Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* My! nurul hayatee, nisful hayatee, kurta aayunin, ana uhibbuka hubban jadidan my ango inasanka kada kabarni kaine rayuwata inasanka inaso mu kare rayuwarmu tare har abada Insha Allah. 25&26 Rumanace cikin kitchen tana wanke wanke, zeeza ce ta shigo itada Aknan, Aknan ce ta rufe kofan kitchen din itadai ido ta bisu dashi zeeza ta karisa ta gaurawa rumana mari har sau uku."ba akanki bane mijina ya mareni to wallahi yau sena kassaraki." ta janyo gashin rumana kuka rumana takeyi, zeeza tadubi aknan."me zamu mata mu illatata."? Aknan tace."fuskarta zamu kona ba tanajin tanada kyauba, to kunna gas." kuka take sosai tana rokonsu ina basujiba, zeeza ce ta kunna gas wuta yanaci sosai suka matsar da rumana fuskarta suka kai setin wutan ihu tasa me karfi da sauri zeeza ta kifeta da mari cikin kuka tace."ku yi hakuri kada ku konamin fuskana." Cikin mugunta Aknan tace."to ki zaba ko mu kona miki fuska ko mu cire miki yatsa." kuka take sosai jin tayi shiru yasa bata ankaraba taga zeeza ta kamo hannunta ta tura cikin wutan, kuka takeyi sosai tana ihu hakan yasa diyam rugowa kitchen din tana bubbuga kofan, bata damu da maganan da mummy take mataba rokonsu take akan su rabu da rumana kada su cutar da ita amma ina ihu kawai take sosai seda sukaga ta kone sosai sannan suka saketa zeeza harda hada mata da mari, suna bude kofan diyam ta shiga da gudu gurin rumana ta nufa data fadi saboda azaba ta rungumota dukkansu kuka suke, can ta tashi ta tallafo rumana sukayi waje, dariya suke harda haj. cikin kuka diyam tace."yanzu meta muku zakuyi mata hukunci da wuta bayan Allah (SWT) shi kadai yake horo da wuta to dukkanku sena fadawa daddy...." taja rumana zasu fita hajiya tace."Ina kuma zakije da ita..."?."Mummy asibiti zamuje..." cikin fada haj. tace."wallahi diyam kika kuskura kika fita da yarinyar nan ko kika fadawa daddynku wani abu ban yafe miki ba dan haka ki ijiyeta ba ruwanki da ita..." diyam na kuka haka ta rabu da rumana tayi ciki da gudu tana kuka. Hajiya ta maida dubanta ga rumana da azaba ya isheta."kadan ma kika gani tunda kika auri mijina kuma kika kuskura koda wasa Alhaji yasan abunda ya faru to ukuban se yafi haka Mtsssww...." taja tsaki, rarrafawa tayi da kyar ta koma daki takasa zaune se safa da marwa take saboda azaba. Koda Alhaji ya dawo a cikin mawuyacin hali ya taddata dan a sume yasameta nan yamata dressing din hannun hankali tashe yamata allurori domin akwai zazzabi me zafi a jikinta yasa mata drip, fita yayi yanata fada akan halin da ya iske rumana, hakuri hajiya ta bashi tareda fadin."ba wanda yasan halin da take ciki domin ba wanda ta fadawa...." tsaki yayi yakoma gun rumana, Koda ta farka ya tambayeta, dame ta kone? " se tace."da mai ne ina soya dankali." tsaki yayi yace."ki dinga kula kinji." ta daga kai, fita yayi yaba hajiya umarni akan kada rumana tasake komai acikin gidan, ta amsa maine kawai, Amma bata canza zaniba domin yana fita zata fara duk da kunanta be warkeba, diyam naso tayi magana amma an toshe mata baki da Allah ya isa... A haka LABARIN Rumana me cikeda tausayi yaci gaba da tafiya a cikin wahala da bakar ukuba amma Alhaji na kokari gurin faranta mata, kuma har zuwa lokacin bata taba fada mishi komaiba dan haka be san komaiba. ###################################### Kwance take kan kirjinshi yana shafa yalayalan sumarta."Rumana ko kadan banasan nayi nisa dake inajin wani iri in Ina tare dake shiyasa tafiyan nan da zanyi jibi zuwa Egypt dake zan tafi daganan zamu biya Saudi Arabia kiga dangina kinga daganan ma nasa likitocin can su dubaki suga meke damunki..." Itadai shiru tayi domin tarasa meyake nufi da aduba meke damunta, wani dadi takeji a cikin zuciyarta domin tasan zatafi jin dadi insuna tare acan egypt din kuma zata huta da ukuban su zeeza nadan lokaci...... Se faman safa da marwa hajiya take abin duniya duk ya isheta, Aknan ne tace."Wai mummy meya farune ki keta kai komo..."? cikin tashin hankali tace."Aknan daddynku yadena sona yanzu wai tafiyan da zeyi Egypt gobe da wannan yarinyar ze tafi bada niba bayan tare muke zuwa duk kasar da ze tafi gaskiya yanzu baya sona." tasa kuka Aknan tace."gaskiya daddy be kyautaba mummy." zeeza da diyam ne suka shigo suna tambayan meke faruwa, Aknan ce ta fada musu komai hakuri diyam tafara ba mummy tana share mata hawaye, zeezace tace."gaskiya yanzu lokaci yayi da dole yarinyarnan tabar gidan nan wallahi mungajj Aunty dena kuka share hawayenki mu tsara yanda za'ayi. Hannu tasa ta share hawayen nan suka tsara plan, Diyam ce tace."gaskiya mummy be kamataba..." hajiya tace."diyam ki rufe mana baki ba muso ki bamu matsala indai kikayi magana sena tsine miki Albarka." haka diyam naji na gani suka tashi bayan sun tsara plan gashi ba dama ta tona a tone mata Albarka...... Murmushi dauke da fuskar haj. ta tari Alhaji duk da ran girkin ummu rumana ne seda yaje ya shirya sannan yafito dinner, idanshi nakan dakin rumana ya dubi hajiya."ya rumana bata fito gurin dinner ba....."? tace."walahi ban saniba kila batajin yunwane.." miyau diyam ta hadiye idanta na fidda kwalla na tausayin rumana, Alhaji yace."Lafiya diyam kike kuka..."? da sauri haj. tace."wai dan cikinta na mata ciwone shine take kuka." Alh. yace."kinsha magani kuwa autah...."? tashi tayi batare data bashi amsaba tayi ciki tana kuka, Shidai har suka gama dinner idanshi nakan dakin rumana, bayan sun gama ya tashi yace."bari na duba ko lafiya..." dakin ya nufa, Murda handle din kofan yayi ya bude... Meze gani????????? Wani katon mutumine tsarara yana ganin Alhaji ya shigo ya buge Alhajin yafice da gudu, kara haj. tasa."mun shiga uku mezan gani haka Aknan zo kuga kwarto a gidanku....." Shiko Alhaji kan gadon yabi da kallo da yake a yamutse ga kayan mutumin a gefe tareda kayan rumana harda pant da bra da alama an kashe arnaye a gadon......... Lol πŸ˜‚ Dai dai lokacin rumana ta fito daga bayi daure da towel iya cinya tana tsane sumarta da take diga da karamin towel....... Alhaji ya bita da wani irin kallo........... Manage this Comments dinku yafara kasa na kusa daina typing kuma idan bakwa comments zan maida book din na kudi duk da a free naso in muku amma kunaso ku canzamin ra'ayi saboda bakusan comments. Mimi queen ✍️ 8/20/21, 8:19 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* My dr meenarh umar farooq inasanki sosai my partner. 27&28 Alhaji yabita da wani irin kallo...... Cikin firgici tace."Alhaji lafiya....."? da sauri tabi gadon da kallo towel din hannunta ta saki da sauri ganin yanda akayima gadon ga kayanta dana wani gardi harda pant da bra tuni tafara kuka tana fadin."wallahi bansan meya faruba Alhaji ba ruwana......" Hannu yasa ya fincikota tsananta ya mamaye mishi zuciya mari ya kifeta dashi."butulu kawai ina tausaya miki ashe ke bakima tausayin kanki da farko da mahaifinki ya fadamin banyardaba gani nakeyi kaman sharri ze miki amma se gashi har cikin gidana kinzo kinamin facikanci kin kawomin kwarto cikin gida, hhmmm naso ace na rikeshi da sena cire mishi kai amma duk da haka kema bahaka zan bar kiba....." ta bude baki zatayi magana yasake wanketa da mari nan danan bakinta ya fashe yafara jini cikin bacin rai yace."kije na sakeki........kuma bahaka zan bar kiba yanzuma yan sanda zan kira su tafi dake fasikar banza kawai Mtsssww......" ya wurgata ta bugu da bango yafice, Kuka take sosai da sauri ta tashi ta lalubi doguwar riga ta zura domin bazata yarda yan sanda suzo su taddata a gidan su kama taba, Alhaji na daki yana waya da yan sanda sukuma su haj. suna falo sejin dadi sukeyi ta fakaici idonsu ta fice daga falon da sauri, daidai lokacin motocin yan sanda ke shigowa cikin gidan aiko da gudu ta fice daga gidan, Waya sukawa Alhaji cewa sunzo se gashinan ya fito yace."yawwa tana ciki." da wata yar sanda suka shiga sedai sun duba ko ina babu rumana ta gudu hakan yasa yabama yan sandan hakuri ya juya ya dingima hajiya fada, akan me tayi sake rumana ta gudu"? shiru hajiya tayi domin taso ace yan sanda sun samu rumana ta kare rayuwarta a gidan yari abun be musu dadi ba dukkansu... Gudu take sosai har kafanta yafara fashewa yana jini domin ba takalmi a kafarta, har ita kanta batasan inda take zuwaba tayi gudu akalla yakai na ba adadi har lokacin kuka takeyi ji take ina zata shiga yanzu tasa rayuwarta a ciki.. Wani guri ta gani da motoci birjik da alama tasha ne, hakan yasa ta karisa da gudu secin kasuwansu suke kaman yanzu gari ya waye rugawa tayi da gudu ganin ana lodi a wata mota, ba tareda ta tambayi inda zasu jeba tayi tsilim ta shige motan burinta daya kada Alhaji ya kamata yasa yan sanda su rufeta shiyasa take alla alla ta bar garin kaduna, charaf condestan ya rikota."ke kinsan ina zamuje kuwa...."? cikin kuka tace."ni ko inane dan Allah ku daukeni daga garin nan inba hakaba zasu kasheni...." yace."To bani kudin motan tukunna..." shiru tayi cikin kuka tace."ka temakamin dan Allah banada kudi." "dalla malama in bakida kudi kisauka dare yanayi mu lodin dare muke.." ba irin rokon da batayi mishiba amma haka ya fitar da ita daga motan se kuka take, wani daga cikin motan ya tausaya mata sosai yace."kabarta ta shigo zan biya mata..." Aiko da gudu ta shiga tana mai godia dama saura mutum dayane ta cika dan haka suka dau hanya......... Zaune yake ya tarbe kanshi hawaye masu zafi suna zuba daga idanunshi hajiya ce ta nufo shi da nufin mishi magana hakan yasa yayi saurin daga mata hannu."banasan jin komai a kyaleni." hakan yasa tayi kwafa ta haye sama. Diyam ce ta sauko hawaye masu dumi suna zuba daga idanunta ganin daddynta na kuka hakan ya kara daga hankalinta, karisawa tayi ta zube gwiwwa biyu a gabanshi cikin kuka take fadin."daddy kayi hakuri dan Allah kadaina kuka, nice laifi nane domin nima kaina naso nayi shiru amma se nayi tunanin innayi shiru hakkin marainiyar Allahn nan yaza muyi dashi duk ko da an daureni da kalamai masu girma amma ganinka a wannan halin ya tursasani dole na bude baki na...." jajayen idanunshi ya dago ya saukesu akanta."Meya wannan abu diyam da kike cewa an daureki a kanshi kuma waye ya daureki..."? tace."daddy mummyce ta daure ni da tsinuwa da Allah ya isa amma daddy gaskiya dayace nasan koda mummy ta tsinemin baze biniba saboda akan fadin gaskiya ne." tanisa."Uhmmm." kana taci gaba."daddy mummy dasu aunty zeeza ne suka shirya komai....." Nan ta fadamai yanda suka shirya komai ta kara da fadin."haka suke azabtar da ita kullum koda yaushe in bakanan hatta kunan da tayi aunty zeeza da aunty Aknan ne suka konata...." nan ta fadamai duk abubuwan da aka dingawa rumana, jijiyoyin idanunshi ne suka firfito tuni nadama da dana sani akan abinda yaima rumana ba tareda bincikeba yayi tausayinta ya cikamai zuciya babban bakin cikinshi yanzu besan inda ta shigaba, daiΒ² lokacin hajiya ta sauko wani kallo ya bita dashi da mamaki take kallon diyam a firgice tace."kin fadamai ko..."? a sanyaye diyam tace."eh mummy kiyi haku......" Ihu haj. ta kwarma."shikenan diyam kin tonamin asiri keba yar arziki bace Allah tsi..........." wani wawan mari Alhaji ya wurga mata tas-tas kakeji seda ya wanke kuncinta da tafi guda hudu sannan yace."kada ki kuskura ki tsinemin ya kuma wallahi se kun kwashi abinda kuka shuka daga ke har magoya bayan naki, kije na sakeki saki daya kuma ku gaggauta barinmin gidana yanzun nan..." Ihu tasa."na shiga uku Alhaji kayi hakuri sharrin shaidan ne..." ko sauraronta beyiba ya dauki waya ya kira DPO akan abinci kamai garin kaduna yatura musu hotonta domin beci ace tabar kaduna yanzuba a dakatar da motocin da suke tashi yanzu. Safa da marwa ya farayi hajiya dasu zeeza suna tsatstsaye sunyi jigum jigum hajiya se kuka take tana rokon Alhaji haka diyam kuka take, Like kaman two hours kiran D.P.O ya shigo da sauri yayi picking. DPO yace."Alhaji kayi hakuri mun duba ko ina bamu gantaba am sorry sedai mu bada cigiyarta....." wayan ne ya sulale a hannun Alh. ya fadi bisa tyles sakamakon jirin daya debeshi shima sulalewan yayi ya fadi, gaba daya sukayi kanshi suna kuka, hajiya na ihu tayi kanshi tana fadin."na shiga uku......" Rumana kam na ganin sun bar kaduna garin gwamna wani kunciyar hankaline yazo mata lumshe ido tayi ta kwantar da kanta a jikin kujeran tunanin mafita take yanzu ya zatayi ina zatasa kanta? ko kadan batason ta koma gida domin ze iya binta can yasa akamata, wata zuciyan ne tace mata."ki shiga duniya kawai gara ki fara rayuwar bariki domin duniyan nan bata sanki......." da sauri ta bude manya manyan idanunta da suka koma jajaye tahau girgiza kai "Ina bazan tabayin rayuwar barikiba indai nai hakan ban godema Allahba kuma banci jarabawan da yake minba kuma mamana zatayi bakin cikin haihuwata domin nayi watsi da tarbiyan data bani Abbana baze taba yafe minba....." da sauri ta fadi a sanyaye, Ta lumshe ido hawaye yafara bin kumatunta bata shareba kuma batayi kokarin hanasu fitowa ba domin in batayi bama batajin dadi, tunanin abinda ya faru a gidan Alhaji tayi ta share hawaye tanajin bakin cikin abinda aka mata sharri akanshi domin in duk duniya zasu juya mata baya bataza taba aikata zinaba, da sauri wata zuciya ta tunatar mata da sakin da Alhaji ya mata, kuka tasa me karfi wanda kowa a motan kallonta yake masu tausaya mata nayi masu yin tsaki nayi, wani ne yace."baiwar Allah ko meke damunki be kamata ki zauna cikin mutane kina kukaba domin in kikaji matsalan wasu naki nafilane dan haka addu'a ya kamata kiyi ki fara tunanin fuskantar abinda ke gabanki a yanzu." ta share hawaye cike da gamsuwa da maganan bawan Allahn nan. Awa biyu da rabi ya debesu zuwa garin da zasuje nan aka fara sassauke mutane hankalin rumana ne ya dada tashi jin ana tambayan inda za'a ajiyeta? shiru tayi har aka gama sassauke kowa cikin fada drivern motan yace."malama tun dazu nake tambayanki ina zan kaiki amma kinyimin banza..." cikin kuka tace."wallahi bansan inda zanjeba domin ni takamamme bansan ma ina nakeba..." yace."muna Abuja ne..." shiru tayi jim tace."bawan Allah katemakamin kaman yanda Allah ya temaka maka ka barni na kwana a motan nan kaga dare yayi in yaso gobe sena nemi gurin zuwa." Jim yayi kafin yace."to shikenan dama se gobe zan dibi passenger mukoma kaduna badamuwa ki kwanta a baya seda safe..." yana fadin haka ya fice ya barta. Kuci gaba da kasancewa dani ummu ramlat danjin yanda labarin rumana me cike da tausayi ze kare shin zatai daria a karshe ko a'a, shin Alhaji sadeeq fadin da yayi mutuwa yayi ko yaya? duk zakuji amsoshin tambayoyinku inkun ci gaba da kasancewa tare dani Mimi queen πŸ‘Έ, Masoyana masoyan litattafaina ina kaunarku ina sanku kuci gaba da kasancewa tare dani leeymart eiser zanci gaba da nishadantar daku, da fadakardaku tare dani *Mimi (ummu ramlat)*✍️ 8/20/21, 8:20 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* My besty Aishat turaki's miss u alot nayi kewarki sosai please ki dawo haka domin ina sanki da yawa. 29&30 Kwance suke suna aikata masha'arsu dukkansu nishi sukeyi domin ba kadan sukejin dadin junansu ba, shushan dake gefe ya zuka tareda hura mata hayakin a baki murmushi tayi tareda dubanshi."Ya faheed muyi sauri mugama kadasu mummy su dawo kasan wannan yar rainin wayan raudah yanzu zata dawo daga school angama musu lecture tazo ta tadda mutane tafara wani musu wa'azi se kace ita bamusan me take aikatawa ba..." tsaki faheed yayi yana sake duban umaima."kanwata nifa ban gaji da cinkiba kinsan ko duka na shanye maganin nan." tayi dariyar mugunta."Allah kara kai sarkin zalama ko..."? yace."Aiso nake na miki cin kacha ne shiyasa.." tayi kwafa."ya faheed niko kadena luwadi meye kake nema a jikin namiji da bakada shi jubeni meye bana baka ka hanani kula kowa se kai kadai amma kai kaki tsayamin ni kadai har maza yi dasu kake haba ya faheed meye dadi a jinsi daya...." murmushi yayi."bazaki gane bane umaima mazan ma sunfi dadi kuma ni gaskiya yanzu yanda na saba da harkan homosexuality bazan iya daina waba domin akwai dadi kuma ana samun kudi sosai." (Wa'iyazu billah) Kwafa tayi ta mike tareda janyo towel tana fadin."gaskiya nagode ma daddy da yayi cikinka gashi nan inajin dadin ka." murmushi yayi."ko kuma na gode maiba dan nine nakejin dadi dan kin zame min tsuka inda nake zuwa inyi ban ruwana duk sanda naso..." da sauri tace."kajika nida bana kula kowa ai ni kaine maji dadina kuma kai dan homo nefa amma lokaci nanan zuwa nima..." da sauri yace."yanzu dai abar maganan." tace."alright bari naje nayi wanka." mikewa yayi batareda komai a jikin shiba yayi sama da ita yana fadin."muje muyi tare." Nan yayi bathroom da ita suna shiga ya kulle kofa sedai na jiyo ihun umaima kasa kasa tana fadin."Ash....ya faheed a hankali wash....." ta buga ihu, nidai nace wa'iyazu billah Allah rabamu da aikata irin wannan abu, uwa daya uba daya ayya wuce wasa, Allah dada kare mana Al'ummanmu Amin ya Allah. ************************************************************************************ Bude ido yayi ya ganshi kwance a daki ga drip dake manne a hannunshi da sauri ya tashi ya fincike karin ruwan yayi wurwuri dashi hajiya tayi saurin jan baya, fuskanshi daure tayi jajawur ya juya yabi hajiya dasu Aknan da mugun kallo cikin tsawa yace."get out, get out I said...." a fusace suka fice, hada kai yayi da tafin hannunshi yana kuka sosai tunanin halin da rumana take ya hanashi sakat tausayinta cike fal da zuciyarshi, ji yayi an dafashi be dagoba domin yasan ko wacece cikin wacce tasha kuka muryarta na cracking tafara magana."daddy kayi hakuri nasan abinda kakeji nasan kanajin cewa kaine silan batan ta, aa daddy bahaka bane kaddarartace tazo a haka kuma insha Allahu zamu ganta." se lokacin ya dago yana maida hawaye saboda beso yar tasa ta gani amma ya maka dansu hawaye ba'a hanasu zuwa, tuni suka fara rolling a saman face dinshi a sanyaye yace."diyam bakomai Insha Allah zata bayyana muci gaba da tayata da addu'a kinji.." ta gyada kai."and daddy in rokeka wata alfarma."? ya daga kai ta marairaice."and please daddy kayi hakuri kamaida mummy kayafe musu kabarsu aunty zeeza suci gaba da zama is not their fault daddy laifin shaidan ne...." Ido yabita dashi yanaso ya musa seya tuna ya mata alkawari dan haka yace."Ina godewa Allah diyam daya mallakamin ya kamarki sedai baki sa'ar mahaifiya ta gariba Allah ya baki uwa meson zuciya da san kanta, Allah miki albarka diyam nayafe mata kuma na maidata dakinta haka Aknan, sedai Allah tsare gaba dan nasan rumana zata dawo cikin gidan nan insha Allahu wallahi suka kara mata wani abu hummmmm......" rungumeshi tayi tana kuka."nagode daddy." Dai dai lokacin haj. ta shigo zubewa tayi tana bashi hakuri ya dubeta."kinci albarkacin yarki diyam na yafe miki dan daba dan itaba bazan yafe miki ba dan haka kema inaso ki yafe mata." ta ballawa diyam harara."na yafe miki diyam Allah miki albarka." murmushi diyam tayi cikeda jin dadin addu'an mummynta a sanyaye ta amsa da."ameen."... ###################################### Kwanan rumana biyar tana gantali a garin abuja batasan inda zata jeba duk tabi ta lalace, kadan daga cikin al'umma mune masu tausayinta suna bata sadaka duba da karancin shekarunta dan wasuma sun dauka mahsukaciya ce yanda take ko mayafi bata dashi balle takalmi, wasu ko ai sedai sukai mata hari da niyyan yi mata fyade Allahne ke cetanta ta samu ta gudu. Yauma kaman kullum rakube take gefen titi jikin wata mota hawaye ke sintiri a kuncinta domin tun rana mazaje ke kai mata hari domin unguwan mabushi unguwace ta karuwai da sauran gangan yan iska, ji tayi an dafata jikintane ya hau rawa tako ina domin tasan yanzu batada maceci se Allah, Kafin tayi wata wata mutumin nan yafara janta harya fitar da ita a tsakiyan motocin nan, duk da kasancewar darene amma unguwan kamar rana dan kowa se harkan gabansa yskeyi, kuka rumana tafara ba kadanba tana rokon mutumin amma ina be jiba, seda ya jata wani lungu da mugunta ya matseta."na kamaki yau bazaki tsere minba." cikin kuka tace."kayi hakuri dan Allah."be nuna ko alaman yajiba hakan yasa ta runtse ido a cikin zuciya tace"ya Allah ka kawomin dauki" hannu yasa yana wasa da sassan jikinta tunanin yanda zata kwaci kanta takeyi domin tabbas indai batai wani abuba ze iya aikata abinda yakeso akanta, dukawa tayi ta rarumo wani dutse ta buga mai akai tana niyyar guduwa ya fincikota ya bugata da jikin ginin dan seda tayi kara kanta ya fara fitar da jini, cizo ta gantsara mishi yasaki ihu tareda kifeta da mari dukunnawa tayi ta wawuso kasa ta watsa mishi a ido da gudu ta ruga, ba tareda ta tsaya duba titiba tashiga da gudu babban burinta ta tsira daga hannun fasikin nan, dai dai lokacin wata farar dypidor ta shararo titin da gudu ba tareda ta lura ba tayi sama da rumana tayi sama ta fado jini ya hau biyowa daga kanta da sauri motan tayi parkin a gefen hanya.... More comments more typing. Comments dinku na kadan. Mimi ✍️ 8/20/21, 8:20 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ *LABARINA* πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ Alkalamin. ✍️ *Mimi.πŸ‘Έ* Haleemart Iserh *(ummu ramlat)* *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ* *M. W. A* *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’–* Amarsu Allah bada zaman lpy my hafsat sunusi Ahmad (babyn farooq) gonna miss yhu sister, Allah bada zaman lpy ya kawo kasantar daki I luv u plenty plenty. 31&32 A hankali ta fara bude idanunta da taji sun mata nauyi harta budesu a saman pop dake dakin juya idanunta tayi zuwa ga hannunta se taga karin ruwa, dakin ta karewa kallo kan ta fahimci a inda take wato asibiti, da sauri ta lumshe idanunta jin alamun za'a shigo zuciyar tane yake bugawa da karfi wani irin daci na ziyartar kan harshenta, a yanayin duk abinda ya faru ke dawo mata, Allah kadai yasan irin abinda takeji a zuciyarta bata fata wata mace yar uwarta taji irin wannan abun, da sauri ta kuma rintse manya manyan bold eyes dinta tareda taune harshenta

Chapter 5 of 14