yaci gaba da
.gce "Alhaji sr ashe Allah ne ya taimaka
ina cw ashe ni matar tawa tana nan ba lafiya."? Cikin
gaggawa na juyo da kaina na kalle shi ido da ido Alahji
Bashir ya yi murmushi ya ce kai Alhaji Aminu ba ka da
dama ai wannan da ka ke yi na da ne, don yanzu
Ameerah ta kusa shiga dakinta ya ce don Allah ka ba ri
Alhaji Bashir ya ce Insha Allahu kai ni zo mutafi ka ji
Alhaji Bashiri ya kama hannunsa suka yi waje ya
waigo ya ce to Ameerak sai da safe Allah ya Kara saukI
na ce amin, Alhaji Aminu har ya fita ya dawo ya ciro
kudI dami guda ya ajeye min a kusa da ni to Ameerah
sai da safe Allah ya-baki lafiya, kafin a sallame ki-in
na ga da hali zan kara zuwa dubaki na ce to na gode.
Alhaji Aminu ya dade ya na cewa ya na sona
tu ina yarinya to ni sai na dauka wasa ne abin na sa
cea na ke irin wasan nan ne na tsokana ya ke yi min.
Bayan ya tafi London ni na manta da shi kwata - kwata
don na yi a kalla shekara ko fiye da haka.
To sai kuma ga shi yanzu ya dawo kuma har
zuwa yanzu dai bai bar kirana da matarsa ba, har yanzu
bai bar fadin irin maganganun da ya saba yi min ba, to
sai dai na yau ya sha banban da na waccan karan, dan
abin da na gani a idon shi a yau babu batun wasa cikin
abin da yake fada.... tunanina ya katse a dai - dai
lokacin da na ji Alhaji Bashir na fadin ai an kusa
aurar da itama, nan gaba bai fi yan watanni ba.
a
Ta ke na lura jikinsa ya yi sanyi da jin wannan
magana, so sai ma kuwa. To in kuwa har abin da na ke
zato a zuciyata ya zamanto gaskiya, to lallai kuwa zan
kuma fuskartar wata sabuwar matsalar dan kuwa ko da
wasa zuciyata na hakikancemin Alhaji Aminu ba tsarar
30
aurena ba ne kuma ma abune wanda yiwuwar sa ke
tattare da gagarumar matsala, hasalima ni bana jin zan
iyason shi a zuciyata, sai dai kuma shi ba na jin kinsa a
cikin zuciyata, ma'ana ba kamar Sunusi ba, wannan
kuwa ba wani bakon abin bane a waje na, dan kuwa a
tun tasowata ba na jin an tabayin saurayin da na ji ya
kwanta min a zuciyata, to ga shi shi kuma ya na fadin
wai ni matarsa kun ga fa wai har ma na zama matar
tashi ma, na yi tsaki a zuciyata nace Allah ya kyauta.
Ban ji shigowar Kaka Aishat ba sai kawai ji na
yi tana cewa ke kuma lafiya ki ke yin tsaki ke kadai.?
Da sauri na dago kai na kallleta na ce lafiya sumul to
meye na yin tsakin ta sake tambaya ta na ce ni na ce
babu komai daga haka sai na juya na rufe idona.
Kamar baccin zanyi ta bi ni da kallo cikin
shakar abin da na fada mata.
Ni kam tuni na yi lamo na yi hakan ne don kada
ta dameni da yawan tambaya nasan halin Kakan Aisha
da bin kwakwkwafi.
**** **** ****
a washe gari ne da misalin karfe dayan rana aka
kwankwasa kofar dakin da na ke kwance kaka Aisha ce
ta umarci mai bugun ya shigo Bebi ta turo ta shigo tare
da yin sallam asalamu alaikun na yi murmushin jin
dadin ganinta na ce sannu da zuwa Bebi ta ce Ameerah
ya ya jikin naki da saukl Bebi ya hanya kin sha zafin
rana maimakon ki bari si ran ata yi sanyi kya zo.? Bebi
ta kalle ni ta ce tun safe na yi niyyar zuwa to kuma sai
na zauna na yi dan wanke wanke shi ya sa wallahi ya
dade ma sai yanzu na samu fitowa. Kaka Aisha ce kin
kyauta ke dai sannu ki da kokari kinji 'yar nan tayi
murmushi ta ce kai ai ba komai abin da ya shafi
31
Ameerah ayya shafe ni daga nan mukai cigaba da hira
muna nan zaune muna ta hira hira ta yi dadl in ka ganni
ba ka ce mara lafiya bace don kuwa ni har na fara
mantawa da yawan tunanin da ake yi ada saboda
munkasance tare da Bebi ta na debe mini kewa. Ba mu
za ta ba sai muka ga an turo kofa dukkan mu
hankalimu ya koma cikin zakuwa da son ganin wanda
zai shigo ras! Gabana ya yi mummunan farduwa da
shigowar shi Sunusi ne kaka Aisha ta ta shi cikin dariya
da sakin fuska ta ce a maraba lale marhabin ku ne tafe
sannunku dazuwa su ka amsa mata cikn girmamawa
bayan sun gama gaiswa ya ke tambayarta yaya jiki
Ameerah? Ta ce jiki kam Alhamdu lillahi ya ce to Allah
ya kara saukl ta ce amin. lokacin da take kokarin fita
daga dakin ya matso kusa da gadona san nan ya yi
murmushi ya ce Ameerah yaya jikin na ki? Ko kallonsa
banyi ba ba re ma na tankamasa Bebi ta mike ita ma da
niyyar bar masa wajan na rilke mayafinta ina kuma
zaki na fadl hakan ne cikin tsuke fuska, ta ce wajen
zani wajan kaka Aisha. Ki yi me? In ta ya ta hira,
kuma kwaji dadin hirarku na ziro da kafata daga kan
gadon na ce to mu tafi tare ko?.Ta ce kamar yaya na се
mu tafi tare ni ma sai muyi hirar tare ta juya ta kallie shi
ya na tsaye ta ce ku da ku ka yi bakko kya ta fi ki bar
shi? Na ce bako fa ki ka ce? Ta yi shiru na ce mu je
mana.?
Sunusi ya ce Ameerah ke da baki da lafiya ina
kuma zaki ki dawo ki zauna mu sai mu tafi tun da dai
ganina ne ya jawo fitarki na yi tsaki a sannann na
kama murin kofar na ce da shi to ai sai ayi waje ko? Ya yi dariya kai wan nan matar tawa lallai ina da aiki а
gaba na ga alamar sai na tashi tsaye saboda wannan
32
tsiwar ta ki, sai burgen ta ke dari bisa dari ya ajiye
ledar da ta ke hannunsa ya ce ga shi nan to Allah ya ba
ki lafiya ni zan tafi sai kunia gobe suka juya shi da
abokinsa suka fice.
Na koma na kwara ina dafe da kirjina ina cewa
waiyo kirjina nan da nan Bebi ta yi waje cikin suri ta
yi kiran wata nos ta shigo da kaka Aisha ganin Be'si da
wata nos din ta ce mai ya same ta ba ance aguji bat
mata rai ba? Kaka Aisha ta ce ai ba wanda ya 6aa mat
rai hasalima yanzun nan muke zaune mu na hira sai da
tayi Baikona ni kuma sai na tashi na fita na barsu
awajen tayi min Allurar bacci, bacci mai karfi ya
daukeni ban san tafiyar Bebi ba.
Da safe ne bayan mun gama abinda zamu yi
Anti ta shigo tare da yaranta gabaki daya suka shiga
suka zauna bayan sun gaisa ne da kaka Aisha ni nana
dan rankwafo na gaishe da ita ta ce Ameerah yaya karin
Parfin jiki na ce da saukI Anti ai na werke. Kaka ta ce
ina fata kin warke ainun ba mu san ranar da za'a
sallame mu ba, Anti tace saboda me lafiya me ya sami
Ameerah? Fadan taba baki ta ce hauka irin nala wai don
jiya yarannan Sunusi ya zo dubata shi ne abin tashi
hankali baki ga yadda ta ji ciwo ya dawo sabo fil ajiya
likitan yai ta fada ba ance a dai na sata bacin rai ba. Ni
kuwa ai ina ganin 6acin rai yanzu ki ka fara fuskanta
shi tunda dai ai babu fashi dama kin sawa rank
dangana kin dauki komai ba komai ba.
Anti ta kalle ni cikin matsanaciyar damuwa ta ce
kai ni wallahi wannan abin ya ishe ni abin har tsoro ma
ya ke ba ni ace abu yaki ci ya ki cinyewa ita hankalinta
bai kwanta ba mu ma na mu bai kwanta ba ina dalili.?
33
Kaka Aisha ta mike tsaye a to haka kuma ni ma
kan na gaji amma kuma ke sadiya ai in kin fadin haka
a gabanta cikin daure mata gindi kar ta yarda ta yi waje
tana gunagunin ta. Anti ta ce a'a goggo ni ba haka na
ke nufi ba, Anti ta mike ta nufo in da na ke kwance a'a
dafa Antina ta mike ta nufo in da na ke kwance ta dafa
haiua ia ve A bani dadin yaucda goggo ta ce da ni
kin yiwa Sunusi ba wallahi Ameerah Sunusi bai can can
ci wulakanci ba, Na ce Anti dukkan wani abu na jikin
ki bayason Sunusi Anti ta dan jinjina kai kana ta ce to
wai ni tsaya in tambayeki Ameerah ko zaki iya gayamin
dalili wannan kiyayyar?
Kaina a sunkuye na shiga juya maganar a
zuciyata a yadda maganar ke da nauyi a gare ni ban ma
san ta yadda ya kamata na fara ba to amma da ya ke
zuciyata ta tabbatar min wannan ita ce muhimmiyar
damar da na ke da ita dan haka ya zama dole na
sanarwa da Anti abin da ya ke cikin zuciyata dan gane
da Sunusi.
Don haka cikin nutsuwa na zayyanawa Antu
labarin farkon haduwar mu da Sunusi da musabbabin
da ya janyo na tsani Sunusi.
Anti ta dade ta na jinjina abin a cikin zuciyarta,
daga bisani ta dago kanta jikin ta a sanyaye ta ce shi ke
nan Ameerah na amince da ke kuma nima ina goyan
bayanki sai dai ki sa ni yawan kuka da yawan tunani ba
shi zai kai ki ga cimmma burin ki ba illa Addu'u kinsan
itace takobin mumini. Addu'a takobin mumini ce ki na
da saninki dai dai gwargwado Ameerah ki yawaita
addu'a ita ka dai ce mafita a gare mu, ni ma zan ta ya
ki dan abin dana-sani na neman taimako ki yawaita
karatun alkur'ani akai akai hakan shi zai taimaka miki
34
kwarai da gaske ko dai kiji kina san Sunusi ko kuma
Allah ya kawo miki canji, mafi alheri amma inaso idan
kin tashi yin addu'ar ki ki nemi zabin Allah, Allah ya
zaba miki ma alheri idan kuma Ubangiji ya kaddaro
Sunusi ne mijinki to ba yadad za muyi idan kuma ba
shi ba ne to da ma haka mu ke so.
Sai dai Ameera ina san ki daukar mana
Alkwarin daga yau ba zaki kuma nunawa Sunusi
kiyayya ba balle ki kuma cewa ba kya sonsa a gaban
wani kin gani da yanzu abin da goggo ta ke cewa wai ni
na ke daure miki gindin kar ki so shi, ta kamo hannuna
ta hada da na ta ta ce "Please 'ya ta kiyi mana wannan alkawarin ki yi hakuri ki daure komai yai zafi da maganinsa."
Na kalle ta nan da nan tausayin Antina ya
kamani na bude baki cikin shishshikar kuka na ce Anti
na yi miki alkawarin hakan ba za ta kuma faruwa ba in
Allah ya yarda ta ce na gode Ameerah Allah ya sa mu
da ce na dan ran kwafa na tashi zaune ya yin da antina
ta yi saurin karan filo a baya na dan in ji dadin jingina.
Na ce da Anti ina son shan ruwa ta mika hannunta ta
dauko ruwan ta miko min na sha. Na kalle ta na ce to
yanzu Anti menene shawararki game da wannan
lamarin?
Ta yi dariya tace Ameerah kamar yadda ki ka
sani ne ba mai iya tunkarar Alaramma da wannan
maganar illa mutum daya shi ma kuma ba wai dan ya fi
karfin Alaramma ba ne, a'a ina ganin zai iya yi masa
magana saboda irin mutanan nan ne ma su fadar
gaskiya komai za ta jama sa. Sai dai duk da haka bai ta
ba jin ya yi magana a game da auran wata ko wani ba.
Saboda sanın halin Alaramma to ina ganin. kya iya
35
zuwa wąjanshi ki roke shi ya taimaka miki ko Allah
zai sa a dace. Sai dai da sharadin idan har kinje to kada
ki kuskura ki ce ni ce na turoki a raba wannan auran.
Cikin zumudl da matsanannaciyar murna na cе
da Anti wanene ya ya sunansa? Ta yi murmushi ta ce
Ameerah ke nan ai ba wani ba ne kakan ki ne..
Na ce wanne kakan nawa? Ta ce kanin Gogg ne
ta na (nufin kanin kaka Aisha) na ce ko (Ko Baba Ali?)
ki ke nufi. Ta ce kwarai kuwa. Na ce to yanzu Anti
yaushe za ni? Tai murmushi ta ce ke da ki ke a gadan
asibiti ai sai kuma randa aka sallamki ko? Na ce wallahi
Anti na warke bari ma in je ince da likitan nawar ke ya
sallameni tai dariya ta ce lallai Ameerah duk dokinki
dai ai kya bari ya sallame ki dai da kan shi tun da dai ya
na ganin ki kuma ya san abin da ya ke damunki, kuma
in kin ji saukin ai ay fi kowa sani, ba wai sai kin ce kin
warke ba.?" Na ce Anti ai.... Ban kai ga karshan
magana ta ba sai na ji shigowar Kaka Aisha ita da yara.
Anti ta ce ina kuka shiga ne goggo? Kaka ta amsa ta
ce muna wajan direban ku mun hira. Anti ta ce goggo
ni dai zan koma ina ganin sai da daddare ko kuma gobe.
Kaka Aisha ta ce yau da wuri haka za ki tafi? Anti ta
mike tsaye ta ci gaba da fadin ai gara mu tafi tun da na
ga jikin na ta ya yi kyau. Kaka Aisha ta ce kwarai
makuwa jikin kan Alhamdullilllahi ya yi kyau. Ni da
har na fara murnar za mu ci gumba to kuma sai ga shi ta
yi mana bukulu gaba dayanmu muka yi dariya.
36
au litinin ita ce ranar da ka sallameni daga Y
asibiti ina zaune a dakin Anti ina shafa mai
Anti tace Ameerah wai kuwa ina za ki ne?"
Na ce "Anti gidan Baba Ali, daga fitowarki, ko
dada jin karfin jikinki ba ki yi ba, a a ki dai bari sai nan
da jibi kya je na yi rau vau da ido na ce don Allah ki yi
hakuri ki bar ni na je kin gani ta..... dagan hännu ya isa
a dawo lafiya. Dajin haka sai na yi gaggawar shryawa
na sa ka doguwar riga da dan takalmina mara tudu s:
dan karamin mayafi na na yafa, na yiwa Antina sallama
na yi gaba, da dora kafata a soron sai mu kyai kicibus
da Kawata Bebi na kalleta itama cikin mamaki
"Ameerah ina za ki?" na kalleta na yi dariya na ce
"Allah ne dai ya kawomin ke kinga... na ce ke dai zo
mu tafi. Kawai ina?" na ce dan Allah ki na batamana
lokaci na ce ki zo mutafi to muje ciki mana ni ma dama
akwai abin da na ke son fada miki na ce zo mutafi dan
iah a hanya sai ki fada min abin da ya ke tafe da ke
to ai kyabari in je mu gaisa da Antina, ko da na ga bata
da niyyar tahowa mu tafi, sai ta batamin lokaci sai
kawai na kama hannunta na yi waje.
**** **** ****
muna cikin tafiya ne Bebi ta ke shaidamin an
kusan kawo kudinta. Na kalleta cikin matsananciyar
murna na ce dan Alláh kai amma na ji dadi kwarai da
gaske na ce yaushe kuma za'a kawo kudin?" jibi su ka
ce za su kawo kudin na ce iye amarya ta yi dariya har
ma na zama amarya ke nan. Na ce Kwarai da gaske
dariya danni a yanzu amarya zan ringa cewa da ke wai
wayaga bakin Abdul dinki, wai washa? Ta dirkan
dundu abaya ke dai wallahi da tsokana ki ke ai banyi
miki haka ba nan da nan na tsuke fuska na ce ke dai
37
inji dadinki waliahi ina ma ni ce ke ni yanzu kin
ganni ma fitowar nan da na yi gidan Baba Ali za ni in
roke shi ya yi min arziki ya je ya sami Alaramma ya
roke shi ya fasa hada ni da Sunusi don kuwa a agaskiya
Kiyyayarda na ke yi ma sa ba ta wasa ba ce.
Lokacin da muka isa gidan Baba Ali, mun tarar
da matarshi goggo Binta ta na sharar tsakar gida da gani
na ta hau yumn tsiya to bera anzo a yimin fashin miji?
Cikin dariya na ma yar mata da martani "Uhm! Sarkin
a inuwa ni me zanyi da wannan tsohon mijin naki kai
duk furfura.?" Bebi ta amshe da fadin "A'a ke dai
Ameerah fadi gaskiya cewa ki ka yi in zo raka ki fadI
Ameerah ta fadi gaskiya Ameerah ki fadi gaskiya.
Gwaggo Binta ta wangale baki harda tafa hannu
amar taci gaba da fadin kyagama bikinki lafiya mijina
bai sonki ya ce baki iya tuwo ba ballanta burabusko."
Na ce "Idan na iya fada miki zan yi na fadi ne a
lokacin da na ke kokarin zama, ka na na dubi Bebi na
ce "Ke kuma "yar ziga sai ki zo ki zauna in kin gama
da ni kana kuma agaisa da gwoggo Binta daga bisani na
ce Gwoggo Baba Ali ya na nan wajansa na zo, Gwoggo
ta yi dariya tace amma ban yarda da zuwan nan na ki
ba....na katse ta cikin wasa Allah da gaske wajen Baba
Ali na zo game da matsalata ki taimaka ki je kisanar
masa gani na zo ina son ganinsa bayan ta je ta sanar mai
da zuwa na sai na mike tsaye na nufi 6angaren da yake
cikin zuciyata kuwa ina ta karanta HASBUNALLAHU
WA NI'IMAL WAKIL dan neman dacewa da yin
nasara.
Lokacin da na shiga falon Baba Ali na tadda shi
zaune bisa sallaya ya na duba alku'ani na yi sallama a
38
sanyaye na shiga dai dai lokacin da ya ke shafa addu'a
ga mi da rufe alkur'anin.
"Ameerah!" dattijon mai kimanin shekara sittin
ya dago kai cikin dan murmushi ni kam a zuciyata,
cewa na ke a "Oh! Ni Ameerah wannan tsoho da
kyanruwa ya ke fuskar nan a washe kuma gashi dai tun
a tasowata na ganshi haka har zuwa yau din nan ya na
nan daram yadda ya ke, fuskarnan a washe kuma a dace
da muhibba ta kasancewarshi musulmi kuma masani
ma'ana (MALAMI)
cikin taushashshen harshe Baba Ali ya amsan
sallamata gami da fadin maraba da uwar gida. Na nemi
gefe na dan zauna, ina dubanshi kaina a duke sabili da
kasancewar shi Kakane a gare ni matsanancin kwarjinin
da ke mamye a fuskarshi shi ke hanani yin wasan jika
da kaka dashi illa iya ka mu yi da matarshi da ke ita
macece.
Kana daga bisani Baba Ali ya kawar da shurin
da fadin ya babar taki ta na lafiya.?" Na ce "Lafiya lau
"Ya ce to "Alhamdulillahi na dan gyatta zama gami da
dan sunkuyar da kai ka na na soma mágana a sanyaye
muryata ta na dan sarkewa. "Uhm! Baba Ali dama na
zo wajan ka ne akan wani taimako da na ke so ka yi
min..." na yi shiru dan jin ta bakinshi.
Baba Ali ya dan girgiza kai gami da fadin "To
Allah ya sa ina da abin taimakon fadI ina jinki.?"
Lokacin da na bude baki da niyyar fara magana shi ne
ya yi dai dai da zubowar hawaye daga idanuna don
haka maganar tawa ta kasance cikin muryar kuka, Baba
Ali na zo ne dan ka taimake ni akan maganarmu da
Sunusi ka na da labarin Alaramma ya karbi kudinshi,
alhalin turko na fito na nunawa shi kan shi Sunusi
39
ba na son shi amma duk dangi sun juyan baya har ya
zamanto bani da mai goyan bayana akan wannan lamari
ni kuma na yi imanin ba zan taba iya jure zaman auren
Sunusin ba, saboda ina yi ma shi kiyayyarda ni kaina
ban san iyakar ta la dan girman Allah Baba Ali kayi
min wannan tair akon.?" Anan na sai kuka ya ci
karfina, na ci gaba da gunjin kuka. "Baba Ali a yanzu
kai kadai ka rage min da na ke da tabbatacin zaka iya
taimaka min akan wannan lamarin.
"Subhanallahi, me ya yi zafi haka?" "Ameerah"
Baba Ali ya fada a gaggauce cikin dinbin mamaki ka na
ya ce "To yanzu shi Alaramma ya na da masaniya akan
hakan.?" na daga kaina fuskata jike da hawaye sharaf -
sharaf na ce 'Bai sani ba kuma ni ina tsoron tunkararshi
da wannan maganar ba ni ba ma duk wani wanda na ke
gani zai iya tunkararsa na je na same shi kowa sai ya ce
ba zai iya ba don haka na ga babu wani wanda ya dace
sai kai don Allah Baba Ali ka taimakamin wallahi ba na
son Sunusi.?" na gama magana da kuka.
Baba Ali ya gyatta zama ka na ya ce "To shi ke
nan dakata, share hawayenki ki saurari abin da zan gya
miki.?"
Na hanzarta na sa gefen mayafina na idanuna.
na ci gaba da saurarsa. Baba Ali ya ci gaba da fadin
"Ina son ki sani Ameerah ina son naji hujjarki ta yi wa
wanna yaron da iyyanki ke son haďaki da shi wannan
kazamar kiyyaya.?" Na amsa "To, to"
Baba Ali ya ci gaba da farko Ameerah ina so ki
san Allah Subhanahu wata'ala ya fada mana "ya ku
muminar idan za ku so dayanku ku so shi dan Allah,
idan za ku ki junanku to ku ki su dan Allah) don haka
40
ina so inji daga gare ki shin wane dalili ne ya haifar da
kiyyayar shi wannan yaron a gareki.?"
Kaina a sunkuye haka zalika murya ta a raunane
na soma fadin "Ko da ma ni ina kin shi ne tun farkon
haduwarmu na fahimci ya na da wata mummunar akida
kazama, wadda duk wani dan musulmi mai imani ya
dace a ce ya gujeta, wannan shine dalilina na kinshi."
Baba Ali ya dan kada kai ka na ya ce "To sh
ke nan Ameerah ina fatan babu yarfen cikin maganarki
sanin kan ki ne Allah (S.W.T) baya barin bawa da lafin
yin yarfe ga dan uwanshi mumini face sai ya yi ma shi
sakyaya a ranar gobe kiyama.?"
Na kada kai na ce "Wallahi baba Ali babu sharrі
a ciki abin da na fada." ya ce "To shi ke nan na amice
zan taimake ki akan wannan batu to amma fa ki sani in
har ki na so in tunkari Alaramma cikin karfin gwiwa
ir.. ganin zai fi kyau cikin manemanki in je mashi da
maganar kin fidda wani ma kafin shi Sunusin da ba ki
SO.
Tas! Gabana ya fadI (wannan shi ne gaba zaki
baya siyaki) ko in cę ana wata sai ga wata. Ni Ameerah
yaya zan yi da raina ni da ahalin yanzu ba ni da wani ba
ya ga shi wannan marayan to ga kuma abin da Baba Ali
ya ke bukata to yyaa zanyi ke nan.?" Jin na yi shiru ban
tankaba Baba Ali ya ce "Kina jina ko Ameerah, na ba k
sati daya ina jiran ki zomin da byaani..?"
Na tarar da Bebi su na hira da ita da giggo
binta. Bebi har kin fito.?" Na daga mata kai alamar
"Eh" a lokacin da na sa gefen mayafina ina goge
gumin da ya ke son jikamn fuska. Goggo Binta
Angama zancan da mijin nawa nedan san ki da iya
kalalle mutum da ai har zan biki to kuma sai
wannannnn kawarta ki ta bani hakuri kuma da sanin
mijina ya fi karfinki duk ki kwarkwasarki Malam sai
ni."
Na yi dan murmushi na ce "Da ma ai wannannn
keyan majinar sai ke din wa zai debarwa kan shi ytari
da rubabbivar maiina.?" Dukkan mu mu kyai dariya.
Bebi ta mike tsaye ta yafa mayafinta ni kam a lokacin
ma nake kokarin zama dan Allah Ameerah ka da ki
zauna kin gani dare ye fara shirin hada shirginsa, kada
mu yi dare da yawa.?" Na ce "To Bebi amma dai duk
saurinki kya bari in dan huta ko.?" "Hutu kuma wane
iri sai ka ce wadda ta yi wani nannauyan aiki tabdi jam
hutun jaki da kay ke nan dan Allah ki ta shi mu tafi ko
kuma wallahi ya zu ki ga Hassan wayan." Na yi dariya
na ce "Menene kuma Hassan wayan.?" Bebi ina nufin
ir yi tafiya ta sai dai ki duba ba na nan.?"
Na mike to muje karki cinyeni dariya mukayi
wa goggo sallama mu ka tafi.
Mu na cikin tafiya da Bebi ta lura lalle ina cikin
matsananciyar damuwa sabili da yadda ta dage ta na ta
faman zira min hira ni kam bani iya tankawa illa iyaka
in ce da ita "Uhm."
Bebi ta dafa kafada ta cikin murmushi
"Ameerah ina fatan dai munyi nasara.?"
Na kalleta na yi ajiyar zuciya na girgiza kai na
ce "Kye Bebi, wannan shine kusan na ce da ke ana wata
ga wata." ki na nufin ki ce ba mu yi nasara ba.?" na ce
"A'a ba haka na ke nufi ba, ai ko ba komai ina iya cewa
da ke tun lokacin da aka fara wannan rigimar babu
wanda ya kalle ni da idan rahama akan wannan batu
face "Antina da shi Baba Ali." Bebi "Ni abin da na ke
san na ji shine ya ya ya amince ko kuwa shi ma ya ki
amincewa.?" Na ce da ita "Ya saurare ni ya kuma ji
duk abin da ke tafe da ni ya kuma tausayamin to sai dai
shi kuma ya zo da wani lamari mai wuya ko in ce ya
kuma jefani cikin tsaka uku mai wuyar fita." Ta dafe
kirjinta cikin kaduwar jin abin da zan fada mata "Wani
kuma lamarin ne wannan Ameerah.?" Lokacin da ta ja.
ta tsaya a hanya ta na kallona. Na kama hannunta mu ka
ci gaba da tafiya. Na сe "Uhm! Cewa ya yi wai ya bani
nan da sati daya in kawo masa wanda na ke so a dai
cikin satin kuma shi wanda nake son zai kawo kudin
aure in ya so shi Baba Alin sai ya tafi da su kuma ya
nunawa Alaramma sauran bayani sai yasan yadda zai yi
wai dan ba za'a mayar da kudin wani ba alhalin bani da
gwani Alaramma idan ya ji haka ba zai yarda ba to