Reading RASHIN GODIYA by HAYATU BABA ZUBAIRU Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayarsa ya kira Aishatu dama niyarsa
kenan su biya a daukota tunda yamma tayi. Ta
fada masa ta gama zata jira ta koma gidan anti
Sauda. Fadila na jin haka ta dauko wayarta ta
tura text.
(Tana gidan nan da na kwatanta maka a yan
kaba. Kayi sauri muna hanya)
Baiyi mata reply ba ya cigaba da kallon gate din
gidan da Aishatu ta shiga daga cikin mota. Ta
kara kyau da haske...sai yanzu ya kara ganin
wautarsa akan yadda yayi treating dinta a
gidansa. Yaro ya gani zai wuce yayi saurin fita
daga mota ya tsayar dashi. Don Allah kace
Aisha tazo inji Huzaifa. Ka fada mata tayi sauri
wayata ce ta mutu. Yaron ya shiga ya fadawa
Sajida sakon ta shiga dakin mamanta ta fada
musu. Aishatu ta tayi saurin gyara fuska Anti
Sauda sai dariya take...na dai fada miki amarcin
nan sai an gama gyaraki. Na fuskanci Huzaifa
ya gama koya miki rashin kunya idan ban kaiki
ba zaki kai kanki. Aishatu ta rinka dariya suka
fito tare. Anti Sauda tace gori zan masa har yau
bai taba shiga gidana ba.
Basu ga motarsa a bakin gate ba har Anti Sauda
na cewa ko dai tafiya yayi wani wurin kila yanzu
zai dawo. Sam bata kula da yadda Aishatu ta
sandare a tsaye ba. Hannunta taji ta damka har
ta danyi ihu ke lafiya zaki karya ni. Kamar me
rada ta nuna mata mutumin da yake tahowa
wurinsu. Anti Sauda tace waye wannan? Ko
Fahad ne? Aishatu ta gyada kai alamar eh.
Assalam alaikum wa rahmatullahi wa
barakatuhu. Anti Sauda ta sha kunu ta amsa da
kyar sannan ta rike Aishatu shige muje ciki.
Fahad yace don Allah Haj ki daure ku saurare ni.
Abinda ya kawoni yana da matukar
mahimmanci. Aishatu ta juya a fusace yayi
saurin cewa don girman Allah ki tsaya. Ba tare
da ta juyo ba ta tsaya. Kan gwiwoyinsa biyu ya
durkusa ki yafe ni Aisha. Ni mai dumbin laifi ne
a gareki kuma wallahi ban taba jin son mace ba
sai da na rabu dake. Nayi nadama mara iyaka
kuma tun a duniya naga sakayyar abinda nayi
miki tana faruwa a kaina. Sai hawaye suka fara
zuba a idanunsa. Ya kalli Anti Sauda ki taimaka
ki bata hakuri ko zanga sassauci a rayuwata.
Bani da wani burin da ya wuce ki furta da
bakinki kin yafe min. Duk maganar da yake kin
juyowa tayi. Tana tuna irin wahalar da ya rinka
bata ciki harda zubar mata da ciki sau biyu. Anti
Sauda tace ni abinda ya bani mamaki ya akayi
kasan tana gidan nan. Yayi murmushi ki roketa
ta yafe min sai kuji abinda ya kawo ni. Wallahi
Aishatu bazan kara cutar dake ba. Ina tsoron
lahirata, ina tsoron wutar Allah, ina kunyar
haduwa da Mahaliccina. Ta dan juyo na yafe
maka amma don Allah ka dena bibiyata haka.
Ya tashi yana kade rigarsa nagode sosai Aisha.
Sai kuma mu koma ga abu na biyu da ya kawo
ni....kafin yayi magana suka ji wani mahaukacin
horn. Dukkansu basu tun san lokacin da Huzaifa
yayi parking mota yana kallonsu ba. Ransa ya
gama baci ji yake kamar ya shake fahad don ya
tabbatar shine saboda haduwar da sukayi a
kofar gidan su Aishatu. Zuciyar Aishatu kuwa
don tsoro da fargaba kamar ta fito waje
RASHIN GODIYA ✂ 48
Gaba daya Aishatu ta rikice ta ma kasa
motsawa. Huzaifa ya fito daga motarsa a
fusace ya janyo hannun Aishatu. Anti Sauda
tace Dr kayi mata a hankali bamu san yana
wurin nan ba. Tamkar ba da shi take magana ba
haka yayi gaba abinsa. Fahad bai ce masa
komai ba har ya tada kura suka wuce. Anti
Sauda ta yiwa fahad kallon banza. Ince ko kaji
dadi ka hada rigima. Aishatu tana fada min
sharrinka sai yau na tabbatar. Mai yasa baka yi
masa bayanin abinda ya kawoka ba. Fahad yayi
murmushi tare da dan tabe baki saboda kishi
mana. Anti Sauda ta yu hanyar gate din gidanta
a fusace Allah wadaran halinka. Fahad yace
please ki saurareni. Maybe na iya fitar da
kawarki daga zargi. Na tsaya sauraronka nima
nawa mijin ya dawo ko. Sannu mugu to ta Allah
ba taka ba. Ta shige tare da bugo gate din da
karfi.
Kana ganin yanayi Huzaifa kasan bashi da
kwanciyar hankali. Babu abinda shaidan bai kitsa
masa ba a zuciyarsa. Wai garin yaya ma Fahad
yasan gidan Sauda? Kuma ya akayi yasan inda
Aish take a wannan lokacin? Fadila ta dan juya
baya inda take jin sautin kukan Aishatu a
hankali. Aishatu wai me ya faru ni kun sani a
duhu. Kaima Abban Aliya meye na fushi bayan
baka kirata ko kayi mata horn ba tunda muka
zo. Ai kaga ba laifinta bane don bata taho da
wuri ba. Mtsw kuma maza da rigimarku. Shiru
babu wanda ya kula ta. Ta sake cewa Aishatu
waye mutumin nan ko dan uwanku ne. Na tuna
shi a wurin walimarki yana ta miki liki. A fusace
Huzaifa yace to uwar jaraba kina mota har kin
kare masa kallo...tayi saurin daga hannuwa
sama yi hakuri na yi tunanin ko dan uwanta ne
ko mijin wannan matar. Daidai lokacin da ya
shiga gidan mal habu na rufe gate Fadila tace
kai amma fa Aisha jininku mai karfi ne don kuna
dibar kama da mutumin nan. Hancinku
yayi....wani irin burki Huzaifa ya taka saboda
yadda ya harzuka. Yace Fadila idan bakiyi min
shiru ba zan tattaka ki wallahi. Tayi dariya
Aishatu yau angonki sai a hankali bari na barku.
Ta fice abinta ta shiga ciki. Aishatu ta dago kai
suka hada ido ta mirror din gaba yace kema ki
fita. Ta soma magana baby ka saurare ni
wallahi...katse ta yayi da tsawa Aishatu ki fita
nace, am not in the mood. Bai taba fadar
sunanta ba sai yau. Yau ma cikin bacin rai. Ba
musu ta fita yayi ribas da motar ya rinka danna
horn har mal habu ya fito da gudu daga bandaki
ya bude masa gate ya fice.
Aishatu ta shiga ciki tana kuka. Komai yayi
mata zafi. Ta tabbatar plan Fahad ya hada
tunda cewa yayi tazo inji Huzaifa. Komai yayi
mata zafi ta shiga daki ta takure akan gado tana
kuka a hankali. Ba ita ta tashi ba sai da taji
kiran magriba.
Fadila tana kallon yadda Huzaifa ya fita ta tafa
hannuwa. Wannan karon ko kinfi kuda naci
Aishatu sai kin koma inda kika fito. Ta kira
wasila suka sha hira hankali kwance.
Masallaci daya suka yi sallah. Sai da ya jira ya
gama gaisawa da mutane ya fito sannan ya biyo
shi waje. Sallama yayi masa mutum ya amsa
cike da nutsuwa. Sai yace kamar Dr Rano ko
mijin Aishan Sauda? Eh nine ya dan saki fuska.
Don Allah magana nake son muyi. Gefe suka
koma Huzaifa yace kaine mijin Haj Sauda ko?
Babban su Islam yace eh nine lafiya dai?
Huzaifa yayi masa bayanin abinda ya gani. Yace
to ni bana son aiki da zargi, nasan halin
mutuminan amma ina neman izini muyi magana
da Saudan ta fada min gaskiyar abinda ya faru.
Alh Adam yace kayi tunani mai kyau Dr. Allah
Ya tsare mana iyali daga sharrin shaidan. Muje
gidan..Huzaifa yayi masa godiya yace haba har
daurin aurenka fa nazo. Rashin zamana yasa
bama haduwa sosai.
RASHIN GODIYA ✂ 49
A falon gidan suka zauna Anti Sauda tayi musu
gamsasshen bayani game da zuwan Fahad. Ta
kare da cewa wallahi Dr matarka tana sonka
kuma tana da rikon amana. Bai kamata zargi ya
shiga tsakaninku akan abinda ka gani kawai
baka bincika ba. Idan da tana son komawa
gareshi ai bazata aureka ba. Huzaifa ya dafe kai
ya kasa magana. Garin yaya ya nuna bacin rai
sosai ga matarsa wadda take yiwa mai lafi
uzuri. Alh Adam yace Sauda kibar kishi, babu
abinda baya sawa. Tace hakane kaga ko ba
komai nasan kanwata tana da babban gurbi a
zuciyar Dr. Murmushi Huzaifa yayi yace nagode
sosai da yadda kike kula da Aish, Allah Ya saka
da alkhairi. Ya tashi zan tafi don Allah idan ya
sake contacting dinku sai ki sanar dani tunda
kince ya fada muku akwai abinda ya kawo shi.
Har bakin motarsa Alh Adam ya rako shi. Sai da
ya fita sannan maigadin ya biyo Alh Adam.
Uhmm Alh ga wannan takardar. Wani mutum ne
dazu ya bani yace na bawa Hajiya sai na manta
yanzu na tuna da na sake gani bako. Alh Adam
yace kuma bai fadi suna ba? Maigadi yace na
tambaya yace idan na bata zata gane. Alh Adam
ya bude takarda ya karanta.
(Nasan ba lallai ku yarda dani amma akwai
bayanin da nake son yi Aisha ko mijinta. Ga
numbar wayata pls contact me.
Fahad)
Alh Adam yayi tsaki kuma shine sai yanzu zaka
bani? Gashi wanda abin ya shafa yanzu ya tafi.
Gida ya shiga ya nunawa Anti Sauda tayi ta
salati ta kira Aishatu wayarta a kashe, ita kuma
bata da numbar Dr Rano. Dole suka hakura sai
washegari.
Huzaifa bai koma gida ba sai da ya nemo wata
kaza da Aish ke so. Duk ranar da rigimarta ta
tashi ta rinka nacin sai ya siyo mata ga layi da
akeyi a wurin. Haka ya zauna yana ta tunanin
halin da take ciki. Fatansa daya ba kuka take yi
ba. Gashi ta kashe waya ya kasa samunta.
Hudu ya siya ya wuce gida. A falonta ya ajiye
nata ya wuce dakin Fadila ya kai mata biyu.
Nata daya na yara daya, ta karba cike da murna,
ita dai ta ga kayan kwadayi kawai. Har zai fita
tace Abban Aliya ina na kanwata? Yana jin
yadda tayi maganar yasan gulma ce kawai.
Yace ban siyo ba ki kyale ta kawai. Ta ce
gaskiya irin haka ba dadi ai sai ya zama rashin
adalci. Ya dan kalleta to ko zaki dibar mata ne.
Tuni ta hade rai kai ne hakkin ciyar da ita ke
wuyanka ai. Kuma nasan idan ka koma kila ya
tashi mai naman ko? Ba komai amma dai ka
rinka adalci. Yace naji kije ki kwanta ki kular
min da baby. Ta sake jindadi ta rufe kofa tana
tsalle da murna. Aiki ya fara kyau saura na gobe
ma.
Huzaifa yana mamakin hali irin na Fadila, ya
tabbatar da ita ce a wannan yanayin Aish
bazata nuna farinciki haka ba. Da sallama ya
shiga dakinta ya tarar bata ciki. Allah sarki Aish
yasan dakinsa ta tafi duk don kada ta nunawa
mutan gidan halin da suke ciki. Can gefen gado
ya hangota tana bacci akan abin sallah.
Zuciyarsa tayi masa zafi ya kara jin tausayinta.
Shiyasa Annabi SAW ya hanemu da daukar
mataki cikin fushi. Ya ajiye ledar naman ya
zauna a gefenta tare da dora kanta a cinyarsa.
Motsinsa ne ya tasheta tayi saurin mikewa tana
murza ido. Tana ganinsa ta soma kuka wallahi
ban san shine yazo ba. Cewa akayi nazo kana
jirana wayarka ba chaji kuma. Kamshin turaren
da take yini ana yi mata ya doki
hancinsa....bakinsa yasa ya hanata magana.
Sun jima a haka hawayenta bai dena zubowa
ba. Ya dago habarta da hannu biyu yana
kallonta...kiyi hakuri nayi kuskure da ban tsaya
sauraron hanzarinki ba. Kishi ne ya rufe min ido
tare da mamakin abinda ya kawo shi har nan.
Wani kukan yaga zata fara yayi saurin
rungumeta, gaba daya ya zaunar da ita akan
cinyarsa yace Aish I love you so much, bana
son tuna kin taba auren Fahad bare na ganshi.
Ya cutar min da ke sosai kokari nake na mantar
dake duk wannan mugun experience din. Tana
kukan tace kai kadai na taba so a rayuwata
baby. Idan ka kasa amincewa dani bansan
yadda zanyi ba. Duk wani farincikina ya
danganta da kai. Haka suka yi ta kara
jaddadawa juna so. Can yace wai kinyi wanka
yau kuwa? Tsami nake ji. Dundu tayi masa a
baya ba kaine ka sani kuka ba. Kuma wallahi
bana tsami duk turaren nan da nake yini a ciki.
Yayi dariya to kauri kike yi no wonder naji dakin
kamar ana girki da itace. Hawaye ta soma tana
kukan shagwaba ta tashi tana tura baki haka ma
zaka ce ko? Duk gyaran nan da nakeyi saboda
kai, to na dena kuma wankan ma na dena gaba
daya. Yana mata dariya yace ashe haka kike da
nauyi cinyata kamar ba a jikina take ba. Yana
murza wurin da ta zauna daga yanzu idan zan
rarrasheki daga nesa nesa zanyi. Kara shan
kunu tayi tana masa mita nima bazan kara zuwa
kusa da kai ba. Ta dauki mayafinta sai da safe
na dena zuwa dakin nan. Ya dago ledar kaza ga
wannan bari na cinye sai kisa a shara. Yadda
tayi murmushi ya burge shi ta dawo da sauri
wasa fa nake yi. Ai duk macen kirki a dakin
mijinta take kwana. Yayi dariya sosai sannan
suka zauna suka ci abinsu. Bayan sun gama
suka yi wanka ya janyota jikinsa suka kwanta.
Aish taji ya kirata a hankali. Naam babyn Aish
ta amsa masa. Wai sai yaushe za'a gama gyara
jikin nan? Naga ya gyaru sosai tun yanzu. Tayi
murmushi sai nan da sati uku. Dan murmushin
fuskarsa ya dauke ki manta da wani sati uku
don bazan bari ba. Wai baki san medically bai
kamata a rinka yawan shakar hayaki ba. Shi
kanshi turaren da kuke yi ba'a so yayi yawa
saboda kada yayi wa jiki illa. Aishatu ta gane
abinda yake nufi tace to ai kaga ba laifina bane.
Wato shi irin wannan gyaran idan ba'a jira an
gama ba to baci zaiyi. Jinsa kawai tayi ya kara
matseta cikin kunnenta taji yace wannan dai yau
zai baci gobe sai a sake wani. Tace to ai Anti
Sauda tace........maganar da bata sami damar
karasawa ba kenan sai da asuba.
Washegari tana kitchen wayarta ta rinka ringing.
Huzaifa da ke shirin fita asibiti ya dauka yaga
ko waye. Sunan Anti Sauda ya gani ya duba
time bakwai da yan mintuna. Sai kawai ya
dauka. Tana jin muryarsa ta gaishe shi sannan
tayi masa bayanin sakon Fahad. Yayi mata
godiya sosai ya fita kitchen wurin Aish ya sanar
da ita. Suna maganar text ya shigo da numbar
da ya rubuta musu. Huzaifa ya kwafa a tasa
wayar ya kira.
RASHIN GODIYA ✂ 50
Yanayin canjin fuskar mijinta yasa ta fara
tsorata ta kagu ya gama ya sanar da ita abinda
ya fada masa. Bayan sun gama yace mata ta
zai je wurin Fahad a hotel din da yayi masauki.
Aishatu ta ce kada ka je idan don nasan karshe
ranmu ne zai baci. Huzaifa ya shafi fuskarta
kada ki damu duk wanda ransa ya baci shi yaso.
Tace ban gane ba. Zaki gane bari nayi sauri.
Kafin ya fita ya kira wani abokin aikinsa ya nemi
alfarmar ya kama masa aiki kafin ya zo.
Fuskarsa a hade ya bi bayan Fahad ya shiga
dakin. A jikin kofa ya tsaya ya rungume
hannuwansa a kirji. Fahad tace don Allah ka
zauna Dr. Magana nake so muyi ta hankali.
Huzaifa yace nan ma ya isa. Fahad yace suit
yourself.
Fahad yace nasan ka sanni ka san wasu
abubuwa da dama akaina. Bayan rabuwata da
Aisha na so ta kamar inyi hauka. Kuma har
yanzu ina sonta. Huzaifa ya daure fuska abinda
ka kirani ka sanar dani kenan? No bashi bane
amma ka sani son da nake mata ne yasa zan
sanar da kai. A shekaru uku da nayi da matata
ta yanzu naso haihuwa sosai. Duk lokacin da
naje asibiti sai likitoci suce lafiyarmu kalau
lokaci ne kawai baiyi ba. A lokacin na rinka
tunanin yadda zanyi na rabaka da Aisha. Sai
watarana naji waazi da ya tayar min da hankali.
Ga tsananin mamakin Huzaifa hawaye ya gani a
idon Fahad. Nayi nadamar zama sanadin
zubewar cikin Aisha har sau biyu. Nayi roki
iyalina, iyayena da sauran yan uwana gafara
game da irin zamanmu da su. Aisha kadai ta
rage min da hakkin rai biyu. Huzaifa abin ya
fara isarsa. Kaga malam ni fa ba tarihin
rayuwarka nazo ji ba. Fahad yayi murmushi ni
kuma sai kaji tarihin zaka fahimci inda na sa
gaba. A halin yanzu dai na shiryu daga munanan
halaye na. Sai dai kwatsam wata rana wata
mata mai suna wasila ta kirani a waya. Suna
neman hadin kaina ne a rabaka da Aisha ni na
aura tunda sun sami labarin ina sonta. Sai a
lokacin Huzaifa ya zauna. Fahad ya cigaba tun
lokacin na amsa mata amma banyi niyar yin
komai ba sai da matarka Fadila ta kirani a waya
da wannan bukatar dai. Naji tsoron idan ban
amsa ba zata iya neman wata watar ko wani
mutumin shiyasa nazo. Tare da sannin matata
don ita ta bani shawarar yadda zanyi. Huzaifa
ya tashi tsaye kana son kace min fadila ta
sanka ne,wato sharri kake son kulla mata. Dama
nasan zuwa wurinka will be a complete waste of
time. Hotuna Fahad ya baza masa akan table
din gabansu. Wasu shi da fadila ne a wajen
makarantarsu Aliya. Sai wasu a gate din hotel
din,wasu kuma a kofar dakin. Jikin Huzaifa ya
soma rawa a sanyaye yace Fahad ka nemi
matata ne? Fahad yace ka kwantar da
hankalinka ko a da ni ba mazinaci bane. Magana
tazo muyi akan yadda zamu bata tsakaninka da
matarka. Ta yaya nasan gidan da Aisha take
jiya?
Huzaifa gumi ne ya jika shi lokaci guda. Wane
irin tashin hankali ne wannan. Ina Fadila zata
kai mugun halinta. Bata laakari da kullum tayi
sai asirinta ya tonu. Wannan yafi komai kure shi
tunda har zata iya kebewa a dakin hotel da
mutumin da ba muharraminta ba. Ya ce da
Fahad to meye next plan dinku. Fahad ya dauko
waya a gabansa ya kira Fadila yasa a speaker.
Tana dauka tace ,yauwa tun dazu nake jiran
wayarka, ya fita itan ma dreban gidan uwarsa
yazo ya dauketa. Huzaifa ya rike baki wai
uwarsa.
Fahad yace to yanzu ya zaayi?
Ta cigaba na gano gyaran jiki take zuwa. Na
riga na yanki key din dakin nata. Fahad da
Huzaifa suka hada ido. Jin anyi shiru yace
Fahad kana ji na?
Eh ina jinki yanzu ya zaayi na shiga dakin yadda
wannan mijin naku zai ganni.
Fadila tayi dariya kada ka damu. Kazo bayan
laasar sai na bude maka dakin. Zan tabbatar
yau ni na daukota ba shi ba. Daga nan sai ka
buya kada ka kuskura ka fito sai kaji muryarsa.
Idan da hali ka rungumeta ma komai ihunta.
Tana dariya fahad ya biye mata suka yi tare.
Huzaifa kirjinsa ya dafe zuciyarsa kamar ana
hura wuta. Fadila ta fi karfinsa yanzu mace me
irin halinta zaman aure ba nata bane sai dai
idan hali ya dace da na mijin. Huzaifa yace
Fahad meyasa ka zabi ka fada min gaskiya?
Fahad yace baka ji lokacin da na ce maka nayi
nadama ba? Da ban amince ba Fadila zata iya
neman wani. Dukkansu suka ajiye kishinsu a
gefe suka tsara plan din yadda zasu bullowa
Fadila. Ita wadda ake yi dominta bata san me
sukeyi ba. Tana can cike da farinciki tana
karasa gyara jikinta domin neman yardar Allah
da ta mijinta.
RASHIN GODIYA ✂ 51
Huzaifa ko aiki ya kasa zuwa saboda yanayin da
yake ciki. Duk cikin 'yan uwansa babu wadda
zai iya fadawa tayi shiru ba tare da ta sanar da
umma ba. Shi kuwa yafi son sai ya kashe
gobarar ma sannan za ta san abinda yake
faruwa. irin wannan sirrin kuwa ba abu bane da
zai iya fadawa aboki. Ciki ba don abinci kawai
aka yi shi ba, wani idan ya sani ma dariya zai
masa ace ya kasa rike mace. Daga karshe dai
office ya wuce amma ya sanar yau bazai iya
ganin marasa lafiya ba. Maaikatan asibitin sunyi
mamaki domin hakan ba halinsa bane. Bai dade
da zama ba sai ga wayar Fadila. Gabansa har
faduwa yayi ya dauka ya kuma yi kokarin nuna
mata komai lafiya yake. Sai da ta gama yi masa
hira tace Abban Aliya kaga wasila ce tazo nan
aka bugo waya yayarta ta karye a kafa. Na fita
rakata muka ga tayarta daya tayi paci. Naga
hankalinta duk ya tashi shine nake son in kaita.
Hmmm kawai ya ce, yanzu ba don yasan
gaskiya ba haka zata raina masa hankali. A fili
kuwa cewa yayi mal Habu ya cire ya daura
mata spare mana. Kukan wasilar yaji fadila ni na
tafi kawai don bansan halin da take ciki ba.
Fadila tace kaji ta ko duk a rude take. Huzaifa
yace to ba komai ki kaita. Allah Ya kiyaye gaba.
Fadila ta ajiye wayar suka tafa da Wasila. Tace
kai amma fadila mijin nan naki akwai matsi
sosai. Ni Kamilu bai isa na tambayeshi fita ba.
Fadila ta ce uhmm nima da bana tambaya,
zuwan shegiyar nan ne naga tanayi shiyasa na
fara. Sake tafawa suka yi sannan ta kira Fahad
tace yazo yanzu.
Basu dade ba kuwa sai gashi kamar yadda ta
fada masa kada yazo da mota bai zo da ita ba.
Ya kira ya sanar da ita yana bakin gate. Sai ta
fito ta ce Mal Habu ya duba mata baya tana jin
kamar motsi, kafin ya dawo ta shige da Fahad.
Wasila ta kare masa kallo tace gaskiya Fadila
na kyasa. Ko kadan bata ji kunyar yana jin
abinda ta fada ba. Fadila ta ce ke duk namijin
duniya ai yayi miki. Fahad yana jinsu dai bai
kula ba. Wasila ta sake cewa ita kuma Aishatu
duk mazan da ke sonta haka suke kyawawa in
dai bazaka damu ba Fahad ina son zama friend
dinka. Yadda take masa kwarkwasa ya bata
masa rai. Wasu matan basu san darajar da Allah
Yayi musu ba. Fadila dai ta dauki key din mota
ta rike mayafi a hannu. To zamu tafi zan
tabbatar ni na dauko ta. Ga dakin ka shiga na
hada maka da keys din falo da na daki. Yace to
nagode amma kuyi sauri. Wasila dai kamar kada
ta fita. Ta dade tana son Huzaifa ma amma
saboda Fadila take hadiye wa.
Ana yin laasar ta sake kiran Huzaifa ta sanar
dashi zata koma gida amma taga wurin yayi
kusa da inda Aishatu take zuwa za ta biya ta
dauko ta. Yace ai yau da wuri ta gama ta tafi.
Ina jin ta isa gidan ma. Amma dai nagode da
kike wannan kokarin na ganin kun daidaita.
Fadila dadi ya isheta dama bukatarta Aishatu ta
riga Huzaifa zuwa gida.
Huzaifa ya ajiye wayar ya kalli Aishatu da ke
zaune a gabansa tana sharbar hawaye. Idanunta
sunyi ja sun kumbura sai ajiyar zuciya take yi.
Yau bata gama gyaran jikin ba yaje ya daukota.
Ya gama yi mata bayanin yadda suka yi da
Fahad kenan Fadila ta kira. Kallonta kawai
Huzaifa yake yi yace Aish menene abin kuka
kuma? Bayan Allah SWT Ya fitar dake ba tareda
anyi nasara akanki ba. Tace hakane amma me
na tsarewa Fadila haka? Idan da Allah bai
kaddari zamanmu ba da tuni mun rabu. Tashi
yayi ya rungumeta yana ta rarrashi ni bana son
zancen rabuwa kinji ko. Duk bawan da ya
dogara da Allah kuma yake gode Masa a
kowane hali bazai tabe ba. Allah bazai dora
mana jarabawar da tafi karfin imaninmu ba.
Shiryuwar Fahad ai ba kokarinmu bane. Ina so ki
kara inganta imaninki ki kasance mai hakuri da
juriya sai kiga rahmar Allah tana bibiyarki.
Aishatu ta kalli Huzaifa tana murmushi tace
Alhamdulillah. Ya rike hannunta ko ke fa. Tashi
mu tafi gida.
RASHIN GODIYA ✂ 53
Kowa na binsu da ido ya kaita gaban
mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata
Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta
mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce
hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna
wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya
hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu
ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina
ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake
su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado
kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya
shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya
bazai mata kyau ba.
Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai
ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye
ana kallon kallo. Umma tace auta don girman
Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna
yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace
Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara
bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila
ta farko. Kowa da abinda yake fada game da
Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take
yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga
abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin
aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka
Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada
baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so
na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila
ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada
baki a kawo namiji dakin wata don miji ya
saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har
ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi
ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace
Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo
take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa
mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel.
Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata
duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma
ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke
faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah
Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki.
Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da
bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba.
Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila
ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo
nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta
soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu
wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya
gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki
uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada
yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami
kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame
masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son
auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka
har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga
Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne
don ku zama shaida saboda kada magana ta fito
ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake
zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don
Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya
ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice
kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya
dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa
ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan
duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab.
Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani.
Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri
ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba
Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don
Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga
cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya
ga Allah fa ba ta tsaya a cewa
ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya
dace ma kin nuna godiyarki.

Please Login or Register in order to submit comment