Reading DIMAUTA Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje, muna fitowa ya bude
kcken dawaki ya sakani, ya sakar masu linzami suka soma
tafiya shima ya biyosu a nashi ingarman dokin, a muka
sulalc muka fita daga kasar daga cikin keken dawakin ina iya
lekawa ta wata 'yar taga ina gano wuta tana toroko a cikin
kasar tamu, hakan yana nuna mani cewar gidajen al'umar
kasarmu sunc suka sha wuta.
Ba mu fi awa da baro kasarmu ba muka juyo takun kofatun
dawakai bayanmu alamar an biyo sawunmu, wannan abin
shi ne ya sa muka kuma sakarwa dawakanmu linzami, duk
da irin gudun da muke amman sai da suka ci
mana, yaima Hamsu ya taresu yaki ya wanzu a tsakaninsu
ya soma saransu yana tashin kawunansu ya zamar masu
tamkar shedani a tsakaninsu ganin irin barnar da ya yi masu

69

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

yasa babbansu ya fito da wata kibiyarshi ya saitashi bayan
ya dana ya sakar masa a baya kibiyar ta huda sulkenshi ta
nutse masa a jiki, amman tamkar ba shi aka harbaba. Hakan
ya yi ta yakarsu har suka soma ja da bayahakan yasa suka
sauya salo na yakinsu, suka fito da kibiyoyi suka yi masa
ruwanta, ina ganin lokacin da wasu da yawa daga cikin
kibiyoyin suka shige masa jiki, amman duk da haka bai
yarda makaminshi ba ya juyo ga dawakaina ya yi tsalle ya
hau kan daya ya zungureshi suka yi haniniya suka yi fitar
burgu daga tsakiyar dakaru suka nausa aguie, ya juyo ya
dubi shugaban dakarun a haka muka nausa muka yi cikin
dawan a guje, suma suka rufo mana baya, haka muka yi ta
gudu har zuwa lokacin da ajali ya kirashi, ran da yake
JIkinshi ya fita, bansan ya mutu ba sai da naga dakarun sun
Ci mana suna zuwa babbansu ya kai masa gawurtaccen
sara yasameshi a hannu bai yi yunkurin karewa ba ya zamo
daga kan dokin ya fado kasa.Na kwala wata razananniyar
kara, domin na tabbatar da cewar yarima Hamsu ya yi
shahada.A haka muka yi ta wannan gudun Suna saran keken
dokin ni ina r.eman taimakon Sarki Allah har muka karaso
gareku, kuka taimake ni a hannunsu."Ta gama basu labarin
rayuwarta.
Suka zuba mata idanuwa su duka suna kallonta cikin
tsananin tausayawa.Jalaludin ya dubeta kana ya ce
mata.Tabbas kina cikin rudani na rayuwa da ya dace a
taimaki rayuwarki, amman kin samemu a lokacin da muke
masu gaggawar zuwa tsiburin Marzak domin isar da
burinmu mu ma da ya shafe mu amman nayi maki alkawarin
idan na dawo zan kwato maki "yancinki a hannun azzalumi."
Maganarshi ta sa ta ta dago ta dubeshi da duban nutsuwa
kana ta ce da shi.

70

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Ya zamar maka dole ka bi ta cikin kasarmu matukar
zakaje tsiburin Marzak, daga kasarmu zuwa tsiburin tafiyar
kwana uku ce."
Maganarta ta janyo hankalin su gaba daya.
"Nesa ta zo kusa." Muhusiya ta ce
"Me kike nufi da hakan?"Sarauniya Samnatu ta
tambayeta.Ta dubeta ta gyara takobinta, kana ta bata amsar
tambayarta.
"Abinda nake nufi shi ne zamu ratsa ta kasarsu mu yaki
azzalumai mu rushe daular zalunci sannan mu karasa zuwa
wurin da muka nufa a lokaci kankani."Lamsu ya mike tsaye
"Haka abin yake tabbas rayuwar mu ta taimakon addinin
Alalh ce kamar yanda bayin Allah suka tafīyar da ita."Haka
suka yi ta hirarsu akan cewar washe gari idan gari ya waye
zasu karasa kasarsu Hajir domin su riski abokan gaba.Washe
gari bayan sun yi sallar asuba, suka karya kumallo kana suka
yi hawa suka nausa, tafiyar awa uku ta
kaisu Rasar tasu Hajir, suna zuwa suka ga kofar kasar a
balle a gefe daya suka saka kai cikin kasar ba tare da
fargabar komi ba, suka soma yin karo da dakarun sarki
Zalman rukuni-rukuni cikin shirin yaki, ko da suka gano
Hajir sai suka zaburo gareta tamkar kura taga akuyar da ta
bata a dokar daji, nan fa wuri ya rincabe da azababben
yaki,karar makamai da haduwar takubbuna ne kawai ke tashi
a wurin, rayuka suka soma salwanta.Mutuwa ta soma
shawagi tana farauce rayukan dakarun sarki Zalman,
Jalaludin ya zamto wani shaidani a
cikinsu domin yanda yake saransu yana sadasu zuwa ga
ajalinsu babu kakkautawa duk wurin da ya saka gaba sai dai
kaga dakaru suna zubowa tamkar ana gididdibar ya'yan
kabewa, haka suma sauran abokan tafiyarsu.

71

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Kafin wani lokaci sun yiwa dakarun fata-fata, suka kuma
matsawa suka yi cikin garin babu kowa a cikin garin ba tare
da shayin komi ba suka nufi hanyar da zata kaisu fada.
Tun daga nesa suka soma hango taron jama'ar Kasar cikin
hali na wulakanci da tozari, duk sun sunkuyar da kansu kasa,
guwowinsu a kasa sun durkushe, sarki Zalman a zaune akan
karagar mahaifin Hajir dakaru sun yi masa kawanya, 'yan
matan kasar a tsaye tsirara babu sutura a JIkinsu don
tsananin tozarci, a gefe a daya cikin kaskanci da tozarci
mahaifin Hajir ne. Suna karasowa idanuwansu suka gane
masu wannan abin takaici mafi girman 6acin rai da tsananin
bakin ciki, suka shigo cikin fadar tamkar an cullosu, sarki
Zalman suka yi kallon kallo dashi da Hajir ya mike da sauri
kana ya kyalkyale da wata madaukakiyar dariya mai amsa
amo,sannan ya ce mata.
"Tabbas nasan cewar ba zaki taba tserewa daga gareni ba,
don haka ki yi sani cewar tabewa ta tabbata a gareki bisa
gagarumin laifin da kuka aikata gareni, tabbas tunda na rasa
dana akan son da yake mani ni zan zamto madadinsa, ran
mahaifinki ya zamto daidai da na dana."Da muryar dagawa
ya ce mata.
Maganar da ya yi yasa mahaifin Hajir ya dago ya dubeta
suka kalli junansu nan take yanayın fuskarshi ya kuma
sauyawa domin ganin 'yarsa ta kuma dawowa wurin daya
guje mata.
Ta taka ta motsa ta dubi sarki Zalman kana ta ce
masa."Tabbas duk wanda ya nemi taimakon sarki Allah
taimakon nashi zai isa garcshi don haka kayi sani cewar
taimakon Allah ya isa garemu tabbas karshen zalincinka ya
zo."Maganar ta batawa sarki Zalman rai zuciyarshi ta hasalo
da fushi mai yawa ya zare takobbinshi ya dagata cikin azama

72

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

ya yi nufin sarewa mahaifin Hajir kai, tamkar giftawar
walkiya wata kibiya ta ratsa ta tsakani sami matsuguni a
hannun sarki Zalman da yake rike da wukar da yake shirin
sarc kan mahaifin Hajir, sarki Zalman ya kwala wata
razananniyar kara mai firgitarwa, ya yi jila da wukar da take
hannunsa Muhusiya ta durgo tsakiyar filin
hanunta yana rike da kibiyar da kwari da bakar ta danata ta
kuma saita sarki zalman ta sakar masa wata da zummar ta
mutane ta halakashi ganin tahowarta yasa cikin matukar
zafin nama ya janyo wani sadauki da yake gefenshi ya tsayar
da shi a gabanshi kibiyar ta sami matsuguni a jikinshi ya
kwala wata razananniyar kara ta fitar rai, sarki Zalman ya
sake shi ya fadi kasa matacce ya daga kanshi suka kalli juna
dashi da Muhusiya, ya mayar da duban shi ga dakarunsa
kana cikin tsawa ya ce da su, "Ku saro mani
kawunansu."Nan take suka zaburo garesu, suma suka
fuskancesu mahaukacin yaki mai girman muni ya gauraye a
tsakaninsu,
Rarar haduwar makamai da adadin mutuwar sadaukai ya
dinga yawaita, karar fitar rai da kai suka ya cika wurin
dakaru suka yi ta zubowa kasa matattu, dawakai suka yi ta
rasa mahayansu, makamai suka yi ta asarar
marikansu,jikkuna suka dunga rasa kawunansu, mutuwa ta
yi ta farautar rayuka, masifa da balai na yaki ya dunga
zubowa yana sauka akan jama'ar sarki Zalman, suka rude
domin ganin bala'in irin wanda basu taba gani ba, suka shiga
yakar kansu da kansu, wasu suka soma neman hanyar
tserewa domin ganin irin masifar irin ta yaki da ake saukar
masu.
Muhusiya ta tarwatsa taron wasu dakaru suka yi gaba da
gaba da sarki Zalman ta yunkura ta kai masa sara ya yi

73

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

zamiya cikin azama, shima ya taso mata suka yi wata
kazamar haduwa, suka soma musayar sara da suka, basu
dauki wani lokaci suna fafatawa ba ta shammace shi ta kafta
masa sara a ciki, cikin ya tsage kayan cikin suka zubo waje
ya kwala wata madaukakiyar kara, ta janyo hankalin
dakarunsa duk suka dakata. Ya zube a wurin a matsayin
matacce, da mutuwa mafi girman wulakanci. Ganin haka
dakarun suka zubar da makamansu suka mika wuya.
Hajir ta ruga aguje ta kwance mahaifinta, suka
Tungume Junansu cikin matukar murna da farin cikin sake
gamuwarsu. Mahaifin nata ya matsa gabansu Jalaludin ya
dubesu da duban nutsuwa kana ya soma masu jinjina. Bayan
sun huta na tsawon kwanaki uku sannan suka yı shiri domin
karasawa tsiburin Marzak domin aiwatar da abinda yake
gabansu na karbo gimbiya Husamatu da kuma kubutar da
mahaifin Jalaludin da boka Hamaran ya mayar gunki, don
haka bayan sun gama shiryawa suka fito domin yin
bankwana da sarki, suka isa fada suka tarar da fada ta cika,
ana ganin shigowarsu cikin fadar kowa da kowa yamike
tsaye domin girmamawa a garesu, suka karasa gaban sarki
suka yi gaisuwa kana Jalaludin ya ce da sarkin.
"Daman mun sanar da kai cewar yau ita ce rana da zamu
wuce domin ci gaba da tafiyarmu domin muyi azamar isa
zuwa tsiburin Marzak don haka mun shirya domin ci
gaba da tafiyar ta mu."Sarki ya yi murmushi kana da
tausasa murya ya ce masa.
"Ina rokon Allah ya tabatar da nasara gareku."
Su duka suka amsa da cewar "Amin." Kana sarki ya ci
gaba da fadin.

74

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Yata guda daya dana mallaka zata zamto jagoranku domin
nuna maku hanya musamman domin zamtowar tasan sirrin
tsiburin."
Yana rufe bakinsa Hajir ta shigo cikin fadar tayi wata shiga
ta alfarma abin alfahari, sirrin ziryar din tsantsar kyawunta
ya fito, Jalaludin ya dubeta ya ji zuciyarshi ta harba a
tsakiyar kirjinshi don kadan ya hanashi zaucewa da
ganin kyawun nata na yanzu, fadar tayi shiru ana kallonta.
Ta taka ta matsa har zuwa gaban Jalaludin kana cikin
tausasa murya ta ce masa.
"Ina tare da kai ya masoyina duk runtsi da wahala."
Da sigar magana mai jan zuciya ta ce masa.
Ya dubeta kana ya yi mata sanyayyan murmushi.Kana suka
yi bankwana da mahaifin Hajir suka juya domin tafiya, suna
fitowa bakin fada suka kama dawakansu suka hau kana suka
nausa domin ci gaba da tafiyar su.
Haka suka wanzu tsawon kwanaki suna tafiya babu abinda
yake tsaida su face salla ko cin abinci.
A safiyar yau ne suka karaso bakin wani bakin shuri da
girmansa ya wuce misali, shurin ya tsare ko ina idan ka daga
kanka sama ba zaka iya ganin iyakarshi ba domin ya nutse a
cikin gajimare, hakama shurin ya rufe ko ina da ina
babu hanyar wucewa, bakin shuri da rashin samuwar rana
hakan yasa wurin yawanzu c
Hajir ta ja ta tsaya kana ta yankc shurin da yake tsakaninsu
ta hanyar fa din.
"Wannan shi ne tsiburin Marzak daga wannan wurin babu
wata hanyar wucewa."Sarauniya Samnatu ta matsa ta dubi
bakin shurin kana
ta juyo ta dubi Hajir kana ta ce mata"Wannan ba shi ne
tsiburin Marzak ba domin shi in tsananin duhu.

75

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

tsiburin Marza ya kasance da farar kasa mai kyalli
yake."Hajir ta yi murmushi mai taushi gareta kana ta ce mata.
"Na tabbata kinsan tsiburin Marzak, amman nayi mamaki
yanda aka yi kika sanshi bayan nasan cewar duk duniya ni
kadaice sai kuma kakana da ya rasu muka sanshi, don haka
sanar da ni yanda kika sanshi."Sarauniya Samnatu ta dubeta
da duban da malami
yakeyiwa dalibi kana tace mata.
"A baya wucewar shekaru ashirin da biyu ni bokanya ce
mai yawan yin bincike akan al'amuran duniya anan nazo
tsiburin Marza domin neman samun wani ilimi na tsafi da
boka Hamaran ya ajiye, amman ban sami ikon shiga cikin
tsiburin ba, hakan yasa na san tsiburin.Hajir ta yi murmushi
kana ta ce mata.
"Wannan shi ne tsiburin da kika zo kuma ki yi
Sanicewar duk she kara tsiburin yake sauya kama don haka
a Shekarar da kika zo gareshi yana matsayin fari a yanzu da
kika dawo kina tarar da shi ya juyc ya zama baki ba komai
bane face tsafi na boka Hamaran."Ta gama maganar tata
tana dubansu.
"Ya kamata mu zAZZagaya domin nemo kofar shiga cikin
tsiburin."Jalaludin ya ce masu, suka karasa bakin tsiburin
suka soma neman kofar shiga cikin tsiburin.Amman sai da
suka tafiyar da tsawon wata daya suna laluben Kkofar shiga
cikin tsiburin amman sun rasa, hakan ya matukar tayar masu
da hankali da girgiza tunaninsu.
Suka zauna suka yi shiru cikin tarin gajiya mai yawa,basu
ankara ba suka ji wata madaukakiyar guguwa tana busa
abubuwa da dama tana daukar abubuwa marasa nauyi tana
yawo da su a cikinta.Bayan wucewar yan lokuta ta lafa, boka
Hamaran ya baiyana cikin mummunar shiga mai muni da

76

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

suka firgice, yana cikin shiga ta bokmanci da ta kuma
munanta mummunar fuskarshi.Ganinsa yasa su Jalaludin
suka mike tsaye a gaggauce
suka yi kallon kallo dajunansu, da muryar fushi Jalaludin
ya ce masa.
"Gamu yau Allah ya kawo mu garcka ranar da Allah zai
tabbatar da nasara garemu."Boka Hamaran ya kyalkyale da
wata madaukakiyar
dariya kana ya hade fuskarshi ya ce masu.
"Tabbas kaskanci ya tabbata gareku tunda kuka zo gareni,
duk duniya babu wanda ya san hanyar shiga cikin tsiburin
nan idan bani ba, don haka zaku yi ta zama ana har tsawon
rayuwarku ba tare da kun gano hanyar shiga cikin tsiburin
ba."
Ya dakata ya mayar da numfashi kana yaci gaba da fadin.
"Zan nuna maku hanyar shiga cikin tsiburin ina kuma
jiranku a ciki a fadata."Yana gama maganar tashi ya soma
zukewa yana shigewa ta wani dan mitsitsin rami mai kama
da na tururuwai a haka ya shige ta cikin ramin, su Jalaludin
suka tsaya kawai suna kallon wurin cikin mamaki mafi
girma a rayuwarsu.
Jalaludin ya mike cikin fushi mai girma ya soke wurin da
takobinshi ya tsaya a wurin yana huci na tsananin fusata,ya
zube akan guwoyinshi ya daga hannunsa sama ya soma
yin addu'a domin neman taimako a wurin sarki Allah.A
haka suka kuma tafīyar da tsawon wata daya suna zaune a
wurin suna masu yawaita ibada ga Allah da kuma neman
taimako gareshi, a ranar da suka cika wata daya ne boka
Hamaran ya kuma baiyana a garesu cikin wata mummunar
shiga wacce tafi ta farkon, ya dubesu ya kyalkyale da wata
dariya mai hauhawa kana ya ce masu.

77

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Tabbas wurin wasan mage bana bera bane don haka kuyi
sani cewar ni boka ne da ya yinisa a cikin lamarin tsafi
tabbas mutuwa tana gaf da isowa gareku."Jalaludin ya zare
takobinshi ya nunashi da ita kana ciki fushi ya ce masa.
"Babu makawa lamuranka sun kusa zuwa karshe domin
mun kusa shigowa cikin fadarka da izinin Allah." Boka
Hamaran ya turbune fuska kana cikin izza ya ce masu.
"Babu wanda ya isa ya shigo da ku cikin fadata."
"Allah zai shigo da mu bisa ikonsa ya kuma bamu nasara a
kanka."Boka Hamaran ya kyalkyalae da dariya, kana ya ce
masu, "Ina sauraron zuwanku."Lamsu ya ce masa. Yana
gama maganar ya soma zukewa ta dan mitsitsin ramin,
Muhusiya ta zaburo a bazata ta kai masagawurtaccen sara
gami da yin kabbara madaukakiya.Wata Kara da girgizar
kasa suka faru lokaci daya, su duka suka rufta cikin wani
rami mali grman hanya, suka fado cikin wata kasaitacciyar
fada ma' abociyar tsaruwa da kayan alatu.Suka mike a fusace
a lokaci daya, suka fuskanci junansu, kana Jalaluddin ya ce
masa, "Allah Ya shigo da mu cikin fadar taka."waniBoka
Hamaran ya girgiza kanshi gami da fadin "Kun shigo cikinta
bayan tun da aka ginata babu wani mahaluki da ya taba
shigowa cikinta, don haka tabewa ta tabbata gareku."
Da tsananin fushi ya ce masu, kana ya ci gaba da fadin,
"Ga gunkin mahaifinka nan wanda ya kasance a haka tsawon
shekara ashirin yana haka ya zamto abin ado a fadata, don
haka ka gwada sihirinka don dawo da shi mutum rayayye."
Yana gama maganar ya bace daga tsakiyarsu ya baiyana
akan kujerar mulkinsa ya zauna ya zuba masu idanuwa, su
duka suka zubawa gunkin Katilu da yake tsaye idanuwa
cikin mamaki mafi girma. jalaludin ya daga hannunsa ya

78

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

soma yiwa Annabi salati kana ya karanto Ayatul Kursiyu ya
tofawa gunkin jikin Kafilu, nan take ya soma matsawa.
Boka Hamaran ya yi wata madaukakiyar kar,a ya zaburo
ya yi dauki kansu. Gimbiya Husamatu ta shigo fadar cikin
azama ta sureshi suka zube gefe daya, Jalaludin ya
Juyo gareshi cikin fushi suka zaburowa juna suka yi
kazamar gamuw,a suka soma dukan juna babu kakkautawa,
basu wani dauki lokaci ba suna fafatawa zamtowar mai tashe
ya kiyayi mai zamani, Jalaludin ya yi masa fata fata ya
dagashi sama ya maka da kasa yasa kafarshi ya take kanshi
ya kama Rafafuwan ya soma jansu da karfin tsiya, boka
Hamaran ya soma yin wani irin gunji yana nishi yana neman
ceto amman a haka da tsananin karfin dantsc Jalaludin ya
tsinke masa wuya wani kakkauran jini ya soma
zubowa,mutuwa mafi girman muni ta tabbata ga boka
Hamaran, Jalaludin ya saki gangar jikinshi ta zubea
wurin.Kafilu da ya dogara ya tashi yaga irin kisan da aka
yiwa boka Hamaran ya taka ya matsa gaban Jalaludin ya
kalleshi kana da murya mai taushi ya ce masa, "Tababs kai
ne dana da na rasa tun kana jaririnka."
Suka ci gaba da duban junansu cikin farin ciki mai
girma.Muhusiya tayi burin ganin ta auri saurayin da take so,
tana fatan kuma shi ne zai zamo mijinta. Lamsu, ya yiwa
Allah godiya da ya sa Muhusiya take burin aurenshi.
Gimbiya Husamantu, tun da ta soma ganin Jalaludin take
begensa ta kuma so ta aureshi kudire a ranta zata aureshi.
Hajir, ta daure ta danne zuciyarta zata zauna da kishiya don
haka ta amince ta auri Jalaludin.Jalaludin, yana sonsu su
duka zai aure su, ko domin suna sonshi.
Sarauniya Samnatu, tana son ta auri Kafilu, ta kuma bashi
sarautarta.

79

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Kafilu, duk da ya tsufa amman ya yarda zai auri sarauniya
Samnatu su yi zamansu cikin aminci.
KARSHE
Masha Allah.
Mu hadu a sabon littafina RANAR MUTUWA.
Mukhtar Kwalisa
08069524699

80


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment