashe kudi ba dan qarami ba,koda wasa babu rahma a fuskarsa, domin kuwa kallo daya zaka masa ka tabbatar shi din cikakken miskili ne nabugawa a jarida,fuskarsa a dinke take babu fara'ah, tunda ya zauna afalon ransa a6ace yake, ba kuma wani ne ya 6ata masa rai ba hakanan yanayin fuskarsa take a koda yaushe, agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa me cikeda gargasa ya kalla yana d'an sakin dan qaramin tsaki acan qasan ransa, yayinda zuciyarsa ta matsu dason tashi daga wannan taron nasu ko zai samu yaje ya watsa ruwa yahuta daga doguwar tafiyar da yayi, tun a jirgi ya gaji, gashi yanzu sun zaunar dashi a wannan waje ko samun damar cire uniform din jikinsa baiyi ba, yayi qasa da idonsa ya kalli kayan dake jikinsa Riga da wandon kaki ne na masu tuqa jirgin sama, sosai uniform din pilot din ya karbi jikinsa, farar riga me dauke da tie blue black, sai kuma wando shima blue black,yarasa dalilin wannan taro, yarasa gane fa'idar tara family gaba daya akan batun mutane su biyu,tunda su bai shafesu ba kamata yayi Hajiya Kaka ta sallamesu. Adede wannan lokacin Alhaji Mahmoud mahaifin Nadra ya sassauta muryar sa alamun lallashi sannan yace da'ita"kiyi shiru ki nutsu zanmiki tambayoyi" ya juya ya kalli mutanan falon idonsa ya sauka akan yaronsa Abdul yayan Nadra, chocolate handsome guy ne Abdul,shima sa'an dr. Arif ne, yanada kyau daidai nasa, sannan yana tsananin kama da Nadra saide ita fara ce sosai yayinda shikuma yakeda duhun fata, Riga ce a jikinsa me kauri kamar rigar sanyi, rigar tanada dogon hannu, duk yanda rigar jikinsa takeda kauri gaba daya ta jiqe da gumi sakamakon tashin hankalin dayake ciki, hannunsa sai karkarwa yake kamar kace masa kyarat yagudu, sanin wannan family ne cewa kowa yayiwa Abdul shedar neman Mata, abune a bayyane kowa yasan haka dabi'arsa take, manemin mata ne na gaske, hakanne yasake jefa Alhaji Mahmoud cikin tsananin damuwa yana tsoron karfa ace Abdul ne yayiwa qanwar sa ciki, ya saki ajiyar zuciya ya sake kallon Nadra akaro na uku yace''dafarko dr. Arif na shaye- shaye ne?" kanta ta girgiza sannan ta goge sabon hawayen idonta har dimples dinta suna lotsawa, cikin qasa-qasa da murya tace"a'a Pumpy" gyada kansa yayi sannan yace" good, abu na biyu kuna samun matsala keda shi acikin zaman dakukai na tsawon wata hudu?" a wannan karon ma kanta tasake girgizawa alamun a a sannan ta bude baki tace" a'a" ataqaice. Alhaji Mahmoud ya jinjina kai yace" to wanne irin zama kuke?, menene yake faruwa atsakanin ku?" wani irin sabon kuka ne yaci qarfinta sosai, kanta ta maida qasa banda sheshshekar kukan ta dake tashi afalon babu abinda kakeji. Har saida Mummy tadaka mata tsawa sannan tayi shiru. Alhaji Mahmoud yace" ina jinki" Cikin tsananin kuka tace" wayyo ni Nadra na banu na shiga uku na nidai, yau na mutu na lalace" Hajiya kaka tace"Malama ki mana shiru anan ki fada mana gaskiya, wannan koke-koken ba shine dalilin zaman muba, dalilin zamanmu shine muji inda matsala take mu taru mu warware ta" Nadra ta dago kanta idon jajir kamar gauta tace"Ku yafemin Pumpy, Mummy dan Allah kuyi haquri kuyafemin" Alhaji Mahmoud yanajin haka ya lumshe idonsa, gabansa banda fad'uwa babu abinda yake,amma duk da haka yanayin sa bai nunaba, ya dubi 'yar tasa yace" Nadra, ki fadamin gaskiya kafin raina yasake 6aci kinji ko?" yamata magana da tattausar murya,ahankali tace"Pumpy tabbas BA CIKIN YAYA ARIF BANE,cikin shege nayi,agida akamin cikin wallahi" lokaci daya falo ya dauki salati, gaba dayan su yara da manya salati kowa yasaka a wajan, Hajiya Kaka harda tafa hannaye idonta akan Nadra,su kuwa iyayen tunda su kaji tace agida akayi mata cikin sai idonsa yakoma kan samarin gidan. Aunty Umaima babbar jikar gidan ta kalleta da tsananin mamaki tace"Nady kinada hankali kuwa?" Nadra koda wasa bata dago ba bare ta kalli ko mutum daya daga cikin mutanan falon, kanta yana qasa sai wani sabon kuka dayake shirin zuwa Mata amma tana neman danne shi, Mama mahaifiyar dr. Arif tagama tafa hannayenta sannan tasaka tagumi tana kallon Nadra tace" tirqashi, amma kin 6ata wayonki, Auta?" Mami qanwar Alhaji Mahmoud da Alhaji Muhammad wato Hajiya Abu kenan, tayi tsaki tace"a'a, kar kuga laifin Nadra, mutanan gidannan kuma kunada laifi, idan Nadra nada laifi kune manyan masu laifi,tsakani da Allah kun bar yaranku sakaka ba control, yara sun balaga amma kuna gani suyita kebewa da mazan gidan, ai gashinan kungani, yanzu saiku girbi ABINDA KUKA SHUKA, ku wai ala dole turawa, mtseww, yanzu naga qaryar boko ai" Hajiya Kaka ta kalli Abu tadaka mata tsawa "Rufe mana baki shashasha kawai,saboda jifa ya wuce kanki yafada kan dan wani shine har kike alfahari?, Idan qaddarar data faru da Nadra akan yarki Umaima tafaru yazakiji?" Mami tayi shiru ba amsa, Hajiya Kaka tasake kallonta tace"nace yazakiji?" Cikin nadama Mami tace"kiyi haquri Mama bazan sakeba" tunda Nadra tayi magana bakin Mummy mahaifiyar ta ya mutu murus, kawai kallon Nadra take tanajin kamar tatashi ta rufe ta da duka, wani irin hawaye ne me zafi ya zubo mata, cikin baqin ciki ta fashe da wani irin gunjin kuka tace" kin cuceni Nadra,ina son da nake miki?, Ina tarbiyar ki?, Ina kaffa-kaffan danake miki?, wato ni kika watsawa qasa a'ido ko?, ai shikkenan ba komai, kanki kika cuta, kuma harki mutu tabon nan bazai ta6a gogewa ba a goshinki, kuma tsakanina dake Allah ya........" Da sauri kaka ta katseta"hankalinki daya?, Sauda wato bakisan kaddara ba ko?, ki tuna Allah SWA yace kayarda da kaddara me kyau da marar kyau, dan haka dole mu rungumeta, sannan kuma yazame muku ishara akan sakaci ku wai turawa, ga karyar turawa nan dan haka banason jin wata magana daga gareki" "NADRA" Pumpy yakirata. Ta dago kanta ahankali saide bata yarda ta hada ido da mahaifin nataba. "waya miki ciki Nadra cikin waye a jikin ki?, sannan da auran ki kikayi ko ba aure?" Nadra ta sunkuyar da kanta qasa tana kuka mai daci amma takasa magana. Cikin baqin ciki Mummy tace"bakyaji ne?" Jan zuciya tayi sannan cikin kukan tace"Wallahi Pumpy bada aurena nayi ba, kafin auren ne....." Mummy tanajin haka ta zabura ta miqe tayi kanta gadan-gadan, kafin mutanan falon su farga ta rufe Nadra da duka, sosai take dukan ta da duka hannayenta biyu, cikin sauri Hajiya Abu da Mama mahaifiyar dr. Arif suka riqe ta, Hajiya Abu tace" Haba Sauda, idan hankali ya gushe ai hankali ke nemo shi, kiyi haquri mana" Mama ta zaunar da Mummy akan kujera tana riqe da hannayenta tareda bubbuga kafadarta alamun tayi haquri. Pumpy ya kalli Nadra data fita hayyacinta tsabar tashin hankali yace"kifadamin waye yayi miki?" Cikin tsananin faduwar gaba ta dago kanta, suka hada ido da yayanta Abdul, cikin sauri Abdul ya daure fuska tareda kauda kansa gefe yana mai runtse idonsa,ahankali ta janye idonta daga kansa, tagama qarewa kowa kallo, sannan idon ta ya tsaya akan wannan kyakkyawan matashin wanda ke sanye da kayan Pilot, cikin rawar baki ta motsa d'an qaramin lips dinta tace"................ Salonsa daban ne Hajiya💃💃 Wait.... a naku hasashen CIKIN WAYE? acikin wannan zataran samarin guda uku? Littafin Cikin waye paid book ne, 500 kacal 8033330504 Amina Muhammad Moniepoint tareda shaidar biya ta wannan number 08033300034 Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Yan Niger ku duba ArewaPen nadora👌🏻 Mrs Usman ce✍️ 🍁CIKIN WAYE ?🍁 (A Confused Family Story) Writing By Amnah El Yaqoub page 3&4 *Wattpad*: AmnahElYaqoub *ArewaPen*: @amnahelyaqoub *Facebook username*: Amnah El Yaqoub *Subscribe* *to my YouTube channel domin sauraren CIKIN WAYE* 👇: https://youtube.com/@amnahelyaqoubnovels?si=-4w3XDkwjZA1hj0k *Whtsapp channel link:* https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45 *Like my page on Facebook👇* https://www.facebook.com/share/1a9oXkTpcy/ ____ Cikin rawar baki ta motsa d'an qaramin lips dinta tace"Pumpy kayi hakuri, ina sake neman yafiyarku akan laifin dana aikata, kayi haquri Pumpy, amma rashin sanin ko waye shine yafi alkhairi" Ta qarasa maganar tareda fashewa da kuka mai qarfi,duk wani me imani saiya tausaya mata fiyeda tunani saboda yanda take faman gunjin kuka kamar ba ruwan hawaye take zubarwa ba. Ran Abdul yayanta ya 6aci, tunda aka fara wannan zama baice uffan ba, asalima tsoro da fargaba ne sukai masa katutu cikin zuciyarsa, kallonta yayi tsaf sannan ya daka mata wata uwar tsawa mai qarfi wadda tasa hatta falon saida ya dauka,nan take cikin dake jikin Nadra ya motsa sabida karfin muryarsa yace "Malama yakike maida mutane 'yan iska irinki ne?, anata magana kinyiwa mutane shiru sai kukan banza da wofi kike uban wani ya aikeki kiyi badalar ne?, mtsww" Cikin 6acin rai Hajiya Kaka ta kalleshi tace"Sannu Abdul,nace sannu, yanzu kai harkana da bakin magana?, wato laifi tudu ne ka take naka ka hango nata ko?, saunawa kana shigo da mata gidannan kana badalarka?, ko ka dauka bansani ba?, ai Abdul abinda kakeyiwa yaran wasu ne Allah ya nuna sakayya akan kanwarka wadda kukeji da ita,ka dauka zaka iya yiwa Allah wayo ne?" Wata irin kunya da takaicin wannan tsohuwa suka mamaye shi Abdul,cikin ransa yace kai wannan mata akwai tonon asiri wallahi, agaban iyaye ta dinga kawo wannan maganar ko waye ya tambayeta?. Pumpy ya numfasa tareda fadin"Hajiya kibarshi, kibar ni dashi,dama ina sane da case dinsa dan duk gidannan ba fasiqi mutumin banza irinsa, banza babban kobo" Cikin sauri Abdul yayi qasa da kansa yanajin wata irin kunya kunya kamar zai nutse, yayi daya sanin bude bakinsa, dama kuma daurewa yayi wajan yin maganar domin kuwa zuciyar sa cike take da fargaba dakuma tsananin tsoro, ahankali yasa hannunsa ya goge gumin dayake zuba daga goshinsa zuwa fuskarsa,kana kallonsa zaka tabbatar shi kansa bai yarda da kansa ba. Mami Abu ta kalli Pompy tace" Yaya ku ajiye issue din wancan baida wani muhinmanci ayanzu, muyi facing abunda ke gabanmu" tajuya ta kalli Nadra tace"Auta kifadi wanda yayi miki ciki tun kafin ranki ya 6aci" Ta qare maganar tana kallon Nadra. Cikin tausayawa Hajiya Kaka tace"Kada kukan da yarinyar nan take yi ya janyo mata wata babbar matsalar, kudaina mata fada kubarta taji da abinda ke damunta a ran ta dan Allah, ni gaba daya banason tashin hankali arayuwa ta, tun inajin taqaicinta har ta dawo tausayi ma take bani" Cikin damuwa Mami Abu tace"Haba Hajiya, shikkenan kuma yarinya baza'a yi mata fada ba saiki bata goyon baya?, idan aka qyaleta haka zamu zuba mata ido muyi shiru kenan?, ba gara tafada mana wanda yayi cikin ayita ta qare ba?" cikin masifa Hajiya Kaka tace"nayi Abu, domin kuwa sanin hali yafi sanin kama wallahi, ku duba kugani yanda yarinyar take kuka mana kamar

Chapter 1 of 4