Reading AUREN BAZATA BY ZAINAB YAKASAI SHUKRA Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fada bathroom don yin wanka.



" A bangaren shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta.

"Bayan kamar 30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma wani a hannun sa yana goge kansa dashi.
" kai tsaye gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare ya wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu.

Bayan da ya gama shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita sannan ya wuce dakin shukra.

"Yana karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam.

Cikin bacci shukra taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana kallonta.
" A zuciyar ta take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada jan tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta.



"Shiko SAFEER juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe.



" Washe gari misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa.
"knocking din da ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar.

"kokarin tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta
" ke bakida hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun kallo...... Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa cikin falo.

"Dan nazo gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka.
" Ammiki din ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta yafi aikinta yawa).

"Wae ke me kika zo mn gida da sassafe.

" Baki ta saka tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?...


"To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na.

Tana ciki ya fada a takaice.
"Au ita bata rashi ba 🤔 ikon Allah koda yake ae da gajiya gwara ta huta.
" Gajiyar me ya fada yana mikewa wane zai daketa.

"Tana ganin haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi.
God save you ya fada yana koma kan kujera.
" To ynx yaya haka xan tafi ban ganta ba.
"Ehhh yace yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu
Fita tayi tana waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa daki tunda bashi da abinda xeyi.

" Aiko miemie na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige.
Kai tsaye dakin shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup.

" Aunty shukra ta fada tana yi mata murmushi.


"Murmushi itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar.
" ya sunanki ta fada tana kamo hannunta.
Sunana miemie.
"Miemie ya gida ya mamah?
" lafiya kalau muke.
Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta tana karewa dakin kallo.

"Bakomai miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba (Tayi mata karya).


Ok na dauka sbd yaga kin gajine bayaso in tashe ki.

" Gajiyar me miemie? Ni ban gaji ba ae.
Uhmm kawae tace tana hayewa gadon.

" Dariya shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta.

"A takaice dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna.
" Sanda miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata.
Godiya sosai tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi.



" Yau ma da safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai yayi ya koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba kawai dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin sa).




" Yau sati biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa shukra a idonsa ba.


Dawowar sa daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae kuwa sai Y xarce dakin.

" Shigarsa yy dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata cinya ba..
Kallon kallo suka shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa.





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/29, 5:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA



Dedicated to miemie bie ❣



0⃣7⃣




Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta fada tana hararar sa..

Hauka ya nanata kalmar a zuciyar sa

"Allah ya baki hakuri ya fada yana juyawa zai fita.
" Yana zuwa bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa.
"Takowa yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya.

" Iya tsorata shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta.

"Hannu yasa ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin mahaukachi yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba tunda kina dashi.

"Kuka tashiga yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake karfin ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau.

" Ganin batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro nakeji, na tuba bazan sake ba.


" Gani kawai shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece. (shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata).


" Tun daga wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar ta.


" Yau ta kama monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin sa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba tunda yasan shukra ba zatayi masa girki ba.

" Yasa kai xe fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita a palour'n ba,

," ya safeer dan Allah xan bika ka kaini gida
To jeki dauko hijabi mu tafi..

Ihu murna tasa ta shige daki da gudu



SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/31, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻




WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


Wishes to congratulates you as you finished your novel that always makes people happy, because it composed a lots of lessons.
May God bless your entire life #MIEMIE BIE
Dedicated to you 👆🏻



0⃣8⃣


"koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba kasan cewar dama a shirye take mayafi kawae ta dauko ta fito ta samu safeer zaune cikin motarsa yana jiranta.

"Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece mata ba haka suka kama hanyar gidan su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka.


"cikin lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer nada aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita cikin gidan ba.


" Ango kasha kamshi abokinsa yace masa yana dariya irinta tsokana.

"Koma bece ba yakaro yana mika masa hannu suka gaisa sama - sama kasan cewar sun kusan makara.


" sanda shukra tashigo cikin gidan bata samu kowa a palour ba hakan nema yasa ta shigewa dakin Ammii kai tsaye.

"zaune ta samesu ita da Areef suna kallon wani serious.
" Da mamaki suke kallon ta kafin Ammii tayi karfin halin mata magana

"ke kuma lafiya kika xomana gida da sassafe, ina safeer din yake ta fada taba kallon kofa kamar me neman shi.

" Ya wuce office in ya tashi zai shigo ae ta fada tana wucewa kan gadon Ammii.

"Aunty shukra yaushe ya safeer xe dawo inji Areef.


" Ban Saniba ta fada tana juya masa baya.

"To Aunty ki kirasa ki tambaye sa mn.

" Karka dameni Dalla malam.

" Bekara cewa komai ba illa ma fitan da yayi daga dakin.

" Duk abinda suke Ammii na jinsu sai da Areef ya fita ne ta juyo tana kallon shukra

"shukra anya ko kuna zaman lafiya da yaron nn

" Ammii wace irin magana kikeyi ne wae, waya gaya miki bama zaman lafiya.

"Halinka nasani ae shukra.
" To Ammii ki kirasa mn ki tambayesa.

"Bazan kirasa ba sai dai in bari shawara kan kiji tsoron Allah kada ki tauye wa yaron nn hakkin sa karki ganshi shiru - shiru ki zaluncesa, idan mu bama ganinki Allah na ganin ki.

" Kai Ammii dan Allah wae waya fada miki bama zaman lafiya me ma ya kawo maganar xalunta da wani tauye hakki.

" kedai kika Sani inji Ammii tana ficewa daga dakin.



"shiru shukra tayi tana tunanin mgnr da Ammii ta gaya mata, tanason daukar maganar Ammii amma shedan yana mata huduba.






4:00 pm


" Daddy ne ya shigo cikin gidan daga office shukra yasamu a palour, da mamaki yake binta da kallo.

"Daddy sannu da zuwa ta fada kafin Ta durkusa har kasa ta gaida shi.

" Ba yabo ba fallasa ya answer sannan ya shige dakinsa, Ammii ma ta fito daga kitchen tabi bayan daddy.

4:40 daddy ya fito palour yace Ammii ta kira masa shukra.

"Bayan Ammii sun fito tare da shukra dukansu suka zauna a kasa suna jiran me xance.


"shukra lafiya na ganki a gida kuma.


Ita abinma mamaki ya bata exactly tambayan da Ammii tamata irinta daddy ya mata.
" Lafiya kalau daddy kasan yau ya koma office shine yace bari ya kawoni gida inya dawo xexo mu tafi.


"Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace to madallah Allah ya dawo dashi lafiya.

Ameen sukace dukkansu kafin kuma shiru ya ratsa palour ' n.

" Shukra ce ta katse shirun ta hanyar cewa daddy daman inason magana da kai.

"Dawo da kallon sa yayi kanta sannan yace ina jinki.

" Daddy so nake asamomin Aiki in dinga zuwa da xaman gida, kaga duk kawayena damuka gama service aiki suka samu.

"sbd kawayenki na aiki shine kema xakiyi Ammii ta tamabeyata.

" A a Ammii gani nayi da zaman gidan ai gwara na dinga zuwa aiki ko.


"To shukra ae alhakin aikinki ba a hannu na yake ba mijin ki keda ikon samo miki aiki baniba.

" To daddy kamishi magana dan Allah ta fada kamar zatayi kuka.

"In banda abinki shukra ae kin fini kusa da safeer ke yakamata ki tamvayeshi, kuma bama wannan ba yana iya yiwuwa in tamabyeshi kuma bayaso amma ya amince sbd ni na tamvaya baxe iya cewa a a ba kuma Kinga ae na shiga hakkin sa ko, Amma idan ke kika tamabyeshi tunda ba tsoronki yake ba xe gaya miki gaskiya in yana so ko baya so.



"To tace tana goge kwallar data cika mata idonta.


Shiko daddy yana gama maganar sa ya tashi ya shige dakinsa.
Ammii ce ma ta tsaya tana bata baki kantayi hkr ta tambayi mijinta inya bari to, in be bari bq kuma sai ta hkr.




6:00 pm safeer ya tashi daga aiki yana cikin tattara files din dake gabansa abokinsa ya shigo.


"Gaisawa suka shiga yi kafin Abokinsa ya zauna,
" safeer wae ya naganka haka ne so silent inji haiydar.

"Bakomai safeer yace yana dauke kansa daga kallon haiydar.

" Da komai safeer sai dai in baxaka fadamin ba, amma a gani na be kamata ka boye min komai a yadda muke da kai Amma bakomai in bakason fadamin bazan matsa mk ba.

"ka gane haiydar wallahi kwata kwata banida kwanciyar hankali tunda akayi auren nn, na dauka bayan auren komai xe dai - daita ashe tashin hnkl ma yana gaba.

" Haba safeer ynx akan wnn ka tayar da hankalin, maxa fa gwagwarmaya aka sansu dashi, ae kai da kanka xaka jata a jikin ka ka mantar da ita cewa AUREN BAZATA aka yimata ka koya mata sonka bawae ka tsaya zuba ido ba.

" Ta yaya haiydar? Taya zan koya mata sona, bayan tunda akayi bikin yau sati biyu knn ban taba sata a ido na ba sai yau, beside ma she is arrogant as a dethroned chief, she is feeling herself because she comes from a very influensive family. Thats why she's doing what she want to me, Amma bakomai idan munada rabon farinta ran juna watarana sai mu faranta idan kuma bamuda shi sai Allah ya kawo mana mafita.


To Allah ya kyauta haiydar ya fada yana mikewa.
Mikewa shima yayi yana cewa Ameen suka a tare inda safeer ya nufi gidansu shukra kai tsaye bayan ya tsaya a well care ya musu shopping.....





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/1, 1:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻



WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA





0⃣9⃣




7:30 pm safeer ya isa gidan shukra bayan yayi parking motar sa ya fito ya nufi cikin gidan rike da shopping din daya yi musu.

"Dukkansu a palour ya samesu, durkusawa yy har kasa suka gaisa da daddy sannan Ammii.

"Bayan kamar 10mints suka fito gabaki daya don musu rakiya, har gaban motar su suka rakasu Ammii na dada yiwa shukra nasiha kan tabi mijinta.

" uncle zan biku "
" A a Areef gobe akwai skul ka bari ran friday zanzo sai mu tafi"
To kadai yace ya koma cikin gidan ransa a bace don ba hk yaso ba.


Minti talatin ne yakai su shukra gida bayan safeer yayi parking ne duka suka fito kowa ya nufi dakinsa.




"To washe gari safeer gidansu yakai shukra daze tafi office.

" Da murnar Mamah ta tare ta, bayan ta gabatar mata da abun motsa baki ta kira mata Aysher ta fice ta basu guri


"Hira sosai sukeyi da Aysher anan ta gane Aysher nada kirki aranta tace dukansu suna da kirki da son mutane sosai.

" Aysher wae ina miemie ne "
" miemie taje skul amma ynx xaki ganta ta dawo sbd suna exams ne"

"To Allah ya dawo da Ita lafiya"
"Ameen Aysher tace" sannan suka cigaba da hirar su.


"Ko da lokacin girki yayi ma tare sukayi da shukra kasancewar shukra ta iya girki sosai.

" 12:14miemie ta shigo cikin gidan da gudun ta kamar an jefo ta aiko tana ganin shukra tayi gurin da gudu ta fada kanta tana murnar ganin ta.

"Itama da murnar ta take tamvayar ta" ya exams "
" Exams Alhamdulillahi Aunty, ina ya safeer?
"Yaje office miemie"
"to kawae tace sannan tashiga cikin don yin wanka.

08:40 safeer yazo ya dauki shukra inda Mamah ta cika shukra da tsaraba suka rakasu har gurin mota.

"Aunty shukra xan biki miemie ta fada a hnkl yadda bazasuji ba
" To jeki debo kayanki mu tafi "
" Aunty Mamah bazata bari ba sbd skul "
" To kiyi hkr ran friday zansa ya safeer yazo ya tafi dake kimin week end a chan ko.
"Ihu murna tasa ta shige cikin gida da gudu.





" Yau ta kama friday kamar yadda safeer yayi Areef alkawari yaje ya dauko shi bayan sun sha Fama da Ammii wae baza shiba ze takura musu.

Ko da suka shiga cikin gidan shukra da miemie da Aysher suka samu a palour suna hira abinsu.

Dakinsa ya xarce bayan sun gaisa dasu Aysher don watsa ruwa.

" mamaki ne ya cika Aysher ganin shukra ko kallon Safeer batayi ba ballan tana ma ta gaida shi.
" Wai dama har ynx basa zaman lafiya ne? Ta tambaya kanta.


"Ataikace dai su miemie yini sukayi agidan da daddare safeer ya maida su gida.

11:00pm shukra, safeer, Areef na zaune a palour suna kallo, safeer ne ya mike yayi wa Areef sai da safe sannan ya wuce da kinsa.

" Uncle ni a gurinka zan kwana inji Areef ya fada yana bin bayan safeer
" To Areef je Aunty tama wanka kazo mu kwanta.
"To ya ce sannan ya wuce dakin shukra.



" karfe uku dai - dai shukra ta farka sbd wNi axababben ciwan mara, dama tayi yi ko wani month, kuka take tayi tana juyi tun tanayi ita kadai a daki har ta saki ihu wanda ya sa safeer farkawa a gigi ce.

" Da sauri ya karaso dakin shukra inda ya sameta tanata juyi a kasa.
" jikin sa har wani rawa yake yana kokari dakata sai jero mata sannu yakeyi.

Haka dai ya daga ta ya kaita motar sa sannan ya dawo dakinsa daukan key.

"Duk wannan abun da akeyi Areef be saniba baccin sa kawai yake hakan ne ma yasa safeer be taba shiba ya dauki key dinsa ya fice da sauri.


Kai tsaye asibitin Aminu kano ya wuce da ita inda cikin sa a a ka karbeta akayi emergency da ita.


"kaiwa da komowa kawae yake a bakin emergency gumi duk ya jika shi, sai tunani yake azuciyar sa 'wnn wani irin ciwo ne yarinya sai suma takeyi (Don sau uku tana suma a hanya kafin suxo).


" yana cikin wannan tunanin ne wata nurse ta fito take gayamasa an bawa shukra gado takuma bashi list na maganin da ake bukata.

" sai asuba bayan safeer ya dawo daga mosque ne yasamu ganin shukra.
"koda yashiga cikin dakin idonta biyu tana ganishi ta dauke kai tare D rufe ido kamar me bacci.
" ya jikin ki ya tambaya yana xaman abakin gadon.

"Kamar baza tayi magana ba sai kuma chan tace 'Da sauki'.
" ALLAH ya kara sauki to"


"shiru ne ya ratsa dakin kafin safeer ya dauko wa yarsa yayi dialing number'n Aysher.
" Bayan sun gaisa ne yake fadama ta shukra ba lafiya ynx hk ma suna Asibiti.


"Dakin Mamah ta shiga ta gaya mata sannan ta wuce kitchen don hada musu breakfast.

" Kallon sa take tanason masa mgn amma takasa.
"shine ya fahimci hkn a nn ya tamvayeta.
" wani abu kike so "
" Ammii nakeso ka kira min"
"komai bece B yashiga dialing number'n Ammii inda yana shiga yamika mata tare da ficewa a dakin.

" kusan tare Ammii D mamah suka iso.
"Bayan sun gaisa ne Mamah ta yiwa shukra ya jiki.
" Da ladabi ta answer sannan ta gaidasu duka.

"shukra wae meke damunki ne inji Ammii.
" kamar baxata answer ba chan tace 'ciwon mara'
Baki sake Ammii take kallon ta da mamaki wae ciwon mara.
"ita dai tasan in mace na ciwon mara da zaran tayi aure take denawa, likitochi da kansu suke bada shawarar auradda mace mai ciwon mara.

" to meyasa har yanzu shukra take ciwon mara, kardai har ynx ba abinda ya shiga tsakanin yaran nan?

Inko hk ne shukra zata gane kurenta.....






SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/2, 12:45 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA



Dedicated to miemie bie 💋❣


1⃣0⃣



SAFEER ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da kaya, a bakin kofa ya ajiye kayan sannan ya karaso ciki ya durkusa kusa da Mamah suna gaisawa da Ammii cike da ladabi.

"ya me jiki Mamah ta tambaya"
"Da sauki

Please Login or Register in order to submit comment