Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
hau kujera ki kwanta ki kuma rufe fuskanki da hijabi, maza maza" Da gudu kuwa ta haye tare da janye hijabinta ta rufe fuskan nata. "Wa'alaikumussalam waye ne kaman Farhuddeen?" Saurayin ya karaso yana sanye da blue riga da wando me taushi tare da hular taɓani kaji hadisi yace "nine Jaddah dama baba prof ne ya aikoni in kira masa Fauxa se kuma Aunty Amarya tace min yanzu ta gama wanke wanke baze wuce nan tayo ba" Jadda tace "eyyaa ai kuwa nan ta shigo zazzaɓi ya rufe ta kwab ɗaya dama wanke wanken ma da kyar ta gama shi sbd kawai Amarya ta matsa ne, ka ce mishi bata jin daaɗi" Ko rantsuwa ze yi baze yi kaffara ba lafiyar Fauxa ƙalau tsabar sonta da jadda ke yi yake sa take goya mata baya lokuta dayawa irin wannan, kwafa yayi yana hararanta kan ya juya ya fice. Seda ta tabbatar ya fita kan ta wanckalar da hijabin tana saukowa hakwaranta farare Kal da kaman jera su akayi a waje. "shiyasa nake matukar yinki tawan, shege ya Farhuddeen ina Kallonshi yana harara ta ta wuyan hijab kawai ba yadda ya iya dani ne" Hira suka cigaba da yi da jadda sbd duk jikokinta kowa ya san mutane biyu ne mafi soyuwa a wurinta se kuma aka samu akasi suka kasance WUTA DA AUDUGA. Dab magrib suka ɗauro alwala a harabar na Jaddah suka fito don zuwa masallaci, ɗabi'ar gidan dole duk me kake yi kan magrib ka tabbatar ka gama daga mazan har matan a kira sallah kana cikin massallaci ana kira kuna amsawa kaman yadda addini ya koyar daga karshe ayi Adu'ar bayan kiran sallah se a yi sallah, in an idar za'a yi azkar bayan an gama za'a yi nafila kan kowa ya ɗauki Alqur'ani daga ma'ajiyar Qur'anai na massallacin a hau karatu har zuwa lokacin da za'a kira isha a gabatar ayi nafila karfe takwas na dare kowa ze koma gida don cin abinci da sauran hidimdimu haka da asuba kiran farko dole kowa ya mike ya hau shirin massallaci har yaro ba'a bari, ɗabi'a ne da suka tashi suka tarar ana yi wadda basu san iya tsawon lokacin da aka ɗiba ana yi ba. Tun kan su isa massallacin suka hango ƴan mata wacce zata ɗara Fauxa ɗaya se kuma waenda basu kaita ba su uku se wasu guda biyu da zasu yi sa'anni da ita duk tafiyar daban dabance. Kau da kai tayi ta cigaba da hiranta da Jaddah, bayan sun shige kowa ya zazzauna chan se ga Aunty Amarya da Ammi sun shigo sanye da hijab, daga bayan su mata ne guda huɗu ras, a kallo daɗɗaya zaka iya faɗin kai tsaye biyu Fulani ne, sbd yanayin haskensu se biyu baƙaƙe waenda kuma suke da zane wato tsaga irin na kanuri. Duk gaban jadda suka duƙa suka mika gaisuwa, ta amsa da fara'arta kaman kullum, Fauza ta kalli wata babbar mace daga ciki tana da dirin jiki Dukda tsufa da ya fara bayyana mata kuma fara Kal me yawan fara'a wadda be ɓoye hakwara biyu na hajji dake bakinta ba tace "Mammi sannu, ya ciwon kafan?" Da tsantsar kulawa Mammi ta kalleta tace "sannu Fauxa, kafa da sauƙi idon ki kenan tun asuba ko?" Murmushi kawai tayi, ta juya ga sauran matan kaman dole tace "maami, umma da dada sannunku" Ba don idanun Jaddah dake kansu ba babu wacce zata amsa a cikinsu sbd haushin rainin wayaun Fauxa da a kullum kaman kara karuwa yake, gyaran muryar loudspeaker da ya karaɗe ilahirin unguwan da kiran sallah yasa duk kowa ya samu sahu ya natsu suka fara amsawa. Har zuwa na karshe wato; Laaa ilaha illallah! A lokaci ɗaya duk suka amsa da (laaa ilaha illallah Muhammadurrasulillah sallallahu alaihi wa salam, Allahumma rabba hazihida'awatit tammah, wassalatul qa'imah, aati Muhammadu Al wasilata Wal fadeelah, wa ba'athhu maqaman mahamuda Allazee wa'ad ta. Allahumma Salli ala Muhammad wa'ala aali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed, wa barik ala Muhammad wa'ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed) "ya ke ƴar uwa shin kin san falalar amsa kiran sallah kuwa? Ko wani irin yanayi kike ko wani irin nauyi ne a gareki in har bakinki ze iya motsawa manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ya ce 'idan kuka ji me kiran sallah to ku faɗi irin abinda yake faɗi, sannan kuyi salati gareni, domin wadda yayi salati ɗaya a gareni Allah zai yi salati goma a gareshi". Bayan an idar da isha duk gida kowa yayi anan aka fara haramar cin abincin dare, ita kam dae Fauza ko kallon inda su Fatima suke bata yi ba suma ba wadda ya mata magana saboda tuwo ne kuma miyan kuka ko shakureta ake ba ci zata yi ba. Mp wadda kowa da kowa ke dashi personal a gidan me ɗauke da memory 32Gb cikinshi karatuttuka ne na malamai daban daban da kuma riwayoyi kala kala sede fa Fauza nata harda wakoki kala daban daban na mawaka mabanbanta, memoryn take cire wa ta kai school wata friend ɗinta ta saka a wayanta su tura wakoki duk ta harhardace rabi da kwata yanzu ma wakar Auta waziri na Kewa ta saka tana ji murya chan kasa kasa, Sam bata ji shigowar shi ba se jin kiran sunanta tayi cikin kaushin murya wadda ya sakata saurin mikewa tana zare idanu zuciyarta na bugawa, yau idan waƙar nan ne ya shiga kunne Baba ta shiga uku!.... DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na huɗu* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️** Da wani kalar sauri ta amsa tana me miƙewa tace "Na'am Alhaji! Sannu da dawowa" Be amsa ba se idanu da ya zuba mata, duk cikin yaranshi itace yake jinta na karshe a cikin zuciyar shi, Allah ya gani babu yadda ya iya ne yake zaune da ita amma ya gaji iya gajiya da halayyarta babu randa za'a wayi gari a yini ba'a kirashi kan case ɗin Fauxa ba, a gida babu irin rashin kunyar da baya ji da kunnuwanshi tana yiwa yayyun ta, duk gidan babu wadda baya girmama na gaba dashi se Fauxa, dokarsu kuwa ba a bakin komai yake ba a gareta. "Ki je Baba Prof na kiranki" Daga haka yayi gaba sbd saƙo ne Yayan nashi ya bashi Idan ya shigo ya tura ta, mikewa tayi da hijab ɗinta dogo har ƙasa kaman ta Allah ta fice, harabar gidan tar kaman rana har ta isa babban parlorn na Baba prof dake gefe da shiga kofan sashen nashi da na matanshi, akwai hanya da ze kaika ɗakunan baccinshi kuma akwai wadda ze kaika cikin gidan nashi ta cikin parlorn. Da sallama ta shiga, babban parlor ne me ɗauke da kujerun alfarma, carpet ne me taushi da tsananin kyau malale bisa parlorn duk girman parlorn Seda ya ɗauke tsab, ga kujerun alfarma na asalin royals, chan gefe shelf ne na littatafai har ba zasu kirgu ba. A tsakiyar kujera ta ganshi zaune yana nazarin wani littafi, ta karasa kusa da kafafunshi ta zube tace "Barka da dare baba" Ya kalleta kan yace "yauwa Fauziyya" Fuskanshi ba alamun wasa yace "me ya hana ki zuwa Islamiyya yau?" Wuri wuri ta fara yi da idanu cikin in ina tace "baba... Am dama.. Dama tunda na dawo makaranta ne na fara ciwon ciki shiyasa ban je ba" Yace "kin san Allah yayi mana hani da karya? Ya kuma kwaɗaita mana riƙe gaskiya a kowanni hali? Karki kasance cikin makaryata sbd daga furucinki zan iya cewa kai tsaye ba gaskiya kike faɗi ba, me yasa baki son karatu daga na boko har na Arabi?" Kanta dake kasa ta girgiza tana forming hawaye tace "kayi hakuri" Yace "na haƙura, na san ki da tsanar karya hakan yasa farar ɗaya na gane ki, Fauziyya karatu na da wani irin muhimmanci a rayuwarmu daga boko har arabi, barin ma arabi da ya zama dole wajibi a garemu mu nema, duk girmanka da tsufanka dole ne ka cigaba da neman ilimi sbd shi ze zama haske a rayuwar duniyarka da lahirarka, Allah SWT yace ku sanni kafin ku bauta mini idan har baku sanni ba to ta yaya Zaku bauta mini? Haka kuma Ayar farko da ta fara sauka da Kalmar 'Iqra' ta fara to meyasa bazaki dage wurin gyara gobenki ba?" Nasiha ya cigaba da yi mata da misali da ayoyi da hadisai masu magana akan neman ilimi musamman Addini, tana shiru bayan ya gama ya sallameta ta miƙe ta fice ba wai don ta ɗauki ko abu guda da yace a cikin nasihohin shin ba. Ya kamata ku san wani gida ne haka? Wannan gida da mutane suka mata laƙabi kala kala wasu su ce "GIDAN F" dalili kuwa duka yaran da suke cikin wannan gida sunansu daga F ya fara. Wasu su ce "GIDAN PROF KAKA" dalili kuwa babu wadda be san waye PROF Ibrahim KAKA ba a faɗin Nijeriya da ma kasashen ketare. Dalilinshi ne ya sanya gabaɗaya unguwan tasu ta tashi daga ainihin sunanta ta koma "UNGUWAN ƳAN BORNO" Wannan unguwa na kafe ne a tsakiyar garin Yola na Adamawa state, zagaye yake da barebari Albarkacin dattijon arziki Baba Prof, asalin su ƴan garin Maiduguri ne na jahar Borno, daga uwa har uba barebari ne, a garin Borno Zulaikha wacce yara suke mata laƙabi da Jaddah ta haife su, su biyu ne rak wurin Mahaifinsu Abubakar Kaka, Baba prof wadda Asalin sunanshi Ibrahim Abubakar kaka da kuma ƙaninshi Sulaiman Abubakar Kaka. Mahaifinsu mutum ne me nagarta kuma babban malami a jahar Borno, karatu da karantarwa gadon su ne sbd abunda suka taso suka samu Mahaifinsu da shi kenan, a wurinshi suka fara karatu na addini ya basu ilimi me nagarta musamman ibarahim da kullum karfe biyun dare haka ze tashe shi ya makala mishi redio yana sauraran karatuttukan malamai tun yana gyangyaɗi yana farkawa har ya dawo daga baya idan ze kwanta da kanshi ze cewa Mahaifinsu idan lokacin karatu yayi a tashe shi fa kar a manta. Wani irin buɗewa kwakwalwanshi tayi da Alqur'ani wadda har ya iya qira'o'i da riwayoyi iri iri, a tsakanin ya shiga boko wadda be hana shi yin karatun shi ba, duba da iyayensu girma ya fara kama su gashi shine ɗan su na fari dayake Jaddah tana yawan haihuwa ne suna komawa, haka ta cigaba ko da bayan ta haifi Ibrahim ya tsaya. Shi kaɗai ya buɗi ido ya gani a gidan hakan yasa ya ci alwashin gadar Mahaifinshi, wadda karantawar tashi wata rana yake fata ta zama sadakatul jariya ga Mahaifinshi, yana da shekaru goma sha biyu ya haddace Alqur'ani, hadda marar gargada bare kame kame, be dena karatun littatafai ba har ya shiga jss3 anan ne Jadda ta sake haihuwa bayan shekaru masu yawa inda ta haifi Sulaiman. Shekarar su uku da Sulaiman ya samu scholarship sbd irin kwazo da ilimin shi da ya baza ko ina a cikin garin na Borno, har wasu state ɗin da idan be je musabaqa ba to ze je su debate, quiz, spelling bee da sauransu be kuma taɓa ɗaukan na biyu ba. Madina yayiwa tsinke inda ya dage ya maida hankali yayi degree ɗinshi na farko har kuma lokacin be dena neman ilimin addini ba, bayan shekaru huɗu ya dawo Nijeria. Alhamdulillah be bar iyayenshi haka ba ko da yake chan, ko da ya dawo ya cigaba da taimaka musu da karfinshi, yayinda Sulaiman ya fi maida hankali a boko Dukda dae ba laifi shima yana da iya nashi karatun na addini sede ba kaman Ibrahim ba. A haka ya koma Madina yayo masters fannin kasuwanci, bayan ya dawo ya tafi America yayi degree ɗinshi na uku fannin halayya, anan ne ya dawo Nijeria lokacin Mahaifinsu na cikin hali na ciwo Sulaiman yana jami'a. Wasa wasa Dr Ibrahim KAKA ya zama sananne a harkar musulunci, karantarwa da da'awa babu inda kafafunshi basu taka ba a Nijeriya, wani wurin har jifa suke sha, ruwa, rana, zafi, iska duk ya ƙare a kansu amma basu karaya ba. A haka Allah ubangiji ya karɓi ran Mahaifinsu yana me alfahari da kaɗan da Allah ya bashi masu albarka sede kuma da takaicin rashin ganin auren Ibrahim sbd har lokacin be maida hankali kan mace ba, ina ka fito karatu ina zaka karantarwa, me kaci karatu, me ka sha karatu haka Ibrahim yake. Sulaiman na Bautar ƙasa a Adamawa aka fara hare haren boko haram tashin farko kuma da matukar zafin su hakan yasa Sulaiman ya nemi Yayanshi Ibrahim da ya riga ya zame mishi uba sbd irin respect da yake bashi ya wuce na wa, akan su zo yola da Jaddah tunda apartment da shi baba prof ɗin ya kama mishi me girma ne. Be ƙi ba haka suka dawo cikin garin Yola wadda ya kasance dawowar kenan, wasa wasa Ibrahim yayi wani irin kafuwa sbd mutum ne me zafin nema Sam baya kwanciya kawai yaji daaɗi, a tafiyan su wani kauye ne na mayo belwa ya samo Aisha(Mammi) gani ɗaya ya mata yaji nan duniya itace macen da ta dace dashi ko da ya dawo kan yayi magana Sulaiman ya tare shi da zancen ya samu mata, shima nan ya faɗa musu yayi mata farin ciki wurin jadda harda hawaye. fili babba ya saya ya samu architecture ya tsara mishi yadda yake so gidansu ya kasance na dindin din kuɗi ya zube aka soma aiki, wata uku aka gama komai sashe uku ne se masallaci da islamiyya babba daga jikin gidan, a lokacin aka yi bukin su. Yadda faɗan boko haram ke tsamari a Maiduguri yasa yake ta sayan kananun Gidaje a unguwan yana saka ƴan uwa da abokan arziki kusan almost rabin unguwan shi ya mallaka musu Gidajen su kuma in har ya kiraka akan ka dawo yola to wannan gida naka ne halak malak. Wani irin buɗi yake samu sbd alkhairanshi dake da matukar yawa, basu shekara biyu da Mammi ba ta haifi Yaron su na farko da ya ci suna FAIZAN(Genorous/Me karamci ko kuma beneficence wato me aikata mai kyau), bayan wata uku da haihuwar Faizan ruqayya(Matar Sulaiman) itama ta haihu ta samu ɗiya mace wacce ta ci sunan Fadeelah(Virtuous wato tagari). Ba'a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo da ake kira Sunkani, itama Fulani ce ba'a ɓata lokaci ba aka yi bukin nasu, shekaranta ɗaya Mammi kaman yadda Faizan ke kira ta sake haihuwar ɗa namiji Faahim(me ilimi or mai fahimta). Ammi itama ta sake haihuwar Falaq(Ketowar Alfijir), Anan hankalin Ruqayya ya soma tashi, dama wani irin zama suke yi marar daaɗi da Maa wadda musabbabin abun Ruqayya ce, tunda ta saka kafa gidan ta fahimci nisan dake tsakanin Ibrahim da Sulaiman kaman nisan dake tsakanin sama da ƙasa ne, wai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau. Bata kara shiga tunani ba seda taga irin girmamawar Sulaiman ga Ibrahim kai tsaye zaka iya cewa matsayin mahaifi ya bashi don ko ratar dake tsakaninsu rata ne me girma, randa ta haihu kuwa taga Sulaiman ya ɗauki yarinyar musamman ya kaiwa Ibrahim shi ya mata huɗuba ya sa mata suna alhali ta riga ta faɗawa Sulaiman sunan da take so a sawa yarinyar, ba karamin rikici suka yi ba akan sunan Fadeelah sede Sulaiman ya fi karfinta haka ta bari, sede daga ranar maganan arziki ita da Mammi babu dama chan sama sama ne, se kuma gashi Mammi na jera maza Ita kuma tana jera mata alhali Ibrahim da Sulaiman basu bambanta dukiyar su ba. Zaman doya da manja ake yi a gidan har Amaryar baba prof itama ta haihu ta samu mace, Falusha(Haske). Bayan haihuwan Falusha Baba prof yayi tafiya Maiduguri inda ya dawo da Auren Zainab, ba karamin rikici aka yi da Hussaina ba kan ta saduda, Mammi kam fatan alkhairi kawai tayi mishi, a lokacin ma tana da tsohon ciki inda ta haifi Fahad(Damisa) ba'a ɗau lokaci ba Ammi ta sake haihuwan Fadyaa(sadaukarwa). Hussaina da yaran suke kira Maami ta sake haifan Farrah(Florence nau'in haske), har lokacin zainab bata haihu ba, Baba prof ya karo aure cikin ƴan gudun Hijira Sakinah itama barebari ce usul, a tare suka fara haihuwa da Zainab wacce su Faizan ke kira Umma, ita ta samu Faraj(cure, waraka kenan) yayinda sakina ta samu Farzan(me wayau). Daga nan dukkansu basu sake haihuwa ba seda aka ɗau lokaci Ammi kuwa ta haifi maza biyu a tsakani Farhan(farin ciki) da Faris (horseman). A lokacin Baba prof ya kara sashe a gefe da masallaci sbd matasan yaran da suka fara tasowa, Mammi ta sake haihuwar Farida(ta musamman ko lu'ulu'u me daraja) daga nan har yau bata sake haihuwa ba. Bayan nan Sakinah (umma) ta sake haihuwan Farhuddeen(farin cikin addini). Sulaiman ya ƙara aure inda ya auri sumayya ta zo gidan da ƴarta Fatima, sumayya sun haihu tare da Ammi(ruqayya), Ammi ta haifi Fauza (triumphant wato nasara) yayinda sumayya ta haifi fa'iza (Gain, wato samu). Bayan su Fauxa, sumayya ta kara yara uku Fadiyah(me kyau), Fakiha(fruits) se Faazila(gaskiya) su kenan yaran gidan karan katakap. Mammi na da huɗu Faizan, Faahim, Fahad da farida. Maami na da biyu Falusha da Farrah. Umma na da guda biyu Faraj da Farhuddeen. Daada na da guda ɗaya Farzan. Gabaɗaya yaran na Baba prof guda 9 ne Allah ya bashi. Se Alhaji wato Sulaiman. Ammi na da shidda Fadeelah, Falaq, Fadyaa, Farhan, Faris se Fauxa. Aunty Amarya na da huɗu Fa'iza, fadhiya,Fakiha da Faazila. Gaɓadaya yaranshi 10. Gidan na da wani irin dokoki ne wadda duk tsari na addini ne, yaran kuwa akwai matukar shakuwa, tausayi da kauna irin ta ƴan uwantaka a tsakaninsu Baba prof baya wasa da tarbiyar su ko na miskala zarratin, duk kuma abunda ze shimfiɗa hannu bibbiyu Alhaji ke karɓa. Ya ƙara samun wani girma ne a unguwan sbd yadda baya banbance ƴaƴanshi da na dangin shi Dukda ba komai yake da iko akai ba sede fa ya san duka yaran don dole a islamiyya ɗinshi zasu yi karatu kuma shi da kanshi yake koyar dasu sbd dumbin falala dake cikin koyarwa da yara addini babban sadaqatul jariya ce wacce bata gushewa har se me wannan ilimi ya gushe idan kuma akwai wadda ya koya daga wurin ɗaya haka ze yi ta gudana har illa ma shaa Allah. Wannan al'ada itace zaɓarwa yara abokan zama masu nagarta, kawai ze kira ka a waya akan Zaku yi baƙo ze zo wurin wacce kaza, ko kuma wane kaza na gidan ka yaje wurin wacce kaza na gidan wane, a haka ya Haɗa wani irin bond me girma tsakanin kaɓilarsu ta barebari da suke nan unguwar, kuma duk zaɓin shi suna alfahari dashi sbd baya taɓa zaɓin banza. Mata da mazan gidanshi kan yi karatu har matakin degree ma idan har maneminki be fito ba, sbd ya san muhimmancin karatu ya kuma san karatu wani makami ne da zaka barwa yaro wadda ba ze taɓa tagayyara ba hakan ne dalilin da ya sa ko maneminki ya fito baki fara makarantar gaba da jami'a ba dole akwai yarjejeniyar ci gaban karatun ki don gudun halin rayuwa. Faizan pilot ne wato matuƙin jirgi wadda aka fi sani da Captain Faizan matashi me jini a jika, kyaun fuska da na hali, ilimi both Islamic and western, his father's favorite, the first born to the house of F, har yau Allah be yi yayi aure ba kaman ba Baba prof ne ya haife shi ba. Fadeelah tana auren wani businessman suna zama a Australia with kids. Faahim Navy ne, an aura mishi Fadyaa suna da ƴaƴa biyu. Auren da saida aka kai ruwa rana da Ammi ta saduda. Falaq har yau bata yi aure ba sbd rashin lafiya da take fama dashi. Fahad na aiki da inland revenue with a wife and a kid. Farida tayi aure some months ago with a costume officer suna zaune Lagos. Falusha and Farrah duk tare aka yi aurensu su biyun duk suna yola suna auren ma'aikatan Gomnati. Faraj, Farhan da Farzan duk suna final year of their studies a Apti American University mabanbantan courses. Farhuddeen da Faris suna SS3 Fatima na SS2 Fauxa da fa'iza na SS1 Fadhiya js1, Fakiha pri5 and Faazila pri3. Tou readers ya kuka ji GIDAN F? A tunaninku duk wani haɗin kai da kaunar juna da zaman lumana dake wakana a wannan gida me cike da addini me ɗaurewa ne har abada? Sheɗan ze iya barin ɗaurewar wannan haɗin kan da kaunar kuwa? Akwai wasu abubuwan da ban sa cikin tarihin gidan ba a hankali a hankali Zaku fahimta in shaa Allah, mu je zuwa🏃♀️🏃♀️🏃♀️. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Shidda* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️** "Wa'alaikumussalam warahmatullah sannu da zuwa Mammi" Cewar Fauxa tana me sakin murmushi. Jaddah ma sannu Da zuwa ta mata, Seda ta amsa na Jaddah kan tace "Fauxa ke kam ba zan amsa ba, riƙe kayan ki" Dariya suka yi duka tace "yi hakuri maa in shaa Allahu zan zo" Tace "na gaji da ji, ke kam gidan mu kaman wadda aka yiwa farraku dashi idan ba'a compound ba ko nan sashen Jaddah ba'a ganinki Sam?" Dariya kawai take yi, wlh ita tana rasa dalilin da yasa take kasa shiga sashen na Baba prof, duk matanshi ma dama banda gaisuwa Mammi ce kawai take sakewa sossai, tana son matan ba tare da ta san dalili ba. "Ina yini Jaddah? Fatan mun sameku lafiya?" Cike da so Jaddah ta amsa mata, duk cikin surukanta babu mafi soyuwa a gareta irin Aisha, matar ta dabance cikin mata, tana da kawaici sossai gata da fara'a bazaka taɓa ganinta bata murmushi ba, tana da son mutane da jan kowa a jiki bata damuwa da kai nata ne ko ba nata ba, tana da kirki fiye da zato, duk cikin matan na Baba prof babu me shiga kitchen da kanshi yayiwa Jaddah girki na musamman ya kuma tako ya kawo ya zauna suyi hira sossai irin Mammi. Dukda tana yawan fama da matsanancin ciwon kafa se ta kwana biyu uku ma bata iya tafiya idan ciwon ya tasar mata amma hakan be sa tayi kasa a gwiwa wurin kula da mijinta da surukanta ba, kuma ita da kanta take taya baba prof kula da mahaifiyar tashi mace ce da a duk lokacin da mijinta ze shigo da wani abu a Leda bazata taɓa karɓa ba se ta tambayeshi ina na Jaddah? Idan har ya manta ko be saya ba sbd ganin ta girma da abun ko wani abu haka zata sa ya koma ya sayo, tana da wani ƙima na daban a zuciyar mutanen gidan musamman mijinta da surukuwarta. "Aisha ya ciwon kafan? Fatan kin ji daaɗin maganin nan na Gamborun gala?" Tana murmushi tace "wlh na ji daaɗinshi sossai Jaddah, kafa yayi sauƙi sosai" Jaddah tace "Toh Allah ya qara afuwa" Suka amsa da Ameen. Chan cikin hiransu Jaddah tace

Chapter 3 of 6