Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
kankani, idan tayi dressing se ka dauka ba Fauxan gidan baba prof bace, Fallin balaga ya buɗe rashin M ɗin ta se abunda ya karu ga rashin daukar raini, se neman tsokananta da yayi sauƙi sede fa ba shi ya hana kana ce mata Kule ta ce maka chass ba. Abunda take yi shine tunda yanzu Sam Sam ba cika zuwa part ɗinsu tayi ba se idan zata gaida Ammi don baba Alhj ma ta manta rabon da su haɗu tunda ya ce baya kaunar ganin fuskanta ta gwammaci ta dinga wasan buya dashi. Idan an tafi school daga an tashi break zata yi bribing gate man sbd su Rahama ma ba cika zuwa suke ba se once or twice in a week, zasu ɗauke ta a gate su tafi gidansu rahama inda wasu abubuwanta suke a nan zasu yi dressing ɗinsu na class su fice yawo, samari kuwa kaman kuda a kan Fauxa hakan yasa ta juya wannan ta waina wanchan ga yadda take sha musu kamshi kaman ƴar shugaban kasa, ɓarin kudi suke mata ba na wasa ba har ta mallaki iPhone 13pro na kanta kuma har gida take zuwa da abunta. Ta chanza mayukanta gabaɗaya zuwa wasu organic masu tsananin tsada, na kafa daban na gashi daban na fuska kala kala, in ta wuce ka se ka jima kana jin kamshin designers perfumes na jikinta. Aka ce akuyar ɗaure in ta samu sake Habaaa, har Sakina da half rayuwarta outside tayi wani lokacin ta kan mutu da kalar gayun Fauxa sede a gida har yanzu babu wadda yayi noticing ana getting to five months. Sau ɗaya fa'iza ta taɓa mata maganan rashin zamanta aji se da ta ja mata katoton layi tayi mata fata fata wadda har ta Haɗa da mahaifiyarta hakan yasa fa'iza dauke kai daga rayuwar ƴar uwar tata. Se dab za'a tashi school take dawowa su koma tare da ƴan gida, wayanta kuwa kullum a ɓoye yake kasancewar ɗakin da take a sashen Jaddah ita kaɗai ce, yanzu damuwanta yadda zata fara fitan dare sbd ana kawo mata cikas sossai da ganin ƙarancin wayewarta sbd rashin zuwa night parties ɗin nan. Zama tayi ta tsara yadda zata ke fita abunta bayan isha zuwa asuba, randa ta fara gwada luck ɗin ta Dukda yadda take a tsorace kuma cikin bugawar zuciya haka ta saka dogon hijab ɗinta bayan ta yi wanka ta gama duk shafe shafenta, fuskanta da ba ko Digon powder se wani ɗaukar hankali yake sbd kyaun da ta kara na musamman, wurin Jaddah ta je tace "Jaddah yau wurin Mammi zan kwana" Jaddah tace "yau kuma ni aka yiwa Hijira kenan, to se da safe" Tana murmushi tace "Allah ya bamu alkhairi" Sashen Mammi tayi ta gaisheta, tace "Mammi bari na tofa miki Adu'ar nan" Kasancewar kullum kaman ka'ida duk dare ta kan je ta tofa mata adu'o'in hakanan kan su wuce school kuma Alhamdulillah sossai Mammi take jin daaɗin kafan kaunar Fauxa sbd Allah na ninkuwa a zuciyarta, kuma duk wadda ya san Mammi se ya ji zancen Fauxa a bakinta sbd irin gudumawar da Fauxa ke bayarwa idan Mammi ɗin ba lafiya. Seda ta shafa mata adu'ar kan ta mike ta nufo hanyar gate, Allah ya taimake ta daidai lokacin baba prof yake baiwa Lawal kuɗi ya amso mishi credit, a jikin flowers ta buya har Seda ya wuce ciki daga masallacin da shi se lokacin yake fitowa, Lawal kuwa yayi waje ta fito da sauri ta fice gabanta na dukan uku uku. Wayanta ta fidda ta kira su Rahama suka zo da driver ɗinsu da shine yake yawo dasu dama suka wuce suna ihun ganinta at this time around. Shiri suka yi suka wuce birthday party ɗin wani saurayin Rahama, wuri ne na manyan yara waenda iyayensu suke da kumbar susa, ado ne kala kala zaka gani da kalar dinkunan rashin kamun kai, kuɗi kuwa ba'a maganan adadin da aka zube don wannan party din musamman. Fauxa ta ja hankalin matasa masu daloli dayawa a wurin kuma kowa so yake ta kula shi, sede fa in tana cikin ji da izzarta ko su Rahama shakkar mata magana suke, Fauxa ta riga ta zama hatsabibiya Dukda bata rabin abunda suke, su suna ɗan taɓa kayan maye hakanan su kan yi soyayyar shan minti sede ko ɗaya Fauxa bata yarda da wannan ba. A nan wurin suka yi till down, gab asuba ta sa wani ya ɗauke ta suka nufi gida, Seda ta bari an shiga sallah kan ta shige da sauri, alwala ta ɗaura kawai ta nufi masallaci dayake ta chanza dressing ɗinta zuwa yadda ta fita, Jaddah dauka tayi ta makara a wurin Mammi tunda Mammi ba koyaushe take samun zuwa masallaci ba. Ba se Fauxa ta samu abun yi ba, se ta kwana waje sau biyu ko sau uku a sati wadda hakan ya kara mata buɗewar idanu ba na wasa ba. **** "Malam kwana biyar ne kawai Don Allah ka yarje mana ka taimaka ka Haɗa wannan plan din, in ba Fauxa ba zamu taɓa jin daaɗin wannan party ɗin ba" Kallon Fauxa da tunda suka shigo bata ce komai ba yayi, yarinyar tana burgeshi tashen balaga ke dibar ta gashi Allah ya zuba mata sanyin kyau, ya jima yana bibiyarta tana wulakanta shi... "Albashinka na wata nawa kake so?" Ta watso mishi tambayar, wani fitinanniyar kallo ya watsa mata kasa kasa yace "just one night stand please Fauxa na jima da ƙishirwanki" Wani banzan kallo da ya kara kunna shi kanta ta mishi tace "am not that kind in baka sani ba ma ya kamata ka sani just say your price!" Rahama tace "Sir please just say your price Fauxa ba irin waennan cheap matayen bane...." "Before the count of three say your price or you loose the opportunity! And I must leave to Abuja" Dukkansu uku kallonta suke da tsantsar mamaki, barin ma malamin wata iriyar yarinyace wannan? Me take nufi? Ba de hatsabibancin nata take shirin sauke mishi ba! Be hankara ba ya ji ta ce "3" Tana murmushi ta danna play a wayanta se ga muryarshi yana faɗin just one night stand please Fauxa wlh na jima da ƙishirwanki... A razane yake kallonta zufa na yanko masa rahama da sakina suka saki murmushi lallai Fauxa ta ci lakabin da ake mata na "Hadari malafar duniya, punkasau babban girki, biri da gatari ajalin mai gona, jan ƙasa na bayan ɗaki kowa ya ganki ya tuna Allah. Kadangaren bakin tulu; a barki ki ɓata ruwa a taɓa ki kuma a fasa tulu. Ba a banza ba, biri ke shan duka a rani, kowacce ze hadiye gatari zamu riƙe masa Kota....." Wannan kirari ne da babu wadda be san Fauxa dashi ba kuma har yanzu idan ana son ganin fara'arta cikakke to ka yi mata wannan kirarin shiyasa yawancin ƴan korensu da hakan suke cin kuɗin ta. Cikin dage gira tace "zaka rubuta mana takarda da sunan zuwa excursion na kwana biyar kuma mu uku kaɗai aka zaɓa daga makaranta. Sannan ka sani ka yi wa kanka don ko biyar ba zaka samu ba! Ka yi abinda na ce kan a tashi or else..." Daga haka ta miƙe ta kaɗa mishi idanu ta juya ta fice suka bi bayanta suna murmushin irin zufan da yake Haɗawa.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank 09039206763 Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Goma* *PAID BOOK* *LAST FREE PAGES* Babu yadda wannan malami da ya shiga tasku ya iya haka ya rubuta don tabbas ya san ƙaramin aikinta ne playing wannan audio wa school authorities daga nan kuma ya san aikinshi gabaɗaya ya rasa, time da ta bashi na cika ta zo ta karɓa tana yi mishi murmushin wulakanci irin nata. Aiko tana isa gida Momma ta kaiwa don ta san daga momma ta amince to Baba Prof ma ya amince ta ci sa'a kuwa babu wadda ya hanata tafiyan suka shirya suka wuce akan ma Gombe ne bayan flight aka biya musu zuwa Abuja. Karfe biyar na yamma suka sauka a birnin tarayya Abuja Motoci har biyu suka zo ɗaukar su Dukda duka duka su ukun ne kuma mota ɗaya suka shiga ɗaya na take musu baya, babban masaukin baƙin da har gomnoni da kusoshin gomnati ke sauƙa matukin motar tasu ya taka birki, masaukin baƙin ba baƙon su bane hakan yasa suka fito kowacce janye da karamar akwati mai taya suka yi ciki. A reception suka haɗe da samarin sakina da rahama suka tarbe su har zuwa masaukin su me ɗauke da parlor da kuma ɗaki daga gani ka san na manya ne, a kujera ta yada zango tana bin su sakina dake lafe jikin samarin su da sunan oyoyo da idanu kan ta taɓe baki ta maida kanta ga wayanta tana cigaba da dannawa. "Ƙawarmu kiyi ordering duk abunda kike so za'a kawo bari mu je mu zo" Najeeb yaron ɗan majalisar tarayya kuma consultant saurayin sakina ya faɗa, kai kawai ta ɗaga musu su sakina suna daga mata hannu kan suka fice. "Wallahi rahama kawarkun nan ta cika ji da kai kamar ƴar sarki" Sakina ta taɓe baki tace "kuma ba ƴar kowa ba ba" Saurayin ta suhail wadda ɗa ne ga ministan lantarki kuma engineer yace "ya zaki ce ba ƴar kowa ba ina gidan Prof kaka ne gidansu? Waye be san su ba a Nijeriya?" Rahama tace "sani daban wayewa daban, gidan kaman rijiya haka yake don ta samu mun fito da ita shine fa ta fimu feleke, ka ga kuwa manyan guys da take Juyawa? Iskancinta na da girma wallahi" Anan suka bar maganan suka cigaba da harkokinsu na baɗala tsantsan rashin ilimin addini da rashin tarbiya suke nunawa a Filin Allah, ba kuma su damu da su su huɗu ne ɗakin ba. Basu dawo masaukin su ba se dare lokacin fita partyn, sun sameta kwance ɗaure da towel tana bacci, tashin ta suka yi kan suka fara shiri suna hiran irin ɗauke hankali da suke son yi barin ma suhail da yace Zubair din jiji da kanshi na dayawa kuma en matan da zasu je wurin are high class hakan yasa suka ƙara zakewa kowacce ta fita fesss kaman ka sure ka gudu. Wani arnen material lace aka yi mata fitted gown dashi wadda ya fitar da duk wani surarta yadda ya kamata ko numfashi me kyau bata yi amma dayake har ya fara bin jiki bata damu ba, kanta ko ɗan kwali babu se wani gyara da ta mishi jelar na reto a bayanta wani high hill shoe da inches ɗinshi ya kusa huɗu ta saka ta rike wayanta suka fito jewelrys ɗinta se dauke idanu suke. A cikin hotel ɗin ne za'a yi sede ta chan baya, ba su isa wurin ba saida aka fara da ɗan jimawa. Kwas Kwas Kwas haka karan takalmansu ya karaɗe ilahirin wurin wadda hakan ya saka celebrant ɗin da ya fara bayani cikin ƙasaita da ji da kai dakatawa. Chak ya tsayar da fitilun ganinsa bisa kanta, Grey eyes ɗinta da ya ji liner se ɗauke hankali yake, Zubair be taɓa ganin halittar da ya tafi dashi a kallo ɗaya ba sai Akan wannan, don kasa cigaba da bayanin godiyan yayi Dukda su Fauxa har sun sama wa kansu mazauni, class ɗin yarinyar ya burgeshi kwarai don har ta zauna kaman bata san ta fisgi hankalin mutane dayawa daga wurin ba. Taɓa shi da suhail yayi ya saka shi farga da ya ɓace a duniyar fauxa Dukda ko sanin ta be yi ba, bayanin ya karasa aka mishi tafi. Yana ba da mic ya koma ya zauna mazaunin shi yana kallon suhail yace "wacece wanchan? Na ganta da buduruwarka" Suhail yace "Zubair in zaka ɗauke kwalamarka kan wannan ka ɗauke sbd ta fi karfin duk yadda kake tunani" Wani banzan kallo Zubair ya yiwa suhail ze yi magana Najeeb yace "kaman yadda suhail ya faɗa nima shawaran da zan baka kenan..." A fusace yace "saboda ita ɗin ƴar waye kenan? Ta kaini? Ni da na Haɗa sarauta da mulki? Karka manta duk wata kwangila Indai daga fadar shugabar kasa ze fita hannuna yake zuwa, ina juya dala da euro so babu wannan magana, ko ka manta ni ɗin Burin kowacce macece da ta san rayuwa da abunda ya kunsa? Kalli ku ga duka en matan da suka taru anan sun yi ado da kwalliya ne sbd su burgeni har su sace zuciyata kuma kun san babu wacce babanta yake ƙaramin mutum me kuke min tsoro? har ta isa ta yarfa ni?" Suhail ya ce "ita ba ƴar kowa ba amma fa uncle ɗinta babu wadda be yi mishi tayin matsayi ba daga mulkin har sarauta ya ƙi, in kana jin Prof kaka to ƴar gidan ce, yarinya ce amma tana da kwarjinin manya daga jininsu ne" Shiru ya ɗan yi, kan ya ce "ni kuma zan baku mamaki akan yarinyar nan Dukda aurenta nake son yi amma na muku alkawari kan ta bar Abuja se na saye zuciyarta da gwagwalan laffuza da salo na" Ihu suka mai, suka yi dariya a tare yana kara cin alwashi akan Fauxa ɗin. Kowa kan shi yake serving sede Fauza bata motsa ba bare ta tashi ta ɗiba, kanta na kan waya tana kallon wani necklace da yayi mugun tafiya da ita.. "Wow wannan tayi! gashi kuwa ba ƙaramin haskata za kiyi ba da zaran ta hau wuyan ki" Ɗagowa tayi ta kalleshi ba laifi kyakyawa ne ajin karshe, magananshi kuma ya ɗan bata dariya Tace cikin basarwa "sai kuma ya kasance bana neman tayin zaɓin kowa kan abunda na san ze yi min kyau ko akasin hakan" Yayi murmushi ya ce "in kin min izini zan iya zama?" Tace "Allah sarki ai bani da hurumi da kujerun nan ɗin don nima a gayyar soɗi na zo" Yayi murmushi me kyau yace "Ai zuwanki ya fi min zuwan shugaban ƙasar Ingila don ni kaɗai na san irin farin cikin da na shiga da ganinki" Ta ɗan ɓata fuska tace "farin ciki??" Yace "yeah, farin cikin na samu matar aure" Kanta ta mayar kan wayanta kaman ba ita ce tayi tambayar ba, kaman ma bata ji amsar da ya bayar ɗin ba, shima shiru yayi yana jan class ɗinshi. Sun shafe mintuna kusan talatin kan yace "Wow! Zaki yi kyau da sarauta" Idanu ta ɗago ta watsa mai kan ta ɗaga tana kallon mutanen wurin da aka fara watsewa ana komawa cikin hadaddiyar club na hotel ɗin inda anan ne asalin chasun, nan an rage lokaci ne da ɗan abinci da snacks. Ba tare da ta ce mishi komai ba ta sake maidawa kan wayanta. "Princess let's go in its time for the real fun" Mikewa kawai tayi suka jera, yace "sunana Zubair turaki am the celebrant, dukda baki tambaya ba" Se sannan tace "oh happy birthday" Yace "thank you! Where's my gift?" Dan murmushi tayi kawai daidai lokacin suka shiga cikin club ɗin da mata suke ta rawan sanda kida na tashi sai de ba sauti sossai. "What do you want as the gift?" Tayi mishi tambayar. "Just ur heart, kina ban zuciyarki kin yi kyautar da ba zan taɓa manta ta ba" Dariya tayi gayen nan na da aiki, basu sake magana ba saboda kiɗar da aka sauya sauti har wani baya jin maganan wani ana ta rawa color bulb na Juyawa daga blue zuwa yellow zuwa red. Cikin ihu yace "Do you mind a drink??" Itama da karfi kaman yadda yayi tace "Non-alcoholic" Kallon mamaki ya mata, kan ya juya hanyar toilet da ya hango suhail yayi yace "bata shan komai?" Kai suhail da yake ba a hayyacinshi ba ya gyaɗa mai, murmushi yayi kawai ya juya ya tafi gaban bar, inda ya sa aka yi mishi mixing kalar fine wines da yake sha, ita kuma yace coke, ana tsiyaya rabi ya sa aka sa mata whiskey marar taste yadda ba zata ji ba, ya riƙo ya kawo mata tace "thanks!" Shan Nashi ya fara yana ganin yadda take rike da nata tana rausayawa a hankali, bakinta na bin waƙar dake tashin. Suuu ta tafi zata zube a sadda ta gama shan drinks ɗin yayi hanzarin sa hannunshi ya rungumo kwankwasonta cup ɗin hannunta ya faɗi ya fashe, murmushi yayi yana shafa fuskanta da Ɗayan hannun nashi yana Juyawa da ita. "Ashe jininki bashi da ƙarfi" ya faɗa a kunnenta in a whisper. Sossai ta bugu tun tana luuu luuu har ta fara ihu da ƙarfi kaman wacce ke jin daaɗin club ɗin ta fara rawa sossai yana rike da ita yana ƙare mata kallo cikin murmushi, be taɓa Tunanin birthday ɗin shin nan ze zama fun haka ba se yanzu. Sun yi rawa har sun gaji en mata dayawa sun kwashi takaicin ganin shi da ita, ita kam gabaɗaya ta rasa hankalinta. Da sauri sakina ta riƙo hannunta tana Kallonshi tace "Zubair kayan maye ka sa mata?" Sakina tace "mun shiga uku! Haba Zubair ka kuwa san me ka aikata?" Yana smirking yace "normal ne fa, am very sure zata ji daaɗin hakan idan ta dawo hayyacinta" "me nufin ka?" Suhail ya jefa mishi maganan, basu kula da surutan ba.. "Guys calm down ba fa abunda nake nufi, kuma babu abunda zan mata..! A hankali time ɗin da kuke yiwa tsoro ze zo, am very sure nan kusa da kanta zata neme ni da soyayyar abunda kuke yiwa tsoro it's just a matter of time" Ya karashe yana dariya sossai, ajiyar zuciya suka sauke sakina tace "ka bi a hankali wallahi baka san kalar haukan Fauxa bane" Riko ta yayi yana cewa "kuyi abunda ke gaban ku" Yana kai nan ya janye ta suka fice. Da sassarfa yake sauƙowa daga matakalar jirgin idanunshi kan tsadaddiyar agogon dake ɗaure a farar fatanshi, sanye yake da baƙin wando da kuma farin shirt wadda kallo daya zaka mishi ka san pilot ne, baƙin necktie ɗaure a wuyan shi, jacket da karamin brief case a hannun hagunshi. Sauƙar su kenan daga Adis Ababa, da sauri aka buɗe mai gaban wata Prado dake Parke don shi ya shige, drivern dake sanye da kaya me tambarin jirgin da ya tuƙon ya ja suka fice da gudu daga airport ɗin. "Sir ina muka nufa?" Ɗan kallon hanya yayi kan yace "transcope hotel" Saita hanya yayi saboda shirun da garin ya ɗauka yayi ta tsuga gudu bai tsaya ko ina ba se harabar na transcope, sauƙa yayi yana furta "thanks" Ciki ya nufa ba tare da ya jira amsar drivern ba, daga yadda yake tafiya zaka san wannan ɗin zakin namiji ne, fuskanshi a kame sai de be hana kyaunshi bayyana ba. Reception ya dakata ya biya room VVIP, ya karbi key ya nufi elevetor daidai lokacin su kuma sun bi ta bayanshi sun shiga, yana shirin rufuwa yayi saurin saka hannu tare da sanya kai ciki... **Tou Readers anan na kawo karshen free pages ɗin Diddigar ƙaya da Naira ɗari uku kachal zaki mallaki sauran ki sha karatu cikin kwanciyar hankali** DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6