irin zabura Alhaji Bala yayi kamar an d'ora mishi wuta yabi Hajiya lubna da wani mugun kallo
Hajiya Lubna sakin baki tayi tana kallon shi cikin tsananin mamaki
d'aurewa tayi tace "Alhaji Lafiya mai yafaru"?
Wani Mugun kallon ya k'ara binta dashi yace " ki fitar min daga d'aki bana San ganinki babu matar dana tsana sama dake wlh naso ace ke kika mutu ba Naila ba yar iska kawai mara mutunci"
Jikin Hajiya Lubna ne ya hau rawa sabida girgiza da tayi da maganarsa hawaye kuwa suka hau wanke mata fuska cikin in ina tace "Mai na maka haka Alhaji"?
" dalla ki b'ace min da gani har ni zaki ringa tambaya mai kika min sabida ke tantiriyar 'yar iska ce agaban idona maza bakwai sukayi layi akanki suna saduwa dake tsabagen kina jin dadin abinda suke miki ko tari bakiyi ba ballantana naji ihunki ballantana akai ga kiyi k'ok'awa dasu akan kar su sadu dake lumshe idonki kawai kikayi kina jin dadi Lubna Ashe ke yar iska ce bansani ba wlh na masifar tsanarki bazan iya cigaba da zama dake ba kyankyaminki ma nakeyi"
Hajiya Lubna zubewa tayi a k'asa kirjinta uwa ya fad'o k'asa ta ringa nanata "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" kallon Alhaji Bala kawai take dayake binta da wani irin kallon tsana cikin matsanacin kukan da ta fashe dashi tace "Bala nice yar iskar a zo har cikin gida ayi mana fyad'e nida 'yata bakayi wani yunkuri dan ka hanasu keta mana haddi ba har na rasa 'yata amma ka ce min 'yar iska kai da kake namiji ma sunfi k'arfinka sai ni danake mace zanyi k'ok'awa dasu"
Wani mugun tsawa Alhaji Bala ya daka mata yana "dalla rufe min baki yar iska sa'oinki da ake zuwa yi musu fashi a nemi a keta musu haddin kinsan irin k'ok'awar da muke yi dasu dan kawai kar a keta musu haddi akwai matar ma da sai da ta gwammace ta rasa ranta da a keta mata haddi Dana 'ya'yanta amma tsabagen ke 'yar iska ce kwanciyarki kawai kikayi suka ringa hawanki suna sauka"
Alhaji Bala Sam bai San ya saki layi ba
Hajiya Lubna kuwa kalmarsa kawai ke amsa kuwaaa a kunenta "
_Kinsan irin k'ok'awar da mukeyi dasu dan kawai kar a keta musu haddi_
Kanta taji ya mata nauyi a hankali ta mik'e ta fara ja da baya tana nuna Alhaji Bala cikin rawar murya da jiki tana "Bala Bala dama kai dan fashi ne har matan mutane kake ketawa haddi"?
Sai a lokacin Alhaji Bala yasan kwab'ar da yayi fuska a d'aure yace "dama bakisani ba ni cikakken dan fashi ne da kud'in fashi kike watayawa da kud'in fashi kike abinda ranki keso da kud'in fashi kike walwalawa na kashe rayuka sunfi dubu na ketawa matan aure da yan mata haddi sunfi Dari da ace banida kud'i bazaki tab'a yarda ki Aureni ba Dana zo Neman Aurenki babu Wanda ya gwada tambayata wane irin Sana'a nake sabida tsabar danginki makwadaita ne su dai kawai tunda sun samu mai kud'i shikenan dan haka Lubna ni Armrobber ne ni killer ne tunda kiringa da Kinsan waye ni I would not spare you kema kasheki zanyi kawai"
Hajiya Lubna aguje ta fice daga d'akin Alhaji Bala ya bita a guje
Cikin zafin nama ya damkota Hajiya Lubna ta saki wani irin ihu tana rok'onsa akan ya kyalleta
Janta kawai yake yi a k'asa har sai da yaja ta wajen bayan gidansa da rijiya yake ya damkota da hannu biyu yace "kin Riga da Kinsan sirrina kasheki shi zai fiyemin alheri idan na barki zaki tona min asiri mutane su San wayeni dan haka zan jefaki a cikin rijiyar nan idan yaso zancewa mutane na nemeki na rasa"
Hajiya Lubna cikin rawar murya tace "Bala wlh bazan tona maka asiri ba dan Allah kar ka kasheni ka tuba mu gina ingantaciyar rayuwa tunda kaga ishara akan tilon 'yarmu Naila abinda kayiwa 'ya'yan wasu akayi mata har sai da ya kai ta ga rasa ranta wlh babu Wanda zan gaya wa dan Allah kar ka kasheni"
Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace "Kasheki shi zai fimin alheri Lubna dan babu digon kaunarki araina bazan iya cigaba da zama dake amatsayin matata ba bayan maza bakwai sun shiga inda nake shiga"
Daga haka ya bud'e murfin rijiyar yana k'ok'arin Danna Hajiya Lubna a ciki sai ihu take
Ji yayi an fusge Hajiya Lubna daga hannunsa ya waiga da sauri dan yaga Wanda ya fusgeta
Na Maliya yagani asaman ruwa fuskarsa a d'aure
Alhaji Bala ko tsorata baiyi ba shima ya d'aura fuska yace "mai kake nema kuma awajena naga wacce kake so na kawo maka ta Riga da ta mutu"
"Nasan da haka shi yasa nazo na tafi da uwarta ta maye gurbinta kai kuma kana k'ok'arin ka
kasheta"
Alhaji Bala murmushin mugunta yayi ya kalli inda Hajiya Lubna ke zube tana rawar d'ari gumi yabi ya wanke mata fuska ta kalli Na maliya ta dawo da kallonta kan Alhaji Bala
"Zaka iya tafiya da ita na bar maka ita duniya da lahira Aljaninka dan saurayi yayi ta hutawa da ita har karshen rayuwarsa"
Na Maliya k'ara d'aura fuska yayi yace "naga alamar farinciki kake ka rabu da ita sabida ba kaunarta kake ba tunda hakane bazan mata komai ba taimakonta zanyi zan maidata garinsu sabida kar ka kasheta idan yaso kai kuma sai na d'auki fansa akanka kai da kwanciyar hankali sai dai a lahira ayanzu zaka gwammaci mutuwarka da rayuwarka a yanzu zaka girbi abinda ka shuka"
Alhaji Bala tab'e baki yayi yana harararsa
Na Maliya ya fashe da dariya ya b'ace
Da sauri Alhaji Bala ya juya yaga itama Hajiya Lubna ta b'ace daga wajen
K'ara tab'e baki yayi ya nufi cikin gidan dan yana ganin Na Maliya ya rage mishi aiki tunda ya tafi da Hajiya Lubna
Waje yayi direct ya nufi cikin motarsa dan ya d'auko wayarsa ya kira su Killer dan tunda yazo garin ya kashe wayarsa
A kashe yaji wayar Killer ya kira na Lion
A lokacin wayoyin suna gaban table d'in Akram da sauri ya d'auki wayar daya ga Alhaji Bala ke kiransa ya nufi wajen da aka kullesu a guje dan ya dade yana expecting d'in kiranshi
Su Lion dake zazzaune duk sun bi sun fita daga hayyacinsu sabida azabar da ake gana musu
Akram da sauri ya mik'a mishi wayar tare da d'ora bindiga akansa akan kar ya kwapsa dan ya Riga da ya gaya musu irin had'in kan dayake so su bashi dan su chapke Alhaji Bala cikin sauki
Lion sai da ya daidaita kansa da muryarsa kafin ya d'aga wayar yasaka a hands free
Kifta mishi ido Akram yayi yayi sauri yace "Oga muna ta gwada wayarka akashe dan mu muka gaisuwar rashin da aka maka da zamu zo black yace kar muzo tunda baka mana izini ba"
"Gwara da Baku zo ba dan ana ganinku ansan ba mutanen arziki bane rashi kam anyi min shi sai na d'auki fansa akan masu shekarun Nailata har sai na aika su Lahira kamar yanda aka aikata Lahira ina sauran suke"?
Da sauri Akram ga kifta mishi ido yana mishi magana da hannu
Lion yace " dukanmu muna nan a villa dake Abuja"
"Dats good dan anan zamu yi operation jibi ina Akram yake"?
" gashi nan oga"
Akram da sauri ya k'arba wayar Killer dake gefe kamar ya fusge wayar daga hannunsa yace mishi Akram Ss ne suna nan a kulle
Akram gaishe shi yayi yana ce mishi ya hakuri
Alhaji Bala ko amsa gaisuwar baiyi ba yace "kai jibi zamuje operation kuma kai zaka mana jagora wlh any slight mistake consider your self dead"
Da Sauri Akram yace "to Oga ina zamuje operation d'in"?
" Babu ruwanka da inda zamuje operation Ku dai zama ready kawai bawa Killer wayar dan na kirashi wayarsa a kashe"
Akram wani irin harara ya wurgawa Killer yana mik'a mishi wayar dan Killer na da taurin kai sai da Akram ya d'auko iron d'in da ake gana musu azaba dashi Killer ya daidaita nutsuwarsa yace
"Oga ina gaisuwa ya hakuri"
Alhaji Bala tsaki yayi yace "mai yasamu wayarka a kashe"
"Wlh oga wayana babu chaji ne"
"OK jibi ina nan shigowa zamuje gidan Alhaji Ghali dan chaji zamuyi operation da ba'a tab'a yin irinsa ba dan sai na d'au fansar kissar da akayiwa Nailata"
"Allah ya kai mu oga sai kazo"
Akram fusge wayar yayi daga hannunsa fuskarsa d'auke da murmushi dan dama burinsa ya San wa zasu je suyiwa operation d'in
Hajiya Lubna kuwa bata tsinci kanta a ko ina ba sai a k'ofar gidansu
Da sauri ta mik'e ta shige jikinta na rawa........
🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅
*A heart touching story*
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Follow me on Wattpad@Sadnaf*
*Page 14*
B'angaren su Samha kuwa rigima ake sosai da Alhaji Nazifi dan dangi sun sako shi agaba akan ya Auri cousin d'insa Nazifa sabida bai dace ya zauna babu mata ba kuma su Samha suna bukatar masu kula dasu
Fir Alhaji Nazifi yace bai San wanan zancen ba babu macen da zai iya zama da ita zai iya kula da 'ya'yansa ba sai yayi Aure ba
Babu yanda dangi basu yi dashi ba har Mahaifiyarsa yace Sam ba zai yi wani Aure ba shi da Aure sai dai A lahira akan dole suka hakura suka zuba mishi ido Nazifa kuwa ta tattara inata inata ta tafi
Daga Alhaji Nazifi sai su Samha da suka rage
Alhaji Nazifi yana iya k'ok'arinsa wajen kula dasu baya bari su zauna su kadai ballantana suyi tunani tsakiyarsu yake shiga yayi ta jansu da hira shi yake kai su makaranta kasancewar Saheeba da Suhaima makarantar gaba da secondary suke yi a university of abuja department d'insu ma d'aya suna level 2 suna karantar mass communication
Samha ce kawai ke final year a secondary school babu abinda suka fasa game da abubuwan da Hajiya Nafeesa keyi na b'angaren sadaka duk ranar jummaa da takewa Almajirai
Samha haka kawai fuskar Akram ya k'asa b'acewa a idonta indai ta zauna ita kad'ai sai tunaninsa ya fad'o mata ta ringa jin wani iri a zuciyarta Wanda ta ringa alk'anta haka da kiyayyar da take musu Dan babu wayanda ta tsana kuma bazata manta dasu ba sama dasu Alhaji Bala har gobe tana hango fuskokinsu a idonta Wanda Akram yafi tsaya mata a zuciya ta kuma rasa dalilin haka babu ranar banzan da zata dungura goshinta a k'asa batayi addu'a akan Allah ya tona musu asiri ba
Su Saiam kuwa suma tuni suka fara warware Dan mazajensu na iya bak'in k'ok'arinsu wajen deb'e musu kewa kullum a cikin waya suke dasu Saheeba addu'a suke sosai Akan Allah yayiwa Mahaifiyarsu Rahama duk da wani zubin su kanyi mafarki da ita a cikin kyakyawan yanayi
B'angaren su Akram kuwa tuni sukayi arranging d'in yanda zasu damke Alhaji Bala aranar da zaije operation gidan Alhaji Ghali inda suka jawa su killer kunne sosai akan su basu had'in kai kar Alhaji Bala ya gane wani Abu har suyi arresting d'inshi
Tuni su Akram suka nufi Dajin da suke zama Dan su jira Alhaji Bala
Inda 'yan sanda kuwa suka yi surrounding d'in gidan Alhaji Ghali ba tare da saninsa ba har da masu video coverage da hotuna
Alhaji Bala kuwa a no mercy d'insa ya nufi Abuja da mugun nufi a zuciyarsa dan tunda Naila ta rasu yaji bai k'i duk Wanda yayi tozali dashi ya mutu ba most especially mata Sa'anin Naila Dan aransa ma ya kuduri idan Akram yau ya bijirewa Umarninsa babu abinda zai hana ya harbe shi
K'arfe goma sha d'aya ya isa Dajin fuskar nan tashi a d'aure yana shiga kantamemen palon dukansu suka mik'e tsaye alamar girmamawa dan dama haka suke gaishe shi
Akram kuwa haka kawai gabansa ya yanke ya fad'i da suka had'a ido da Alhaji Bala take ya hau Jan addu'oi aransa akan Allah ya basu Nassara har su damke Alhaji Bala batare da wani failure ba
D'aya bayan d'aya Alhaji Bala ya ringa binsu da kallo wanda da ace da wadatar haske awajen babu abinda zai hana yaga yanda su killer suka fita daga Hayyacinsu gaban Akram kuwa sai fad'uwa yake
A hankali ya sauke idonsa akan Akram dan shine a k'arshe gabansa yaje ya tsaya ya damko kafad'arsa yace " Akram a yau inaso kasani babu tausayi babu imani a cikin al amarina kayi taka tsan tsan karka bijirewa umarni na dan wlh yau slide mistake idan kayi sai ka tafi lahira na d'au alwashin sai na d'au fansar Kisan da aka yiwa 'yata Naila wlh babu Wanda zan ragawa yau Dan haka u guys should be very carefull"
Killer ji yake kamar ya fito yayi magana yace wa Alhaji Bala Akram pretending yake ayau za'a kama shi dan ayanda yake ji aransa gwara a kashe Akram inyaso a kamasu gabad'aya take yayi amana da shawara da ya yanke
Ya bud'e Baki yace "Oga inada Magana"
Gaban Akram ne yayi wani irin Yankewa ya fad'i ya zubawa Killer ido
Killer kuwa ya d'auke kai ya kalli Alhaji Bala ya bud'e baki zai yi magana bud'e bakinsa ke da wuya yaji an d'auke shi da wani bahagon mari daya sa ya kusa kurmancewa
Dafe kumatunsa yayi da hannu biyu ya waiga da sauri Dan yaga Wanda ya zuba mishi wannan Marin
Hajiya Nafeesa ya gani a gefensa ta gwallo ido tana kallonsa sai huci take
Wani razannan ihu yasa ya kankame Black yana nuna hajiya Nafeesa da Hannu
Su Alhaji Bala kuwa suka bi inda yake nunawa da kallo basu ga komai ba
Wani ihun ya k'ara sawa A lokacin da Hajiya Nafeesa ta ringa doso shi yaje ya kankame Alhaji Bala yana k'ok'arin magana
Amma ina amadadin yayi magana sai gwaranci yake yi kamar mai koyon magana
A zuciye Alhaji Bala ya ture shi daga jikinsa ya d'auke shi da mari yana "wanan wane irin iskanci ne zaka ishe mu da ihu menene yake tsorata ka wani sabon iskancin ne haka"?
Killer zaro ido kawai yake yana gwaranci yana nuna Hajiya Nafeesa da hannu sai k'ok'arin kankame Alhaji Bala yake
Ihu kawai yake yana zagaya wajen yana gwaranci Dan Hajiya Nafeesa tsorata shi take sosai
Akram kuwa mamaki ya ringa yi na abinda yake tsorata killer haka har maganarsa ta koma ta yara
Alhaji Bala a zuciye ya damko killer ya wulashi d'aki ya kulle ya dawo cikin palon ya kalli agogon hannunsa yaga k'arfe sha biyu da minti ashirin
Bak'ak'en kayansa ya d'auko ya sa ya d'auko mask d'insa ya saka a fuskar shi with Command yace su wuce su tafi is time
Da sauri suka ringa ficewa jikinsu na d'an rawa Alhaji Bala ya ringa mamakin yanda akayi basu da kuzari kwata kwata sai da ya koma d'akin daya sa killer ya saka seletep ya rufe mishi baki sabida ihun da ya ringa yi Dan har fitsari ya saki a wando
Sannan ya fito suka d'auki hanyar gidan Alhaji Ghali yana ta sake saken irin muguntar da zai yi
Basu sha wahalar shiga cikin gidan ba dan Alhaji Bala sai da ya shirya sosai kafin su taho mai gadi ma gindin bindiga ya buga mishi ya zube awajen a sume
Da zuwansu da shigarsu cikin gidan 'yan sandan dake kewaye da gidan duk suna Sane tuni suka k'ara gyara tsayuwarsu suna jiran abasu Umarni banda masu video coverage da hotuna da suma suka zama ready suna jiran su fara aikinsu duk da wasu sun fara d'aukansu video a lokacin da suka shigo
Alhaji Bala k'afa d'aya akan d'aya ya d'ora a center table d'in dake cikin palon yana girgiza k'afa a lokacin da su Black suka raba Kansu suna fito da mutanen dake cikin gidan ciki kuwa har da Akram da wani irin farinciki yake ratsa shi na cikar burinsa finally Alhaji Bala yau asirinsa zai tonu
Alhaji Bala kuwa wani irin dariyar mugunta yake a lokacin da yaga ana hankad'o keyar 'ya'yan Alhaji Ghali Dan dukansu sun zo Hutu su wajen Uku had'add'un yan mata kyawawa dasu
Alhaji Bala sai Lashe lebb'e yake yana matsa cinya yana hararo yanda zai musu fata fata har sai sun koma ga mahallicinsu
Alhaji Ghali kuwa da matansa biyu jikinsu rawa kawai yake
Sai da ya gama karewa 'yan matan kallo ya maida kallonsa kan Alhaji Ghali yace "kasan abunda ya kawo mu ba sai ka b'ata mana lokaci ba"
Alhaji Ghali jiki na rawa ya shiga gyad'a masa kai
Alhaji Bala kuwa ya kalli Lion da black sukayi sauri suka tisa keyar Alhaji Ghali suka shiga ciki suka hau fito da kud'add'e a brief case suka hau ajiyewa agaban Alhaji Balan daya tsurawa 'ya'yan Alhaji Ghali ido da suka cure waje d'aya jikinsu na rawa
Sai da suka gama ajiye kud'in agabansa ya kalli Alhaji Ghali da jikinsa ke rawa yace
"Ka tabbata duk kud'in dake cikin gidanan kenan"?
Girgiza masa kai Alhaji Ghali kawai yayi dan yama k'asa magana kwata kwata
Alhaji Bala murmushi yayi ya mik'e ya nufi wajen 'yan matan yana wani lashe lebb'e
Alhaji Ghali kuwa yayi sauri yasha gabansa cikin rawar murya yace " bawan Allah Dan Allah dan annabi karka tab'a min yarana idan kud'i kake so zan k'ara maka"
Alhaji Bala wani Mahaukacin dariya ya kwashe dashi yace "ko duk kud'in duniyan nan zaka bani wlh babu abinda zai hana ni yaga yaran can"
Gaban Alhaji Ghali ne yayi wani irin fad'uwa ya durk'usa akan gwiwarsa yace "bawan Allah ka rufamin asiri dan Allah karka tab'a min yarana"
Alhaji Bala wani dariyar ya k'ara kecewa dashi yace "ai ba iya yaranka zan tab'a ba har da wadancan guzumayen"
Akram kallonsu kawai yake yana murmushi
A lokacin da 'yan matan suka fashe da kuka suna k'ara kankame juna
Alhaji Bala ture Alhaji Ghali yayi daga gabanshi ya nufi wajensu yana wani dariya
Alhaji Ghali kuwa yabi bayansa da Sauri yana rok'on shi
Fuska a d'aure Alhaji Bala ya juyo ya kalli Akram da still murmushi yake shimfid'e a fuskar shi yace "take care of this fool"
Akram cikin takun kasaita ya nufesu yana wani irin murmushi adai-dai lokacin da Alhaji Bala ya finciko d'ayarsu ta saki wani wawan Ihu
Wani bahagon Mari Alhaji Bala ya shimfid'a mata a fuska ya jawo rigarta zai raba gida biyu yaji an d'ora mishi bindiga a k'eya yaji ana " thousand days for the thiefs one day for the owner Alhaji Bala your cups is full"
Alhaji Bala a hankali ya juyo dan ya gaskata muryar Wanda yaji............ 🧐🧐🧐🧐🧐
🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅
*A heart touching story*
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Follow me on Wattpad@Sadnaf*
*Page 15*
Da Mad'aukakin mamaki Alhaji Bala ya zubawa Akram ido dake wani irin Murmushi
Akram kuwa yace "Kana mamaki ne Alhaji Bala yau dubunka ya cika asirinka ya tonu yau mutane zasu San wanene kai yau duniya zata San irin mugayen abubuwan da kake aikatawa yau za'a San irin sana'ar da kake yi har kake taimakawa mutane ake maka kallon mutumin kirki nan kuwa babu Wanda ya kai ka zalunci a d'oron k'asa am not who you think am not one of you nashiga cikinku ne Dan na k'ara Sanin kai waye Alhaji Bala despite abinda ya faru da ya kamata ya zame maka ishara na fyaden da aka yiwa 'yar ka har ya kai ta ga rasa ranta wannan bai sa ka saduda ba kayi nadamar abinda kayi kasan cewar abinda kake yiwa yaran wasu ne ya juya kanka amma me a madadin kayi nadama a lokacin ka k'ara shan Alwashin yanda zaka cigaba da farautar dukiyoyin jamaa kana ketawa 'ya'yansu haddi not any more Alhaji Bala a yau"""
Wani mahaukacin Dariya Alhaji Bala ya fashe dashi yace "kayi kuskure Akram da kayi tunanin wannan soki burutsun da kake yi zai tsoratani I thought as much kai ba Alheri bane awajena and ayau zanyi finishing d'inka Lion Black before counting of 3 Ku bud'e mishi wuta"
Alhaji Bala yace yana buga k'afarsa da kasa tare da rik'e hannun Akram dake rik'e da bindiga
Su Lion ajiye bindigogin hannunsu sukayi amadadin su bi umarninsa
Alhaji Bala ya saki baki yana kallonsu cikin tsananin mamaki Akram kuwa ya saki murmushi yana girgiza kai
A tsawace Alhaji Bala yace "kanku d'aya kuwa ko Baku ji mai nace ba shoot this fool before counting of 2"
Lion a hankali ya girgiza kansa yana "oga bazamu iya ba"
Alhaji Bala jikinsa ne ya fara rawa for the first time yaji gabansa ya fad'i
Shammatar Akram yayi ya d'auki bindigarsa da ya ajiye a k'asa.
A tare sukayi pointing juna da bindigar
Alhaji Bala kyalkyalewa yayi da dariya yace "Akram you are such a big fool wlh babu abinda zai hana yau na kasheka Sai a yau nake dana sani Dana taimake ka Mai gida ya yaudareni da ya bari na jawo ka jikina tayaya mutane zasu San abunda nake aikatawa tayaya dubuna ya cika Do u have any prove against me no u don't have now drop your gun or I else"
"Or else what Alhaji Bala wat can you do"? Yaji an fad'i daga bakin k'ofa
Da sauri ya waiga Dan yaga Wanda yake magana
Abdullahi ne ya shigo 'yan sanda suna take mishi baya tare da pointing d'inshi da bindiga
Alhaji Bala Ido ya waro sosai a lokacin da 'yan sanda suka zagaye shi 'yan jarida da video coverage suma suka hau haska su da cemarorinsu
Bindigar Hannun Alhaji Bala subucewa yayi daga hannunsa cikin tashin hankali yafara binsu da kallo d'aya bayan d'aya jikinsa na rawa
Akram kuwa ya k'ara sakin murmushi yace " yadai oga y are u speechless da ka gansu I thought ai zaka bud'e musu wuta ne da suka shigo"
Juyawa yayi ya kalli masu video coverage da hotuna yace "Ku d'an Matso kad'an kuga Wanda ke mana wannan aika aika kuga Wanda ke farautar dukiyoyin jama'a da yiwa yaran mutane fyad'e"
Da sauri suka matsa kusa da Akram Dan burin kowa yaga shi ya fara d'aukan wanan mugun Dan fashi da ya addabi jama'a
Alhaji Bala jikinsa in banda rawa babu abinda yake yi gani yake kamar mafarki yake yi wai shi yau 'yan sanda suka zagaye da 'yan jaridu
Akram kuwa a hankali ya matsa kusa da Alhaji Bala 'yan sanda kuwa suka k'ara saita shi da bindigoginsu in case in zai yi gardama
Akram da murmushi ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya Ciro mask d'in fuskarsa
Alhaji Bala yayi sauri ya rik'e mishi hannu yana "Akram Dan Allah karka min haka ka rufa min asiri kar ka kunyatani"
Wani irin murmushi Akram yayi ta gefen baki yace "kunya kuma Alhaji Bala kunya fa kace ai babu batun kuma jin kunya a yau babu batun rufin asiri ayau a yanzu zan cire wanan Mask d'in fuskar taka kowa yasan kai waye"
Alhaji Ghali da sauri yaje ya tsaya a gefensu Akram dan ya matsu yaga waye
Alhaji Bala runtse idonsa yayi da k'arfi jikinsa na masifar rawa a lokacin da Akram yafara k'ok'arin cire Mask d'in fuskarsa
"Alhaji Balaaaaaaaaaaaa" Alhaji Ghali yace cikin shock tare da nuna shi da hannu
Wayanda kuwa basu San Alhaji Bala ke wannan ta'asar ba suma jikinsu ya hau rawa suka k'ura mishi ido har da masu k'ara Murza idonsu dan su tabbatar da shine ko ba shi bane.
Alhaji Bala kuwa runtse idonsa yayi gam yak'i ya bud'e idonsa dan flash d'in camerori ke haska shi ko ta ina
D'aya daga cikin 'yan sandan ne ya matsa kusa dashi ya kamo hannayensa ya saka mishi ankwa
Alhaji Bala da sauri ya bud'e idonsa sakamakon wani mahaukacin dariya dayaji a gefensa
Na Maliya ya hango akan ruwa sai yawo yake asaman ruwa yana kyakyata dariya
Alhaji Bala kuwa hawaye ya hau zubo mishi a idonsa
Na Maliya yace "Alhaji Bala mai akayi da maza ai baka ga komai ba tukuna sai na taso maka wayanda zasu na d'ebe maka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13