Reading FARAR HAIHUWA Part1 by Batul Mamman Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng FARAR HAIHUWA💰1

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching
this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction,
non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with
thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin
bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin,
soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu
a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.




Bismillahir Rahmanir Rahim



Kai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin
rashin sanin halin da kanwarta take ciki. Inna Uwale dake zaune a kan tabarma ta
daga hannu sama idanunta duk sun ciko da hawaye tace Ya Allah ka bani farin jika ko
wanne iri ne. Ya Allah fari kyakkyawa kamar ni. Zulai aminiyarta tace amin amin
Uwale ai ranar sai munyi sadaka. Tani dake kai kawo da sauran matan da 'yan uwansu
ke cikin dakin haihuwar suka zuba mata ido. Ta kuwa cigaba da adduar farin jika
kamar yadda ta saba. Cikin kunar rai Tani tace amma Uwale baki da mutumci ko kadan.
Kanwar tawa tana ciki rai a hannun Allah kina wani fatan a haifa miki farin jika.
Farin jikan yaci.....bullowar mal Yakubu yasa tayi shiru ta share hawayen bakin
cikin da ke shirin sauko mata. Ita kuwa Inna Uwale tace ashe baki da kunya Tani?
Ban girmi uwarki Baraatu ba? Ita dai Tani shiru tayi don tana gani mutumcin Mal
Yakubu mijin kanwarta. Yayi gumi sharkaf saboda tafiyar da yayi zuwa asibitin a
kafa bayan dan Tani din ya bishi gona ya sanar dashi halin da ake ciki. Ramlah da
Sadi suna ganinsa suka mike suna murna suka tsaya a gabansa. Daukar Sadi yayi itama
Ramlah tasa kuka sai an dauketa. Tana kukan bata sani ba ta taka kafar Inna Uwale.
Wata kara ta saki kafin ta hankade ta ta fadi kasa. Matsa can gun yar uwarki,
shegiya baka mummuna. Mal Yakubu yace haba inna a nan din ma. Tani ta dauke ta tana
goge mata bakinta da yasha kasa. Yarinya sai kuka take. Yo ba kaine duk ka cuceni
ba dan nan. Mata aka sami abin kallo jin yadda Uwale ta bude murya. Ta cigaba dube
ni nan ga fari ga kyau haka Allah Yayi ni tun kuruciya don ma girma yazo. Ta daga
siririyar kafarta ta hagu wadda shan inna ya shanye tace da wannan Allah Ya ragewa
aya zakinta duk kyan dire na ban sami mijin arziki ba sai ubanka. Allah dai Ya
jikansa. Babu irin adduar da banyi ba da cikin ka don ka fini sanin baki ne. Allah
Ya taimake ni na haifo ka fari tas ga kyau. Sai hawaye shar suka sauko mata ya
durkusa kasa don Allah Inna kiyi shiru. Sauran matan dake wurin suna ta kallo an
sami labarin kaiwa gida yau. Yaron nan da yake mai bakin kashi ne ya rasa wadda zai
aura sai yar maiduguri. Wallahi kunga wannan yayar tata ta nuna Tani har ta fita
haske. Kalarta fa kamar dauda yadda dai kuka ga 'ya'yan nan. Ba yadda banyi ba har
da kwanciya a asibiti duk don a fasa auren yaki jin maganata. Ga haihuwar balai duk
shekara. Yanzu wannan cakurkurar, ta nuna Ramlah zaayiwa kani na biyu. To ni
mijina ba arziki har ya mutu shima dan babu. Ni kuwa kafin na mutu sai naje makka
da kudin jika ko na mijin jika. Haka kawai yadda nake da kyan nan bazan bar baya
bakikkirin ba. Mal Yakubu ya share hawayen idanunsa. Inda sabo ya saba da halin
innarsa amma irin wannan a cikin mutane ta gama zubar masa da mutumci.

Goron bakinta ta furzar tace wallahi indai ta haifi fari ko fara nayi alqawarin yi
mata wankan jego da hannuna. Ga mutane suna min shaida. Ni ban tsani Munari ba
harkar bakar fata ahalin tsiya da talauci ne bana so. Tana gama magana wata nurse
ta fito tace ina wadanda suka kawo Maimunatu Ado? Mal Yakubu yayi saurin matsowa
gaba. Inna uwale ma ta cangalo kafa tace Nas fada min me aka samu. Fari ne? Ko
kallonta nurse din bata yi ba tace masa ta sauka lafiya za'a fito da ita zuwa dakin
hutu. Uwale tace tana zaro manyan idanunta ke yar nan karki min rashin kunya, ya
ina tambayarki me aka samu zaki min banza. Ki fada min gaskiya fari ne ko baki? Don
wadan can yaran ko irin farin nan na jarirai wallahi baa haifesu dashi ba. Nurse ta
kalli mal Yakubu tace masa namiji ne tayi gaba abinta.

Zulai kawar uwale ta kama hanci ta rangada guda. Uwale ta kuwa make ta, to uwar
kinibibi ai baki ga kalar dan ba zaki cika mana kunne.




Batul Mamman💖
[8/22, 2:50 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰3



Mal Yakubu ya fito da dan kudi daga aljihunsa ya nuna mata. Kinga na ajiye saboda
siyan rago amma tunda haka Allah Ya qaddara mana sai ki fada min abinda kike so na
saya miki. Tasan duk don ya kwantar mata da hankali ne saboda abinda inna Uwale
tayi mata. Tace haba baban Ramlah ka bari muje gida mana. Ya girgiza kai kinsan
Allah maimunatu bana son Yaya Salihu yaji zancen nan. Kinga lokacin haihuwar Sadi
da inna ta hana a yanka masa rago cewa yayi na sake ki ba dole bane auren.
Maimunatu bazan iya rayuwa da wata mace ba bayan ki. Don girman Allah kada ki bari
a raba mu. Murmushi tayi bata manta yadda ya rinka rokon yayanta ba har saida iyaye
suka shiga maganar. Tace ni da kai Malam Yakubu mutu ka raba. Dariya yayi sosai
sannan ya fita neman taxi da zata kai su gida.

A tsakar gida Inna uwale da zulai suka zauna tana ta bambami tun a hanya. Ni munari
zata cuta? Ni uwale wallahi sai anyi min farar haihuwa a gidan nan. Sai naga jika
mai kyau da daukar hankali zulai, sai jikana mace ko namiji yayi kudi. Ni banda
abin namiji ma ina tsiya ina bakar fata. Munari fa banda hakora ni ban taba ganin
wani abu mai haske a jikinta ba. Zulai dai sai bada baki take don tana samu a wurin
aminiyar tata. Bayan sunci abinci Uwale tace ke ni a ina zaki samo min farar mace
bazawara mai 'ya'ya ne.? Zulai ta ware ido farar bazawara mai 'ya'ya fa kika ce
uwale. Eh saboda su hadu da dannan su haifi farare. Ko wacce iri ce indai fara ce
ina so. Don ma duka yaranki sunyi aure ne ai da ko Sabuwa ya aura dama ita naso
masa tuntuni. Zulai tace to zan duba Uwale gashi kinga Sabuwan ma suna ta fada da
mijin gashi haihuwarta biyu. Dan karen kwadayi gare da zulai duk talaucin gidan
Uwale sun fita arziki nesa ba kusa ba ga rashin abinci. Uwale tace ki barta a
gidanta a samo wata saboda idan an kashe auren sai tayi idda fa. Ni kuwa so nake
nan da sati biyu ma amarya ta tare. Zulai tace to bari na tafi kinsan da zafi zafi
ake dukan karfe.

Gidan Sabuwa ta nufa ta tarar da ita da mijin suna fada saboda babu abinci a gidan
ga yaranta suna jin yunwa. Zulai ta zakalkale kamar ba suruka ba yana ta basu
hakuri suna zaginsa. Karshe zulai tace kaga Inuwa ka sakar min 'yata yanzu wallahi
ko in hadaka da 'yan sanda. Yaro mara kunya haka ko yau ka saketa zata sami mijin
aure. Ai farar mace kadara ce. Idan kaki kuma wallahi sharri zan kulla maka wanda
zaisa ka raina kanka. Yace haba Gwaggo meyayi zafi haka? Ni bazan saketa ba. Sabuwa
tace Gwaggo ban fa gaji da auren ba kawai don babu abinci sai kice ya sake ni. Ta
zumburo baki. Zulai ta make bakin banza zan miki gata kina min fitsara. Zulai ta ja
hannunta suka shiga daki ta fada mata hadin da take son yi. Kinga idan kika haifi
farin da uwale ke jarabar so wallahi sai yadda muka yi da ita. Kina kallo dai yadda
kike wahala nan ga fararen 'ya'yan shegen mijinki baya gani. Sabuwa ta bata rai
Gwaggo nifa ina son sa gaskiya. zulai ta saki wata ashariya Sabuwa zan miki rashin
mutumci fa. Bar ganin ni na haifeki bani da kyau a harkar samu. Ki tada balli a
daren yau ya sallameki kawai.


Batul Mamman💖
[8/22, 2:51 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰2



Da dafa bango Munari ta fito daga dakin nurse na biye da ita da jaririn. Tani ta
gyara goyonta ta mika hannu zata karbi dan Uwale tayi saurin shigewa gabanta tace
bani nan. Ni na haifi ubansa. Tana bude zani ta kwala ihu ta mikawa zulai dan ta
kai goshinta kasa tayi sujjada. Allah nagode maka...ta kalli surukarta munari kin
kwaci kanki wallahi. Ke dai Allah Yayi miki albarka. Da kanta ta rike Munari suka
karasa dakin aka bata gado. Tani da mijinta suna ta yi mata sannu. Inna uwale ta
sake karbar dan tana ta washe baki tace jamaa kunga abin arziki ko. Yarinya mai son
gamawa da duniya lafiya kenan. Ashe tumatir da su mangwaron dana rinka siya miki
yau kinga ranarsu ko. Ashe banyi asarar kudina ba. Zulai ai na fada miki duk miyar
kadi ko harkar daddawa sai da na hanata gashi kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu.
Kiri kiri ta hana kowa daukarsa saboda tsabar murna. Zaninta taji zai kwance ta
mikawa Zulai dan ba don taso ba tana magana. Ai sunan babana zaa saka maka yaro.
Nima a nan na gado farin da kyau har kaima ka dandala. Zulai ta dan jujjuya yaron a
firgice Uwale tace ya haka ne? So kike ya fadi? Zulai tace a'a fa Uwale gani nayi
kamar baya motsi. Kinga fa ko kuka baiyi ba. Allah tsine mai karya ta fada tare da
karbe dan. Ai kuwa abinda zulai ta fada gaskiya ne. Uwale ta juya shi shiru ba
motsi. Yaro ga shi fari kato ga kyau amma bai zo da rai ba. Da cangala kafar uwale
ta fita kiran nurse kuzo ku daba min dannan na shiga uku na ni Hadiza ina zan sa
kaina. Nurse tazo tace a'a maimunatu baki fada musu yaron bashi da rai bane? Hawaye
ne ya sauko mata tace yanzu zan fada. Tani ta zauna gefen gadon ta rungumeta. Yi
hakuri Munari Allah Yasa mai ceton mu ne Ya yi masa rahma. Mal Yakubu ya ajiye
Sadi ya karbe yaron daga hannun Uwale ya kare masa kallo sannan ya rufe shi sosai
da zanin. Uwale cikin kuka tace yanzu mai kyan ne ya mutu? To wallahi kasa a ranka
Yakubu kamar kayi aure ka gama. Kan uba ni zaki yiwa haka munari? Ki haifi bakake
digirgir farin kuma ya koma. Yar purse dinta ta dauka tace Zulai zo mu tafi gida.
Daga bakin kofa tace tsakanin na dake munari Allah Ya isa, muguwa mai bakar aniya.

Suna fita Tani tace gaskiya baban Ramlah abinda Inna tayiwa Munari bata kyauta ba.
Wannan wane irin rashin imani ne. Mace ta rasa danta a rinka binta da bakaken
maganganu. Wallahi sai na fadawa Yaya Salihu ai ba daga sama ta fado ba tana da
dangi. Munari tace Yaya Tani kiyi hakuri don Allah. Ya zaki bani hakuri bayan ke
aka batawa Munari... mal Yakubu ya rinka bata hakuri. Yaya Salihu mutumin kirki ne
amma akan yan uwansa bashi da kyau duk da kasancewar ba uwa daya suke ba amma
iyayensu na zaman lafiya. Jafaru ta kira danta mai kimanin shekaru takwas. Yana
shigowa yace Umma Munari sannu. Ta dan murmushi yauwa dan albarka. Tani ta goya
masa Sadi ta rike hannun Ramlah. Bari mu tafi munari yaran nan basu ci abinci ba na
taho dasu. Mal Yakubu ya kara bata hakuri. Yanzu zamu taho muma zan nemo dan tasi
ne saboda jikinta.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:00 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰4



Sabuwa duk abin duniya ya isheta saboda yadda Zulai ta rinka yi mata fada. Tana
kwance kan katifarta zuciyarta tana mata saka da warwara. Inuwa ne ya shigo dakin
ya nemi kwanciya kusa da ita. Wani tsami ne ya daki hancinta ta mike cikin fada.
Don wulakanci banda rashin abinci a gidanka kullum sai ka kwanta min kana wari? Don
Allah ni ka tashi jiki sai tsami kamar kayi wanka da kwata. Ya tashi ya kai mata
duka ta rike hannun sannan ta kwada masa wani kwantareren takalmi a ka. Cikin
karaji ya biyota waje suna ta fada sai ta tuna hudubar zulai. Nan da nan ta fara
zaginsa tana cewa ya saketa sanin cewa yana da saurin fushi. In sake ki ko Sabuwa?
Ni kike cewa na sake ki ko? Ta eh in dai ka haifu cikin uwa da uba. Ransa ya kara
baci har kin manta sakin da nayi miki kwanaki Zulai ta rinka hadani da Allah na
mayar dake ko? Ai da kenan Inuwa yanzu kuwa na gaji bazan zauna yunwa ta kashe min
'ya'ya ba. Yayi dariya makota duk sun saba jinsu kije Sabuwa na sake ki saki daya
amma wannan karon kada kuzo biko don wata zan nema. Kuma ki tafi ke kadai don a nan
kika sami yaran ba dasu kika zo ba. Ita kalmar sakin kawai taji tasa kuka wallahi
inuwa wasa nake don girman Allah ka mayar dani kafin kowa ma yaji. A zuciyarta
fatan ta daya ya mayar da ita. Ina zata idan ta bar gidansa? Gwaggonta da kyar take
ciyar da kanta gashi sauran yayyenta duk sunyi aure. Me ya kaita ma yarda da
shawarar gwaggo. A wurin girki ta kwana washegari yayo fatali da ita da kayanta.

Cikin kuka ta karasa gida. Gwaggo Zulai na ganinta da kaya da kumburarriyar fuska
ta tashi cikin sauri. Ya sake ki ko Sabuwa? Ai dadina dake jin magana. Sabuwa ta
turo baki ta zauna kan tabarma yanzu Gwaggo baki damu da dukan dana sha ba sai saki
ko. To ya sakeni amma wallahi idan baki yi min tanadi mai kyau ba sai na jawo miki
magana a unguwar nan. Zulai ta rike baki lallai yar nan baki da kunya. To ki
kwantar da hankalinki Yakubu zan tabbatar kin aura.

Tani duk ta zayyanawa iyayen su abinda Uwale tayi wa Munari. Babar su Tani Inno
tace to ai inda sabo ta saba sai tayi hakuri. Shi kuma yaron Allah Ya jikan shi.
Inna Ladi kishiyarta babar su Salihu tace Allah Ya shiryeki Jummai. A fada miki
abinda tayiwa auta shine zaki wani tabe baki. Allah Ya jikan Malam amma da yana nan
bazai lamunci wannan abin ba. Bari Yayan ku ya dawo daga birni Tani da kanshi zashi
gidan. Inno tace haba Yaya don Allah kada ma ya sani. Yanzu sai kiji yana cewa a
sako masa kanwarsa. Inna Ladi tace to tashi muje gidan. Inno tace ni ba zani ba
Yaya rigima ce bana so. Inna Ladi ta sabi mayafi suka fita ita da Tani bayan ta
ajiye yaran wurin Inno.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:00 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰5



A tsakar gida suka tarar da Munari tana iza wuta ga hayaki saboda yanayin damina
icen duk ya jike. Inna Ladi tayi saurin zuwa wurin ta karba. Da kyar Munari ta iya
durkusawa ta gaisheta. Inna Ladi tace haba mike...ina kike Uwale fito Allah Ya tona
asirin ki. Yanzu yar ta haihu jiya, haihuwar ma mai ciwo tunda ba dan amma don
tsabar wulakanci da kanta zata dora ruwan wanka da wannan icen haka? Uwale ta
cangalo kafa daga daki ta fito. Idan kun damu da ita sai ku dora mata. Inna ladi
tace tafiya muka yi jaje gidan kanin babanta garin kwari shiyasa tani bata same mu
a gida ba . Dama tace jiyan ma ita ta dora ruwan. Haba Uwale rashin imanin naki har
ya kai nan. Uwale tayi wani juyi ita ga mai kyau...ta tafa hannuwa yafi nan Ladi.
Ki tambayeta abinda tayi min. Dan farin ne fa ya mutu sai wadan can gawayin kullum
su nake gani a gidan nan. Sannan ace bazanyi fada ba. Inna Ladi tace Munari dauko
gyalenki wallahi na gaji da wannan diban albarka. Idan yayanki ya dawo sai ayita ra
kare. Tana gama magana Mal Yakubu ya shigo da dan guntun ragonsa kafi zuru. Jin
abinda ake fada ya karasa gaban matarsa. Munari don Allah kada ki tafi. Inna Ladi
ki rufa min asiri kada ku raba ni da ita. Hawaye ne taf a cikin idonsa Uwale na
gani tace kwarankwatsa ka bari hawayen nan suka fito gaban surukarka sai na daga
maka nono. Da kaji anyi zancen saki sai kuka kamar ka auri hurul...hurul me
ma? .oho matan aljannah dai nake. To ka zabi daya ko ka sake tan ko kuma nan da
sati biyu ka auri duk wadda na zaba maka. Da hanzari yace zanyi auren inna. Ya koma
kallon Munari koma daki in dafa miki ruwan kinji. Kinga rago can na siyo zan gasa
miki. Sosai Inna Ladi taji tausayinsa amma sai ta dake ni dai tafiya zanyi da ita
mun gaji. Uwale tayi tsaki aikin banza kin saki baki kishiyar uwa zata kashe miki
aure kin zata sonki take. Makirci ne kawai irin namu na mata. Munari sai a lokacin
tayi magana.. Inna ki dena fadin abinda kika ga dama kan Innarmu don akanta wallahi
zan....zaki me??? Kaji ko dan nan matarka zata zageni. Inna Ladi tace Tani dora
ruwan wankan ko sake kallon Uwale bata yi ba taja hannun Munari suka koma daki.

Bayan kwana hudu da haihuwar munari Uwale na zaune karkashin bishiya tana shan fura
Zulai ta shigo. Tana ganin furar yawunta ya tsinke. Ita kuwa uwale bata san tana yi
ba kuma bata yi mata tayi ba. Can ta lura da kallon da Ramlah ke yi mata. Ta ja
tsaki shegiya mayya duk ta kafa min ido zo ki karba. Yarinya ta taso daga wurin
wasanta tazo gaban uwale. Dan yatsa ta tsoma cikin furar ta dangwala mata a harshe.
Ramlah ta lashe tas ta koma wasa. Zulai dai abin duniya ya isheta sai ta fara
tunanin abubuwan tausayi da suka sameta kamar rashin abinci da rashin tayin fura
daga kawarta. Nan da nan sai ga hawaye Uwale ta tande baki tace lafiya zulai. Uhmm
ina fa lafiya Uwale. Ina ta faman nema miki yarinyar da Yakubu zai aura jiya da
daddare sai ga Sabuwa. Uwale tace fara gaya min zancen yarinyar kafin muyi zancen
sabuwan. Zulai ta sha kunu Uwale baki da kara fa. Aurenta fa ya mutu. Ajiye ludayin
tayi eyye kika ce me? Nace aurenta ya mutu. Ashe wata biyar kenan da mijin ua
saketa bata fada ba ta zauna gidan tana son ya mayar da ita gashi har iddah ta
kare. Jiya yayi mata korar kare. Sai wasu hawayen ke zubuwa daga idon Zulai ganin
kudaje na bin kokon furar tasan sarai uwale na gani zata zubar da ita gaba daya.
Uwale tace to ai ki bar binciken haka tunda har ta gama iddah kuma na tuna duk
yaranta farare ne. Ki bar komai a hannuna ranar asabar zata tare a gidan wannan
alqawari ne. Zulai sai murna , uwale tace ga fura ki sha. Kafin ta rufe baki Zulai
ta janye kokon ta kafa kai. Mayunwaciya Uwale ta fada a sarari.

Tana zuwa gida ta sanar da Sabuwa yadda suka yi. Ni dai na fada musu kin gama iddah
idan ba haka nayi ba kinsan uwale da rashin hakuri kamar zawo sai ta bashi wata.
Sabuwa ta hadiyi yawo da kyar tace Gwaggo ina jin ciki gareni fa wata kusan biyu.
Muhuci zulai ta kwala mata a ka. Baki da aiki sai ciki ne duk yunwar gidan inuwa.
To bari kiji. Ranar asabar zaa daura aurenku sai kiyi shiru da bakinki. Idan kika
haihu sai muce bakwaini[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:02 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰6



Sabuwa ta ware idanu kai Gwaggo ai kinga auren babu iddah ma ba kyau ko? Zulai ta
banza rufe min baki. Inji uban wa aka ce ba kyau. Aure kan aure ne ba kyau kuma dai
ba shi zakiyi ba tunda ya sake ki. To cikin fa? Shi ciki ai ba matsala kinsan Uwale
babu abinda ba zatayi ba akan farin jika. To nasan tana da gonaki biyu na gadonta
kinga ko ita muka samu mun huta. Sabuwa dai bata gamsu ba tace Gwaggo zunubin fa.
Ai dan zai zama shege...kul kika kira shi shege da ubansa fa. Ina fata bai san da
cikin ba? Eh bai sani ba. Zunubin kuma zamuyi ta cewa astangafirillah sai kiga
Allah Ya yafe. Sabuwa tace Astagfirullah dai Gwaggo. To naji yanzu dai kin amince
ko. Na amince Gwaggo. Sukq zauna suka kulla duk yadda zasuyi a gidan Uwale idan
aure ya yiwu. Saar su daya kauyen da Sabuwa ke aure daban da nasu saboda haka da
wuya yaji labarin auren.

Shirye shirye ya kankama na bikin Sabuwa da Mal Yakubu. Uwale da Zulai le kidansu
da rawarsu don shi angon ko a ransa. Kullum yana rarrashin Munari ta kara hakuri
idan ya sami kudi zai raba musu gida da Inna Uwale. Ana saura kwana biyu Yaya
Salihu yazo garin Danmarka gaida iyayensa shi da matarsa Ruma. Tani na jin
labarinsa ta tafi gidan ta zayyana masa halin da Munari ke ciki. Fada ya rinka yi
iyakar karfinsa Inno tana bashi hakuri. Inna Ladi tace ni bazaka burge ni ba sai
kaje gidan kayiwa uwarsa barazana yadda zata yi shayin takurawa 'yata. Kamar jira
yake ya tafi gidan cikin fushi. A bakin kofa ya gamu da Mal Yakubu ya fara zazzaga
masifa. Mal Yakubu duk ya tsorata yana ta bashi hakuri. Har gidan ya shiga sukayi
ta da Uwale yace ke Maimuna dauko mayafinki ya kama hannun yaran..birni zamu tafi
kai kuma ka biyoni da takardarta. Mal Yakubu dai harda kuka itama Munari tana yi.
Da kyar Yaya Salihu ya aminci ya barta amma ya dauke Sadi dashi zan tafi. Mal
Yakubu yace wallahi na bar maka shi don girman Allah kada ka rabani da matata. Yaya
Salihu yace mata zan kaiwa Ruma kinji ko munari sai ta hada shi da Ali su shiga
makaranta idan sun dan kara girma. Godiya tayi masa ya kawo kudi ya bata. A waje ya
sake jaddadawa Mal Yakubu ya kular masa da kanwa sannan idan anyi auren zai sa ido
a kansa. Daidai da rana daya yaji zance mara dadi zai dauki mataki.

Ranar lahadi da karfe biyun rana bayan an idar da sallar azahar aka daura auren Mal
Yakubu da Sabuwa. Dakinsa aka saka amarya ya zama bashi da daki a gidan sai na
wadda take da girki. Da daurin gindin uwale Sabuwa ta goge da yiwa Munari wulakanci
a gidan. Kullum hakuri take saboda yadda mijinta ke iyakar kokarinsa wurin kyautata
mata. Watan Sabuwa biyu a gidan ta fara bayyana cikinta kamar yadda suka yi da
Zulai. Uwale kamar ta lashe ta don so. Kullum Zulai tana gidan abinci safe ,rana da
dare duk an mata kwano. Habaici iri iri Munari take sha idan suka hade kansu
karkashin bishiya da yamma. Kirikiri Uwale ta hana Sabuwa girki kullum Munari keyi
idan dare yayi kuma ta tubure tace sai Mal Yakubu ya shigo dakinta ranar girkinta.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:02 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰7




Haka rayuwa ta kasance a gidan Mal Yakubu yau fari gobe tsumma a wajen Munari. Ba
don soyayyar da suke ma juna ita da mijinta ba da tuni ta bar gidan.

Sabuwa na kwance a kofar dakinta da daurin kirji tana shan rake Uwale ta fito daga
bandaki tace kai sabuwa ki raba kanki da zaki fa saboda nakuda. Kinji ki Inna kamar
wata sabon shiga? Haihuwa ta uku har sai kin karanta min yadda zanyi? Ta yatsina
fuska ke fa daya kawai kika yi ta tsaya miki cak. Munari daga cikin dakinta tace
Allah Ya kara ta cigaba da yiwa yarta Ramlah kitso. Uwale har wani tsoron sabuwa
take ta ajiye butar hannunta tace to Allah Ya baki hakuri uwar biyu. Wannan ciki
naki badai girma ba. Gaban Sabuwa ya fadi ita bata taba ciki mai girman wannan ba
ma gashi a karyar da tayi baifi wata bakwai ba. Bata sake tankawa Uwale ba don kada
a ja maganar ta cigaba da shan rakenta.

Bayan sati uku wata rana Uwale da zulai sun fita unguwa tun safe nakuda ta kama
Sabuwa. A muguntar Uwale kulle gidan tayi ta waje wai kada munari ta fita saboda
taji Mal Yakubu yana cewa ta dawo da wuri tasan sarai unguwa zata. Da munari ta
shirya ta shirya yarta zasu fita taji kofar a garkame. Ta gaji da ja ta dawo daki
rai a bace. Dama gidan kanwar Inno zata je ziyara. Tana ajiye gyalenta taji kamar
ana kiranta daga dakin Sabuwa. Shiru tayi ta tabbatar sannan ta fito cikin sauri. A
kwance ta ga Sabuwa tana nishi da kyar duk ta hada gumi duk da sanyin gari. Munari
jika na rawa don itama bata saba ba tace Sabuwa kinga Inna ta kullemu ta waje kuma
saboda zurfin soro babu mai jinmu kiyi hakuri na dubaki. Cikin masifa tace kiji
dadin kasheni ko...ki fita ki nemo taimako Munari don idan na mutu sai nayi miki
fatalwa. Babu irin bugun da Munari batayi ba babu wanda yazo kashe reza ta samo a
daki ta dawo kan sabuwa. Tace kiyi hakuri inajin bakwaini zaki haifa don kai ya
fito. Da taimakon Allah Munari tana ta yi mata addua ta samu Sabuwa ta haihu.
Yarinya ce santaleliya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment