Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
ya tambayeshi jiki, cikin girmamawa ya amsa da da sauki Alhamdulillah, bayan shirun seconds kan yace. "In Allah ya kaimu Laraba zan koma Abuja sbd akwai tafiyar da zamu yi da shugaban ƙasa" Murmushi baba ya saki, a ko menene ya kan yi alfahari da wannan yaron nashi, Faizan ba irin normal pilots bane, yana daga cikin manyan pilots da idan ba da su ba shugaban kasa baya tafiya ko ina, bayan nan yana da hannayen jari da kampanunnuka ba daya ba ba biyu ba, Sam be dogara da aiki ɗaya ba, yaro ne shi me tsantsan biyayya ga iyayenshi, babban ɗabi'ar shi kuma kunya yanzu ya san akwai abunda yake son faɗa mishi ne sede yana jin nauyin maganan shine yake ta kwana kwana. Baba yace "masha Allah, Toh Allah ya kaimu ya nuna mana" Yace "Ameen baba!" Baba ya kalleshi yace "akwai wani abu ne kuma? Naga kaman kana son yin magana" Kanshi ya dukar yana shafa kwantaccen Suman keyanshi yace "dama akan maganan Fatima ne" Murmushi baba ya fadada yace "masha Allah, ka shirya auren kenan.. Toh tunda har ka furta wani satin in shaa Allah zamu je wurin mahaifinta mu tambayar maka ita, ai Fatima yarinyar kirki ce ta samu tarbiya me kyau daga Mahaifiyarta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Da Ameen Faizan ya amsa, dukda maganan magana ne da ya kamata yayi farin ciki sede ko kaɗan be wani ji daaɗin hakan har chan ba, hira suka taɓa kadan da baban har baba Alhj ya shigo suka kara tattaunawa kan ya musu sallama ya fice. Bayan ya koma aiki da kwanaki biyar aka tambayar mishi Fatima kuma an bashi sede an ja auren se ta gama secondary school in ya so se ta fara jami'a a gidanshi. **** Kwance take kan gadonta jikinta yayi tsami da bugun da ya Farhan ya mata da magrib ɗin saboda bin wata ƙawarta da tayi gida bata dawo ba se da ana kiran sallahn magrib tun karfe 1:30, da farko basu so dukanta ba sede Sam ta ƙi faɗan inda taje hakan yasa ya Farhan da Ya Faraj suka zane ta har Seda Baba prof da za shi masallaci ya karɓe ta, Allah ya isa take ta ja tana cin alwashi kala kala a kansu, fa'iza dake ɗakin tun da suka dawo daga sallar isha'in bata ce mata komai ba... Suna daga ɗakin Fatima ta shigo a wurin Aunty Amarya da Ammi dake bisa taburma a tsakar gidan suna cin Tuwon dare ta zauna, tace "waii wallahi Aunty mammi na jin jiki, ciwon kafan nan baya mata ta daaɗi ɗan zaman da na yi na awanni a wurintan nan baki ga ba, komai se an yi mata" Ammi tace "Allah sarki, Allah dae ya bata lafiya ai kafa shine komai a jikin mutum, Allah dae ya sa kaffara ne" Aunty Amarya tace "Ameen Ammi, Fatima se ki dinga zuwa kina taya Asiya (ɗiyar Yayar mammi ɗin) kula da ita" Fatima tace "In shaa Allahu Aunty ai Mammi kaman uwa take a wurina, bari na shiga na dubo su Fa'iza mu ci abinci" Mikewa tayi ta nufo ɗakin nasu, tana shiga suka Haɗa idanu da Faozia dake kallon kofan, ɗauke kai Fatima tayi yayinda Faozia tayi tsaki me karfi tace "Fa'iza kin san Allah ko?" Fa'iza tace "me aka yi kike tambayana na san shi mana" Faozia tace "Daaɗina dake baki iya cin riban zance ba, ko da shike manta ma... Dama Tambayarki zan yi da munafukin ɓoye da na bayyane don Allah wanne ya fi?" Fa'iza da bata fahimci zancen ta ba tace "ai munafunci ko ya yake sunan shi munafunci kawai dae gwara wadda ze nuna maka a bayyane ka san dashi da wadda ze nuna maka Musa a fuska fir'auna a zuciya" "sannan in zaka yi abu kayi don Allah da nufi ɗaya ni fa shiyasa bana son hulda da duk munafuki a duniya.." Fauza ta karasa Fatima da ta tsaya kikam tana Kallonsu se hawaye ya fara kwaranya a fuskanta, Aunty ce ta fara shigowa ta buge Bakin Fa'iza tana cewa "yanzu ƴar uwarki zaki Haɗa kai ana cusguna mata a gidan nan Fa'iza? Tana gayamin ina karyatata ashe da gaske ne? Fa'iza..!" Ammi da ita ma ta shigo tayi kan Fauxa zata make tana cewa "Ai ba ita zaki daka ba Auntynsu ita uwar iyayin nan zaki mara har se taga wuta.." Dira Faozia tayi ta Ɗayan gefen kan Ammi ta zagayo ta fice da gudu harda bangaje Aunty goshinta ya ƙume da kofa salati duk suka saki ita kam ko waiwaye babu tayi sashen Mammi da gudu. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Takwas* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️** Karshe dae Aunty bata iya bacci ba seda Baba Alhj ya danne mata goshin aka shafa man zafi, takaici ya hana shi cewa komai, ya aika a kira mishi Faozia ɗin aka tarar bata nan sede Jaddah bata ce bata nan ba kawai cewa tayi a ce tayi bacci Dukda bata san wani laifin ta sake aikatawa ba. Ita kuwa Faozia tana zuwa wurin Mammi ta shagwaɓe tana faɗamata abunda ya faru, Mammi tace "Gaskiya Farhan da Faraj basu kyauta ba ai da lafiyata ƙalau babu wadda zan bari ya taɓa ki su da suke gantalinsu akwai wadda ya hana su ne?" Cikin jin daaɗin goyon bayan da aka bata tace "ai shine" Mammi tace "Faozia am ki rage nemarwa kanki magana kin ji? Bana son yadda kowa ya buɗe baki yace Faozia, Faozia ɗin nan wallahi har raina bana jin daaɗi" Fauziyya tace "In shaa Allahu Mammi bazan sake ba" Mammi tayi murmushi Dukda ta san labarin kanzon kurege ne kullum haka take cewa baze hana gobe tana fita ta jajiɓo wani tashin hankalin ba. Ƙin zuwa wurin jadda tayi wai tana fushi a lokacin da su Farhan ke bugunta jadda bata zo ta karɓeta ba kuma ta tabbatar sarai tana ji. Asiya mammi ta kira akan ta zo ta dubo wa Fauzan abunda zata ci. Faozia tayi Charab tace "Mammi bari na shiga kitchen ɗin da kaina" Har ta fita ta dawo tace "ke fa Mammi kin ci abinci?" Tace "Ina ga Tea zan sha Faozia kubewa suka girka a gidan ni kuma ba so nake ba, je kiyi abunda zaki yi ke kam" Kitchen ta wuce, Asiya dake zaune a parlorn ta bita da harara ko Kulata Faozia bata yi ba don ta jima da sanin Asiya irin mutanen nan ne da suke bari hassadar wani ya gurɓata musu rayuwa, ba tun yau ba ta fahimci Asiya bata ƙaunar ta shiyasa itama bata shiga harkarta. Hijab ɗinta ta ajiye ta fara dube dube a kitchen ɗin Seda ta fidda duk abunda zata bukata na aikin da take son yi kan ta fara aikin, Yawan bin kawaye da take har ana dukanta duk akan girki ne tana matukar kaunar girki babu abunda yake bata nishaɗi a rayuwa irin ta ganta a katon kitchen tana girke girke, idan kaga Faozia a school ta natsu to kallon recipes take a wayan kawaye don gidansu kam ba'a abubuwan zamanin nan. Shawarma da suka yi ɗazu har sanadiyar shi aka Chasa ta tayi guda biyu na beef, banda kamshi babu abunda ke tashi a kitchen ɗin tana yin Shawarmanta kuwa tana biski ba me yawa tayi ba ɗan kaɗan ne sosai da kidney sauce, fancy plate ta ɗauka ta zuba biskin daga gefe in a stylish way kan ta zuba kidney sauce ɗin shima a gefe ta watsa parsley a kai kaɗan yadda ya bada wani garnish na burgewa. Shawarmanta guda biyu ta ɗauko suma ta saka su a plate ta ɗaura Duka a tray ta ɗauko ruwa masu rangwamen sanyi tare da daukawa kanta wani mango drinks ta nufi ɗakin Mammi, tana zuwa ta ajiye tray ɗin tace "Mammi guess what I made?" Mammi tana murmushi tace "Ina zan sani ina zaune a nan na dae ji kamshi na tashi kuma duk hasashe na na rasa gane menene.." Buɗe plate ɗin biski da kidney sauce tayi tana dariya cike da jin daaɗi tace "Tadaaa..!" Tana dariya sossai wadda ya saka Mammi murmushi tace "Masha Allah, Kice daughter na na shirin zama Chef eyee a ina kika koyi irin wannan delicious ɗin?" Shagwaɓe fuska tayi tace "ba irin su bane na bi Zee koyo a gidansu kuma da nisa shine ban dawo da wuri ba su ya Farhan suka bugeni ba..!" Mammi tace "masha Allah, am impressed gaskiya karki damu in shaa Allah na miki Alkawari da kaina zan saka ki a catering school ƴata ta zama Chef Faoza.." Murna Faozia ta fara harda tsalle, Mammi na ta dariya Faozia is such a wonderful child da zama da ita kaɗai ka iya saka ka farin ciki she's so lively in har ka san yadda zaka tafi da ita, Mammi ta matsarwa plate ɗin tace "bismillah Mammi" "thank you bitty" Spoon ta sa ta fara ci tana yabon hannun na Fauza a girki, itama Shawarmanta taci tas ta cinye ta sha mango juice ɗin kan ta tattare wurin ta fitar, da taimakonta Mammi taje toilet tayi duk wani abunda zata yi ta dawo da alwala, ita ta taimaka mata har ta kwanta... Tana shirin shiga wanka se taji sallaman Baba Prof hijab ta saka, Seda ya shigo ta gaishe shi ya amsa da kulawa kan ta fice ta bar su da Mammi, ɗakin yaya farida da babu abunda Mammi ta taɓa ciki ta shiga, akan gyara akai akai hakan yasa ta nufi toilet ɗinta tayi wanka, bayan ta fito ta duba wardrobe ɗinta ta kuwa samu kayan bacci sabo dal a Leda Dukda ya ɗan yi mata yawa haka ta saka. Seda ta ɓata lokaci mai yawa kan ta fito ta koma ɗakin Mammi ta samu Baba prof ya tafi, Har zata juya Mammi tace "Fauza" Dawowa tayi tana cewa "Na'am Mammi ko kina bukatar wani abu ne?" Mammi tace "A'a ki hau gado ki kwanta, kiyi Adu'a kin ji?" Kai ta gyaɗa tare da rage musu hasken ɗakin ta hau gadon na Mammi ta kwanta tare da jan bargo. Chan cikin dare Fauza ta tashi saboda fitsarin da ya matse ta se ta hangi Mammi zaune dafe da kai, da sauri ta mike tace "Mammi!" Mammi bata ɗago ba, sauƙa tayi ta nufe ta ta duƙa a gabanta tace "Mammi lafiya? Baki jin daaɗi ne?" Tayi maganan hawaye na cika mata idanu Mammi ta ɗago idanunta duk sun sauya tace "Na kasa bacci Fauxa kafana se harbawa yake" Hawaye ne ya zubowa Fauxa cikin tausayin Mammi, zama tayi gaban kafan tace "bari na miki Adu'a Mammi" Bismillah tayi sau Uku kan ta ɗaura da بِسْمِ الله! بسم لله!! بسم الله!!! "أَعُوذُ بِااللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شِّرِ مَا أَجِدُ وَأُهـَٰذِر" "Bismillah! Bismillah!! Bismillah!!! Auzibillahi bi qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadhir". Kafa bakwai ta shafa mata a kafan ta kara da qulhuwa uku, falaki uku, da nasi uku. Manzon Allah yace babu wani ciwon dake damunka da zaka dafa wurin ka karanta wannan Adu'a ba tare da Allah ya yaye maka ba, walau ciwon ciki, ciwon kai, ciwon kunne ko ma wani irin ciwo ne. Cikin ikon Allah bayan ta gama yi mata ta ci gaba da massaging kafan har Mammi ta Samu bacci ya ɗauke ta, wani irin ciwon kafa ne wannan Fauxa tayi maganan a zuciyarta tana kallon tarin magungunan na Mammi, daga na Asibiti har na gargajiya zuwa na musulunci, komawa gadon da Fauxa bata yi ba kenan a nan kasa ta kwana se da Asuba taji Mammi na tashinta. Mikewa zaune tayi tace "Mammi ya kafan?" Mammi tayi murmushi tace "sannu Fauziyya! Sossai na ji daaɗin Adu'ar da kika min kwanana hudu rabona da baccin dare se gashi yau nayi harda mafarki" Murmushi Fauxa tayi tace "to bari na sake miki" Adu'ar ta fara mata yayinda ma ta zuba mata idanu tana kallo, ta rasa me take hangowa a rayuwar Fauxa wadda kowa baya hanga kowa kawai ya tashi Fauxa bata ji, Fauxa kaza Fauza kaza ita Sam banda haske babu abunda take gani a rayuwarta, yarinya ce me tarin ɓoyayyen baiwa amma influence na mutanen dake zagaye da ita ya hana shi bayyana. Jin za'a shiga sallah yasa tace "Fauza tashi je kiyi alwala ki tafi masallaci bari nima na miƙe" Da taimakon Allah ta kai kanta bayi tayo alwala yayinda tuni Fauxa ta fice masallaci, anan tayi sallah ta sake kishingiɗa tana me sake samun wani baccin saboda sauƙin kafan. Fauxa ko ɗar bata ji ba ta wuce sashensu abunta, yau itace da wanke wanke da kuma gyaran ɗakin su, Seda ta fara shara da gyara ɗakin tana cewa "Wallahi in an ga dama a wargaza kan a tafi ba ruwan Fauxa" Falaq tace "amma kin san dole a shirin su Fakiha su wargaza ɗakin nan kam ko?" Cikin kunkuni tace "suna da hannu ai, se su gyara! Ni de na san nayi" Tana kai nan ta hau sharewa ta fitar da Sharan a memakon ta kwashe se ta watsa tsakar gida alhali Fatima ta riga ta wuce nan a shararta na tsakar gida, tana watsawa ta bi ta kan tsintsiyar Fatima da ta sake baki tana kallonta tayi wurin wanke wanke ta fara yi, dama kowa ya san wanke wankenta kwanuka kam se sun bugu iya buguwa in akwai na fashewa kuwa to se ya fashe. Ammi da suke aikin kari da Fa'iza bata ce mata komai ba, don in tace zata yi magana kuka ze iya fin karfinta Fauziyya ta riga ta fi karfin duka yanzu kuma se Adu'a. Da yamma bayan sun dawo makaranta Fatima na wankin uniform na su Fakiha yayinda fa'iza ke wanke wanke, ita kuwa uwar gayyar kitchen take tana taya Aunty Amarya sa magana tunda ba aikin take ba duk abunda Aunty Amarya ta saka ta se tayi mata shirme da gangan. "Ni sumayya! Yanzu Fauziyya daka attarugu ma se kin zuzzubar a ƙasa haka? Ai ko Faazila dake karama a gidan nan karankap zata daka min kayan miya in kwashe lafiya lau ke kam babu abunda kika iya goɗe goɗe dake se sa mutane magana? Wani irin jaraba ne wannan?khaih Allah ya shirya mana in na shiryuwa ne" Kunkuni wadda Aunty Amarya bata ji ta hau yi. "Yen yen yen yen... Se ki zo ki shirya ai tunda charbi nake ko jigida" kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faɗan da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai. Aunty Amarya tace "tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don baki dauke ni da daraja ba tunda ba ni na haife ki ba jeki karki sake sakamin hannu a aiki" Mikewa kuwa tayi ta fito ko a jikinta, ta zo wucewa ta gaban Fatima suka Haɗa ido a saman labbanta tace "munafuka" tana ball da bucket ɗin wankin har ruwan ya kwararare. "Fauziyya!" Baba Alhj ya kirata cikin wani irin kaushin murya. Se Fatima ta fara kuka mikewa tayi ta wuce ta gaban Fauziyya ta duƙa a gaban Baba Alhj tace cikin sanyin murya "Baba Don Allah ina so kayi min izini ina so in koma wurin mahaifina haka..." Cikin tausayinta yace "Babu inda zaki koma Fatima, nima mahaifinki ne in akwai wacce tafi cancanta da ta bar min gida Fauziyya ce!" A razane Fauziyya ta ɗago ta kalleshi, Ammi ma da ta fito se idanu ta zuba mishi yana kallon Fauziyya yace "Eh kin ji abunda na faɗa! Na gaji bazaki kasheni tun kwana na be kare ba, ke kaɗai ranki guda kin zama sheɗaniy...." "A'uzubillahi Sule!" Jadda da ta shigo bikon ƴar gidanta sbd ta ƙi shiga wurinta tun jiyan nan ta faɗa tana karasowa ta kama Fauxiya da ta zama speechless tana kallon mahaifinta. "Ƴarka na cikin ka kake kira sheɗaniya Sule? Wani irin baki ne wannan? Me tayi maka da zafi haka?" Kanshi a ƙasa yace "Mama na gaji da halayyar Fauziyya, dubi goshin uwarta Sumayya yadda tayi mata jiya, babu wadda ze faɗa magana Fauziyya bata bashi amsa ba, ta sakawa yarinyar nan karan zuƙa tana mata gadara da gidan uba! Ita ɗin ai ba daga Bishiya ta faɗo ba, gwara Fatima sau dubu don bata sa uban ta da uwarta zub da hawaye ba... Wallahi wallahi Mama Fauziyya ta gama sane min cikin yarana har raina na gaji da komai nata" Ammi kuka ta fashe dashi tace "ba kinji ba Fauziyya? Wallahi ki guji duniya, uban da ya haife ki ma yace ya gaji dake to wa ze iya zama dake? Da wannan halayyar naki Fauziyya gwara ki sa wuƙa ki mana yankan rago mu huta da zafin zuciya kullum a kanki" "Ruqayya! Sulaiman!! Ya isheni haka, tunda mutuncina da ganin idanuna be sa kun kasa amayo da kalaman bakinku ba, ni kuwa ba zan tsaya in cigaba da saurara ba, karku manta yaranmu kaman kiwo suke a garemu Allah ya kan jarabceka ta hanyoyi daban daban maybe ita ɗin itace jarabawar taku, idan kuka yi hakuri a matsayinku na iyaye kuka kai zuciyarku nesa kuka cigaba da mata adu'a har zuwa sadda Zaku Rabu lafiya kila ku samu rabauta ta sanadiyar ta, yanzu da duk kuke aika mata da kalamai marasa daaɗi ta karasa lalacewa kuma haka Zaku ɓata lahirarku saboda se Allah ya tambayeku, abunda ya saura ku ce shine kawai ta fita ta bar muku gida tunda har ka fara attempting to zan tafi da ita sashena ku zuba ruwa a ƙasa ku sha" Tana kai nan ta janyo hannun Fauza da take tsaye kaman icce suka fice. DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰 Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid* *Shafi Na Tara* *PAID BOOK* ƊANƊANO **WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️** Ƙurawa kanta idanu tayi a Door size mirror na ɗakin tana jin sukar kalaman iyayenta a kanta, lallai kam basu faɗi abunda ze gyara mata rayuwa ba se ma wadda ze ɓata saboda hango abubuwan da zata ke yi musamman wadda a da gudun ɓacin ran nasu yasa ta danne burinta take rayuwa yadda ta taso ta gani Dukda baya cikin tsarinta, kallon kanta take da kyau tare da lumshe idanu tana tuna maganar sakina. "Ke yadda kike da kyaun nan da sura wallahi kika fara ɗaukar wanka kika zama ƴar gayu ba karamin rububi maza zasu yi a kanki ba, kin san kuwa irin baiwar da kike dashi na fusgan hankalin mata ma ba maza kaɗai ba? Babe ki waye pls ki dena kunshe kanki cikin hijab" Ajiyar zuciya ta sauke tana tuna amsar rahama. "Ke wallahi abunda Sakinah ta faɗi gaskiya ne baki ganin yadda duk muke rayuwa cikin wayewa da aji da izza? Don Allah hakan baya burgeki? Amma ku kullum gidanku hijab hijab Ina ka fito karatu ina zaka karatu, babu babban waya, babu samari babu hangout da su party, wallahi kuna cikin duhu" Ba kalaman nasu bane ke tunzura ta sede illa irin tsarin rayuwar da take so ɗin kenan se ya haɗu da maganganun su yake tasiri a hankali a ranta sede yanzu kalaman iyayenta ya hauhawa su kaman tashin farashin man fetur, a yanzu take jin zata fara nunawa su baba prof ba irin rayuwar su take so ba, ko da zasu yanka ta su fige tane. Rahama da sakina ƴan ajinsu ne waenda suka shigo third term na SS1 ɗinsu asali a Abti suke sede rashin jinsu, da yawace yawace yasa iyayen Rahama suka cire ta suka dawo da ita Elkenemy ganin makarantar musulunci ne kila ta shiryu sede ba tare da sun sani ba sakina ma ta uzzuruwa iyayenta suka sake dawowa suka jone a ajin su Fauxa, tunda suka ganta suke admiring kyaunta da kalar idanunta suka fara nuna mata yadda zata ja hankali tare da tada hankalin maza a tiktok sede bata mai da hankali ba, iya kaci taji wakoki da wayoyinsu tayi ta kallon mata masu class a Instagram waenda har ga Allah suke burge ta. Tana matukar son gayu da class sede su gidansu ko ba hijab baka isa fita ba, a daren ta fara tsara yadda zata sauya rayuwarta zuwa ra'ayin kanta ba ra'ayin wasu ba, sallamar Faazila ya sa ta ɗago idanunta da suka sauya ta zuba mata, birkicewa yarinyar tayi don ta san sarai yanzu se Adda Fauxa ta mammake ta yadda take a harzuke ɗin nan. "Me??? Kin zo kin wani yi min kerere kina kallona?" Baya ta ja tace "Mammi ce tace in kira ki" Dauke idanunta tayi ba tare da ta amsa ba ta juya ta dauki hijab ɗinta ta saka tare da fitowa zuwa sashen Mammi, tana shirin shiga ɗakin Fatima na shirin fitowa da gayya ta bangaje ta har Seda tayi baya tana kallonta sede ko kallo bata ishi Fauxa ba ta wuce zuwa wurin Mammi tana daidaita fuskanta Gaisawa suka yi Mammi tace "Fauxa zo don Allah kiyi min tofi a kafan nan" A ladabce tace "to Mammi" A gabanta ta duƙa ta fara se Fatima ta shigo da bowl na fruits a hannunta ta ajiyewa Mammi ɗin tana cewa "Mammi Adu'a ce ake yi?" Mammi tace "eh wlh jiya da ta min baki ji yadda na ji daaɗin kafafun ba" A fakaice Fatima ta aika mata da wani kalar kallo tare da taɓe baki, ina Fauxa ta ma san tana yi, wai harara a duhu, bayan ta gama mata ta fice don bata jin magana in kuma ta zauna inuwa daya da Fatima karshe se Mammi ta raba faɗa. Washegari a class bayan an tashi break ta kalli rahama tace "am interested in ur way of life taya nima zan fara?" Rahama da sakina suka yi wani ihu tare da tafawa suka ce "welcome to the club babe" Sakinah tace "dama akwai wasu Zafafan dinkunan da zamu yi har ma mun yi placing order ɗin materials ɗin amma tunda zaki yi bari na sa dake" Fauxa tace "amma fa bani da kuɗi kun san gidanmu ba wani bada kudi ake banza banza ba" Rahama tace "don't mind dear! anything for you precious " Sakina tace "bare ma kwana biyu zaki fara rike wasu makudan kuɗin da se kin ji tsoro just chill babe" Aiko gwada ta suka yi suka turawa tailor ɗin su, nan suka fara nuna mata mahaukatan dinkunan tana kallo cike da yabawa.. Iyaye ya kamata mu san cewa duk fushin ka da yaro ba kowacce kalma ya kamata ka furtawa ɗa cikin fushi ba domin baka san irin influence da zaka yiwa yaro ba idan har Allah ya amsa. MAFARI Dukda rashin son karatun Fauxa ta kasance mace mai son karance karance, hakan yasa bata rabo da littafi ko na turanci ne, babu kalar abunda bata karantawa hakan yasa abubuwa dayawa tana da masaniyar already aikata shi a fili ne kawai bata yi ba. Wani irin kalar Juyawa rayuwar Fauxa yayi cikin lokaci

Chapter 5 of 6