Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
hankali kwance yace “Inasonku kaida mahaifiyarka ɗana...." “A hakan?" Yaji an faɗa ya juyo da sauri yana sauke injin idanunsa kan Abdallah da Mommy dake shigowa Isa tayi gaban gadon ta ɗage rigar Rafi'ah ta fara dubata sosai tare da sauke idanunta kan Rafi'ah sosai taja numfashi tare da murmushi tace “Zaɓin da kikayiwa kanki kenan da nake nuna miki aibin hakan gani kike tsanarki nayi, ki rayu cikin aminci keda iyalinki Ɗiyata Allah yaci gaba da baki kariya" Juyawa tayi ta fice ba tare da ta ko kalli Abdulƙadir ba domin da gaske takejin haushinsa ita ta kasa yarda baya gari ne domin kalmomin Rafi'ah kafin ta rasa hayyaci sun nuna yasan halin da take ciki ya kasa bata gudummawa, bayan fitar Mommy ne Abdallah ya dafashi yace “Shiyasa nake yawan tuna maka zuciyar ɗa da mahaifi sarrafuwar ubangiji ce jini ne ya jiyar da baiwar Allan nan halin da ƴarta take ciki harta bibiyi abarta da babu ita a rayuwarta da tuni ba wannan zancen akeyi ba tabbas uwa uwa ce amma fah wata uwar tafi wata duk da saɓanin ra'ayi bai hana Mommy jin ƴarta a jininta ba so kayi taking care" “Abdallah!" Ya faɗa da ƙaraji idanunsa na canza launi yaci gaba da cewa “Akwai abinda ya faru ne da gazawata ta bayyana hakan yau ne ko yanzu Rafi'ah takemin ƙaryar ciwo kawai don batada ra'ayin sauke haƙƙina dake kanta Abdallah na fara gajiya da tuhumar nan da kukemin kaida Ya Hajja akan Rafi'ah wai ku kuka ɗaukomin ita ne ko fina sonta kukayi da kuke ɗora zargi a kaina Please ku bari banason zanyi rashin mutunci akan hakan wlh" yana gama faɗin haka ya juya yayi ficewarsa yaron ya kaima Ya Hajja ya tambayeta meye ake buƙata ta sanar dashi ya fita ya nufi gida ya fara haɗo masu kayan sai yanzu asuba tayi babu shaguna a buɗe shiyasa ya ɗebi iya abinda ke a gida ya juya ya fita ko a motar tunani ne barkatai a cikin kwakwalwarsa lumshe idanunsa yayi yana ajiyar zuciya a baya yayi neman mata amma tunda yayi aure sai yakejin bazai kuma ba zai daina to meye kuma yanzun yake neman mai dashi ruwa? Rashin kulawar matarsa ko meye? Gari ya fara wayewa lokacin daya koma asibitin daidai lokacin ne kuma Rafi'ah ta samu farkawa da kalmar shahada ta tashi ta zubawa ɗakin idanu dadai sa'ar da likitan ya turo ƙofar ya shigo idanunta a kansa har ya ƙaraso yayi mata sannu tare da fara duba jinin dake maƙale a jikinta ya cireshi ya ɗauki wata ledar ya saka mata ya juya gareta yace. “Da wani abu da kike buƙata ne?" Lumshe idanunta tayi tace “Ina Mijina" kallon nurse yayi yace “Zaifi ki tambayeni abinda kika haifa" bata kuma cewa komai ba ta kawar dakai ya fice daga ɗakin babu jimawa kuma saiga Abdulƙadir ya shigo yana ɗauke da babyn daya karɓa a gurin Ya Hajja domin itama ta samu ta watsa ruwa. Tunda ya shigo suke kallon kallo har ya ida ƙarasowa ya zauna a kujerar dake gefenta cikin Muryar lalura ta buɗe baki tace “Abnoor nasan ni me laifi ce a wajenka saidai banyi tunanin girman laifin dana aikata a gaɓar lalura yakai kayimin wannan mummunan hukuncin ba don Allah kayi hƙr...." Shigowar Ya Hajja ce tasashi saurin murmushi yace “Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa ba'a tashi daga taron ba na taho amma dai yanzu kinajin karfin jikinki ko?"jinjina masa kai tayi ajiyar zuciya Ya Hajja taji daɗi a ranta daya tabbata ba halin rashin tausayin nasa ya nuna mata ba ita dai tanason yarinyar kuma tana jiye mata tsoron halin Abdulƙadir da turjiya da kafiya akan ra'ayi" A takaice Saida suka kwana uku a asibitin sannan aka sallamesu suka tafi gida Gana Hajja ce ta taho Ya Hajja ta koma ita ta rinƙa kula da Rafi'ah wani abu daya dawo musu da matsalarsu sabuwa tunda suka dawo gida kwanansu biyu da dawowa ya shigo dakin nata da dare tana zaune tana bawa yaron nono ya zauna a gefenta yana kallon yanda take feeding na yaron abin yana burgeshi yakai hannu ya gyara mata riƙon yaron yace “Kwana nawa yau da haihuwar nan?" Batare data ɗago ba tace “biyar" jinjina kai yayi yace “Addini ne yace “Idan mace ta haihu ta raba shimfiɗa da mijinta?" Girgiza masa kai tayi yaja ajiyar zuciya ya miƙe yace “Ok al'ada ce kenan? To ni ban yarda da wannan al'adar ba nasan daidai Rafi'ah saidai bazan iya aikata daidai a daidai gaɓar da aka yimin badaidai ba Please kiyimin daidai nayi miki daidai ki dawo shimfiɗata ki tallafeni yafi sauƙi akan abinda zai iya biyo baya Noor inashan wahala da sanyi inason ɗuminki a kusa dani" Gana Hajja dake fitowa a bathroom ce ta cafe da cewa “ka kunna room Hit bazatazo ba anya kuwa Audu kai ba hariji bane to in banda haka yarinya daga haihuwarta ko sati bata rufa ba ka fara kafa mata sharraɗin komawa turaka ubanme zatayi maka tana fama da kanta" idanunsa kan Rafi'ah da tayi ƙasa da kanta baka iya gane asalin yanayin da take ciki yace “Ba hariji bane Ni saidai Ni namiji ne me son kulawa abinda na faɗa miki kenan Rafi'ah saura ya rage gareki" Ficewa yayi abinsa ta ɗago idanunta da suka ciko da hawaye Gana Hajja tace “Taɓ ah yarinya dole ki rame wannan fitina haka to ubansa zakiyi masa" batada abin cewa shiyasa ta kulle bakinta kawai ta kwantar da Hisham itama ta kwanta ƙasan zuciyarta ji take yi kamar ta tashi taje taji me yake buƙata to inma taji ɗin tanada maganin matsalarsa ne? Dole ta kwanta tanata juyi can cikin dare taji tashin motarsa ta tashi tayi kasaƙe tanason tashi saidai batada ikon mikewa a daidai lokacin gabaɗaya zuciyarta ta ƙuntata da wannan sabbin ɗabi'u da yaketa fito dasu itadai bata sake rintsawa ba har garin Allah ya waye suka gama abinda zasuyi bai shigo gidan ba a takaice har washegari bai shigo ba kuma bai kira ba saida Gana Hajja ta gaji ta kirasa yake faɗa mata ya yi tafiya ne kuma zai iya ɗaukar sati biyu kafin ya dawo" *Oum Hairan* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9