kyautata mishi zan yi komai don in
faranta mishi ba zan lamunci ganinshi cikin
Gacin rai ba, balle har in juri bata mishin."
Zuwairiyya ta ce "Saboda an muku auren
soyayya ne ya sa hakan."
Tasce "E zan iya yarda da maganar ki zan
kuma iya gaya miki cewar ni ko auren dole aka
yi min ba zan lamunci irin zaman da ku ke yi ba,
tunda na san masu rubutu: lada da alhaki ba
zasu dauke alkalamin rubuhinsu a kaina ba don
kawai ni an yi min auren doie."
Nura ya yi sallama duga bakia kofa ta yi
26
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. SodangI
maza ta tashi ta leka, "Me da me za akkawo
muku zan tura ne a je a yi muku take away din abinda ku ke bukata."
Nana ta ce "Ai ni girki zan yi, yanzun nan
mazamu fito mu shiga kicin ina girki muna
hirarmu."
Ya ce "Haba Nana wacce amarya ce ta ke
shiga kicin daga kwana biyu?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Sai dai in ba
ta matsu angon nata ya rinka soma kwasar garar
da ta zo mishi da ita ba."
Ya ce "To ai shi kenan Nana ina fata dai
kin san muna da yawa don ki san abinda ya
kamata ki girka, kin san ba zai yiwu in cioni
kadai in bar abokaina ba."
Та се "Haka ne."
Yana fita, ta kma cikin dakinta ta ce "To
Zuwairiyya mu je kicin ina girki muna hirarmu."
Zuwairiyya ta ce "Kai ke kamida dorawa
kai dawainiya ki ke ki bari kawai aje akkawo
mana abinda zamu ci kin wani ce ke za ki girka."
Nana ta ce /"E aini da ki ke ganina in har
akwai abinda ba zan iya lamunta babbai wrce
barin mijina ya rinka cin abincibawwajebbaTa
kowane hali zan tsare. mishi yunwar ciknshiba
27
ryaplardDa Kamar Wuyуа 2
vcikin gida."
Hafsat C. Sodangi
hZuwairiyya ta galla mata harara ta cе "Тo
in kuma mai son ci a wajen ne fa ya ya za ki yi
mishi?"
Nana ta ce "Haba Zuwairiyya ya ya za a
yi namiji ya ajiye matarshi ta aure a gida wacce
ya aureta saboda yana sonta, sannan kuma ya
zamo bai son cin abincinta, in har ta iya yin
abincin? Kin ga dai in saukin kashe kudi ne ya fi
in nutsuwa ne ya fi, in jin dadi ne ma haka,
tunda za ka rinka ci ne ana tarairayarka, to ai sai
mu je kiçin din in ji Zuwairiyya."
Suka fito suka nufi dakin Umma Talatu
kafin su shiga kicin din don fara girki bayan sun
gaisheta Nana ta ce "Umma girki nake so in yi
shi ne na ce bari in tambayeki me Baba ya fi son
ci?"
Umma ta yi murmushi ta ce "Shi kam
Malam ai in don ta shi ne to kullum a yi tuwo shi
bashi da wani abincin daya fi dadi a wurinshi sai
dai a yanzu ina ganin na riga na dora mana
abincin rana yanzunnan za ku fara jin kamshin
shi, yana tashi da zarar tukunyar ta fara tafasa,
dambun zogala ne ga kuma kunun zaki nan dana
hada na saka a freach don ya yi sanyi."
28
Du Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi Ta yi maza ta sa hannu a freach din ta debo kunun zakin a ko kofi ta mika musu suka karba suka sha suna fadin "Kai ai kuwa ya yi dadi ga kayan ya ji ya ji gashi ya yi wani gardi,
suka kuma bai yi yawa ba."
Umma ta ce "Eh ai mijin na ki ba
ma'abocin shan zaki ba ne, kafin in fahimceshi
ranbada mishi suga nake yi cikin duk wani
abinda zan ba shi sai in ga bai sha ba ya dawo
dashi idan na yi magana sai ya ce ya koshi ne,
daga baya ne sai na shiga cancanza mishi yau in
na ba shi mai zaki gobe sai in ba shi mara zaki
sai in ga ya sha, daga nan sai na gane to haka
muka yi ma a kan dandanon gishiri da yaji."
Nana ta zauna nan suna hira da Umma da
Zuwairiyya cikin hikima kuma wasu al'amura na
mijinta take kokarin sani wurin Umma Talatu
wacce har a lokacin ba ta san dangantakar da ke
tsakaninsu ba.
Tunda Umma Talatu ta hutar da su Nana
aikin abincin rana sai suka yi shirin yin na dare
sai da suka idar da sallar La'asar, sannan suka
shiga kicin din su.
Zuwairiyya ta kalli Nana da ke kokarin
harhada kayayyakin da za ta yi amfani a su ta ce
29
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
nnata ai kuwa dai ba haka na ga gwanayen girkin
suna yi ba, inz asu fara girki alhali da wani a
kusa da su."
Nan ata kalleta ta ce "Me suke yi?"
Zuwairiyya ta ce "Sai sun lissafa abinda
za su yi amfani da su sannan su fadi lokacin da
girkin yake dauka, kan ya kammala."
Nana ta yi murmushi ta ce "To ai ni dama
ban ce miki ni din gwana ba ce, dan dai wanda
zan yi in tarairayi mijina da bakin da zasu shigo
cikin gidana shi nake gaya miki to amma tunda
kin bukaci sanin abubuwan da zan yi amfani da
su to bari in lissafa miki su kamar yanda ki ke
kallnsu, kammale, anan zan yi miyar agushi ne
da zan duddunkulashi don in kara kayatar da
miyar tawa tare da tuwon semovita, don haka sai
na tanadi kayayyakin amfani kamar haka:-
(1) Naman saniya, gwargwadon bukatarki
(2) Busasshen kifi kato guda daya ko
kuma madaidaita guda biyu.
(3) Alayyahu shima gwargwadon yawan
miyarki tunda ke ki ka san yawan iyalinki, sai
tumatur, attaruhu, albasa, tattasai da nikakken
agushin sai kuma manja, maggi da gishiri, kuma
don kara dandanoE ty
30
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi Nana ta kalleta cikin murmushi ta ce "Ina fata kin fahimta."
Zuwairiyya ta gyada kai ta kuma bude baki ta ce "Na fahimta."
Ta ce "Tо tunda kin fahimta bari in ba ki
aikin agushin nan rabashi kashi uku ki dauki
kashi biyu ki yayyanka wannan albasar a ciki
gutsi-gutsi. Ki maggi sai ki hada ki yi ta
mutsuttukawa har sai mia ya fito, sannan ki
rinka mulmulawa amıma 'yan kanana kina
ajiyewa." Anan ta sake mika mata wani plate din
da take bukatar a saka a ciki ita kuma ta koma
kan aikinta inda ta dora tukvunya a kan murhu ta
zuba manja tana kokarin harhada kayayyakin da
take bukata, bí da bi kan ka ce menene wannan
tuni gidan ya gauraye da kamshin miyar Nura
sai kaiwa da kawowa yake yi, yana tambayar har
yanzu ta a gama bane? Gara fa n yi a gama tun
katin muiaise su watse a waje, don bai kamata in
ci abincinkadai ba
Nan da nan Nana ta tuka tuwon semovita
da ya yi matukar vir kyau, har ya zama tamkar
sakwara ta zuba mishi na su ya fita da su don
neman wadanda za su rayáshi ci, a cikin gida
kuwa ta zubawa Umma Talau da mijinta suma
31
Da Kumu IWuya 2 Hafsat C. Sodangi
suka dauko nasu suka shiga daki suna ci suna
hirarsu, sai da suka yi sallar Magariba sannan
Nura ya dauki shatar tasi ta maida Zuwairiyya
gidan mijinta, shi kuwa ya shigo daki ya tasa
amaryarshi a gaba yana ba ta labarin yanda aka
yi wawason abincin ta a waje, ita kuwa Umma
Talatu sai cewa ta yi "Ke Nana ni fa na gai da
sintirin karawa Malam miya na dauke tukunyar
gaba dayanta, zan kai mishi."
Nana ta yi murmushi ta ce "To Umma."
Kwanakin amarcin Nana a gidan kwanaki
ne da aka kwashi garar abinci a gidan da yake
daga Malam har angon nata maciya tuwo ne,
yawancin girkin nata sai ta tafi kan yawan tuwo
kala daban-daban, tuwon acca, tuwon alkama,
tuwon alabo, tuwon dawa, tuwon samobita,
tuwon shinkafa, da kuma tuwon amala, ko
wanne kuma ta kanyi shi ne da irin miyar da ta
dace a ci shi. Wannan dalili ya sanya gidan nasu
ya zamo mai dadin zama kwarai, kullum gari ya
waye in Nura ya gama abinda zai yi ya fita itamа
sai ta kammala abinda za ta yi ta fito wuria
Umma Talatu ta tayata a ya kanta su zauna
Umma ta dan yi mata hira in kuma lokacin yin
abincin rana ya yi sai Umma ta tashi ta dora
32
이
Da Kamur Wuya 2 Hafsat C. Sodangi musu girki inda ta kan yi musu abincin gargajiya inda nan ma Nana take tayata tana kuma kara sa ido sosai akai don ta lura mijinta mai son irin
wannan cimar ne, wani lokaci su yi gauda wani lokacin dan wake wani lokaci dambu, na zogale ko na yadiya wani lokaci alala da dai makamantansu ga shi kuma itama Umma gwana
ce kwarai akan irin wannan girkin.
Nana ta cika wata guda a gidan Nura a
lokacin nan kuwa ta yi matukar canjawa ta yi kyau ta yi haske, gashi ya yi hip hip kwance a
jikinta tamkar wacce sanyin A.C. ya ratsata, ta yi kwalliyarta sai wani kamshi ke fitowa daga
jikinta ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce mishi
"Amma dai ai ka san karatu mai yawa ne yake
wuceni ina zaune ba na komai kullum kuma na
yi maka magana akan ina so in fara zuwa sai ka
ce wai in dai kara yin hakuri in saurareka
tukunna."
Ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata "Ba
kya komai fa ki ka ce mun Nana wato duk
al'amuran nan da suke afaruwa da duk
dawainiyoyin da ki ke yi a gidan nan ba komai
ba ne sai kin je makaranta? Ban ce miki zan hanaki karatun ki ba tunda na yi alkawarin
33
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
barinki ki gama to amma fa ina so ki sani
karatun kawai za ki yi babu maganar yin aiki, ni
a wurina wannan dawainiyar da ki ka ce ba
komai ba ne ta fi mun ki rinka fita kina yin wani
abu a waje, kin gane?"
Ta ce mishi "E."
Yá ce "To yanzu ma ki kara saurarona
don ina ganin kamar ke da zuwa makaranat sai
mun koma mazauninmu in mun koma wurin
iyayena tukunna amma anan amarcinmu kawai
zamu ci kuma da so nake mu yi sati shida zuwa
wata biyu kafin mu tafi ko me ki ka gani?"
Nana ta ce "Ni duk yanda ka fada daidai
ne a wurina."
Ya yi murmushi ya mike zai fita ta daga
ido ta kalleshi ta ce "In ka fita za ka dade ne?"
Ya juyo ya ce "Menene?"
Ta yi shiru ta sunkuyar dakanta kasa ya ce
"In ba kya son fitar nawa in dawo in zauna."
Та се "А'a dama na ce ko za ka bari in je
gida ne? Ina son ganin su Rahamä."
Ya ce "A'a bari in je in sa a kwo miki su."
Та се "To."
Zama mai dadi ake yi tsakanin Naza da
mijinta da kuma Umma Talatu, itama da nata
34
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi mijin dan tsukukun dakin da take zaune a ciki bai rage mata komai ba na daga farin cikinta da kuma cin amarcin ta, kowane lokaci cikin
wasannin faranta rai suke da ita da mijinta ga
kuma su Umma Talatu da suke ji tamkar su
lasheta don tsananin kauna, ita kanta Antinta
kusan kullum sai ta yiwo mata aike duk girkin da
ta yi sai ta sa an zuba a kwano an kawo mata sai
dai matsalar kawai ita ce ba ta aiko su Rahma da
'yan uwanta sai ko masu aikin gidan ta kawai
suma kuwa suna zuwa zasu bayar su juya saboda
ta gaya musu kar su je su zauna su dade ko da
kuwa ta nemi su dan zauna su huta ko su yi mata
hira zasu gaya mata ta yi hakuri Anti babba ta ce
kar su dade.
Ranar Laraba da yamma suna daki suna
hirarsu Nura ya kalleta ya ce "Yau dai in kin
gama girki da wuri kin yi wanka ki ka mun
kwalliya in har na ga ta burgeni kwalliyar ta ki,
to zan kaiwa Anti ke itama ta ta yi gani."
Nana ta yi murmushi mai gamsarwa cikin
nuna alamer jin dadi da farin cikin jin
kalaminshi ta ce "Kai ka ce yau har da su jan
baki ka ke son ganin na shafa?"
Ya ce "E in kuma ki ka yi rashin dace
35
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
kalar le66anki ya fi kalar jan bakin burgeni in ce
ban zuwa ko ina."
Da daddare Nana da Nura suna zaune a
gaban Alhaji Sani a cikin hamshakin falon shi
shi kuma yana cin dambun naman kajin da Nana
ta zo mishi dashi, "In ce ko dai ke da kanki ne ki
ka yi wannan dambun ba yi miki aka yi ba?"
Nura ya sunkuyar da kai cikin ladabi ya
ce "Aí gwanar girki ce."
Alhaji Sani ya yi murmushin jin dadi ya
kara yafa dambun a bakinshi yana taunawa yana
kuma yi musu nasiha, kan sha'anin zaman aure,
Nana ta tashi ta shiga cikin gida bayan ya ba ta
izinin yin hakan ta nufi wurin Antinta, tana barin
falon Nura ya kalli Alhaji Sani cikin girmamawa
ya ce "Baba na zo wurinka ne don neman
izininka in ka amince ina so zan koma gida
gaban iyayena."
Cikin sauri Alhaji Sani ya kalleshi ya ce
"To Nura in za ka koma wurin iyayenka sai ka
nemi amincewata?"
Ya sake sunkuyar da kai cikin ladabi ya
ce "E, saboda ban yi bayanin hakan a farko ba,
ban ce ba ánan zamu zauna da ita ba, shi ya sa na
ce to barí in nemi izininku kan tafiyar tamu don
36
Da Kamur Wuya 2 Hafsat C. Sodangi kar ku ga tamkar so nake in fiddo da wani halin
da ba a san dashi ba."
Alhaji Sani ya ce "Ko kadan Nura babu
mai fadin haka, itama ce ana daura maka aure da
ita ai shi kenan kuma ta zama mallakarka
al'amarinta yana hannunka don haka kana da
cikakken iko a kanta in har kuna bukatar tafiya
za ku iya yin hakan."
Ya kara sunkuyar da kai kasa cikin nuna
alamar girmamawa ya ce "To Baba na gode
Ubangiji Allah ya kara girma."
A dakin Hajiya Salma kuwa. kukan
shagwaba Nana ta zauna tana yi, kan wai
Antinta ta hana yara zuwa wurinta."
Hajiya Salma ta yi murmushi ta ce "To
Nana sai ki yi hakuri wai ni a nawa tunanin bai
dace a rinka zarya agidan amarya ba balle ku
wannan daki na ku."
"A'a gaskiya ni ban yarda ba sauran yara
da suke zuwa fa?"
Ta ce "E ai shi ne na ce ki yi hakuri Nana
sa rinka zuwa miki hirar."
Ta ce "Uhun."
Hajiya Salma ta kalleta cikin murmushi ta
ce mata "To yi maza ki share hawayen naki kar
37
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
angon ya shigo ya sameki kina kuka, ya zaci ko
bugar mishi ke na yi."
Nana ta yamutsa fuska ta ce "To ina
ruwanshi?"
Hajiy a Salma ta bude baki ta ce "Kin san
matsayin miji kuwa Nana? Shi miji da ki ke
ganinshi matsayi mai girma ne dashi daga yin
aure sai ka zama a karkashin ikonshi duk wani
abu da za ki yi zai zama da yardarshi ne za ki yi,
haka nan shi ne wanda ya zamar miki dole ki yi
mishi biyayya don kuwa an ce aljannar ki tana
karkashin tafin kafafuwan shi ne kin gaue?"
Nana ta gyada kai tare da cewa "E na
gane."
Hajiya Salma ta ci gaba da cewa "To
yanda aka ce mace za ta yi wa mijinta biyayya
ne ta samu daraja ta shiga gidan aljanna haka
nan aka ce shi namiji tashi aljannar tana daga
irin biyayyar da ya yiwa mahaifiyarshi ne kin ga
kenan in kina son mijinki sai ki taimakeshi ya yi
wa mahaifiyarshi biyayya, in kun ga ya manta
bai rnata wani alherin ba ki tuna mishi in ta bata
muku ku yi hakuri saboda kin san tana da
matsayi mai girma a wurinshi na kuma dai san
tunda kina son mijinki ai za ki bi yanda ku ka yi
38
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi rayuwar duniya tare ku yi ta lahira ma haka ko?" Da sauri Nana ta ce "Kwarai kuwa Anti, tunda dai wannan rayuwar ma 'yar kankanuwa
ce kwarai, rayuwar lahira ita ce rayuwa ta har abada."
Hajiya Salma ta ce "Yauwa Nana gara da Allah ya sa ki ka fahimci haka kin ga sai hirar
tamu ta fi dadi, yanzu shiga falo da na yi Alhaji
ya gaya mui Nura yana so zai koma garinsu
wurin iyayenshi ya kuma fadi cewar yana da
uwa da uba, 'yan uwa maza da mata, kakanni da
iyaye shi kanshi mahaifinshi matan aure uku ne
da shi, kinga kuwa in haka ne ba sai na gaya
miki cewar yana da dangi ba ko kuwa?"
Nana ta sunkuyar dakai cikin faduwar
gaba ta ce "Haka ne."
Та се "То in kun je ki zauna da su bisa
amana da kyautatawa ki dauki iyayenshi tamkar
naki haka nan 'yan uwanshi naki ne in ki ka
dauki hakan za ki sawwakewa kanki mu'amala
dasu zamanku zai yi dadi, sabanin in ki ka dauka
su din nashi ne shi kadai kin gane?"
Ta sake cewa "E, to ga dai mijinan Allah
ya yi miki baiwa dashi Nana ko sanda ya ke
zuwa gidan nan a matsayin gurgu na gaya miki
39
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodang!
shi din ba karamin baia aka yi miki da shi ba, to
balle yanzu da ya bayyana mana cewr ba gurgun
ba ne ki tattali mijinki ta yanda kullum soyayyar
ku za ta rinka karuwa maimakon raguwa, don
kuwa duk yanda ma'aurata suka kai da son
junansu matukar za su zamo masu musgunawa
junansu wata rana soyayyar za ta ragu don kuwa
ita zuciya an halicce tane da son mai kyautata
mata ko ba ta son mutum in har zai dimanci
kyautatawa mai ita yau da gobe to wata rana zai
wayi gari ya ji yana son mai kyautata mata din."
Nana ta dan yi ajiyar zuciya ta ce "To
amma dai ai za ki rakani ke da su Rahama ko?"
Hajiya Salma ta ce "A'a ba sai mun bi ku
yanzu mun tafi tare ba, in kun je ma a hankali in
an kwana biyu sai in zo in ga wurin naku."
Nana ta ce "A'a ni dai kawai mu je tare
Anti amma kwana biyun nan haka ki ka ce sai an
kwana biyu ki zo ga shi har yau din nan ba ki zo
ba, sai da mu muka zo."
Ta yi murmushi ta ce "To dama kwana
biyu wurin Hausawa, Nana ai ba gobe da jibi ake
nufi ba."
Nura ya yi sallama ya shigo falon Hajiya
Salma ta shiga yi mishi sannu da zuwa da
40
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi gaisuwa irin ta surukuta ta yi mishi fatan aleri kan shirinshi na komawa gida gaban iyayenshi bai bata lokaci ba ya tashi ya koma falon Alhaji
Sani saboda lurar da ya yi Hajiya Salma
kunyarshi ta ke yi sosai ba ta iya sakewa a
gabanshi don haka shima bai dadewa sosai a
gabanta.
Bayan fitarshi ta kalli Nana cikin jin dadi
ta ce "Kin yi aurenki mai dadi mai ban sha'awa
kin zabi mijinki ba don komai ba sai don kina
sonshi kawai saboda Allah, wannan shi ne zabin
aure na gaskiya ba don kyau ko dukiya ba.
Kuskure ne a gina aure da wadannan dalilan don
kuwa dukan su suna gushewa ko da yake dai ba
laifi aka yi ba in an yi saboda su din."
Alhaji Sani ya yi sallama ya shigo cikin
murmushi yana tambayar ina matar gidan take?
Hajiya Salma ta taya shi murmushin tare da
fadın bayan wacce take zaune gabanka? Ya
shiga rarraba ido yana kalle-kalle cikin raha da
nishadi wai nemanta yake yi, ya ce "Au ashe ke
ce anan sai na ganki kamar wata 'yar yarinya
budurwa, shi ya sa ki ka so ki 6ace mun."
Ta yi dariya ta cc "Ai ka saba ita kiwa
Nana sunkuyar da kanta kasa ta yi tana jiL Şı.
41
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
saboda ita dama girmamawar da da mahaífine a
tsakaninsu.
Alhaji Sani ya rage murmushin da yake yi
ya ce "To kin dai riga kin ji maganar tafiyar su
Nana?"
Ta ce "E na ji."
Ya ce "To ya ce yana bukatar a yi musu
rakiya don a ga wurin nasu saboda ko za a
bukaci zuwa ganinsu wani lokaci, na nuna mishi
ba sai an yi musu rakiya ba, don karya je yana
dorawa kanshi wani nauyi."
Ya ce "Babu matsala shima yana bukatar
rakiyar don zai so a ga 'yan uwar matar shi sun
yi mata rakiya don haka sai ki samu mutane ko
guda biyar in kun hadu da ke da yara ku kai
goma kar ki yarda ku wuce hakan don tafiyar
jirgi ne ta ce "To ai ma ya yi kokari in dai haka
ne ko can ma wurin su Umma Talatun ai ba za a
rasa masu tafiya ba."
Ya ce "Kwarai kuwa." Yajuya ya tafi, sun
dawo gida suna zaune suna hirar su Nana take
tambayarshi "Amma dai ai za ka kaini gidan
Zuwairiyya ko?"
Ya kalleta cikin nutsuwa ya ce "Me za ki
je ki yiwo?"
42
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Ta ce "Kar ta ji mun tafi bamu yi mata
sallana ba ka ga idan na je na gaya mata na ba ta
hakkinta, mai yiwuwa ta ce itama za ta rakani
mai yiwuwa kuma ta ce ba za ta samu zuwa ba
sai mu yi sallama ko me ka gani?"
Ya ce "Ya yi daidai Nana kin yi tunani
mai kyau gobe in Allah ya kaimu da azahar in
mun yi sallah sai mu je in rakaki ko kuwa?"
Ta ce "To na gode."
Washegari da Azahar suka isa gidansu
Zuwairiyya cikin tasin da Nura ya dauka shata,
shi da kanshi ne ya fita ya je ya kwankwasa
kofar gidan cake garkame ya dawo ya zauna
kusa da Nana yana fadin "Mun zo musu gida ina
ganin a lokacin da bai dace ba, tunda ga motar
maigidan nan gashi babu alamar za a bude kofar
gidan kin san yanzu lokacin barci ne?"
Ta kalleshi ta ce "Y anzu?"
Ya ce "E yin barci tsakanin sallar Azahar
da La'asar ba. Ina ganin ko zmau juya ne kawai
don kar mu takura musu?"
Nana ta yi mazda ta ce "A'a gara dai a
Kara Kwankwasawa kofar kawai."
Nura ya nuna rashin amincewarshi kan
hakan ta yi kamar ta ce mishi ba fa wani shiri
43
Da kamat Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
sukeyi ba don ta samu ya yarda a koma a kara
kwankwasa kofar sai kuma ta ga rashin dacewar
tona asirin kawarta wurin mijinta ta dai dage
kawai kan ko dai aje a kara kwankwasa kofar
gidan ko kuma su yi ta zama cikin tasin su jira
fitowarsu tukuna, ya ce "To bari mu gani in kara
zuwa amma daga wannan ba zan sake komawa
ba don kar su naidani mara hankali."
Ya nufi kofar don ya kara kwankwasawa
Nana kuwa tana zaune cikin motar tana fatan
wani ya zo ya bude kofar don kar su tafi ba tare
da ta ga aminiyartata ba. Yana fara kwankwasa
kofar sai ga Umar ya zo ya bude sanye yake da
doguwar jallabiya kanshi babu hula da sauri
Nana ta zo za ta wuce Nura a hankali ya ce mata
"Kin -gani kb? Ba yanzu ne ya kamata a rinka
zuwa gidajen mutane ba."
Ba ta kulashi ba ta karasa Umar yana
ganinta- ya saki murmushi "Kar dai ango da
amarya ne a gidan namu yanzu?"
Kan wani daga cikinsu ya amsa ya shiga
yi musu sannu da zuwa ya wuce ya tari Nura
cikin farin ciki yayin da ita kuma Nana ta wuce
cikin gidan ta isa dakin Zuwairiyya wacce ke
zaune tana ta faman nazarin littattafanta "Yau
44
Da Kamar Wuya 2
dai da alamar kun shirya."
"Mun shirya me?"
Hafsat C. Sodangi
Da sauri Zuwairiyya ta tambaycta "Kun shirya mana." Nana ta sake gaya mata "In ba haka me ye wannan garkamc kofa haka da tsakar rana?"
Zuwairiyya ta tabe baki ta ce "Mugun
halinshi ne ya motsa bai son a shigo mishi gida."
Nana ta rike baki ta cc "Ke Zuwariyya
kanki daya? Mijinki ki ke kira mai mugun hali"
Kina jin wa'azi kuwa? Kina zuwa makarantar
Islamiyya Zuwairiyya? To gaskiya ki yı maza ki
gyara don kuwa wannan abin da ki ke yi ba za
fissheki ba. Dama kin sauke duk wani irman
kai da ki ke ji in har kin ga ke da kanka ki
yin gyaran ba to ki je gida ki kai magaban
iyayenku in sun san irin zaman da ku ke vi ai za
su yi gyara tunda ba sun hadaku ba ne don ku
rinka wannan mugun zaman a tsakaninku."
Zuwairiyya ta ce "Nana ke nan ke kina
ganin kamar kowane namiji irin mijinki ne mai
saukin kai da saukin mu'amala shi fa dubi yara
ma yanda yake yin mu'amala dasu kai ka ce dai dai dasu yake."
Zuwairiyya ta ce "E kowa da halinshi ba
45
Hafsat C. Sodangi Da Kamar Wuya 2
zai yiwu duk mutane su taru a kan halayya guda
daya ba, to amma don mutum bai yi maka yanda
kake so ba, kuma ba zai yiwu ba ka ce shi din ba
mutumin kirki ba ne ko kuma a'a sai dole ka
dawo dashi bisa halayyar da kai din ka ke so.
Gaskiya ni dama can na sha gaya miki ba zan iya
jurar irin wannan da ku ke yi ba saboda ni din
raguwa ce kwarai akan abinda yake gaba ne ko
makamancin haka to balle kuma yanzu da
kullum da gamu da Anti sai ta yi min bayani kan
matsayin miji a kan matarsa zan fi gane in kai
zancen wurin wadanda suka hadamu su su san
abinda muke ciki in sun ga zasu gyara to in sun
ga ya wuce nan rabawa za su yi shi kenan sai
kowa ya huta."
Zuwairiyya ta ce "To na ji ina angon naki
yake?"
Ta ce "Tare muka zo yana tarc da Umar."
Nura ya kira Nana ta wayar dake
hannunta ta tashi cikin sauri ta nufi falon tana
fadin "Kar dai har zamu tafi ne?" Tana shiga ta
gaida Umar cikin nutsuwa shima ya amsa mata a
fara an ce a dalilin mutunta juna da suke yi duk
cikin kawayen Zuwairiyya Nana ce kadai wacce
yake kulawa har suke gaisawa in ban daita duk
46
Da Kamar Wnya 2
sauran muzurai ne a tsakaninsu.
Hafsat C. Sodangi
Nana ta matsa kusa da mijinta ta yanda
babu mai jin maganar da zai gaya mata ta ce
mishi "Me ya faru?"
Ya cc "Gida nake so mu je."
Ta ce "Tun yanzu ango?"
Ya yi murmushin