Reading RASHIN GODIYA by HAYATU BABA ZUBAIRU Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maza biyu ne bai damu
ba ya nuna musu hanyar dakin ya haye kan
kujera ya tsaya kamar yadda Aishatu tayi yana
bada umarni. Ku duba har karkashin gado da
cikin toilet din kunji ko? Ba kyauta zaku min ba
zan biya wallahi.
Dariya ta rinka cin Aishatu tana ta gimtsewa.
Can ta sauko kaga kamar gashi nan a kasan
kujera. Tana mika hannu ya sona ihu ki barshi
su zo su dauke kar ki taba. Ko sauraronsa bata
yi ba ta janyo mayafin tayi cilli dashi kansa. Ihu
ya kwalla tare da faduwa kasa a sume. Mazan
da ya kira kira suka fito tace ai ya fita ta taga
amma sai da ya fado masa a jiki. Suka taimaka
mata aka kai shi daki ta yayyafa masa ruwa ya
farfado. Tun daga ranar ya wani kara hade rai
kada ta raina shi, a nata bangaren kuwa dariya
yake bata sannan ta kai an yanko mata irin key
din kitchen da rana tana diban abinci kadan
yadda bazai gane ba ta dafa ta ci. Lokacin
horon yunwa ya kare.
Haka Aishatu ta rinka cin karenta ba babbaka
har na tsahon sati uku. Ranar alhamis da tsakar
rana tana zaune tana cin shinkafa da mai da yaji
ya shigo gidan ba ko sallama dama bai fita da
wuri ba duk yunwa ta isheta ga fushin ya hanata
zuwa Getso duba G. Juma. Tana cin abincin
tana mita ita kadai sai ganinsa tayi a gabanta.
Kallon da yake mata ba karamin tsorata ta yayi
ba. Cikinta ya dori ruwa....ya kalleta sai ki fada
min gidan uban wa kika sami abincin nan? Bara
kika fara ko roko, ko kuwa aljanu sun fara ciyar
dake? Nan take idea tazo kanta ta yi wani
murmushi sannan ta cigaba da cin abincinta.
RASHIN GODIYA ✂ 14
Ya sake cewa Aisha ba magana nake miki ba.
Nan ma bata kula ba ta cigaba da cin abinci
harda fara 'yan wake wake. Rai a bace ya kai
hannu zai dauke plate din ta fizge. Dama kanta
ba kitso sai kawai ta jefar da dankwalinta ta
canza murya. Tunda bazata iya yin ta maza ba
sai ta kara rage ta ta...idan ka taba mata abinci
zamu tabbatar munga bayanka Fahad. Dan ja
yayi da baya don idanunta ta kafe a kansa ita a
dole aljanu take yi. Ya danyi ta maza ke ni zaki
yiwa aljanun karya? Lallai tunda rashin kunyarki
har ta kai ga haka dole zanyi maganinki mara
kunyar banza. Aishatu dama ta samu! ta cakumi
wuyansa ta kwada masa mari wanda yayi
matukar shigarsa. Kumatunsa ya rike da kyau
idanunsa sunyi ja ya rasa tantacewa gaske ne
ko gangan. Sai dai Aishatunsa matsoraciya ce
bazata taba iya yi masa haka ba. Yarinyar da
sai yadda yayi da ita kuma ta kasa fadawa
kowa a gidansu. Baya ya kara matsawa Aishatu
tana kallon yadda jikinsa ke bari tace mu sittin
ne a jikinta. Munzo kwatar mata 'yanci ne
saboda irin cutar da kake mata. Ka zubar mata
ciki har sau goma...bakinsa na rawa yace
wallahi biyu ne kawai kiyi hakuri. Ta sake make
murya kai ni namiji ne ba mace ba. Kuma bazan
hakura ba sai ka gyara halinka. Idan ba haka ba
zamu dawo Fahad,idan muka dawo rayuwarka
zamu nema. Wayar chaja ta dauko ta rinka
zambada masa yana ihu har waje ana jinsa.
Tana jin takun Maryam ta dena dukansa ta
samu daidai kan kujera ta kwanta tana fitar da
wani irin sauti. Maryam ta shigo a tsorace
Fahad ihunka naji. Me ya faru? Jiki a sanyaye
yace Anti ashe aljanu gareta. Ji yadda ta rinka
duka na. Ki dauke ta kawai ku sauka kasa. Anti
maryam ta samo ruwa ta tofa addua ta shafa
mata. Ka kaita daki ka kwantar da ita ina jin
abin ya sauka. Amma me ya faru har suka
tashi? Yace daga yi mata wasa fa...abinci take
ci nace zan dauke plate din shikenan. Aishatu
tana kwance tana jin yadda yake karya. Kadan
ma ka gani ta fada a ranta. Daki aka kaita bata
dade da kwanciya ba sai bacci. Tana farkawa
Mama ta gani a kanta da Anti Lawisa suna mata
sannu. Har ta ma manta abinda tayi da farko ta
dan kalle su Mama me ya faru? Anti Lawisa
tace kwanta abinki sannu. Allah Ya kara sauki.
Mama dai bata yi magana ba sai kallon Aishatu
take tana tausaya mata.
Jinya sosai tayi har sati biyu. Abinci da kayan
kwadayi kala kala Fahad yake kawo mata
saboda yan uwanta da ke zama a gidan kullum.
Anti Maryam ma tana nata kokarin sosai.
Shi kuwa Fahad tsoronta yake ji don baya
yadda su kadaice a daki.
Ya dawo gida a gajiye ya nufi kitchen dibar
abinci don yanzu baya yadda ya takura ta.
Ciwon karyar ya sake tashi cikin dare ta masa
duka shiyasa ya fita harkarta. Yana kofar
kitchen din ya ji muryarta tana waya da kaninta
sadiq da baya gari tana fada masa abinda
tayiwa Fahad harda zancen macijin karya. Shi
kadai take iya fadawa sirrinta, tana magana
yana dariya. Kofa taji an taba ta juyo. Fahad
yaji duk yunwar da yake ji ta tafi ya ce mata ta
shirya su je gidansu gaida G. Juma yaji ance ta
shigo kano. Murna ta kama ta suka tafi ko
abincin bai ci ba. Gidansu Fahad suka fara shiga
yace da iyayensu su biyo su zasu gaishe da
kakarta.
Suna zazzaune a falo Baba yace ni fa bangane
wannan tara mu da kuka yi ba Fahad. Me yake
faruwa ne? Fahad yace babu abinda ke faruwa
ina so in sanar daku na saki Aishatu saki uku!!!
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Hajiyan Fahad
tace ka fara shan kwaya ne? Saki uku kamar
baka da hankali. Aishatu bata san lokacin da
tace Alhamdulillah a fili ba. Mama ta magareta
baki ji sakinki yayi ba kike hamdala? Iyayensu
babu wanda yaji dadin abinda ya faru. Fahad
dan sarkin kuka ya fara hawaye. Ashe Aishatu
ba aljanu gareta ba, na karya tayi kawai don ta
doke ni. Kwanaki ma macijin karya ta jefa min
na suma. Babu abinda bana yi mata amma
yarinyar nan na fuskanci rayuwata take nema.
Kowa yayi mamaki amma tunda ansan ba sonsa
take ba sai suka yarda. Aishatu kamar an cire
mata kaya tace ni bazan taba tona maka asiri
akan irin abinda kake min ba,amma idan na
cuceka Fahad Allah zai saka maka idan kuma
ni...Baba ne ya rufe ta da duka bata gama
magana ba. Ke dai anyi mutuniyar banza. Ki
dawo gidan sai muci abinda muke ci tare.
RASHIN GODIYA ✂ 15
Iyayen Aishatu sam sun ki fahimtarta. Bata da
wani sukuni indai ba tana tare da yan uwanta su
Nurain ba. A haka ta gama iddarta cikin kunci
da tsangwama. Mama har hantarar take idan
tayi magana, a dole suna bayan Fahad.
Da kyar da sidin goshi Baba ya biya mata kudin
WAEC. Ta dukufa karatu sosai saboda
shekararta uku rabonta da makaranta gashi ko
aji shida ma bata yi ba. Lokacin da result ya fito
tayi saar samun credits takwas da pass a
history. Baba duk abinsa yayi murna amma dai
ya kafa mata sharadin bazata cigaba da karatu
ba sai ta sake aure. A haka Aishatu ta kwashi
shekara daya da rabi babu abinda take yi sai
zuwa islamiyya da yin zobo da meatpie wanda
almajiri yake sayar mata tana biyansa. Shi kuwa
Fahad watansu biyu da rabuwa ya sake aure.
Matarsa yar kanin Alhaji ce wai nan anyi masa
auren huce haushi tunda Aishatu ta ki shi.
Yahanasu amarya dai bata da matsala da yan
uwansa. Hatta anti maryam da basu dena
mutumci da Aishatu ba suna zaman lafiya da
ita. Da yake ya saba da keta lokacin da ya fara
kokarin kwatanta mata irin zamansu da Aishatu.
Ranar da ya kulle kitchen yana fita tasa tabarya
dama turminta a baranda yake tayi rugu rugu da
kofar. Da ya dawo zai fara fada tace kar ma ya
soma idan ba yana so ta fada a gida bane. Irin
kayan ciye ciye da yake shigowa dasu da ya
cinye gaban Aishatu kuwa da karfi take kwata.
Tun yana hakuri har aka fara jin kansu. Bata
shiru yana fada tana fada. Karshe ma Alhaji ta
fadawa karya da gaskiya akan Fahad to sai tayi
rashin saa son dansa ya rufe masa ido yaki
yarda. Wata rana suna fada ta biyoshi har kasan
bene da tabarya saboda yaki siyo mata naman
miya. Da rarrashi Khalid ya samu ta hakura ya
aika aka siyo mata naman. Suna zaune a
falonsa Fahad ya dora kankara akan
kumburarren goshinsa Khalid ya rinka masa
nasiha. Fahad rayuwa fa bazata taba tafiya a
haka ba. Banda keta da hada sharri baka iya
komai ba. Hakika Allah SWT Yayi gaskiya da
Yace idan muka gode Masa zai kara mana, idan
muka ki kuma to azabarSa mai tsanani ce. Ka
fini sanin tun bata sonka Aishatu aka tilasta ta
aure ka har ta kwantar da hankalinta don ku
zauna lafiya amma kiriri ka rinka cutar da ita.
Ko sau daya bata taba fada min abinda kake
mata ba amma ai ina da idanu. Duk ta rame
kamar wata kazar mayu. Shiyasa idan ka fara
wannan kukan ko kadan bana yarda da kai
tunda tun muna yara ka iya wannan sharrin.
Fahad ya dan harare shi yana magana da kyar
saboda ciwo yace yanzu dai Yaya me kake son
cewa? Khalid yace abu daya ne kawai. RASHIN
GODIYA ga Allah akan ni'imomin da Yayi mana
komai kankantarsu masifa ne a garemu. Ya baka
mace tagari mai hakuri da sannin hakkin aure
amma sai da ka kaita bango ta yi maka bore.
Sau nawa kake dukanta da yin abubuwan da
zasu saka ta a cikin matsala da iyayenta? Duk
ta shanye saboda ka iya toshe duk wata kofa da
zata yiwa wasu bayani su fahimta. Bansan
cikakken abinda ya faru ba amma nayi imanin
laifinka yafi nata. Abinda kayi mata ne Allah Ya
baka mace irin yahanasu wadda bata barin ta
kwana. A sanyaye fahad ya tashi don ya san
gaskiya dan uwansa ya fada masa.
Cikin ikon Allah sanaar Aishatu tayi albarka dan
kudin da take samu ta ke tarawa a banki.
Sauran kuwa gidansu take taimakawa da kanta
duk da iyayenta basa gani bare su yaba. Maza
suna ta neman aurenta saboda yadda ta
murmure tayi kyau. Lokacin shekarunta ashirin
da biyu. Wani ma bazai yarda ba idan aka ce ta
taba aure. Rannan ta kira Maryam a waya su
gaisa khalid ya dauka yace suna asibiti ne anyi
mata aiki ta haifi mace. Aishatu tayi murna
sosaita tambaye shi asibitin don bazata iya
zuwa gidansu ba saboda surutun mutane.
Atampa tasa mai kyau wanda aka yiwa riga da
wrapper skirt sai mayafi babba da ta yafa.
Fuskarta kwalliya tayi kadan tasa takalmi mai
dan tudu sai yar purse dinta da ledar kayan
barka. Tayi kyau sosai ta fito tayiwa Mama
sallama zata fita...tabe baki tayi haka dai aka
iya sai yawon tsiya an kasa aure. Koda yake
waye zai auri mai dukan miji. Zuciyarta ba dadi
ta fita ta tafi. Sun sha hira sosai da maryam.
Suna zaune Khalid da Fahad suka shigo tare da
Yahanasu tayi wa maryam girki. Yaran maryam
na ganinta suka rungumeta suna murna.
Yahanasu ma sun gaisa lafiya ta gaishe da
khalid tare da dauke kanta daga Fahad tayi
musu sallama ta fice. Tunda Fahad ya ganta
gabansa ya fadi. Gaba daya ta canja ta kara
kyau. Fita yayi yabi bayanta yana kiran sunanta.
Kamar yana magana da dutse bus na tsayawa a
gabanta ta haye ba ko waige. Daga ranar Fahad
ya soma wani tashen sonta, zance kadan sai ya
sakota. Abu kamar wasa sai gashi bashi da wani
sukuni idan baije gidansu ba duk da bata fitowa.
Da baba yayi masa magana ma cewa yayi saki
uku cikin fushi ai a matsayin daya yake. Baba
yace abu daya zaisa ka kuma aurenta sai idan
ta auri wani ta fito. Shi dai yana kaunar Fahad.
Duk da baya son ya ganta da kowa dole ya karbi
shawara. Ganin bata sauraron kowa Fahad ya
tura mata kanin abokin shi Audu mai suna Tijjani
suyi auren kisan wuta ba tare da ta sani ba.
Anyi saa ta damu da rashin karatu babu wani
bincike iyaye suka shiga maganar duk da ba
wani sonsa take ba ta amince aka yi aure
saboda su baba sunce idan ta wuce wannan
shekarar ba aure zasu yi fushi da ita. Duk
abinda ake Baba da Fahad suke shawara yasan
auren kisan wuta ne. Amma idonsa ya rufe shi
dai a mayar da aurenta da fahad musamman da
yaga kudi sun fara zauna masa har ya sayi
mota. Anyi aure ita dai Aishatu tana zaune ne
kawai saboda biyayyar iyaye. Bayan wata daya
Fahad ya hurawa tijjani wuta ya sakota tare da
infection din da ya sa mata. Tana gama idda
Fahad ya dawo. Sai dai kafin ta bashi amsa
ciwo ya bayyana a jikinta. Hajiya tace bazata
yadda a mayar da aurensu da fahad ba. Da
kansa yace ai shi ya jawo mata har ma ya fadi
duk irin zaman da suka yi a baya duk don a bari
ya aureta. Shi da gaske yanzu sonta yake. Su
baba sunji kunya sosai tare da tsanar fahad.
Shiyasa duk yan kudin su da nata a neman
lafiyarta suke karewa domin sunyi nadama.
Alhaji da Hajiya ma sun bata hakuri sannan
Alhaji yace idan ya kuskura ya saki yahanasu
zaiyi fushi da shi.
Aishatu ta numfasa ta kalli Sauda wannan shine
labarina wanda da zan buda miki sosai sai mun
kwana a nan. Fahad yasa na tsani maza saboda
muguntarsa da tsantsar iya sharri. Sauda tace
Aishatu tabbas kinga rayuwa Allah Ya baki
wanda zai zama haske a rayuwarki.
RASHIN GODIYA✂ 16
Sai da suka yi sallar laasar suka koma asibitin.
Sajida da Islam basu so Aishatu ta tafi ba har
gate suka bisu suna daga mata hannu. Sun
zauna har shida saura babu Dr Rano babu
dalilinsa. Karshe Sauda ta ce mata gara su tafi
gida, nurse suka tambaya tace sai wani satin
ranar talata zai shigo. Suka yanke shawarar
dawowa ranar. Har phone number suka yi
exchanging.
*
Tamkar wata jaka haka Huzaifa ya rinka jan
hannun Fadila har suka shiga dakinsa ya bude
drawer din da yake ajiye kayan wanki. Wata
farar leda ya dauko ya bude ya fito da wando da
safa wadanda duk suke da digon ja a wurare
daban a jikinsu. Saboda bacin rai da kyar yake
iya magana ita kanta fadila ta gama tsorata da
yanayinsa..ba a nan kika dauko rigar ba. Kai ta
daga masa a hankali. Ya ce saboda kin gama
ginawa zuciyarki zargi baki dauko sauran kayan
ba kika fito da shirt din ita kadai ko. Sabo mai
wanki ne ya fada min ya jika su da wasu kayan
masu zuba wadannan sun baci shine na hadasu
a leda zan bayar. Idan baki yadda ba na yarje
miki ki dauki wayata ki kirashi ki tambaya. Yana
gama magana ya fice daga dakin ya koma falo
zuciyarsa na kuna ta rufe idanunsa.
Hasbunallahu kawai yake karantawa don a
yadda yake ji idan Fadila ta shigo hannunsa zai
iya yi mata rauni da duka.
Inda ya barta haka ta tsaya kusan minti goma
ta kasa fitowa daga daki. Wani irin so take yiwa
Huzaifa wanda bazata iya hada shi da komai ba.
Shiyasa take tsananin kishinsa. Duk irin yadda
mata suke nuna sonsa musamman abokan
aikinsa bai taba tunanin biye musu ba. Idan har
zai kula mace sai ya tabbatar aurenta zaiyi. To
bai tashi aure ba tunda ko shekara biyar baiyi da
auren fari ba shiyasa yake kama kansa. Hakuri
yake sosai da Fadila saboda irin yadda take
yawan zarginsa da yi masa rashin mutumci idan
abin ya motsa. Falon ta biyo shi ta durkusa a
gabansa tare da rike masa hannu. Abban Aliya
don......daya hannun nasa ya daga ya dakatar
da ita. Kada ma kice don Allah don baki san
girmanSa, isarSa da buwayarSa ba. Fadila ba
kya gode masa duk abinda ya baki sai ki rinka
hangen wani abun daban kawai don ayi ta zama
cikin tashin hankali. Bakin gwargwado ina
kokarin kyautata miki amma na rasa dalilin da
yasa ba kya kyautata min zato. Ko dai kin taba
ganina da wata a zahiri, waya ko text? A'a
wallahi duk sharrin shaidan ne kayi hakuri. Yace
ke zan bawa hakuri tunda kice aka yiwa laifi.
Abu daya nake so ki sani wallahi idan kika kaini
bango bazan nemi matan banza ba amma sai na
cika gidan nan da matan da suka fiki komai.
That is a promise. Baki bude ya barta a zaune
ya dauki key din motarsa ya fita.
Gidansu ya tafi ya shiga dakin Umma
mahaifiyarsa ya tarar tana sallar laasar. A kan
kafet ya zauna ya jingina bayansa da gado yana
jira ta idar. A nan bacci ya dauke shi saboda
gajiya da tension da suka yi masa yawa. Tana
idarwa ta kalle shi cike da tausayinsa. Filo ta
dauko zata gyara masa kwanciya yayarsa Kubra
ta shigo. Aurenta ne ya mutu ta dawo gida suna
ta rigimar wanda zai rike 'ya'ya ita da mijinta.
Sauri tayi ta karbi filon ta saka masa ya gyara
kwanciya ya cigaba da bacci. Tace yanzu
Umma wannan katon magidancin kike gyarawa
kwanciya sai ya karasa ki. Umma tace ina
ruwanki, danki ko nawa?
Wai ina ni ina wannan zabgegen dan kalen
hanjin. Nasan bazai wuce yar banzar yarinyar
nan bace ta bata masa rai. Kina ganinsa kinsan
bashi da kwanciyar hankali. Mtswww ina ma ya
saketa kowa ya huta. Umma ta harareta ke
bana son rashin hankali don kin kaso naki auren
sai na kowa ma ya mutu. Yaya Kubra tayi dariya
umma kinsan dai ba laifina bane. Umma ta ce
haka kuke fada ke da mijin naki magulmata
kuna so kuna kaiwa kasuwa. Dariyar Yaya kubra
ce ta sa Huzaifa ya farka. Yana tashi ya gaishe
su Umma tace autan umma yau ba aiki ne ka
dawo wuri? Wallahi umma akwai, wata yar
matsala ce ta....idanunsa ne suka kai kan
agogon dakin ba dai biyar da rabi ce zata yi ba?
Yaya Kubra tace ya lafiyar idon ne likita. Da
sauri ya tashi yana saka takalmi zan dawo ko
zuwa gobe ne umma yau na kusa karya alqawari
. Yana tuki yana adduar Allah Yasa yarinyar bata
jira shi ba. Sai yanzu ya tuna ma a gabanta
Fadila tayi wannan tsiyar. Karshenta ma ta
gama baza labarin kowa ya ji a asibitin. Wani
tsakin yayi ya cigaba da tukinsa.
A bakin gate ya ganta tana kokarin tare mota ga
wata mata daga cikin motarta suna hira. Har ta
samu za ta shiga yayi saurin tura maigadi ya
tsayar da ita. Kafin ya karaso ta shige mota ita
ma Sauda taja tata motar ta tafi. Hannu ya
buga kan sitiyari duk Fadila ce ta ja masa. Allah
kadai Ya san patients nawa ne suka tafi da
haushinsa a rai.
RASHIN GODIYA ✂ 17
Magungunanta na farko ta cigaba da sha sannan
ta rinka yin yadda likita da Anti Sauda suka bata
shawara. Ita kanta taji dadin jikinta kuma
wannan karnin ya ragu sosai ga kurajen duk sun
mutu. Mama sai washe baki take don murna
'yarta ta fara samun lafiya. Da yamma tana
sharar tsakar gida yaro ya shigo yace wai Aisha
tazo inji Fahad. Sai da gabanta ya fadi don
rabonta da shi zai kai wata shida. Daga bakin
yan unguwa taji wai aiki ya samu a Abuja.
Likafa ta cigaba ta fada a ranta. Ta san dole ya
karo wulakanci. Da can ma yana fama da lifan
ya aka cika. Mama tana daga daki tayi saurin
fitowa ta kalli dan aiken, kaje ka fada masa
babanta yace duk ranar da ya sake zuwa kofar
gidan nan hukuma ce zata rabasu. Dan banzan
yaro ga karyar tsiya. Aishatu ta kwashe da
dariya kai Mama sirikinki ne fa Fahad. Ni
gaskiya ki barni inje. Biyota tayi da maficin
hannunta tana cewa kaniyarki Shatu. Ita kuwa
daki ta ruga tana yiwa Mama dariya don ba
karanar tsanarsa tayi yanzu ba. Yadda yake iya
tara hawaye a idonsa ya fadi karya da gaskiya
yasa Mama tace ita tsoronsa ma take ji.
Yaro ya maimaita sako yadda aka fada masa
Fahad yace to nagode. Kofar gidansu ya koma
ya zauna har ya hango Mal Sa'id ya dawo zai
shiga gida. Sauri yayi ya tarar da shi suka gaisa
fuskar nan ta Baba a hade. Har mamakin kansa
yake yadda ya tsayawa Fahad akan Aishatu
kamar wani wawa. Yarinya duk tabi ta motse
amma a lokacin gani yake kamar ita ta jawowa
kanta. Fahad yace Baba don Allah kuyi hakuri
ku bari nayi magana da Aishatu ita ma na
roketa tayi hakuri.
Ba sai ka ganta ba inji Baba, zan fada mata
kuma tunda yarinya ce yar albarka nasan da
gudu za ta yafe maka. Kai ka sawa ranka ta
yafe amma wallahi ka nesanta kanka da gidana.
Duk irin magiyar da zaiyi yayi amma sam baba
yaki amincewa. Karshe ma dai shigewa cikin
gidansa yayi ya bar fahad a tsaye.
Sunyi waya da Anti Sauda har sau biyu. Mama
ma tayi mata godiya saboda yadda ta ke nuna
kulawa ga Aishatu. Ana gobe zasu koma asibiti
ta sake kira tayi mata tuni. Aishatu tayi mata
godiya sosai.
Sai karfe tara na dare ya dawo gida a gajiye.
Shopping din kayan abinci da sauran kayan
bukatun gida yayi. Boot din motarsa a cike har
seat din baya. Shi da maigadin gidansa suka
rinka jidar kaya suna shiga dasu store. Motsinsu
yasa Fadila fitowa da doguwar rigar bacci.
Huzaifa yayi mata muguwar harara saboda tana
ganin maigadi amma taki komawa ta sa ko da
mayafi ne. Sai da suka gama ya ce cikin fada
yanzu don Allah Fadila kin kyauta kenan? Ki fito
gaban M. Bala da irin wannan shigar ba ko baki
da aure ai kinsan tsiraici haram ne. Zumbura
masa baki tayi to ba gidana bane. Duk wanda
ya kalla yayi wa kansa, ta wuce shi ta shiga
kitchen. Tsaki yayi ya bi bayanta ga kaya nan ki
jera yadda ya kamata. Kinyi min papper soup din
kuwa? Dan tsaki tayi banyi ba wani film ne ya
dauke min hankali yanzu aka gama. Nayi tunanin
za ka yi aikin dare ne shiyasa ban yi ba. Huzaifa
girgiza kansa yayi kawai yace to ki fito da kazar
daga fridge ta dan saki kafin ki dafa.
Ai ban saka ba ma, ni tunda ka fita ban shigo
kitchen din ba. Yace a takaice dai kina nufin
tana cikin sink tunda na ajiye miki da azahar.
Bata kula shi ba ta dauko tukunya zata dora
yace ta barshi ya fasa zai sha tea kawai. Tace
to babu bread mantawa nayi ban kira ka ba.
Fadila what is wrong with you, me Aliyu zai ci
gobe? Kinsan baya cin komai sai bread da safe.
A hasale ya fita don ya gama kulewa.
Haka yasha tea da madara ya shiga wanka.
Yana fitowa wayarsa na soma ringing. Lokacin
shadaya saura. Kafin ya dauka Fadila ta riga
shi. Tana dubawa taga ansa lady K tasan mace
ce ta dauka ta fara masifa....to kadangarun
bariki masu hana matan aure sakewa da
mazansu. Me zaiyi miki da tsohon daren nan
kike kiransa. Muryar Yaya Kubra taji tace Fadila
rashin da'ar taki har yazo kaina? To tun wuri ki
shiga taitayinki ko na saba miki, shashashar
kawai. fizgar wayar taji yayi yana magana yana
harararta.
RASHIN GODIYA ✂ 18
Daren ranar damuwar Fadila tasa da kyar bacci
barawo ya dauke Huzaifa. Gari na wayewa tun
bakwai da rabi ya fice. Fadila tana tambayarsa
ko zaiyi breakfast bai kulata ba ya tafi.
Sai da ya gama ward round a asibitin sannan ya
shiga office wurin karfe goma. Lokacin Aishatu
da Sauda suna zaune a baya suna ta hira. Yau
Sauda aka fara kira, bayan sun gaisa ya
tambayeta progress din da ake samu game da
jikinta ta sanar dashi. Yace to ya akayi baki zo
ba last week. Ko lafiya ta fara samuwa zaki fara
wasa da ita. Murmushi tayi haba Dr ai kasan ina
kulawa. Nazo last week kana cikin duba Aishatu
sai ka fita ita ma baka gama dubata ba. Mun
dawo around 5 muka jira shiru sai aka ce sai
yau za ka sake zama. Dafe kansa yayi da yake
masa ciwo, ta fada muku dalilin fitar da nayi
ko? Sauda tace eh to, cewa tayi kace idan zamu
iya mu dawo karfe 5. Sai da ya gama yi mata
tambayoyi ya kara mata wasu maganin ya ce ta
turo next patient. Har ta je bakin kofa taji yace
ita dayar kin santa ne? Sauda tace ai tana nan
ma muna tare. Na dai riga ta zuwa ne kawai.
Mutum uku ya gani bayan Sauda kafin Aishatu
ta shigo. Yau sai yaga tayi fes ba kamar
zuwanta na farko ba. Fuskarta dauke da
murmushi tayi sallama. Bin ta ya rinka yi da ido
har ta zauna bayan ya amsa sallamar. Dr ina
kwana
Ajiye biron hannunsa yayi sannan ya amsa lafiya
kalau. Ya jikin ina fata kina samun sauki.
Alhamdulillah da sauki. Yace to yanzu me yake
damunki? Yadda ta sunkuyar da kanta bata iya
bashi amsa sosai saboda kunya yana burge shi.
Gata kyakkyawa sai yau yayi noticing....she
looks so innocent.
Zafin bai tafi ba.
Kamar daga sama yaji muryarta a kunnensa. Sai
a lokacin ya dawo hayyacinsa. Ya kama zancen
zuci..amma Fadila kin cuce ni, ace daga ganin
patient na fara wasu irin tunani a kanta.
Hmmm kika ce zafin bai tafi ba ko? Eh ta amsa.
Allurai ya rubuta mata da wani magani na
shafawa. Ki cigaba da shan wadancan har su
kare. Wayarsa yaji an kira sai ya share ya
cigaba da bayani don yayi tunanin Fadila ce.
Godiya tayi masa ta tashi zata tafi aka sake
kiran wayar sai ya dauka. Abokinsa ne Abdul
wanda shi kadai Huzaifa ke iya sanarwa
matsalolin gidansa. Alama yayi mata da hannu
kada ta fita.
A yadda yake kallonta kamar wadda batayi
karatu ba sai kawai ya rinka magana da turanci
yana bawa Abdul labarin irin kuncin da yake ciki
a dalilin Fadila. Duk maganar da yake idanunsa
basu bar Aishatu ba. Ita kuwa kasa take kallo
amma tana tausayawa likitan da baiyi dacen
mata ba. Ko da yake samun wuri tayi. Ita idan
taga mace na yiwa miji iskanci har mamaki
take. A hankali taji ya ce Abdul i need a second
wife. Bata san me abdul din ya fada ba amma
dai ta ga Dr Rano ya sake kallonta yayi
murmushi.
Ajiye wayar yayi...kiyi hakuri na bata miki lokaci
sosai ko. Dama ina son baku hakuri ne game da
abinda kika gani wancan zuwan naki.
Murmushin da ya soma jindadin gani a fuskarta
tayi masa sannan ta mike tsaye. ba komai Dr
nan gaba dai ka dena hirar sirri a gaban
patients don da yawanmu muna jin yare daban
daban. Ba shiri ya tashi yana kiran sunanta ta yi
gaba. Maimakon yaji ba dadi sai ya sami kansa
cikin nishadi. Sai da ta fita ya tuna ashe kansa
na ciwo kuma yana jin yunwa.
Kai Aishatu kamar bazaki

Please Login or Register in order to submit comment