An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Ameerah
RABI MASIDI ABUBAKAR
(Hajiyar Birni )
(Mrs Ayuba Yahaya Ibrahim )
Hakkin Mallaka (m) Rabi Nasidi 2003
Copy Right (c) Rabi Nasidi 2003
Shekarar Bugu
2003
Kamfanin da ya yi dab'І
Tare da Tsata rubutu a Na'ura Mai Kwakwalwa
Mashi Printing & Publishing co.
NDneji Qtrs, S/titi Mandawari Kusa da Sehad
Storss Kano.
Tei-064 331928
Godiya
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki
tsira da aminci su tabbata ga Annabin tsira (S.A.W) Ina
godiya ga Allah da ya bani damar Rubuta muku
wannannnn dan Littafi.
Ina mika godiyata ga Haj. Halima Yusuf
(ummi) Yakasai saboda muhimmiyar rawar data taka
wajan ganin littafin ya kammalu gami da bada shawarwari gyare- gyare da ta yi babu abin dazance mata sai
dai ince Allah ya sakamata da alheri ya kuma buda
mata basirar rubutu Amin, HajiyaHalima Yusuf Ummi
(Ni ko ita) (Lokaci ne) na gode na gode na gode.
SADAU KARWA
Na sadaukar da wannan Littafi ga mijina Ayuba
Yahaya Ibrahim, saboda goyan bayan da ya bani na
gode Allah ya barmu tare.
GAISUWA
Ga kanwata Maryam Nasidi Abubakar da Sameeran
Rabi'u K/Ruwa da .Zainab Uba Sameerah Mustapha
Baba kusa da Jamila Sulaiman, Hauwa Usman Maryam
Muhd da Amina (Ummi).
MUHIMMIYAR GODIYA
Ga Mahaifana saboda kulawar da suka yimin na gode
Allahu ya sakamusu da alheri Amin,
TAKU
RABI'ATU NASIDI ABUBAKAR
(Hajiyar Birni)
3
meerah ki hanzarta kije a kitsemin kanki kada Aya yi tsami ke dama gaki da jin zafin kitso....
Ina daga daki na amsa to anti dama yanzu nake
da niyar tafiya na dan tsaya ne ingyara miki dakin kafin
intafi, Anti ta danyi murmushi kana ta ce indai gyaran
dakina ne, dan yau daya abarshi na yafe zo kije ayi
miki kitson diyata, na ajiye dan hankicin dake hannuna
wanda dashi ne nake goge- gogen kana na nufi inda
man kitso na ke ajiye na zari mayafina na nufi waje.
Da jefa kafata cikin zauren farko mukayi
kacibus da kakata wadda muke kira da Aishat, ta sako
kai tunkis-tunkis na sheke da dariya kana nace Lah,
barka da zuwa kakalena (haka nake kiranta idan naso
yin tsokana) yau kace a gidan namu, kaka tadan tsaya ta
dubeni ita ma dai cikin sakin fuska ta soma fadin ta
berange ina zuwa haka da La'asariyya? Nasan dai baki
da saurayi ballantana ince shine yazo koda yake yanzu
kin kusa ki huta da gorina tunda munyi miji.......
Cikin matsanan cin mamaki game da firgita na
tsirawa kaka Aishat idanu, bansan lokacin da nayi subul
da baka nace ke kaka wane irin miji? Ana zaune kalau
nida bansan yadda ake fadin ba ballantana muce ga
wanda zan aura, maimakon kaka Aishat ta bani amsa
sai ta dan gogeni ta wuce tana fadin ke ni bani waje in
shige bansan shirman nan naki ko ma menene kyaji a
bakin uwarki......kaka Aishat tayi cikin gida abinta,
nayi kamar in juya inbi bayan ta, dan a zahirin gaskiya
zuciyata na hakIkance mani cewa akwai bukatar inyi
cikakkiyar tambaya a game da maganar da kaka
Aishat.... Ma'ana suna Bukatar karin bayani.
4
To amma a yanzu idan na koma zatayi kamar
nayi tsaurin ido dan haka sai na zarce gidan kitson,
zuciyata nacike da tunanin game da ınaganar da kaka
Aishat wadda na sanya mata alamar tambaya?
******* ******* *******
Har zuwa lokacin da Habi mai kitso ta fara
yimin kitson ni dai zuciyata nacan cikin tunanin
maganar data firgitani, a zuciyata na yawaita yiwa
kaina tambaya game da shin me kaka Aishat take nufi
da fadin munyi miji?.....haka zalika me take nufi da
fadin koma menene kyaji daga bakin uwar ki, na kada
kai tabbas akwai alamar tambaya cikin maganar kaka,
tabbas muna wasa da kaka aishat amma tunda nake bata
tabayi min irin wannan maganar ba, idon har zanyi
la'akari da rin al'adar gidan mu saboda su tun farko
suna da wata gidauniyar akida wadda ta samo asali tun
daga kan kakan kakan mu.
Har zuwa yanzu da daukacin gidanmu muke
karkashin ikon kakana wanda ya haifi mahaifin
mahaifiyata, kuma shi din nan dai ya haifi mahaifiyar
mahaifina ma'ana iyayen nasu idan mace da dan namiji
Mal. Musa wanda akafi sani da Alaramma sh mutum
ne mai tsattsauran ra'ayi wanda idanya ce e! to babu
wanda ya isa yace a a kuma ya zao tunda gasu kansu
ya samuo asalin auren zunci akayi sai dai a hada
'y ar wanna da dan wvana batare da su kansu yaran da
za'a hada auren sun sani ba, sai dai kawai ranar maulidi
yari na zaune taji an daura mata aure kuma dole ta
hakura ko tana so ko bataso to tunda dama shi na.niji ya
hakura ke mace ai dole ki hakura.
Ni kuma gashi Kaka Aishat abin da take fada
dole ne hankali na ya yi masifar tashi Allah Allah nake
Habi mai kitso ya gama min kitsan inje inji abin daake
shukawa acikin gidan mu ana gama kitsan na mike
tsaye Habi ta ce tsaya mana in tufke miki kitson mana
nace barni Habi ina sauri ne kawai aikin dana tuna
zanyi kuma banyi ba nake saurin inje in yi shi to
shikenan.
Na isa cikin gida amma zuciyata take da
fargabar to me ya kawo Kaka Aishat gidan nan da
yamma ina yin wannannnn tunani ananma na kuma
tabbatarwa da kaina ni dai a sani na ban taba ganin
kaka Aishat da maraice haka ba sai yau.
Nayi sallama na shiga kaka Aishat tana kokarin
ta yarda kabbarar sallar magariba nima naje nayi alwala
nazo na fara bada farali Kaka Aishat ta rigani idar da
sallar sai da na idar da tawa na juyo sai naga kamar ni
take jira akwai bayani a tare da ita na kalleta kawai ni
yau na sake miki kamane sai kallona kike yi? Ta gutsuri
goron banun ta ta miko ungo ni in zaki ci a'a Allah ya
kivaye sai kace wata ke.
Anti na shigowa itama ta nemi guri ta zauna ta
mika hannu ta rage karar TV ta jiyo ta kalleni Ameerah
na juyo na kalleta Na'am inason zan tambaye ki ne
bance komai ba illa kallon ta kawai da nake kinsan
wani Sunusi nayi shiru a'a bansan shi ba nace da ita ina
nufin duk cikin samarin ki ba mai wannan sunan nace
A'a babu suka kalli juna ita da kaka Aisha suka yi shiru
suna tunani da mamaki.
Ras gabana ya fadı da na tuno da wani wanda
muka taba haduwa da shi yace dani sunan sa Sunusi
laliai na tuna, dashi in dai har shine to in kuwa shine ma
Sunusi yake nufi dani tunda tun farko nace dashi
6
banason sa asalima yau kusan wata biyu ko uku da
rabuwar mu dashi.
Ya naga kina gumi ne Antina ta ce dani na
kalleta, ko kinsan shine na share gumin da yake fuskata
natuna dashi amma yanzu bama tare dashi shi dama
muke san muji kin sanshi ko baki sanshi ba kuma tunda
dai kinsan shi ai shikenan magana ta kare inji Kaka
Aishat.
To shi Sunusin ne ya dauki kudin aure ya kai gidan Alaramma yau kwana shida kenan da kai kudin
ko da yake su iyayen nasa sun jene akan dan Allah
abaiwa dan nasu Izinin neman auren ki don haka suka
kama kafa da manyan ki to cikin sa'a kuma lokacin da
suka je sai suka yi sa'a yasan wan baban shi sunusi.
Bayan sun gama gaisawa ne sai shi wannan
baban Sunusin mai suna Alhaji Muktar sai ya fadI abin
dake tafe dasu to nan da nan Alaramma sai ya yi farin
ciki da jin wannan bayani nasu yace ai ba wani abu kar kuji komai kuma kuce dashi yaron kar ya damu ya cigaba da zuwa wajenta indai Ameerah ce na bashi ita,
indai da rammu kamar ya aure ta ya gama naji dadI
kwarai da gaske wannan abin ai duk na gida ne. To ganin haka shi wan Baban Sunusi Alhaji
Muktar yasa hannu a aljihun ya fiddo da kudin aure ya bawa Alaramma shi kuma- Alaramma bai yi wata wata
ba ya sa hannu ya karbа.
Bakin ciki da takaici suka hadar mini cikin kukа
nace ni wallahi banason shi kuma ni bazan auri wani
wai shi Sunusi ba.
Ban gane nufin ki ba in ji Kaka Aishat ta fadI
ne tana tsattsareni da idanu nace to ma wai ke kin taßa
ganin yadda akayi haka kawai akarbl kudin mutum ni
7
bansan shiba kamar yaya baki san shi ba yanzu kika се
da mu kinsan shi kuma yanzu daga baya kice baki
sanshi ba kuma in ban dake-cikin zuri'ar mu waye ya
taba sanin mijin da zai aura basai dai in an daura auren
yaji ba cikin matsanan cin kuka na cigaba da fadin ni
wallahi bana Kaunarsa na amince ku hada ni dako
wanene amma banda Sunusi Anti ta dubeni a fusace ta
jinjina kai kana ta ce Ih! lalle to wallahi ko dashi wanda
zaije ya fadawa Alaramma bakyason shi? Ko kina
tsammanin ni zan iya tare Alaramma da wannan
tatsuniya.
Na yi kuka ya ishe ni lalle in ko haka ne an
hadani da bala'in da ko a mafarki ban taba tsammanin
zan shige shi ba wai Sunusi zan aura sai yanzu ne hoton
lokacin da muka hadu ya fado min arai.
Ba zan taba mantawa ba ranar juma'a ne da dan
hantsí anti na ta aikeni gidan wata kawar ta, toni ga
aladata nariga na saba bana sanyin tafiya ni daya, sai na
nemi dan rakiya koda kuwa yaro ne.
To ayau ma sai na kira Ummi diyar Anti na mai
kimanin shekara hudu tazo ta rakani. To muna cikin
tafiya ne sai yarinyar ta nuna ta gaji da tafiyar ta ce
lallai sai na dauketa ni kuma nace bata isaba nakI na
dauke ta.
Take yarinyar tasa kuka nay lallashin duniyar
nan akan tayi shiru amma taki takuma ja ta tsaya taki
yin gaba ganin haka sai nayi gaba na barta da niyyar
intaga kamar zantafi inbarta to zata biyoni to dai dai
inda muke kusa da wani shago ne don haka lokacin da
Ummi ta sake tsanyarewa da kuka sai naga anturo kofar
shagon an bude wani saurayi dan dogo dashi ya fito
yana murmushi ya kalleni ya kalli yarinyar ya dan
8
matsa inda take ya kama hannun yarinyar, yi hakuri
Kanwata Antinki ce takI ta dauke ki ko? Ummi ta daga
kai alamar Eh! Yaci gaba to yi hakuri in kinje gida saiki
fada azaneta ko? Da sauri yarinyar ta amsa to, yasa
hannu a ajjihu ya ciro biskitya ce ungo naki ne ke
kadai kada kibawa Anti kinji ko? Ta gyada kai kana yà
dan dago kai yana wani irin murmushiya ce
matsomana Anti ki rike hannun ta mana, take azuciyata
na soma raya cewa .....kai wannan mutum da kirki yake
ko kuma ince da son yara yakeе.
To sai dai kuma ga mamakina ban idar da
wannan tunani ba, sai naga an daga labulen shagon
wata yarinya ta dan leko da kanta tana fadin wai ina
katafi ne ka shanyani gaskiya kazo ni tafiya zanyi kada ayimin fada agida yadan juya cikin murmushiya ce yi
hakuri kijirani minti biyu yanzu zanshigo.
Duk wannan abu dake faruwa ina kallonsu
tashi farko tunanina ya fara ayyanamin duk yadda akayi
wannan saurayin yana daya daga cikin irin lalatattum
samarin nan da nake jin labarin su masu yaudarar 'yanmata suna lalatasu. Don haka take naji matsananciyar tsanarsa ta dira azuciyata hara ya zamto
ina la'antarsa acikin zuciyata dashi da mesu irin
halinsa: Nan danan na riko hannun Umma da niyar
mukama gabanmu tun wani bai ganni tsaye wurin ba.
To a lokacin yadan dada mat..owa yana fadin 'yan mata
ya va zaki tafi baki fadaram sunanki ba, nadan kauda
kai na ce idan na fadamaka amfanin mai zai yi maka?
Yavi murmushiya ce ai amfanin ba mai musaltuwa
bane sou haka bansan yadda zan kira shiba, tuni na juya
ina fadin kayi hakuri wannan sunan ba mai facduwa
bane.
9
Nan da nan ya sha gabana yana fadın don Allah
ki tsaya mana koda minti biyu ne ina so zanyi magana
da ke, nadan tsuke fuska nace wace irin magana kuma
daga haduwar kan hanya?ya ce don Allah ina son insan
gidan ku gabana ya fadI nace acikin zuciyata a awai
mai wannan mutumin yake nufi dani ne? take dabara ta
fado min nace sunana Hadiza nai masa karya haka
zalika nai masa kwatancen karya wanda kwata
kwatama bai shafi unguwarmu ba.
To azuciyata ina Allah Allah na bar wajen cikin
murmushin jin dadī ya ce nikuma malama Hadiza ba
aso asan nawa sunan ne? cikin ko sawa dayin maganar
da nake dashi nace bahaka bane nasan zaka fadamin
shiyasa ban tambaykea ba,ya ce ya ya akayi kika sani?
Nace kaga duk wannan iambaya bata taso ba kai dai
kawai fadamin sunanka sauri nakeyi kada aga na dade
ayimin fada, kwarai kuwa kina da gaskiya nima ba
zanso evi miki fada ba, to ni dai sunana Sunusi Ibrahim
Hashim.
******+* **********
kwata-kwata na manta da mun hadu da wani
shaf a rayuwata, na manta dashi in yawan bin hanyar
tunda Antina tana yawan aikena gidan kawarta amma
na manta dashi saboda baya gabana na hangeshi yana
yimin murmushi naji bakin ciki yake mani sai yanzu na
tuna dashi nace lallai yau yaya zanyi na fada cikin
raina, take dabara ta fado mini nasha mur saboda ina da
tabbacin sai yaga fuska zai sami damar yimin magana
to amma da yake irin wadannan mazan be zuciya gare
su ta tuni ya hau murmushi haka zalika ina matsowa
dab dashi yadan daga murya yana fadin ina godiya fa
akan kwatancen bogi da akayi min naje na bige da shan
10
wahala nayi kamar ban ji shiba nama kawar da kaina
daga bangaren da yake abin takaici wai sai ma ya taso
ya biyoni ya jeru dani yana malama Hadiza yaya akai
naje gidan da kika kwatanta mini har wajen sau uku
amma ana cewa ba gidan bane cikin takaici wannan
naci da yake nuna mini na juyo na dubeshi a fusace
kana nace to kana bina bashi ne ko me naci ban biya ba
da har zaka matsu lallai sai kasan gidan mu ya dan
girgiza kai cikin yake ya ce babu ko daya Hadiza illa
iyaka dai so da kauna.
Naji wan: kuna a zuciyata yadda kika san ya ci
ka min kibiya a zuciyata bansan lokacin dana furta... ka
gani tun wuri ka fita daga harka ta idon kuma kakI wallahi zan dau mataki akan ka naja wani dogon tsaki mits!!
A tunani na zai ji haushi hakan dana yi masa ya
rabu dani amma mai makon haka sai naga ya yi murmushi kana ya ce kiyi hakuri Hadiza bana nufin in
bata miki rai illa yaka na shiga wani matsanancin hali
na tsabar kaunar ki don haka bazan taba damuwa ba da
duk wani mataki da zaki dauka akaina, ba kuma zan gaji da birki sannu a hankali ba har sai naga burina ya cika na samu hadin kanki, dan haka ki daure ki sanar
dani inda zan same ki a tsiwace to shikenan ni dakai
aga dan halak nayi gaba ban ko sake saurare sa ba.
Bayan na koma gida ne Anti ke cewa dani
amma dan yau kin dade da yawa, nace wallahi da naje
na tarar bata nan ta shiga makota sai dana jira ta dawo
shine ya sa kika ga na dade Anti ta ce to iceko dai kinyi
sallah ko? nace la Anti nayi sallah mana yama za'ayi in
kai har iyanzu karfe wajen biyar banyi sallar la'asar ba.
11
A daran ranar ne dai ina gindin famfo ina wanke
hannu na bayan na gama cin abunci, wani yaro ya shigo
yace wai ana sallama da Hadiza nayi gaggawar juyowa,
nace da yaron nan gidan babu Hadiza kaje ka sanar wa
da wanda ya aiko ka, ya juya ya fita ni kam tuni na
shiga tunanin magana... bana ko tantama ire-iren
samarin da nake yiwa karyar chenjin suna ne wani
yazo.... ban ida tunani ba sai ga yaron ya dawo yace
ance wai to ke kizo.
Nace kai wai waye ne wannan ke aiko ka? yace
nima ya takura min da aike, ba nan ne gidan su Hadizan
da yake nema ba to menene na koma na sake aiko ka?
kuma kaima ai nasan kasan cewa a duk gidan nan babu
wata Hadiza ko ba nan Unguwar kake ba? ya ce na fada
masa yace wai shidai alallai nan ne gidan, ya kuma
tambaye ni wai yaya ne sunan yarinyar da take nan
gidan....... Na katse yaron da fadin shine kai kuma
dan baka da hankali ka fada masa ko?.
To menene kuma nayi wa yaro fada amira dan
aike ai bashi da laifi.... Anti ce ke magana tana tsaye
ne a bakin kofar dakin tana kallon mu.
A raina nace shikenan ta faru ta kare dama bana
kaunar Anti taji to yanzu kuwa ta riga taji dan haka
zance ya kare nasan cewa za tayi dole sai naje,
Nace Anti bafa ni yake kira ba yaron ne da shir
manshi, Anti ta ce duk da haka yafa mayafim ki kileka
kiyi mashi bayani in yaso sai ki koma.
Nadan marei raice nace Anti bafa ni yake nema
ba kuma ni sai in fita? Ni gaskiya ina ganin bai dace in
fita ba tunda bani bace Hadizan da yake nema ba,
Anti ta gyada kai game da fadin duk da haka ki
dai daure ki leka da kanki kiyi mashi nasan
12
magana
zaifi yadda da maganar ki akan ta yaron ba mamaki
idan yaron ne ya koma ya sake dawo dashi, na kalli
Anti cikin haushi nace toni yanzu idan naje mai zance
dashi, Anti ta shiga daki tana fadin Oho miki ni dai ga
abin da nace dake kiyi in zaki yi to in kuma ban isa ba
ne ya rage naki.
Dole ne na zari mayafi in fita ina kumburi, na
isa gareshi na taddashi sai faman murmushi yake yi ina
karasawa inda yake naji gabana ya fadl bakin ciki
game da takaici suka rufe ni.
Ada da farko dana fito ban sheda kowa ye ba to
amma yanzu dana karaso har inda yake na fahimce mai
kiran Hadizan, ba wani bane illa Sunusi (Sarkin naci)
mutumin da nayi wa cin mutunci dazu dazun nan.
To amma ga mamaki na sai gashi tsaye a zauren
gidan mu, tunani na farko shine..... yaya akayi ya gano
gidan? lallai wannan ya isa akirashi basara kan
naci.....ya katsen tunani na da fadin barka da dare
Malama Hadiza yaya ki kazo gida? Koda yake na lura
kina cikin mamakin ganina.
Na dubeshi na kauda kai a zuciyata nake
cewa....lalle wannan mutum ya zama dole inyi da
gaske akan shi tunda wurwuri tun bai jawo min wata bahaguwar rigimar ba, abin nufi kar tafiya tavi nisa nzo
in rasa yadda, zanyi dashi dan haka ya zama wajibi a
gareni inyi maganin shi a yau din nan ya fita harkata.
To mu gaisa mana ya mutanan gida? Lafiya lau
na bashi amsa yace hadiza sai kuma kika ganin yanzu
ko? Nason zakiyi mamakin ganina kina iya cewa da
zumnan fa inuka rabu dashi amma gashi yazo gidan mu
kina iya cewa koda ma yasan gidan ne yace dake bai
sani ba.
13
Ya cigaba da zuwa kamar kanyar din ya ba
dadl, yace ai da zunnan bayan mun rabu dake sai nayi
tunanin fushi ba nawa bane kamata ya yi in biki in ga
gidan ku tun da kinki fada min, tona biki a baya har
muka zo nan kika shiga sai nace da wani yaro nanne
gidan ku? Saiya ce dani Eh nan ne nayi farin ciki sosai,
da sai gobe nayi niyyar zuwa to amma sai naji zuciyata
ba zata yi hakurin sai gobenba gara dai nazo yau tunda
dai nasan gidan, ina zuwa dana aika yaro sai ya dawo
ya ce wai ba Hadiza a gidan, har hankali na ya tashi sai
ak tula sni nace yace kize tunda na tambaye shi --
cewa waya fada masa yace wata budurwa ce.
Tuni haushi ya rufe ni duk ya cikani da surutu
bai masa ni a tsayiwar da nake kamar kan kaya nake ba
dak nake gara na bar wurin, sai ci gaba nai sauri na
daga masa hannu nace ya isa haka na juyar dakai gefe
gud ya kalleni cike da mamaki lafiya kuwa? Ya
tambayc ni nace lafiya illa dai sauri da nake yi kawai
sai dai duk da saurin ba zai hana iu tsaya in fada maka
gaskiya ya ce to ina sauraren ki, naci gaba.
A gaskiva ni dai yezu bani da lokacin yin
soyavya dan haka sai kai hakuri dan karkace na yaudare
ka, ban iya yaudara ba kuma ban san a yaudare ni shi
yasa na fada maka gaskiya danni kai ma na taba
tsayawa dashi nayi zance dashi dan haka ni dai inay
maka addu'ar Allah ya baka wadda ta fini Ameen.
Ya yi shiru har anayin zaton ma ba zai iya cewa
dani komai ba na kauda shirin da cewa to sai anjima ya
dago da kanshi cikin sauri minti biyu, kamar karna
tsaya sai dai na juyo ina sauraren abin dazai ce dani, ni
ina ganin duk wannan bawani abin damuwa bane idan
har kin amince dani Juk bazai gagara ba koda kuwa
14
shekara nawa zaki yi kina karatun zan iya jiran ki fatana
dai ki soni ki kuma bani hadin kai ta yadda zamu
cimma burinmu na aure, dan a gaskiya ina cikin
matsanan cin hali nasan ki tun ran da Allah ya hadani
dake, kuma wallahi Allah kadai yasan halin da nake
ciki ki taimaka, ni dai nasan sonki Allah ne ya jarrabeni
da shi ta yadda banajin zan iya hakuri dake, na galla
masa harara lallai kana cikin wahala toni bari ka jima
kwata-kwata ana kaunar ka bana son tunda dai haka
kake son kaji ko? Nayi maka hannun ka mai sanda ka
gani ka wane irin mutum ne banajin ko ana yin dole?
Ban ma tsaya naji me zai ce dani ba na shige cikin gida
na basrshi yana faman kirana.
Anti ta ce har ya tafi nace eh ya tafi ta ce bake
bace? Eh bani bace to ai kinga haka yafi ni dai na shiga
daki na barta anan gudun karta gane cewa raina a bace
yake tun daga ranar bai kuma zuwa basai kuma gashi
yau Akaka Aishat ta zomin da wani labarin daban, tun
lokacin da Kaka Aishat suka fadamin wannan maganr
kwata-kwata na rasa abin dayake yi min dadı, hankali
na a tashe yake kullum cikin kuka bani da aiki daya
wuce kukan, hakanan bani da inda zanje inji dadI inba
wajen kawata Bebi ba.
*
lallai Idon ki kenan sai yau akeganinki yau kika
tuna dani ko dai batan kai kika yi ne? nai dariya nace
kai Bebi wadannan tambayoyi haka ai sunyi yawa,
wanne irin batan kai zanyi sai kace wacce bata san
gidan ba, ai gani nayi kwana biyu kin yada ni ne?
wallahi Bebi ina son zuwa kinsan komai sai Allah ya yi,
yanzu ma wata gagarumasr matsala nake fuskanta
shiyasa nazo kiban shawara.
Ameerah ta kwashe duk halin da ta shiga ta
gayawa Bebi tai ajiyar zuciya ta ce Ameerahwallahi ni
nama rasa abincewa hakIka kina cikin babbar matsala,
to amma ina ganin mai zai hana ki nemi goyon bayan
Atinki,tunda naga tana jida ke, na dafa kirji na nace
bebi rufan asiri duk yanda kike zaton wannan lamari ya
wuce nan, Anti fa da bakinta take cewa wai indai na
bijirewa wannan maganar wai zamu raba gari ba ni ba
ita don bazan janyo mata musiba ba tana zaune lafiya,
Bebi ta ce ito dama maganar iyaye ai ba abin bijirewa
bane Ameerahshawarar da nakeso inbaki shine kibi
maganar iyayenki