Reading MATAR SO Complete PART 2 by MAI DAMBU Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addu'a dan an zubda cikin jikinkine, kina bani mamaki."
Jiri nake gani, tare da duhu na rike cikina ga wani zufar dake bin jikina kamar ina cikin zafi. Jinine ya tsinke yaje zuba sosai komawa nayi da baya ina runtsa idanuna, duk ilahirim jikina rawa yake, sosai ya taka motar ganin yanda lokaci guda nake sauke haki.
Babbar asibiti yayi dani sannan yakira dr Nafe ya faɗa mata, kwatancen matenity tayi mishi, da gudu ya isa gurin,.

Parking yayi ya fita tare da zagayowa ta gurin da nake ya buɗe, sannan ya cironi ganin yanda jini ya jika min kayana daga kan zanina har hijab ɗin jikina, ga kuma wanda yake zuba.

Cak ya ɗaukeni bai taɓa ganim jini haka ba, sai yau. Yana shiga dani ciki kowa sai binmu yake da ido tsabar tashin hankali.
Gadon marasa lafiya dr nafi da wasu nurse suka turo, ya ɗaurani akai, da sauri suka wucce dani ɗakin yan ɓari, lokacin bansan waye akaina ba, jikinshi duk ya ɓaci, kita yayi ya shiga mota sai gida. Kayan jikinshi yake son sakewa, a falo ya sami Fareeda da Balkisu, ganinshi cikin tashin hankali ga jini na bim jikinshi, kallonshi Fareeda tayi, cikin tashin ɗimauta tace.
"Ka zubda cikin ko? Ka zubda hankalinka ya kwanta, hmmm amma kasani kasayi tashin hankali da hannunka, ka zubda abinda zai hanaka barci, ka zubda namu ka kwana lafiya wannan da ka zubda sai ya zame maka alakakai kaida ganin farin ciki har abada, mi zanyi da azzalumi irinka mugu fasiki, dan shine yake aikata duk abinda Allah ya haramta, ka kuma turo min da sakina dan na gama zama da kai."

Bakin ciki ya hana balkisu magana itama sama ta haye ta ciro kayanta daga wardrob ta shirya a wani babbar jakanta, tare da fashewa da kuka, tabbas duk abinda Yunus ya aikata da sa hannunta, dan da ta zama mace ta gari da babu yanda Yunus zai taɓa zubda cikin wata ba, itace ta fara nuna mishi bazata iya rike huda ba, yau gashi kuskurenta yaja kowa ya rasa farin cikinsa. Da yau ta cire mulki da son jiki da babu wacce zata zubda hawaye da yunus da ta amshi matsayinta na mace da Yunus bai zama abinda ya zama na mugun hali ba, ina zata kai hakkin Maryam. Mi zata cewa Ubangiji sabida kuskurenta Yau Iowa yana Kuka.

Mikewa tayi zuwa d'akinta Fareeda ta take zube a gabansa abin sallah tana Kuka mai con rai. D'agota Balkisu tayi cikin Kuka tace.
"it's my faults, banyi deserve yafiyarku ba, dan nice na nuna mishi yara basu da daraja, haka ma mace tana da lokacin da ta dace ta d'auki ciki, kosa halinshi nice na fara lalata shi, dan dama ance matar fari ce ke lalata miji kuma na yarda da haka Fareeda ku yafemin Dan nasan hakkinku bazai tabari barina na zauna lafiya ba, Ynx a wani hali maryam take ciki."

Mikewa Fareeda tayi daga duken da take ta janyo gyalenta suka fita, duk suka zauna a falo.
Can sai gashi ya fito jikinshi a sanyayye ya fita, bin bayanshi sukayi suka Shiva mortar fareeda.
Juyawa yayi yaga sun shige motarta, jan motar yayi har suka fita, daga gidan suna bin bayanshi.
Koda suka isa asibitin, har inda aka shiga dani.
Koda suka iso kiran Dr Nafi yayi, yace ya dawo.
Dama suna can ana rikici akan karfin alluran da aka min, koda ta fito ba tare da damuwa ba tace.
"Yallaɓai badan ina ganin kimarka ba da babu abinda zan taɓa yiwa matarka. Ka dubi abinda ka janyo min ana ganina da kima kasa an farq zargina da cewa ko nice nayi mata alluran da yafi karfin jininta, kasa manysn.likitoti suna cin mutuncina kimanin shekara goma sha biyar ina nan ban taɓa samun matsala da kowa ba, sai akan case ɗinku ka kaita am mata allura mafi hatsri wanda ba lallai bane tasake ɗaukar ciki. Wallahi baka kyauta min ba ka nemo jini a saka mata dan jininta yayi matukar zuba badan Allah ya takaita cikin ya fita ba a cikin jini da bansan yanda zanyi da wannan tashin hankali."

Tana gama faɗar haka ta juya tabar gurin kowa sai masa kallon Allah wadarai suke, dan da da farko sun tausaya masa jin abinda yayi muka bai musa ba, yasasu, ji haushi har wani mutum yace.
"Wallahi kayi asara, cikin sunnah ba shege ba, ni ynx zuwana asibiti na goma sha ɗaya kenan ina niman ko ɓarine Allah ya bani a cikin gidana kai da kasamu har kana kai matarka wa i gurin aka zubda cikinta kasan kuskuren da ka aikata kuwa, Kai da Allah."

Kuka balkisu take, sosai can wata nurse ta fito akan jinin da za'a karamin, lab suka nufa aka ɗibe jininshi, dake grp (O) jininshi.
Koda aka saka min amadadin jinin ya gwauraya. Kusan awa ɗaya da saka jinin sai ga borin jini, sosai ya feso har kan fuskana dole suka cire jinin, dr Nafi ta fito cikin jin haushi tace.
"Toh jinin yaki, zama dan ya feso mata da borin jini, dan jininta A+ ne kuma da nakan zai mata, amma dole sai an nimo mai irin jininta sak."
Rike kanshi yayi ciki tashin hankali ys laluɓi nomber Yaya hayat ys kirashi dake a cikin asibitin yake, kallon dr Nafi yayi yace.
"Don Allah ki taimaka min kar yasan abinda ya faru, Kanwar Dr Hayat Omer ne."

Zaro ido tayi cike da mamaki, can sai ga Yayan ya iso, faɗa mishi halinda nake ciki Dr Nafi tayi da jinin da ake bukata, lab ya wucce aka ɗabi leda biyu sannan ya kira Hamdiya da shema'u da Suhaima matarshi. Ya faɗa musu,.lokaci kusan guda suks iso asibitin.

Cikin damuwa, har an wanke min mara sannan aka turoni a gadon bayan an sauya min kaya da wani dark green. Aka gunguroni zuwa ɗakin yan ɓari,

Sharaf nake kwance babu alamar numfashi, sai ma wani irin haske da nayi, fuskana a kumbure. Idanuna sun shige ciki, sau uwar karan hanci. Har za'a shiga dani yace.
"Ko zaku maidata aminity ne." karkata gadon sukayi zuwa wani keɓetacciyar shashi daban. Daki na biyu aka sakani a ward B....

Hankalinshi ya gama tashi, a tsorace yake da kowa, musaman matanshi da kuma ni.

Kiran Umma Aunty Shema'u tayi, can sai gasu tare da Mama suka shiga har ɗakin da nake ban sani ba.
Kallon yanda Fareeda ke kuka Umma tayi, cikin murmushi tace.
"Kiyi hakuri mana, Allah da ya amshi wannan shi zai baku wani, cikin ikonshi da buwayarshi, karki manta itama maryam ɗin bata wuci Allah ya amsheta ba, kinga kenan kukan ya kare,kuyi addu'a Allah ya maida muku, wanda suka fi wanda ya tafi Allah ya bata lafiya yasa masu cetone, ya kuma sake baku mai amfani da inganci."

"Amin, Umma Amin." Inji shi, har bakinshi na rawa.

Komawa gida Umma tayi, tunda Mams tace zata zauna. Gurin Azhar sai ga Rahilah da Aman, sunzo har da abinci suka zo dashi. Aunty Hamdiyya da Auntƴ shema duk sun koma gida, sai matar Yaya aka bari da Rahilah.

Balkisu itama ta koma gida, Fareeda kan gidan iyaƴenta ta wucce.
Can bayan La'asar sai ga Mamie, itama Ahmad da Rahimah har zuwa wannan lokacin ban farka ba, sai bin likitoti yake. Suna zuwa suna fita hankalinshi duk ya tashi. Bai taɓa shiga tashin hankali haka ba.

Yakira Hajiya zai faɗa mata tace mishi.
"Nagode ! ka zubda cikin ba? Ai balkisu ta faɗa mana komi."

"Hajiya kuskure aka samu."
"Ba kuskure bane Yunus, son kaine ita yarinyar ka sameta a sauki ba, dan babu sisin kwabonka akanta duk kuɗina ne, sannan ka cire mata cikinta da karfin tsiya, ka sata zubda kwalla. Yunus ni bazan maka baki ba sai dai fatar shirya Amma tabbas hakkin maryam sai ya tambayeka, yarinyar da tunda ta shigo gidanka kake wahalar da ita, bata taɓs faɗawa Iyayenta ba. Tsabar tana ganin zata iya da kai, kasan tulin zalincin da akayi gurin aura maka ita, yarinyar da batafi sha takwas ba, ka ganawa azaba ta hanyar rabata da farin cikinta, zaka ribanci abinda ka aikata, kuma zaka biya shi lokaci na zuwa da zaka ɗanɗana kuɗarka dan wannan bashine hakkin maryam kuma sai ka biya shi."

Tana gama maganar ta kashe wayar.

Dafe goshinsa yayi kaman zai tsage.
Har dare ban farka ba, dole yasashi tafiya gida amma badan yana son haka ba.

....... Koda ya isa gida wanka ya shiga, yana kwance ruwa na ratsa shi, tunanina da kukan da nake yasashi buɗe idonshi a gurguje ya fito ya sauya kayanshi na barci, ya kwanta dake yayi sallah a can masalacin asibitin.

Karfe biyu da hamsin da uku na dare, zaune yake a ɗaki tare da laptop ɗinshi ya nutsu yana, aiki. Kukan jarirai da shashekar kuka yake ji. Sosai kukan ya hanashi sukuni, mikewa yayi ya fito. Har falonshi baiga kowa ba, can sama yaji kukan dan haka ya haura yana bin kukan, har bakin kofar falona saka hannunshi yayi zai murɗa kofar yaji ya taɓa abu kamar ruwa, ɗaga hannunshi yayi yana dubawa, jini ya gani.
Ƙifar ɗakin ce tq buɗu ya kutsa kanshi, kwance ya hangoni cikin jini. Ga jarirai akwance a jikina muna kuka tare dasu. Sai kuka suke, suna kara rikeni tare da shigewa jikina, jikinsu duk jini.

Takowa yayi ya nufi kaina d sauri aka janyeni zuwa cikin duhu. Dariya aka mishi sannan aka ce, "Dole kabiya abinda ka aikata."

Muryan ce ta sauya irin tawa aka ce mishi "daddy karka zubar min da cikina" ta bayanshi juyawa yayi ya sake ganina a duke ina zubda jini, da sauri yayi kaina, aka sake mishi magana.
"Karka zubda min da ɗana."

Lokaci guda ya birkice ga jariran da suka rufa mishi, a jiki suna hayewa jikinshi, tare da zubda jini, ga wani irin kuka da suke mai cika kunne.

Durkushewa yayi yana sin kwance kanshi jinin dake bin jikinshi tare da kiranshi yasashi ɗagowa, yana kirana da gudu ya faɗa cikin ruwa tare da nutsewa kasar ruwan kaman ana janshi......

A firgice ya tashi tare da sake salati, tsabar ya tsorata gumi ke zubo mishi ta ko ina, tashi yayi zuwa ban ɗaki yayi wanka da alola, ya fito.
Sallar nafila yayi da addu'o'i ya kwanta.

Ko minti ɗaya bayi ba, yasake wani mafarkin damu, ina rike da jariran ina kuka sosai duk yanda yaso magana ya kasa dan dole ya shiga binmu dan idan yana kusantoni kamar janye ni ake.

Nan ma cikin ruwa ya faɗa, cikin mugun tashin hankali da firgici ya farka lokacin har ana shirin shiga masalaci, alola yayi fita da sauri dan jin kukanrmu yake kamar zai fasa mishi dodon kunne.

Koda ya shiga masalaci nan yasami nutsuwa yayi sallah bayan fitowarshine, ya koma cikin gidan ya sauya kaya ya nufi asibiti, tun da ya shiga ward ɗin yake jin faɗuwar gaba.

Har ɗakinmu. Murɗa kofar yayi ya shiga, a nutse tare da sallama. Ganin yanda aka kwantar dani tun jiya haka nake yasashi jingina da kofar ɗakin, tare da faɗawa mugun tunani.

Take ya soma jin kamar mafarkin da yayi yana dawo mishi, ɗago kanshi yayi ya zuba min ido dake akwai firgici a ranshi take idanunshi suka shiga nuna mishi abinda ya faru a mafarkin, dafe goshinsa yayi tare da barin ɗakin.

........ Cikin lokaci kalilan daga jiya zuwa yau Yunus ya gigita ya fita hankalinshi dan banda sautin kukana babu abinda ke mishi zarya a kunne.

Koda yaje gurin aiki kasa taɓuka komi yayi, ga wayar da yake akai akai. Kamar zararre haka ya koma ba halin ya runtsa ido toh zai tashi a firgice.

........Hankalin kowa yayi matukar tashi ganin har lokacin ban farka ba, sabida tashin hankali sai da Asthmar Mama Amarya ya tashi, haka muka na sake kwana, anan ne fa aka shiga niman mafita Aman da Ahmad sun bada shawaran a fita dani Jidda, yayinda Umma tace abarni zan farka kar ayi ɓarnan kuɗi.

Sai da nayi kwana uku, wanda a cikin kwanakin nan Yunus yayishine takar mahaukaci dan ko shi ɗaya ne kuka yake ji.

A binka da wanda bai magana sai abin ya shiga taɓa shi sosai dan har ana tunanin ko dan halin da nake cikine.

Hajiyarsu tana nan kaduna dan a gidan shi ta sauka. Mama kilishi ta koma.

Zaune suke kowa ya zubawa gadona ido.
Can na motsa hannuna, mikewa sukayi yana jingine a jikin kofa, ya zuba musu ido.
Sake motsawa nayi tare da bud'e idanuna, wanda duhu ya cika min cikinshi. Rufewa nayi can kasar makoshina nace "Umman !!! Zan sha ruwa."

Ruwan ɗumi ta ɗiba tare da mikawa Shema'u ta ɗaga kaina, ta bani nasha. Har ina kwarewa, maida ni tayi kwance,

Kowa na mamakin irin soyayyar da nakewa Ummanmu ba komi bane yaja haka sai yanda tajani a jikinta. Fiyye da sauran yaranta dan takance duk ciknki nafisu zurfin ciki, shi yasa takee mannani da jikinta, dukda bata koya mana faɗar damuwarmu ba, bawai dan bata son sani ba sai dai Umma tana da riko da saka abu a rai idan da tasan halinda nake ciki, bazata taɓa hakuri da abinda yake min ba.

Dafa goshina Aunty Hamdiya tayi, tace.
"Sannu Auta."
Sake buɗe idanuna nayi sabida duhun da nake gani. Ina kallon inda tanake jin muryanta.

Shigowar dr Nafi yasa duk suks fito sai shi ɗaya da ya rage a ɗakinki, dubani tayi sosai sannan tace min.
"Maryam Ina ke miki ciwo?"
"Babu, cikin yafita ko?"
Rike hannuna tayi cikin tausayawa tace.
"Allah zai baki sama da wanda ya fita. Ki yarda da K'addara mai kyau ko mara kyau."

"Dr kenan! Ai tunda na kasance musulmai na amshi k'addarata hannu bibiyu, tun daga ranar da aka halicceni har zuwa ranar da zan koma ga Ubangijina, akwai kurakuran da sai mun gyara da kanmu kafin musamu rabauta."

Ina gama faɗar haka na juya mata kaina ina jin ciwo a cikin zuciyata fiye da kima, runtsa idanuna nayi dan naji fitarta. Jin kamshinsa yasani kara jin wutar tsanarshi.
Shafa kaina yayi zuwa fuskana nayi maza na rike hannun, na kalleshi cikin ido nace.
"Kasanyawa zuciyarka, cewa tankar bamu taɓa zama a inuwa ɗaya ba, ka ji aranka ni mafarkice nazama wata shuɗaɗɗiyar karni da aka jima da yinta, ka janye tunaninka akaina dan haka shi zai tsiratar da kimarka da Mutuncinka da iyayena suke gani, Kace bani da dajara ynx zamu fara wasan. Kamar yanda ka azbatar da zuciyata da ruhina, ka sani kuka ka kuma katngeni da farin cikina. Ka maida min zuciya wata iri na daban kasani tsanar ka, idan baka manta ba kace min zaka rabu dani sai lokacin da kayi niyya, toh ynx kabani idan kuma ka k'i kuma tabbas duniya zata jimu daka kafita dan bana kaunar ganin fuskar, idan ka takura min toh kasan suwaye iyayena da kuma abinda suka sani akan addini toh zan faɗa musu susan yanda zasuyi dakai ko su kaika kotu ko kuma su nuna maka cewa ni nafi zinari da azurfa daraja da kima kuma wallahi Ubangiji sai yayi min sakayya dan ban yafe maka ba"

"Kiyi hakuri Maryam wall"
"Bazaka kafita bane?"
Na tambayeshi a hasale.
Zai sake magana nace.
"Waje"
Jikinshi babu kwari ya fita, tun daga ranar ya shiga sintiri. Ga mugayen mafarkan da suka sakashi a gaba.

Ni kuma naki kula al'amarinshi. Hajiyarshi da tasan komi bata taɓa damuwa ba, sai ma nuna min, kulawa na musaman fareeda da balkisu kullum suna asibiti. Sau ɗaya Aneesah tazo.

Kwana na goma sha biyar, suka bani sallama koda aka haɗa kayana. Na kalli Umma nace.
"Gidanmu zaki wucce dani."

Cike da mamaki umma ta zuba min ido.
"Kiyi hakuri muje gidana."
Kai tsaye nace mishi.
"Lallai ma kuwa, kaje akwai mata masu daraja da kima, kana da kuɗin da zaka iya auren Yar shugabar kasa, ni Yar malamai ce bamu da kuɗi sai yarda da Allah."

Duka Umma takai min ranta a ɓace tace.
"Wallahi ki wucce kibi mijinki."
"Babu inda zan bishi."
Na faɗa kaina a sunkuye.
"Toh wallahi zan kira Malam."
"Umma sai dai kuyi min duk abinda zaku min amma badai gidan Yunus ba."

Ga baki ɗaya ɗakinmu ya hautsine da tashin hankali sun kafe nima kuma wani mugun taurin kai ya kafar dani.

Har Malam yazo shima yayi juyi duniyar nan naki har da barazana yayi min idan ban koma gidan yunus ba toh zasu zareni a cikin yaransu.
Kallon Yunus nayi cikin.muryan kuka nace.
"Mai nasara, kayi nasara rabani da farin cikina, Yanzun kuma da iyayena ko? Toh wallahi da na zauna da kai gwaara nafita, duniya ka zauna kai da naka iyayen lafiya hakkina sai ya kama kowa dan a dake ni an hanani kuka."

Ina faɗar haka nasa kai zan fita, kusan yanayin ɓari, ban kai bakin kofa ba jini ya sake ɓale min, a gurin na yanki jiki na suma.
Tashin hankalin da na shiga Allah kaɗai ya sani, dan sabon jinya ce tasake dawowa.
Ga jinina da yayi mugun hawa........

Fatan alkhairi gareku......Masoyan Yunus naso kai typing ɗin irin 6k....Amma iya kanshi...5.440k....Nagode



🤭🤭🤭🤭🤭
🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂

_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_



*BOOK 2👈*
*Page...7*
Fushi Umma tayi taki zama a jikina, Hajiyarshi ce ta zauna min, kullum sai yazo kamar maraya, ga tashin hankalin da yake ciki na mugayen mafarkai.

A haka muka ɗibe kwanaki, sannan aka sallameni. Gidanmu Hajiya ta kawoni. Dan tana son magana da su Umma, amma dole sai Alhajinsu Daddy yazo dashi da Sulaiman.

Karfe biyu suka iso, harda shima daddyn. Ina kwance a ɗakin Mama Aunty gausiya tazo kirana, mikewa nayi na fito. A nutse har falon baki, da sallama na shiga na gaida kowa na falon sannan na koma gefen Malam na raɓe, dan umma taki sake min fushi take dani.

Da sallama Alhaji ya buɗe taron da Addu'a sannan, yace.
"Da farko kafin nace wani abu ina bawa Maryam hakuri abinda abinda Yunus ya aikata mata, munyi haka ne dan kuma iyayenta kusan halin da take ciki, nayi bakin ciki da alhinin abinda Yunus ya aikata, amma ba komi kanshi yayiwa. Sannan abinda ya kawo mu anan shine.."
Har yakai aya, sannan ya ɗago kanshi yana duban malam da umma, wnda mamaki ya kusan sambaɗesu zuwa lahira, cigaba yayi da cewa.
"Allah ya gani nafita hakkinshi na masa komi da uba yakewa ɗa nayi na fita hakkin Yunus, amma idan bazaku damu ba zanso naji Ra'ayinku akan abinda ya aikata muku."

Sunkuyar da kai Malam yayi yana girmama al'amarin, shiru yayi sannan ya kalleni cikin sanyi murya mai bayyana tsantsar hakurinshi yace.
"Tabbas anyi kuskure, sai dai mu bamu da ikon hukunta mijin maryam, kuma idan muka ce zamu ɗauki mataki ai kimar zata iya zuɓewa, mi kike gani Hasina."
Kallon Malam Umma tayi cikin mamaki tabbas ranshi ya ɓaci, girgiza kai tayi, sannan tace.
"Malam!!! Kaine mahaifinta duk abinda kace ai duk ɗaya ne."

Kallonta Malam yayi tare da kallon Alhaji yace.
"Mu dai a matsayinmu na iyayenta, munyi hakuri babu wanda yafi karfin laifi, sai dai bazamu tauyeta ba gata nan idan ta hakura shiknn."

D'ago kaina nayi cikin matsanancin kuka ina kallon Malam bakina narawa.
Alhaji yace.
"Mun gode sosai da wannan dattakon, maryam muna jiranki."
Kallon Umma nayi na kalli hajiyarshi kauda kanta hajiya tayi, sannan na kalli Mama amarya gyaɗa min kai tayi, cikin murmushi umma kuwa bata iya kallona ba, shi nakalla. Ya gama zuba min ido, girgiza kaina nayi yanda nake tuna rashin imanin da yayita min, cikin wani irin murya nace.
"Bazan yafe ba, ya cutar dani, ya dakeni ya tunkuɗeni."
Dafani malam yayi na ɗago kai cikin kuka nace.
"Kabarni na faɗa dan idan na cigaba da rike haka mutuwa zanyi, malam zuciyata kamar zata kama da wuta, ya sani kuka amma wancan ba komi bane, idan na tuna tsantsar rashin imanin da nagani a cikin kwayar idanunshi, bazan iya zama dashi ba, Umma kin koya

Please Login or Register in order to submit comment