Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
taya ni rikon amanarsu tun a yau da kika soma sanya su a idanunki. Kar ki bani kunya mana!" Daga haka ya sa kai ya fice a gidan. Inna Mairamu ta kasa motsa koda yatsa balle ta bi bayansa. Wasu ruwan hawaye masu ɗumi suka zubo saman fuskarta, ta shiga ambaton sunayen Ubangiji a cikin ranta. Lallai ta su da wadannan yanmatan ba za ta zo ɗaya ba. Tun yanzu? Tun ba a wuni tare ba sun soma ƙulla mata zarurrukan sharri? Ta sauke ajiyar zuciya, ta daurewa zuciyarta har aka yi sallar isha'i sannan ta fito zuwa falon Malam din. Yana zaune su Hajara na gefensa suna hira da dariya. Sallamarta ya sanya suka haɗe rai gami da amsawa ciki-ciki saboda ganin idanun Malam. Shi kuwa wani irin mutum ne marar riƙo, yanzun zai yi faɗa amma zuwa wani lokacin sai ya manta bar shi dai da daukar magana. Ransa ya dan yi sanyi musamman ganinta cikin ado kamar koyaushe. Murmushi ya yi itama ta mayar masa da martani. Ta nemi wuri ta zauna. Safiya ce ta soma mikewa ta bar falon ranta a jagule ganin haka itama Hajara ta bi bayanta. Malam ya bisu da kallo hakanan Inna Mairamu wacce ta ke musu kallon mamaki na yanda har babu kunya ba tsoron Allah suka haɗa ta da mijinta akan laifin da ba ta aikata ba. "Don na maki magana wato shi ne ko ki zo ki ba ni abinci ko?" Ya furta, kai ka ce ba shi ya gama sababin an taɓa yaransa ɗazu ba. "Ba haka bane, sallah na tsaya nayi. Akan abin da ya faru kuma ina mai ba ka hakuri. Nidai har ga Allah na sani ba zan iya cutar wata halitta ba balle kuma jininka, yaranka ai nawa ne. Ina mai ba ka hakuri bisa abin da suka ce na aikata, sai dai don Allah idan ranka ya ɓaci ka bar saurin yanke hukunci akan magana har sai ka ji daga bakin mutum. Mai yiwuwa kuskuren fahimta ne." Ya numfasa. "Shikenan, dama na sani za ki riƙemin amanar ƴaƴa, kawai dai yanayin da na gansu ciki ne ban ji dadi ba. Kin san ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da mahaifiyarsu ba, wannan ne dalilin da ya sanya sai a hankali za su saba da ke. Kema kuma ki dinga kokarin jansu a jiki, in sha Allahu za ku ji dadin zama da juna domin yaran ba su da matsala." "Uhum." Shi ne iyakar abin da ta ce haɗi da ɗan murmushi ba don ta gamsu ba, tun a yanzu ta hango matsalarsu, ta kuma san ba ƙaramin abu za ta fuskanta a zamanta da su ba. Ya shiga jan ta da hira karshe ta watsar da zancensu itama ta sakarwa mijinta tamkar wani abu bai faru ba. *** Kamar dai yanda Innar ta yi zato hakan ne ya kasance, fitsara da rashin kunya iri-iri haka ta dinga cin karo da su a wurin Safiyya da Hajara. Ko tsinke ba sa kawar wa a gidan sai dai idan ta gyara su ɓata. Sai sun tabbatar ta yi shara sannan za su share nasu ɗakin madadin a kai kwando a zubar sai dai a watso tsakar gidan, ranta kan ɓaci sai dai kawai ta kai zuciya nesa. Abinci kuwa sai a faki idonta su ƙara uban gishiri a cikin nasu kason, idan Malam ya dawo su hau kukan munafurci su ce wai kashe su Inna ke son yi. Ganin haƙansu na cimma ruwa, Malam din na yarda da su ɗari bisa ɗari idan sun faɗi laifin Inna, ya sa duniyar ta ke gara musu sosai yadda suke so. A haka watarana Safiyya ta kimtsawa Hajara sharrin da ya dace su yi ga Inna wanda take da yaƙinin idan haƙansu ya cimma ruwa to zai wahala auren Inna da Malam bai zo ƙarshe ba. "Amma kina ganin zai sake ta? Nifa sai naga kamar yana sonta." Cewar Hajara bayan gama sauraron ƙullin da Safiyya ta ke son su aiwatar akan Inna. Safiyya ta ja tsaki. "Wane so? Ke kike ganin hakan. Malama ba wani sonta da yake yi kawai dai yana maneji ne. So ai ya ƙare a kan Uwarmu. Duk wacce za ta biyo baya kuwa, sai dai wani sunan amma ba so ba. Ke dai kawai ki yi abin da nace, ni na tabbata yau kwanan Mairamu ya ƙare a gidannan." Suka yi dariya har da shewa. *©Rufaida Umar* https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a *** *Kazar Kwanci...* *Ƙarshen free page* 07 A ranar wata Asabar abin ya faru, hadari ya haɗu sosai a garin, cikin gaggawa Inna Mairamu ta kammala girkinta a gawayi ta kashe ta gyara wajen ta tattara gidan tas, abin rufewa ta rufe, na killacewa ma haka. Sai da ta kai komai ɓangaren Malam kamar yanda ta saba tunda hatta su Hajara sun koma ci tare da shi idan ya dawo hakan yasa ba ta ware musu. Malam din ma ya ce ai ya saba al'adarsu ce tun Asma'u na raye sukan haɗu da yaransa su ci abinci wannan ne dalilin da ba ta karambanin zuba musu daban. Na almajirinta Lurwanu ma sai da ta ajiye mishi a kicin duk da ba ta zaton zai samu ɓullowa sakamakon yayyafin da aka fara kaɗan-kaɗan. Ban da kiɗa babu abin da ke tashi a ɗakin su Hajara, ita ba ta nan ma ta je makaranta sai Safiyya a gidan amma ko leƙe da sunan taya Innar aiki. Ita dai ɗakinta ta shige bayan ta ɗaura alwala ta ja ƙofa ta rufe da zummar ɗan kimtsawa kafin Malam ya shigo gidan. Tunaninta gaba ɗaya yana kan Hajara, ko ya ya za ta yi da ruwa? Sosai take jin damuwa akan haka tamkar ƴar cikinta. Ta kasa jurewa ta fito ba ta damu da ruwan da ya soma ɗan ƙarfi ba ta shiga ɗakinsu. Safiyya tana ta danne-dannenta a wayarta tana faman hira a 2go ba ta ma ji sallamar Innar ba sakamakon kiɗan da ya cika dakin. Inna ta ƙarasa ta ɗan bubbuga ƙafarta ta kuwa yi zumbur ta miƙe tana huci, ganinta ya sanya ta jan tsaki gami da kashe rediyon. "Mene ne haka za ki tsorata ni?" Inda sabo ya ci ace ta saba don haka ta shanye tambayar ta shiga magana. "Ki kira Hajara ki ji tana ina? Ni ba kati a wayana. Ga ruwa nan ya fara ƙarfi kar ya yi mata illa a waje." Safiyya ta harare ta. "Ji? Sai ka ce damuwar ki ka yi dagaske. Uhum, ta ciki dai na ciki na sani. Toh Hajara ta cemin gidan Anti Hafsatu za ta kwana kuma ta sanar da Malam ma." Inna ta ɗan yi shiru, sai kuma ta amsa da shikenan daga haka ta fice ta bar ɗakin. Safiya ta bi ta da wani murmushi na zallar mugunta. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abin ya zo musu a daidai, wato sun shiryawa Inna tuggu, sai kuma ga ruwa Allah ya kawo. Shakka babu abin zai ba da citta sosai. Ta dannawa Hajara kira, bai yi ko ƙara uku ba ta ɗaga. Ƙasa-ƙasa ta soma magana. "Ke ya ake ciki? Kin ga Allah ya na sonmu, ga ruwa ya sauka yanda komai zai fi tafiya daidai ko?" Tana jin sautin dariyar Hajara ita ɗin ma taya ta tayi. "Ke dai bari ƴar uwa. Ni kaina ina ganin yanda hadari ya haɗo na ji wani sanyi a raina. Faɗuwa ta zo daidai da zama." Suka yi dariya. Safiyya ta ƙara da cewa. "To ina Yusuf din? Ku na tare ko? Kin ƙara masa bayanin komai?" "Yes, ba mu da matsala da shi. Ya san abin da zai yi. Ina fatan wayar tana hannunki?" Safiyya ta gyaɗa kai. "Ai dole. Shashashar ba ta ko yi cigiya ba kin san fa babu dangin da za su neme ta." Daga haka suka ƙara darawa sannan suka yi sallama. Safiyya ta yi wata ƙwafa kafin a fili ta ce. "Yau Mairamu za ki kwanan gidanku." Ana cikin sallar isha'i Malam ya shigo gidan da sauri-sauri ya faɗa ɗakinsa. Kayansa har sun ɗan jiƙa. Inna ta ji shigowarsa amma kasancewar ta tayar da sallah ya sanya sai da ta idar kafin ta nufi falonsa da sallama ɗauke a bakinta, ta tabbata ruwan ne ya tsaida shi har isha'i. Lokacin ruwan ma ya tsagaita sai iska mai karfi da yayyafi, sai ko rugugi da ke nuni da har lokacin akwai sauran ruwa wanda idan Allah ya nufa zai iya zuba a kowane lokaci. Ganinsa a tsaye da waya a kunne ga Safiyya durƙushe a gabansa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya ya sanya kirjin Inna bugawa da ƙarfi, a fili ta kira sunan Allah kafin ta dubi Safiya karo na biyu san nan ta maida duba ga Malam. "Lafiya? Meyafaru?" Ta furta hannunta a saman ƙirji don sosai ta tsorata. Tunaninta ya fi karkata kan ko wata mutuwar ce aka yi. Malam bai ko kalleta ba fuskarnan a matuƙar ɗaure ya cigaba da magana a wayar. Da ta nutsu sai ta gane kwatance yake yi wa wani na gidan, karshe ta ga ya kasa nutsuwa yana fadin bari ya fito ya tarbo shi, daga haka ya zura takalminsa ya bi ta ƙofar waje ya fice. Inna wacce daga kallon da Malam ya bi ta da shi ta sha jinin jikinta a sanyaye ta ƙara jefawa Safiyya tambayar da ba ta da tabbacin samun amsa gareta sai don ƙarfin hali. "Safiyya, wani abu ya faru ne a gidan?" Ga mamakin Inna sai gani ta yi Safiyya ta miƙe tsaye tana wani murmushi haɗi da dariya kafin ta amsa a sheƙeƙe. "Ba za ki gane abin da ke faruwa ba sai yau kin yi kwanan gidan Jibo Ladan. Dama ai mun faɗamaki akwai ranar ƙin dillanci." Tana kai wa nan ta saka kai ta bi hanyar da Malam ya bi ta bar Inna da sakin baki gami da bin bayanta da kallo. 'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!' Inna ta shiga maimaitawa a zuciyarta a sadda ta ga Malam ya dawo falon ɗauke da Hajara a hannunsa gami da kwantar da ita saman doguwar kujera. Gaba ɗaya ya ruɗe, a rikice ya ke faɗin. "Kar ki yi min haka Ƴar Malam, ki buɗe idanunki ko hankalina zai kwanta. Ya Allahu!" "Kar ka damu Baba, in sha Allahu fa yanzu komai ya daidaita, kawai allurar ce ba ta gama sakinta ba. Amma za ta farka a kowane lokaci a yanzu." Saurayin da ba ta san ko waye ba ne ya faɗi hakan, dalilin kenan da Inna ta maida hankali ga dubansa, sannan ta dubi Hajara wacce fararen kayanta duka sun ɓaci da ƙasa. Kanta babu ko ɗankwali sai farin bandeji da aka zagaye kan ga alamun jini da ya tsassafo ta cikin bandejin daga gaban goshin, babu inda ke motsi a jikinta idan ka cire hawa da saukar da kirjinta ke yi shaidar tana numfashi. Can kuma sai ta soma ɗan motsa kanta kamar irin a firgice, tarr ta buɗe idanunta ta miƙe zaune a gigice take faɗin. "Wayyo Allahna! Ga shi nan! Ga motar za ta taka min kai! Wayyo!" Malam sosai ya rirriƙe Hajara, Safiyya ma ta shiga taya shi ta hanyar riƙe ƙafafunta tana kiran sunanta da karfi. Sai da Malam ya haɗa da addu'a sai kuma ta nutsu. Ta dubi Malam kawai ta fashe da kuka tana ruƙunƙume hannunsa. "Babana kai ne? Dama akwai rabon mu kara ganin juna? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Malam wanda idanunsa suka kaɗa sosai, yana jin kirjinsa ya mishi wani irin nauyi daƙyar ya haɗiyi miyau ya soma magana. "Ni ne ƴar Malam, Alhamdulillah. Babu abin da zai raba ki da Malam kin ji ko? In sha Allahu ko mutuwa za ki yi, ba ta wannan hanyar na tashin hankali ba." Hajara ta jinjina kai hawaye ya jiƙa fuskarta. "Mamana Allah ya gafarta maki. Yau na ga tashin hankali Malam, ni dai na san na fito daga makaranta ana ta iska tun wajen biyar na yamma, na dinga kiran wayar Inna yana ta ƙara ba ta ɗagawa. Anti Safiyya kuma nata a kashe dama tun kafin na fita ba ta da chaji. To ni dai ban ji ƙarar babur ba sai ji nayi wani ƙarfe kamar ya buge ni na faɗi na buge kaina. Daga nan ban san fa meke faruwa ba." Saurayin anan ya yi gyaran murya ya ɗora zancensa. "Wanda ya yi mata wannan lahanin guduwa ya yi bai tsaya ba, ni na kai ta chemist mafi kusa tare da wasu mutum biyu, komai ya zo da sauki ma babu karaya babu komai. Bayan an tabbatar da lafiyarta ƙalau ne shi ne na yi amfani da wayarta na fara kiran lambar da na gani a karshe wanda ta rubuta Inna Mairamu yana ta kara amma ba ta kusa, shi ne na kira lambar da ta saka Sis Safiyya." Malam ransa idan ya yi dubu to ya ƙara zafafa dangane da lamarin Inna, ya kara yiwa saurayin da ya ce sunansa Yusuf godiya ganin ya na bankwana zai tafi gida saboda dare, har waje ya taka masa inda yana fita Hajara da Safiyya suka tafa gami da yiwa Inna gwalo. Inna dai ta yi mutuwar tsaye tana kallon irin wannan zargen da aka ƙulla mata mai wuyar kwancewa. To ta ina ma za ta fara fidda kanta a wurin Malam? Wayarta ta faɗomata a rai, sai a sannan ta tuna ita tun da ta ajiye wayar saman kujera ba ta kara bi ta kanta ba don lamarin waya sam bai dame ta ba matukar ba labaran safe za ta ji ba. Tun sadda Zakari ya ba ta kyautarsa sai dai ko shi ko Hafsatu su kira ta sai kuwa jifa-jifa idan Kawunta Jibo ya kira ko kuwa yaransa a gaisa. Ba ta kai ga gama tunanin ba ta ji muryar Malam a tsakar kanta. "Mairamu!" Ta ɗago tana dubansa ba tare da ta iya cewa uffan ba. "Kin ba ni mamaki kodayake bai ma kamata na yi mamakin komai ba! Tunda Hajara ba ɗiyarki ba ce ba! Ba ki san ciwon haihuwa ba wannan na tabbata shi ne babban dalilinki na yin watsi da lamarin budurwar da ta wuce ƙa'idarta na dawowa gida ba ki ko tuntuɓa ki ji lafiyarta ba! Ni na san da ace ke ki ka haifi Hajara, ba za ki kasa nemanta a waya ba, ba kuma za ki ƙi amsa wayarta da gangan ba! Ok, Mairamu kin nuna min kin gaji da zama da yarana ko? To ai wanda ba ya son ɗanka ba ya sonka kai ma! Don haka yanda ki ka kusa ajalin ɗiyata, na rantse a yau a yanzu ba za ki ƙara ko mintuna ashirin a gidana ba. Ki fice ki bar min gida a yanzu tun kafin na ɗauki mummunan matakin da ya zarce wannan!" Ya ƙarashe a tsawance, Inna Mairamu da tun fara maganarsa ta ke kallonsa ta maida duba ga Hajara da Safiyya waɗanda duniyar ta yi musu mugun daɗi har wani murmushi suke yi a sace. Ta juya don ta fice a ɗakin sanin da ta yi babu wani bayani da zai wanke ta a zuciyar Malam a wannan dare. Tana hawaye ta ɗauki abin da duk ta san za ta buƙata, tana shirin zura hijabinta ta ji an bugo mata abu mai kama da ƙarfe ko dutse a goshi, Safiyya ce. "Ga wayarki. Ke da gidan nan kuma har abada muna mai tabbatar maki. Sakin da ba a yi a gabanmu ba na tabbatar zai biyo ki har gidan tsohonki." Tana kai wa nan ta fice tana ƴar dariya gudun kar Malam ya ji. Inna ta kai duba ga wayar da haskenta ya sa ta fahimci me Safiyya ta wurgo mata. Hannu ta saka ta ɗauka gami da duba kiraye-kirayen da suka shigo, eh tabbas an kikkira wayar sai dai ta sani koma mene ne shirinsu ne. Murmushi mai kama da yaƙe ta yi sannan ta share hawayen da ya zubo mata. Ɗakin ta rufo ta koma ta rufe na falonta sannan ta fice daga gidan ko hanyar wajen Malam ba ta kalla ba. *** Kawunta Jibo da matarsa Dada sun shiga tashin hankalin ganinta a daren, ga wani zazzaɓi da ya rufe ta har haƙoranta na haɗewa wuri guda. Ransu ya yi mugun ɓaci don dama suna da labarin irin haƙurin da Inna Mairamu ke yi a gidan. Kawu Jibo ya rantse ba zai nemi Malam ba har sai sadda ya kawo kansa gareshi duk da cewa Inna Mairamu ba ta basu labarin komai ba kawai dai ta ce Malam yace ta taho. Shi babban ɓacin ransa bai wuce na yanda babu ko tausayi ba ya koro masa ɗiyarsa a dare ga kuma ruwa da ake yi wanda har ya soma ƙarfi. Daga yanayinta kaɗai sun fahimci ma a ƙafa ta tako. Nan da nan Dada ta ba Inna kaya ta sauya, ta sha magani amma a wannan dare bacci bai iya ya ɗauke ta ba saboda damuwar abin da Malam ya yi. Sai da Inna ta shafe watanni biyu a gida babu ko ƙeyar Malam, Hafsatu da Zakari wanda ya zo ganin gida har sau biyu, sun yi zarya a gidan Kawu Jibo har sun gaji kan ya yi haƙuri ya kira Mahaifinsu a sulhunta Inna ta koma ɗakinta musamman ma da suka ji daga bakin ɗiyar Dada ta biyu mai suna Hajjo cewa Innar na dauke da juna biyu. Ƙarshe Kawu Jibo cewa ya yi matuƙar ba za su bar batun komen Inna ba to kar su ƙara tako ƙafafunsu gidan. Haka suka ja bakinsu suka yi shiru. A bakin Hafsatun ne Inna ke jin auren Safiyya ya taho ana ta shirin biki don har an kawo lefe. Ta taya murna har ranta gami da sanyawa lamarin albarka. Har aka yi bikin Safiyya, Inna ba ta gidan Malam. Zuwa lokacin gaba daya Malam din ya yi sanyi, kewa da kuma damuwa akan rashin Innar ya ci ya cinye shi. Amininsa Alhaji Abubakar babu yanda bai yi da shi akan ya je su sulhunta ba ya yafemata amma ya ƙi. Hakanan manya a danginsu. Ya sha faɗa sosai sai dai kuma yana jin dagaske ya kusa rasa ɗiyarsa sanadiyyar Inna Mairamu, to akan me zai je ya maido ta gidansa? Koda bikin Safiyya ma, a can gidansu na gado aka yi komai har tariya. Sai lokacin bikin ne yake jin labarin cikin dake jikin Inna daga bakin Hafsatu wacce ta cire kunya da ma tsoro ta sanar da shi duk a kokarinta na lallaɓa mahaifin nata kan ya yi haƙuri ya maido Inna ɗakinta. Wannan ne ya sanyaya jikinsa sosai musamman da ya tuna gorin haihuwar da ya yi mata kafin ta bar gidan, da ya tsaya lissafi sai ya ga kenan cikin zai yi watanni huɗu a lokacin. Wannan ya sa da taimakon Alhaji Abubakar suka ɗunguma zuwa ga Kawu Jibo don dama shi Alhaji Abubakar ya je yi wa abokinsa biko har sau biyu ba tare da ya aika shi ba amma Kawu Jibo yace ya fidda hannunsa don wannan ba huruminsa ba ne ya bar su da shi kawai. Ranar farko da ya gansu bai ko ba su damar magana ba face takardar Inna Mairamu da ya ce lallai Malam ya rubuta ya ba shi. Malam ya ga duk inda yake hasko rashin saukin lamarin abin ya shallake tunaninsa. Ga shi a ɗan ganin da ya yiwa Inna Mairamu ta gifta a tsakar gida ya ji nan duniya babu abin da yake so sai ya ganta a kusa da shi. Ta ƙara kyau da haske abinta, kana ganin yanayinta ka san tana ɗauke da juna biyu. Sam bai sanya ta muni ba. A ɓangaren Inna kuwa, ta riga da ta cirewa ranta damuwar Malam da lissafin yaushe zai zo bikonta, hankalinta kacokam ya koma ga rainon cikinta. Ko babu komai ita ma za ta ga gudan jininta a doron ƙasa da yardar Allahu. Ita a lokacin duk abin da Allah ya hukunta a aurenta da Malam tana ji a ranta lallai za ta karɓa da hannu bibbiyu. Ba za ta ce tana ƙin Malam ba, amma tana jin cewa duk auren da babu yarda da aminci a ciki, to fa za'a yi ta samun matsaloli barkatai fiye da misali. To dai idan zama bai ƙare ba, kome ya zama dole koda kuwa zuƙata ba su kai ga gama hucewa ba. Cikin hukuncin Allah Kawu Jibo ya sauko ya haƙura Inna ta koma ɗakinta da zama. Sadda ta je babu kowa a gidan don Hajara ma tun bikin Safiyya take can gidansu Malam ba ta dawo ba. Amma tana jin labarin Inna Mairamu ta dawo kuma wai tana ɗauke da juna biyu, ta tattaro ta dawo gidan a lokacin Innar tana da sati uku a gidan. Ganin tsinin ciki a jikin Inna Mairamu ya sanya wani abu mai ɗaci ya tsaya a maƙogwaron Hajara. Dama kafin ta zo gidan ta ci kuka sosai saboda tsananin baƙin cikin wai Malam zai samu wasu yaran kuma ba daga Mahaifiyarta ba. Inna kamar babu abin da ya faru haka ta tarbe t da murmushi saman fuska gami da yi mata sannu da zuwa. Hajara ta ja dogon tsaki a fili ta ce. "Aikin banza, Allah ta wadaran wacce ba ta da zuciya." Tana faɗin haka ta shige ɗakin da yake mallakinta ita kaɗai a yanzu ta banko ƙofa garam! Inna ta girgiza kai, dama ta san ai mai hali ba zai fasa ba. Sam ba ta ji zafi ba ta cigaba da cin kwaɗon zogalen da makwafciyarta Habiba ta aikomata. Kusan za ta ce duk a makwaftansu Habiba ce kaɗai sai kuwa Mama Iyabo wacce ba bahaushiya bace, suka taka har gidansu domin jajanta mata abin da ya faru. Saura kuwa kasancewar tsofaffin makwaftan Marigayiya Asma'u ne, sai suke shakkar shiga sabgarta saboda ganin yaran ba sa jituwa da ita. A wajen ma mutane da dama a layin gani suke yi dagaske Inna Mairamu mugunta take yiwa yaran don ba ita ta haife su ba. Suna kuma amfani da hirarrakin da suke ji daga wajen Safiyya da Hajara ne. Don a cewarsu har rowar abinci take musu, babban burinta ma ta raba su da mahaifinsu baki daya. Wannan ya janyowa Inna Mairamu baƙin jini a wajen mutane da dama idan ka cire Habiba da ba ta wani jima da tarewa a unguwar ba sai ko Mama Iyabo wacce ta san Marigayiya Asma'u amma hakan bai hana ta shiga sabgar Inna Mairamu ba, hakan kuwa ya ja mata zagi da baƙin jini a wurin su Hajara. Idan ma ta zo gidan kallo ba ta ishe su ballantana a kai ga gaisuwa. Ɗinkin da suke kai wa shagonta ta yiwa musu kasancewarta tela, sai gaba ɗaya suka gwammace su haƙura su nemi wani wurin. Zaman Hajara da Inna Mairamu sam ba ya yiwa kowannensu daɗi. Koda dai nace ma Innar tunda ita Hajara sai dai ta haɗa mata wani sharrin ta bar ta da fushin Malam. A haka a daddafe Inna Mairamu ta shiga watan haihuwarta, komai na buƙata kuwa sai da Malam ya siyo. Hajara kasa ma zama ta yi a gidan tsabar baƙin ciki ta tattara ta koma gidan Hafsatu ta cigaba da zuwa makarantarta ta can bayan ta fake da cewa Malam karatun jarrabawa take son yi a nutse ba ta son duk wata hayaniya. Bai matsa mata ba kuwa ya biye mata. Inna da aka yi zancen a gabanta ba ta ce musu uffan ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, Inna Mairamu ta haihu ta samu ɗiyarta mace mai matuƙar kama da ita kamar an tsaga kara an karya. Soyayyar yarinyar ta cika ko'ina a zuciyarta. Sanadiyyar wannan haihuwa da dama a makwaftan sun shigo barka, wasu don kawai su yi gulma ne su ganewa idanunsu irin kyawun da ake faɗi na yarinyar don a cewar masu kai musu tsegumin, kaf gidan Malam ba'a taɓa yi masa haihuwar fara mai kyau irin Halimatus-Sadiya ba. A ɓangaren su Baba Habu yaran Malam kuwa, babu wanda ya tako ya zo. Kunyar ma shigowa unguwar suke yi balle a tarbe su da yi musu barkar haihuwar matar ubansu. Shi kuwa Malam ko a jikinsa, fuskarsa a washe duk sadda ya ɗauki jaririyar yakan ji tamkar kada ya ajiye ta. Yana jin kaunarta a zuciyarsa. Ya so ace Asma'u ya

Chapter 3 of 4