Reading DIMAUTA Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mafarki
yake ba, don ya tabbata idan don albashinsa da cuwacuwar
da yake samu zai tara, to har ya mutu ba zai tara koda
rabin duniyar ba.
"Na aminta zan yi matukar farin ciki, idan zan samu
wannan dukiyar, amman zan nuna muku wata asirtacciyar
Kofa, ta nan za ku dunga shigowa duk lokacin da za ku
zo." Ya ce da su.
Gimbiya Suhaila ta ji wani dadi ya lullube mata zuciya
"To gabatar da mu gare shi. la ce a tausashe"To ku tasu
mu je." Suka tashi suka bi bayansá shi kuma ya shige.A
wani daki suka ganshi a dauc cikin sasarin da ganshi da
farko. Gimbiya Suhaila ta ce da Jal, "Kwance masa
sarkar,"Jal ya gabata gare shi ya dube sa ya ce da shi.
"Ya kai ma'abocin kamala ka y! sani yar sarki ta zo
gareka bisa aminci, don haka muna son don aninci ka
saurareta, kuma za mu kwance ka, don ka samu
nutsuwa,amman kar ka cutar da ita, don darajar abin da
kake bautawa."Sadauki Kafilu ya ji an đaurc shi da
jijiyarsa, don haka sai ya kudurce a zuciyarsa bubu

18

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

zallunci ga duk mutumin da ya nemi aminci a gare shi,
don haka da ya kwance shi bai ko kalle shi ba, ya yi mika,
ya yi godiya ga
Ubangiji Allah sannan ya tattara gashinsa ya watsa
baya,ya juyo ya kalli inda su gimbiya Suhaila suke. Ya
ce,"Menene yuke tafe da ku?"
Ai ko da suka ganshi a tsaye sai su ka kuma dimaucewa,
wutar son sa ta kuma kona zuciyar Suhaila, ita kantaZulza
sai ta dmauce.
"Zuciyarta ta kamu da Sonka ya kama zuciyata hakan
yasa na kasa daurewa sai na zo na sanar maka abinda yake
cikin raina, ko hakan yana nuna cewar za ka rike ni a
matsayin kuyanga a gareka,don na tabbatar ba zan rayu ba
idan na rasaka"A dimauce tace masa. amma jin abinda
tace yasa ya dubeta nan take shima ya ji Zuciyarsa ta
kamu da begenta. "Ba zan iya cewa bana sonki ba, domin
kin cancanci haka, kuma ita soyayya daman tana rayuwa a
zuciyar wanda bai taba tsammani ba, amma abin da nake
son da ke kuma nake son nusar da ke shi ne, ki yi sani ni
Musulmi ne, mai bautawa Ubangiji daya, ko kuma kuba
kuke bautawa, don haka abin da zai hanani soyayya da ke
kenan."Yana gama gaya mata haka sai ya matsa zuwa
kuryar dakin, ya jingina da katangar dakin.
Gimbiya Suhaila ta yi duba zuwa ga kuyanga
Zulza,ganin haka sai kuyanga ta sunkuyar da kanta kasa ta
ce,"Duk abin da kika yanka daidai ne a gareni."Nan da nan
gimbiya Suhaila ta matsa zuwa gareshi ta ce,
"Ka yi sani cewa ni yanzu kuyangarka ce, kuma komai
ka bida daga gareni zan aikata maka, don haka ina kira

19

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

gareka da a yanzu maza ka sanar da ni addininka ni kuma
zan
shiga da gaskiya, matukar kuma za ka kauna ce
ni."Kafilu ya ji wani dadi ya lullube masa zuciya, domin
jin ta ce za ta Musulunta. Nan da nan ya dauki kalamai
masu dadi yana fada mata yana yabonta da kyawunta.
A wannan lokacin haka suka kasance tsawon wani lokaci,
suna cikin kyautatawa junansu da farantawa
rayukansu.Kafilu ya sanar da su kalmar shahada suka
karba, suka Musulunta da gaskiya.
Nan suka zauna suka soma hira, kuwa yana baiwa dan
uwansa labarin abubuwa mafiya al'ajabi na rayuwa, a 1aka
suka tafiyar da lokacin mafi girna, a lokuta, har dare ya
shigo, sannan suka yi sallama da shı suka sulale. Suka bar
kurkukun suka nufi hanyar zuwa gida
Zuciyar ginbiya Suhaila fal da farin ciki. A wannan
daren haka ta tafiyar da shi tana mai kyauta ga bayinta.
**
A sannu a hankali soyayya ta kullu matukar kulluwa a
tsakanin Kufilu da gimbiya. Kamar yadda ta saba yau ma
suka sulale ita da kuyangarta suka nufi kurkukun. Suna
zuwa suka tarar da Jal a barauniyar hanyar yana jiran
zuwansu, Lamar yanda ya saba, suna karasawa ya fadi ya
yi gaisuwa gare su. Gimbiya Suhaila ta amsa sannan ta
mika masa nau'in dukiya kamar yanda ta saba.
Ya amsa ya yi godiya. Ita ta wuce zuwa wurin
masoyinta, shi kuma suka zauna tare da kuyangarta
Zulza. Ganin gimbiya Suhaila ta shiga kamar yanda ta
saba,sai Jal ya yi duba ga ulza duba irin na ma'abota bege

20

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

ya ce da ita."Ki yi sani ya Zulza son ki ya kama zuciyata,
domin tun lokacin da na soma ganinki na ji na abka a
duniyar begenki."
Zulza ta yi duba a gareshi duba na nutsuwa, sannan ta
haskake shi da murmushi. "Kamar yanda ka kasance haka
nima na kasance, to
amman ka yi sani ba damar soyayya a tsakanin mu da ku
don abu guda daya."A dimauce ya dubeta.Wane abu ne
wannan na gaggauta biya miKi shi da kuwa duk duniyar
da kuka ba ni ce?"Zulza ta yi murmushi.
"Ba dukiya ba ce, face banbancin addini .i Musu ce, kai
kuma kuba kake bautawa.
Jal ya dubeta a nutse. Sannan ya ce.
To yanzu idan na dawo addininki za ki soni, ki
kuma zauna tare da ni? Ta ta yi murmushi.
"sosai."To maza sanar da ni na shiga wannan addini
naki."Nan da nan ta sanar da shi, kalmar shahada, ya
Musulunta da gaskiya.
"To taso mu je gaban shugabanmu ka jajjada
gabansa"Bai yi mata gardana ba, ya mike. Suna zuwa
suka tarad da sSu sun shagala a duniyar soyayya. Ganinsu
shi ne ya dawo da su zuwa gare su Nan da nan Zulza ta
kwashe labari ta gaya musu. Ai ko da Kafilu ya ji haka sai
ya tashi da gaggawa ya sumbaci Jal. ya soma yabonsa da
kalamai masu taushi. Gimbiya Suhaila ta yi duba zuwa ga
Zulza ta ce da ita.
"Daga yau ya Zula na 'yata ki kin zama yantacciya." Ai
ko da Zulza ta ji haka sai farin ciki ya lullubeta, ta rasa
inda za ta saka kanta, dan haka sai ta sabi wasu baituka na
waka.

21

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

A wannan lokacin Jai ya bayar da sadaki aka daura masa
aure da Zulza, shina Kafilu ya ciro wani zobensa da Wani
kambo da ke hannunsa ya buiwa Suhaila a matsayin
sadakin aurenta.
Su Zulza suka tasihi suka bur su Kafilu a zaune yana
cike da farin ciki. A wannan lokacin Kafilu ya gabato
zuwa ga Suhaila ya soma ambaton kalaman bege a garera.
A wannan daren suka yi raya daren cikin aminci na
angwanci ya santa a matsayin 'ya mace
Wannan ranar a haka suka tafiyar da ita, kowa yana mai
matukar farin ciki, da anashauwa. A wannan kwanciyar ta
samu ciki, ita ma Zulza ta samu nata cikin.
Kwance tashi suka fahimci suna da juna biyu,
hakan ya yi matukar tayarwa da gimbiya hankali, don
susann asirinta ya kusa tonuwa, to amman sai wata dabara
ta fado mata.
Yana daga al'adarta duk shekara ta fita wani gidanta da
ke bayan gari ta shiga ita kadai ta yi ta neman yarjewar
Kuba a gareta, kuma idan ta shiga tana samu akalla wata
biyar a ciki ba ta fita daga gidan sai ranar bautar kuba, don
haka sai ta yanke yau ita ce ranar tafiyarta, don kada
asirinta ya tonu.
Ta gabata gaban mahaifinta ta sanar da shi, sarki ya yi
mata kyakkyawar addu'a kamar yanda ya saba ta đauki
kuyangata Zulza suka nufi gidan, bayi da barada biye da a
su.
A daren Jal ya dauki Kafilu suka sulale suka nufi gidan
kurkuku. Ba su samu wata matsala ba suka gamu
masoyansu, don sun tsara duk yanda komai zai gudana

22

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

daman. A haka suka wanzar da wannan daren. Suna masu
kyautattawa ga junansu, kowanne ya mayarwa da dan
uwansa kalmar bege.
A haka su gimbiya suka ci gaba da rainon cikin har ya
tsofa. A daren wata rana ne gimbiya Suhaila ta haifo danta
namiji kyakkyawa, ita kuma Zulza ta haifo mace.
**
A zaune a dakin bokancinsa yana zaune yana nazarin
bokanci,can sai wata guguwa ta turnike a dakin bokacinsa
su ka soma tarwatsewa
nan da nan hankalin boka Kanzal ya tashi.
Bayan wucewar wani lokuta, sai komai ya lafa,
sannan wan jibgegen aljani ya bayyana, ma'abucin
kalaman tsoro, ko shi Kan shi bOka Kazal sai da ya tsorata
da ganin aljanin Aljanin ya kalle shi da idonsa daya ya ce
da shi.
"Wane irin sake kuka yi aka haifi masifa, bala'i a duniya,
ba ku kadai ba har gamu duniyar aljanu, mun shiga uku da
abin da aka haifa a zuri'ar, kun zamto gafalallu na' abota
gafala."
Boka Kazal ya dubi aljanin nan ya ce da shi.
"Waye kai, kuma a ina aka haifi masifar?" Aljanin ya yi
dariya, sannan ya ce.
"Nine aljani Jagar-Jagar, bokan da ya gagari duniyar
aljanu, kuma boka da kc kuba shi ne ya sanar da ni, sirrin
alkaluma, kuma na tabbata duk lokacin da ya tashi daga
barcin da ya shiga ya tara da abin kunyar da kuka cikata
Sai ya hukunta ku, kuma ina kira garcka da ka duba
zuwa ga madobin tsafinka, ka baza alkaluma ka nemo

23

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

gimbiya Suhaila za ka samu labarin komai, ka kuma duba
labarin abin da aka haifa. Tir! Da ku gafalallu."
AlJani Jagar-Jagar yana gamawa ya bace a fusakce. Nan
da nan boka Kazal ya zuba alkaluma ya fitar da uwa ya
haifar da ita, nan da nan komai ya bayyana a
gare,hankalinsa ya baci, ranshi ya baci, zuciyarsa ta
dimauta bakinsa ya soma kumfa "An haifo bala'i da masifa
ga mutanen duniya. Boka Hamran ne kawai zai iya yarje
mana wannan bala'in"
Nan da nan mike ya nufi gidan sarki a kufule
wa ya wuce har zuwa turakarsa, ya same shi ya Sa Biya
ya yi tatul ga wasu akusai tana zuba a gabansa. Ganin
yanda ya shigo yasa sarki Shamal ya yi
girigza, domin ya san babu lafiya. BOka ya zube kayan
aikinsa ya dubi.sarki ya ce da shi.
"Dubi abin da yarka ta jawo mana, ta jawo mana masifa
da bala'i." Ya nuna hoton dan da ta haifa ya ce.
"Na rantse da kuba wannan yaran da aka haifa yafi
mahaifinsa bala'i, yafi shi masifa, don shi aljanu ma sun
shiga uku."
Sarki Shamal ya mike a matukar fusata, idonsa ya kada
ya yi ja, kumfa ya soma fita ta bakinsa.
"Na rantse da kuba sai na azaftar da Suhaila sai na yanka
ta ga kuba, daga ita har dan nata."
Sannan ya saurara yana huci.
"Shi kuma Kafilu sai na kuna shi da ransa na watsa tokar
tabi iska."Nan da nan ya dakawa wasu sadaukai tsawa ya
ce su je gidan bautar Suhaila su kamo masa ita.Minti
kadan sun gabato da ita gaban sarki. Tana

24

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

wulakantacciya."Ina dan nata, ina kuyanga Zulza?"A
fusace ya ce da su, wani sadauki ya sukunyo ya ce,
"Raina fansa ne a garcka ba ka ce mu taho tare da su ba.
"
"Ko kuma ko zo mini da komai nc da ke gidan, ko da
kuwa kiya shi ne."Nan da nan sadaukan suka juya suka
kuma yiwa dawakansu kaimi, suka nufi gidan.To amman
lamarin Zulza tana ganin haka sai ta sulale ta nufi kurkuku
ta sanar da su Kafilu, abin da yake faruwa, ai ko da. Kafilu
ya ji haka sai ransa ya baci zuciyarsa ta dugunzuma,
tsohuwar kiyayya ta dawo masa sadaukantaka ta motsa.
Ya yi duba ga Jal da Zulza da ya'yansu ya ce da su."Yanzu
abin da nake so da ke ku sulale ku tafi can kasar Misira ku
zauna ni zan biyo ku daga baya na same ku."
Suka amsa a tare. Jal ya nuna wa Kafilu wurin a jiyar
kayan yaki na Kasar. Kafilu ya fasa wurin ya shigo ya yi
shigar yaki. Da ya tito sai da Jal da Zulza suka tsora da
ganinsa.Ya kama dawakai guda uku ya hau daya ya dora
su akan guda biyu, suka fito daga cikin gidan yarin.Suna
fitowa suka tarad da taron sadaukai sun yi sahu sahu suna
jiransu. Ai ko da Jal ya ga rundunar sai ya sadaukar ya
saduda, ya kalli Kafilu ya ce da shi.
"Mu mika kanmu kawai." Kafilu ya yi murmushi, ya çe.
"Bara na tarwatsasu ka ganı na samar muku hanya, in ya
so gobe na dawo na yake su ido na ganin ido, na dauki
matata na biyo ku."Jin maganar tasa ta saka hantar cikin
Jal motsawa.Don ya san sadaukantar rundunarsu.
Wani sadauki ya zaburo ya fito a cikin shigar yaki sai
huce ya ke yi, ya ce da su Kafilu.

25

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Ku gabato gabanınu kuna wulakantattu, mu kai ku uwa
ga shugaban ya yanka muku hukuncin zunufin da kuka
aikata masa" Kafilu ya kalle shi a wulakance ya ce.
"Kai mata maza, tsayawa mayar da magana ragwanta
nan ni Kafilu garcku, na rantsc da Ubangiji Allah sai na
shayar da ku gidauniyar mutuwa nan da sa'a guda". zuciya
kamar dutse, Suma suka kifu akanshi da wa kawuna Nan
makamai suka soma shawagi a sama, ya tsuntsaye, Jukuna
suka
wata Yana gama fadar haka ya yi dauki kansa dawakai,
suka wanzu ba mahayansu. Kafilu ya wanzu a da b suka
soma tashi kamar tsakiyar su kamar wani shaidani. Jini ya
dunga kwarara tamkar kwata, masi na yaki ya dunga sauka
a kan sadaukan kasar Hamra Kafin wani lokaci Kafilu ya
karar da su gaba dayansu Abin ya yi matukar baiwa Jal da
Zulza mamaki don ba su taba ganin yaki kamar wannan ba,
ba su taba jin labarin sadauki kamar Kafilu ba, hakan ya
abin ya Hamran gimamu a gare su.
Suka gabato gare shi suna masu jinjina da yabo na daga
irin bajintarsa.
A haka suka dunguma suka bar garin. Bayan sun yi
tafiya mai nisa, sannan ya tsaya ya amshi dansa ya
Sumbace shi, hawaye suka kwaranyo masa, ya cire wata
azurfa da ke wuyansa ya daura wa dansa a wuya, sannan
suka rabu ya kama hanyar komawa garin, don dauko
gimbiya Suhaila, su kuma suka dauki hanyar zuwa kasar
Misira.
A wani wuri mai komai da fadama ya sauka ya

26

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

yi Sallah Asuba, sannan ya gyara kayan yakinsa. Daga
nan ya hau ya nufi cikin garin Hamran, ya yiwa dokinsa
kaimi yana mai azama da himma.
**
Sadauki Kafilu ya wanzo yana mai azama har
karaso kofar garin, yana zuwa ya tarar kofar a bude,
ganin haka batare da ya jira ba ya tura kai zuwa cikin
kasar.Sai da ya shoga ne sannan ya fahimta ashe-barad sun
zagaye katangar garin, kowannensu daüke da kibiya
amma bai damu ba sai ya ci gaba datafiyarsa, lokacı daya
kuma ya yarda Takobinsa da ke tare da shi ya saduda. A
haka dokinsa ya ci gaba da tafiya har tsakiyar birnin yana
karasawa dakaru suka ba shi hanya yana shiga wasu
sadaukai suka watso masa sarka suka zarge shi. kafilu ya
daga kai ya kalli masoyiyyarsa Gimbiya Suhaila dake
daure cikin sarkoki duk ta taggayara,wani tausayinta ta
kamasa bai san lokacin da wasu hawaye suka Zubo masa
ba domin bai taba tsamanin faruwar hakan ba.
koda sarki shamal ya ga kafilu ya wanzu q faire. sai ya
gabato Gare shi yace "Ka kawo kanka cikin ruwan sanyi
makaskanci bawa,yanzu zan yanke maka hukunci akan
abinda ka aikata amma kafin nan sai na soma yankewa
'yarta Hukunci akan abinda ta aikata na cin amana"Yana
kammalawa ya juya ya dubi 'Yarsa a wulakance yace mata
"Kiyi sani ya 'ya ta na kyautata miki tsawon lokaci,na
kaunace ki matukar kauna,amma kin zo mun da abinda
gwara na halakaki"Gimbiya Suhaila ta yi duba ga
mahaifinta duba na nutsuwa, sannan ta yi murmushi.
"Ina Raunarka ya mnahaifina, kauna ta hakika

27

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

kuma gareka da hakan shi ne ya sa da na samu shiriya
nake kira gareka zamto shiryayye kamata, wato ka shiga
cikin addinin tsira." Jin maganar ta batawa sarki rai.
"Amman babu gafalalliya kamarki, tabbas kubba tana
fushi da ke."
"Allah shi nc abin bauta, kuma shi kadai nake neman
taimuko gareshi." Ta yi duba ga Kafilu ta ce da
shi."Yanzu na soma sonka ya masoyina, kuma soyayyarka
ba zan daina ba."
Ran sarki Shamal ya kuma baci. Ya yi matukar
fusata ya dubi 'yarsa ya ce.
"Ina kira garcki da ki yi imani da kubba ki dawo
kyautatawa garcta, idan ba haka ba yanzu na shay ar da
ita jininki don kar ki yi tunanin ke kadai ce 'yata zan iya
salwantar da rayuwarki gareta." Gimbiya Suhaila ta dube
shi ta yi yalwataccen murmushi, sannan ta girgiza kanta, ta
ce.
"Allah shi ne abin bauta, tir! Da kubba ma'abociyar bata
wacce ba ta amfana da ku ko... Ba ta karasa maganar ba ta
kama mata ciki, sakamakon abin da ya faru. Da zafin
nama sarki Shamal kuma mahaifin gimbiya
Suhaila ya zare takobinsa daga gidanta, ya yanka mata
makogwaro, jini ya yi tsartuwa ya bata fuskarsa da ta
Kafilu da wasu sadaukai dake wurin, boka Kazal da ke
wurin ya yi sauri ya faki rdon sarki ya dti jinin ya zuba a
wata kwalba. Kafilu ya kwalla wata irin kara, ya zube a
kasa bisa gwoyoyinsa.
Gimbiya Suhaila ta dunga wani wutsul-wutsul,domin
zafin fitar rai. A haka har ta karasa: Fuskarla ta kara kyau,
murmushi a makale da fuskar ta,Sadauki Kafilu ya dago

28

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

kansa ya kalli Suhaila, nan da nan ya ji wani karfi ya zo
masa. Cikin matukar fusakta ya mike ya janyo sadaukan
da suke daure shi da sarka ya gwara kasú kan ya larwalse,
ya yi tsalle ya haye dokinsa, ya aburc shi ya hau da shi har
zuwa wurin da Suhaila take, ya kurawa gawarta idanu,
hawaye suna ta kwararowa daga idonsa, bai taba tsammani
zai kashe ta ba.
Da sauri ya zura' hannunsa a Kasan dokinsa ya zaro wani
bakin al'amudi' ya soma wujijiga shi, ya dubi kan waziri
Kazal da ke tsaye kusa da gawar ya shımfida masa shi
Kafin waziri ya yi yunkurn wani abu na daga bokancinsa
har al'amudin ya sauka akaņsa ya tarwalse,kwakwalwa ta
zuba, ganin haka ya Sa mutanen gari suka rude suka
kidimo, suka soma guje-guje.
Sadauki Kafilu ya zaro wata tükobi a cikin
damararsa ya kifu cikin sadaukan da ke tare da-sarki
Shamal ya soma risko da su zuwa ajalinsu. Sarki Shamal.
ya juyo da gudu ya haye dokinsa ya juya da gudu don tsira
da rayuwarsa Ganin haka ya sa sadaukan dake
saman.katanga suka soma ruwan kibiya, babu Kakkautawa.
Kafilu ya dunga kadewa da al'amudinsa yana bugewa da
takobinsa, katin
wani lokaci sun Karar da 'yan uwansu. Nan shi ma
Kafilu ya aro wala kibiyarsa ya soma mayar da martani
gare su. kafin wani lokaci ya zubar da mafiya yawansu
sauran kuma kibiyoyinsu sun kare don haka suka soma
'yar boya harbo sal su noke.
Ganin suna neman bata masa lokaci, sai ya
dokinsa ya nufi hanyar da za ta kai shj fada. Ai koda ya
kusanceta sai ya ga Wasu gungu na Sadaukaj sun tunkuare

29

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

shi. Nan shi ma ya kifu kansu Suka soma sokckeniya, suna
kaiwa junansu sara da suka babu Rakautawa, ko'ina Kalilu
ya saka gaba sai ka ga kawuna Suna yawo a saina Kamar
tsuntsaye Ya dunga saransu yana dokansu da alamudinsa,
ya dunga yakarsu, da wata zuciya nai karti kamar dutse, ya
dunga saukar musu da Rofofi na bala'i da masifa ta yaki,
soma kuma rundunar suka kuma azana da hinma don
ganin sun kare martabarsu.
Wannan yakin nasu haka ya wanz1 suna yin sa har
duhun dare ya shigo. Gari ya kuma wiayewä mman bubu
wanda ya gaji a Cikinsu. kowa kara himma yake don
ganin ya hakewa dan uwansa ya ribace shi Can da hantsi
ya diaga sar sadaukan sarki Shamal suka soma sarewa, da
Kafilu yu fuskanci haka sai ya kuma azama, don ganin ya
cim musu. Nan da nan suka dimauce domin ganin wani
bala'in da yake saukar musu da shi Tin ya dunga kwaranya.
kamar wata mayanka Kawuna suka wanzu zube a kasa,
jikuna suka wanzu kama
fikar
alkalami,
dokuna
suka
wanzu
babu
mahayiansu.mutuwa ta dunga surarsu tana gaggauta su da
makomarsu, Kasa ta sha ta batse da jinin bil'adama haka
ya dunga ratsawa ta tsakaninsu yana kashe su, nan da nan
sadaukan sarki Shamal suka kidime. dorn suna ganin tun
da an kwana zai iya galabaita ya sare, to amnman sal su ka
ga wani sabon karti ne ya zo masa ma, domin yanda ya
kuma azana.
Ganin yanda ya taKura su yana neman karar da su, ya sa
'yan tsirarun da sUka ragC, suka yarda makamansu suka
ari takalmin kare, domin tsira da rayuwarsu, don sun
fahimci ba za su wanu na sa'a daya ba a gabansa face ya

30

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Karar da su Ganin sun tsera ya sa Kafiulu juyawa domin
tunkarar kofar fada, don gabatar da aniyarsa ga sarki
Shamal.
Shamira ita ce mahaifiyar gimbiya Suhaila tana matukar
sonta, musamman domin ganin ita kadai ce 'yarta, kuma
duk matan sarki babu waccc ta taba haihuwa sai ita, hakan
ya sa ta dauki son duniyar ta durawa yarta. Tun lokacin da
labari ya risketa akan abin da 'yarta ta yi da kuma a yanda
aka kannata sai hankalin Shamıra ya dungunzuma ta
kidime, hawaye suka soma kwaranyowa daga cikin
idanuwanta. Da sauri ta fito da zumar zuwa ta samu Sarki,
to aminan tana fitowa sai ta ga wasu murda-murdan
sadaukai a tsaye suna ta muzurai."Kai bukaken macizai
ina sarki yake?" Shamira ta ceSu. Babu wanda ya daga
kansa ya dubeta. Karnar da duwatsu ta yi magana.
Ganin haka sai ranta ya kuma tsananta bace, ta nufi
hanyar turakar ta sarki, amman tana zuwa sai sarkin
dogarai ya tareta ya ce'da ita.
"Sarki ya bada.izinin cewar ko waye kada a barshi ya
shiga."
Jin maganar ya yi matukar batawa Shamira rai
matukar, daman kuma gashi ranta ya yi matukar bace,
don cikin dakin, sarkin dogarai ya yi tsalle ya tsaya a
gaban "Ki yi hakuri ya shugibali, doka ce daga sarki"Ta
daga masa harara ba a
"Kasan da son da sarki yake mini da kuma Sa aikata duk
abin da na ce ya yi mini, to ina rantsuwa da kuba zan saka
ya mayar da

31

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

kai mai jiran Kofar gari"Ai ko da sarkin doparai ya I
yanarla, sal jikinsa ya yi sanyi ya matsa ya bata wuri Ta
wuce ta sami sarki a Zaune ga
tukunan giya nan a gabansa sai sha yake babu
kaukautawa, daga ya ajiye wannan sai ya kuma daukar
wata, ganin haka Ta gaggauta zuwa gare shi ta tsugunna a
gabansa, shi na ya dago ya dubea, duba irin n nasu uzuri,
sannan ya kawar da kansa zuwa gereta
"Wai mai kake shirin akatawa ga 'ya ta ne"ta kawar da
shirin da ya samu natsugunni a tsakaninsu.Sarki Shamal
ya dubi matarsa gami da kawar kansa.
"Zan hukuntata akan abin da ta aikata a gaba
mutane, donin haka ya zamto darasi ga duk mai sha'awar
aikata haka anan gaba."Shamarn ta zaro idanuwa, domin
jin abin mijin nata ya ce. hawaye ya soma kwaranyo mata
duk idanuwanta babu kakkautawa,ta sunkuya
gwiwoyinta ta tsugunna a gaban sarki Shamal
"Ka yiwa yata adalci kasan ita kadai muka haifa"Kwar ta
kadaice 'yarmu, amman duk duniya bamu da abokin gaba
tamkar Musulmi, kuma gashi ta shiga cikinsa don haka
yanzu 'yala ta zamto makiya a gareka kuma nan yi
rantsuwa ga kuba duk son da nake mata matukar ba ta fita
daga addinin da ta shiga ba ta dawo ta gaba da bauta da
kyautayi ga Kuba sai na shayar da kuba jininta"
Shamira ta yi duba ga sarki Shamal duba na
gafalallu, sannan ta kuma turbune fuska.
"Wai da kan ka kake tutiya za ka shayar da jinin 'yata ga
kuba?" A wannan karan giyar da ya sha ta soma yi masa
karo burci ya soma daukarsa. Hawayc ya kwacewa
Shamira, ta

32

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

soma shashshckar kuka.
"Ba ma kaunar 'yarta."
"Duk wanda ya'taba kuba zan taba shi."
"Ma'ana da gaske kake za ka iya kasha yar tawa?"
"Kwarai matukar ba ta bar sabon addinin da ta shiga ba."
"Yanzu duk soyayyar da nake maka kaima kake mini da
abinda kenan za ka saka mini." Ya dubeta duba na
nutsuwa.
"Har kullum Shamira babu wanda nake matukar so kanar
ke, da 'yarki, amman ba zan taba kyale yata da Wannan
lefin ba, don jama'ar kasar nan za su samu damar bayyanar
da addininsu, wata rana za a wayi gari an daina bauta ga
kuba, amman a yanzu duk wanda ya ga hukunci dana
yanke gareta, kowa sai ya zamto a cikin taka-tsantsan
Yana gama maganar ya kishingida, kal.. wani lokaci barci
ya dauke shi.
Shamila ta ji wani abu ya sarke mata zuciya "Kada ka
aikata haka ga yata, don gaba
a ta tsakaninmu da kai, mai yawa don sai na daneSiga
fansa matukar ka aikata haka a gareta." Da matukar fusata
ta ce da shi. Idanuwanta sai Zubar da hawaye suke,
amman bata kuka sosai ba, har ya yi nisa
a duniyar barci.Ta tashi ta fita da zumar da safe ta koma
ta same shi.Amman tana kumawa sai ta kasa barci, don
yawan tunani,da safe da ta tashi da zummar fita sai ta tarar
ann saka wani katon kwado an kulle dakin nata.
Ta dun ga dukan Rofar tana kuka, tana kiran sunan yarta,
babu kakkautawa, hawaye suka dunga kwaranyo mata, ta
kidime ta zabure, ta rude ta dunga ja da baya tana tawowa
da gudu tana dukan kofar da kanta da hannunta da jikinta.

33

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

A tunaninta hakan zai saka ta bude. Amman ko motsawa
ba ta yi, duk ta jiwa kanta ciwo ta koma ta yi zaman 'yan
buri a tsakar dakin tana wani irin kuka, duk ta yi kacakaca da duk kayan dakin.Tana nan zaunc, bayan shadewar
wani tsawon lokaci, ta ji an budc kofar, sannan wasu
dakaru suka dana kai cikin dakin kowanne shege cikin
kayan yaki, sal nuzurai suke suna masu kokarin kaiwa iska
sara da makamansu.
Wasu kuyangi suka shigo suma da saurinsu, suna zuwa
suka zagaye ta suka kamata suka soma tafiya da ita,suna
fita suka sakata a cikin wani keken doki, sannan ba tare da
an juya ba balle a barta ta yi tambayar dalili aiko doki
daukarta, suka bulo ta wata barauniyar hanya.
Sai da suka yi tafīya mai nisa sannan ta juya ta yi duba
ga wata kuyangarta da ke zaune a kusa da ita, tana mata
fiftita. Ta ce da ita.
"Menene ya faru, haka na ga mun fito tanan? Kuma ina
muka dosa?". Kuyangar ta rusuna a gabanta, ta cc a
tausashe."Wani sadauki ne ya gallabi jama'ar garin nan da
yaki, don ya ci karfin garin hakan ya sa sarki ya ce da a yi
gudun hijira zuwa birnin Farisa, can garin amininsa, don
ya yarje masa wannan bala'in."
Shamira ta rausaya da kanta.
"To ina gimbiya kuma?"Kuyangar ta kuma sunkuyawa a
gaban Shanira.
"Labari ya iskeni wai sarki ya yankata. "
Ai ko da jin haka sai Shamira ta zube a wurin
sumammiya, ganin haka sai hankalin kuyangar nan ya yi
matukar tashi ta rude A wajen kuma sarki Shamal ya

34

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

shigowa cikin gida,sai ya dakawa sadaukan kofa tsawa, ya
ce da su.
"Ku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment