Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai abun yi dan Allah ka taimaka min dan ni Dana San matar nan haka take wlh da ban soma ma kasheta ba da iya shegun zan d'ebo na fito" Alhaji Bala yace cikin rawar murya Mai gida ajiyar zuciya ya sauke yace "Abu biyu zaka iya yi ta rabu dakai na d'aya ka koma gidan ka d'auko wanan hular nata ka kona shi na biyu kaje gidan ka durk'usa agaban mijinta da yaranta kace su yafe maka idan sun yafe maka to zata rabu dakai amma idan kuwa acikin biyun nan ba'ayi d'aya ba to ni kam babu abinda zan iya yi akai kuma Abubuwa na dab da jagule maka ga rashin kwanciyar hankali da zakayi ta fama dashi" Hankalin Alhaji Bala idan yayi dubu ya kai kololuwa wajen tashi a firgice ya mik'e yana "mai gida kasan mai kake cewa kuwa ta ina zan iya samo hular da ta cire?ta yaya zan koma gidan a matsayina na Wanda ya kasheta haba maigida ya zaka fad'i abinda ba zai yiwu ba" Mai gida ce mishi yayi to "iya abinda na duba kenan Wanda zaka yi ta rabu dakai amma bayan shi babu abinda zaka iya yi akai amma dai zan baka wasu Abubuwa idan ka dace ba zata ringa zuwar maka ba" Da sauri Alhaji Bala ya zauna yana "dan Allah ka taimakeni matar nan ta firgitani har tsirara nayi agaban 'yata bansani ba" Mai gida wani kwarya ya d'auko Wanda aka nannad'e da jajayen k'yalaye ya mik'a mishi yana " idan ka tashi ka warware wanan Jan k'yallen ka daura akan goshinka da k'afarka akwai wani kullin magani guda biyu a ciki bak'in jikawa zaka yi ka shafa a jikinka gabad'aya wari ne dashi kamar kashi amma haka zaka d'aure idan gari ya waye sai ka wanke D'ayan kuma turara d'akinka zaka yi dashi kafin ka kwanta bacci" Hannu yasa ya d'auko Wasu jajjayen candles ya kuma mik'a mishi yana " ka kashe wutan d'akinka sai ka kunna candles d'in idan dai kaga tazo maka bayan kayi abubuwan nan to babu abinda zan iya yi akai face dai zabin farkon Dana baka" Alhaji Bala da Sauri yace "insha Allahu ma ba zata kuma zuwar min ba indai nayi yanda kace" Mai gida girgiza kansa kawai yayi bai ce komai ba ahaka Alhaji Bala ya ajiye mishi makud'an kud'i ya tafi........... [2:36PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫 *Written by* 馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝 *A heart touching story* 庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* _莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *HEA MASOYANA FANS D'INA INA FARINCIKIN SANAR DAKU INA UPDATING NOVEL D'IN BAK'IN DARE A WATTPAD ACAN ZAN RINGA POSTING KAFIN WATSAPP SO PLS IF U ARE REALLY I DIE FAN DONT FORGET TO SEARCH FOR SADNAF FOLLOW AND VOTE ME THERE I WOULD B GREATFUL WEN I START COUNTING YOUR VOTES*馃檹馃檹馃檹 *Page 8* Wasa wasa sati biyu kenan da Alhaji Bala yaje wajen Mai gida abunda ake cewa kwanciyar hankali Sam Alhaji Bala bashi dashi dan Duk abinda Mai gida yace yayi ya yi amma Kullum sai Hajiya Nafeesa tazo mishi a cikin mafarki ko a zahiri yabi ya zama kamar mai k'aramin tab'in hankali Dan ko yaya yaji motsi sai ya firgita ya zunduma Ihu Hajiya Lubna da Naila kuwa hankalinsu yayi masifar tashi da halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Dan tunda ya fara shafa wani magani mai Warin kashi a jiki ga jajayen candles da yake kunawa duk dare suka fara tsorata da lamarin Alhaji Bala Naila b'uya ma take a d'aki dan ta fara zargin Daddynta yafara samun tab'in hankali kowane lokaci zai iya rufesu da duka dan abun nashi ya kai yanzu har da rana Ihu yake shi kad'ai idan yana zaune a cikin Palo ya kuma k'i gayawa Hajiya Lubna abinda ke faruwa idan ta matsa mishi da tambayoyi sai ya rufeta da fad'a tamkar zai daketa A haka suka zuba mishi ido suna mishi addu'a samun sauki B'angaren su Saiam kuwa Addu'a suke babu dare babu rana akan Allah yayi wa Hajiya Nafeesa Rahama ya kuma toni asirin Alhaji Bala har akayi sadakan bakwai bakinsu na d'auke da azumi idan kagansu sai sun masifar baka tausayi dan kowacensu kalar idonta ya koma ja sunyi shak'uwa da mahaifiyarsu fiye da tunanin mai tunani ko abinci basa iya ci ballantana akai ga cikakken bacci ahaka nasu nafila ne akan Alhaji Nazifi tunda danginsu dake tayasu zaman makoki suna dan kwantar musu da hankali sabanin Alhaji Nazifi da ke wuni a d'aki baya fitowa ba um bare uhum uhum haka zai yi tagumi yana kallon Hoton Hajiya Nafeesa lokaci lokaci yana share hawayen dake zubo mishi duk Wanda yazo mishi gaisuwa sai dai ya hakura ya tafi dan Alhaji Nazifi baya ko motsawa daga inda yake kiran Sallah kawai ke sa ya tashi Sallar ma a d'aki yake yinta a k'arshen sujadarsa kuwa kuka yake fashewa dashi yayi ta yiwa Hajiya Nafeesa Addu'ar Rahamar Allah Sai da akayi Sati biyu da Rasuwar Hajiya Nafeesa Alhaji Nazifi ya d'an fara dawo wa dai-dai a inda ya nemo wani babban Mallami mai tarin ilimi yace ya taya shi da addu'ar Allah ya tonawa azzalumin da ya kashe Hajiya Nafeesa Asiri shi da zaman lafiya har Abada Mallamin kuwa yace ya kawo kud'in Sadaka ya had'a kan Almajirai ya raba musu ayoyi da addu'oi insha Allahu asirinsa na dab da tonuwa Makud'an kud'i Alhaji Nazifi ya bashi tare da yi mishi godiya A Daren ranar suna zaune a Palo gabad'aya kowanensu hannunsa d'auke da carbi yayan Hajiya Nafeesa Alhaji Musa da tun magriba yana gidan kallon Alhaji Nazifi yayi dayake Jan counter kansa a sunkuye yayi yace mishi yanzu sai dai a d'aga Auren Safna da Saiam idan Hajiya Nafeesa tayi Arba'in sai a d'aura musu Auren dan ba dan rasuwarta ba da gobene d'aurin Auren Saiam juyar da kanta tayi dan ita yanzu Sam Auren bama ya gabanta bata jin zata iya Aure ta rabu dasu Sahiba gwara ta zauna ta kula da kanenta tunda itace Babba Alhaji Nazifi sai da yafara Sauke ajiyar zuciya kafin ya d'ago yace " A goben za'a d'aura musu Aure insha Allahu babu abinda za'a fasa dan Nafeesa ta rasu bashi zai sa a d'aga daurin Auren ba dan ko an d'aga ba dawowa zatayi ba ni nasan burinta bai wuce taga ranar d'aurin Auren Su ba kuma insha Allahu zan cika mata wanan burin nata dazu na yiwa iyayen mazajen waya akan su zo da shirinsu gobe k'arfe goma sha d'aya za'ayi D'aurin Auren in yaso sa tare idan an kwana biyu" Tunda Ya fara magana Saiam da Safna suka d'ago arazane suna kallon shi kuka suka fashe dashi kamar had'in baki Saiam tace"Daddy dan Allah kar a d'aura mana Aure gobe mummy satinta biyu da rasuwa yau ya za'ayi a d'aura mana Aure gobe ni wlh na hakura da Auren zan zauna na kula da kanena idan mukayi Aure waye zai kula dasu Daddy Dan Allah mun fasa bama San Auren" Saiam ta karashe maganarta cikin matsanacin kuka Alhaji Nazifi Da ji yake kamar shima ya fashe da kuka girgiza kai yayi ya mik'e daga kan kujera ya nufi inda suke a zaune Zama yayi agabansu ya tank'washe k'afafunsa ya kira sunan Saiam da Safna yace "Karku manta ni ina rayye ban mutu ba ni zan kula dasu har zuwa lokacin da suma zan Aurar dasu burin Mahaifiyarku Kullum bai wuce taga ranar Aurenku ba kuma ni nasan a yanzu idan aka d'aga d'aurin Auren nan sabida ita bazata ji dadi ba gwara in cika mata burinta duk da bata Raye idan ta kanenku ne insha Allahu ni zan kula dasu ba wai ana d'aura Auren gobe a goben zaku tare ba sai an d'an kwana biyu haka mun d'an k'ara samun nutsuwa mun k'arasa sauran shirin namu sai Ku tare" A takaice da k'yar Alhaji Nazifi da Alhaji Musa suka shawo kansu Saiam suka yarda za'a d'aura musu Aure a gobe Su Suhaima kuwa tausayin Kansu ne ya k'ara lullub'esu dan ahaka da suke d'an ganin juna hankalinsu ke kwanciya ayanzu kuma idan Saiam da Safna suka yi Aure gidan girma zai k'ara yi musu B'angaren Akram kuwa suna nan suna shirye shiryen yanda zasu kama Alhaji Bala cikin Sauki shi da yaransa inda Akram ke kiran su Lion da suka Dade da komawa gidansu dake Daji dan cika Umarnin Alhaji Bala Akram kuwa karya ya ringa musu da Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa bai dawo ba amma kafin ogansu ya dawo zai dawo Akram ganin anyi sati Biyu Alhaji Bala bai kira shi ba yasa yafara shan jinin jikinsa yana tunanin ko dai Alhaji Bala ya gano cewa shi Ss ne Lambar Alhaji Bala ya gwada kira bai d'aga ba sai da ya mishi miss call biyar bai d'aga ba take hankalin Akram ya tashi oganshi ya kwantar masa da hankali yace ya kira su Killer ya bugi cikinsu yaji idan kuwa suma basu d'aga ba to tabbas sun gano shi Yana kiran Killer ya d'aga wayar Akram yace mishi a cikinsu akwai Wanda sukayi waya da oga kuwa dan yana ta kira bai d'auka ba Mamaki ne ya rufe Killer yace mishi suma tun jiya suke kiranshi baya d'auka yanzu nan ma fire ya gama kiranshi bai d'auka ba Hankalin Akram ne ya kwanta da yaji abinda yace sai yace mishi to bari zai cigaba da kiran shi watak'ila yana hutawa ne da haka suka yi Sallama Oganshi yace ya kwantar da hankalinsa tamkar Alhaji Bala ya gama zuwa hannu ne B'angaren Alhaji Bala kuwa ayau yafi kowace rana shiga tashin hankali dan Hajiya Nafeesa bata b'acewa idan ta zo mishi a yanayi na ban tsoro take zuwar mishi sosai Hajiya Lubna sallati kawai take yi dan ita bata ganin abinda yake firgita shi yake ihu yana zagaye d'akin abinda Alhaji Bala ya kwana yana yi kenan Naila kuwa kuka kawai take tana tunanin ko aljanu ne suka sako Alhaji bala agaba Sai da aka fara kiraye kirayen Salla Alhaji Bala ya daina ganin Hajiya Nafeesa A guje ya fito daga d'akinsa duk yabi ya firgice kamar bashi ba daga shi sai dogon bak'in jallabiya babu ko dogon wando a ciki yaje ya hau motarsa ya bar gidan Rabonsa da yaji shi cikin kwanciyar hankali tun kafin yaje gidansu Hajiya Nafeesa a 360 ya ringa fisgar motarsa ikon Allah kawai ne ya kai shi mai duguri wajen mai gida Yana parking yasa hannu abayan seat d'in motarsa ya zaro k'aramar bindigarsa yasaka a Aljihunsu fuskar nan tashi a turb'une Sai da mai gida ya gama uzurinsa kafin ya fito daga cikin gidansa Ya zauna akan buzunsa yana kallon Alhaji Bala daya k'afe shi da ido ya tsaya tamkar wani soja Murmushi mai gida yayi yace "kura ya dai ko dai fatalwar ce duk ta firgita ka haka dama na gaya maka wanan zabin farkon shi zaka bi ka ta rabu dakai idan ba haka ba wlh sai ta zarar dakai" Alhaji Bala wani irin kallo yayi wa mai gida yace "mai Mara bata da zararren ai babu dan ta zarrar Dani duk inda nayi sai na ganta yanzu mai gida kana so kace min babu abinda zaka iya yi wanan matar ta rabu dani"? Mai gida wani kallo ya watsa mishi yace "idan da akwai zan tsaya b'ata wa kaina lokacine babu abinda zan iya yi akai zabin nan dai nafarko shi zaka bi ta rabu dakai" Dariyar mugunta Alhaji Bala ya kwashe dashi yace " yanzu dai kana so kace min Fatalwa ta fi k'arfinka kana so kace min duk abubuwan nan da ka rataya da aljanun da suke maka aiki bazasu iya min maganin matar nan ba"? Mai gida zuba mishi ido yayi yana kallonsa a dai dai lokacin da zoben daya saka a hannun shi ya fara mishi zafi Take Mai gida ya mik'e hankalinsa a tashe yana kallon Alhaji Bala dan yasan ba alheri ne ya kawo shi wajensa ba kafin ya kai ga wani tunani Alhaji Bala ya zaro bindigarsa daga Alhajinsu ya nuna shi dashi yana "Mai gida banga amfaninka a doron k'asa ba tunda bazaka iya magance min matsala ta ba idan dai k'asar da kake bugawa ta gaske ce bai kamata ace da ka buga bai gaya maka gidan matar nan da zamuje zai zame min masifa ba dan haka gwara na kasheka tunda yanzu ba amfani kake min ba kafin mai gida yayi wani yunkuri Alhaji Bala ya sakar mishi bullet hud'u Mai gida take ya zube a k'asa jini na ambaliya wajen yafara dan girgiza Alhaji Bala dake huci yayi tsaki yajuya ya nufi wajen motarsa Alhaji Bala sai da ya bar wajen mai gida yafara tunanin wajen wa zai nemi taimako wane mallami zai samu ya iya mishi aiki Hajiya Nafeesa ta rabu dashi yana cikin wanan tunanin wani tsohon Mallaminsa Mallam na maliya ya fad'o masa arai shima wani hatsabibin Mallami ne dan shi akan ruwa yake zama a dalilin Mai gida ya watsar dashi Bai tsaya wani dogon tunani ba ya d'auki hanyar Sokoto bashi ya isa kungurmin dajin ba sai Tara na dare Sai daya sha bak'ar wahala ya iya gane wajen Tunda ga nesa ya faro jiyo muryar Mallam na Maliya na mishi maraba tun bai k'arasa ba ya hau fad'a mishi abubuwan dake tafe dashi Alhaji Bala kuwa da hanzarinsa ya k'arasa wajen da yaji muryarsa na fitowa Sai da yayi kamar zai yi mishi sujadda kafin ya d'ago ya kalli Mallam Na Maliya dake ta juyi asaman ruwa a zaune shi ba a k'asa ba shi ba a sama ba Sai da ya fara kwashewa da wani mahaukacin dariya yace "Kura matar nan da ka kashe tana da k'arfi rabaku sai an sha wahala amma awajena Abu mai sauki ne zan baka wani ruwa ayanzu kayi wanka da shi zaka daina ganinta na 'yan kwanaki kafin ta cigaba da zuwar maka kafin lokacin kasan yanda zaka je kabarinta ka haka rami agefen kabarin nata kasa wanan wuk'a da layan ka binne idan dai kayi haka ta rabu dakai kenan har abada" Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa yace "Na Maliya ai bansan a inda aka binneta ba" "Wanan yafi komai Sauki kaje unguwarsu idan kaje ka samu wani Mara k'arfi kace ya raka ka makabarta zaka je kayiwa mammata addu'a daga nan zaka iya bugar cikinsa kaji a inda aka binneta tunda sunan mijinta ba b'oyayye bane kana cewa Ashe matar Alhaji wane ta rasu ni kuwa ina kabarinta yake da haka zaka bugi cikinsa bayan kayi mishi alheri ni nasan zai nuna maka daga nan sai ka aiwatar da kudurinka indai ka samu ka binne ni nasan zata rabu dakai har Abada" Wani nanauyan ajiyar zuciya Alhaji Bala ya sauke Dan gani yake abin da kamar wuya kansa ya k'ara sadawa k'asa kamar zai mishi sujadda kafin yace "Godiya nake Na Maliya menene ladan aikina" Wani Mahaukacin dariya Na Maliya ya kwashe dashi kafin yace " kai ma kasan bana fad'a sai komai ya kammalla kuma duk abinda nace ayimin idan ba'ayi min ba kasan mai zai biyo baya dan ba iya fatalwar matar zan sa ya ringa bibiyarka ba har da sauran mutanen daka kashe" Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace angama indai Hajiya Nafeesa zata daina bibiyarsa da haka yayi mishi sallama da zumar sai ya dawo ya mik'e a gajiye yaje ya hau motarsa ya kuma d'aukar hanya....... [2:37PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫 *Written by* 馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝 *A heart touching story* 庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* _莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *Follow me on Wattpad@Sadnaf* *Page 9* Alhaji Bala ba k'aramin farinciki yayi ba a lokacin da yaga ya kwana biyu Hajiya Nafeesa bata zo mishi a amafarki ko a zahiri ba Tuni yafara dawowa dai-dai hankalinsa ya fara kwanciya sai a lokacin yaje ya samu Naila har cikin d'akinta sabida ta daina fitowa gabad'aya sabida tsoronsa da take ji Hajiya Lubna kuwa ido kawai ta zuba mishi bata k'ara bi ta Kansa ba tunda taga alamar baya so ya fad'a mata abinda yake damun shi Naila da sauri ta mik'e a lokacin da taga ya shigo Alhaji Bala ya sakar mata murmushi yana "zo nan babyna kar dai kice gudun daddynki kike"? Naila itama murmushin ta sakar masa da ta Gan shi a nutse ta tafi da gudu ta rungume shi tana "Daddy what happened to you" Murmushi Alhaji Bala yayi a lokacin dayake kwantar mata da dogon gashinta San tilon 'yarsa na ratsa mishi zuciya yanda yake jin San Naila he can do anything bcos of her Zame ta yayi daga jikinsa ya rik'e hannyenta ya nufi dogon kujerar dake d'akin ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta tare da kuma rik'e hannayenta yace " am so sorry dear Some thing came up that Daddy could not handle but now am fine u should not be scared again" Naila murmushin farinciki ta saki tace "Daddy yanzu ka warke babu abinda yake damunka" Alhaji Bala cikin farinciki ya gyad'a mata kai Naila kuwa ta tashi ta fara tsallen murna kamar wata yarinya dama yarinyar ce ma tunda she is 14yrs Alhaji Bala mik'ewa yayi yace ta shirya anjima zasu tafi shopping ta zabi duk abinda take so Naila wani tsallen murnar ta k'arayi tare da rungumeshi tana " I love u daddy you are d best dad eva " "I love you to Darling" Alhaji Bala yace adai dai lokacin da yake barin d'akin fuskarsa d'auke da tsantsar farincikin yayewar matsalarsa D'akin hajiya Lubna ya nufa dan ya rarrasota dan yasan fushi take dashi Bai sha wahala wajen rarrashinta ba abunka da mata da miji sai gashi sun bige da soyayya dan dama tunda ya dawo basu had'u ba sabida rashin kwanciyar hankali sai da komai ya wakana Hajiya Lubna ta hau bashi shawarwari akan ya daina wasa da Sallah dan ita tasan aljanu ne suka ringa tsorata shi sabida babu wani kariya a jikinshi Murmushi kawai Alhaji Bala yayi yace mata to zai gyara daga haka ya mik'e ya fad'a band'aki Siyayya yayi wa Naila na fitar hankali Hajiya Lubna sakin baki kawai tayi tana kallon shi dan siyayyar ma har Dana banza bata kuma isa ta hana shi ba idan ma tayi magana cewa zai yi ita kad'ai ce dashi gwara ya kashe mata Sai da magriba suka dawo gida bayan ya kaisu wajen shakatawa aka ringa jido musu siyayyar da sukayi ana shiga dashi cikin gida Alhaji Bala yana tsaye aka gama shiga da kayayyakin Hajiya Lubna da Naila kuwa dama sun Dade da shiga ciki Wajen motarsa ya koma ya shige ciki tare dasa lock Wayarsa dayake communicating dasu killer ya d'auko daga bayan seat d'in motarsa dan baya shiga da wayar cikin gida sabida tsaro Bai yi mamakin ganin miss call d'insu ba dan yasan Dole dama su neme shi Layin Killer ya fara kira bugu d'aya ya d'auka Yana amsa gaisuwar da Killer ya mishi yace "karku damu oll is fine na d'an shiga rububi ne hope duk kuna villa( sunan da yake cewa gidansu dake daji) Killer ce mishi yayi " eee oga duka muna nan AKram ne kawai har yanzu bai zo ba sakamakon mom d'insa bata da lafiya yama ce zai kiraka ya fad'a maka" "Zancen banza zancen wofi ina ruwanmu da wani Mom d'insa bata da lafiya who even cares ko mutuwa tayi dole ya dawo bakin aikinsa bansan mai yasa yake so ya ringa take umarnina ba amma babu komai zanyi wa tufkar hanci tunda mai hanani is gone let me call the fool" Bai bari Killer yayi magana ba ya kashe wayar yana huci tare da dialling number Akram Adai-dai lokacin da Akram ke kan Sallaya yana Jan carbi idonsa a lumshe fuskar Samha nata mishi yawo a ido dan kwanaki nan shi kad'ai yasan mai yake ji akan Samha duk fitar numfashinsa sai ya tuna ta bai tab'a jin San 'ya mace a zuciyarsa kamar yanda yake jin San Samha duk da Sau d'aya ya tab'a ganinta Ringing d'in wayarsa ne yasa ya bud'e idonsa tare da d'aukar wayar ganin mai Kiran ne yasa ya mik'e da sauri tare da gyara zamansa ya d'aga wayar Alhaji Bala fad'a ya rufeshi dashi yana "wai meyesa kake so kaga kana bijirewa umarni na ne? Yanzu kawai Dan uwarka bata da lafiya shiyasa Baka koma Villa ba tuntuni yo ko mutuwa tayi na baka umarni kak'i bi Akram abubuwan da kake min ya isa haka not any more yanzu ba zanyi tolerating wanan nonsense d'in naka ba idan muka fita operation dole ka ringa participating idan na saka doka dole kuma ka bi baka isa kuma ka bar cikin mu ba Dan idan kayi joining d'inmu ba fita idan kuwa ka dage zaka fita sai na kasheka na kashe family d'inka gudun tonuwar asirinmu yanzu ba anjima ba ka shirya ka tafi Villa jibi muna da operation and kai zakayi leading d'inmu ranar kaji mai nace ko baka ji" Da k'yar Akram ya iya cewa naji sabida tsananin mamakin Yanda Alhaji Bala ya canza take ya fara tunanin ko dai Mai gida ya fara ganowa shi d'an lek'an asiri ne Jikinsa na rawa yafara Neman oganshi Abdullahi dan ya gaya mishi halin da ake ciki Shima mamaki ne ya rufe shi daya gama jin abinda Akram yace ajiyar zuciya ya sauke yacewa Akram "tabbas Alhaji Bala is up to some thing tunda kaji yace yanzu kai ma dole ka ringa participating idan ya fita operation" Akram hankali a tashe yace "oga yanzu ya za'ayi nifa bazan tab'a iya wani Abu ba idan ya fita rashin imaninsa har fyad'e fa yake sawa ayiwa yaran mutane da matan su ni aganina kawai tunda mun Riga da mun samu evidences kawai gobe aje har gida ayi arresting d'in shi" Da Sauri Ogan shi yace "aa Akram ai inaga yanzu ya fara gano ka ne so shi yasa yake so ya tabbatar ko kai d'an lek'an asirine yanzu abinda za'ayi idan yasan wata ai bai San wata ba ka shirya kaje ayau d'in kamar yanda ya bukata inyaso kafin Ku fita operation d'in ka ringa k'ok'ari kana sanin wanda za'aje ayiwa operation d'in idan yaso sai ka sanar damu ko ta text message ne mu kuma zamuyi sauri mu sanar dasu akan su bar gidan da dukiyarsu kar su kwana a gidan kai kuma u would pretend ka jagorance su aranar kai ma irin no mercy d'inan kaga idan kuka je ka babu Wanda zaku samu mun Riga da mun ruguje mishi plan bai Sani ba haka zamu ringa mishi a duk lokacin da zaku fita ka dai kawai ka ringa sanar damu gidan da za'aje kaga ahaka zamu kama shi red handed dan inaso aranar da za'a kama shi a har video covering da yan jarida zamu tafi inaso kafin muyi arresting d'in shi yafara samun failure a duk fitar da zakuyi" Wani irin murmushi Akram ya saki yace "hakan yayi oga dama fargabana ace nima zan aikata wani Abu da hanuna da sunan investigation amma tunda zaa ringa rushe mishi plan fine ni kuma zan ringa updating d'inku inda za'aje operation Dan yana fad'a mana so I have to get going Dan yanzu yace na tashi na tafi wanan dajin" Girgiza kai Ogan shi yayi game da jinjina k'ok'arin Akram akan aikinsa yace "Allah ya tsareka ya kare ka da karewarsa addu'ar mu na tare dakai" Murmushin jin dadi Akram yayi yace "Ameen oga ngd bari na kira Mahaifiyata itama tayi min addu'a" ahaka sukayi Sallama Akram ya kira mahaifiyar shi itama ta raka shi da addu'a Alhaji Bala kuwa yana gama waya da Akram ya fito daga motar ransa a b'ace yana tunanin bai San mai Akram ya d'auki kansa ba dama mai gida ke hana shi yaci

Chapter 6 of 13