jin kalamin ta ya cс "То
ango yana fita unguwa ya dade nc? Kin kuma
san ni mai yawan shan...."
Nana ta yi maza ta ce "Na sani amma in
dai don wannan ne ina zuwa. Nan ma gidanc
Zuwairiyya arniniya ta ce bari in je in kawo ma
akwai maganar da nake so mu karasa don
muhimmiya сс."
Ya ce "To babu laifi." Ta tashi ta koma
dakin "Ni Zuwairiyya ba ki gaida angona ba
balle ki kai musu ko da ruwan sha ne haka ki ke
yiwa bakin Umar in sun zo?"
Zuwairiyya ta tafe baki ta ce "Kin san ba
na shiga falon nashi, shima duk abinda yake yi
in ya ganni bari ya ke yi ya tsuke fuska sai ya ga
na fita sannan ya ci gaba ke Nana ba ki fa san
abinda yakemun ba ne wulakancin tsiya ne fa
dashi, ran nan fa da su Ramla suka zo baya
shigowa nan wurina amma har kofar dakin nan
47
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodang!
ya zo ya tsaya ya cemusu kai ku fito nan. Muka
yi shiru, sai ya daga labulen ya ce da ku fa nake,
ku yi waje yana tsaye a wajen bai tashi ba sai da
ya ga sun fita sai kuma ya ce idan na sake
ganinku a gidana duk abinda na yi muku ku ku
ka jawa kanku."
Da sauri Nana ta ce "Yana da gaskiya
saboda ya san su suke kara zugaki zan kuma
gaya miki in har baki yiwa kanki fada ba, za su
iya yi miki ingiza mai kantu ruwa, suna zuwa
suna tayaki zagin mijinki su kuma kara miki
shawarwari na abinda za ki rinka yi kina
musguna mishi to da kuma hali zai yi ya ce yana
son wata daga cikinsu da kin sha mamaki don
kuwa aureshi za su yi da kuma kin kwashi
kashinki a hannu kuma tunda ba ki iya karbar
bakin mijinki ba to kin ga tafiyata don ba zan
zauna anan ina zuba zance in bar mijina ya
takura ba dama zuwa na yi in gaya miki ya ce
zamu tafi garinsu."
Zuwairiyya ta biyota tana tambayar
yaushe? Ita kam tuni ta nufi falon Umar hira ta
samu suna yi, amına tana shiga ta ce mishi "Mu
tafi." Shima bai bata lokaci ba ya mike Umar ya
biyosu don yi müsu rakiya, har jikin tasin da ta
48
Da Kamar Wuya 2_ Hafsat . Sodangi
kawsu ita kuwa Zuwairiyya biyosu ta yi tana tambayar Nana yaushc ne tafiyar taku? Nana ta
ce cikin satin nan da na zo ne in gaya miki in
kuma roki Umar ya bar ki ki yi min rakiya,
tunda akwai masu tafiya-da yawa to amma na
janye tunda na lurakina da aminan da suka fi ni
masu ba ki shawara kina dauka."
Zuwairiyya ta ce "Wacce sharawa suke
bani?"
Nana ta kalleta a nutse ta ce "Taki 6atawa
mijinki mana. Kina nufin shi bai san abinda yake
yi ba ne da ya koresu a gdianshi? Ni ko mugun
kallo ban taba hadani dashi ba nima kuma
kawarki ce ta dalilinki muka san juna ni dashi
inda haka kawai yake korar mutane da nima
yakoreni, kuma tunda na gane'ni tawa shawarar
da nake baki ba ta miki amfani ba kya ma gwda
aiki da ita don ban kai matsayin hakan ba, a
wurinki to zan kame kaina."
"Ba haka ba ne Nana kin san ko kana son
yin wani abu ma fa sai ka ga fuska."-
Nana ta ce "A'a ba don Allah ki kayi
niyya ba ki yi don kin san Allah zai yi sakayya
akan dukkan al'amuranmu ki ba shi hakkinshi da
ya hau kanki shima in ya dama ya ba ki in bai
49
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
gani ba wannan tsakaninshi da Ubangijinmu shi
kenan to shi kenan Nana yanzu dai zan
tambayeni in zo in miki rakiyar."
Ta yi maza ta ce "Na fasa ban gayyaceki
ba, randa ku ka shirya in ki ka gaya mishi zia
kawoki." Ta yi tafiyarta, ba tare da ta tsaya sun
yi wata doguwar sallana ba.
Da daddare Nura ya shiga dakin Umma
ya sametatana zaune, shima ya nemi wuri ya
zauna suna hira. Umma ta kalleshi tace "Ni jibi
ne ai tafiyar taku ko?"
Ya ce "E Umme:"
Ta ce "Iko sai Allah, Allah Ubangiji ya
nuna mana lafiya yakuma ba ku sa'a."
Nura, ya kalleta cikin murmushi ya ce
"Ku ba za ku rakamu ba ne Umma ke da Baba?"
Umma Talatu ta yi maza ta ce "Rakiya?
Na ji fa an cehar da shiga jirgin sama ko?"
Nura ya ce "E, Umma to ku ba za ku hau
jirgin ba?"
Ta ce "To na ga ana ta hidimar yara wa ke
ta 'yan tsofaffi?"
Nura ya yi maza ya ce "A'a Umma tsoho
kuw. aai shinne yakkamataa yis ta tashi ai mu
addininmu ya mutunta tsoho ya kuma ba shi
50
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
daraja mai girma don haka wanda bai san abínda
yake yi ba shi ne bai san darajar tsoho ba."
Umma Talatu ta yi maza ta ce "Ai fa haka
ne Nura kai kam ba mu da abinda za mu ce maka
sai dai mu roki Allah ya saka maka da alheri.
Tun daga zuwanka gidan nan al'amura suka
sauya mana, rashin lafiyar da Malam yake ta
fama da ita na ciwon kirjinshi duk ya daina ashe
dama duk wahala ce ta yi mishi yawa, mu kam
mun gode da zuwanka yanzu kuma in kun tafi ko
sai yaushe oho?"
Nura ya yi murmushi ya ce "Ai kun riga
kun zama iyayena Umama ba zai yiwu a ce na tafi
na daďe ban zo na dubaku ba, har da hakan nema
ya sa nake ganin yana da kyau in tafi tare da ku
don ku ga wuri akwai 'yan abubuwan da nake so
in shirya muku to amma hakan zai zamo bayan
na sake zuwa ne kar kuma ki yi zaton zan dade,
tunda ma ai ga 'yar unguwar na aura. Kin kuma
san ba zai yiwu Nana ta dade ba ta zo ta ga
Antinta da yara ba."
Umma ta yi murmushi ta ce "Ai fa Allah
ya sanya kauna mai yawa a tsakanin su."
Kwana biyu bayan nan Nura ya kammala
shirye-shiryenshi na komawarshi gida, ita kanta
51
Da Kumar Wuya 2
Hafsat C. Sodangi
Umma Talatu ta gayyaci aminiyarta mai kuli
kamar yanda Nuran ya gaya mata ta nemi wata
cikin aminanta ta yi mata rakiya.
Tun safe ren nan a ke ta hidimomi tamkar
wani sabon bakin akc sakewa yara sun cika gida
sai koke-koke suke yi kowa na fadin zima zan bi
ka Nura, ya tarasu ya yi musu nasiha sannan ya
gaya musu zai tafi da mutum uku a cikinsu don
su bi shi su gano garinshi amma ba zai zabi
masu tafiyar da kanshi ba zai yi rubutu ne ya
watsa cikin kwali kowa ya sa hannu ya dauka
wanda ya dauki tafiya za mu tafi tare dashi
wanda ya dauki hakuri zai bakura ya zauna sai
wani lokacin idan na zo."
Gaba daya suka amince akan hakan, nan
danan ya koma dakinshi na zaure da da yake ciki
ya soma rubutu a guntayen takardu yana
nannadewa ta yanda ba zai bude ba sai in
budewar aka yi, sai da ya rubuta adadin yaran
gaba dayan su sannanya watsa cikin kwali ya
fito ya ajiye a tsakar gida ya koma can gefe ya
zauna kan turmi yana kallonsu suna zuwa daidai da dai-dai kowa ya zo ya dauki guda daya ya
koma gefe yana jiran agama a bada izinin
budewa, don kowa ya ga abinda ya dauka, sai da
52
Da Kamar Wuya 2 Hafsar C. Sadangi
suka gama gaba dayansu sannan Nura ya kawar
da kali ya sake kawo wani kwalin da shi kuma
ya cika shi da mikakkun cnvelope da ya lillikcsu
ya ajiye a inda ya dauke wancan kwalin ay sake
komawa kan wannan turmin ya zauna ya cc
musu "Yanzu zan ba ku umarnin ku bude don
muga abinda ku ka dauka, amma kar kowa ya cс
zai yi kuka ko ranshi ya baci don ya bude ya ga
hakuri sai kawai ya wuceya sa hannu cikin
wancan kwalin ya dauki envelope guda daya
kun gane?"
Suka ce e sun gane ya ce "To maza a
fara."
Nan da nan suka shiga bude takardunsu
suna ganin abinda ke rubuce sai su wuce su
dauki envelope su koma gefe su tsaya har aka
gama mutane uku da suka dauki tafiya suka
ware a gefe sauran kuma suma suka tsaya a gefe
rike da envelope a hannunsu.
Nura ya kallesu cikin nutsuwa ya ce musu
"Na gode muku bisa bin maganata da na yi muku
ga shi mun gama dukkanmu babu alamar bacin
rai a tare damu ko ba haka ba nc?"
Suka ce "Haka nc."
Ya ce "To wannan cnvelope din da ku k
53
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
rike dashi ku je gida ku kaiwa iyayenku kudin
da ke ciki a yi muku amfani dasu a wajen biya
muku kudin makaranta, kun gane?"
Da iyakacin karfinsu suka amsa "Mun
gane yaya Nura mun gode Allah ya saka maka
da alheri."
Suka yi waje da gudu suna rige-rigen
tafiya gidajensu don kaiwa iyayensu alherin da
Yaya Nura ya yi musu, su gani shi kuwa ya
wuce ya ci gaba da shirye-shiryenshi yayin da
sauran yaran uku suma suka nufi gidajensu don
shirin tafiya.
A gidan Hajiya Salma kuwa nan ma
tamkar wani bikin ake yi, 'yan uwa da abokan
arziki sun hadu sai ciye-ciye da tande-tande
suke yi masu tafiya kuma suna ta shirye-shiryen
tafiyar su sai da aka ci aka sha sannan aka
dunguma cikin motoci don zuwa airport, shima
Nura da tashi tawagar can aka samesu.
Tun kafin su tashi Nura ya yi waya ya
sanar a gida don a san yana nan bisa hanya tare
da jama'a don haka suna isa babban filin jirgin
saman garin nasu suka samu an dade da isowa
don taryensu suna sauka a jirgi motocin gidan su
Nura ne suka dauke su zuwa asalin babban gidan
54
Da Kamar Wнуа 2 Hafsat C. Nodung!
su inda 'yan uwa suka tarye su cikin murna da farin ciki irin yanda aka samu gidan cike da
masu yiwa Nura murnar dawowa ya isa ya tabbatarwa wadanda suke tare dashi wafanda ba
su san ko shi wayc ba irin asalin gatan da yae da
ita ko da baa tsaya an yi musu wani bayani ba,
tunda aka sauki su Hajiya Salma da su Umma
Talatu a wasu fakuna guda biyu da suke kallon
juna ake ta shiga da fita da nau'o'in abinci, iri-iri
ita kuwa amarya ko sanin nda aka sauketa ba su
yi ba tana can tare da angonta da kuma su
Rahma ita kam Hajiya Salma ita kadai ta san
yanda take jin zuciyarta don dadi ganin irin
daular da 'yar uwarta ta shigo, in ban daAllah wa
ke ni'ımta bawa da irin wannan ni'imar a rana
daya? Ita kuwa Umna Talatu mamakin Nurane
ya kamata, yanda aka yi ya iya zama cikin dan
tsukakken dakin, zauren da suka ba shi mai
yawan shirgi sai daga baya ne ma suka kwashe
shirgin nasu suka hbar mishi dakin a haka.
Ita kam Umma Talatu a wurinta ba ta
tabaganin mutum mai rashin girman kai da
tawali'u da iya mu'amala da na kasa dashi irin
Nura ba, tsawon zaman da ya yi dasu bai taва
nuna wata alama da za ta iya ganc shi din wane
55
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodungi
iri ba ne, ta soma tunanin ta ko wane hali shi din
ya fito daga babban gida ne ta dalilin yawan
alherin da yake musu ita da mijinta, dama
wadanda yake yiwa a waje masu shigoa suna yi
mata godiya, saboda zaton da suke yi ita din
uwarshi се.
Nana kuwa tana can a inda aka yi mata
masauki ita da Rahma a dakin uwar mijinta
Hajiya Kubra ga 'yan aiki sun kewaye ta kowane
motsi ta yi sai sun tambayeta ranki ya dade kina
bukatar wani abu ne? Ta ce musu a'a nan kuwa
babu abinda take so cikin zuciyarta irin ta samu
kebewa tare da Antin ta don su samu zantawa
kan wannan abin mamaki da suka samu kansu a
ciki sai dai ta rasa yanda za ta yi ta yi haka din.
Hajiya Kubra da kanta ta sbiga dakin da
ta sa aka sauki su Hajiya Salma bayan da aka
nutsu ta samu wuri ta zauna cikin fara'a da nuna
girmamawa a garesu suka gaisa cikin dan
takaitaccen lokaci suka saki jiki da juna har suka
yi hira saboda irin yanda ta nuna musu cewar ita
din mai matukar fahimta ce.
"Amma dai ai za ku dan mana kwana biyu
ku dan huta kafin ku tafi ko?" Ta yi tambayar
bayan ta mike za ta fita.
56
Du Kamar Wuya 2 Hafsal C.Sodangi
Hajiya Salma ta ce mata "A'a mu kam in
so samu ne ai kuma gobe sai mu koma garinmu."
Ta ce "Gobe-gobe, haba ai idan ma ba za
ku tsaya ku ga komawar amarya gidan mijinta ba
sai ku bari sai jibi ki dan huta kadan tukunna ba
su yi musu ba suka amsa da to Allah dai ya nuna
mana ta ce musu amin.ta fita.
Cikin kwanaki biyun nan da suka yi babu
abinda akeyi sai hidimar biki ga 'yan uwan Nura
sun cika gida maza da mata harkarsu kawai suke
yi duk wanda ya zo kuwa sai ya shiga wurin da
aka sauki su Hajiya Salma ya gaishesu cikin
girmamawa ya kuma tambaya ina Umman yayan
take? Ace musu gata nan a nuna musu Umma
Talatu ita kam Umma gajiya ta yi ta cc kai in ka
ga ma dai maikudi yana wulakanta talaka ko
yana wani jiji da kai to shima arzikin nashi bai
kai ya kawo ba nc, tunda ga Nura da 'yan uanshi
da iyayenshi a wurinata baata taba ganin masu
arziki irinnasuba bata kuma taba ganin
mutanen da suka kaisu sanin darajar dan adam
ba da kuma girmamashi kwana biyun da su
Hajiya Salma suka yarda zasu yi suna cika aka yi
musu sallama ta girmamawa alherin da aka yi
musu nai matukar yawa ne,cita kam Umma
5757
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Talatu ma Nura ya s ne ta yi zamanta zuwa wani
'raci da shi din zai samu zarafin da zasu taho
tare don ya shirya musu abinda yake son yi musu
wanda ya ce sai ya dan samu nutsuwa tukunna
zai yi.
Ta ce mishi a'a gara dai ta je gida tunda ba
ta nemi izinin dadewa wurin tsohon mijinta ba,
don haka bai dace ya ganta shiru ba sai kawai ya
ji labari a wurin wadansu Nura ya ce "Haka ne
Umma Ubangiji ya sa muma mu yi koyi da
halayenku a zamantakewar aurarrakinmu na
wannan zamani."
Ta ce "Amin dan nan amma kai kam ai
ina ganin ka dace da damun mace ta kirki mai
tarbiyya da sanin darajar mutane, to kai ma
kuma haka kake don haka in Allah ya yarda ba
zaka samu matsala a gidanka ba sai dai kawai
mu yi muku fatan Allah Ubangiji ya ba ku zuri'a
wacce take dayyiba."
Nura ya ce "To Amin Umma." Ya sake
kawo wani alherin bayan abinda ya san
mahaifiyarshi ta yi musu ya ba ta ya ce "Wannan
rikewa za ki yi a hannunki Umma kina tafiyar
wa a hankali ba na so in zo in samu ke ko Baba
wani ya sake shiga wani hali na wahala."
58
S
KB
ta
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Tana murmushi tana fadin "Wahala kam
ai mun fita daga cikinta tunda ga ranar da Allah
ya kawo mana kai."
Gaba daya aka debesu aka kaisu filin jirgi
don su koma garin su, babu abin da bai yiwa
Nana dadi ba irin dagewar da Antinta ta yi kan
sai ta tafi da Rahma a cewar ta wai in dai
Kananan yara Nana take so, to gasu nan cikin
dangin Nura don haka in har ta kyautata
mu'amalar ta dasu to kullum sai sun cika mata
gida.
Kwana ku bayan nan Nana ta tare a gidan
mijinta wanda ya sha gyara aka kuma kawatashi
ta yanda zai dace da abin da Nuran yake bukata.
Dawowarsu cikin danginshi ya kara
bayyanar wa Nana wane irin miji ta aura, Nura
mutum ne mai yawan 'yan uwa mai yawan
harkoki mai yawan jama'a, amma hakan bai
hanashi ba ta hakkinta na zama tare da ita ya yi
hira ya yi. wasa da ita ya kula da dukkan
al'amuranta kamar dai yanda shari'a ta bukaci
namiji ya yi wa matarshi wadannan halaye nashì
sai suka kara sawa itama Nana at kara
himmatuwa wajen ganin ta kyautata mishi ta bi
umarniusii ta faranta mishi rai, ta girmama
59
Da Kumar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
iyayenshi ta yi mu'amala mai dadi tsakaninta,
tunda shi da yake namiji yake sanar da ita ya san
ya girmamata ya ba ta hakkinta to ita kuwa a
matsayinta na matarshi wacce take zaune a
karkashin shi me zai hana ta yi mishi biyayya
takuma kyautata mishi?
Watanni biyu bayan nan Nana tana zaune.
tare da mijinta a falonshi hidimar abin
karyawarshi take yi, inda ta shirya mishi speedy
orange cake Nura sai kallonta yake yi yayin da
ita kuma ta maida hankalinta kan hidimarshi da
take yi zuwa can ya gaji ya ce mata.
"Ni Nana ya ya muke ne?"
Ta yi maza ta juyo ta kalleshi tare da
tambayarshi "Na me fa?"
Ya sake kallonta cikin nutsuwa, hakan ya
tunatar da ita abinda yake nufi ta yi maza ta
kawar da kanta ta ci gaba da abinda take yi, ba
tare da ta sake tanka mishi maganar tashi ba, ya
kammala hidimominshi ya gama shiri ya yi mata
sallama zai fita ta ce "To a dawo lafiya Allah ya
bada sa'a."
Ya amsa cikin jin dadi ya fita ita kuma ta
dawo ta ci gaba da ayyukan gidanta da ta saba yi
kullum duk da 'yan aikin da take da su, Nana ba
60
Da Rumar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
ta amince da bar wa 'yan aikinta dukkan
hidimomin gidanta ba ta fi amincewa da ta tsare
hidimomin mijinta in ya so sauran ayyukan su su
yimata.Sallamar da aka yi ce ta dawo da
nutsuwarta zuwa wurin da sallamar ta fito, ganin
Zuwairiyya a tsaye ya sa Nana ta kurma ihu nan
tke kuma ta daka tsalleta isa wurin da
Zuwairiyya ke tsaye ta kankameta cikin murna
da farin ciki ganin aminiyarta abinda ba ta taba
zato ba, a wannan dan Kanknain lokacin.
"Zuwairiyya." Nana ta sake fadi cikin
matsanancin farin ciki, ta kamo hannunta sukа
wuce ta tsakiyar falon zuwa inda falonta yake
kai tsaye har cikin dakin kwanciyarta ta kai ta
kan ta ce matakomai sai Zuwairiyya ta kalleta ta
ce mata "Yallaßan fa yana waje?"
Nana ta kkalleta ccikin onutsuwa tana
tambayarta "Wanene yallabai?"
Zuwairiyya ta yi murmushi ta ce"To wa
ki ke zaton zan kira yallabai a yanzu in ba Umar
ba."
Nana ta kyalkyale da dariya ta så hannu ta
rike baki ta ce "Haba ke ki ce mun duniya ta yi
dadi, gaskiya mana na ganki kin wani canza mun
$61
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
to bari in gayawa Nura isowarku sai in ji abinda
zai fadi."
Nan da nan ta jawo wayarta ta sanar da
Nura zuwan su.
Nan da nan Nura ya bar abinda ya ke yi,
ya taho gida don taren bakon nashi, Nana ta isa
falon mijinta cikin sutura mai yalwa da hijabi,
don ta yiwa mijin aminiyar tata barka da zuwa ta.
kuma gabatar musu da dan abin tabawa kafin ta
kammala shirya musu abinda zasu ci, tana
dawowa dakinta ta ce "Ke Zuwairiyya ai zuwa
za ki yi mu shiga kicin don mu shirya abinda
zamu ci."
Zuwairiyya ta ce "Ni da ko gama hutawa
ban yi ba za ki sani wani aiki."
Ta ce "Mu je in ba ki kujera ki zauna ni in
yi aikin ban ce sai kin tayani ba."
Та се "Тo wannan kuwa." Suna shiga.
kicin din Zuwairiyya ta ce "Waw Nana ya ya za
a yi a gaji da girki a cikin wannan kicin din?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Hala kicin din
ne zai hana gajiya?"
Zuwairiyya ta ce "Kwarai kuwa ta sa
hannu ta dauki wani lafiyayyen tumatur da ya ba
ta sha'awa ta wankeshi ta soma sha, Nana ta dan
62
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi kalleta ta ce "Hala mai son tumatur muka samu?"
Zuwairiyya ta yi tsaki ta ce "To daga an shirya kuma sai a fara cewa an samu an samu?
Shima yaliabai din ya wani tasani a gaba wai bai yarda ba ya ga alamar da wani abu a makale."
Nana ta yi dariya ta ce "To ko ke fa Zuvairiyya daga shiryawarku dubi yanda ki ka
canza amma da kına zaure a gida kun wani
takurawa rayuwarku kuma duk laifinki ne."
Zuwairiyya ta ce "Babu wani laifina
shima ai miskilanci ta sake mika hannu ta dauko
wani tumaiur ta ci gaba da sha Nana ta ce "A'a
bale da alamar maigidan yana da gaskiya akwai
wani abu a makale bari a yi mishi cushen
tumatur da kwai. Zuwairiyya ta kara matsowa
kusa ta ce "To ni dai ai kin san na fi son a gaya
mun kayan hadin kafin a soma girkin."
Nana ta ce "Haka ne ga abubuwan da
muke bukatar nan kın gansu na kammala su wuri
daya tumatur masu tauri gwargwdon yawan
iyalinkin kamar n da yake mu hudu ne zan yi
amfani da guda takwas, kwai takwas, nama
dakakke cokali takwas, butter cokalf uku sai
kayan kamshi ta ci gaba da harhadawa yajin da
63
Da Kamar Wuya 2 Hufsat C. Sodangi
sakaci gaba da hirarsu ta dauko, ke ki ce min dai
kawai maigidan gara yake sha, Zuwairiyya ta
fadawa Nana, Nana ta yi murmushi ta ce "To ina
arafanin ka iya girki ba ka ciyar da mijinka
abinci mai dadi ba?"
Zuwairiyya ta ce "Kina da gaskiyar ki
Nana, ai nima yanzu shawarar taki nake bi."
Nana ta yi murmushi ta ce "Ke ki ce mun
zama ya yi dadı."
Zuwairiyya ta tayata murmushin ta се "Ai
wannan tafiyar ma ba tawa ba ce ta Umar ce
cewa ya yi wai in yi mishi rakiya ya zo ya yi
miki godiya kan irin shawarwarin da ki ka rinka
ba ni wai ya san in ban da ke da har yanzu muna
nan muna irin wannan zaman da da can muke
yi."
Nana ta ce "To in ban da ke Zuwairiyya
miji in an riga an yi aure ai ba a irin wannan
zaman dashi tun da kin riga kin dawo karkashin
zamanshi in kin gyara zaman kin gyarawa kanki
ne kamar yanda in ki ka bari zaman ya lalace za
ki tarar mafi yawancin lokaci macen ce a wahala
mai yawa, to balle ke da tun farko ba wai ba kya
son Umar bane kwata-kwata ke dai kawai wasu
daga cikin halayenshi da dabi'unshi ne ki ke
64
Du Kamar Wuyu 2 Hafsat C. Sndangi
anin ke ba su yi miki in ki ka kyautata
mu'amala tsakaninki da shi za ki iya canza mishi
wasu daga cikin halayen daba kya son abinda yа
gagara kuma sai ki yi hakuri dashi a kansu." Zuwairiyya ta cc "Ai ni a farkon zaman
priskilancinshi ne ya kara sawa na Kara Kin shiga
harkarshi tunda ina ganin tamkar zai iya wulakantani duk da dái na sani tun farkon
wana gidan babu abinda ba ya yi min na
akkina da yake kanshi in ban da bai shiga
harkata bayan tafiyarki kuma da na yi mufin yin
vani saboda shawarwarin da ki ka bani sai na
auki matakin in na yi girki in zuba mishi, in kai
mishi in ajiye mishi a falonshi, in yi tafiyata na
ki mishi abin karyawa da safe, bai tababa na jc
dáuko lokacin da na kai mishi na rana, shima
nmaajecna ajiye mishi na dáre na samu bai taba
haş, naz ajiyes wandaa na kais mishi: naa dauko
wannan har na dawoo dákinaaina tunanin in har
obe ma na wuni ina ajiye mishi bai taba ba zan
diinaa dom ba zan iya lamuntar hakam ba, sai
gashi ya turo kofaaya shigoxfakina wandá hakan
shi ne karoona farko tum zuwana gidan idan ma
wataa magana zai yi daga bayan labule yake
bayawa, ya gaya min, ina ganin shigowarshi na
65
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
yi kamar ban ganshi ba, sai na ji ya yi magana
cikin murya mai cike da nutsuwa, ni abincin da
ki ke ajiyewa a falo na wane ne? Ban daga kai
na kalleshi ba na ce mishi naka ne, ya kara sakin
fuska ya ce to haka ki ka ga ya dace a yiwa
maigida Zuwairiyya aje a dangwarar mishi da
abinci kawai a tafi ba tare da an tsaya an ga ya ci
ko bai ci ba? Ban amsa mishi ba, sai ya ce ai
tunda dai ki ka gane ina da bukatar abincin naki
to sai kawai ki karasa aikin naki don ki samu
cikakken ladanki, ban kula ba sai ya miko
hannunshi ya kamo nawa ya daganiyana fadin
mu je ki zuba min abincin in ci, ban yi musu ba,
na biyoshi muka taho falon nashi muka zauna na
soma zuba mishi, maimakon ya soma ci sai ya ce
sai dai mu ci tare don bai ga lokacin da nima na
ci wani abu ba, tun daga wannan lokacin sai
kuma ya zama duk lokacin da ya ganni zan shiga.
kicin zai biyoni mu shiga in ina girki shi kuma
yana tayani da wani aikin har sai mun gama mu
dauko mu zo falo mu zauna mu ci tare, bamu fi
kwana uku a haka ba sai kurna ya bijiřewa
kwana a dakinshi shi kadai, tun daga nan şhi
kenan sai kuma komai ya wuce al'amura suka
daidaita, yanzu kuwa kinga kullum cikin cin
66
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
amarcinmu muke. Jiya tun safe ya ce mun in
shirya zamu taho ya zo ya yi miki godiya, kan
irin shawarwarin da ki ke ba ni."
Nana ta ce "To ko ke fa Zuwairiyya me ya
fi zaman lafiyatsaanin mata da miji dadi."
Zuwairiyya ta ce "Gaskiya babu."
Suka kammala girkin da suke yin Nana ta
shirya musu abin sha gaba daya suka kwaso
suka kawo falo inda Nura da Umar suke zaune
suna hira tare da dan motsa baki, Nana ta sake
ajiye musu cushen tumaturin da abin sha а
gabansu ta kuma nemi wuri ta zauna kusa da
mijinta tana kula da abinda yake ci yayin da
itama Zuwairiyya ta matsa kusa da nata mijin
"Ni fa yanzu wani ji da ni ake yi."
Umar yana cia abirci ya ke maganar.
Nura ya yi murmushi ya ce "To ai an kyauta
dama can abinda ya dace a yi maka kenan."
Uman ya sake wani mrumushin ya ce "A
to ban samu, hakan ba sai da Madam dinka ta sa
baki tukuna aka