don ku rabu lafiya kin san....
Haba Bebi na fada miki bana sonsa bana
Kaunarsa inkuwa na aureshi to ina mai tabbatar miki da
cewa mutuwa zanyi don bakin ciki, tai dariya ta ce
yanzu Ameerah bakin cikin wani yana iya kashkei?
Haushi gami da takaici suka cikan zuciya nace Bebi na
gode ai dole kiyimin dariya tunda ke kina zaune gidan
mijinki hankali kwance, haba Ameeraha inariga nasan
duk abin da kike ciki na kuma gamsu dake sosai ta taso
daga inda take ta dawo kusa dani ta dafa kafada ta ta ce
yanzu abin da zamu fara yi shine muje wajen Kaka
Aisha mu baiyana mata komai da komai mu fahimtar da
ita duk yadda lamarin yake idon idan munga ta fahimci
abin da muke nufi sai mu roketa da taje wajen
Alaramma tai mai bayani kamar yadda mukayi mata,
idan kuma muka ga taki fahimta to sai muje da kanmu
muyi masa bayani, nace uhn! Bebi kamar ba yau muke
tare dake ba kin manta da halin zuriyarmu kuma kinsan
nasha gaya miki irin tsatstsauran ra ayinsu sannan kice
wai muje gidan Alaramma ai kinsan ma kawai cewa
zaiyi suzo jibi a daura auren kowama ya huta, Bebi ta
ce to yanzu kamata ya yi mutashi muje wajan shi
Sunusin mu lallasheshi ya janye maganar Auren ko ya
kika gani? Nayi shiru nasan ku yarda kaina tunhanin
sannannn na dago nace da bebi kai bana jin Sunusi duk
lallashin da zamuyi masa zai janye wannan abune mai
wahalar gaske, ke dai baki sani ba tunda ance sai an
gwada akan sannan na kawarai kuma a rashin tayi akan
bar araha, dan haka ba zakakiyi saurin yanke hukunci
ba zuwa zamuyi mu lallame shi Allah Annabi in kukai
haka kila yaji tausayin mu ya janye, to shikenan Bebi
si ki bari zuwa jibi ki same ni a gida kinga in na rakoki
sai mu wuce wurin sa muji wai nar da yake toya wa
tunda in ba haka ba futa yanzu a bune mai wahala, to ai
shike nan Ameerah Allah ya kaimu.
******** *********
A washegari ne kuma ina tsakar gida ina yiwa
Anti tsintar shinkafa ita Anti tana daki sabili da a yau
ma Kaka Aishat tazo suna can suna tattaunawa nasan
dai a kaina ne, daga baya ne Anti ta kira ni nayi sallama
nashi ga cikin daki, ganin Anti ta kalleni...... cikin
barara ta ce bani nake kiran ki ba ga mai kiran ki
nan.......Kaka Aishat ta ce Ameerah me yasa kike son
ki ta dawa mutane hankali, ki sani ko ni kaine ba'asan
raina za'ayi miki auren nan ba, tunda dai ba kya so to
amma ya muka iya, ai sai dai hakuri in Allah ya yadda
ba za ki bekin ciki ba, na sa kuka ni wallahi ba na sonsa
ni dai ku hada ni da kowaye amma ba Sunusi ba, don
ba na sonsa ko kadan. To Ameerah wallahi da kaina
naje wajen Alaramma amma banyi nasara ba, ba kiji
irin fadan da ya yimin ba, wai shi ba za'a mai da shì
karamin mutun ba, tun da ba'a son Ameeral ta, ba ta
zo duniya ba a kewa Yarinya g ka gama
borenta daga baya a zauna lafiya lau cikin kwanciyar
hankali.
"Ni dai na bashi hakuri, na ta shi na taho, dan
hakak ni dai abinda zanjaddada miki bai wuce ki dai yi
hakuri ba." Ni kam ban da kuka babu abin dana ke yi,
ni kaina bansan a kan me na ke kukan ba, kukan bakin
cikina ko na takaici ko kuwa na mamaki abin da Sunusi
ya yi min ne.
cikin wannan haline Kanin Antina, da muke kira
Kewu Aminu ya shigo ya iske mu a haka nan dai nan ya
shiga tambayar su... wai meye ta ke kuka.?" ya
tambaye su. Kaka Aishat ta ce "A kan dai maganar nan
ta aurenta ne da wai ba ta son mijin ka ganta nan
rarrashin duniyar nan babu wanda ban yi ba amma ta ki
hakura."ya ce "To kuma me nene na rarrashinta ba sai
ku kyale ta tayi ta yi ba, in ta gaji za ta dai na......
Na katse su da fadin "Vallahi Kawu tun farko
na gaya mu su ni ba na son shi kuma duk tsanani ba zan
aure shi ba." Ban san lokacin da ya dira a gabana sai
ganinsa kawai na yi har inda na ke ta ke ya fitar da
hannu ya shararan mari, ya kuma cigaba da fadin "dan
ubanki sa'o inki ne ki ke fada musu wannan maganar
da ba ta dace ba, ta shi ki fita ko kiji ba dadi.?" Na
mike ina kuka na fita tsakar gida na zauna.
A washe gari ne bayan mun shirya ni da Bebi
sai muka nufi ioda muke da tabbacin zamu samu Sunusi
na nunawa Bebi shagon nasa kinga shagon nan ni dai
anan na san shi, domin anan muka taba haduwa da shi,
to ni ban sani ba kó nanne ko kuma zuwa ya ke yi
cho." Ai kuma a kulle ya ke ba mamaki ya tafi
masallaci tun da yau Juma'a an fara tafiya masallaci.?"
18
Na yi shiru dan ni ina ganin kamar ita ke nan
damar da nake da ita kuma ta wuce ni shi ke nan yanzu
ta wuce ni, yanzu auran dole za'a yi min zan auri
wanda ko a mafarki ban san inganshi balle ace yau shi
ne mijina.
Bebi ta dafa kafadata "Haba Ameerah ke fa
halin ki ke nan komai na ki sai kinyi kuka kullum cikin
kuka ko gajiya ba kyayi, kiyi hakuri Insha Allah komai
zai zo da saukI." Na yi dan murmushi lokacin dana
share hawayen da ya batan fuska nace "Ba komai Bebi
na gode da kulawarki a gare ni zo mu tafi.?"
"Lafiya me kuke nema.?" Aka tambaye mu.
Gaba daya muka juyo muka kalle shi wani dan
kaukauran saurayi ne wanda zan iya kiransa wankan
tarwada ya kara so kusa da mu ya na fadin """"yan mata
lafiya ne kuke tsaye anan wajan.?" Na yi saurin
waigowa da dan takaitacen murmushi nace "A a ba
komai dama munzo neman wani ne wai shi Sunusi to
kuma sai muka tarar da shagon a kulle." Ya yi dariya ya
ce "Af ku na nufin ku ce kun zo wajan Sunusi ne.?"
"Ina fatan dai lafiya.?" Cikin murmushi Bebi ta ce
"Lah! ba komai wallahi hala kai abokinsa ne.?" da sauri
ya gyada kai yace "Ah! ai in ki kace haka kin takaita
don kwa ni ina ganin na zarce aboki sai dai amini." Na
kalli Bebi, Bebi ta kalle ni to amma tun kafin mu yi
magana sai ya ci gaba da fadin "Idan wani sako ku ke
da shi kwa iya gaya min, in ya so in ya dawo sai na
fada masa domin rabona da shi, na dan kau da kai na ce
"To ba komai in ya dawo ace Amira ce ta zo nemansa
ba ta same shi ba.?" ya ce "To shi ke nan insha Allahu
da ya dawo zan sanar masa." Shi ke nan mun gode
muka fada kusan a jere ni da Bebi. **** ****
19
Bayan saukowa daga masallaci ne aka aiko ana
kirana a waje. Na ce "Je ka ka ce ba ta nan." Kai tsaye
Antina ta kalle ni "Ki je mana ki ga wanda ya ke
kiranki.?" na mike na fita. Na figi mayafi ina kunkuni
ba tare da raina ya so ba na taddashi yana tsaye kusa da
babur din shi ya na ta faman murmushi ya ce "Malama
Ameerah ya gari, ya kuma kuka zo gida dazu, na zo na
sami sakon ki a wajen abokina Muftahu, ina fatan
lafiya.?" Nayi kokarin sakin fuskata tare da kago
murmushin dole na ce "Lafiya lau illa dai kawai na je
ne akan wata alfarma da na ke nema.?"
"A wajena!?" ya fada yana mai nuna
mamakinsa yace "kwarai kuwa."ya ce "To ta me.?" Na
ce "Tabbas nasan ka na so na, so sai kuma na riga na
fada maka cewar ba zanyi aure ba to amma duk dana
fada maka hakan baka hakura ba har ka dauki kudinka
ka aika da shi to duk da hakan ba taci ba na san so na ne
ya jawo, to sai dai ni a waje na sai aka sami akasi hakan
ba zan iya aurarka ba, hakan ne ya sa tun farko na fada
maka gaskiya to amma kai ka ki ka gane me ya dace ka
yi don haka alfarma da na ke nema ita ce ka yiwa Allah
da Manzansa ka Hakurar min wannan masifar ka janye
abin daka ke nufi a kaina, wallahi na shiga wani hali na
daban dan Allah ka tausaya min kayi hakuri kai ka dai
ne wanda zan kaiwa kuka na ka share min hawayena
har ga Allah ni ba na son wannan auran.?" ina kuka ina
rokonsa.
Munfi minti uku ba wanda ya yi magana bayan
na gama maganata ni kuwa ban da kuka ba abin dana ke
yi ina cewa "Don Allah ka tausaya min ka taimaka
min.?"
20
Ya katse ni yace "Ya isa Ameerah share
hawayen ki ki kuma saurareni ni kaina ina tausayin
kaina ina cewa ina ma Ubanginji bai kaddaro haduwar
mu ba ina bakin ciki idan na tuna da wai Ameerah da
na ke so na ke kaunar ta fiye da kaina na ke kuma kasa
barci saboda tunaninta ita ce bata so na, take wasu
siraran hawaye suka soma zirara daga idanun shi ya
kuma cigaba da magana cikin raunanniyar murya ki yi
hakuri Ameerah na yi imani har abada ba zan daina son
ki ba, ki yi hakuri ki dauki wannan a'l'amari а
matsayin kaddara garemu kuma ni a kullum cikin
yakinin wata rana za ki so ni, ki tai mana addu'a' Allah
ya zabar mana abinda ya fi alkhairi a garemu cikin kuka
ya ce "Yaya za'ayi kace wata rana zan so ka alhali ni na
san ba zan ta ba son ka ba har iyakar rayuwata."ya ce
"Zan so ki?" Ya yi murmushi shi ke nan Ameerah ki
ta ya ni addu'a ni ma Allah ya cire son ki daga cikin
zuciyata shi ko.?" Na daga kai alamar I, ya mike tsaye
daga.kan babur din to yanzu sai yaushe Ameerah.?"
Nace shi ke nan ina jiranka in ka ji ka daina son nawa
ka aiko a karôl kudinka ni ban ce ka kuma zuwa
wajena ba na juya na shiga cikin gida na barshi anan.
Ina shiga gida na wuce Anti a tsakar gida Can ko
kalli inda take ba kai tseye daki na wuce da sniga ta na
fada kan gado na bude wani sabon babin kukan.
Ban ji shigowar Anti ba, sai kawai ji na yi tai
kiran sunanana sanyaye, kunan da ke cikin zuciya ta ta
hanani in iya amsa wa Anti, kiranta na ci gaba dai da
gunjin kukana.
Anti ba ta hakura ba sai ta sake kiran akaro na
biyu to wannan karan ma dai ban amsa ba kukan dai na
ke yi lalle Ameerah amma kin bani mamaki wato a yau
21
kiyi wayon da zaki nunan ba ni na haife ki ba ko.?"
Kin nunan iya kata tunda har nayi kiranki ban samu ko
amsawa ba, saboda ba ni na haifeki ba, to amma
Ameerah da kinyi tunani da baki yimin haka ba, ko ba
komai na rike ki amana. Ta yi waje fuu cikin fushi.
"Wa iyazu billahi ban san lokacin da na
hanzarta tashi zaune ba, duk da matsanancin tashin
hankalin da ke tattare da zuciyata sai na jisu ba komai
ba ne akan na yanzu wato abin da anti ta fada game da
ni ko kusa ko alama abin ba haka ya ke ba, yaushe
zanyi wani yunkuri dan in gwadawa Anti iyakar ta,
cewa ni ba ita ta hateni ba duk da irin halaccin da ta
nuna min.?"
nti
******* ***** *******
Sadiya shine cikakken sunanta kuma
kanwace a wajan mahafiya ta uwarsu daya
ubansu daya tun lokacin da auran mahaifiyata
ya w a lokacir ina yar shekara shida kuma dama
yawancir hutuna nafi yin sa ne a gidan Anti don haka
matsananciyar shakuwa ta shiga tsakaninmu sai ya
zama d dai lokaci da auran mahafiyata ya mutu ya zo
dai da da lokacin hutuninu ina gidan Anti don haka
iokacin ban sake komawa gida ba hakan ya samo
asaline daga wajan mijin Anti saboda shima yana
matsayin abba a wajena, ta bangaren kaka Aisha don
haka ta tsaye szi na zarce da zama gidan Anti na taso
cikin matukar kulawa da samun cikakkiyar tarbiyya
saboda macece mai hakuri da zumuci ba ta bambanta
tsakanimu da 'ya'yanta haka zalika shi ma mijinta
mutunne mai kirki ya na bani kulawa sosai.... Jikina a
sanyaye na tashi na nufi wajan Anti na iske ta zaune a
tsakar gida tana zaune kan kujera 'yar tsugune ta yi
22
tagumi da hannayenta biyu fuskarta dauke da
matsanancin bacin rai. Na tsuguna a gabanta cikin
muryar kuka na kira sunanta "Anti na zo ne don na ba
ki hakuri saboda yadda na ga ranki ya baci kuma
hankalina yai mummunan ta shi saboda jin lafazin
bakinki, wallahi Anti ina so ki sani na rike ki uwane
tamkar yadda ki ka rikeni 'ya a gare ki kuma harga
Allah ba ni da niyyar yin wani abu don janyo bacin rai
a gare ki ballantana nayi abin da zai zama na nuna ki ba
ke ki ka haife ni ba. To amma Anti game da maganar
Sunusi a yadda na ke ji a zuciyata da na aure shi gara
rayuwata gaba daya na tsane shi na ki jininsa don haka
bana kaunar ganinsh Anti.... Sannan sai kuka ya ci
karfina cikin karaji kukan naci gaba da fadin "Don
Allah Anti ki taimake ni don bana san Sunusi ba zan
iya auran Sunusi ba, Anti duk da ni 'yar nan Anti, babu
mai iya sharemin hawaye na sai ke don haka ki
taimake ni Anti ki goyi baya na akan a kyale ni da
maganar Sunusi.?"
Anti ta dago kai cikin matsanancin tausayi ta
riko hannayena ga mamakina sai naga hawaye ya soma
zuba daga idanuwata cikin raunananniyar murya ta
soma fadin "Tun farko Ameerah da da yadda zanyi da
nayi don ganin tsatstsauran ra'ayin Alaramma bazan
iya dosar wata mai kama da wannan ba to amma ni
shawarata mu dukufa da du'a i ina ganin ita ce hanyar
samun mafita a garemu.?"
****
***** ****
komai ya rincaßemin ga shi duk wanda na je
wajansa akan ya taimakamin kowa sai yace da ni in yi
hakuri amma babu mai iya cewa Alaramma mai da
kudin nan kowa na tsoronsa, wani baban abu da ya fi
2
bani mamaki dai dai da mahaifina ya san halin da na
ke ciki amma ya nu na halin ko in kula saboda tsoron
Alaramma
ko da ya ke su duk a hangensu wannan wata
sabuwar fitinace da na zo da ita saboda yadda aka saba
aurar da yarinya ba sai lalle ta san mijinba, ballantana
ayi maganar so don haka duk inda na shiga babu mai
goyan bayana.
To a yauma Juma'ace da tsakar rana na dirar
ma Kaka Aisha da kukana, kaka Aisha ta dubeni a
galabaice cikin gajiyawa da wannan al'amari ta ce
"Tabdijan nan ke yanzu da abaki hakura ba.?" "Lallai
kina da aiki a gabanki to waima me ye da Sunusin ina
ce yaran yana da dan abin hannunsa wanda zai iya rike
mace ba shi da mugun hali me ake nema da mutum
haka kawai duk kin bi kun kwarzabi kanki to Allah ya
kyauta.?"
Na gaji kirki kuma zuwa ki tunkareni da
wannan maganar kinji na fada miki kuka ne kije kiyi ta
yi har ruwan idonki ya kare.?" Nace "Ni yanzu....." na
kasa ci gaba da maganar saboda kuka ya ci karfina.
Kaka Aisha ta katse ni ke bari na fada miki
gaskiya aure dai babu fashi in dai ba wani ikon Allah
ba, don haka in zaki hakura ki hakura in kuma kin kI
kije ki tayi.?"
**** **** ****
A daran ranar ni dai dan tsabar nace da rashin
zuciya Sunusi ya sa ke zuwa ya aiko kirana cikin tsawa
9
na kori yaran nace ya tafi ya ce na ki na zo.'
Nan dai Anti da ke cikin daki ta fito tana fadin
tashi kije mana, ba na son irin haka Ameerah.
24
Nai shiru kai na a sunkuye ban ko motsaba
ballanta in tanka mata, cikin tsuke fuska Anti ta ce
yanzu Ameerahn ina yimiki magana ki na jina ko.?"
Saboda kin mai dani 'yar iska, shi ne ki ka yi min shiru
to walahi ba dai a gidan nan ba, don ba zaki jawo min
tashin hankali ba. Don ba zai yiwu ace ni na ke zuga ki ba haka kawai.
"Anti me nayi miki kuma.?" Ta ce tun yaushe
nace da ke ki tashi ki je kiran da Sunusi ya ke yi miki
amma kina jina ki ka yi kamar ba ki ji ni ba. Na mike cikin saurin naja mayafina akan kaure na yafa na fita.
Yana soro ya na jirana na fito ya kalle niya ce
sannu Ameerah duk na ji abin da ya faru ina jida kunne
na sai dai ina mai baki hakurin da ki je ki daure ki bani hadin kai micimma burinmu ko in ce na cimma burina,
ni kuma na yi miki alkawarin ba za ki tabayin dana sanin aure na ba tun da.... Na katse masa hanzari na се
kai dakata min me ka ke san ka ce da ni, meye ya ba ka yi min ba? Haka ake son.? Ka ce dama kana sona ka kuma jefani cikin masifa da tashin hankali ka hadani da iyayena akar ka iyayena suna fushi dani ko kana nufin
ka ce da ni duk a cikin da ka ke yimin ya ke.? Na girgiza kai cikin bacin rai na ce to bari na fada maka wallahi ko a mafarki ba zan aure ka ba, in kuwa ka
ganni a cikin gidanka to tabbatar da cewa gawata ce aka
kai. Ka ji na fada maka ya dan yt shiru kana ya share
gumin daya bata masa fuska. ya ce to Ameerah naji abin da kika če amma don ki taimakamin da ruwan
sha. Kanar kar naje to amma daga baya sai na canza
shawara na yi tsaki sannan na juya na shiga cikin gida.
25
Na ce Anti wai ruwa ya ke san zai sha. ta de to
dauki wannan (Jug) din ki dibar masa mai sanyi cikin
firji na dauki kofin na debi ruwa na fita.
Ban yi wata wata ba sai kawai na kwara masa а
jikinsa gaba dayan ruwan ya sheke tun da ga fuskarsa
har jikinsa. Cikin gaggawa ya dago da kansa ya dubeni
ya dubi jikinsa ya yi murmushi ya ce Ameerah ke nan
wannan kuma menene fa'idarsa.? Na kalle shi çikin
harara na ce ai kafi kowa sanin fa'idarsa. Ya ciro
hankici cikin aljihunsa ya fito da shi ya goge fuskarsa
ya bude but din babur din ya ciro wata leda sannan ya
mifonin ya re ungo wannan na kalle shi na kalli ledar
in yi me da ita.?
Ya ce siyo miki na yi yanzun nan da zan taho
nan sai naji ina jin yunwa to shine na shiga kanti na
siyo biskit din to dan naci sai na ji dadin sa shi ne na
a ya kemata ke ma in sayo miki.
FHuushi da takaici su ka kamani na mika hannu
na karba sai na farke ledar biskit din a kasa duk na
tattaka sıka zama gari sannan na tsuguna na de bi garin
biskit din na watsa masa nace me zan yi da abin ka ance
da kai ní ma wadayayyyiya ce irin ka.? ya ce lokacin
ds ye ke kade biskits din dana zuba masa Ameerah ke
nan wallahi ki na bani sha'awa kuma komai ki ka yi
burgeni ki ke yi don haka na ke kara son ki ko banza
dai na san na sanu matar da ba zata bari a raina ta ba,
kin san wani abu kuwa? Na juya na shiga cikin gida yai
ta fi vman kirana amma ko da wasa ban wai goba.
*营 ******
A gaskiya na shiga wani hali da ban taba
naninan shige shi ba a rayuwata sabili da haka ni
'yar gata ce awni io amma a yanzu a sanadiyar
26
Sunusi ta yi watsi da ni ko abu ne za a ba ni in mikon
kafin in kai gare ta sai ta jehomin haka zalika ko mai
nayi sai harara ni ba abin in ce zan koma hannun
mahaifiya ta ba, to ma in na tafi can ma itama ba wai
abu da yimin tunda ko hirama ba ta yadda ta yi da ni
ballantana ban taba yin ko da wata 'yar doguwar
magana da ita ba sabili da wai ni ('YAR FARI CE) dan
haka babu ruwanta da ni, hakanne ya satun farkon fara
wannannin rikici ba ta taba sanya bakinta ba.
A yanzu haka ya zamo a cikin gida ba ni da
abokin hira tsakanina da kowa sai kyara da tsangwama,
ba ni da abinyi da ya fice kuka haka zalika a makaranta
wani lokacin nakan ce to waini AMEERAH DA MЕ
ZAN JI.
**** **** ****
A cikin wannan hali ne ranar wata Asabar ina
kwance ina fama da wani irin zazzafan zazzabi da
ciwon kai, ga shi duk ilahirin jikina bani jin dadinsa,
haka zalika ga kunan da zuciyata ke yi wanda ya sanya
a dalilin lamarinmu da Sunusi da ke damuna. Kawata
Bebi ta shigo dakin da nake kwance ina rawar dari
dama a yanzu komai na wa ya koma can dan tunina
daina shiga cikin mutane haka nan kuma na dena
karanta duk wani Littafin da ya kunshi soyayya dan ni
ina ganin hakan shi ne ya fi dacewa da ni tun da ni ba
masoyi ne da ni ba kuma wama zan yiwa so da har zan
koya.? Bebi ta daga labule tare da kunna fitilar dakin
haske ya gauraye dikin tai kiran sunana Ameerah!
Ameerah!! Na amsa da kyar na amsa lafiya ki ke cikin
kuryar daki cikin zafin nan ko zafin ma ba kya ji na ce
Bebi shigo na yi karfin hali na ce zauna ina tarawar
dari hakorana suna haduwa da junansu nace lafiya lau
27
daga ina ki ke haka? Tace a'a ina fa lafiya me ke
damunki ne cikin kankanin lokaci lallai to yanzu wai
ina tambayarki me ya ke damunki.?
Na ce zazzzabi ne kawai ya ke damuna ta kai
hannunta wuyana dan taji yanayin jikina kai kai kai
haka jikin ya yi zafi to yanzu kinsha magani nace ban
shaba tace amma ki ke anan yanzu haka ma baki
fadawa Anti cewar ba ki da lafiya ba ko nayi murmushi
lokacin da na ke kokarin kwanciya nace wa ki ke san
na je na fadawa ni da ba ni da gata a yanzu? Ni yanzu
ma addu'ar da na ke yi itace Allah yasa sanadiyyar
mutuwa ta ce ta zo inna mutu ai kowa ya huta ko? ni in
huta suma su huta da yawan yin fadan naki bin abin da
su ke so. Bebi ta kalle ni cike da matsananciyar
damuwa hade da tausayina ta ce haba Ameeraha komai
hakuri ake yi da shi ki dinga yin hakuri da lamarin
duniyar kar kije ki jefa kanki cikin wata babbar cuta
kuma ki je ki illata kan ki abanża da wofi nace to yanzu
Bebi ya ya ki ka san na yi da kaina ne? wai kuwa Bebi
kin san kiyayya kuwa? A gaskiya da kin şani na
tabbata da kin tausayawa rayuwata. A gaskiya kiyayya
bala'I ce na fashe da kuka ina ta jujjjuya kaina nan da
nan na ji kirjina ya yi bala'in zafi zuciyata kamar zata
fito dan matsanacin zafi da na ke ji daga gare ta. Na
dafe kirjina da hannuna ina cewa waiyo Allah Bebi
kirjina zai tsage ki taimakamin ki danne shi can naji ina
nunfashi sama - sama ban ankaraba kuma sai wani
bakin abu ya sauko ya rufen idona ban san yadda akayi
ba kuma sai ganina nayi akan gadon asibiti an samun
karin ruwa, a hannuna na dama wata nas ce ke tsaye
akaina tana rike da allura da sirinji a hannunta lokaci da
ta ke kokarin zuko ruwan a sirinji. Sannu Ameerah ya
-28
ya jikin naki? Na juyo la kaina jin da rayi maganar
Antina ce a tsaye fuskarta cike da matsanancin tasuyina
na ce da sauki Anti to Allsh ya kara sauki. Bebi yaushe
ki ka zo tace ai tunda aka kawo ki muna nan dukkan
muna nan tun yaushe na anan din? tace n jiya da
hantsi muka kawo ki na ce na gode Bebi.
Yau kwana na uku a asibiti amma iďma ka
ganni sai ka zac na shekara a kwance duk na fita aga
hankalina, na yi jeme - jeme na yi baki ba yi mesifa
ramewa ramata ita ce zata fara baka mamaki in dai ka
ganni in har ka sanni to kai da kanka zaka iya cewa ba
ni ba ce Amegra da ka sari ada 'yar kwalliya. Zuwan
da mijin Antina ya ke yi ko kuma na сe (БABA). Idan
ay tashi zuwa ya na zuwa da mutane abokansa to
rannan sunzo duba ni ne.
Akoda yaushe su Antina su na asibiti wajena su
ke wuni ya yin da Kaka Aisha ce ta ke jinyartawa. Yau ma kamar kullum ya zo shi da abokinsa
suka shigo gaisa da kaka Aisha ya ya jikin nace jiki da alhamdu lillahi, ya ce Allah'ya kara sauki amin a
lokaeinne kaka Aisha ta dauki kwanu kan da ака се
abinci dasu ta je waje. Sannu Ameerah ya jikinnaki in ji mijin Anti ko in ce (BABA) na ce da saukI, Baba da yake da ma haka na ke cea da shi. Abokinnsa ma ya ce Allah ya sauwake na ce amin na gode.
Ya ce amma Alhaji Bashir Ameerah ta rame da yawa. (Sunan mijin Antina ke nan) ya ce wallahi don ni wannannnn har tscro ya ke ba ni, Ameerah ta ce na waiga na kalli mai cewa na rame da yawa sai yanzu na gane abokin Alhaji Bashir ne da ma ya na zuwa gidan
to dag abaya kiuma sai naji Anti ta ce ya yi tafiya zuwa Lonhdon shi ne dalilin dana daina ganinsa, kuma na
29
shi kwatá kwata sannan