An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DA KAMAR WUYA
HAFSAT CSODANGI
Da-Kamar Wuya 2 Hufsat C. Sodangi DA KAMAR WUYA...
2
TAM
НАЛУА HAFSAT C. SODANGI
(Mrs Yunus Abdullahi Daбai)
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
DA SUNAN
ALLAH
MAI RAHAMA
MAI JIN KAI
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take
Subhanahu wata'ala masanin yau da gobe, abinda
yake boye da wnada yake bayyane, mai kowa mai
komai gwani mai hikima cikin dukkan
al'amuranshi.
Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen
talikai Manzon tsira Annabin Rahama,
Muhammadu (SAW) da alaycnsa da sahabbansa
da wadanda suka bi wa tafarkinsa na gaskiya har
zuwa ranar alkiyama.
Bayan haka godiya mai dimbin yawa
gareku makaranta littattafaina a ko ina ku ke na
gode da irin kulawar da ku ke nuna min,
Ubangijinmu Allahu ya kara kauna a tsakaninmu.
Na gode,
Taku Hafsat C. Sodangi.
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
3
Hafsat C. Sodang! Da Kamar Wuya 2
Daga Littattafan Sodangi
Uwar Miji
Naga Ta Kaina
Wayyo Duniya
Rabon Kwado
Cikar Alkawari
Yiwa Wani
Abu Naka
Tabbataccen Al'amari
Nufin Allah
Garin Banza
Mata Masu Duniya
Kifi Na Ganinka
Hattara
Biyan Bukatar Rai
Gani Gareka
Mc Zamu Ce Da Maza?
Da Kamar Wuya
4
Da Kamar Wuya 2 _Hafsat C. Sodangi
Littattafan Hajiya Hafsat C. Sodangi ba sa nufin yi da wani ko habaici ga kowa an yi su ne kawai don fadakarwa da nishadantarwa ga jama'a
ana neman afuwa ga duk wanda ya ga wani abu ya yi kama da abinda ya faru dashi ba da shi ake yi ba dace ne kawai.
Fatan alheri gareku duka na gode, da kulawarku.
SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta mahaifana ne.
Alhaji Chindo Muhammad Sodangi da
Hajiya Fatima C. Sodangi
Ubangiji madaukakin sarki ya saka muku
da alherinsa bisa reno da tarbiyyar da ku ka yi min.
TUKWICI
Tukwicin littafin naku ne masoyana,
makaranta littattafaina wadanda kullum sakonku
na fatan alheri ya ke samuna na gde kwarai da irin
kulawar da ku ke nuna min tare da rubutuna, Allah
ya kara karfafa kaunar dake tsakaninmu yakuma
saka muku da mafificin sakamako, amin, na gode.
5
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
JINJINA
Jinjinar littafin ta ki се:-
Rabi'atu Ibrahim daga Abuja
Rabi'atu Muhammad Lawal
Rafi'atu Ibrahim Sharif
Rahinatu Umar A. Bauchi
Rahina Absaisa
Rabi'atu Abubakar A. Gumel
Ramatu Abdulhamid
Rashida Muhammad Inuwa
Rashida Muhammad Yola
Rukayya Muhammad Gusau
Dukkanku na gode da kulawar ku,
Allah ya saka da alheri, amin summa
amın.
6
Da Kamur Wuya 2 Hufsat C. Soda ngi
YABO
Yabon naku ne
Fa'iza Sulaiman Ishak
Fadila Muhammad
Farida Yahaya
Fatima Yusuf Sulaiman
Fatima Sulaiman Muhammad
Fatima Galadima
Fatima Bala B.K.
Fatima Wada Sale
Fatima Abdulkadir
Fatima Habib
Fatima Sirajo Jibrin
Fatima Abubakar M.
Na gode da kulawarku
7
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Fatan alheri
Fatan alheri gareku
Safara'u U. Rabi'u
Safiya Magaji Ado
Suwaiba Umar
Suwaiba Hoza
Suwaiba Abdullahi
Suwaiba Sulaiman
Suwaiba Fashcет
Sumayya Umar
Sudaida Ibrahim Kafancan
Shafa'atu Isa Zaria
Shafa'atu Muhammad Lala
Shafa'atu Ibrahim Gamawa
Shafa'atu Musa Minjibir
Sha'awa Kabir
Sa'adatu Zamfara
Saudat Abubakar Wudil
Saudat Muntaka Ibrahim
Saudat Nazir Muhammad
Salamatu Nazifi Adam
Salamatu Yahaya Maska
Salamatu Dahiru Gombe
Dukkanku ina fatan gaisuwar fatan alberi
sameku cikin koshin lafiya, nagode da yawan
kulawar da ku ke mun, Ubangijinmu Allahu ya saka
muku da alherin sa, amin summa amin.
ta
8
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
KUNA RANA
Hauwa'u A. Garba a Bauchi
Maryam Muhammad Umar
Harira Sa'id daga Ondo
Hauwan Coach a Bauchi
Atika M. Ubali (Mrs Sadik Falalu
Jahun, Jigawa State)
Nafisatu Inuwa Illelah
Salamatu Dan'azumi Illelah
Hajara Ibrahiim Alabura, Bauchi
Da Karmar Wuyt 2 Hafsat C. Sodangi
TA'AZIYA! TA'AZIYА!!
Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un.
Ina mika ta'aziyya ta ga miji, iyayc, 'yan
uwa da abokan arziki bisa rasuwar:-
SAMIR AH MUHAMMAD D/KAKALE
GUMEL
Ubangijjinmu ALlahu ya ji kanta da
rahamarsa ya sa kuma aljanna ita cc makomarta,
amin.
Mun yi sabo da Samirah ta dalilin
sakonninta gareni sai muka yi zumunci mai dadi
muka so jun a saboda Allah duk da bamu taba
saduwa ba, na girgiza kwarai a lokacin da na samu
labarin rasuw/arta, ko da yake dukkanmu mun sani
kowane rai rnai dandanar mutuwa ne, Ubangiji ya
sa mu cika dla imani, amin summa amin.
Ina ro kon Kulluhuwallahu kafa daya daga
daukacin Musulmin da littafin nan ya shiga
hannunskii da fatan Allah, Ubangiji ya kai ladan
cikin ka'barinıta.
'Ubangiji ya amfana zuriya da ta bari a
bayanta, amin.
10
Da Kamar Wuya 2
N
Hafsat C. Sodangi
ura ya yi sallama a bakin kofar
dakin cikin yanayin muryarshi ta
kowane lokaci.
Nana ta mike tsaye cikin sauri, bayan ta
amsa sallamar da ya yi mata ta shiga kaye-kayen
'yan kayayyakin da take ganin zasu tare wuri
cikin dan tsukakken dakin nasu da nufin samar
da wurin da Nura zai iya shigoa da kekunan shi
na guragu, tayi iyakacin kokarinta filin da ya
samun bai gamsar da ita ba ba sai an gaya mata
ba, ta san wurin ya yi kadan.
Ta tsaya tana kallon wurin da ya samu a
dakin cikin zuciyartá kuwa tunani take yi mai
lalura irin wannan ya ya zai yi ya ji dadin zama a
irin wannan tsukakken dakin? In ban da kar shi
da iyayenshi su ga kamar an raina musu ai da ta
yiwa Antinta magana ta gayawa Baba a ba ta
gidan da za ta zauna a ciki ita da mijinta, ba don
wai ta same warin zuba kayanta da aka mayar da
su gida ba,sai dai dn mijinta ya yalwata
tunda ga irin lalurar da ya ke da ita.
Nura ya sake y'r wata sallamar a bakin
kofar dakin nuna alamar izininta yake sauraro
don yana bukatar shigowa, ta amsa sallamar
daga ciki ta kuma shiga yi mishi bayani "Wai so
11
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
nake in dan yi kaye-kayen da zan iya samar
maka wrin da za ka shigo cikin sauki kadan kara
hakuri kadan."
Ya ce "Mata to." Ya ci gaba da tsayuwar
da yake yi dabarar Nana ta kare wuri bai samu
ba don haka ta yanke shawarar dauke katifar
dake yashe a tsakiyar dakin ta jingineta ta bar
filin dakin ya dai samu wurin shigowa in ya so
ko a kasa sa zauna ya ri mata, yana waje yana ta
faman jiranta don haka ta nufi bakin kofar dakin
cikin sauri don ta bude mishi ta kuma taimakeshi
shigowa da hanzarinta ta mika hannayenta a
sunkuye don ta jawo mishi keken nashi zuwa
cikin dakin nata, lokacin ne ta ganshi tsaye
kyam a kan kafafunshi, da sauri ta juya dakin
cikin razana zuciyarta sai harbawa take yi cikin
sauri, ta yi maza ta danno kofar dakin nata ta
rufe ta kuma jingina jikin kofar idonta a rufe sai
faman karanto addu'o'i iri-iri take yi na neman
tsari cikin ranta kua tunani takes yi wane ne
wannan ya zo ya tsaya mata a bakin Kofar
dakinta mai murya irin ta mijinta?
Tana cikin wannan tunani ta ji an yi
magana daga waje cikin murya mai sanyi da
nutsuwa ya ce "Haba Nana, haba amarya yа ya
12
Dd Kanmar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
za a yi ki rufowa angonki kofa? Dan bude mun kofar in shigo."
Ta yi kamar ta gasgata muryar tashi ta bude mishi kofar sai kuma wata zuciyar ta
kabeta mutane da yawa a yau mugaye ne haka
kawai wani ya kwaikwayo muryar mijinki ya zo
ya rudeki da dadin baki ya yi dalilin da ki ka
bude mishi kofa ya shigo miki dakinki, to in ban
da batan kai ma me zai sa ki ruďu da mutumin
da ki ka ganshi a tsaye kikam tnda dai ma kin
san mijinki ga yanda yake.
"Nana bude min kofa mana." Ya sake
roko cikin wata muryar mai sanyi. Ta yi shiru
tamkar ba ta ji shi ba, sai ma fadi da ta yi cikin
ranta cewar "Ka yi ka bari."
Ganin da Nura ya yi ba zai, samu biyan
bukatarshi ta shiga dakin ba matukar ta hanyar
roko ne ya sashi yanke shawarar saka karfi don
haka ya sa hannu ya tura kofar duk da kokarin
da ta yi na dagewa a jikin kofar bai 6atalokaci ba
kofar ta bude ya tura kai ya shiga nan take ta
soma bashi hakuri cikin rawar jiki da rawar
murya saboda tsorata da shi da ta yi.
Nura ya kalleta cikin murmushin jin dadi
ya ce mata "Haba Nana ai kin so ni so na hakika,
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodang!
kin so ni soyayyar da babu son rai a cikinta, kin
so ni irin son da ba ki taba yiwuwa in face miki
ba, kin so ni son da babu komai cikinsi sai son
zalla, don haka kar ki ce mun ba ki ganeni ba,
kar ki ce min na bace miki ind ai kin yi fushi
saurin tashin da na yi daga kan keken nawa na
guragu ban jira kin dagani da hannunki ba to na
yarda da laifina a shirye kuwa nake in ba da
hakuri in e na tuba, in kuma yadda da
kuskurena."
Ya kara matsawa kusa da ita, tafiya a
hankali cikin sanyi tare da fadin "Ni ne gurgunki
Nana, ni ne gurgun da ki ka so alhalin yana
zaune cikin keken guragu, me zan yi in saka
miki wannan alheri da ki ka yi min Nana? In ban
da in yi ta sonki in yi ta sonki in yi ta sonki."
Ya Karasa gabanta bai saurari jin wata
kalma da-za ta fito daga bakinta ba ya kura mata
idanu yana kallon ta da wani yanayi a fuskarshi
tamkar dai tsoro yake kar wani ya ce mishi ba
tashi ba сe.
"Ni ne Nuran Umma Talatu, Nana a yau
kuma na zama Nuran Nana zan yi ta zıma
Nuranki ba zan taba gajiya da hakan ba." Ya ce
"Mu je mu yi alwala, mu ze mu yi saliah me yi
14
Da Kamar Wuya 2 Hufsat C, Sodangi
Allah godiya Nana da ya nuna mana wannan
ranar mai albarka."
Ba ta yi musu ba, suka je suka vi alwalar
su ka zo suka yi sallah, suka yi addu'o'insu suka
shafa, ya juyo ya kalleta cikin murmushi da
sakin fuska ya ce "Nana wai ko irin dan oyoyo
din nan ma ni da na dauka in ki ka gama ba
Karaniar tarba zan samu a wurinki ba.".
Ta ce "Ai kai ka hana in yi maka tarbar."
Cikin h.ınzari ya tambayeta "Da na yi me?"
Ta cc "Da ba ka shigo mun a yanda na
sanka ba, da ka zo a yanda na saba ganinka daka
ga irin tarbar da na yi maka."
Ya yi maza ya ce "To bari in je in dawo a
yanda ki ka sannin."
Ta ce "Ai an riga an wuce nan kuma, ya
ya jiki?"
Ya kara matsawa kusa da ita "Haba
Nanana, in ki ka ce ba za ki tarbeni ba me ki ke
so in yi? Iiakuri za ki yi dani, ya zamar min dole
no in bar keken tunda har da iyayena sun zo
wurin daurin aure ba zai yiwu in je gabansu a
haka ba don haka ki yi hakuri kin ji Nana."
Ta ce "Na ji amma zan huce ne in har ka
gaya min dalilin ka na yin abinda ka yin."
15
Da Numur He 2 _Hafsat C. Sodangi
Ya ce "Na yarda Nana na yarda da duk
wata kalma da ta fito bakin ki ko kuma za ta fito
nan gaba ni dai a yanzu kawai ina neman afuwa
ne da sassauci duk wani bayani da ki ke son ji ki
daga mun fafa a kanshi.
"Assalamu alaikum." Sallamar da suka ji
an yi ta katse shi daga kalaman da yake yi da
sauri kuma ya mike ya nufi bakin kofar dakin
cikin kunya da nuna girmamawa, tare da fadin
"Umma ai na leka dakin na ki dama shigo na
tarar kina sallah."
Ta ce "E, ai na yi lattin yin sallar ne ban
yi ta tun wuri ba saboda cikowar mutane, ungo
wannan." Ta-mika mishi kwano a rufe ya sa
hannu biyu ya karba tare da fadin "Sannu da aiki
Umma. Bayan duk dawainiyar da ku ka wuni a
ciki kuma sai da ku ka dorawakkanku wata
dawainiyar?"
Ta ce "Dawainiyar me farfesun kaji ne
don na san daga kai har amaryar da kyar ne in ba
da yunwa kuka wuni ba." Ya sake wani
murmushin tare da fadin "Ai kuwa kamar kin
16
Da Kumar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi sani Umma ni dai da yunwar na wuni duk da dai ban jita to amma dai na san tana nan tunda ba
zan iya tuna abinda na baiwa bakina ba, a yau."
Umma Talatu ta yi murnushi ta ce "Ai
haka hidima take." Ta juya ta nufi dakinta, ta
barshi yana fadin "Ubangiji ya saka da alheri."
Ya dawo ya zauna gaban Nana ya bude kwanon
ya zuba mata ido yana kalionta, "Na dai san ke
ma babu komai a cikin cikin nan naki don kuwa
na ji shi yana kuka."
Ta kara tsuke mishi fuska ya kalleta ya yi
murmushi ya ce "Ka ganni da shiririta ina so wa
amarya ta sake ta yi ta mun zancen ina jin
muryarta mai tsananin dadi ashe ma zumudı ya
sa na manta ban sayi bakinta ba.
Yana fadın hakan ya yi maza ya mike ya
yi waje, Nana ta bi bayan shi da kallo cikin
zuciyarta tana fadin "Allah da iko yake duk
abinda ka yi domin shi za ka ga kyakkyawan
sakamako a kai. Mijinta mijine da kowace mace
za ta yiwa kanta sha'awar shi ta tuna lokacin da
yake zuwa wurinta irin kawayenta da uska rinka
ce mata haba Nana duk ajin nan naki kuma sai ki
kare a auren gurgu? In yana da kyau a fuska sai
me ai nakasasshe ne, kuma wannan sharbeben
17
Da Kamar Wuya 2 Mafsat C. Sodungi
mutum ma yanda ya lankwashe nan dawainiyar
shi ma kadai ta isheki.
Ta yiwa Allah godiya da ba ta saurari irin
kalaman wadancan kawayen nata ba, gashi a yau
ta mallaki mijinta santalele ga tsawo ga zati ta yi
mamaki cikin ranta yanda aka yi Nura ya iya
sarrafa jikinshi ya maida kanshi tamkar gurgun
gaske a wancan lokacin.
Nura ya dawo cikin dakin fuskarshi dauke
da murmushin angonci a yanzu yana sanye ne da
Kananan kaya da suka yi matukar karbarshi ya
zo ya tsuguna a gabanta ra fiddo wani dan
akwati da yake sunne dashi ya bude shi a kusa
da fuskarta ya sa hannu ya dauko sarkar cake
ciki ya mika mata tare da fadin "Ta sayen
bakinki ce amarya."
Ta zuba mishi ido tana kallonshi cikin
nutsuwa, ta ce "Gaya mini gaskiya menene
labarinka?"
Nura ya maida sarkar cikin dan akwatin
ya ajiye ya kalleta cikin nutsuwa ya ce "Haba
Nana ya ya za a yi ki yi zaton samun labari
wurin angon da yake cikin tsananin farin ciki a
daren angoncinshi na farko kamar ni?"
Ya sake kallonta ya ce "Saurin me ki ke
18
Da Kamar Wuya 2__ lafsat C. Sodangi yi? Ai yanzu abin da kawai na san zan iya gaya
miki shi ne ina sonki, ba zan taba daina son naki
ba, zan yi adawa da duk wani abinda zai Eata
miki rai. Saboda na san kina sona ba sai kin bata
lokacin ki wajen gaya mun hakan ba ni kuma
dama abin da nake so kenan Nana a so ni. A so
ni a yanda nake to kin yi min,kin yi min fiye da
yanda na yi zaton zan samu."
Nana ta yi shiru tana sauraron kalamanshi
cikin zuciyarta kuwa wani sun yi take ji mai dadi
har ba ta san sanda ta ji wani irin farin ciki mai
gamsarwa a ranta ba, ta rinka jin tamkar ta narke
a rayuwarshi.
Tsawon lokaci suna cikin wannan hali
kafin ya ce mata "Nana yunwa fa muke ji gaга
mu ci abincin nan da Umma ta kawo mana."
Ba ta yi musu ba, ya bude musu kwanon
farfesun kajin suka soma, ci, isuna hirar su ta
farantawa juna rai.
Tsawon dare ran nan basuysamu sun
runtsa ba, duk da gajiyar da ke tare da'su..
wasannin farantawa juna kawai suke yi,
Nana tana kwance a gefe sai faman zuba wa
Nura shagwaba take yi, yayin da shi kuma ya bar
kmai ya shagala wurin tarairayarta.
19
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
"To ai ni har yanzu ba ka gaya min yanda
aka yi ka nannade kanka ka zauna cikin keken
guragu ba, da dalilin da ya sa ka yin hakan?"
Ya kalleta ya yi murmushi ya ce mata
"Ba yauza ki ji wannan ba Nana, ai ni yau
abinda za ki ce min in yi in yi shi cikin sauri
jikina yaha 6ari kawai wannan ne. Ina son ki
Nana. Zan ci gaba da sonki, zan yi ta snki har iya
rayuwata, don kuwa kin yi min abinda ki ka
cancanci hakan a wurina."
Da asuba bayan sun idar da sallar asuba
suka zauna suka kammala laziminsu, da
addu'o'in dazza su yissai Nura ya waiwayo ya
kalli Nana cikin sakin fuska, ya ce "Ran amarya
ya dade ina kwana?"
Nana ta yi maza ta sunkuyar da kanta kasa
cikin nuna alamar kunya, da girmamawa ta ce
"Ai ni ce ya kamata in fara gaishe ka tunda kai
ne babba."
Ya ce "To Nana ai duk yanda ki ka ce
hakan za a yi."
Ta ce mishi "Ina kwana?"
Ya amsa cikin murna saboda ganewar da
yayimatar tashi yarinya ce da ta samu
ingantacciyar tarbiyya ta girmama na gaba da
20
Da Kamar Wuyd 2 Hafsat C. Sodangi ita, ga kuma ladabi da nutsuwa. Ya mika hannu
ya dauko dan karamin rediyonshi da nufin jin
labarai sai ya jiwo muryar Umma Talatu da
mijinta a tsakar gida suna magana ya yi maza ya
mike tsaye cikin hanzari ya fita tsakar gidan
yana fadin "Kar dai yau ma Baba sammakon zai
sake yi?"
Ya kalli Nura cikin murmushin farin ciki
ya ce "E Nura so nakein fita yanzu tun kafin rana
ta yi zafi."
Nura ya ce "Ai fa ana kwallara rana a 'yan
kwanakin nan." Ya nemi guri ya tsugunna yana
gaishesu cikin girmamawa ya kalleshi ya cсе
"Wane wuri ka ke zuwa ne haka?"
Ya ce "E to na dai koma wurin aikina ne
na tara Kasar nan tunda ai na huta na samu
saukin hakarkarin nawa sosai Nura ya kara
sassauta murya ya ce "Amma Baba ai sai na ga
kamar na ce maka ka dan saurareni tukunna
kafin ka koma."
Ya ce "E haka ne ai dubawa na yi na ga
hidimar ta yi yawa."
Nura ya sake yin magana a hankali cikin
nutsuwa ya ce "Ina ganin dai Baba a dan kara
yin hakuri a saurareni ina sane da maganar da na
21
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangl
yin ba mantawa na yi ba. In kuma akwai wata
matsala ne da ta taso wacce ban san da ita ba saí
a gaya min."
Da sauri Umma Talatu ta ce "Babu komai,
ai mu tunda Allah ya kawo mana kai babu
abinda zamu ce sai godiya ga Ubangiji don kuwa
rahama ce ta sauko mana, Allah dai ya yi maka
albarka ya sa ka wanyc da duniya lafiya."
Malam ya ce "Amin, amin."
Nura ya koma dakinshi ya samu Nana a
kwance kan katuwar katifar dake yashe a dakin
ya zauna kusa da ita, yana tambayar ta me suka
fada a labaran?
Ta tabe baki ta ce "Ai ni ban saurara ba."
Nura ya kalleta ya ce "Ana labarai ba za
ki saurara ba."
Та се "Ai ni ban cika sauraron wannan
labaran nasu ba, ba su mun dadi kullum sai an ce
an kashe mutane kaza da keza, don haka ba na
sauraro don kar raina ya rinka 6асі."
Ya yi murmushi ya ce "Ban taba jin
wanda bai sauraron labarain duniya ba sai ke to
ai ko don ka san halin da duniya ta ke ciki ka
rinka sauraro."
"To shi kenan sai in fara sauraron tunda
22 i
Da Kumar Wuya 2
ka ce akwai amfani." Hufsat C. Sodangi
Ya yi murmushi ya ce "To yaushe ki ke ganin zamu iya tafiya?"
Ta daga ido ta kalleshi cikin nutsuwa ta tambaye shi "Ina?"
Ya yi murmushi ya ce "Gurin da na fito mana
Nana ko kuwa kina zaton ni dan garin nan ne?"
Ta dan kawar da kai daga kallonshi a
dalilin shi ma ita yake kallo ta ce mishi "Ban
sani ba."
Ya ce "Ai kuwa ya kamata ace kin sani
tunda dai ke 'yar unguwar nan ce, yaushe ne ki
ka soma gañina? Ko kuwa kina ganin tamkar
dama ina nan lura dani ne kawai ba ki yi ba?"
Ta ce "Uhun ban sani ba."
Ya ce "To zuwa na yi ko dama can kuwa
ke ce dalilin zuwan nawa, fitowa na yi nemanki
na kuma sameki ai sai tafiya ko kua?"
Shiru ta yi ba ta ba shi amsa ba, ya ci gaba
"Zan so in koma gida a wannan lokacin to amma
hakan zai kasance ne bisa amincewarki tunda
ban yi miki wannan bayanin ba a farko ba zai
yiwu a yanzu in tilasta miki hakan ba, don haka
in har kin ga kin fi amincewa da zaman nan to
sai mu je in kaiwa mahaifana da 'yan uwana ke
23
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
su ganki ki gansu sai mu dawo in samar mana
wurin zama."
Ta ce "Uhun ni duk yanda ka yi duk daya
ne a wurina."
Ya yi murmushi ya cc "To shi kenan Nana
Allah dai ya saka miki da alheri."
Ya tashi ya fita saboda jin sallamar yara a
tsakar gida suna tambayar Umma Talatu Yaya
Nura, ya fita ne? ta ce musu bai fita ba, amma
kuma bai tashi daga barci ba.
"To ina ne dakin nashi mu tasheshi tunda
ba mu ganshi a dakin zauren ba?"
Ta ce "A'a ku dai je an jima ka dawo."
Ya yi maza ya ce "Su tsaya kawai Umma
gani nan fitowa." Yana fitowa suka sa mishi ihun
sowa, walimarmu muka zo jin yaushe zamu yi
ta?"
Ya ce "Ku dakata ku ji ku dakata mana in
fa ba haka ba zan koma daki in turo kofa."
Suka dan saurara don su ji abinda zai
gaya musu, "Ku je ku shiryo ta sai ku zo ku gaya
min nawa ku ke bukata, idan na ji kun yi abin
bisa tsari sai in ba ku ku je ku yi, in kuwa ba ku
yi tsari mai kyau ba in ce babu ruwana."
Da sauri suka juya waje da gudu suna
24
Da Kamar Wuya 2 _Hafsat C. Sodangi fadın "Kar fa ka je ko ina, yanzun nan za mu dawo."
Nana kuwa tana dakinta tana jin su cikin zuciyarta tana tunanin mu'amala irin ta mijinta
da ta fahimci saukin halinshi da soyayyarshi ga
yara kanana.
Kwana biyu da kammala bikinsu Nana,
Nura ya shiryawa yara kasaitacciyar walima a
kofar gidan su Umma Talatu inda ya wadatar
dasu da abinci da na sha iri-iri, an kuma yi dace
a ran nan Zuwairiyya ta zo ta kara ganin dakin
amarya suna cikin dakin suna hirarsu ta ke ce
mata "Ke Nana Allah ya taimakeki ya ba ki miji
son kowa kin anda ya rasa gashi kuma mai kyan
hali da saukin kai, dubi yanda ya ke mu'amala da
yara ya maidasu tamkar su ne abokanshi."
Nana ta yi murmushin jin yabon da kawar
tata ta kewa mijinta ba tare da ta tofa komai ba
sai ma ta kawar da zancen da tambayarta "Ni
Yaya Umar ya zo daurin aurena kuwa?"
Zuwairiyya ta tabe baki ta ce "Ban sani ba
bai gaya min ba ni kumą kin san ba zan
tambayeshi ba don bai isa ba."
Da sauri Nana ta kalleta "Bai isa ba fa ki
ka ce?"
25
Da Kamar Wuya 2 Hafsat C. Sodangi
Ta ce "E abinda na fada kenan, tun da ba
ya magana dani ni ce zan rinka bin shi ina
magana da shi?"
Nana ta ce "Ai in kin yi hakan ba faduwa
ba ne tunda mijinki ne na aure kuma gaskiya zan
gaya miki Zuwairiyya idan ma Umar yana da
wani irin hali ke ma kina dashi saboda fitowar da
kalmar bai isa ba daga bakinki yana nufin kema
kina da wani hali da ki ke mishi mara kyau
wanda bai dace ba. A gaskiya ni kin ga dai
kwana biyu ne kawai da gama bikinmu amma a
zaman da muka yi na kwana biyun sai na
fahimci cewar ni dai mijina duniyata ce zan yi
komai don in