Reading FARAR HAIHUWA Part1 by Batul Mamman Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara tas irin wadda Uwale take so. Munari ta yanke cibi ta
taimaka mahaifa ta fito. Kai Sabuwa wannan 'ya da takai wata tara ban san irin
girman da zata yi ba. Ruwan wanka ta dora ta wanke jaririya ta kaiwa sabuwa ruwan
wanka. Sai bayan laasar Uwale da zulai suka dawo. Tun daga tsakar gida uwale ke
yiwa Munari dariyar keta ta hanata fita. Munari ko a jikinta tace Inna kinyi kawa
fa. Ko kulata bata yi ba harda tsaki zata wuce tace Inna nace kinyi kawa fa Sabuwa
ta haihu. Zulai ta yi dakin cikin sauri Uwale tana binta tana cangala kafa. Allah
Kasa fara ce, Allah Kasa fara ce. Haka take fada har ta shiga dakin. Baby ta dauka
ta rungume. Yarinyar akwai kyau ga hasken da Uwale ke buri. Zulai ta rike yarta.
Sabuwa bakwaini kika haifa? Me ya faru haka? Waya karbi haihuwar? Sabuwa tace
nakuda ce ta kamani gashi kun kulle gidan. Munari ce tayi komai, Uwale ta rungume
yar ta fita. Munari ta gani tana kwasar tuwo ta dan saki fuska nagode fa Munari
sannu da kokari. Zulai da ta gama zige yarta a cikin daki ta fito da sauri wace
godiya zakiyi mata uwale? Ashe kina fita ta kama Sabuwa da kokawa shine haihuwar
tazo ba shiri. Ai don kada a kamata da laifin kisa ta karbi haihuwar. Uwale ta bata
rai muguwa azzaluma da mai kyan zaki kashe min. To ta Allah ba taki ba baka mai
bakar aniya. Tuwon ma bazata ci ba kada kisa guba. Kwashe abinki ki bace min da
gani. Hawaye ne ya saukowa Munari ta je har kofar dakin ta leka Sabuwa na kwance a
kan gado. Cike da takaici tace Sabuwa abinda zaki saka min dashi kenan ko? Allah na
gani kuma baya bacci. Zulai tayi tsaki muguwa kinga farar haihuwa kina bakin ciki.

Mal Yakubu dai yayi farinciki daidai gwargwado yace to Inna sai asa mata sunanki
ko. Tunda kan Ramlah kika ce kada asa sunanki. Uwale tace yo haka kurum zaka sawa
wancan mummunar abar sunana? Ya jawo abarsa ya rungume suk yaransa yafi sonta. Inna
tace itama wannan bazaka sa mata sunana ba saboda kyanta. Akwai sunan gayu dana
taba ji wallahi wata rana dana je gidan Harira jikanta ya kunna talabijin. Sabuwa
tace ni fa Inna kada ki bata wa yata suna. Inna tace ni dai Hannan naji an fada ai
ko yayi dadi ko? Sabuwa ta bata fuska Hannan kamar marowaciya Hanan ake cewa. Na
yarda Malam a saka mata. Mal Yakubu yace to Allah Ya raya ya dauki Ramlah ya tashi
yayi waje.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Hanan. Uwale sa guda ta bayar aka yanka cikin
shanunta uku. Anyi bushasha ranar suna kamar haihuwar fari. Yan uwan Sabuwa suna ta
zuba habaici ga Munari. Ga 'ya mai goshin arziki an haifa. Haka dai akayi ta taro
Munari da nata yan uwan suna daga cikin daki. Yayar sabuwa na suyar nama ta bawa
duka yaransu aka tsallake Ramlah. Ta rinka binsu da kallo har Uwale ta kula tayi
tsaki ai idan baki bata ba Hanne yarinyar nan kamar mayya sai tasa ki kone da mai.
Cillo mata kashi ta gwaigwaya. Hanne ta dauko wani guntun qashi ta jefawa Ramlah.
Qashin bai zame ko ina ba sai bakin rijiya Ramlah ta bishi da dan gudunta. Tana
zuwa bakin rijiyar takalminta daya ya zame daga kafarta santsi ya kwasheta sai
cikin rij[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:03 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰9




Sai da cikin Munari yayi wata shida Uwale da sabuwa suka san dashi. Gaba daya
Sabuwa hankalinta a tashe yake tana tsoron kada Munari ta sake haihuwa hankalin Mal
Yakubu ya koma kan abinda ta haifa. Yanzu ma kamar yasan Hanan ba yarsa bace baya
bi ta kan ta sai Inna Uwale ta dame shi. Ita kuwa kullum tana rike da ita a tsakar
gida ko dakinta tana mata waka. Hannan farar jikar Uwale. Zaki auri mai kudi mai
mota,zaki kaini makka da madina.

Duk wahalar da Munari ke sha saboda cikinta yakai watan haihuwa Uwale bata daga
mata kafa akan girki ba irin yadda aka yiwa Sabuwa gata. Ganin aka Mal Yakubu ya
siyo risho har biyu yasa a kitchen din. Uwale bata san dashi ba sai da ta fito da
goyon Hanan tana ta cangala yar kafarta. Eyye me zan gani haka? Fito fiti kinibabbe
ta kirawo Mal Yakubu daga daki. Wato don munafurci shine zaka wani siyo risho
saboda matarka ta dena wahala ko? To ban yarda ba. Ni nafi son abincin da aka dafa
da itace. Yafi dadi da inganci. Sabuwa tace a'a fa inna waye baya son sauki ni
gaskiya nafi son rishon. To...to ai shikenan saboda kada fatarki tayi duhu a bakin
murhu ba. Ta harari Munari kunyi sa'a uwar mai kyau tana son rishon ba don haka ba
da kunga tsiya wallahi. Kamar kullum shi dai Mal Yakubu sai aikin bada hakuri.

Tun dare Munari ke fama da ciwon baya kadan kadan tana daurewa. Zuwa asuba abin ya
ta'azzara gashi ba girkinta bane. Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar dakinta.
Dakin Inna uwale ta nufa tana tafiya da kyar. Tana ta kwankwasawa Uwale na jin
muryarta ta sake gyara kwanciya....aikin banza haihuwa ta hudu ai zaki iya da
kanki. Haka ta koma kofar dakin Sabuwa tana bugu. Mal Yakubu ne ya fito ya kamata
zuwa dakinta yace Sabuwa ta tashi Inna su kula da ita sannan ya fita zuwa gidan
makocinsa mai akori kura ya taimaka masa su tafi asibiti. Yana dawowa daga bakin
kofa ya jiyo kukan jariri. Da gudu ya karasa ya ganta kwance kan tabarma ita kadai
da baby a gabanta. Duk ya rude yace bari na kira Inna...hannu ta daga masa barshi
kawai Malam ga reza can dauko ka yanke cibiyar.

Su kadai suka yi abinsu su Inna ko leqe. Ya fita ya bawa makocinsa hakuri ya dawo
ya buga kofar daki cikin fushi. sabuwa ki fito kafin na shigo dakin nan don wallahi
na shigo jikinki zaiyi tsami. Ta fito tana mika...yanzu don wulakanci ince ki tashi
inna ku taimakawa Maimunatu sai ku barta ita kadai? Inna ta fito dan nan ni kake
cewa munyi maka wulakanci? To mungode Baba sai ka fadi me kake so muyi yanzu. Inna
ni ba haka nake nufi ba amma ai ko sannu ayi mata. Sannu maigida to me aka samu?
Mace ce ya fada ya kasa boye murnarsa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:05 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰8



Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko
cirko an rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru. Uwale tace ni dai ba
ruwana ,fa bani bace. Munari tace wai meye ne? Me kuke leqe a rijiyar? Wata
makociyarsu ce tayi karfin halin fada mata...Ramlah ce ta fada.

Wata kururuwa Munari tayi cikin zafin nama ta nufi rijiyar ana rirriketa. Tani tace
cikin rudewa garin yaya ta fada? Wata yar cin shinkafar sunan tace qashi ne Hanne
ta jefa mata bakin rijiya shine ta bishi ta fada. Mal Yakubu aka fita kira a
majalisarsu. Munari tun tana kuka da sauti har muryarta ta dashe....wayyo Allah
kawai take cewa. Abin tausayi ta zama.

Mal Yakubu ya shigo yana tambayar me ya faru ake nemansa. Munari ta mike ta rije
wuyan rigarsa. Baban Ramlah idan na rasa 'yata bazan zauna a gidan nan ba. Yi
hakuri ki fada min abinda ya faru. Wani yaro yana cin nama yace 'yarta ce ta fada
rijiya. Mal Yakubu yace Ramlah? Babbar riga ya tube zai shiga shima aka rike shi.
Uwale ta soma kuka don Allah dan nan kada ka shiga kaima ka mutu. Suna haka Sabi
mai hakar rijiya ya shigo da wasu maza. Igiya mai kauri aka daura masa ya shiga.
Duk sakan a wurin su Munari tamkar shekara suke jinsa. Kamar wata zautacciya haka
ta koma. Sai bayan kusan minyi goma ya fara jan igiyar. Cikin sauri aka jawo shi da
Ramlah a kafadarsa. Mal Yakubu ya karbe ta ya kwantar akan tabarka. Cikinta ya
danna ruwa y rinka fita ta bakinta da hanci. Munari ko wurin bata je ba tana zaune
inda wasu mata suka riketa ta share hawaye Allah Ya jikanki Ramlah kawai take fada.

Duk yayi iya yinsa ya tabbatar yarsa ta rasu. Cikin kuka ya bude hannun da yaga ta
damke sosai. Qashin data dauka ne ashe ba rabonta bane. Wace 'yar....din ce ta jefa
kashin bakin rijiya? Jin kowa yayi tsit ya sake kunduma zagi cikin tsawa. Aka samu
wata ta nuna Hanne. Kanta yayi kamar zaki cikin fushi wani abokinsa ya rike shi. A
tsorace tace Uwale ce tace min mayya ce na jefa mata qashi shine tautsayi yasa na
jefa bakin rijiya. Suna wannan fadan Munari ta dauke gawar yarta ta kai daki ta
fara shirin yi mata sutura. Taron suna ya koma na mutuwa ita dai Uwale tayi tsit
don yau dan nata ya bata tsoro. Yana matukar son Ramlah sosai. Bayan an tafi kaita
ne Munari tana zaune gaban iyayenta da suka zo ta fara jan numfashi da kyar. Mal
Yakubu aka kira ya zo ya fitar da ita a rude. Ya kalli innarsa cikin bacin rai.
Idan itama ta mutu yau zan saki Sabuwa kuma ta tafi da yarta bana so. Asibiti suka
nufa inda likita ya tabbatar jininta yayi mugun hawa kuma tana dauke da ciki na
wata daya. Duk da bakin cikin dake damunsa Mal Yakubu yayi matukar murna. Ta taga
yake leken matarsa saboda ance a barta ta huta sosai. Yana adduar ta sami lafiya.

Bayan kwana takwas da rasuwar Ramlah Inna Ladi tazo gidan da sauran yaransu mata
hada kayan Munari. Mal Yakubu yana ta bada hakuri yana zubar da hawaye. Inna Ladi
tace kaga ka bari mu tafi ta laluma kafin yayanta ya zo kaima tunda baka ganshi ba
kasan baya gari ne. Kiyi hakuri inna ya zan saki Maimuna a wannan lokacin ga rashin
'ya ga kuma rabo a tare da ita. Inna Ladi ta kalle ta Munari da gaske ne? Kanta ta
sunkuyar kasa sai hawaye. Yi shiru kinji kada ciwonki ya tashi. Ta dubi Uwale dake
zaune tana yiwa Hannan rawa Sabuwa tana bacci a daki. Yakubu kasan kashe min jika
akayi da gangan muka hakura yanzu haka zata zauna cikin bakin cikin rayuwa a
gidanka? Kiyi hakuri inna babu fa wani yanayi mai dorewa. Zan kula da ita muddin
raina bazan bari wani ya wulakanta ta ba,yana magana yana kallon Inna Uwale. Ta
dago kai nasan dani kake dan nan ka cigaba da zargina don kawai yarka ta mutu. Ba
ga wata Allah Ya baka ba? Girgiza kai yayi ya cigaba da bawa su Inna hakuri.

Tun daga lokacin babu me shiga harkar Munari a gidan saboda yadda iyayenta suka sa
musu ido. Sai habaici daga gefe. Mijinta kuma yana nuna mata so da kulawa sosai
suna ta rainon cikinta cikin sirri. Wata rana suna cin abinci tace ni kuwa Mal
meyasa baka so su inna su san ina da ciki? Munari kenan ai ba murna zasu yi ba.
Karshenta a rinka yin abinda zaa bata miki rai har ciwonki ya tashi. Ko kin manta
Yaya Salihu yace duk ranar da jininki ya hau ko zanyi kukan jini sai na sakeki.
Dariya tayi masa aikuwa gobe zanyi masa aike. Au tsokanata ma kike ko? Zan rama
ne... yanzu dai kiyi ta sa hijab da zaman daki so nake kawai Inna taji haihuwa.
Allah ba don darajar ta haifeni ba da tuni nasa an daure....hannu tasa ta rufe masa
baki. Haba Mal? Ka manta Allah Yace kada mu fadi kalma mara dadi game da iyayenmu?
Kada ka manta kwananta ne ya kare mu kuma hakurinmu shine ladanmu. Hakane Munari
nima yau na dana. Allah Yayi miki albarka Ya saukeki lafiya. Amin M[truncated by
WhatsApp]
[8/22, 3:06 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰10



Inna uwale ta tabe baki sai mace ta takarkare ta haihu amma karshe kaga bakin
jariri. Allah Ya raya dauko min abin na gani a nan bana son doguwar tafiya saboda
kafa. Ba musu ya je ya dauko mata 'yar da kansa ya kawota. Ba yabo ba fallasa itama
dai bakar ce amma ba sosai ba gata kyakkyawa kamarsu daya da mal Yakubu. Inna tana
kallonta ta mika masa gata nan bari naje nayi sallah. Ita kuwa Sabuwa ko kallon yar
bata yi ba ta juya zata koma daki. Dawo nan ya daka mata tsawa. Wuce kije ki dora
mata ruwan wanka. Inna uwale tace ka ma isa...ita da take da jaririya. Dama ai gasa
ce tasa munarin haihuwa yanzu. Girgiza kai yayi cike da takaici yaje ya dora ruwan
da kansa.
Daga ranar 'yan uwan munari ke yi mata komai. Ana saura kwana biyu suna tace Mal
wane suna zaka saka mata ne? Haba munari ai shawara zamuyi dake. Ta sunkuyar da
kanta kasa nasan wanda ya mutu baya dawowa amma inda hali a saka mata Ramlah.
Murmushinsa ya fadada dama haka naso ina dai tsoron yi miki fami ne. Allah Ya raya
mana ita. Tace amin. Uwale dake bakin kofar dakin ita da Zulai wanda dama gulma
suka zo ji ta shigo tana matsar kwalla. Yanzu dan nan ko kara bazaka min ba kasa
sunana sai zabin matarka. Inna ke fa kika ce ba kya so tun a haihuwar marigayiya.
Akan Hanan ma kika sake cewa bakya so kika zaba mata wanan sunan. Ta dan fito da
ido ni dan nan? Abin harda sharri? To ba damuwa ka saka mata sunan da kake so. Tana
juyawa zata fita Munari tace haba Inna kiyi hakuri sunanki za'a saka mata. Ba haka
inna uwale taso ba, so tayi Munari ta ce bata son sunan sai ta hadasu fada da
Yakubu. Tsaki tayi ta fice Zulai na rufa mata baya. Duk da abin baiyiwa munari
dadi ba sai ta nuna wa Mal Yakubu jindadinta sosai.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Khadija. wata yar uwar baban Mal yakubu ce tazo
ta karbi jaririyar wanzami yazo za'a cire mata beli. Uwale ta gama lura da yadda
munari ke matukar kaunar jaririyarta sai ta fita wurin wanzamin tare da waziriyarta
zulai. Basu dade da fita ba aka jiyo sautin kukan Khadija da katuwar murya kamar
zata shide. Mata an sami abinyi suka yo soro da gudu. Tani ce kan gaba tana zuwa ta
tarar uwale ta kwaye gefen fuskarta wanzan yana kallon kalangunta ya fara zanawa
jaririya a gefen fuskarta na dama. Fizgota Tani tayi ta koma cikin gidan da sauri.
Munari ta karbeta zata bata nono amma taki karba sai wani irin kuka take. Har dakin
Uwale ta biyosu. Amma Tani baki da ta ido. Yanzu nace ayiwa yarinya kalangu zanen
fulani irin nawa shine zaki dauketa. Munari tana hawaye tace yanzu Inna duk gidan
nan wa aka taba yiwa zane a fuska shine zaki ce ayi mata. Au kema rashin kunyar
zaki min? Bani ita a karasa mun barshi a zaune. Munari tasa zani ta goya yarta tana
ta kuka. Wallahi Inna idan kinga anyi wa yarinyar nan zane a fuskarta to mutuwa
nayi. Ya kike so nayi da raina ne? Matsalar yau daban ta gobe daban. Allah bari Mal
ya dawo idan mutuwar aurena ce tazo sai dai na tafi da yata. Zanen nan fa Allah Ya
tsinewa maiyi da wanda akeyiwa. Kuka wiwi Uwale tasa ita a dole anyi mata rashin
kunya. Nufinki Allah Ya tsine min ko? To yau zanga wanda dan nan zai zaba cikin mu
biyu.

Daga gefe wasu mata suka ce gidan uwale duk taron suna sai anyi dirama. Ai munari
ta kyautawa kanta yau.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:09 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰11



Wasa wasa har magariba ta gabato ana ta mayar da zance a gidan Mal Yakubu. Shi dai
tun a kofar gida da labari ya riske shi komawa yayi ya kira wan babansa Baba Hadi.

A tsakar gidan ya tarar dasu gaba daya da sauran mata 'yan jin kwakwaf. Baba Hadi
na shigowa yace duk su fice su bar gidan. Sum sum suka rinka fita daya bayan daya.
Ba dai haka aka so ba don sun so jin yadda zata kaya aji dadin ba da labari. Suna
fita Inna Uwale cikin kuka take labarta masa abinda ya faru. Baba Hadi yace ba
matsala ke Munari bani yar . Ba musu ta mika masa jaririyar bayanta. Yace to Yakubu
karbo yayarta ya nuna Hanan dake hannun Sabuwa. Bari na sa Yau ya kira wanzamin duk
sai ayi musu. Shima Sadi idan suka zo gari sai a karbo shi a yi masa. Uwale ta
wurgo kafa cikin sauri bangane ba Yaya Hadi wai harda Hannan za'ayi wa? Eh ya amsa
a takaice. Dukkansu ba jikokinki bane? Tayi tsuru tsuru da ido...anya ayi harda
ita? Sabuwa ta ce Al-Quran ba za ayi mata ba. Mal bani 'yata. Baba hadi yace au ita
wannan da baki isa da uwarta ba shine zaki ce kada ayi mata, amma ita munari ko
kadan baki damu da lamarinta ba? To wallahi ki fita idona Uwale. Akan yadda kike
takurawa matar yaron nan zan nuna miki ni ba marigayi bane. Shine yake jure halinki
na tsiya. Kai ta sunkuyar kasa bata ce uffan ba. Ya mikawa munari yarta. Ki kara
hakuri kinji Maimunatu. Allah Ya raya muku yaranku. Tana ta godiya ya fita Mal ya
raka shi.

Tun daga lokacin uwale ta kara kunnawa Munari karan tsana. Duk lokacin da Mal
Yakubu ya fita sai wulakanci kala kala. A can birni kuwa Yaya Salihu yasa Sadi a
makaranta tare da yaransa. Lokacin da Ummita ta shiga wata na ashirin da haihuwa
Munari tayi shirin yayeta. Wata rana tana kwasar tuwo Ummita tana ta zillo a
bayanta. Tace haba mamana so kike na kona hannu ne? Uwale wadda tuni zulai ta bata
shawarar yadda zata kori munari daga gidanta ta daga waje ni kuwa munari kin fiye
kinibibi yaushe ta zama mamanki. Na zata sunan uwarki Baraatu. Munari tayi murmushi
Inna ai kema uwata ce. To indai haka ne daga yau tunda dai nike da iko da kowa a
gidan nan yarinyar nan zaa rinka kiranta Dijengala. Ni na tsani suna Ummita dinnan.
Gara dai a kirata dijengala a gargajiyance. Munari tace to ba komai inna ai yadda
kike so haka zaayi. Ba haka inna uwale taso ji don fada tazo takala. Sabuwa ta fito
daga dakinta tace inna kinji da yadda ta amsa miki kuwa? Ai gatse tayi miki. Allah
Ya kyauta uwar miji ace bata isa da surukarta ba. Ni kina ji ai sanda ta sawa tawa
yar suna. Wannan ma idan na haife ita zata sa suna.

Munari dai bata kula ba don tasan neman rigimar tasu ne ya tashi. Da Uwale taga
haka zama tayi a wurin sai da mal yakubu taji sallamarsa tasa kuka. Karya da
gaskiya ta rinka hada masa Sabuwa na mara mata baya. Ganin ko kadan bai yarda ba
tace kai na gaji so nake indai ba tare na haife ku ba ka saketa ta koma gidan
ubanta. Munari ta soma hawaye tana bata hakuri. Ta tabe baki kyayi kya gama. Yau
abincinki ya kare a gidan nan. Idan baka saketa ba yanzu a gabana ba wallahi sai na
tsine maka albarka. Haba inna ya kike so nayi ne? Babu abinda kike nema da bana
miki. Don Allah kiyi hakuri. Itama kukan tasa masa idan baka saketa ba Allah Yakubu
zan maka mugun baki. Naki jinin bakar matar nan. Ka saketa yanzu.

Munari tace mal idan kana son gamawa da duniya lafiya kabi umarnin Inna. Yana kuka
tanayi yace na sakeki saki daya. Wani kukan ne ya zo mata da karfi ta shiga daki
dauko mayafi. Inna don ta kara kuntata mata tace kwanto goyon ai ba dashi kika zo
ba. Dama yar ta isa yaye. Munari ta kalli mal yakubu yace Inna don Allah. .hannu ta
daga Allah Ya tsi....da sauri munari ta kwanto yar da take matukar so ta bashi ta
fita daga gidan cikin kuka.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:10 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰13



Da gudu ta karasa don yau akan wannan yar Mal yakubu yana iya karairaya ta. Tana
dagota wani irin tari ta rinka yi har uwale ta jiyo su ta fito. To 'yar nema zaki
fara sanaar tarin ne....kai lafiya sabuwa me ya faru? Wallahi Inna bansani ba. A
cikin robar wanka na ganta. Na shiga uku na yau a gidan nan. Ba kuka zakiyi ba
dauko gyalenki mu kaita kemis. Kila ruwa ta shaqa. Su 'ya'yan munari kamar kifaye
kowa ya tashi mutuwa sai ya tsumbula ruwa.

Basu tarar da mai kemis ba dole suka wuce asibiti. A nan Mal Yakubu ya hadu dasu
bayan dan aiken su inna ya riske shi. Likita yace gaskiya Mal akwai ganganci a tare
daku. Yarinyar nan ba karamin kamu sanyi yayi mata ba tun kafin yau. Sannan idan ta
tashi za'a sake yi mata wasu gwaje gwajen amma gaskiya a yadda na fahimta
kunnuwanta sun tabu. Da kyar zata ji kamar da. Shi kam mal yakubu sarkin hawaye har
ya fara. Sabuwa taci fada don ma inna ta tsaya mata ne. Karshe yace idan ta sake
bari wani abu ya sami yarsa sakinta zaiyi ya hadata da hukuma.

Labarin abinda ya sami Dijengala ya sami su Inno. Hanawa sukayi a sanar da munari
son kada tace zata taho tunda ta fara karatu a wata makarantar addini. Inna Ladi da
ce taje gidan ta bukaci a basu ita tunda basa sonta. Bayan doguwar muhawara tace su
jira shammaci daga kotu. Wannan kalami nata na karshe ne yasa Zulai ta bawa Uwale
shawarar suje wurin wani malami a dauke musu hankali daga kan Dije. Anya ayi haka
Zulai? Nifa gaskiya bana son inyi shirka. Haba Uwale malami ne fa ba boka ba. Ai
irin malaman nan ba bokaye bane, suna da ilimin islama gashi idan kika je zaki ga
littattafai da carbi kala kala. Sannan idan kika bari aka shiga kotu daurin shekaru
zasu yi miki duk da tsufanki da yar kafarki. Tuni Uwale ta tsorata .A haka ta ja
raayin Uwale suka je wurin malamin. Bukatarsu biyu ce. Mal Yakubu yaso Sabuwa ya
hakura da abinda ya faru sannan Munari da 'yan uwanta a dauke musu hankali daga kan
Dije da zancen zuwa kotun nan. Ya kasance munari ta manta ma da yar tata gaba daya.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰12



Cikin kuka ta shiga gidansu da sallama. Inna Ladi ta ajiye butar hannunta ta taro
ta. Me ya faru Munari? Ta shafa bayanta taji ba goyo. Ina 'yar? Ba dai ta mutu ba.
Munari ta kasa magana sai kuka. Inno tace wai ba magana ake miki ba. Inna ya
sakeni, inna uwale tace idan bai sakeni ba zata tsine masa. Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un. Ita kuwa Uwale tana son gamawa da duniya lafiya? Ina ruwanta da
zaman ku inji Inna Ladi. Inno dama bata saka baki a lamarin gidan yarta saboda kara
amma yau bakinciki ya isheta. An sako mata 'ya da magaribar fari. Tace ina goyon.
Munari ta sake fashewa da kuka tace ba dashi nazo ba. Inno tace Alhandulillahi in
anyi duniya don Manzon Allah SAW kin bar gidan Yakubu har abada. Saurin dago kai
tayi haba Inno wallahi ba da son ranshi bane. Na dai fada miki...munari ba fa
sadakarki aka bani ba. Haihuwarki nayi kamar kowanne da. Kyautace Allah Ya bani to
nayi hakurin da zanyi Allah Ya yanke miki wahala. Inna Ladi tace hakane amma kada
muyi saurin yanke hukunci.

Sallama suka ji daga waje. Inna Ladi ta amsa don ta gane mai muryar tare da yi masa
izinin shigowa. Yana shiga gidan ya zube a kasa yana basu hakuri. Inno tace ai ni
so nake ka cike mata sakin gabadaya. Inno kiyi hakuri don girman Allah. Zan kama
mata gida sai na mayar da ita can. Kaga tun ina ganin mutumci da kimarka ka bar
gidan nan kafin ayi abun kunya. Yadda Uwale ta karbi Ummita to zan aikawa Yayansu
ya dawo maka da danka. A'a inno na bar masa ki dena maganar nan don Allah. Ya kalli
Inna ladi ki bata hakuri, ko kula shi bata yi ba taja hannun munari tana tirjewa
cikin dakinta. Haka ya gaji da zama ya koma gida.

Washegari kafin azahar Inna Ladi ta aika Tani tazo da mai binta Shafa suka raka
Munari birni gidan Salihu bisa umarnin iyayensu.

Haka Dijengala inji kakarta uwale ta tashi cikin kuncin rayuwa da wahala.
Mahaifinta ne kadai gatanta. Tana da shekara biyu Sabuwa ta kara haihuwa. Dama ba
wata kulawa Digengala ke samu ba hatta wanka sai babanta ya matsa ake yi mata.
Watarana ya fita da sassafe Sabuwa ta kai ruwa bandaki a katuwar roba ta kira Hanan
da Dijengala tayi musu wanka. Tana gamawa yarta tace muje in shafa miki mai
tukunna. Dije wadda aka yiwa tsirara sai rawar dari take saboda sanyi tace Mama
nima wanka. Wani mari Sabuwa ta gaura mata ta dauki yarta suka fita. Dije tana kuka
ta taka sabulu ta zame ta fada cikin robar ruwan. Sai da sabuwa ta gama shirya
Hanan bayan kusan minti goma ta dawo ta tarar da Dijengala ta kusa shidewa a robar
ruwa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰14




BAYAN SHEKARA 17

Cikin daga murya irin na wadanda basa ji sosai tace Inna ina kwana? Uwale ta sha
kunu matsa can ni kada ki tofe ni da yawo kinzo kina min ihu a ka. Dijengala tace
naam? Alamun bata ji abinda kakarta ta fada ba. Tsaki Uwale tayi tare da daga hannu
lafiya nace. Murmushi tayi wanda yake kara mata kyau tace au banji ba ne. Dama ai
ba jin kike ba. Ta sake daga hannu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment