Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin an turo kofan an shigo, duk da ba'a yi magana ba amma masifaffan kamshin designer turaren daya ziyarci kofofin hancin tane ya tabbatar mata da namijine ya kabeta, cikin matsanancin kuka take fadin."meyasa na rayu meyasa ka kawoni asibiti daka barni na mutu, rayuwata batada wani amfani mutuwa nakeso nayi inaso natafi inda mahaifiyata take me kaunata ita kadai ke sona duk duniyan nan....banasan duniyan nan......." ta fashe da kuka duk da idanta a runtse suke hakan be hana hawaye zubowa ba, da sauri ya fice daga dakin bude ido tayi taga ya fice dukar da kai tayi da aka nade mata shi da bandage taci gaba da kuka, likitace ta shigo ido ta bita dashi har ta gama hada injection din sannan tamatso se tinta cikin kuka ta fara ja da baya."banasan allura please kada kimin......." dr. teemah tayi murmushi ganin yanda ta rude."to bazan mikiba." A cikin drip din ta juye alluran sannan ta dubi rumana."ki dena kuka mara lafiya ba'aso tana kuka it can affect u..." rumana ta share hawaye."to.......to.....na daina." doctor tayi murmushi ta fice, ko minti biyar ba'ayiba bacci ya dauke rumana saboda alluran harda na bacci a ciki. Yana zaune a office files ne dayawa a gabanshi wanda zesa hannu amma yakasa taba ko guda daya, tunanin MK gaba daya yana kan rumana daya bige yau kwana uku, tausayin yarinyar fal zuciyanshi sema maganganun da tayi dazu a gabanshi hakan ya nuna tana cikin kuncin rayuwa, domin yayanshi ya fada mishi komai a yanzu yayanshi na matukar bukatar rumana amma baze fada mishi tana gunshiba harse ta samu sauki ya maidata gun mijinta, ganin baya gane konai yasa ya daga waya, cikin cool voice dinshi yace."rayyan kafadawa D. one da namej bazasu samu signing contract dinnan a yauba coz abubuwa da sukayi min yawa sedai su jira nan da 2days." "okey." kawai ya kara ya katse wayan, tareda tashi ya zari key din mota ya fice nan bodyguards sukayi kanshi. Doctor na ganinshi tace."Maheer taji sauki yanzu bacci takeyi amma taki daina kuka har yanzu." kai tsaye dakin da take ya nufa still har lokacin bacci takeyi tsayawa yayi yana kallon beauty face dinta, tsintar kanshi yayi da yin murmushi har beauty point dinshi ya lotsa, ya jima yana kallonta kafin ya fice gurin doctor ya koma yace."doctor na baki amanarta ki kulamin da ita." tace."bakada matsala yallabai." nan ya fice. Koda ta farka taga an cika dakin da kayan ciye ciye da abinci kala da kala nan doctor tazo ta lallabata da kyar taji abincin kadan. Yau satin ummu rumana biyu a asibitin ta warke sosai tasamu sauki, har yau batasan wanda ya kawota asibitinba domin tun ranan MK be sake zuwaba doctor ce ke kula da ita, ita kuma a bangaren rumana ta matsu tasan wanda ya ceci rayuwarta yake kula da ita sosai dan a sati biyun da tayi a asibitin ta ciko ta danyi kiba domin tanacin abinci kuma hankalinta a kwance kullum se tayi wanka fiyeda biyu a rana, doctor na kokari wajen ganin ta hanata damuwa da yawan tunani, koda ta tambayi doctor "waye ya kawoni".? doctor tayi murmushi."zaki ganshi ze zo." domin beba doctor teemah daman bayyana shiba. Suna zaune a gurin meeting a table din meeting da ma'aikatan shi kwararrun mawaka na gida nigeria, larabawa da turawa dan yan kasar wajema sunfi yawa a companyn da larabawa yan uwanshi, dama sabbin mawaka shine head of the meeting yana zaune a tsakiya suna tattaunawa duk cikin harshen turanci suke maganan, wayan shine tahau ruri yayi duba da soccer din wayan doctor ce, hakan yasa yayi picking ya kara a kunni kowa a gurin shiru yayi yana kallonshi, dan be taba daga waya a gurin meeting ba aka sarima shike fada akan adena dan yana cikin roles and regulations na kamfanin, Global records, bayan sun gaisa doctor tace."sir rumana ta samu sauki sosai dan tuntuni muka sallameta kuma se tambayan ka takeyi." jim yayi kafin yace."okey yanzu ina meeting ne give me 30 mints I will be soon there insha Allah." yana fadin haka ya katse tareda duban mutanen duk kunya ta kamashi ya karya doka yace."am sorry." suma sun mai unzuri dan daga gani wayan me mahimmanci ne tunda ya daga, nan sukaci gaba da tattaunawa. ************** Zaune take ta zuba uban tagumi tunani take kala da kala abinda yafi tsaya mata bai shige yanda Alhaji ya yanke hukunci ba tareda bincike ba, tana wannan tunanin taga an turo kofan kai ta dago tana kallon me shigowa da kamshin shine ya isa ya tabbatar mata shina daban ne, ....A razane ta mike tana zaro ido idanta nakan beauty face dinshi tayi baya da sauri tana neman gurin boyewa da sauri, ganin ta rude yasa ya karisa gareta da sauri kokarin shigewa cikin blanket ta buya take hakan yasa ya rikota da sauri, cikin kuka tana kokarin kwatar kanta ta soma fadin."please kayi hakuri kada ka maidani kamani zesa ayi kuma wallahi banyi komaiba nasan ya turo kane danka maidani please ka rabu dani....." duk ta rude rike kafadunta yayi da karfi sosai yace."ki natsu tsaya ki saurareni...." Ina bata jiba se kuka dataci gaba tana fadin."katemaka min kada ka maidani." ganin taki nutsuwa yasa cikin tsawa yace."kimin shiru...." tsit tayi se jikinta daya hau rawa ta sankare domin ta tsorata da tsawanshi, ganin yanda ta firgice hakan yasa ya dada tausaya mata ya sake rukota a sanyaye yace."zo muje..." hannunta ya riko da kyar ta iya tashi suka fice, seda suka biya sukawa doctor sallama ita dai har lokacin kuka takeyi doctor ta dubeta."rumana yau rigima ta kare ga MK nan." shiru tayi idanta naci gaba da zubda kwalla doctor tayi dariya."au kukan farin cikine na ganin maheer."? da sauri ya dada yima doctor teemah godiya sannan ya bata kudi masu yawa daganan yaja hannun rumana sukayi waje...... Manage this! kunsan sallah ta kusa yaune jajubari aiki ne yamin yawa kuyi hakuri. Happy arfat day, ina jiran ragon layyana, Allahsa ayi sallah lpy, Ameen. Babyn Amjad ce....✍️ 8/20/21, 8:21 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* Happy sallah to u oll. Eid Mubarak in advance Allah maimaita mana. ya karbi ibadunmu ya yafe mana zubanmu. Amin ya Allah. Appy eid kabeer to you oll fans, I love you plenty plenty Inasanku da yawa, Nagode sosai fans da rakumin layyan da kuka hada kudi kuka siyamin Allah saka da alkhairy πŸ˜…. Kun siyawa *Ramlat* dan kamfai πŸ€” Tnx Allah saka. Wannan page din Appy sallah ne ga masoyan *Mimi* masoyan litattafanta nagode sosai dears really appreciate πŸ₯°. 33&34 Ganin ya sanyata a mota ya shiga ya kulle motan yasata cikin kuka tanaso ta bude motan take fadin."dan Allah katemakamin kabarni na mutu dan Allah kada ka maidani gidan nan, wallahi niba mazinaciya bace......" cikin fada yace."bazaki yimin shiruba wai waya fada miki wanine ya sana daukoki nina bigeki kuma babu wanda na fadawa, amma in kina sone sena kira yaya in fada mishi....." da sauri a razane tace."A'a..a'a dan Allah kada ka fada mishi.." shiru yayi yana kallonta a hankali ya fara tuki, sunyi tafiya sosai kafin sautin kukanta ya cika motan cikin kuka take fadin."Mutuwa ya kamata nayi meyasa ka ceceni? daka barni na mutu..." taci gaba da kuka, ko kallonta beyiba wayan shine ta dau ringing me dadi ko ba'a fadaba yasan ko wanene, bloodline din shine dubanta yayi tareda yin murmushi."yawwa gama yinan yana kira..." da sauri ta dago tana bashi hakuri yayi picking idanshi na kanta itama shi take kallo burinta kada ya fadawa yayanshi suna tare."Hello yaya." ya fadi tareda yin murmushi har beauty points dinshi ya bayyana,."haba yaya Insha Allah za'a ganta kadena sawa kanka damuwa." lokaci guda yaji tausayin yayanshi ya kamashi se yaji kaman ya fada mishi hakan yasa yace."Yaya ai muna tar.........................." bai karisaba rumana ta fada jikinshi tareda sa hannu ta rufe mishi baki tana girgiza kanta hawaye na zuba daga Idanunta zuwa dakalin fuskarta, Janye hannun nata yayi daga bakinshi yace."am sorry yaya ina driving ne zamuyi waya later." ya katse tareda dubanta."ke kinada hankali kuwa."? sauka tayi daga jikin nashi tana fadin."please katemakamin kada ka fada mishi dan wallahi sawa zeyi akamani a tafi dani prison." murmushi yayi, A haka suka karisa maitama a dankareren gidanshi mai kama dana tsohon gwanan Ph ROTIMI AMECHI yayi horn, da sauri me gadi ya bude mishi wagegen gate din ya shiga yayi parking a haraban gidan inda motocine birjik manya manya masu bala'in tsada a pake irinsu range rover, toyota sterlet, ferrary, toyota hiace, 202, tapanese box van, costom van kazu kiauto, ga dai sunan dai kala da kala dan kaf daga kasar waje aka kawo mishi su dan MK baya hawa karamar mota, yanayin parking ya fito ya bude kofan inda take yace."Fito." ba musu ta fito tabi bayanshi har cikin dankareren gidan bayan ya amsa gaisuwan me gadi. Sama ya haye hakan yasa tabi bayanshi ganin yana kokarin shiga wani part yasata yiwa kanta mazauni a daya daga cikin danka dankaran kujerun dake sitting room irin masu amfani da AC dinnan wanda inbata suke saurin lalacewa, ya jima a ciki kafin ya fito ya dubeta."Zo muje muci abinci." ta yamutsa fuska."na koshi." domin ita yanzuma tsoro ya fara bata, dan gidan yayi kama dana masu shan jini amma data tuna matsayinshi da kuma daukaka irin nashi cetace, wannan ai bakomai bane, ya marairaice. "To muje ki rakani.." ba musu ta tashi suka jera zuwa hadaddan dinning room din da yake hade da kitchen, Inda cucu meyi mishi abinci ya riga ya gama komai, zama yayi tareda dubanta."Zuba min mana." tashi tayi ta janyo warmers din ta dauko dishes da saving spoon ta bude, ita kanta kamshin abincin ya mata amma ta daure haka ta zuba mishi ta ajiye a gabanshi, bismillah yayi yasa spoon yafara ci yana lullumshe ido yana fadin."uhmmmm abincin da dadi, ko zakiyi test ne."? ta dubeshi tareda hadiye miyau ya mika mata spoon."amsa kici kada ayi baki." ta turo baki."bari nayi testing kawai amma bawai dan inajin yunwa ba." ta amsa spoon ta fara ci, shiko murmushi yayi domin dama haka yakeso seda taci sosai sannan tasha madara shiko ido ya bita dashi yana kallon natural beauty. Bayan tasha madara ta dubeshi."Nayi testing amma ni banajin yunwa....." murmushi yayi ya tashi."Zo muje muyi magana." Kan cushion ya zauna ta taso tazo ta zauna kan carpet, ya kirata dago da kai tayi."Na'am..." yace."rumana inaso ki bani labarinki dan daga gani kin fuskanci jarabawa da yawa a rayuwarki." tuni hawaye suka fara rolling kan face dinta, ganin hakan yasa ya tashi da sauri ya isa gabanta ya zube gwiwowinshi a gabanta tareda riko fararen hannayenta a marairaice yace."Rumana trust me am ur friend share ur life with me...." tasa bayan hannu ta goge hawayenta."hummm *LABARINA* kakeso in baka to kada ka damu ka bude kunnuwanka da kyau dan sauraron LABARINA." ta nisa"uheemmm." kana ta fara bashi labarinta tun tasowarta cikin kunci, har I yau seda ta fada mishi. Shiru yayi yana tunanin rayuwar yarinyar tabbas rumana abun a tausaya wane tayi hakuri da juriya a rayuwarta, wanda ko shi da yake namiji baze iyaba, da kyar ya iya dago kanshi ya dubeta yanda taketa rusan kuka bejin ze iya hanata kuka domin yana ganin hakan ne kawai zatayi ta samu saukin abunda takeji, A sanyaye yace."hakika naji labarinki kuma na tausaya ma LABARIN ki ainun, kuma kin burgeni matuka da baki aikata aikin dana saniba kikaci gaba da hakuri a yanda rayuwa tazo miki, domin mafiya yawan mutane idan rayuwa tayi musu zafi sesu kashe kansu kosu shiga sabawa ubangiji ta hanyar zinace zinace ko shaye shaye, gaskiya rumana kin burgeni kuma naji dadi da kika yarda dani kika bani labarinki, ni kuma na miki alkawari Insha Allah zan tayaki magance damuwarki, zan maidake gurin yayana inyaso seya maida auranki kuci gaba da rayuwa...." a razane ta dago tana girgiza kai, ya bita da ido."bakiso. "? ta daga kai cikin kuka take fadin."please kada ka maidani kuma banaso yasan inanan, inaso kabarni anan ko kuma kabarni na nemi inda zani." jim yayi duk tausayinta ya kamashi yace."okey naji kibani dan wani lokaci zan yanke hukunci, yanzu taso muje na nuna miki dakin da zaki kwana dare yayi." ba musu ta tashi ya nuna mata hadaddan dakin shi kuma ya wuce nashi...... Fatima 🎀 banga ragon layyaba. Eid kabeer once again πŸŽ‰. Babyn Amjad ce ✍️ 8/20/21, 8:21 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* Much love abokiyar yarinta, Aishat salis Allah sarki rabin rai taya zan manta dake ina kaunarki sirikata. 35&36 Cikin dare rumana na kwance jigum ta kasa bacci jikinta se rawa yakeyi haka nan ta tsinci kanta da jin tsoro, duba da wagegen gidan kuma ya kawota dankareren daki ita kadai, tashi tayi a hankali cikin sanda ta fito ta nufi part din dataga ya shiga dazu, sankarewa tayi a tsaye tana kallon yanda gurin yake ko a kasar waje albarka gaskiya gidan ya hadu ainun, tsoron tane ya kara tsananta duba da jerin kofofin glass din dake gurin ta rasa gane wanne zata shiga lokacinne taji kaman ana taba mata gashi dan haka batasan sanda ta ruga da gudu ba cikin firgici ta nufi daya daga cikin kofar glass din takoci sa'a a bude take dan haka ta shige da gudu, Yana zaune ga kayan music nan birjik a gabanshi ya makala abun music a kunni yanabin wata wakan arabi da yayi, yaga ta shigo da gudu tashi yayi da sauri tareda cire abun daga kunninshi ya isa gabanta ya rikota yana tambayanta."meke faruwa..."? kankameshi tayi sosai ta rungumeshi cikin firgici take fadin."tsoro nakeji bazan iya kwana ni kadaiba kada ka barni please..." ganin duk ta rude yasa ya rikota gefen makeken family bed dinshi ya zaunar da ita, ya karanta mata ayatul kursiyu ya tattofa mata nan da nan bacci ya dauketa kwanciya ya gyara mata ya rufeta da blanket ya koma yaci gaba da aikinshi, bayan ya gama ya kwanta kan three sitter idanshi na kanta. Kashe kari Tajima tana bacci koda ta farka lokacin ya dade da ficewa office yadai barwa kuku sallahu akan yabata abinci, koda tayi break setayi wanka cikin kayan da yaita siya mata da tana asibiti tasa wata doguwar rigar abaya brown, lokacin ne taga al'adanta yazo gashi ba pad hakan yasa ta kimtsa kanta ta fito da niyyar aiki, ta taras an gyara ko ina kaman aljanune sukayi aikin domin an gyara gidan tsaf ko ina da ina dan haka ta shiga kitchen inda kuku ke shirye shiryen fara girki. Kuku da becika jin hausaba se turanci ganin ta shigo yasa shi gaidata dan a zatanshi aure MK yayi, da kai ta amsa yayinda yaci gaba da aikinshi dubanta yayi cikin turanci."dame zan temaka miki madam."? itama cikin turancin ta mayar mishi."please inaso ka bari muyi girkin tare." ba musu ya bata hanya nan tashiga hada hadan girki cucu na temaka mata. Misalin uku MK ya dawo kuku ya tareshi da sauri tareda fada mishi abinci na dinning room, cikin sauri MK ko kallon kuku beyiba cikin turanci yace."a koshe nake banajin yunwa." kuku shima cikin turancin yace."oga daka daure kaci domin girkin madam ne..." be rufe bakiba maheer ya juyo da sauri jin yace rumana tayi yasashi saurin ajiye brief case ya nufi dinning room, tunkan ya karisa kamshin abincin ya cika mishi hanci dan haka da sassarfa ya karisa ya janyo plate ya bude hotter lokacin ne ya kusa sumewa jin kamshin abincin, faten doyane yaji kayan ciki da hanta se farfesun dawisu da jellof na shinkafa da yaji kifi, loman farko seda ya kusa faduwa saboda dadi tunda yake a duniya be tabacin abinci ko makamancin wannan ba, seda yaci sosai sannan yasha strew berry juice din data hada mishi wanda ko kuku da ba'a kasar yakeba baze iya ko makamancin wanda tayiba, domin shi duk masu aikin gidan daga kasar waje suke har gate man, Dai dai lokacin ta shigo dinning room din tana sakin mai wannan best smiles din nata ya shagala sosai gurin kallonta har besan sanda bakinshi ya furta."kinyi kyau."ba ta lumshe manya manyan idanunta brown golden ta budesu akanshi yace."waya koya miki irin wannan girkin haka."? tayi murmushi har cute one side dimple dinta ya lotsa tace."yayi dadi ne." ya daga kai tareda fadin."Eh mana, banaso ki kara girki domin bashi kikazo yiba." ta shagwabe fuska."yallabai...." da ido ya amsa yana kallonta ta sadda kai kasa alamun jin kunya yace."na'am inajinki..." cikin in ina tace."dama....uhmmm....inaso ka siyamin....uhmmm.....pad..." ta rufe fuska da sauri dan murmushi yayi."sorry kinsan ba mace a gidan shiyasa bana ajiyewa amma jeki shirya ki fito muje ki siya duk abunda kikeso..." Seda ya shirya ya fito sannan suka jera kaman wasu masoya a bakar Mercedes Benz (300 suka fita. A mota waka yasa mata wanda yayi tana saurara se faman dariya take shiko se faman kallonta yake yana kallon dimples dinta shima yana murmushin wanda besan daliliba, babban boutique sukaje seda yamata siyayya manyan kaya da kananu irinsu, abaya da dogayen riguna da sauransu daganan suka nufi shagon atampopi da leshika, swis swis, bowels dadai sauransu, yayi mata siyayya da yawa daganan suka biya suka bada dinkunan, duk inda sukaje kowa ya ganshi rudewa yake an dingi zagayeshi kenan itako tana gefe tana kallon yanda yake yiwa mutane fara'a duk matsayi irin nashi amma bayada girman kai, murmushi tayi tanajin wani iri akanshi, bayan sun fito shop rite suka nufa, nan ma sunyi siyayya a babban shopping mall din harda su pad da sauransu, anan dinma yan matane da samari kowa so yake yayi selfie da MK adon garin yan mata da samari, rumana ganin ya shareta yasa ta fita daga shopping mall din zuciyarta na mata zafi ta shiga mota, kuka ta fara tanajin wani iri a cikin zuciyart ko kadan bataso taga wata mace ta rabeshi batasan daliliba, shiko ganin ta fice yasa hankalinshi komawa kanta da sauri ya ba mutane hakuri ya fice, Yana shiga mota ya janyota jikinshi yana fadin."Sorry rumana mutanene suka rufeni kuma kinga be kamata na share suba..." ta share hawaye ta janye daga jikinshi tana fadin."shikenan..." Bayan ya hau titi ya dubeta."kin meye."? ta girgiza kai yace."In kina kuka kinfi kyau...." tayi murmushi a haka suka karisa gida. Unin ranan suna tare har dare dan da daddarenma tana dakinshi dan tsoro takeji ta kwana ita kadai dan haka tana kusa dashi, matsamai tayi seya koya mata waka dan haka ya makala mata abun sauraron music yanayi tanaji ahaka har tayi bacci... Manage this. Kunsan ana hidiman sallah. Taku me kaunarku. Serdeeyeer ✍️ 8/20/21, 8:21 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* Babyn umar inasanki sa'adatu Aminu umar (Ummi) kina raina, I want you to know dat you magalize in my heart. 37&38 Bayan wata uku. Shakuwa sosai ya shiga tsakanin MK da rumana, zuwa lokacin tayi iddarta ta gama yanzu sun shaku sosai, Ya jima beje kaduna ba se waya ake mishi dan haka wannan weekend din ya shirya tafiya, fadawa rumana yayi ta dingi kuka domin bataso ya tafi, lallashinta yayi sosai nan ya bata sabuwar waya IPhone 11 pro max yace."Inna tafi zamu dinga waya." Yau ya sauka a kd inda yan uwa kowa ya saukeshi yana murna ya tausayawa yayanshi ganin halin daya shiga duk an bincika ba labarin rumana an yayyada ako ina amma bata ba labarinta, se yaji kaman ya fada mishi sedai shima a yanzu yana bukatar rumana a rayuwar shi domin yanzu ya saba da ita a rayuwar shi. Tana kwance wayan da MK yabata ta dau ruri seda rumana tayi kara saboda tsoratan da tayi da sauri tayi picking cikin kuka take fadin."tsoro nakeji kadawo please......" cikin kwantar mata da hankali yace."yi shiru saurareni ina tare dake kinji..." ta daga kai kaman yana ganinta, yace."to share hawayen ganinan ki dena jin tsoron zan zauna dake harse kinyi bacci." cike da gamsuwa da magananshi ta share hawayenta tareda sakin ajiyar zuciya, Nan ya shiga bata labari dan kawai ya debe mata kewa, dariya tayi tace."yallabai...." da sauri yace."banace kidena cemin yallabai ba." tace."uhmmm..to mezan ce maka." yace."ki kirani da cuddle buddy..." fuska ta rufe cikeda jin kunya tace."to cuddle buddy kasan meye.."? yace."se kin fada.." tace."I miss u..." ta kareshe maganan tareda rufe fuska kaman yana ganinta. yace."Miss u too..." ta turo baki."bayan kana can tareda zeeza wacce zaka aura.." ta karashe tareda da shaahshekan kuka da sauri yace."Noo rumana yi shiru ki dena kuka, bahaka bane rumana ki dena kuka..." nan ya shiga lallashinta, seda hankalinta ya kwanta sannan ya shiga rera mata waka cikin zazzakar muryarshi tanajin dadi seda yaji alamun tayi bacci sannan ya kashe wayan ya kwanta. Da kyar ya daure yayi kwana uku a kaduna sannan yace ze koma domin yayi bala in kewan rumana, nan Alh yace."bayan kajima baka zoba yanzu kuma daga zuwa zaka tafi."? yace."ai yaya aikine sukamin yawa amma inna samu hutu zan dawo." zeeza ma rigima tasa wai baze tafiba da kyar ya lallabata ya koma abuja. A kullum wani yanayi yakeji in yana tareda rumana domin ita wata iriyar gifted ce da duk wanda yake tareda ita se yashiga wani yanayi daurewa kawai yakeyi domin she's available as well. ***************************** Suna zaune shida rayyan a office, rayyan ya lura kwana biyu wani abu na damun abokinshi yana yawan tunani, duban MK yayi da yayi shiru."big man wai meyake damunkane kwana biyu."? MK ya nisa."umhhhhmmm." kana yace."rayyan aure zanyi.." dariya rayyan yayi."me kakeci na baka na zuba, befi yan watanni auranku kaida zeeza ba." yayi tsaki."dalla bada zeeza ba watace nakeso na aura kuma a cikin satin nan nakeso a daura mana aure, batareda kowa ya saniba a gida." da sauri rayyan yace.saboda me MK."? Nan Maheer ya kwashe komai ya fada mishi, shiru rayyan yayi."amma baka ganin baka kyautawa yayaba inya gano zeji haushi." MK yace."sedai in kai ka fada mishi itama bataso kowa ya san muna tare." rayyan yace."to ya zakayi da zeeza."? yace."itama zan aureta amma a kd zan ajiyeta ni kuma inanan tareda da kaunata..." tashi yayi yana kokarin daukan key din mota, rayyan ya mike."bari nazo muje na ganta tunda rowanta akemin." MK yace."kuma kada ka kallan min ita sosai in ba hakaba zan kwakule maka ido." na suka fice rayyan na dariya. Suna shiga daidai lokacin ta fito sanye da jan batik Amima tayi kyau sosai, suman tsaye rayyan

Chapter 6 of 14