raɗamata amma kuma ganin Inna Mairamu ta cire kunyarnan ta fulani ga yaran fari ta nemi alfarma akan ya raɗamata sunan mahaifiyarta ya sanya shi haƙuri da nasa ƙudirin don ya faranta mata ganin ta sha wuya sosai don sai da ta yi sati tana naƙuda. Inna Mairamu ta ji daɗin wannan karramawar da ya yi gareta. Ya nemi ko a ɓoye sunan ita kuwa ta ce aa, sai dai ko a kira ta da Sadiya tunda an fi sanin mahaifiyarta da suna Haleema.
Haihuwar Halima da watanni biyu ne Hajara ta dawo gidan. Ko ganin jaririyar ba ta taɓa yi ba ita da Safiyya. Koda ta dawo ba ta bi ta kan Inna ba ballantana ta yi mata barka. Inna tuni ta wartsake mai tayata wanka ta tafi, ita ke yin komai na gidanta da kula da Sadiya.
Ranar da Hajara ta fara sanya Sadiya a idanunta, a ranar ta soma jin tsanarta mai yawa a zuciyarta. Tabbas Allah ya yi halitta a fuskar yarinyar, duk kuma kushen mai kushe, ya yi kaɗan ya kalli Sadiya ya kushe ta. Dalilin kyau da kuma haushin Malam bai saka sunan Mahaifiyarta ba yanda za ta samu damar ƙara ƙuntatawa Inna Mairamu ba, su ne suka haɗu suka haifar da tsanar Sadiya a wajen Hajara.
Wahala kuwa da Sadiya ta sha a wurin Hajara mai yawa ne, don hatfa da ruwan zafi Sadiya ta taɓa ƙonewa a cinya da shi sakamakon barinta da Inna ta yi a tsakar gida ta shiga wanka. Sai fitowa ta yi ta ga yarinya na ihun kuka da azaba ga ruwa ya zuba a cinyarta. Ba ta ga kowa ba, ta kuma sani Sadiya ba ta fara rarrafe ko jan ciki ba sai zama balle ta kawo ko ita ta zubawa kanta. Wani lokacin idan ƙiriniya irin na yara ya tashi, ta faɗa ɗakin Hajara, Inna Mairamu sai dai ta ga yarinya ta fito tana kuka. Wani lokacin ma har da fasasshen baki za ta fito duk sadda Hajara ta siyo wani abin kwalam din, sai ta fake da cewa wai ta fiye kwaɗayi ne shiyasa ta buge bakin.
Azaba dai iri-iri babu wanda Sadiya ba ta gani ba a wajen Hajara har ta shekara uku, lokacin Inna ta kara samun ciki har ya fito sosai. Wannan kuwa har waƙar mai ciki Hajara ke rerawa a tsakar gida tana habaice-habaice har da fadin wai duk dai maita irin na wata, ba za ta taɓa haihuwar bakwai cif kamar Asma'u ba. Kuma ba za ta haifi abin da zai ƙwace soyayyar da Ubansu ke musu ba.
Inna dai ba ta ko kallonta. A lokacin ne ta dauki Sadiya ta kai ta can gidansu hannun Dada. Tana shiga watan haihuwarta ta sauka lafiya ta samu ɗiya mace wacce daga kallo za ka san jinin Malam Sa'ad ce saboda kamanninsa da ta ɗauka gaba ɗaya. Baƙa ce amma baƙinta bai kai na su Hajara ba sai ita ta kasance mai ɗan haske sakamakon nonon farar mace da take sha.
Hajara tun sadda Malam ya raɗawa jaririyar sunan mahaifiyarta Asma'u ta ce a dinga kiranta da Husna. Abin da yake bai wa Inna Mairamu mamaki bai wuce ganin yanda Hajara kan tsallako ta shigo har ƙuryarta ba ta sa hannu ta dauki Husna ta fita da ita tana bata kulawa. Ta yarda lallai dagaske ba karamin so da kaunar Mahaifiyarta take yi ba. Ba ma ita kaɗai ba, hatta Safiyya sai da ta zo gidan ganin Husna har da kayan jarirai ta kawomata. Mustafa da Hashimu da Baba Habu su kansu wannan karon sun zo sun ga Husna.
Inna Mairamu da ɗiyarta, amma Hajara babu irin tuggun da ba ta shirya mata ba sanadiyyar Husna.
©Rufaida Umar
https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a
*Akwai pages na gaba har guda biyu a manhajar arewabooks. Kuna iya bibiya a can*😃🥰
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels