Reading DIMAUTA Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinsa gareshi, ana jiran ganin abinda zai iya
faruwa tsawon lokaci ba tarc da wani ya ce kala ba face
kallon da sarauniya Samnatu da take yiwa
Jalaludin.Wannan kallon da take mashi haka yasa
gimbiya
Husamatu taji wani irin zafi a zuciyarta, wata kulewa
ma tarin yawa ta mamaye mata rai, tana da masaniyar
inda wadannan mutanen masu mulki ma'abota son
kyakkyawan saurayi ne don hakan da ta ga sarauniya
Samnatu tana masa kallon sai taji ranta yana ci gaba da
baci.akan yasa tayi wata irin fitowa da ba a tada
tsammani ba, wanda motsin nata ya zamto motsi na
farko aka yi a cikin fadar, ta shige gaban Jalaludin ta
tsaya ita fuskanci sarauniya Samnatu, faruwar hakan
yasa komi ya soma dawowa daidai. Sarauniya Samnatu
ta yi wani yalwataccen murmushi
garesu da kwantar da murya ta ce masa.

52

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Barka da zuwa Kafilu."Maganar da tayi ta tattaro
hankalin su Jalaludin.Gimbiya Husamatu ta dubeta da
duban tsana kana da
muryar kishi ta ce mata.
"Wannan ba Kafilu bane, wannan Jalaludin ne."
Maganarta tasa sarauniya Samnatu ta mayar da
dubanta gareta, kana da muryar sarauta ta ce mata.
"Kada ki yi shisshigin shiga lamurana ta yaya zaki
karyata abinda idanuwa na suka gane mani babu shakka
wannan masoyina ne Kafilu wanda boka Hamaran ya
mayar gunki ta hanyar zuba masa ruwan sihiri."Maganar
da tayi tasa fada tayi shiru baka jin motsin komi sai
motsin zuciyoyin mutane. Maganar da tayi tayi matukar
sa bacin rai a cikin zuciyar Gimbiya Husamatu,
musamman domin ganin cewar abinda tayi zargi shi ne
yake shirin faruwa domin gashi nan tana kokarin cewar
saurayinta ne.Ta tabbatar da cewar ciwon hauka yana
damun sarauniya ta kasar Farisa.
Jalaludin ya fito ya tsaya a gabanta ya dubeta da duban
nutsuwa na tsawon wasu lokuta kana a hankali ya ce
mata.
"Ko zaki ya gaya mana labarin ki da alakar da ta
hadaku da shi Kafilu?"Ya tambayeta yana rutsata da
idanuwa, fadar tayi shiru tsawon lokaci daga bisani
sarauniya Samnatu ta komo ta zauna akan kujera
sarautarta cikin takama da nuna isa ta muiki tayi masu
nuni' da wurin zama suka zauna fada tayi shiru ana jiran
a ji labarin da zata bayar.Bayan tsawon lokaci ta nisa
Kana ta soma basu labarin rayuwarta da ta Kafilu. Ta

53

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

gaya masu komi.Tana gama basu labarin Jalaludin ya
mike tsaye dubeta da duban damuwa wannan karon
kamanninsa sauya zuwa ga tsananin damuwa, haka ma
kamannin 'yar
uwarsa Muhusiya kowa ya mayar da dubansa
garesu.Ya dubi sarauniya Samnatu da muryar jarumta ya
ce ya Sun mata.
Tabbas mahaifinmu ya taba gaya mani cewar ba shi ne
ya haifeni ba ya kuma bani labarın mahaifina da
rayuwar da suka yi da yanda ya taho da ni zuwa kasar
Misira, don haka ina rantsuwa da girman Allah sai na je
har zuwa fadar boka Hamaran na ciro kanshi na ceto
rayuwar mahaifina."Wannan kalaman nashi sun matukar
baiwa gimbiya Husamatu mamaki, don haka ta dubeshi
a tsorace ta ce
mashi.
"Ka bari mu koma gida mahaifina ya baka taimakon
mayaka mana."Muhusina ta dubeta da jarumta ta ce
mata.
"Abokin gabanmu ne shi yasa ya so ya halaka mu da
dakarun da ya aiko mana, don haka ina mai tabbatar
maki cewar insha Allahu babu wani taimako da zamu
nema na Isar masa da ni da dan uwana."Ta ce tan2
duban Jalaludin shi ma ya dubeta, ya girgiza kanshi.
"Zan yi tafiyar ne dake 'yar uwata domin kar nayi
rashinki."Ya ce mata.
Ta dubeshi a nutse itama ta ce da shi."Zan zamto mai
taimakonka duk runtsi duk wahala."
Lamsu ya mike ya dubi Muhusiya kana ya ce mata.

54

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Ba zan iya rabuwa dake ba domin san da nake maki
don haka ina tare da ke."Gimbiya Husamatu ta mike
tsaye ta dubesu duka kana ta mayar da kallonta ga
sarauniya Samnatu a hankali ta ce. Yanzu kin tabbatar
ba Kafilu banc Jalaludin nc don haka kama da wance
bata wance."
Ta gaya mata magana a fakaice, sannan ta juya ta dubi
Jalaludin ta ce masa.
"Duk da bani da jarumta zan kasance tare da kai cikin
tafiyarka."Maganar ta yiwa Jalaludin dadi da kara mashi
kwarin gwiwa game da tafiyar da zai yi, ta nemo boka
Hamaran. Sarauniya Samnatu ta mike zaune daga kan
karagarta,hakan ya yi daidai da tashin wata bakar
guguwa mai tsananin &arfi, duka jama'ar dake fadar
suka zuba mata idanuwa guguwar ta dauki tsawon
lokaci tana busawa daga
bisani ta soma dakatawa har ta yaye boka Hamaran ya
baiyana a cikin fadar.
Akayi carko-carko ana kallon-kallo, Jalaludin yana
dubansa a matsayin matsafi batacce, shi kuma yana
dubanshi a matsayin jarumi kamar mahaifinsa, sarauniya
Samnatu tana kallonsa a matsayin wanda ya rabata da
saurayinta.
Ya kyalkyale da wata irin dariya mai saka tsoro ga
zukata kana ya turbune fuska da muryar takama ya ce
masu. "Bokan duniya bokan da ya sanar da mashahurin
bokaye ilimin bokanci shi ne ya zo gareku don komi
naku ya baiyana gareni, ni ne boka Hamarna wanda
bana shayin mu yi gaba da gaba da jarumi, bana gwada

55

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

tsafi ga wanda ba matsafi ba, sai nayi amfani da karfin
dantse gareshi, in matsafi ne nayi amfani da sanin
alkaluma na karya shi.
Da muryar ji da kai ya ce masu. Jalaludin ya fito ya ja
ya tsaya ya dubeshi da duban Jarumta ya mayar masa da
martani ciki fushi na fusatar zuciya."Lallai 6ata ya
baiyana garcka mushuriki wanda AllahYa ara maka rana
tsawon zamani, tabas da iznin Allah zan shayar da kai
dacin mutuwa."Maganar tashi ta matukar batawa boka
Hamaran rai da matukar fushi ya dubeshi kana ya mayar
masa da magana cikin zafin rai.
"Kai yaro ne karami mai rangwamen karfi domin ko
mahaifinka da muka yi gaba da gaba da shi yaji babu
dadi."Maganar tashi tayi matukar harzuka zuciyar
Jalaludin,da azama ya zare takobinshi ya yi nuni da ita
ga boka
Hamaran kana cikin murya mai amsa amo ya ce masa.
"Nasara tana ga bawa mai dogaro da Alalh don haka
kayi sani cewar mai tashe ya kiyayi mai zamani."Yana
gama maganar ya yi dauki ga boka Hamaran a matukar
fusace, shima ya daga hannunsa sama wata takobi ta
baiyana bisa tsafī ya tareshi suka yi wata kazama
gamuwa da ta saka ginin fadar ya yi wata irin
girgiza.Sauran baradan da suke tsayc suka tsorata suka
zabura waje a guje domin ganin muguwar gamuwar da
aka yi.Suka yi zamiya suka kuma juyowa ga junansu a
fusace, suka kuma yin muguwar gamuwa, tartsatsin
wuta ya yi sama, suka soma musayar sara da suka a
tsakaninsu cikin gwanancewa ta yaki.

56

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Basu dauki wani lokaci ba Jalaludin ya shammaceshi
ya kafta masa wani sara a baya, saran ya sashi
kidimewa,bai bari ya dawo hayyacinsa ba ya sumameshi
ya rikoshi ya
dagashi sama ya maka da kasa, ya bishi ya damko
kafarshi ya daga shi sama ya yi hajijiya da shi da
zummar ya maka kanshi a jikin ginin fadar ya mutu
kowa ya huta, amman ga matukar mamakinsa sai ya ji
ya zame daga hanunsa kana lokaci daya ya koma bakar
guguwar ya bace daga wurin,Jalaludin ya jinjina abin a
cikin ranshi domin ganin rashin
samun nasarar da suka yi.Ya juya a hankali a lokacin
yaga bakar guguwar ta turnike a cikin fadar boka
Hamaran ya kuma baiyana ya dubeshi cikin fushi ya ce
masa.
"Matukar kai jarumi ne mai ji da jarumta kakan iya
samuna a fadata da takc tsiburin Marzuk domin ka
amshi mahaifinka da yake a matsayin gunki, ka kuma
taho da 'yar sarkn ku na Misira."Yana gama maganar ya
nufi wurin da gimbiya Husamatu take ya damketa. Da
zafin nama Muhusiya ta zarc takobinta takai sara
gareshi.Amman sun makara domin ya bace daga cikin
fadar cikin sirikan alkaluma, guguwar ta dunga yayewa
a hankali har ta yaye, wurin ya wanzu babu gimbiya
Husamatu. Jalaludin ya kurma wani irin ihu mai hauhawa ginin fadar ya girgiza, Muhusiya ta ja ta tsaya tana
duban shi itama Lamsu yana kallonta suka yi shiru kowa
ya kasa

57

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

magana domin girman takaici da yake damunsu
zuciyarsu tayi baki na bakin çiki.
Sarauniya Samnatu ta matso garesu suka mayar da
dubansu gareta.Jalaludin ya dubeta na tsawon 'yan
lokuta kana ya ce mata a hankali da muryar tashin
hankali.
"Ko kina da masaniyar hanyar zuwa tsibirin Marzau?"
Da muryar jarumta ya tambayeta.
Samnatu ta dubeshi da duban takaici da yake damke a
ranta, tayi shiru na tsawon lokaci tana dubanshi daga
bisani ta nisa kana ta ce masa.Bana tunanin cewar akwai
wanda zai nuna maku hanyar zuwa tsiburin Murzau idan
bani ba."Ta ce tana dubansu, kana ta ci gaba da magana
a nutse.
"A cikin tsiburin Marzau ya zamto tsiburi da aka
ginashi a bisa alkaluma na tsafi, amman babu wani abin
cutarwa a cikinsa domin matukar yarda da boka
Hamaran ya yi da kanshi, yasan cewar duk duniya babu
mahalukin da zai shiga har can ya cI shi da yaki domin
yasan cewar karfin
tsafi da tsananin jarumta duk duniya babu sama da shi
domin sadaukan jaruman aljanu guda goma ne a jikinshi
wanda suka gama karfinsu a wuri guda a jikinshi hakan
yasa ya zamto gwarzon jarumi mai matukar
sadaukantaka da duk wanda suka yi gamuwar farko da
shi yake rinjayarsa hakan yasa baya shayin kowane
sadauki a duniyar nan, a fanin tsafi ya zamto uba wurin
matsafa domin shi ne ya kirkiro adadin tsafi guda dari
da casa'in da uku ya sanar da bokayen duniya guda

58

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

casa'in da tara ya ki sanar da guda darin wanda hakan
yasa ake shayinsa mutum da aljan." Ta gama maganar
tata tana duban Jalaludin. Su duka suka yi shiru kowa
yana duban dan uwansa daga bisani Jalaludin ya nisa
gami da fadin. "Duk duniya babu wani abu da zai
dakatar da ni da zuwa tsiburin Marzau don kubutar da
mahaifina da kuma gimbiya Husamatu."
Sarauniya Samnatu ta girgiza kanta, ta yi tattausan
murmushi gareshi, da karfin zuciya ta ce masa."Tabbas
kayi dace da ka zamto jarumi mai zuciya tamkar
mahaifinka Kafilu don haka zan zamto tare da kai ina
mai nuna maka hanya har zuwa can"Muhusiya ta dubi
dan uwanta kana ta ce masa.
"Nima ina tare da kai dan uwana duk ruwa duk iska
babu wata wahala da zata rabamu da kai sai
mutuwa."Lamsu shima ya motsa ya dubesu.Ya zamar
mani dole nima na zamto daga cikinku ko don alherin da
yake ciki tafiyar."Da kwarin gwiwa ya ce masu."Bari na
shiga gida na shirya na fito domin tafiyar."Tana gama
maganar tata ta juya ta koma cikin gidan su kuma suka
tsaya suna sauraron fitowarta.Bayan shudewar mintina
tamanin ta fito cikin wata shiga ta yaki da ta zamto ta
boye suffarta, tana sanye da wasu jajayen kayan yaki da
wasu takubbai a jikinta wanan shigar ita ce shigar da
mahaifinta yake yi a duk lokacin da zai fito yaki.
Taja ta tsaya jama'ar fadarta suka mike suna dubanta,ta
taka ta matso gabansu ta nada wazirinta a matsayin
wakilinta kana aka gabato mata da wani ingarman doki
tayi tsalle ta haye shi suka yi wa jama'ar kasar sallama

59

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

suka juya suka dauki hanyar zuwa tsiburin Marzak,
domin riskar boka Hamaran.
Haka su ka dauki tsawon kwanaki suna tafiya a cikin
surkukin daji ba tare da sun gamu da wata halitta mai
cutarwa a garesu ba, duk wurin da suka wuce sai dai kaga
kura ta bi bayansu don tsananin gudun da sukeyi tamkar
wasu taron yuyar rundunar mayaka. Haka suka tafiyar da
wani lokaci mai tsawo na
kwanaki suna tafīyar tasu cikin matukar azama da burin su
isa zuwa tsiburin Marzak, a safīyar yau bayan sun sauka a
daren jiya sun huta don haka da safiyar yau suka daura
Sirdinan dawakansu suka hau domin su ci gaba da tafīyarsu
basu yi nisa da soma tafiya ba suka hango wata kura ta nufo
wurin da suke, hakan ya sa su suka dakata suka ja linzain
dawakansu suna sauraron ganin abinda zai tunkarosu.Bayan
wucewar 'yan lokuta sannan suka gano wasu Zaratan jarumai
su kimanin dubu kowane makaminshi a tsirara sun rufarwa
wani keken doki sai saranshi suke yi ta Ko ina, duk jikin
keken dokin sun hudashi da sara, hakama dokin da yake jan
keken dokin sun sassareshi jini yana fita ta jikinshi amman
domin kariin Juriya da jajircewa dokin yaki dakatawa.Su
Jalaludin suka tsaya suna sauraran ganin abinda
yake faruwa, a haka dakarun suka karaso garesu, wani
barde ya zaburo yasa wani mashi mai kaifi da tsini da guba a
jikinshi ya soke dokin da shi, dokin ya yi wata haniniya ya
fadi a Rasa wata yalwatacciyar kura ta tashi a wurin, keken
dokin ya hantsila yayo wajen su Jalaludin, wata
yalwatacciyar kara ta fito daga cikinsu, kana da wata murya
irin ta neman taimako aka ce.

60

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

"Ya Allah! SubahanalLah." Muryar ta fita fada tana kuma
nanatawa, har abin ya gama daidai ta a kasa, su Jalaludin
suka ci gaba da duban
abin da ga bisani ya kada linzamin dokinshi ya nufi
wurin,yana zuwa bai yi wata wata ba ya saka hannunsa ya
bareshi,wani farin kyalle ya baiyana, a lokacin wani
gawurtaccen sara na bazata ya nufoshi cikin tsananin azama
ya yi kokarin gocewa amman ya makara domin sai da saran
ya sameshi a hannu, ya dubi wurin ciki matukar mamaki,
kana ya kai dubanshi ga wurin, suka yi musayar kallo ga
juna. Duk da zamtowar ta rufe fuskarta da farin kyalle mai
raga raga hakan bai hana kyakkyawar fuskarta fitowa fili
ba,tsantsar kyawunta ya baiyana, domin tun da Jalaludin
yake jin labarin kyau a duniya bai taba jin labarin
kyakkyawa kamar wannan ba.
Suka ci gaba da kallon juna daga bisani ya nisa gami da
fadin.
"Masha Allah."
Maganar da ya yi ta sata ta saki takobin da take hannunta,
ta dubeshi.
"Waye kai?"Da murya mai taushi ta ce da shi. Ya kauda
kanshi gefe daya, a lokacin dakarun da suka biyo ta suka
karaso suka ja daga, ya juya ya fuskance su, suma suka
fuskance shi, ya juya ya dubeta yaga yanda ta tsaya tana
dubansu ba tare da tsorata da labarin su ba.
Shugabansu ya zaburo ya fito fili ya dubesu da duban
Raskanci kana ya ce masu.
'Ki karaso garemu kina wulakantatta mu kasheki domin
babu abinda zai hanamu kasheki da duk wani ma'abocin
musulunci irin ki."Maganarshi tayi matukar konawa su
Jalaludin rai tamkar yanda garwarshin wuta yake kona kaya.

61

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Ta zaburo ta fito ta saka hannunta ta yaye kyallen da yake
fuskarta kyakkyawar surarta ta baiyana, kana da
muryar jarumta ta ce masu.
"Bana shayin mutuwa don Allah shi ne mai kashewa don
haka ku yi sani cewa da izinin ubangijin musulunci zan
yakeku yanzun nan har nayi shahada."Maganarta ta baiwa
dakarun dariya suka yi ta son ransu kana shugabansu ya
turbune fuska gami da fadin.
"Baku da wani tasiri garemu duk a inda kuke ma'abota
musulunci.Muhusiya ta zaburo ta fito taja daga ta
fuskanceshi da fushi ta ce masa."Kai gafalalle wanda ya
zamto batacce, tabbas addinin musulunci ya sha gabanka
ahir dinka ka ciwa addinin Allah fuska karya kake."
Maganar ta matukar konawa shugaban dakarun rai da
matukar fushi ya ce masu.
"Tabbas kin jawowa kanku da kukayi shisshigin saka
kanku cikin abinda bai shafeku ba tabbas mutuwa ta tabbata
a kanku." Yana gama maganar tashi Lamsu ya zaburo gami
da fadin. "Karya kake Raskantacce." Shugaban dakaru ya
dabesu a fusace cikin tsawa ya ce masu.
"Ku saro mani kawunansu." Yana rufe bakinshi, dakaru
suka taso masu a matukar
fusacc suka yanyamesu, kasuwar yaki ta soma ci kara
gamuwar makamai ta cika wurin, ihu da hargowar sadaukai
ta karade ko ina, kawuna suka soma yawo a sama kamar
tsintsaye, mutuwa ta yi ta farauce rayuka, jini ya yi ta
zubowa tamkar gabar teku, makamai suka yi ta zamewa daga
hannun masu su.
Jalaludin ya zamto tamkar annoba garesu duk wurin da ya
saka gaba sai dai kaga matattu suna zubowa tamkar wuta a
cikin gonar auduga, haka ya dinga farautar rayukansu yana

62

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

sadasu ga ajalinsu, hakama sauran 'yan uwansa.Basu tafiyar
da wani lokaci mai tsayi ba suka gama da gaba daya dakarun,
duk wurin daka duba gawarwakinsu ne a kwance, suka
dakata suka fuskanci junansu kowane a
cikinsu yana jinjina jarumtakarsa, babu motsin komi a
wurin sai na ajiyar zuciya da suke yi, Jalaludin ya motsa a
hankali motsin nashi ya zamto motsi na farko da akayi a
wurin ya matsa zuwa ga bakuwar budurwar ya dubeta da
duban nutsuwa duk da zamtowar yakin da tayi ta sauya kama
domin yanda jini ya bata mata jiki ha>an bai hana kyawunta
ya zauna ba, Jalaludin ya girgiza kanshi cikin gamsuwa da
dumbin baiwar kyau da Allah ya yi mata da tausasa murya
ya ce mata.
"Tsarki ya tabbata ga Allah da ya halicci kyakkyawar sura
mai girgiza zuciya." Maganar da ya yi ta sa ta ta dago daradaran fararen
idanuwanta ta kalleshi, ta masa wani marayan murmushi
mai kurmanta zuciya, kana cikin tausasa murya ta ce masa.
"Godiya garcka ya gwarzon namiji abin burgewwa
zuciyata." Ya dubeta da dumbin mamaki, mamaki mafi
girma a cikin duk wani mamaki da ya taba yinshi a
rayuwarsa, kana
ya ce mata.
"Ta yaya na zamto abin burgewa garcki bayan ban zamto
daga cikin jarumai ba." Maganarshi tasa ta kuma yi masa
wani yalwataccen murmushi kana ta ce masa.
"Ba domin ina cikin tashin hankali da kunci na rayuwa ba
da nake tunanin mutuwa zanyi da nace maka duk duniya
babu wanda zuciyata ta taba gani ta ji tana kaunarsa sai kai,
domin ina jin zugin sonka a raina, kamar yanda na tabbatar
da cewar kaima kana jin abinda nake ji a ciki zuciyarka."

63

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Maganarta ta ratsa masa rai ya zuba mata idanuwa yana
kallonta, suka dan jima a haka kana ya kuma nisawa ya ce
mata.
"Tun da nake a rayuwa kece mace ta farko da naji kaunarta
ta shigar mani rai a, karo na farko, bayanke sai wata wacce
muka yi alkawari da ita na aure."Ya dakatar da maganarshi
ya daga kanshi ya dubeta, kana ya ci gaba damaganar tashi
cikin sanyaya murya.
"Wane kunci ne na rayuwa da yasa kike tunanin mutuwa za
ki yi wanda zai zamto tsani na rabamı alhali bamu
dandanawa juna zumar so ba?"Tambayarshi ta sa ta dago ta
dubeshi, ta motsa ta sami wuri ta zauna, wasu hawaye masu
zafi suka soma zubo mata, cikin muryar tausayi ta soma
gaya masa abinda yake ranta.
Jalaludin, Lamsu, Muhusiya, sarauniya Samnatu, suka yi
shiru suna sauraronta. Ta soma da cewar. "Mashahuran
malamai ma'abota addinin musulunci sune suka yiwa kasar
tamu kawanya suka zagayeta, muna da arzikin noma da
albarka cikin harkokinmu, zukatan jama'ar Rasarmu ya
zamto abin koyı da sahabbai don duk wani abu mai kyau da
suka ji sahabbai suna yi suma suna zamtowa masu
kwatantashi a cikin rayuwarsu hakan yasa zaman amana ya
tabbata a kasarmu Mahaifina shi ne sarkin da yake mulki a
kasar, yana gudanar da mulki bisa tsari na addinin musulunci,
yana hukunci da littafin Allah.
Haka rayuwar mutanen kasarmu ta kasance, har zuwa
lokacin da na zamto budurwa, mai kyawun wuce sa'a,
kyawun da ya zamtowa kasarmu matsala mai girina. Domin
tun lokacin da labarin kyawuna ya watsu a
duniya, manyan sarakuna, da ya'yansu uka soma tururuwar
zuwa ganina da kuma bukatar aurena.

64

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Amman zamtowarsu ba musulmai ba mahaifina ya hana
kowane daya da ya zo gareni, domin yakan kafa masu
sharadi da cewar ba zai basu aurena sai wanda na zaba na
fito da shi, shi ba zai zabamani mijin aure ba. Haka muka yi
ta gamuwa da matsin lamba daga wurin sarakuna da
'ya'yansu da kuma wasu daga cikin manyan sadaukai na
duniya, wanda hakan yasa hankalin mahaifina ye yi matukar
tashi domin ya rasa samur sukuni a
rayuwarshi don ganin yanda manyan 'ya'yan sarakai suke
Zarya akaina.
Ba wai wani abu ne ya dagawa mahaifina hankali ba abu
biyu ne na farko baya son yaki don kar rayukan jama'arshi
ya salwanta, na biyu ba zai bayar da aurena ga mushuriki ba,
wanda ya tabbatar idan ya hana auren nawa
dole za a yi yakin domin a kwaceni ta karfin tsiya hakan
shi ne ya tayarwa da mahaifina hankali ya zamto ko wane
lokaci vana cikin tunani, wanda tunanin abubuwan ya zamto
ya haddasa masa rashin lafiya mai tsanani Faruwar hakan ya
matukar tayar mani da hankali musamman zamtowar ni
kadai ce 'ya garcshi yana matukar nuna mani tsananin so a
fili, don haka na kidime na rasa ina zan saka kaina, bana fita
ko ina a ko wane lokaci ina zaune wurin mahaifina ina kula
da shi, shi kuma yaki ya gaya mani dalilin cutarshi sai dai
duk wayewar gari yakan ce da ni.
"Hajir ina kira garcki da ki zamto mai ruko da
addininki da neman taimakon Allah a lokacin da kika shiga
cikin tsanani, ki zamto kin zabi miji na gari nagartacce mai
ruko da addinin Allah." Wannan ita ce nasiyar da yake yi
mani duk wayewar gari har muka sami tsawon kwanaki
goma sha shida yana kwance kullum sai ya gaya mani.

65

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

A rana ta sha shida ne na fita fada domin riskar dumbin
masoyana da suke jiran jin matsayinsu. Ina shiga fadar na
isketa ta cika makil ta batse ga dumbin masoyana nan birjik,
suna ganin surata suka dimauce suka zauce, na sami wuri na
zauna suka zubo mani idanuwa su kuma suna kallona tamkar
kura data ga dan akuya a dokar daji.
Muka dauki tsawon lokaci a haka daga bisani na mike na
tsaya a gabansu kana na soma magana garesu a tausashe.
"Ku yi san' yaku taron masoyana na yanke hasashen
sadakina shi ne dole duk wanda yake son aurena sai ya
zamto daga addinina na musulunci, ya kuma mayar da
jama'ar birninsu duka musulmai wannan shi ne kadai
sadakina."
ina rufe bakina fadar ta hautsine da surutu, hankalin duk
wani masoyana da yake wurin ya tashi.Ban jira wani abuba
na juya nayi shigewata cikin gida fada ta tashi, masoyana
kowa ya kama hanyar zuwa kasarsu. Kasar Lamsan ta zamto
a karkashin mulkin sarki Zalman wanda danshi Sham'u ya
zamto cikin masoyana suna da matukar karfin runduna ta
zaratan mayaka abin tsoro ga kowace kasa.Sham'u ya zamto
da guda daya da sarki Zalman ya haifa, ya dora mashi son
duniya don ganin shi ne dan shi daya da yake da shi, don
haka a lokacin da yajewa da mahaifinsa abin da nace shi ne
sadakina sai ran mahaifinsa ya yi matukar baci, zuciyarshi
tayi baki ya fusata da fusata mai girma, ya dubi danshi da
duban dabuwa kana ya ce
masa.
"Ka kwantar da hankalinka ya dana abin soyuwa a raina,
tabbas ko tana so ko bata so sai ta aureka ko da kuwa rayuka
zasu salwanta."

66

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

Maganar da mahaifinshi ya yi itace ta sanyaya masa rai,
suka rabu da mahaifinshi a haka, ya shiga gidan shi tunanina
ya dami zuciyarshi da tunanina ya yi ta fama har ciwon
zuciya ya kama shi, abin ya tayar da hankalin mahaifinshi
don ganin halin da danshi ya shiga, hakan yasa ya aikowa da
mahaifina takarda yana mai cewa ya zamarwa mahaifina
dole ya aurawa danshi ni idan ba haka ba zai
kwace ni da karfin tsiya.
Mahaifina bai yi kasa a gwiwa ba ya mayar da martani da
cewar ba zai aura da 'yarshi ga kafuri ha idan suna son
aurenta sai dai su zamto sun bayar da sadakinta da kalmar
shahada.Wannan sakon ya yiwa sarki Zalman daci ya
matukar fusata da fushi mai daci.
Sham'u ya ce wa mahaifinshi ya aminta shi zai amshi
addinin musulunci domin ya aureni, zai cika duk wata ka
ka'ida da nace sai ya cika, wannan maganar da ya yi ta
matukar konawa sarki Zalman rai da yasa baisan lokacin da
zuciya la debeshi ya gaurawa mara lafiyar dan nashi mari ba,
marin yasa numfashin dan nashi daukewa, a fusace ya ce
mashi.
"Tabbas rudanin soyayya ya debi zuciyarka ya watsata
cikin rudani na halaka, don haka ina mai kira gareka da kar
ka kuskura ka gujewa abin bautarmu da muka gada kaka da
kakanni."Yana gama maganar ya fuce daga cikin dakin fuu!
Tamkar kububuwa.
Bai fi minti talatin da fita ba labari ya riskeshi cewar
Sham'u ya hadiyi zuciya ya mutu, wannan shi ne
mummunan labarin da ya taba riskar sarki Zalman. Bayan
komi ya daidaita ya yo hawa da rundunar dubunan zaratan
sadaukan shi suka nufo kasarmu domin yakar mahaifina, tun
kafin Karasowarsu labarin yawansu da dalilin tahowarsu ya

67

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

riski mahaifina. Amman an sami matsala domin labarin
zuwansu ya riski mahaifina a kurarren lokaci ne don haka
kafin ya yi yunkurin wani abu labari ya kuma riskar sa cewar
an balle
kofar gari mutanen kasar Lansam sun shigo, ba tare da
saurarawa ba suka soma sara mutane baji babu gani, gari ya
hautsine, fada ta watse kowa ya nufi gida domin kare kanshi
da iyalinsa. Mahaifina ya shiga cikin gida a matukar rude
ya nufi shashena y"na zuwa ya shiga da kanshi ya iskeni a
tsaye ina shirin yaki ya dubeni da matukar mamaki kana ya
ce da ni.
"Yake'yata guda daya wacce tafi komi soyuwa a raina ki
sani cewar yanzun nan ya zamar maki dole ki yi hawa ki ta
daga kasar nan domin zuwa kasar aminina don tsira da ranki
daga wulakanci na rayuwa, don tabbas matukar ina numtashi
a duniya ba zan taba aurar da 'yata ga wanda ba musulmi
ba." Da tausasa murya ya ce mani.Na juyo na dubeshi da
fuskar tausayi hawayen jimami ya kwaranyo mani a hankali
na ce masa."Ya kamata ace tare zamu yi tafiyar nan domin
bamu san irin Barnar da makiya suka yi mana ba."Mahaifina
ya dago da kanshi ya dubi kana ya ce da ni.
"Ba zai yiyu na yi hijira ba alhali talakawana suna cikin
yaki, tabbas ba zai yiwu na tafi na barsu ba zan kasance tare
da su har zuwa karshen hukuncirn da Allah zai mana domin
taimakon Allah zai zo garemu."Yana gama maganar tashi ya
juya ya fice daga daki nawa, ya nufi sashenshi na zube a
wurin na soma kuka na tsananin takaici da nadamar
zamtowata kyakkyawa domin kyawuna ya janyowa jama'ar
kasa yaki yana shirin halakar
da mahaifina.Kukan tsanani da damuwa da takaici ya ci
gaba da mamayar zuciyata, har zuwa lokacin da naji wasu

68

DIMAUTA

MUKHTAR KWALISA

hannuwa sun dafani na dago da idanuwana muka yi musayar
kallo da shi ba kowa bane sai dan wazirin mahaifina wato
yarima Hamsu. Yana matukar nuna kulawarshi a gareni,
yana nuna
damuwarshi a kaina idan yaga ina cikin damuwa.A hankali
ya ce da ni. "Sarki ya ce na zamto maki dan rakiya har zuwa
kasar amininsa."
Na dago idanuwana da suka pi ja domin kukan da nayi na
dubeshi, kana na ce mashi.
"Ina mahaifin nawa'?" Ya dago idanunshi ya dubeni."Ya yi
shirin yaki ya tunkari abokan gaba."Da kwantar da murya ya
cemani.
Wannan maganar ta zamto ita ce magana mafi girman
lamari da na taba jinta, hankalina ya matukar tashi, ya matso
gareni ya kamoni ya dagoni kana ya ce mani.
"Ba lokacin zama bane domin sun kusanto mu sosal. " Ya
ce mani kana ya jaw0 ni muka yo

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment