Reading BACCIN SO BY M SHAKUR Chapter 31 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

he s having wani feeling na wlh zai iya turining duniyan nan up side down idan har zai iya samin Amirah abun yanasa yawa ya gangara gefen titi yayi parking yadauki wayansa daya dauko daga gidan daya fito yanzun nan kaman yazare yashiga tattaba wayan baida lokacin neman contact na Marwan yashiga saka number sa sai yayi dialing amman har wayan yagama ringing ya katse ba a dagaba ihu yayi a mota yace  pick up the call, pick up the call you monster yana zaune a motan nan Marwan kawai yake kira yakira Marwan yakai sau"

30 Marwan bai daga ba saiya shiga turamai message.

" Dan gindin ubanka nine kadaka? Ni kama jina jina? Wait for me, wait for my comeback, Marwan we will"

"settle this score saina maka shegen duka da saika koma wajen uwarka Mami kana kuka ta lallasheka, and let me make this clear to you, Amirah is mine she belongs to me, wlh wlh wlh if you touch her, or"

"sleep with her, I will kill you Marwan ."

Turamai messege din yayi saiya jefar sa wayar jikinsa har rawa yake saiya kara kunna motan yaja kaman

"yazare saiya wuce gidan da aka bama Daddy a old GrA, parking yayi a kofar gidan dasauri ya tsaya gaban gate din yana dukan gate din kaga Saleem zaka dauka yazare, Maman Baby ne tafito anci gayu dan su yanzu duniya tamusu dadi tace  waye haka ke knocking kaman mahaukaci jama a tai wajen gate din tana lekawa daidai Daddy dabai dade na dawowa ba shima yana fitowa yace  dakata Sweetheart tsayawa Maman Baby tayi Daddy yazo saiya leka Saleem yagani wanda kallo daya yakai ya ganesa saiyace  koma ciki tabe baki Maman Vaby tayi takoma ciki abinta, bude gate din Daddy yayi dasauri Saleem yajuya yakoma motan yabude bayan motan yaciro akwatin daya hada dazu saiya dawo yace  Ina wuni Daddy dakemai kallo ganin kaman ya sami matsala ga kansa duk bandage yace  lafiya Saleem?"

Shigo shigowa Saleem yayi Daddy yajawo gate din yarufe yayi gaba Saleem na binsa yana jan trolly suka

shiga falo Daddy yasami waje ya zauna yakallesa yace  meke tafe dakai Dasauri Saleem da jikinsa ke

"rawa yaduka yashiga bude akwatin, bundle bundan na yan dollars yashiga cirowa yana ijiyewa agaban"

"Daddy akasa guda ashirin, sai yaciro takardun filayensa da motoci duka yashiga ijiye gaban Daddy jikinsa duk rawa yake, yace  duka wannan nakane Daddy inhar zakamin abinda nakeso da sauri Daddy ya gyara zama yace  ina jinka numfashinsa har wani karkacewa yake idanunsa na motsi ganin dukiya da takardun assets, yace  me kakeso Saleem? Dasauri Saleem zuciyansa nayin wani haske ganin yanda har yayi winning DDdy over yace  kasan rannan daurin auren nan banzo ba shine aka daura auren da kanina Marwan dasauri Daddy cikeda fadanci yace  ko kadan ban kaunar wannan likitan ni dama tunda yamin rashin kunya a asibiti Saleem yace  nima bana kaunarsa yanzu danya yaudareni ya auri wacce yasan inaso, abinda nakeso kamin yanzu shine inaso karaba auren! Dasauri Daddy ya kallesa dan baitaba hararo abinda Saleem keso ba, ganin yanayin Daddy yasa Saleem yace  nikeson aurenta! Diyarka ce kana iko karaba auren idan bakaso dan haka nabaka kwana uku kasa yasaketa karaba auren, nikuma nakama alkawari gabaki dayan gadona da share dina na duka na Kamapaninmu na gold zan baka gakuma wannan danake baka yanzu, Yayana bazai taba iya baka abin nan danake baka ba, inhar kasa yasaki Amira zan baka share dina na companyn mu namaka alkawari, Amirah kadai nakeso aduniya rayuwana"

ma zan iya badawa danna sameta!

"Daddy kallon Saleem kawai yake dayake mai kallon kaman yasami tabin hankali hankali, kaman baida"

"lafiya lafiya, koko tsabagen obsession ne? Tunda yake baitaba ganin kalan wannan offer da kalan dukiyan nan da mutum yake kokarin ya salwantar sabida kawai yasami Amirah mahaukaciya ba jikinsa har tsuma yake dukawa Daddy yayi yashiga daukan kudaden yana dubawa ko fake ne yaga original kudi ne saiya shiga kirga bundle bundul yana jefawa a akwati,  daya, biyu, uku, hudu, biyar& .. kirgawa yagama yi tsaf yajera kudin saiya dauki papers yana dubawa filaye uku a manya manyan waje dakuma motoci guda uku, ya kallesa yace  yaushe za a aikomin da motocin ? Wani murmushi Saleem yayi yaji yana son mutumin nan yace  ko anjima kakeso zansa akawo maka gyadamai kai Daddy yayi yazage jakan tsaf ya mikar ya maida akwatin gefensa yace  ko duniya zata hade sama da kasa zata kama da wuta saina kashe auren Amirah da Marwan na aurama Amirah kai, kwana ukun sunmin yawa bani address na inda zanga Marwan Saleem baisan takamaiman gidan da Marwan ke zama da Amirah ba yace  bansan gidan dasuke ba amman zan baka address na unguwan mu especially masallacin mu dole zaka gansa Abba yace  angama turomin awaya tashi katafi Son Dasauri Saleem yaturamai saiya tashi Daddy ma haka sai kawai Saleem yawani hugging Daddy yace  thank you Daddy, thank you Daddyyyy, dagayau kaine Daddyna Daddy yawani kwashe da dariya yanajin son Saleem sosai yace  ka tsani Marwan ko ? Gyadamai kai Saleem yayi yace  bafa asalin kanina bane, kanin matar Yayana ne, dan riko ne wani dadin news din Daddy yaji, Daddy ya gyadakai yace  aiko zan kartamai rashin mutuncin dayafi tozarcin dayamin a asibiti, sai yayi nadaman abinda yamin wallahi Saleem yace  we are team suka wani kashe shida Daddy, Maman Baby dataji komi itama tafito tace  nima ina cikin team din kuma zan taka maka rawan gani Saleem kai kunga dadin da Saleem yaji tafiyan da baiyi va kenan suka zauna aka"

shiga kulle kulle abinda za ayi.

TOHHH FAHHHH!!!

EPISODE

**

"Suna fita daga asibitin Saleem na tsaye bakin titi trying yatare abin hawa, yaga motan Marwan nafitowa"

"daga asibitin bin motan yayi da kallo yanajin abu na zuwanmai wuya, da ace kallo na kisa da kallon da Saleem yakebin motan dashi daya kashe Marwan, Marwan ya fizgi motan da mahaukacin gudu shima yawuce sa abinsa, hakan yakara kuntatama Saleem rai sosai, irin shi Marwan yakema abubuwan nan sabida yaga yau yaci lagonsa yadakesa zaiko gwadamasa shi dan iska ne bashi yaci wanda he will pay"

komu jima komu dade.

"Sosai Marwan ke sharara uban gudu akan titi, wani kalan tsoro Amirah takeji, gabanta na faduwa sosai,"

"gabaki daya atakure take cikin motan ko inda Marwan yake takasa kallo at all, kanta na kasa sai wasa take da yatsunta, ahaka har sukakai gida, Marwan yadanna remote gate din yabude yashiga da motan yayi parking, yakashe motan batare dayayi motsi ba bai kuma ce kala ba, dan kallonsa Amirah tayi for the first time sai kawai ta runtse idanu da gudu sabida yanda yamata wani kwarjini yakuma kara kyau, farin T-shirt ne ajikinsa dawata 3quater na common flag green kaman na sojoji, fuskansa yayi ja, idanunsa sanye dawani glass farare dasuka kara masa kyau sosai, gashin kansa yayi coils sosai kaman bai taje ba dayayi wanka hakama sajensa da dan karamin gemunsa, yakai kusan 1min a motan sai kawai ya yunkura yabude kofan motan yafito yawuce wajen kofa saiya tsaya tareda juyowa yama motan wani"

"mugun kallo dayasa Amirah taji kaman zatai fitsari ajiki, hannunta na rawa takai ta bude kofa tafito"

"ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta batare data kallesa ba, tamaida kofan tafito tafara"

"tafiya ahankali tana zuwa wajen, dudda yanda Marwan baiso yama daura idanunsa akanta amman kasa daurewa yayi, daura manyan jajayen idanunsa yayi akanta wani abu na fizgansa yana fada da abin dan he s trying his best ya danne any feelings na so dayake dashi akanta dan he s so damn angry with her, ya tsareta da idanu yana kallon kafafuwanta daga hijabin da ake gani abu yakara zuwa wuyansa sabida wani mugun fitinannen kishi, abun ya tsaya yamai katutu awuya, harta karaso wajen, sumsum tabi ta gefensa tashiga falon danya bude mata kofan daman ahankali, shima shigowa yayi kawai saiya maida kofan ya kulle kofan da key hakan yasa Amirah tajuyo ta kallesa, juyowa yayi yazare key yasa a aljihun wandonsa yawuceta kaman baisan tana wajenba yayi staircase yafara hawa Amirah tabisa da kallo yanda bai kulata ba, bai kalleta ba, yana abu kaman baisan wacece itaba ya tsayamata arai kaman ya"

tsaneta.

Abu taji ya tsaya mata a wuya ganin ko kallo bata ishesaba kawai saita fashe da kuka ahankali tazauna

"akan kujera awajen tana matsa hawaye, first of all batasan metayi ba exactly, Miemie ta taba cemata Ya Umar nada kishi to shima Ya Marwan nada kishin ne? Sabida tarike hannun yayansa? Ai mistake ne tadauka shine kayansa yasaka, mesa yake fushi haka? Kuma ita bazata iya mai magana ba tsoro takeji"

karya mata duka itama.

Tana zaune awajen gashi batai salla ba amman tsoron zuwa sama ma takeyi tashi tayi ahankali saita

"shiga bayin dake nan falon ta dauro alwala tafito tana kallon falonta dayayi kyau tana kokarin tuna gabas nan da nan tagane dan tayi salla agidan ai rannan saita fara salla cikinta namata ciwo na yunwa, sai kallon kitchen take ahaka tana zaune har la asar tasake zuwa tai salla abinta, jin yunwa kaman zai"

halakata yasa tamike tsaye ahankali tawuce kitchen data gani a wajajen dinning a falon.

Gab da za ayi bikinsu daga rannan da Ammi tace an mata aure suka fara koyamata girki da yanda ake

"amfani dasu gas, shiga kitchen din tayi saita tsaya jimmm, ganin gas din dake nan ba irin gas din dasu Ammi suka koya mata yanda ake amfani dashi bane, kusan burners 6 ne akan gas din ga buttons dayawa na kunnawa chunkushe waje daya wanda batasan wannene na wannan, wannene na wanchan ba, cire hijab na jikinta tayi ta ijiye kan daya daga cikin kujerun dayake zagaye a island na tsakiyan kitchen din, saita tsaya saikuma tajuya tawuce tashiga store na kitchen din, the first abu da idanunta suka gani is kwalin indomie dasauri tadauka tabude dan bama abude ba saita ciro indomie guda daya ta maida kwalin ta ijiye ta dauki egg guda biyu tafito tazo gaban gas din ta tsaya tana kalle kalle saitakai hannunta ta kunna guda daya tadaiji shuuu amman batamasan wani gas ta kunna ba, saita rufe garin rufewa ta"

"kunna another one kadan amma gas din yahau fita amman babu kara sabida kadan ta kunna, all this"

"while bata saniba ta tsaya sai lissafe lissafe take, saitasa hannu tadauki lighter na kunna gas din tarike a"

hannu takai hannunta ta murza another different gas yafara kara& &

Cikin bacci mai nauyi daya kwashe Marwan yaji warin gas dasauri yabude idanunsa yamika hannu

"yadauki glass yasaka ya kunna wuta yana tashi zaune, warin gas yaji sosai, kawai Amirah ne tafado aransa yana tuna the first abu dayaji tafadi this morning she s hungry, bugawa kirjinsa yafara baisan sanda yawani yaye bargo ya dirko daga gadon dagudu ba dagashi sai dan short ba singlet ko dogon wando jikinsa, yashiga saukowa daga stairs dawani kalan sauri yayi wajen kitchen daidai Amirah na kokarin kunna lighter, daga wajen yayi wani ihuuuu.  Amirahhhhhhhh! Awani kalan firgitce Amirah tajuyo daidai yataho dagudu kaman zaki ya fizgota zuwa jikinsa tawani fado cikin kirjinsa atsorace, ya karbe lighter hannunta ya jefar yakai hannu yana kukkulle gas guda biyu data bude yariketa gam ajikinsa yawuce yashiga bude window na kitchen din dan gas din yafita Amirah tadan saç1 kallon fuskansa he looks so damn worried and scared she could feel yanda kirjinsa ke bugawa gashi yarike gam protecting her with his entire life kaman yar baby dinsa kawai taji zuciyanta yawani narke yayi melting yabude kofan kitchen din na baya shima sannan ya tsaya awajen sai alokacin ya lura da yanda ya kankameta ajikinsa dasauri yasaketa ahankali Amirah takoma baya kanta akasa, cikin tsananin fushi Marwan yace  what are you doing in the kitchen? Kasa kallonsa tayi takuma kasa magana, tsawa yadaka mata.  Badake nake magana ba ? Dan dagokai tayi saita kasa kallonsa ahankali tace  yunwa nakeji indomie da 2 egg dayagani kan island yabi da kallo kirjinsa na bugawa cikin tsananin fada yace  bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso nayi da kaina?"

"What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu?? Ahankali Amirah tadago kanta for the first time takalli fuskansa jin maganganun dayayi that were shouting I love you Amirah I can t leave without you, hada idanu sukayi wani kunya Marwan yaji da maganganun daya fada da baimasan tayaya yafadesu ba, juyawa yayi dasauri strictly yace  leave this kitchen kafin ranki yabaci ahankali tajuya sumsum tawuce tafita, ya tsaya a kitchen din shi kadai har lokacin bugawan zuciyansa bai dawo daidai ba, kusan 5min sannan ya kunna gas din da Kansa ya ja tsaki yadauki pot yasa akan gas din cikin 5min yadafa mata indomie da boiler eggs, yasa mata a bowl yadauki fork yasaka yakashe komi yafito daga kitchen din dan dagokai Amirah dake falon tayi suka hada idanu dasauri tasauke kanta, ijiye bowl din yayi akan dinning kawai yawuce stairs yayi sama abinsa Amirah tasake binsa da kallo saita taso ahankali tazo dinning din ta kalli indomie daya dafa mata saita kara kallon sama wani sanyi taji aranta"

saitaja kujera tazauna ahankali tashiga ci maganganun dayayi dazu nadawo mata akai.

 bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso

nayi da kaina? What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu??

"Wani shauki taji ya lullubeta, he s angry but he s still very sweet and caring even though he is angry."

EPISODE

"Daki Marwan yawuce yashiga, har lokacin his heart was racing zuciyansa nata gayamai wat if something"

"yasameta dayaya zaiyi? He was so scared, kodayakai sama saida ya tsaya yakara lekota ahankali ta saman bene yaga takai indomie baki tadanyi murmushi kadan ya tsareta da idanu, wani kalan sonta yakeji a zuciyanta kaman zai halakasa, kokarin dago kanta sama Amirah tahauyi hakan yasa yabar wajen da sauri baiso tagansa, soyake yayi wanka yayi salla, baimasan ya akayi bacci mai nauyi yadaukesa ba, wayansa ne yahau ringing hakan yasa yakai hannu yadauka yaga Farida ne, hannu yasa yadauki wayan batare dayayi magana ba dasauri tace  Yaya muna kofar gida Mami tabamu abubuwa mu kawoma Ya Amirah dan jim yayi saiyace  okay cire wayan yayi daga kunnensa alokacin yaga text message from Saleem he knows Saleem so well da yasan yana bude text message dinnan ransa bac1 zaiyi kawai saiya ijiye wayan akan gado, yawuce closet dinsa yasa jallabiya saiya fito Amirah na dinning tanacin indomie ta yafito tadan saci kallonsa ko inda take bai kalla ba, yawuce kofa yasa key yabude saiya fita yabude gate, Farida da Faiza yagani da flask har biyu saikuma wayan Amirah, strictly yace  get in wucewa ciki sukai da sauri, shiya tsaya yana maida kofan yarufe suka shiga falo Amirah na ganinsu ta mike tana murmushi suma haka suka taho wajenta da sauri da flask din suna ijiyewa kan dinning Faiza tace  indomie kikece ga abinci mun kawo, wannan kazanki ne Mami tace ke kadai zakici dasauri Amirah tasa hannu takarvi karamin flask din tana budewa tace  Mami ta dafamin, girkin Mami dadi duk suna tsaya suna kallonta yanda take magana saita dago manyan idanunta ta kallesu tace  ku zauna muci tare tai maganan daidai Marwan na shigowa falon dan satan kallonta yayi sabida aya da maganan yafito straight daga harshenta was so unlike her, suna kokarin bata amsa Marwan yace  Kids dasauri suka juyo suka kallesa yau kowa is minding his business sabida ansan ransa abace yake, wani mugun kallo yamusu yace  kuzo kutafi wani iri Amirah taji wlh taso su zauna saiga hawaye yacika idanunta Farida tace  ga wayanki don t cry gobe ma zamu dawo gyadamusu kai Amirah tayi hawayen na suakowa takai bayan hannunta ta share suka wuce suka fita Marwan yarufe kofa yajuyo yawuce staircase harya fara hawa saiyadan kalleta yanda take share hawaye kaman zaiyi magana kawai saiya wuce abinsa, dago kai tayi ta ballamai harara tana turo baki saita bude kulan kazanta tadebi Kazan da romo sosai tazauna tafara ci dadinsa baima bari tagane Kazan magani bane tass ta cinye ta shanye romon saita wuce takai pates kitchen ragowan kazanta tasaka a fridge, shikuma dayan tabarshi a dinning tawuce tadawao falon bayan tasaka hijabinta ta zauna akan kujera tana danna wayanta tanaso takira Ammi da Miemie but bataso takirasu yana gidan, daganan tafarajin kamshinsa saukowa yashiga yi ya chanza kaya zuwa kaftan ash color riga da wando yana baza uban kamshi dan Satan kallonsa tayi kirjinta taji yana bugawa wani abu na fizganta tsabagen yanda yayi kyau looking very classy and expensive dasauri tadauke kanta ta kwanta a kujera tai lamoooo"

ko kallon inda take baiyiba yawuce kifa yasa key yafice tanaji yana kara kulle kofan da key jin bai dauki

mota ba yasa tadanji sauki danhar tafara tsoro ita kadai a gida an kulleta maybe masallaci zaije ko wajen

Mami saida taji fitansa saita daga wayan dasauri takira Ammi.

Ringing daya Ammi tadauka dasauri Amirah tace  Ammiiiiii tana maganan hawaye na cika idanunta

"kafin Ammi tamayi magana kukan data dade tana rikewa kawai saita fashe dashi cikin kuka sosai tace  Ammiiiiii nayi kewanki sosai dan Allah kizo ki daukeni ni wajenki nakeso nadawooo, kinji abu daya yayi capturing attention na Ammi yanda take magana tana kukan her speech sounds so eloquent anatse tace  Amirah dasauri Amirah ta tsagaita kukan tace  na am Ammi Ammi takara shiru sai anatse tace  meya sameki Amirah? Bata gane question na Ammi ba batasan in what context Ammi ke mata tambayanba amman ayanda Ammi tamata tambayan sai kawai tahau magana tace  Ammi Ya Marwan fushi yake dani kuma ba da gangan namasa laifi ba baya wani kulani ayanda take magana saitaji kuka ya kara kufce mata deep down she misses him so soo much, cikin kuka tace  yau bayan nayi salla nafito daman gidan Mami muka kwana  Gabaki daya taba Ammi labarin harda dukan dayama Saleem da yanda aka"

kaisu asibiti tace  shine tunda natashi sai inda aka samin bandage akaina yanadan min ciwo amman

yanzu nadena yanda da nakeji kaman cikin kaina na rawa naji yadena zafi kawai wajen kan yakemin

Wani abu Ammi taji a kirjinta abun yafi farin ciki farin ciki ijiye wayan tayi kawai saitai sujjada tadago

"tana share hawaywn daya fado daga idanunta tana murmushi sosai amman duk sai bata nunaba cus batason Amirah yazama distracted tace  ba kyau matan aure na yawo da kayan bacci bayan kinsan ba agidanku kukeba, maisa baki fito da hijabi ba eh, dole yaji badadi ai dole yayi kishi, yanzu abinda nakeso dake shine ki lallashesa kibasa hakuri dan turo baki tayi ashagwabe tace  salon yamin masifa baki Ammi tabude saitace  Amirah tsiwa kinsan mahaimmancin miji kuwa ? Dan shiru tayi kafin ahankali tace  Ammi ni banso madinga lallashin miji ina basa hakuri hakan yakesa sudingayin abinda sukeyi kaman"

yanda Daddy yamiki shiya bani hakuri ya lallabani!

EPISODE

"Wlh Ammi mutuwan zaune tayi jin kalaman da Amirah tafadi, so all this while ciwo yasa Amirah was the"

"way she is amman tana ganin komi dake faruwa tana recording akanta, did she just say bazata ba Marwan hakuri ta lallashesa ba sabida experience datake dashi na Babansu, she always watch the way"

"Ammi kena Daddy hakuri har dukawa take wani zubin tana basa hakuri Daddy yayita tsula tsiya, wani"

"dan tiny bangare na zuciyan Ammi saitaji ta yarda da abinda Amirah tace but then as a mother dole ka koyama yarka bada hakuri especially idan ita tai laifin it doesn t matter girman kai baida kyau inhar ke kikai laifi learn to say sorry hakan yana kara kauna a zamantakewan aure, akwai wasu misunderstanding da za a samu da zaki nade kafa kiki bada hakuri but in this case Amirah needs to say sorry, cikin hikima Ammi tace  karna karajin kin misilta mijinki da Babanku, Marwan mutum ne mai imani, hakuri, da kirki, and duk sanda mai hakuri yayi fushi daman fushinsu baida kyau kuma basu iya fushi ba, Amirah ke bakisan so ne yasa yake fushi hakaba wani yaganemai mata abun alfahari ne ai mijinki na kishinki haka eh, kamosa zakiyi ki lallashesa ki goge fushin daga zuciyansa kaman tacema Ammi tayaya zata kamosa ta lallashesa ta goge fushin daga zuciyansa amman kuma saita kasa kunya taji, Ammi tace  Mama Lami tace magungunan ki dasu taumin ki duk an samiki a fridge dasauri tace  wannan juice dinnan da Ya Miemie kesha? Ammi tace  eh shi dasauri ta tashi tana magana da Ammi tawuce kitchen aiko tabude ta gansu dayawa gora daya tadauk tabude tafara sha sunyi magana mai tsawo da Ammi had saida aka fara kiran magrib Ammi tamata sallama dasauri tashiga kiran Miemie, ringing daya Miemie tadauka dasauri Amirah tace  Ya Miemie ance na warke Miemie ta zaro idanu tace  Amirah Amirah Amirah mene dariya Amirah tayi tace  faduwa nayi yau a stairs kaina ya buge har hospital aka kaini tunda natashi I ve been fine inata magana fine tsaya tsaya zan baki labarin nan kinsan menene Miemie dake tsananin farin ciki tace  a a menene ahankali tace  kinga Ya Marwan ne ke fushi dani, nafadama Ammi wai nabasa hakuri Miemie ni banso inta lallaba miji haka Ammi ta lallaba Daddy tadinga cin wahala, ni yaya akeyi ko zan basa hakurin ma dan kadan zan basa dariya Miemie tayi tace  eh rudasu ake yanzu dai yaya yake miki fushin? Turo baki tayi tace  shareni yakeyi Miemie tace  to aiko kiyitamai abubuwan da ko bayama Allah saiya kulaki dasauri Amirah tace  me da me ? Miemie tace  shagwaba na masifa, kin fadi, kin buge, ihun tsoro irin kinga kyankyaso ko wani abu, kihanasa sukuni kawai kuma kiyita mammannamai nono bansan ya Marwan ba Amman kinga Ya Umar Nono na shine mumu point dinsa"

baya ganinsu ya kyale

"Ko fushi yake, kulle fuska Amirah tayi adan kunyace murya chan kasa tace  ni tsoro nakeji namai haka"

"sex ai zaimin kuma dazafi Miemie tace  dalla zafin sau daya say biyu ne, wlh kinga yanzu ni nadan fara"

"jin dadi, nakosa ma yadawo daga gareji muyi zaro idanu Amirah tayi kunya yasa tace  yaushe zakizo nan Miemie tace  zan gayama Ya Umar duk randa zai kawoni zan gayamiki gyadamata kai Amirah tayi."

"Miemie tace  yanzu jekiyi wankan dare kici gayu Gyadamata kai tayi ta katse wayan, ta ijiye wayan kan"

"kujera ta tashi tashiga bayi alwala tafara dorowa tafito tai salla saita kalli sama sai kawai tawuce dakin daya kaita yanuna mata kayanta nan ta_an1 wani yake nashi kawai tabude kofan ahankali tashiga dakin smells like him sosai ko ina tsaf tsaf bayin tashiga tai wanka tun safe yau sabida bala i sai yanzu take wanka, tafito daure da towel tana kamshi sosai tashiga closet tadauki manta abubuwanta daya nuna"

mata tashiga shafawa ta feffesa body mist na jiki sannan tadauki wani rigan bacci fari mai lace pant

tasaka ya rabbi sun zauna ajikinta sun mata kyau kana ganin boobs nata tasama sosai daidai ana kiran

isha i tai salla.

Koda akai sallan magrib zama yayi cikin masallacin yadauki Qur ani yafara karantawa ko zai denajin zafin

"abinda yakeji Alhamdulillah yasami natsuwa sosai ahaka akai sallan isha i aka idar yadan bata time kadan sannan yafito yana kallon gidansu yanaso yaje wajen Mami but he knows she s still angry gwara yabari gobe, tun daga nesa yahango Saleem tsaye gaban gate dinsa da kwalban giya a hannunsa ga karan taba

Please Login or Register in order to submit comment