Reading FARAR HAIHUWA Part1 by Batul Mamman Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi ki bani wuri. To..to..to ta mike ta koma
dakin su ita da Hanan da kanwarsu Zaliha.

Wata yaloluwar katifa ta nufa ta kwanta. A hankali idanunta suka ciko da hawaye.
Ita meyasa bata da Umma? Ina dangin ummanta suke? Hawayen ne suka gangaro sai tari
ya sarke ta. Zaliha ce ta ganta bayan ta dawo daga makaranta. Yaya Dije sannu ta
dafe mata kirji. don idan ta fara tarin numfashinta har neman daukewa yake. Rashin
kudi sosai yasa Babanta ke yawo da ita gidan masu maganin gargajiya, wasu suce
sanyi wasu suce asma. Zaliha ta dago kan dije ta bata ruwa bayan tarin ya lafa. Ta
daga murya Yaya Dije kuka kika yi ko? Tayi saurin girgiza kai tari ne Zaliha. Allah
Yasa da gaske kike, bari naje na dauko mana abinci nasan yunwa kike ji ma.

Haka dokar Sabuwa ta koma abincin Hanan daban, Zaliha da Dije tare ake hada musu.
Tunda Dije ta gama secondary school wadda ba wani abin kirki ta iya ba saboda
rashin kunne kullum sai ta jira Zaliha ta dawo zasu ci. A cewar sabuwa kada dije ta
cinye abincin. Babansu bai taba sanin wannan dokar ba don har yanzu yana so da kula
da lamuran yarsa. Shekararsu goma sha biyar da baro kauyensu suka koma birni da
zama. Takurawar iyayen Munari kan sai an basu Dije yasa Uwale sayar da filayenta
harda gidansu ta matsa masa sai sun tashi indai ba so yake ya kulleta a gidan yari
ba. Tayi mamakin yadda aikin malam bai kama su ba sai dai kuma bata kara jin
duriyar Munari ba tunda tasa Yakubu ya saketa. Aikin gini da noma yake yi a haka
yake ciyar da iyalinsa yake saka su a makarantar gwamnati. Tun tafiyarsu wadda basu
yiwa kowa sallama ba iyayen Munari suka sanar da ita duk abinda ya faru. Tayi kuka
sosai saboda tana matukar son 'yarta kuma ta kara tsanar Yakubu akan guduwa da yayi
da ita. Allah Yasa ma Sadi yana wurinta.

Hanan ta fara karatu a polytechnique ta garin kano tana ji da kyau da gayu. Duk
gidansu babu wanda take so kamar kakarta Uwale saboda yadda take shagwabata tana
kuranta kyaunta. Duk yar yaudarar samarin da take da izinin kakarta take yi. Tana
kwance kan gadon uwale tana chatting Mal Yakubu ya shigo dakin. Wani wuntsulowa
tayi da sauri zat gudu. Hannunta ya rike ya dawo da ita dakin munafuka ina zuwa. Ya
zaka kirata munafuka dan nan ka kiyayeni fa akan Hannan wallahi. Inna kina bata
yarinyar fa. Kalli wayar hannunta abinda take saurin boyewa kenan kada na gani.
Uwale tayi murmushi zancen banza ai kudin dashi na na bata ta siya dashi. Hanan
tace Allah Baba ita ta bani.bari saurin rantsuwa ni tsakanina daku shawara ce. Iya
abinda zanyi miki nayi na tarbiya. Allah Ya shirya.
Ficewa yayi rai a bace ya tafi dakin yaran wurin Dije da Zaliha. Baba sannu da
zuwa...yauwa Zulaihatu. Taba min yayarki nasan bata ji shigowata ba. Tsinkin
tsintsiya Zaliha ta sawa Dijengala a kafa ta mike a firgice. Wayyo Allah...muryarta
duk ta cika gidan. Tana ganin babanta ta matsa kusa dashi. Baba kaga Zaliha
ko...zan zane ta fa. Guje guje suka rinka yi a tsakar gidan yana dariya. Yaran nan
biyu kadai ne suke wanke masa bacin ransa da damuwa. Sune kuma Uwale bata so don
abin mamaki duk farin Sabuwa haka ta haifo Zaliha baka har tafi Dije duhu. Shiyasa
uwale bata shiga sabgarsu kamar babu su a gida.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:12 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰15




Ranka ya dade ga takardun filayen guda uku aka samu a wuri daya. Alh Sulaiman
Hassan ya kalli sakatarensa Modibbo nagode dan fillo. Zanyi magana da managers din
sauran kamfanin sai muyi finalising project din. Modibbo yace hakan yayi ranka ya
dade amma akwai sako daga wurin Hajiya fa. Murmushi yayi alamun yasan sakon Hajiyar
yace nasan cewa tayi ka tabbatar yau na tashi da wuri ko? Shima Modibbo murmushin
yayi ni dai umarni nake bi kuma lokaci ya riga yayi. Wai ni waye ke biyanka ne ni
ko ita? Ai Alhaji da kai da kaya duk mallakar wuya ne. To naji ya fada tare da
mikewa.

A hankali yake tuki don yau drebansa bai zo ba matarsa ta haihu. Karatun Al-Quran
yake ji kira'ar Sheik Khaleel Husary yana bi cikin nutsuwa har ya isa gidansa a
unguwar bompai ta cikin garin kano.

A falo ya tarar da ita ta gama hade rai alamun tana fushi dashi. Mata ne biyu zaune
tare da ita. ko da ya gaisheta da kyar ta amsa masa shima yasan yayi laifi bai
matsa mata ba yayi hanyar bene tace cikin fushi Sulaiman ina zaka je kuma? Umma zan
canja kaya ne na dawo. To kayi sauri yaran kawata ne suka zo gaisheni shine nace su
jira kazo ku gaisa. To kawai yace a ransa kuwa harda dariya...umma kenan ta zama
matchmaker karfi da yaji ita a dole sai yayi aure a wannan shekarar. Shima kullum
yana adduar samun ta gari yasan kuma Allah mai jin rokon bayinSa ne.

Wanka yayi yasa kananan kaya ya sauko. Yana zama Umma ta mike to bari na duba
abinda ake dafawa. Yasan so take ta basu wuri ya ce to kawai. Tana tashi dayar
wadda take ta yi masa kirikiri da ido tace Yayanmu ni sunana Ainau wannan kuma
kanwata ce Bilkisu. Ko kallonsu baiyi ba don basu yi kama da masu kunya ba ya zaro
kudi a aljihunsa ya mika musu ga kudin mota nice meeting you. Sai anjima muje nasa
dreban Umma ya kaiku gida. Ainau ta bata rai ai Hajiya tace mu jira zaka kaimu da
kanka idan ka dawo saboda kaga gidan. Ashe ma doluwa ce yarinyar ya fada a ransa.
Kinga naji ciwo a hannun bari a kaiku. Bani number dinki zan kiraki musamman.
Kanwar tace nifa? Itama karbar tata yayi yana so suyi su fita kafin Umma ta dawo.
Sai da yaga fitar motar daga gate din gidan ya dawo ya zauna. Muryar ummansa yaji
tace Sulaiman ina su Ainaun suke. Ai sun tafi wai sauri suke yi...amma yaron nan
baka da kirki. Wai so kake na mutu banga jika na ba shekarunka talatin da shida
fa...jin ta fara shakar hanci yasan kukan blackmail ne ya tashi. Kiyi hakuri Ummana
na sami mata ina jira mu gama daidaitawa ne. Ta washe baki hakoran makkanta suka
bayyana. Da gaske Sulaiman? Da gaske Umma..to ai da kayi magana da wuri bazan kira
yaran nan ba, dama nima duk basu yi min ba. Yadda tayi maganar yasa shi dariya
sosai.

Modibbo da abokinsa Mal Yakubu suna zaune kofar wani gida da su mal yakubu ke aikin
ginawa yace mutumina Alhajin kamfaninmu ya sayi wasu filaye manya guda uku. Ban dai
san abinda zai gina a wurin ba amma naga so yake ayi ginin da wuri. Zanyi masa
magana akan ka ka samu shiga cikin masu yin aikin. Nagode Modibbo Allah Ya bar
zumunci. Wallahi kudin karatun yaran nan da ciwon Dije sune suke damuna. Kada ka
damu in sha Allah zaka sami wani abin yanzu don Alh Sulaiman akwai kirki. Haka suka
zauna suna ta hira har laasar tayi suka tafi gida tare.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰16




Hannu yaji ya sakalo masa wuya ta baya. Daddy oyoyo...tashi yayi ya daga Ammar sama
yana ta dariya. Umma ta fito ni kun cika min gida da ihu abinda kuka iya kenan.
Dariya suka sake yi mata Ammar yace Daddy dazu mamana tazo kafin ka dawo daga
office. Umma ya kalla tace Ammar je ka daki ka dauko wa daddy tsarabar da tayi
maka. Yana fita tace zuwa tayi ta sanar dani ta sami mijin aure. Ai gara tayi auren
ta dade shekara shida ai ba kwana shida bane. Sulaiman yace Umma Allah Yasa dai ba
fushi kike dani ba akan rashin aurenta. Gyara zama tayi ko kadan duk uzurin da ka
bani na karba. Idan ka kai mata Ammar ranar jumaa sai kaji ko waye mutumin.

Alh Sulaiman Hassan shine da na biyu a wurin Haj Bintu. mahaifinsa babban dan
kasuwa ne kuma yana da kamfanin yin kafet har uku a kasar. Shekarar Sulaiman
ashirin da daya baban nasa ya rasu bayan yasha jinya yayansa Yusuf ya cigaba da
kula da kamfanin baban. A lokacin da yake masters dinsa a fannin aikin banki ,
Yusuf ya rasu sakamakon hatsarin mota da yayi. Ya bar matarsa sakina da ciki wata
biyar. Bayan ta haihu ne Umma tayi ta kokarin hadasu da Sulaiman yaki yarda a
cewarsa bazai dena kallonta a matsayin matar wansa ba. Shekaru shida kenan sai
yanzu ta sami wani zata aura.

Saboda matsin layin daga can baya Sulaiman yayi parking motarsa shi da Modibbo suka
taka da kafa zuwa kofar gidan Mal Yakubu. Kwata ce a kofar gidan dole suka shiga
daga dan zauren waje inda Uwale ke kiwon tumaki. Banda wari da zarni babu abinda ke
tashi a wurin. Sulaiman ya gimtse fuska. Modibbo sarai ya gane warin ke damunsa
yace yallabai kayi hakuri shiyasa nace ka zauna a mota na kira shi.
Ba komai Allah Yasa ya fito yanzu dai.

Wata kyakkyawar yarinya ce ta fito fara tas harda dan karin mai. Cikin yanga take
tafiya. Gaba daya hankalin Alh Sulaiman ya koma kanta. Baba yace yana zuwa ta fada
ba tare da tayi musu sallama ko gaishe su ba. Ciki ta koma tana taunar cingam.

Mal yakubu ya fito ya gaishe da Alh Sulaiman sannan ya gabatar da kansa. Alh
Sulaiman yayi masa bayanin wurin da filayen suke ya kuma bukaci yazo kamfani ya
same shi washegari.

Ihun da suka ji yasa su yin shiru Dijengala ta fito da gudu tana kuka. Murya can
sama tace Baba kaga Mama ta hanani wanka yau ma wai zan karar da ruwa. Kaji yadda
nake tsami kuwa...matsawa tayi gabansa tana daga masa hannuwanta har gashin hammata
Alh Sulaiman yana gani. Kuma fa jinin wata na yazo tun jiya . Subhanallahi Dije
sauke hannun mana ya kama hannunta zai koma cin gidan da ita. Tirjewa tayi Baba
dukana fa zata yi kuma kullum Yaya Hanan tana yi da Zaliha. Duk kunya ta kamashi ya
daga murya don taji abinda yake fada...muje nace zan mata magana. Burinsa kawai su
koma cikin gida. Sai lokacin taga mutane tsaye...lahh baba modibbo sannu da zuwa.
Sai ta rike baki au...duk kunji abinda na fada ko? Wayyo kunya ta dafe kai tare da
komawa cikin gida. Alh Sulaiman kuwa dariya ce ta kwace masa ganin yadda Dije take
baragada a gabansu. Sai dai fa akwai wari dan kare.
Batul Mamman💖
[8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰17



Wani murmushin ya sake yi shi kadai Umma ta jefe shi da pillow din kujera kai ni
dariyar me kake yi kamar kwancen hauka....wata dariyar ya sake yi sannan ya bata
labarin Dijengala kurma. Itama dariyar tayi maimakon ka taimaka mata shine kake
dariya. Ni mubar wannan zancen dai ya sunan yarinyar da kayi min zancenta ne? Ga
mamakinsa sai yaji yace Hanan.

Daren ranar tunaninta ya rinka yi. Tana da kyau mai daukar hankali gashi da gani
tana da tsafta ba kamar Dijengala ba. Wani murmushin ya sake yi da ya tuno yadda
take magana. Daga nan har yayi bacci tunaninsa yana kan Dije yana dariya.

Ranar litinin duk ya kagu modibbo ya iso. Yana zuwa kuwa tambayarsa tayi ko anyiwa
Hanan miji. Modibbo yadan yi turus...Hanan dai yar abokinsa ce amma ko kadan bata
da hali. Ranka ya dade ba ayi mata miji ba a iya sanina. To ka sanar da mahaifinta
idan ya amince zan nemi aurenta. Modibbo ya nuna farincikinsa a fili amma ba don
yadda Dije ta tashi ba sai shirme da shiririta ga lalurar kurumta da ita zai so
Alhajin ya nema.
*******************
Rana duk ta dami Hanan a kofar banki inda take jiran kawarta. Wata mota take ta
kallo, ba karamin kyau tayi mata ba...duk mai motar nan ko ba'a fada ba mai kudi ne
kuma mai kyau. Tayi dan tsaki ita kyau ma bai dameta ba indai akwai kudi. Tana
zaune a wurin wani matashi ya fito ya bude motar. Gaba daya ya tafi da hankaliñta
ta bishi da ido. Kana ganinsa kaga kudi don yawan shige shigenta tana gane mai kudi
tana gane yaron mai kudi. Wannan matashin kam shine da kudin. Tashi tayi ta kade
skirt dinta tayi saurin zuwa gaban motar inda yake shirin rufe kofa tace Alhaji
kwana biyu. Ya dan dago kai a dakile yace ya kin sanni ne? Tayi baya yi hakuri sai
naga kamar wani da na sani ne. Sai kashe murya take tana magana ciki ciki. Ya bata
rai bashi bane to...matsa na rufe kofar. Kafin ta gama matsawa ya bugeta da kofar
ya figi motarsa. Kafin ya bace ta gama haddace numbar motarsa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰18



Kawarta Hajara ce ta fito jaka cike da kudi. Sorry Hanan na barki jira ko? Gaskiya
da mita zan miki amma na fasa. Wani kamu nayi mai kauri. Hajara tace haba a yana
ina? Hanan ta fada mata yadda suka yi. Amma zancen gaskiya kawata yayi min akwai
kudi. Ji nayi kamar kudin jikinsa yana kirana. Shegiya uwar son kudi nasan wannan
mai cangala kafar zaki kaiwa. Allah sarki innata tafi kowa kaunata. Ni ba wannan ba
Hajara ki rakani gidan Babba mana. Akan mutumin nan sai anyi aiki.

Dayake halinsu yazo daya shiyasa kullum a makaranta tare suke. Hajara da Hanan suka
wuce gidan Babba wani malamin tsibbu. Don yanzu bin malamai harda yan mata. Allah
Ya kara shirya mu. Bayan dukkan bayani Babba yace Hanan kin san sunansa? A'a amma
ga numbar motarsa, ka taba yi min aiki akan wannan wawan malamin da numbar waya ai.
Ba damuwa Hanan ga wanan turaren ki saka kan garwashi sai ki rubuta numbar motar a
takaddu goma ki rinka dorawa akan wutar har su cinye duka. Sai ki lazumci zuwa
wurin da kuka hadu na kwana goma. Idan baki ganshi ba to motar ba tasa bace. Godiya
tayi sosai tace idan ciniki ya fada zaka ganni.

Bayan kwana uku Modibbo ya sanar da Mal Yakubu bukatar Alh Sulaiman. Murnarsa
bazata misaltu ba ya sanar da Uwale. Burinshi dama tayi aure ya gaji da sintirin da
samari ke yi masa a kofar gida. Sabuwa ma tayi murna har ta sanar da babarta Zulai.
Cikin dare ta bawa mijinta shawarar ya aurar da Dijengala. Banda abinki Sabuwa ina
Dije take da saurayi. Tayi wani murmushin keta...wani kurma ne dan uwan Zainab
makociyarmu. Tace a kauyensu yake Kura. Hade rai yayi dakata malama ni 'yata bata
gama kurmancewa ba kinji ko. Ki rike abinki rabonta na tafe. Kuma dama ina son yi
miki magana Allah ranar da kika sake hanata ruwan wanka zaku yini a gidan nan ba
ruwa. Yar hirar tuni ta watse ya juya yayi kwanciyarsa.

Gari na wayewa cike da zumudi Uwale ta sanar da Hanan zancen Sulaiman. Ta wani
harareta jiya tasha uban hayaki akan wani yau a kawo mata zancen wani Alh Sulaiman.
Kinga Inna ki bar maganar nan ina da wani. Haba Hannan mutumin nan fa kudi gareshi
sosai. Mafarkina a kanki ne zai tabbata. Hanan ta wuce zata shiga wanka. Kinga Inna
ki bar maganar nan ku bashi Dijengala ko Zaliha. Auzubillah uwale ta fada tana
tofar da yawu. Dije ai ai musaki irinta. Yarinya ga baki ga muni.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰19



Hanan tayi sati daya tana zuwa bankin da suka je da Hajara tun safe har sai sun
tashi amma mai motar bai dawo ba. Rai a bace ta koma gida duk ta kusa gama kashe
kudin hannunta a hawa motar zuwa banki.

Dakinsu ta shiga zata cire kayanta tayi wanka Dije ta shigo tana waka da karfi.
Hakan ya kara batawa Hanan rai ke rufa min baki banza kawai. Ta fice tana tsaki.
Babanta ta gani a kofar kitchen yana magana da Sabuwa...yauwa zo hanan dama
zancenki muke yi. Ta turo baki gaba ta karasa gabansa ta tsaya. Nasan an fada miki
maganar Alh Sulaiman ko. Wanda kuke aikin gini dashi baba? Eh ya amsa mata. A zuci
tace tabdi magini zan aura? Allah Ya kiyaye, itama Mama tsautsayi ya kawota gidan
nan. Mal yakubu yace dama tafiya ce ta kamashi amma ya dawo zai zo yau da daddare
inji modibbo. Uhmm tace ta wuce bandaki. Wallahi bazai sameta a gida ba ma. Me
zatayi da talaka.

Haj Bintu tana ta kallon yadda Sulaiman ke shirin fita daga dawowarsa ko abinci bai
ci ba. Ina zaka ne don nasan wannan shigar bata zaman gida bace. Hular hannunsa ya
gyara Umma gidansu Hanan zani amma da Ammar zan tafi saboda zan kaishi aski. Wato
ka dawo zaka nuna min ban iya kular maka da danka ba ko? Yana dariya ya bata
hakuri. To ina tsarabarta ko haka zaka tafi? Mata fa sai da ihsani. Zan biya na
siyo wani abun a hanya. Hannun Ammar ya kama suka tafi yana ta yi masa hira.

Hanan ta rasa yadda zata yi ta fice daga gidansu tunda babanta yaki fita tun safe.
In ba rashin aikin yi ba kakkarfan mutum kamarsa ya zauna a gida wuni guda....tayi
tsaki. Zaliha tace lafiya. Hararar ta tayi ban sani ba ta bata amsa tare da fita
daga dakin. Mal Yakubu na fita zuwa masallaci sallar magriba ta fice ba tare da
sanin kowa ba.

Alh Sulaiman yana dosar gidan ya fara jin warin kwatar kofar gidan. Shifa harkar
warin nan baya kaunarta. Ya rasa dan aike gashi bashi da numbar wayar kowa a
gidan.Ammar ya tura ciki ya sanar da zuwansa. Yaro ya shiga kai tsaye dakin da ya
hango haske ya nufa. Uwale ce da Sabuwa suke kallo yace salamu alaikum wai daddy na
yace ya zo. Sabuwa ta kalli dan kyakkyawan yaron kai kuma daga ina wa ya turo ka?
Mal Yakubu ya shigo yace dan Alh Sulaiman ne mai son Hanan. Kirata Sabuwa yana
jirantaa soro.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:15 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰20




Sau uku ta kira taji shiru. A zaune ta tarar da Dije tana gyangyadi kafin Zaliha ta
dauko musu tuwo. Shureta tayi da kafa ke kurma tashi...a firgice ta tashi tace mama
me ya faru? Ta dungure mata kai tare da rage murya ubanki ne ya faru. Dije ta bata
fuska tana nuna kirjinta ubana? Ubana?? Sai hawaye...ke yi min shiru munafuka ana
magana sai kiyi ta kallon bakin mutane ina Hanan? Dije tace ta fita tun dazu. Kai
yarinyar nan zata ja min masifa ta koma daki ta fadaw Mal yakubu.

Ransa yayi matukar baci gashi yar wayar tasa ma ba kudi bare ya kirata. Uwale tace
yarinyar nan neman tona min asiri take ga wayata kirata. A kashe suka ji wayar.
Bari na fada masa kawai ,ita kuma yau tamu ce ni da ita.

Jin Zaliha bata dawo daga dauko musu tuwo ba Dijengala ta duba kitchen bata ganta
ba ga yunwa yana cinta. Ita kuwa Zaliha cikinta ne ya kada ta tafi bandaki. Wata
tsohuwar naira ashirin ta dauko a kasan akwatinta ta saci jiki zata je siyan wainar
fulawa a gidan Zainab makociyarsu. Tana saka kafarta a soron aka dauke wuta, saboda
duhu hannunta take mikawa kamar makauniya tana neman hanyar fita, wani mulmulallen
abu mai dan gashi gashi taji ta shafa ta tabbatar ba kan daya daga tumakin Sabuwa
bane. Ammar data tabawa kai ihu ya saka. Daddy kamani naji an taba min kai.
Sulaiman yace ina zuwa Ammar wayata nake nema. Dije sake taba kan tayi don ta
tabbatar da abinda ta taba, gashi tana jin kamar maganganu amma ta kasa gane me ake
fada. Ihu tasa iya karfinta wayyo Allah baba nayi gamo. Sulaiman tuni ya gano
muryar yar kazamar yarinyar nan yace ke rufa mana baki yana neman hannun Ammar su
fita. Ta soma kuka Al'Quran naira ashirin ce a hannuna waina fulawa zan siyo a
gidan Zainab yunwa nake ji. Gashi don Allah kada ku mayar dani kaza ko doya. Ba
shiri sulaiman ya soma dariya...hannun dansa ya kama. Yana jin yadda Dijengala take
tsalle da ihu. Mal Yakubu ne ya iso soron da yar fitila. Shima bai kula da su
Sulaiman ba don ya zata sun tafi. Dije dena ihu nine...tana ganinsa tayi saurin
matsawa kusa dashi tana magana da karfi, baba aljanu ne suke son bude min ido,
dansu suka turo min shegu. Kul kike zagi dije...shima baba zuciyarsa ta kusa bugawa
daya ji ance daddy mu tafi. Sai a hankali ya gane Alh Sulaiman ne da dansa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰21



Da kyar ya iya tsayar da dariyarsa yace Mal 'yar nan taka tana da abin dariya. Ai
nima na tsorata don nayi tunanin kun tafi. Ammar ya nuna takalminsa ne ya kwance na
tsaya daure masa sai aka dauke wutar kuma ina tunanin wayata tana mota. Sake
sallama suka yi kafin Sulaiman ya gama fita yaji mal yakubu yana tambayarta ina
zata.. wallahi baba yunwa ce kuma zaliha bata kawo abincin ba, dama wainar fulawa
zan siyo ta ashirin. Dariya yayi haba Dije wainar ashirin ai sai da kiyi kuskurar
baki da ita. Me kace baba? Banji ba. Muje na baki nawa abincin kici a daki kada
sabuwa ta gani. Daddy mu tafi mana wari nan. Sai a lokacin sulaiman ya dawo
hankalinsa yaja hannun Ammar suka fita bakin layin inda yayi parking motarsa.
****************
Ashir ya rasa abinda ke masa dadi. Tun washegarin zuwansa banki zuciyarsa ke masa
radadi ya rasa dalili. Ji yake kamar ya koma bankin ya nemi yarinyar da ta yi masa
magana amma shi ko fuskarta ma bazai iya tunawa ba don bai kalleta da kyau ba.
Wata biyu ya rage bikinsa amma yan kwanakin nan baya son ko jin sunan matar da zai
aura. Dama dai auren baya gabansa don shine na uku ma. ba ya dadewa da mata suke
rabuwa, hakan na damun yan uwansa shiyasa wannan karon babansa ya yanke shawarar
hada shi da yar kaninsa da mijinta ya rasu shekaru shida da suka wuce, wato sakina
mahaifiyar Ammar. Gidansu Ashir suna da rufin asiri dai dai gwarwado. Lokacin da ya
fara aikin kwangila ga aikin office shine kudi suka zauna masa sosai. Kasa nutsuwa
yayi karshe ya yanke shawarar zuwa bankin a daren bayan yayi magriba a kofar
gidansu.

Hanan na sauka daga adaidaita sahu suka hada ido da mutumin da take ta nema.
Gabansa ne ya fadi yana ganinta. Banda kyawunta wani yanayi ya shiga mai wutar
fassara. Idan bai auri yarinyar nan ba rayuwarsa tana cikin matsala. Har wani gumi
ke keto masa. Karasawa yayi inda take ba tare da yayi mata magana ba ya mikawa dan
sahu dubu daya yace mata zo mu karasa bakin motata. Ba musu ta bishi...lallai aikin
Babba yayi kyau.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰22



Bude mata yayi ta zauna a seat din gaba. Shima yana zama yace me ya fito dake a
daren nan? Ta rausayar da kai tana kare masa kallo, ga kyau ga kudi.ready made
kenan..kai ya kamata nayiwa wannan tambayar. Hmm ina jin abinda ya fito dani ne ya
fito dake. Me kenan ta tambayeshi ciki da jindadi. Yana kallonta yace tunaninki
mana. Duk kin hanani sakat...ina tunanin kema hakan take a wurinki. Ni fa kudi nazo
dauka ba wurinka nazo ba. To fitar min daga mota indai hakane. Tsoron kada garin
jan aji ta rasa shi yasa tayi saurin cewa wasa nake maka. Nima ka hanani nutsuwa
tun ranar da muka hadu. Yaji dadin amsarta...ni sunana Ashir Sani. Ina aiki a NNPC
sannan ina harkar kwangila sosai. A takaice dai i am a very busy man. Ina ruwanta
da yawan aikinsa indai akwai kudi. Ta fada masa nata sunan daga nan hira suka rinka
yi kamar sun dade da juna. Ganin tara ta wuce yace muje na kaiki gida.

Alh Sulaiman na fitowa daga layin gidansu Hanan ya hangota cikin motar wani. Ina
taje a daren nan ya tambayi kansa. Motar na kara matsowa yaga kamar yasan mai tukin
amma ya kasa tuna ko waye. Bai kawo komai a ransa ba ya tafi gida.

Cikin sati biyu soyayya ta kullu sosai tsakanin Ashir da Hanan. Ta sanar da uwale
da sabuwa komai game dashi. Tuni ta sace zukatansu bare da suka ga irin hidimar da
yake mata. Mal Yakubu dai ya nuna rashin amincewarsa. A cewarsa bazasu mayar dashi
karamin mutum ba. Ya riga ya amsawa Alh Sulaiman har yace zai turo iyayensa don
baya son a dauki lokaci. Uwale tace to dan nema mai toshe kofar arziki. Shi
Sulaimanun nawa ya taba bata tunda yazo. Inna ki dena koyawa yarinyar nan son kudi,
zuwansa uku fa kullum ba ta gida. Yau idan ta dawo sai naci mutumcinta. Shegen yawo
kamar kaza. Uwale ta sha kunu bana son irin haka fa, ka manta tana karatu ne? Ni
dai na gama magana yarinya Ashiru zata aura. Jiya da ya shigo dubu goma ya bani. Ni
Uwale da dubu goma tawa ta kaina. Ka sallami wannan abokin ginin naka don bazan
bashi jikata ba.
Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰23



Abokin gini kuma Inna? Ni da na fada miki gini zanyi masa yana da kamfani. Sabuwa
da tun farko bata yi magana ba tace haba Malam wai kai a dole sai ka nuna baka son
yarinyar nan ne? Ya arziki na binmu kana sa kafa kana shurewa. Babu wanda ya isa
yayi mata dole. Wanda take so zata aura. Idan kuma dole ne sai ks bashi Dijengala
ai itama mace ce. Inna Uwale ta tuntsire da dariya...wa yaga barahaza. Ba yadda ya
iya dole ya kyalesu idan suka hade masa kai don baya iya musu da Inna Uwale. A
zuciyarsa ya gama yanke shawarar sanar da Modibbo ya bawa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment