sassauta mun shi ya sa na zo in
yi godiya."
Gaba daya uka yi dariya.
Wuni suka yi suka kwana sannan
washegari da safe suka kama hanya suka tafi
67
Hafsat C. Sodangi Du Kamar Wuya 2
bayan Nura da matarshi sun yi musu alheri mai
yawa.
Watanni shidan farko na zaman Nana
cikin dangin Nura ta yi amfani da hikimominta
wajen janyo 'yan uwanshi a jikinta ta yi matukar
yin kokari wajen kyautata mu'amala a
tsakaninsu don haka sai ya zamo an samu
shakuwa mai yawa a tsakaninsu ta kuwa zamo
mowa kwarai a wajen mahaifiyarshi kullum a
cikin yi mata aike take ita kuwa Nana duk abin
da ta girka sai ta aike mata dashi nura ya yi
matufar jin dadin yanda Nana take tafiyar da
al'amura tsakaninta da 'yan uwanshi.
Ita kuwa Nana ta na ta Gangaren ba ta da
wata miskila tsakaninta da mijinta da kuma 'yan
uwansu in ban da wasu da ta riga ta fahimci
babu wani abin da za ta yi ta burgesu don kuwa a
zahiri suka nuna mata ita din sun tsaneta don
haka babu wani abinda za ta yi ta burgesu tana
zaure tare da Nura da hantsi cikin furanni, shan
iska suke yi Nana ta kalli Nura cikin nutsuwa da
girmamawa, ta ce "Ni in ba za ka damu ba in
tambayeka mana."
Ya zuba mata ido yana kallonta cikin
sakin fuska ya ce "Haba Nana me za ki
68
Da Kamar Wuyu 2 Hafvat (. Sodangi tamabyeni ni kuwa in samu damuwa akai."
Ta cc "Ni da so nakc in san me ke
tsakaninka da Naja'atu?"
Nura ya kalleta ya cc "Mc ki ka gani?"
Ta dan dago ido ta kalleshí ta yi kamar ta
gaya mishi abinda ta ganin sai kuma ta fasa ta ce
"Babu komai ni dai kawai na dan yi zaton ko
akwai wani abu ne shi ya sa na ce barí in
tambayeka."
Ya ce "To babu komai Nana kc dai kawai
in kin ga wani abu ne sai ki gaya min haka nan
in ta miki wani duka kina iya yi min bayani."
Ta ce mishi ba ta mun komai ba suka cі
gaba da hirarsu.
Naja'atu ta ci gaba da zama matsalar Nana
a dalilin yawan shiga sabgoginta da take yi sai
dai in Nana ba z ata shiga cikin gidan su Nura
don gaida mahaifanshi ba, sai ta san abinda ta yi
mata na wulakanci, in kuma magana ta yi to za
ta san yanda ta yi ta karyatata duk kokarin Nana
na ta gyara mu'amalar a tsakanin su abin va
gagara tun abin baya damunta sosai har ya soma
damunta a dalilin ba ta san menene laifinta a
wurinta ba, ana cikin haka kanwar Nura karama
Nusaiba wacce take sakandire aji uku ta zowa
69
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Nana hira ta dawo daga makaranta tana falo tare
da Nana suna hira lokacin da ta ga Naja'atu ta
shigo cikin gidan kai tsaye ta wuce falon Nura
ba tare da ko kallon inda suke ta yi ba balle ta
gaishe su, Nusaiba ta bi ta da kallo ta ja tsaki
tare da zobara baki Nana ta ce "Lafiya irin
wannan tsakin?"
Nusaiba ta ce "Haushinta nake ji lokacin
da ake so a hadata aure da Yaya Nura kememe
ta ki amma yanzu ta ga ya je ya auroki sai bakin
ciki take yi, tana wani kamun kafa a wurin
Hajiyarmu don ta matsawa Yaya Nura ya yarda
ya aureta, itakuma Hajiya ban san dalili ba duk
abinda take so itama sai ta tayata son shi."
Nana ta kalleta cikin nutsuwa ta ce "Dama
ba Hajiyar ce ta haifeta ba?"
Nusaiba ta ce "A'a ba ita ba ce ita 'yar
Kanwar Babanmu ce amma a wurin Hajiyar ta
girma lokacin da ta ce ba ta son Yaya Nura ita
Hajiyar ce ta ce kar a matsa mata yanzu kuma ta
dawo tana so kuma wai tana tayata."
Nan da nan kishi ya kama Nana sai dai ta
yi kokarin dannewa ba tare da ta yarda Nusaiba
ta gane ba, lokacin ne kuma ta ji dadewar
Naja'atu wurin mijin nata ya dameta nan take ta
70
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
mike tanufi falon mijin nata don ta ga abinda
take yi sai kawia suka gamu a hanya tana fitowa,
yayin da ita kuma Nana take shiga ciki, murmushin da taje ta tarar a fuskar Nura shi ne
abinda yakara bakanta mata zuciya, maimakn ta
zauna sai kawai ta juyo za ta dawo wurinta da
sauri Nura ya kirata "Zo mana Nana kin shigo
kuma kin juya, ba tare da kin ce min kmai ba,
ina ce dama wurina ki ka zo?"
Ta ce "A'a na dai shigo ne kawai." Ta ci
gaba da tafiyarta, ya yi maza ya tashi ya bi
bayanta ya lamota "Zo mana Nana zo ki gaya
min me ya fata miki rai na ga yanayin fuskarki
"
ya caıza.
Ba ta amsa mishi ba haka nan ba ta iya
dago fuska ta kalleshi ba saboda takaicinshi da
ya kamata.
"Menene bebina?" Ya fadi hakan cikin
muryar rarrrashi "Zo ki ji, zokı gaya min abinda
ya dameki ni ne? Ni ne na yi miki laifi?"
Та се "Вa ka mun komai ba kawai dai
mu'amalar da ke tsakaninmu ne na ga kana nema
ka canzata."
"Da na yi me bebina?" Cikin sauri ya yi
tambayar. Ta dai bar maganar ta ce mishi "Mu
71
DàKamar Wuya 2 Hufsat C. Sodangi
bar maganar kawai."
Taljuya ta nufi kicin dinta, "Zo Nusaiba,
zo mu je ki tayani girki kin ji."
20 d Nusaibu ta bi bayanta da sauri yayin da
shima Nuraya shiga kicin din "Jeki gida
Nusaiba yi sauri in kin je ki ce da Hajiya ina
gaishe ta, nima ina nan zuwa."
Nusäiba ta ce mishi "To." Tana fita Nura
ya kalli Nana ya ce mata akwai alkawari a
tsakaninmu 'Nana na gayawa juna gaskiya don
haka ban ga dalilin da zai sa in ganki a wani
yanayi da ban saba ba sannan in tambayeki
menene ya faru ki ki gaya mun gaskiya, kin ga
ke nan ke ce ki ke nema ki kawo wani canji a
tsakaninmu in kuwa ki ka yi haka ina ganin ba ki
yiwa zamanmu adalei ba."
Nana ta daga ido ta dan kalleshi nan da
nan kuma ta kawar dá fuskarta ta ce "Idan ma na
yi-hakan bani ce na canża yanayin zaman ba kai
ka fara don kuwa kaine farkon wanda ya fara
boye min gaskiya don haka kmai na yi tayaka na
AOMI BES 8ទ ចទ G បបយ
Ta ci gaba da aikinta, yana taimakonta har
kemala Kamar kullum ta jawo foodflask
fita inai kyautå bude ta cikashi da abin da ta
72
Da Kumar Wuya 2 Hafsar C. Sodangf girka sannan ta kira mai aikinta ta mika mata ta
cemaza a je a kaiwa Umma ta karba cikin sauri
takama hanya, ta fita ta jc kaiwa ita ma Nana ta
dawo kicin din ta debe abincın ta je ta shirya a
falon Nura ta dawo mata falon ta baro mishi
abincin shi kadai tana zaune tana tunanin
maganganun da Nusaiba ta yi mata, sai kawai ta
sake ganin Naja'atu ta zo za ta sake wucewa ta
shiga inda nura ya ke sai kawai ta mike cikin
sauri ta ce mata "Ji mana baiwar Allah rinka yin
abu kamar kina da hankali kin ganc? Daina
shigo min gida haka kawai babu sallama."
Naja'atu ta tsaya ta yi mata wani
lalataccen kallo ta ce mata "Gidanki fa ki ka ce
min? Kina nufin nangidannaki nc?"
Nana tace "Kwarai kuwa ina,kuma da yancin
hanaki shiga cikinshi musamman da yake na lura
ba ki da hankali."
"To ai kuwa yanzun nan zan nuna miki
rashın hankalina." Ta daga hannu da nufin kaiwa
Nana mari a fuskarta ta yi maza ta cafe hannun
nata ta murdeshi da iya Karfinta har sai da ta
kwallara kara abinda ya sanya Nura fitowa cikin!
sauri yana zuwa ya ga abin da ke faruwa cikin
sauri ya ce "Saketa Nana ba ta yi musu ba la
73
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
saketa, yi maza ki fita min daga gida ya baiwa
Naja'atu umarni "Ko ba ki ji abinda nake fada ba
na ce yi ki fice min daga gida in daina ganinki."
Ba ta Gataloakci ba ta sa kai ta fita tana
sharar hawaye a dalilin wai Nura ya shigar wa
matarshi fadan.
Nana ta koma wurin zamanta ta zauna
shima Nuran ya bi ta ya jeya samu uri ya zaına
yanı mata magana "Kar ki rinka daka ta wannan
yarinyar Nana in kin lura da kyau za ki ga ita din
tamkar daban take a cikin gidan."
Ba ta tanka mishi ba ta yi shiru har yayi
ya gama ba ta ce mishi komai ba ta tashi ta tafi
wurinta.
Kwana biyu bayan nan Nana ta yi mata
tana zaune a gabanta cikin ladabi yayin da
Naja'atu ke kwance a jikin ta tana ta faman
shagwaba, Hajiya Kubra te kalli Nana, fuskarta a
daure ta ce mata "Kiranki na yi in ji shin da
gaske ne wai kin hana Naja'atu zuwa wurin
wannan yaron?"
Nana ta sunkuyar da kanta kasa ta yi shiru
ba tare da ta dago kai ta kalleta ba balle har ta
bude baki ta ba ta wata amsa. Sai ta ci gaba da
cewa.
74
2
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangl "Shi mijin naki bai gaya miki abinda yake tsakaninshi da Najar ba ne? Ita Naja'atu da ki ke
ganinta ko babu aurc tsakaninta da shi wantane
don haka babu wata matar da ta isa ta shiga
tsakanin su to balle ma kuma auren ki da ya yi
ba zai hanashi auren 'yar uwarshi ba, tunda suna
son juna ko jiya kuma da na tuntubeshi a kan
maganartaya amince da auren don haka daga yau
sai yau kar in ji kar in gani kar in sake jin wata
magana ta sake tasowa na cewar kin hana wani
shiga gidan balle kuma Naja, wacce itama nan
ba da dadewa ba za ta shigo, in kin kalli wannan
yaron ma da kyau ai kin san ba zai yiwuya zauna
da ke ke kadai ba kamar yanda ki ke zato tunda
dangine dashi bila adadin tun daga wurin
Babanshi har nawa to ya ya za a yi a ce ya rasa
auren kowa a cikinmu sai ya je waje ya auro
bare? Kuma ace wai da ita kawai zai zauna ai
aurenki dashi kawia an tayashi so ne saboda shi
dan yau tayashi son abinda yake so ka ke yi in
har kana son zama lafiya da shi in ya so daga
baya in an nutsu kaima sai ka sashi ya yi kaima
kan da ka ke so din don haka kar in sake jin
wata magana a tsakaninku, gara tun wuri ki yi
tattalin da za ku zauna lafiya in ta zo in kuwa ba
75
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodungi
ki yi hakan ba to duk abin da ya biyo bayan haka
ke ki ka jawo in fatan kin ji ni?"
Nana ta amsa "Na ji Umma na gode." Ta
mike za ta fita, Naja'atu ta yi maza ta cc mata
"Ai tashi za ki yi ki fita tun ba a sallamcki ba?"
Ba ta saurareta ba ta yi tafiyarta tana shiga
cikin falnta Nura ta samu a tsaye yana ta faman
zirga-zirga a falon alamar dai cikin bacin rai
yake yana ganinta ya kara tsuke fuska cikin
muryar tashin hankali ya soma tambayar ta "Ina
ki ka fito?"
Kan ta ce mishi komai sai ya ce mata
"Juya kawai ki koma inda ki ka fito don ba zan
lamunci irin wannan sakarcin ba."
Nana ta tsaya ta yi galala tana kallonshi
cikin mamaki da kaduwa ya sake daka mata
tsawa mai tsananin karfi ya ce "Kauce daga nan
ki bani wuri na ce ko ba ki ji ni ba."
A hankali ta bude baki ta ce mishi "Na ji,
yanzu kuma zan yi hakan." Tana fadin hakan ta
yi maza ta juya cikin hanzari ta fita ta bar gidan.
Mu littafi na uku don jin karshen
labarin.
gamu a
Sai an jima,
Taku Hafsat C. Sodangi.
76
AKARA CITY
OKSHOP
027614161
Tsarin Bango:
ANKA - GRAPHICS FAGGE
07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels