Reading DIMAUTA Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufe kofar nan kar ku bar wani mahaluki ya
shiga."Ya juya ya yi cikin gida a matukar dimauta, ya
shiga dakin da yake ajiye kayan yakinsa ya yi shigar yaki,
ya yi tigijim ya fito kamar wani kurmar dutse, ya nufi
barauniyar hanya, don ficewa daga gidan don tsira da
ransa.Bayan ya fito dag garin sai ya sakarwa dokinsa
linzami da zumar zuwa garin Farisa, don tsira da
rayuwarsa.
**
Sadauki Kafilu yana Rarasowa zuwa ga bakin kotar Sai
ya ji Rofar a rufe ya matsa, kusa da ita ya ja, ya danna ta ji
ko motsi ba ta yi. Yana cikin haka ashe wani bakin yana
makale yana ganinsa, da ya fahimta hankalinsa ya tafi ga
kokarin ganin ya bude kofar, sai ya dauko wata kwarinsa
ya dana mata kibiya ya seta shi.Ya sakar masa kibiyar ta
iafi ta same shi, a gefen damararsa, ta shiga jikinsa. Da
ząlin nama ya Juyo don jin abin da ya same shi, ai yana
juyqwą sai ya ji saukar wata Kibiyar ta ratsa masa
hannunsa. Nan-1a ya soma jin ruwan kibiyoyi ta ko'ina, da
zafin nama ya soma kadewa da takobinsa ya zaburi
dokinsa ya bar wurin.
Ya yi dauki a kan bakin bawan da ke tsayc da kibiya,a
hannunsa, ya tabcta ya scta faffadan kirjin Kafilu. Shi ma
Kafilu ya sakarwa dokinsa linzami. Ta ko'ina ya wuce sai
ya ji wucewar kibiya ta gefen kansa. Bakin bawan nan ya
sakar masa kibiyar nan ta tawo da matukar gudu daidai
kirjinsa, amman kafin ta karaso

35

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Kafilu ya yi tsalle sama ta wuce ya dawo kan dokinsa.Ya
soma wasa da takobinsa a sama, yana karasawa zuwa ga
bawan nan yasa kailin takobi ya tashi kansa sama, kafin
kan ya dawo kasa, ya tsarga jikin biyu cikin gwaninta,
dokin ya wuce da gudu, ya yi girjiya ya juyo da shi, gami
da zaro kwarinsa ya đana bakarsa, ya kuma yiwa dokinsa
kaimi.Duk wurin da ya wice sai ke ga sadaukai Suna
ubowa daga saman katangar. kafin wani lokacı duk
gawarwakin sun yawaita, gatin shiru babu motsi. Ya dawo
tsakiya ya yi tirjiya, ya yi duba ko'ina shiru babu motsin
komai. Waye mai karar kwana? Wane tsara ne ya yi su Ina
sarkin na ku ya fito na gaggauta sadar da shi zuwa ga
ajalinsa, na dandana masa dacin mutuwa. Amma shiru ba
motsin kuwa.
Daga shi sai gawar gimbiya Suhaila da ke tsaye a daure
a Jikin dirka a saman kubar. Amma duk sauran sadaukan a
kwance mutuwa ta yi daukar wulakanci a gare Su,Ya juyo
ya kalli gawar Suhaila ya ji wani bakin ciki ya kuma
lullube masa zuciya, hawaye suka kuma soma
kwaranyo masa. Da sauri ya kawar da kansa gcte ya juya
gà kallon kofar fada, da ke fuskantarsa.
"Barn na dauko fansarki ya masoyiyata, tarc da ta
mahaifina da azalunin mahaifinki ya aikata."
Ya ce a fusace. A cikin muryar kuka, ya juyo ya
kalleta, ya sakarwa dokinsa linzami ya nufi kofar, yana
mai jujjuya bakin al'amudinsa da ke hannunsa, yana zuwa
ya dakawa kofar al'amudin nan da nan ta karye,Kafilu ya
cusa kai.cikin gidan sarautar, wasu tsirarun dakaru suka
kifu akans hi suna ta gurnanı, kamar wasu mayunwatan

36

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

zakoki.Nan da nan aka soma cinikin rayuka a tsakaninsu
da
sadauki Kafilu, ya soma tayar da kawunan sama, yana
feke su kamar bakin alkaluma, yana dukan su da
al'amudinsa.Wani sadauki ya dauki numfashinsa ya duka
masa sara a tsakiyar kai, amman kwalkwalin da ya saka a
kanshi ya hana wukar ratsa shi, amman kwalkwalin sai da
ya tashi sama, gashinsa ya tarwatse. Ganin haka sai ya
bata nasa rai, kuma ga gajiya tana neman ta kasara shi,
amman da yake da zuciyar maza yake, sai ya ji duk gajiyar
ta gudu,ruYa juyo ga sadauki ya daga al'amudinsa ya
sauke masa shi a tsakiyar kansa ya tarwatsaa masa kai.
Ta Juyo da zazzafar zuciya akan sauran, katin wani
lokaci ya karar da su, sai gawarwakinsu, zufe, da yawan
yaranyar jini, kamar gabar teku; kawuna a warwtse,
dawakai suna yawo babu mahayansu, makamai duk a
zube babu madaukansu. Kafilu shi kadai tsaye a tsakiyar
gawarwakin zube a gabansa. Ya zaburi dokinsa ya yi cikin
gidan, yana dubawa sako da loko yana duban sarki Shamal,
amman babu alamarsa, nan da nan ran Katilu ya kuma
baci, hankalinsa ya dugunzuma.
Wani bakin ciki ya lullube shi, domin ya fuskancisarki
Shamal guduwa ya yi. Ya juya makaninsa ya tasa me ye
abin da ya kamata ya yi. Hawaye ya dunga kwaranywa
daga cikin idanuwansa.
"Na rantse da girman Ubangiji madaukakı ko da an
sutura sha gidauniyar mutuwa, sai na nemuka duk inda ka
shiga a fadin duniyar nan, na shayar da kai gidauniyar
mutwa, Kayatace kamar yanda ka aikata ga masoyiyata da

37

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

iyayena. Na suture tabbata ba za ka sira daga garcni ba
face da kalma guda Juyo daya wato kallamar tsira."
Kafilu ya ce da daga murya, sannan ya juya
al'amudinsa ya dubi ganuwar garin ya juya kanta ya
soma dokanta yana rushetaa, yana tarwatsata ba
kakkautawa Kamar wani ifiritun aljani bai wani dauki
lokaci mai tsawo yana dukan ganuwar ba, ya arwatsa
wurinan da
zamto kamar wani birni bai taba wanzuwa a wur r Rasa
Domin yanda ya zubar da duk Kasar gani, ya rushe duk
wani gida da ke a cikin garin.Ya tsaya yana mai maida
numfashi, ya d shi ganinsa, sai ya hango gimbiya Suhaila
a tsuye nan a daure, Nan da nan hawaye su ka soma
Kwaranyowa daga idanuwansa ya zaburi dokinsa ya nufi
wurin da take a daure Ya hau da dokinsa har zuwa ga
wunn, ya sauka ya kwance daurin da aka yi mata, ya
kwantar da ita a kasa Hawaye suka dunga kwaranyo
masa.Ya gangaro ya soma haka mata kakabi, yanayi yana
tuna. Yana mai tuna irin soyayaya da suka yi da irin
kaunar da ta nuna masa, kalamanta na soyayya suka dunga
dukar masa cikin zuciya.HaKar yake yi, amman hawaye
suna zubowa daga idanuwansa, babu KakKautawa. A haka
har ya gama, ya aka ya koma zuwa ga wurin da gawar tata
take, ya yi mata sutura.Kyakkywar fuskarta har Lókacin
da akwai kayataccen murmushi akanta, ya suturce ta. ya
yimata addu'a. Sannan ya haye dokinsá ya juyo ya dibi
kubar da ita kadai ce a garin ta yi saura.
"Kin wanzar da kafurci da shirka, ga mutanen garin tir!
Da ke." Ya ce da ita, sannan ya zaro al'amudinsa ya soma

38

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

dukanta sai da ya yi rugu-rugu da ita, ya mayar da wurin
turbaýa
Ai kuwa bayan wani lokaci sai kafilu ya soma ganin
wani bakin hayaki yana tasowa daga cikin kubar yana
tashi sama. A haka hayakin har ya cure wuri guda. nan
take wani mummunan mutum ya bayyana, da dogon
gemu har Kasa da gashi duk jikinsa fari fat, kamar na
tunkiya.fuskarsa abin tsoro bayansa ya rankafa kamar
baka ya juyo ya kalli Kafilu da ke tsaye yana kallonsa,
yace da shi.
"Kayi shishigi, ka tayar da bala'i ga duniya, don laifin da
ka aikata gafalale,daman labarinka ya wanzu gareni tun
tsawon wani zamani Sannan ya yi siiru na yan lokuta,
kana.
"A yau shekara dari da shiga cikin kubar nan ina barci,
ba ni da abin ci Sar Jinin Musulmi, to a ka tayar da ni, da
kuma sannu zan hakuntaka
akan laifinka, na kuma baiwa zuri'ata kadin abin da ka
"Na sani ba ka da masaniyar ko ni wane, to nine Boka
Hamran, wanda ya sanar da Bajakade sirrin tsafi ya
koyawa Marganu bakonci, ya sanar da Makan sirin
safi,wanda ya ilimantar da Sakaradisu da Sakaradiyanu"
Yana gama maganar ya kyalkyale da wata dariya ya yi
nuni ga hannunsa sai ga wasu jibga-jibgan aljanu sun
bayyana runduna guda, kowanne dauke da wasu in
miyagun makamai; yawansu babu iyaka. Ya yi nuni ga
Kafilu da yatsansa ya ce.
"Ku kamo shi ku kawo mishi zuwa kogon tsafina don na
azabtar da shi kafin na kashe shi kisan wulakanci."

39

DIMAUTA

M

MUKHTAR KWALISA

"Karya kake gafalalle." A fusace Kafilu ya
ce.
Boka Hamaran ya kyalkyale da wata dariya.
Kafilu ya nufo shi a fusace, amman kafin
ya kara har ya taka takan iska ya soma tafiya,
a sama ya bar Ka yana ta kallonsa.Yana juyowa ya ga
halitun aljanu har sun kusa zu gare shi. Daga nesa wani
aljani ya harbo masa wata kibiya ta samu Kafilu a baya, ta
ketashi ta shiga jikinsa. Nan ya soma ganin juwa tana
daukarsa. Amman duk da haka sai da ya daure ya ja tunga
zuciyarsa cike da jarumtaka.

FARKON LABARI
uhusiya farar mace mai kyawun cikar diri. ma'abociyar
kyakkyawan hali da nutsuwa da kamala mai kwarjinin
fuska da babu namijin da zai kalleta bai ji sonta ba, mai
dogon bakin gashi baki sidi da shi da gashingira da
manyan idanuwa farare kal, mai cikakkiyar fuska babu
wanda kyawunta baya daukarshi, duk fadin kasar Misira
babu wata kyakkyawa da tafi Muhusiya kyawu sai
gimbiya Husamatu 'yar sarkin Misira Huzafu, itama ba
tsenanin kyawu ta fita ba ta fita ne da tsananin sarauta
hakan yasa suka zamto taurari masu haske a cikin birnin
na Misira.
Baya ga tsananin kyawu, Muhusiya tana da tsananin
jarumta da tumbe a fagen fama, tana da sani cewar babu
wani sauran jarumi da take tsoron gamuwa da shi gaba
da gaba sai dan uwanta Jalaludin wanda ya yi mata
fintinkau a jarumta ba kuma ta tunanin akwai wani
sadauki a duniyar nan da ya kaishi jarumta.

40

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Tana zaune ita daya tana tunanin abubuwan da suke
damunta ta rasa meye yake damunta a rayuwa tana
matukar kishin dan uwanta don haka bata son ya yi nisa
da ita don haka wannan tafiyar da ta sameshi zuwa kasar
Farisa domin laka gimbiya Husamatu da dan uwanta
lamsu dumin ziyarar wazirin kasar don zuwa su ga 'yar
uwarsu da take auren waziri yana matukar tayar mata da
hankali.
Tun daga lokacin da aka nadashi ya zamto sarkin
yakin kasar ta Misira, mafiya yawancin abubuwa ya
koma gareshi, don haka take jin damuwa mai yawa ga
wannan Tafiyar da ta zowa dan uwanta, amman tana ji
ajikinta cewa
ba zata iya rabuwa da shi tsawon lokaci ba zata
lallabashi ya yarda su tafi tare, ta yarda da abinda tayi
tunani ta zauna awurin tana sauraron dawowarshi daga
wurin da ya tafi. Bata jima a zaune ba tana jiran
dawowarshi suka shigosu biyu da Lambu babban dan
sarkin Misira, ta dube su da duban da ta saba yi masu, ta
rasa ta yaya suka shaku da junansu ko yaushe suna tare
da junansu, suka matso gareta suka zauna suna masu
fuskantarta.
Daga bisani Jalaludin ya mike ya shiga can cikin gidan
ya barsu a zaune su biyu suna fuskantar
junansu.Muhusiya ta sunkuyar da kanta kasa kana da
kwantar da murya ta cewa Lamsu.
"Don Allah ka yiwa dan uwana magana akan tafiyar da
zaku yi domin nima ina son a yi ta da ni don ina son
naje naga birnin Farisa a daina bani labarinsa."Lamsu ya

41

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

uubeta da duban nutsuwa ya jima da soma son
Muhusiya, amman ya kasa gaya mata, don haka yake
ganin cewar dama ce ta zo masa da zai yi amfani da ita
idan ya zamto suna tare da junansu.
Don haka ya dubeta a nutse da tausasa murya ya ce
mata."Kar ki damu insha Allah za ayi tafiyar nan dake
bari Zanyi masa magana yanzun nan."Da kwantar da
murya ya ce mata. "Nace mata ni na yarda ta bi mu
tunda tafiyar sadazumunci ce." Jalaludin ya girgiza
kanshi.
"Kaima 'yar uwarka ce duk abinda ka yanke shi ne."Ya
ce yana dubanshi, ya juya ya mayar da dubanshi
gareta."Sai ki je ki gayawa su baba abinda ake
ciki."Suka mike su duka suka fita daga gidan ita kuma ta
shige cikin gida.Da lokacin tafiyarsu ya yi kowa ya taru
a fada,Jalaludin yane sanye da wasu kayan yaki da suka
sha ado na fararen karafa, yana rataye da takobinshi a
baya da wasu kananu a sossoke a jikinshi, da wani gatari
na bakin karfe a gefen kugunshi ya yi damara ta bakin
nadi, ya tattara gashin kanshi ya mayar da shi baya.
Fada tayi shiru ana sauraran fitowar sarki da 'yarsa,
bayan tsawan wasu lokuta aka jiyo tambarin fitowar
sarki bayan wasu 'yan lokuta sarki Huzafu ya fito,
gimbiya Husamatu tana bayanshi cikin shiga ta alfarma
da ta dauki hankalin duk wanda yake a cikin fadar,
Lamsu yana tsayea hannun daman mahaifinshi, fada tayi
shiru.Sarki ya yi duba ga Jalaludin da nutsuwa ya ce
masa.

42

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Tafiyar da 'yaryana zasu su yi zuwa Farisa ta sada
zumunci ga 'ar uwarsu tana karkashinka kai ne mai kula
d'a lafiyarsu da basu kariya, zan hadaka da abokan
rakiya dakaru dubu uku domin su taimaka maku."
Yana gama maganar ya zauna akan kujerar fadanci
malamai suka soma yin addu'o'i na fata suje lafiya su
dawo lafiya.ayan an gama suka fito suka hau dawakansu
suka dauki hanya suka nausa suka dauki hanyar da zata
kaisu birnin Farisa.
Ta yi masa tattausan murmushin da ya so zautashi, a
hankali ta ce masa.
"Godiya t tabbata garcka bisa taimakon da ka bani."
Ya kalleta a nutse ya kau da kanshi gefe daya, a lokacin
Jalaludin ya fito, ya zo ya zauna a kusa da shi suka
danyi shiru zuwa wani đan lokaci, daga bisani Lamsu ya
nisa kana ya gaya masa bukatar Muhusiya.
Ya juyo ya dubeta ya yi shiru yana kallonta daga baya
ya juya ya dubi Lamsu a nutse ya ce masa."Kai mai ka
ce mata?"
Lamsu ya kawar da kanshi gefe daya kana ya ba shi
amsa da cewar. Suka wanzu suna tafiya har sawon
kwana shida hakan yasa suka dakata a daidai bakin wata
korama mai ni'ima suka sauka suka kafa tantina, kowa
ya soma samun nutsuwa, Jalaludin da shi da Lamsu da
kuma Muhusiya suna zaune a wuri daya suna hira,
gimbiya Husamatu ta fito daga tantinta suka dakata da
hirarsu suka dakata suna dubanta, ta matsa daidai wurin
yayanta da sassauta murya ta ce mashi.

43

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Zan dan zagaya nan baya ka dan zan shiga ruwa
domin naji sanyi a jikina." Jalaludin ya jinjina dadin
muryarta a ranshi duk da zamtowar tun da yake a
rayuwarshita duniya bai taba ganin fuskarta ba baima
taôa jin ta yiwa wani magana ba, don haka yake mata
kallon wata mace ce da take da girman kai
mai takama da sarautar mahaifinta, don haka ya ji bata
burgeshi domin baya kaunar mutum mai girman kai,
amma yau muryarta tayi tasirin garesa.
Suka yi shiru su duka suna dubanta, bata jira wani ya
yi magana ba tayi gaba abinta, Jalaludin ya dakata da
kallon ta, kana ya dawo da dubanshi garesu suka ci gaba
da hirarsu.
Can bayan wucewar mintina goma sha biyar suka juyo
wata kara mai karfī, Jalaludin ya yi wata mikewa da
azama ya nufin barin da ya juyo kara da gudu tamkar
kibiya da aka harba a jikin kwari, sannan dakaru suma
suka zabura
kowa ya warwatsu nema ci' in surkukin daji.
Yayi ta kewaye-kewaye neman gimbiya Husamatu
amman bai ganota ba, can ya kuma jiyo wata kara mai
hauhawa ta kuma cika masa kunnuwa da tsananin
jarumta ya nufi wani tudu da yake gabanshi.Yana zuwa
ya leka kasan tudun ruwa ne garai garai a CIKin ruwan
ya ganota ta kasa gaba ta kasa yin baya wani kumurcin
maciji ya fasa kai a gabanta. Babba ne mai matukar
girma da zai iya hadiye mutum lokaci daya ba tare da ya
sha wata wahala ba. Jalaludin ya yi tsalle daga saman
tudun ya yo Rasa cikin ruwan, ya fada ruwan ya yi nutso

44

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

ya dago gaba daya, a daidai lokacin macijin ya kawo
mata wafta da zummar dauketa ya hadīye, CiIkin
gwaninta ya yi gaggawar tureta
gefe daya macijin ya yi sara a wurin da ta bari, ya yi
gaggawar rikota ya jayota da zummar su fito daga cikin
ruwan ta noke taki motsawa ya ja ta ta ki yin motsi ya
dubeta a fusace, a daidai lokacin macijin ya kuma
dawowa garesu, da muryar fada fada ya ce mata.
"Ki fito daga cikin ruwan mana." Ta dubeshi ta girgiza
mashi kai, sannan ta nuna masa jikinta alamar babu kaya
a jikinta, Jalaludin ya girgiza
kanshi ay juyo ya tunkari macijin shima ya taso masa
yana zuwa ya kawo masa sara ya yi tsalle ya bar wurin
ya đane bayanshi cikin azama ya zare takobinshi ya yi
masa wani gawurtaccen sara a tsakiyar kanshi.Macijin
ya yi wani ruri da tsiwa domin jin shigar sarar wani jini
mai kauri ya yi tsartuwa sama, gawar macijin ta fada
cikin ruwa, ya juya yana dubanta duba na farko da ya
taba yiwa fuskarta a hankali ya cire rigar da take jikinshi
ya mika mata ta amsa ta lullube jikinta ta fito daga cikin
ruwan. Kyawun dirinta ya tafiyar da zuciyarshi
numfashinsa ya soma daukewa.Su Lamsu suka karaso
wurin da suke, Muhusiya ta dubi girman gawar
mataccen macijin ta girgiza kanta, ta kuma tabbatar da
jarumtar dan uwanta. Suka dawo sansaninsu suka zauna
aka soma maganar macijin, a haka dare ya yi kowa ya
tafi tantinsa ya shiga domin kwanciya, masu gadi suka
ci gaba da kaiwa da
komowa.

45

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

A lokacin da gari ya waye bayan sun karya suka yi
hawa domin ci gaba da tafiya, suka ci gaba da yinta
cikin azama basu kuwa dakatawa ba sai da suka soma
hango katangar birnin na Farisa don haka suka dakata
domin hutawa su lzuma aika dan a fito taryarsu, kowa
ya sauka aka kafa tantuna.
Suna tsaye suna shirin sauke kayansu suka soma jiyo
saukar kibiyoyi babu kakkautawa tako ina, dakarunsu
suka dimauce suka dinga zubowa kasa suna masu
shahada. Ruwan kibiyar ya yi ta karuwa a garesu
dakarunsu suka yi ta mutuwa da azama, Jalaludin ya
zare takobinshi ya soma karkade kibiyoyin da suka
nufoshi, ya nufi tantin da gimbiya Husamatu take ciki da
matukar gudu, su Lamsu suka ja daga suna nazarin ta
wurin da ake yi masu ruwan kibiyoyi.
Yana zuwa ya shige cikin tantin kai tsaye, ta juyo a
fusace suka hada idanu wa dashi, ta dan ja baya a razane
rigar da zata saka ta zame daga hannunta, da azama ya
sunkuya ya daukota ya mika mata, ta amsa ta dorata
akan
wata ta saka, ta dubeshi da tsananin fushi ta sharara
masa mari.
Marin ya zo masa a bazata ya kuma matukar kona
masa rai."Meye zaka shigo mani tanti tsabar rashin
mutunci ba zaka nemi izini ba."
Ya dubeta da matukar kulewa, wata kibiya ta hudo
tantin ta nufota ya yi azamar tureta ya sa takobi ya
kadeta, ta juyo ta dubeshi, ta mayar da kallonta ga
kibiyar. Bata zata ba itama taji saukar wani karkafar

46

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

mari da ya sata tayi baya taga-taga, tun da take a
rayuwarta babu wani mahaluki da ya taba marinta, abin
ya matukar kona mata rai, ta dube shi da duban damuwa.
"Ka san wanda ka mara kuwa?" Ya dube ta sosai, "Na
sani mana gimbiya Husamatu ce." Ya ba ta amsa kai
tsaye. Ta girgiza kanta, "Za ka yi nadamar marina da ka
yi, nadama mai yawa. " Ta tabbatar masa.
A lokacin wasu adadin kibiyoyi suka hudo tantin suka
nufosu, da matukar zafin nama ya kade waya ya saka
daya hannunsa da babu takobin ya riko gimbiya
Husamatu ya yi wani juyi da ita ta dawo daya barin
kibiyar da ta taho
sameshi a gefen kafada, jini ya fantsamar mata a
fuska.Ya juyo ya dubeta da duban jarumta, ya saka
hannu ya cire kibiyar daga kafadarshi, bai jira ta kuma
mai motsi ba ya surcta a kafada ya yo waje da ita a guje
adadin yawan kibiyoyi ya ci gaba da karuwa.
Ko ina ka duba dakaru su ne a kwance mutuwa ta
dauke ransu, ganin muguwar barnar da aka yi masu ya
matukar kona mashi rai, ya ja ya tsaya ya yi wata
kururuwa cikin tsananin fushi.
Bayan wani lokaci komi ya dakata, sannan suka hango
wata adadin runduna ta sadaukai mai matukar yawa ta
fito daga sashe da sashe na wurin suka matso suka saka
su a tsakiya.
Jalaludin ya sauke gimbiya Husamatu daga kafadarshi
ya yi duba ga rundunarsu dakarun da suka rage basu fi
mutum ashirin ba sai su hudu da suke tsaye ranshi ya
kumna matukar 6aci domin ganin barnar da aka yi masu.

47

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Babban sadaukin rundunar ya fito ya dubesu da duban
wulakanci ya kyalkyalc da wata muguwar darīya.
Jalaludin ya dubeshi a fusace kana ya ce masa. "Su
waye ku da har kuka aikata muguwar barnar nan
garemu?"
Sadaukin ya dubeshi shima bayan ya dakata da
dariyarshi kana ya bashi amsar tambayar da cewar.
Dakaru ne daga boka Hamaran, bokan duniya mai iko
akan komi da kowa shi ne ya aikomu da mu saro ma
kawunanku."Jalaludin ya kuma fusata da jin amsar
tambayarshi ya juya ya dubi Lansu ya mayar dakallonsa
ga 'yar uwarsa Mahusiya ya gansu kowa yana cikin
shirin yaki ya girgiza kanshi.Ya dubi gimbiya Husamatu
ya zaro wata takobi daga jikinshi ya mika mata, kana ya
ce mata.
"Tunda kin iya marin mutum zaki iya kare kanki daga
halaka domin babu mai kare ki."
Ta dubeshi a tsorace, ta kuma dubi wukar.
"Ban dogara da cewar wani ya isa ya kareni ba babu
mai iya kareni daga halaka sai sarki Allah."Ya dubeta da
mamaki, domin ya tabbatar maganarta haka take; ta saka
hannu ta amshi takobin da take hannunshi. Suka juya
kowanne kashi ya fuskanci daya bari, da daga murya
Jalaludin ya ce masa "Muna jira gareku da ku zo ku
đauki ranmu, kuma ku shirya riskar mutuwa." Maganar
ta konawa baban sadaukin rai ya yiwa dakarunsa tsawa
da su yi dauki garesu su yi masu sukuwar sallah.
Basu jira wani abu ba suka yo dauki kansu da zummar
su murkushe su tashin farko, su ma su Jalaludin suka

48

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

zabura suka taresu aka gwamitse, aka cure karar
haduwar makamai
ya cika wurin, sara da suka ya wanzu a tsakaninsu,
kasuwar yaki ta soma ciki, mutuwa ta soma shawagi a
tsakaninsu, jiniyasoma malala tamkar an bude teku.
Jalaludin ya zamto annoba a tsakaninsu yana yakin
nashi cikin tsananin fushi na fusatar zuciya haka ya sa
ya amar masu wata masifa duk wurin da ya saka gaba
sai dai Kaga dakaru suna zubowa, kawuna suna yawo a
sama. Haka Lamsu, hakama Muhusiya ta zamar masu
wata annoba 'yan koluta kadan suka kuntatasu suka
dinga saukar masu da masifun yaki babu kakkautawa,
hakan yasa suka rude suka kidime domin ganin masifar
da suke riska a vakin suka yarda makamansu ba tare da
sun shirya ba suka juya da baya aguje domin tsira da
rayuwarsu. Faruwar hakan ya matukar konawa babban
sadaukin rai domin abinda bai taba faruwa ba a gareshi,
tun da yake da boka Hamaran bai taba bashi aiki bai yo
nasara ba, domin a duk ayyukan da yake bashi wannan
shi ne aiki mafi kankanta, amman yake da kyauta mai
yawa don haka da
zazzafar zuciya ya dubesu cikin muryar tsawa ya ce da
su.
"Tabbas kaskanci ya tabbata gareku bisa abinda kuka
aikata don haka ku yi sani cewar ni dinnan yanzun nan
zan saro kawunanku na tafi da shi zuwa ga shugabana
boka Hamaran."
Jalaludin ya zaburo ya fito wajen filin da matukar
fusata ya mayar masa da zazzafan martani.

49

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Duk duniya babu mai iko da rayawa ko kashewa sai
Allah dan haka kayi sani cewar ni na fito zuwa gareka
domin ni na saro kanka a maimakon namu da zaka
saro." Yana gama maganar tashi ya yi dauki gareshi,
shima ya taso masa, suka yi wata kazamar gamuwa da ta
saka kasar wurin tayi girgiza, tartsatsin wuta ya tashi a
lokacin da makamansu suka gamu wuri daya, suka yi
zamiya suka. kuma juyo wa a fusace suka kuma
gamuwa da juna su ka soma musayar sara da suka a
tsakaninsu cikin tsananin gwaninta de gogewa wurin iya
sarrafa takobi. Suka tafiyar da lokaci mai tsayi suna
musayar sara da suka a tsakaninsu daga bisani Jalaludin
ya sauya salon yakinshi zuwa wata kala hakan yasa ya
kuntata shi ya takurashi ya shamace shi ya kai masa
wani gawurtacce sa ara ya sameshi a wuyanshi ya tashi
kanshi sama, Jini ya yi tsartuwa, gangar jikin ta zame
tayo kasa mutuwa ta yi gagawar daukeshi. Jalaludin ya
dubeshi da duban nutsuwa kana ya mayar da dubanshi
ga gawarwakin mutanansu da suka yi shahada ya ji
zuciyarshi ta yi daci ya girgiza kanshi cikin girman
takaici. Su Lamsu suka karaso gareshi suna masu jinjina
gareshi suka harhada gawarwakin musulmai suka yi
zana'izarsu suka binne, suka matsa daf da birnin Farisa
suka sauka da zummar gari ya waye Kowane ka duba a
cikinsu cikin tarin gajiya domin yakin da suka yi duk
kamanninsu ya sauya jini face face a jikinsu a hankali
Jalaludin ya daga kanshi ya dubi Gimbiya Husamatu
itama ta dubeshi suka dubi juna tsawon lokaci ya ga
yanda lokaci daya ta sauya kama domin gwagwarmayar

50

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

da aka yi tamkar ba ita ce macen da ta gwanance wurin
iya kwalliya wacce take yiwa kwalliya kyau, wacce
kyawun
fuskarta yake dimauta duk wani sadauki ko sarki da ya
ganta, amman wahala yan lokuta ta wujijiga ta Ya kawar
da kanshi daga gareta gami da yin marayan murmushi
gareta don ganin yanda 'yar gata wacce ake lele ba a son
a ga tasha wahala dan gata, amman ita ce ta rike takobi
domin kare kanta, a hankali ya mike daga wurin da yake
ya nausa cikin daji, bayan tsawon lokaci ya dawo yana
dauke da ruwa a cikin salgogin ruwa manya da aka
dinka da
fata, ya sauka ya mikawe kowa yana zuwa ga Gimbiya
Husamatu ya dubeta da duban nutsuwa kana ya ce mata.
"Yakamata ki dauraye jikinki ki gyara ki koma tamkar
tauraruwar ki don washe gari ki tashi tas dake abun
haskakawa garemu."
Da tausasa murya ya ce mata. la dago ta dubeshi da
duban nutsuwa ba ta ce masa kala ba ta saka hannu ta
dauki salga daya ta soma wanke Jikinta ya bita da kallo,
kana ya sami wuri ya zauna. Lamsu da Muhusiya suka
ware gete daya suka yi zamansu suka ci gaba da
hirarrakinsu cikin tsananin jin dadi Washe gari sakon
zuwansu kasar Farisa ya isa ga waziri ya yi hawa da
kanshi tare da dakaru suka zo suka
taresu, matarshi tayi matukar farin ciki mai matukar
yawa domin ganin yan uwanta suka yi masu jagoranci
domin shiga cikin birni suka nufi fada domin zuwa
sukai gaisuwa ga sarauniya.Suka shiga fa dar daya

51

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

bayan daya sarauniya Samnatu tana zaune akan
karagarta cikin nuna takama da sarauta.
Tun tsawon lokacin da sarauniya Samnatu ta zamto
sarauniyar kasar Farisa babu wani mahaluki da zai ce ya
taba ganinta cikin farin ciki ko dariya babu wani
mahaluki da ya taba ganinta tayi, duk da zamtowar
mulkinta ya zamto a bisa tafarkin adalci.Suka gama
shigowa daga baya Jalaludin yahigo,idanuwan sarauniya
Samnatu ya kai gareshi suka yi musayar kallo da ita, ta
mike da sauri daga kan karaga, fadawa suka mike a
razane.
Ta zubawa Jalaludin idanuwa, haka yasa kowa ya
tattara

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment