kinji
yarda mu ka yi da shi."
Na isa gida cikin sauri domin an fara kiran sallar
magariba gab da zan shiga cikin gida ne kuma sai na ji
anyi kirana "Malama Ameerah da ga ina kuma haka.?"
Nai saurin juyowa dan inga mai kiran nawa na kalle shi
ya na ta faman murmushi na dawo da baya, na nufi in
da ya ke. Ko kun san kowane ne?"
Alhaji Aminu ne ya na jingine da motarsa
hanyansa harde cikin kirjinsa na dan rankwafa na ce
ina yini, ya ce lafiya lau Ameerah, ya ya karin karfin
jikin naki kuma.?" Na amsa da "Sauki." Ya ce
"Ameerah kinga rabona da ke tun a asibiti ko? to
wallahi tafiya ce ta kamani cikin gaggawa kuma ta
zama dole amma da badan haka ba da ba yadda za'ayi
in tafi ba tare na zo na kara dubaki ba dan shi kanshi
Alhaji Bashir bai san da tafiyar tawa ba, sai bayan na
yi tafiyar ne na buga masa waya na sanar da shi kiyi
hakuti Ameerah ba'a san raina hakan ta faru ba, wallahi
43
har na je na dawo kece a raina dan haka ma ina dawowa
gida ruwa kawai na watsa a jikina ina ta Allah - Allah
in zo in dubaki da fatan dai komai lafiya.?"
Na ce "Lafiya lau ni kuwa in ban da tunani babu
abin da na ke yi wa ni me ke damun Alhaji Aminu ne?
me ya shafe shi da rashin lafiya ta? me ya sa ya ke
fadamin wadannan naganganun alhali inaga ya san ni
ba wani amfani za su yi min ba....." ya katsemin
tur mina "Ameerah lafiya ina magana amma hankalinki
ba ya guna ya na wani waje.?" Na kalle shi na ce
"Lafiya kalau, kawai dai ina sauri ne saboda magariba
ta yi kada Antina ta ga dadewata." Ya ce "To yanzu sai
yaushe ke nan.?" na ce "Sai kuma mun kuma haduwa
ko?" ya yi murmushi "Ameerah ke nan to yanzu wa za
ki samo ya dauke miki kaya cikin mota dan ni dai
bazan barki ki dauka ba, ko da kuwa ki na da
cikakkiyar lafiya bare kuma ba ita ce da ke ba."
Na yi dariya na ce "To bari na shiga cikin gida
na samo yaran da zai iya dauka.?" Na juya na shiga
cikin gida abina. Hanyar da zan gudu na ke nema sai
kuma cikin sa'a ya ce haka na shiga cikin gida babu
wanda na yiwa magana na dai yiwa Anti sannu da gida
lokacin ta na gindin famfo ta na alwala ni kuwa sai
shigewa na yi bandaki dan yin tsarki na yi na dawo na
yi alwala.
Ina idar da sallar da ko tashi ban yi ba daga kan
sallayar wasu yara biyu suka shigo da kaya akan su
suna cewa a zo a sauke musu, na kalle su ina kokarin
tashi in nade daddumar da na yi sallar. Anti ta tawo da
carbi a ahannunta kai waya aiko ku da wannan kayan.?
Su ka ce "Wani ne, ya ce a ce da Ameerah ya tafi,
Amma zai dawo ko gobe ne.." anti ta kalle ni
44
"Ameerah da ma kun haďu da shi ne a wajan.?" Na yi
tsiru - tsuru da ni na ce "Eh, amma gaisawa kawai mu
ka yi da shi." dama na ce kunyi wani abıte da shi
abayan gaisawar ta kalli y an sannunku ko ta juya ta
shiga cikin daki jum kac in ta fito da naira hamsin
(N50) ta bawa yaran. "Ungo ku raba sannunkaf:"Su
ka karba suna murna an gode hajiya daya daga ci asu
ya fadi, "in zo in dinga yi mu ku aiki.?" Hajiya Anu ta
na dariya to ai mu muna da 'yan aiki sai dai ba laifi ba
ne don kai ma din zaka taimaka kuma ba zamu rasa
abin da za ka ringa yi ma na ba." cikin zumdi ya ce "To
na gode hajiya har sun fita sai suka dawo "Salamu
alaikum.?" Ni da Anti mu na zaune mu na kallon
labarai a (T.V) yaran Anti kuwa gaba dayansu duk sun
bai baye kayan da Alhaji Aminu ya kawo kowa ya dauki abin da ransa ya ke so ni kuwa ko kallan kayan
banri ba danni ba su ne a gabana ba, matsalar da ta ke
gabana tafi Karfin wannan, anti da su "Lafiya?" daya
yaran ya ce "Dama mantuwa mu ka yi ya bamu wannan
ya ce mu'kawowa Ameerah sai muka manta mu ka tafi da ita.?" Ya mika miņ ni kuwa ina zaune ko motsi na
kasa yi sai da Anti "Karbi mana kin bar shi ya na tsaye.?" Sannan na mika hannu na karba su kuma yaran
su ka fice waje.
Fitarsu ke da wuya waya ta dau ruri Anti ta tashi ta nufi gurin wayar da aka yi. tafiyar Anti daukar
wayar shi ya ba ni damar bude takaradar Alhaji Aminu.
AMEERA.
"Ya ya ki ke? Kin shanya ni daga bari ki turо
yaran da zai dauki kaya ki ka ki dawowa ko da ya ke
ban sani ba ko yaran ne baki samu ba, to amma kuma a
kalla ai kya fito ko sallama mu yi ko? To amma duk da
45
ti Saci ba ina an ina jiran wayarki yau da
dado ina da muhimmıniyar magana da ke kifa kirani
s wayar na gode maki."Ga lambar nan 034-5678989
AMINU USMAN.
Na yi tsaki gami da kudundune takardar na ce
Allah ya sauwake na yi masa waya.
Antina ta dawo ta danyi dariya "Kai Hajiya
Zainab ke nan ita komai sai na zabar mata. ta kalle ni
Ameerah Hajiya Zainab ce ita wai akace zancan kaya
ne za mu dinka shi ni da ita to ita sai dai ni in zabar
mana ita ba zata zaba ba.
Nayi murmushi na ce to Anti basai ki zaba din
ba.?" "Kai rabu da ita, ita ma wannan karan dai ta
zabar mana da karta muga irin na ta zaban." Na yi
daiya na ce "Gaskiya kuwa" (Hajiya Zainab Matar
Alhaji Aminu.) mu na shirin kwanci ya ne Anti ta dube
ni "Ameerah na ce?" na ce "Na'am ni kinje gidan Baba
Ali amma ni har yanzu ba ki ce da ni komai ba.?" mu
ka hada ido da Anti na ce da ita "Ni da ma yanzu na
ke shirin fada miki yadda mu ka yi da shi.?"
Bayan na gama fadawa Anti yadda mukayi
dashi sai nace to ni yanzu wana ke so a cikin
masoyana.?" na ce "Ni wallahi Anti ban da wanda na
ke so." duk cikinsu Ameerah.?" Na ce "Eh! Wallahi."
Anti ta yi shiru tsahon lokaci bata ce komai ba can ta
nisa Allah ya sauwake, amma kuma Ameerah ki na
sane da halin danginmu kuma kin riga kinsan ba ki da
wata mufita ko in ce wata kwakwkwarar hujja da za ta
taimaka miki tun da ba ki da wanda ki ke so ai dole a
hada ki da wanda suka ga dama. Don haka ina baki
shawara da ki yi hanzari ki fito da gwani tun wankin
hula bai kai ki dare ba kinji ko?" na daga kaina ina
46
share hawayen da ya ke fuskata "Wai kuwa ni da na yi
magana sai ki yi ta kuka to me kuka zai miki kuma.?"
"Na fada miki kuka ba abin da zai tsinana miki a
rayuwa kiringa yawaita addu'a ina fada maki kullum
haba Ameerah kuma na ga alamar ba abin da ki ka taba
yi walau addu'ar ko yawaita karatun alkur'ani dan na
ce da ke kiringa yi amma ban sani ba ko yawan kukan
zai taimake ki.?" Ta mike ta yi waje
Ina ma ban zo duniya ba wai ni Ameerah ce
cikin wannan hali lallai Sunusi a acuce ni ya gama da
rayuwa ta yaya ma zanyi na so shi ko dan irin halin da
ya jefani to ma wai me ya sa..... karar wayar sadarwa
ce ta katse ni daga tunanina da na ke kamar kar na
dauka to amma ko ba komai dai na huta da yawan
karar da ta cika min kunne nan na yi tsaki lokacin da na
dauki kan wayar an kara a kunnena "Hello" na ji daga
can daya bangaren an fada nima na amsa da cewa
"Hello, wa ke magana.?" das! Gabana ya yi mummunan
faduwar gaba lokacin da naji ance Alhaji Aminu ne ya
ce ranki ya dade gimbiyar mata ya gida yaya mulki
gimbiya na ce mulki kamar yaya ya ce yanzu mulki ki
ke ji tun da na ce a yimin waya Anti mata sauraran
wayar ki na ji shiru kuma na ga ba ki da halin ganina
shiya sa ni na bugo miki na ce a'a ba haka ba ne ina yin
aiki ne dai shi ne dalili ya ce Ameerah ya kira suna na
ya yi shiri ban amsa ki na jina Ameerah? Ya fada tare
da dan jim wani irin numfashi na ce eh cikin jin tsoron
abin da zai fada min ba abin na ajeye wayar ba Alhaji
Aminu ya fi karfin haka a waje na ke ba dai komai sai
dan darajar Alhaji Bashir.
Ya ce ki sani Ameerah batun yan zuba Allah ya
doran sanki kuma sanki da aure ni kan na riga na sani
47
cewar wannan san namu daga Allah ya ke Ameerah ina
so ki sani kuma ina so ki bani hadin kanki wallahi naji
Alhaji Bashir ya ce anyi miki miji to ni dai ban hakura
ba tun da dai ba aure aka daura ba ana daura aure a
warware bare kawo kudi kawai dan Allah Ameerah ki
bani hadın kan shi kawai na ke nema a wajanki kin ji
Ameerah, ba ki ce komai ba? na ce uhm to me zance.
Ya ce ban fahimci abin da ki ke nufi ba? Na ce to ai ni
a burina da ca za kai saboda ni dai ina ganin tafiyar mu
ne,..... cikin sauri ya ce me ki ke son ki ce da ni? Na ce
babu komai dan Allah ki kara abin daki ke yi niyar fada
min. na ce a'a shi ke nan ina san dai ka bani lokaci na
yi tunani akan wannan maganar. Ya ce "Ameerah meye
na tunani kuma? Na ce ai ka riga kasan komai yau na
bukatar tunani da shawara dai ko? Ya ce haka ne to
yanzu sai yaushe? nace inna gama tunanin zan nema ka
ya ce to shi ke nan sai dai dan Allah ki taimake ni kada
ki bari tunanin naki ya dauki lokacin dan Allah. Na ce
to kawai sai na ajiye wayar nan munti biyu ina ta
tunanin me zan yi na mafita ko kuwa na Alhaji Aminu.
A zahirin gaskiya dai Alhaji Aminu ba ya cikin
zuciya ta kwata - kwata dan ni ba ma na kawo shi
cikin masoya na a da ni ma dauke shi a matsayin uba
zance tun da dai abokin Alhaji Bashir ne Alhaji Bashiri
kuwa uba na dauke shi.
To amma ga mamakina kuma sai ga shi ya zo da
wani sabon lamari tabbas ya sha cewa da ni matarsa sai
dai ni alokacin ina yarinya, ya san na dauki abin kamar
wasa ne, to ashe shi malamin da gaske ya ke yi. Lallai
ina fadi a cikin raina kana da aiki.
**** **** ****
48
ntina ta kalleni a lina jifa ro ya na A
magana baki ce nun Nomai ba baile ki ba shi
amsar da zai fadwa wanda ya aiko shi. Na kalli yaran cikin kuuan rai va ce ina zuwa.? ilas dole
in fita tunda anti taua wajna mike cikin sanyin jiki
na yi cikin daki na dauki 1ayafina ina kokarin fita ne
Antina ta kira sunana Ameerah na juyo na ams a се kiyi taka tsan - tsan da samarin zamani ki kula ki ge
nuna kiyayyarki a fili ga mutum saboda yau muruı ya
zama ba a amince masa, wallahi indan ki ka hadu da
mugu ya na iya kai ki ya baro ki yi sannu - sannu.
Na ce to Anti ta ce ina so ki tuna da alkawarin
da ki ka yi min na cewar kin dena nunawa Sunusi kiyayya kin dai riga kuma kin san muhimmacin
Alkawari ta ce a dawo lafiya sai kin dawo. Ta shige cikin daki tabar ni anan.
Yaya zanyi dole na bi umarnin Antina ko don
ita mo dan in faranta ma ta rai.
Yana tsaye a gefe guda ya na kallon soran
kodan ya ga ta inda zan fito. Na daure na cije na yi
masa sallama ya amsa cikin matsanancin zumudi yace gimbiya Ameerah ya ya jiki cikin gajarerar magana "nace lafiya" na yi shiru ya ce Ameerah kin san wani abu kuwa? Na yi karfi halin cewar a'a ya ce wallahi Ameearah a kullum kwanan duniya kara sanki na ke yi nina rasa dalili a gaskiya Ameearah ni kaina ina cikin wani hali na daban lallai na yarda Ameerah da ake cewa kowa ya rasa masoyi ya yi kuka wannan haka ya ke
Wannan magana da Sunusi ya ke yi na san harga Allah ya na yi ne a tunanin sa ko zai shawo kaina
na so shi sai ni abin da bai sani ba shine ni wannan
maganganun da ya ke yi shi ya ke kara wutar kinsa a
49
cika ta dan ni k m kwanan duniya buriņa bai
wuce a ce yau Sunusi ya anja ma anarsa ba.
Na dago kai inaj masa nuni da ido na sake
gargadinsa dan yasan har yanzu ina nan akan bakana
na kinsa. To amma hakan bai yuwuba sakamakon wani
karkarfan kuka da ya zomin. Dan haka kawai sai na
juya na shiga cikin gida ina kuka.
Na yi sa'a na taki sa'a lokacin da na shiga ban
sami kowa ba saboda Antina tana cikin daki, da shiga ta
daki na afka kan gado na shiga raira kuka sai da na yi
kuka mai isata kana na mike na fara shiri ina tunani a
cikin raina wannan kukan ba in da zai kai ni tunani
daya da ke cikin zuciyata shi ne hanya daya da zanbi
kwakwkwara inga cewa na yanke wata alaka da ke
tsakaninmu da Sunusi tun bai sani hawan jini ba.
To ni Ameerah wane mataki ya dace in dauka
na jinjina maganar a cikin zuciya ta ke wani sha shi na
cikin zuciyata ya soma shawarta ta"Ameerah ki na da
muhimmiyar dama wadda in har kin bita za ki cimma
burinki na ganin karshan nacin Sunusi da kawo Karshan
duk wani rigingimu da ki ke fuskanta idan har kinbi
wannan shawarar itace damar ki ta karshe kiyi amfani
da damar da kika samu wajan Baba Ali ki amince da
Alhaji Aminu ko da ba za ki so hakan ba a cikin
zuciyarki Akalla dai ba na yi masa kiyayyar da nake
yiwa Sunusi" na nemi guri na zauna a gefen gado na sa
hannuna biyu na yi tagumi ina jin jina shawarar da
zuciyata ta bani anya kuwa wannan shawarar abar
dauka ce a gare ni? Na jinjina abin a cikin zuciyata eh
to tabbas wannan shawara idan har zan bi ta babu
mamaki akwai mafita a cikinta ko ba komai Alhaji
Aminu kamar uba ya ke a gare ni dan haka na yi imanin
50
ko da bayan auranmu ba zan sha wahala ba ta wajen shawo kan kansa ya fahimce ni ya sauwakemin auransa da yake kaina dan haka zanyi duba cikin wannan lamari.
**** **** ****
51
ashe gari ma Alhaji Aminu da yamma ya Wsake yo min waya ta neman amincewa ta to a
yauma dai ina dauka na sake ba shi hakuri
akan ya bar ni dai in kara yin tunani da kuma neman
shawarar Anti n. dai da haka na san na rabu da Alhaji
Aminu.
Allah sarki ni kaina ina mamakin kin wannan
...atsanancin son da Alhaji Aminu ya ke yi min, to
amma wata daban ko na cewa da Alhaji Aminu zan
nemi shawarar Anti na fadi ne kawai dan yabani lokaci
in nutsu in san abin yi amma na san tunkarar Anti da
wannan maganar kai bama zan iya ba kwata - kwata
saboda yadda Anti su ke da Hajiya Zainab ya cewa
Kawance sai dai amintaka to amma fa duk da haka ya
zama dole in san abin yi dan ba zan bari wannan damar
ta wuce ni ba.
a
Haka zalika washe gari ma Alhaji Aminu baiyi
Kasa a gwaiwa ba ya tako da kansa ya zo Allah ya rufa
siri a dai dai lokacin da ya aiko yaro kirana Anti tana
wanka dan haka ban bari ta ji ba na ja yaran zaure na
rada masu na ce ya je ya ce bana nan ya je ya dawo
wani lokacin.
52
KARSHEN ALEWA KASA.
ashe gari ne i laddare mune z a falo ni W
da Anti da sran yara mulon sabon
fim dir Indiya(K rz) falon yay. tsii kowa ya
shagala da kallon TV wayar sadarwar dake ajs gefen
kujerar da nake zaune ta dau ruri, anuna da yake
hankali na yana kan kalion da na keyi saı-sam bamma
jiba, har saida Anti ta juyo ta dubeni kana tace Amira a
taimaki Telpone yaza burari, nace to Anti kana na
rarumi wayar na kara a kunne na to amma fa duk da
haka hankatina yena ka kallon bani kaunar nzyi
Missing.
Hello na fad cikin kaguwa,
Tashin farko miryar Hajiya Zainab na tsinkaya daga ji
kasan tana cikin matsancín tashin hankali yadda ta kira
unan Antina a firgice Hajiya Sadiya kece.
Cak! Numfashina ya dauke haka zalika gabana
ya cigaba da wani matsanan cin bugu fat-fet nama kasa
budar baki in tanka mata, bansan kuma abinda ya haifar
da hakan ba illa iyaka dai ina da tabbacin a zuciyatz ko
menene bazai rasa nasaba da abinda ke tsakanina d
mijin ta ba.
A sanyaye na tashi na tashi abin sadar d
maganar na dauki wayar kana nace ma Anti kizo Hajiy
Zainab ke magana, Anti ta taso cikin hanzari ta amshı
kan wayar,
To ni dai a zuciyata babu nutsuwa na shiga cikin
tsarguwa dajin wannan wayar gaggawa daga Hajiya
Zainab take naji ina mai matukar san inji abinda wayar
ta kunsa, dan haka sai nayi dabara na sulale na fice
daga dakin na nufi falon Alhaji Bashir saboda in
53
saurars ia kan wayar dake can (saboda duk lambar daya
ce). Da daukata sautin da Anti ta tarar kana ta dan jima
kunnena sallama kana naji ta cigaba da fadin.......
wallahi bani da labari Hajiya Zainab daga daya
Gangaren ita kuma, Hajiya Zainab tana magana cikin da
dashashhiyäi muyar kuka...... Hajiya Sadiya kin sanni
da matsanan cin fushi kuma koma ba wannan ba ko
kece kika ji yadda Alhaji ke sambatu akan sanda ya
kewa Ameerah "gabana yai wani har" ya iya budar baki
yace in taimake shi ya cimma burin sa ya aureta har da
magiyar sa wallahi sai kin tausaya mini Hajiya Sadiya a
ganinki me yafi wannan bakin ciki? Duk irin
dawainiyar dana keyi wa Alhaji duk akan in kyautata
masa amma har yana neman zautuwa akan wata yarinya
'yar cikin mu dan abin kunya ta karashe maganar, ta
cikin kuka.
Anti tayi ajiyar zuciya kana tace kiyi hakuri
Hajiya Zainab nayi miki Alkawari in dai ina numfashi a
doran kasar nan bazan taba barin Ameerah ta auri mijin
ki ba zan dauki duk wani matakin dana ga zai dace dan
ganin na sasanta ta rabu dashi koda kuwa hakan na
nufin zamuyi uwar watse da ita, Hajiya Zainab ta
cigaba da magana cikin kuka A'a Sadiya ba'ayi haka ba
ki dai bita cikin lallashi....... Anti ta katse da fadin,
Hajiya tsakani na da Ameerah babu maganar lallashi
dan kuwa a yanzu na fuskanci Ameerah bata san mu
zauna lafiya da ita, idan banyi da gaske ba wata rana
zata fi karfi na dan haka ki barni da ita zanyi maganin
ta.
Iyakar abin dana iya tsayawa naji kenan bansan
lokacin da wani matsanancin jiri ya debeni ba ya watsar
dani a gefe INNALILLAHI
54
WA'INNAʼILALIHIRRAJI'UN, ita kadai nake ta
faman maimaitawa a zuciyata.
Shin wane irin mataki Anti zata dauka akaina?
Mu hadu a na biyu dan jin cikakkiyar amsar dukkan
abinda ya shigar mana duhun
TAKU HAJ. RABI NASIDI ABUBAKAR
Hajiyar Birni.
55
ALBISHIR.
Shin ko kina da labarin sananniyar marubiciyar nan
Hajiya Halima Yusuf (Ummi) Marubuciyar littafin
DAME ZANJI 1&
LOK ACI NE
SIRFIN ZUC.
NIKO ITA
BUR 1&2
A yanzu haka tana shirin fito muku da wani
kayataccen littafi wanda yake kunshe da wata iri
mirdaddiyar rigima wanda babu irin shi ! damuwa
wadda babu kamarta, matsala wadda bata da mafita sai
a cikin littafin ME NE NE WANNAN ?.
NA
Hajiya Halima Yusuf (Ummi)
Don miss it.
56
ALBISHIRIN KU MARUBUTA
KAMFANIN
MASHIPUBLISHIR
Shha fuaceen kamfanin buga fistattals MSUIPUBLISHERS Na sanar da daukaein marubutan suke a buga ma atattafan hankali da dadin rai, babu maganar jeka ka dawo su cikin kw anciyar kankanizamu aikinka kam malam a
cikin farasbi mar sa 1
kwarewarmu akan aikitafi Turaner gaban da
buga
na Larabci littali
Hausa da sauransu kadai. Muna buga littatta fan
tallatawa Muna kuma
marubuta sada marubuta
littattafansu dı 'yan kasuwa. Bamu tsäya nan ha munyi fice wajen kazalika 'yan Fim ma bama atsu abaya ba aikin
Wai mune wai tallata waikam musu
fanin fina
finansu MASHI cikin baryrkasa Mujallu da littattatar, mastallah shike da riba. Daurin Aure, a gwiwa ha wajen buga muku katunan Memo, Sticker, Kalanda makamantansu har da riga mat hote ke fastocin 'yan siyasa da
Kwarewa gogewa da sanin makamar aiki shinetakénmu. Don karin bayani sai ku tuntubemu a ofishinmu dake:- No. 331 Daneji Qtrs. Sabon Titin m andaw ari, Kusa da Sahad Store, Kano. Ko akwatun gidan waya P.O.Box 11842 Kano N
ZAMAM CKИВА
1-2
Email-mashi-@yahoo.com
Tel. 064- 331928
ig cria
M
ANTY HAFSAT BELLO
KOMAI DADE VAR
L
Haj Halima Tugnl (Unimy)
Cons
Ameerah
ANTY HATEAT DATO RABI NASIDI ABUBAKAR
Maria
Mailidde
Eliely Uman
2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels