Reading BACCIN SO BY M SHAKUR Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

folder yayi yarufe saiya taho ya tsaya gaban gadon daidai tarin na tsayawa hannunsa yasa yadauki black sock dinta dake gefen gadon batare daya kalleta ba yace  baki iya gaisuwa ba sai kallon mutane dayan hannunta takai tasa abakin tahada duka biyun ko tadanji dama daman abinda takeji cikin yar karaman very tiny bedroom voice din tace  ina kwana  how are you Ameenah? Ya amsa da very husky manly voice yana kallon fuskanta ganin wani katon pimple guda daya daya fito mata a kumatu wanda babushi jiya yana gani yasan kuma na menene, shiru tayi takasa magana, saiya sa mata safa a kafa without touching her skin juyowa tayi ta kallesa dukawa yayi saiya dauki canvas nata ya zazzage datti dake ciki yashiga samata yana kulle igiyan yasa mata Second one din saiya mike yakalleta dasauri tadena kallonsa yace  kinaso kiga Ammin ki? Dasauri tajuyo ta kallesa lumshe idanu yayi yabude yace  let s go dasauri tawani sauko daga gadon jikinta har wani tsuma yake dudda fuskanta is normal ba farin ciki nor bakin ciki saiya juya yayi gaba tabisa da sauri yabude kofa yajuyo yana jiranta danya lura bata iya tafiya da sauri ba ficewa tayi yafito yarufe kofan yawuce tana biye dashi har zuwa office nasa, bude kofan yayi Ammi tamike dasauri hakama Miemie Marwan ya matsa yana kallon Amirah yamata alamu data shiga dawani irin sauri ta shiga ganin Ammin wani tsuma jikinta yafara kaman tai shekara bataga Mamanta ba kawai saita wani irin kwasa da gudu tai wani tsalle kaman yarinya tawani rungume Ammi ta kankame Ammi gamgam tana manna"

"fuskanta sosai a kirjin Ammi kaman zatasha nono, batace anything but kalan hugging Mamanta datayi"

"says morethan enough, she misses mahaifiyarta, kankameta Ammi tayi idanunta na ciko da hawaye"

"sosai duk yanda Ammi taso kartai kuka amman takasa sai hawaye tana shafa bayanta tace  Amirahhhhh Miemie ta share hawaye tana kallonsu she s so happy taga sister ta, Marwan yadade yana kallonsu dazai shigo office dinne amman saiya maida musu kofan yarufe yawuce they need the"

time.

EPISODE

Ammi taciro Amirah daga jikinta da bataso ta barta taga yarinyar kaman ma takara kyau ne tana bin

"jikinta da kallo tundaga sama har kasa tace  Yammatan Ammi ta tsare Ammi Amirah tai da idanu tana kallonta batako kyafta idanu, Miemie tace  ni barakimin magana ba ko kallonta Amirah tajuyo tayi saita shige jikin Ammi dasauri tai lamo amman still tana kallon Miemie dake murmushi sosai, Ammi tacirota daga jikinta ta zaunar da ita cikeda kulawa irin na mahaifiya ta taba uniform din tace  wayake samiki kayan nan Amirah ? Ahankali tana kallon Ammi da yar karaman muryan tace  ni Ammi tace  an ina ? Ahankali tace  bayi Ammi tace  wanka fa waya miki ?ahankali tace  ni Ammi tace  da me da me nace babu kyau namiji ko mace su taba miki idan sun taba kiyi ihu ki gudu ko kiyi cizo sannan ki sanar dani ahankali Amirah ta nunama Ammi boobs da wajen fitsari, cikeda hikima Ammi tace  wata ko wani yataba? Girgixama Ammi kai tayi alamun a a, wani ijiyan zuciya Ammi tasauke tace"

" Alhamdulillah ,Alhamdulillah Ammi takai hannunta tadaura gefen fuskanta tana murmushi sosai hawaye naso su kara zuba amman ta tsaresu tace  bari Dr yazo saimu tafi gida ko sake hawa jikinta Amirah tayi ta kankame Ammi wlh kaganta zaka dauka nono zatasha she s super clingy to her Mom, Knocking kofan akayi Ammi na kokarin cireta taki fita daga jikinta tai lamo Marwan yabude kofa tashigo batare daya kallesu ba yamaida kofan yarufe Ammi tabisa da kallo kawai taji zuciyanta ya natsu da Dr ganin diyarta is fine babu wanda yayi kokarin cutar da ita a facility or take advantage of condition na yarta na rashin wayau da shirme haka, zama Marwan yayi ahankali Ammi tace  Doctor Marwan dan dago kansa Marwan yayi dan baitabama tunanin Ammi zata rike sunansa ba ko ta kirasa in full hakaba, baki Ammi tabude zatai magana but she s so emotional saitai shiru kafin tace sauke iniyan zuciya tace  this past kwanakin nan sune the saddest day of my life Ammi takai hannu ta sharce hawayen daya zubo mata hakan yasa Marwan yasauke kansa kasa Ammi tace  banda tunanin daya wuce is y ata fine? Taci abinci? Tana ina? Yana wajen wa? Yarinya na bata magana, what if wani ko wata take advantage of condition nata kaganta ba uhm ba uhmhum ba wayau ba& .. Ammi tai shiru sabida kuka dayake cinta, Ammi tasauke sauke ijiyan zuciya tace  naga diyata she is fine, healthy, babu abinda yasameta, she looks healthy than yanda takema a gidana, zzzabin yatafi nobody took advantage of her, she s well taken care"

"of and it s all thank to you Dr Marwan, dan haka nagode nagode, Allah yayi Albarka sannan Allah"

"yabiyaka nagode dakin duk akai shiru, ahankali Ammi tace  zan iya tafiya da ita ai ko Dr? Dan shiru"

"yayi saiya dago kansa yakalli Ammi yace  before that akwai maganan danakeso muyi dake saiya mike yazagayo yayi wajen kofa yace  Maryam keda Amirah ku biyoni dasauri Miemie tamike tana mamakkin yanda yakirata cikeda izza kaman yana kiran kanwarsa, ahankali Ammi tadaga Amirah daga jikinta tace  bi Miemie kuje zamuyi magana da Doctor gani nan zuwa awani kalan shagwabe Amirah takara kwakwume Ammi, Marwan na kallonta kai tsaye yace  come with Maryam Amirah ba musu tasaki Ammi ta taso, saitazo sai yayi gaba wani room yabude kayan wasa ne adakin da tv saiya bude yace  ku zauna anan shiga sukayi yamaida kofan yarufe yawuce yakoma office din Ammi tabisa da kallo tace  ina fatan komi lafiya lau Dr ahankali yace  eh, sit here yanunama Ammi kujeran dake gaban table hakan yasa Ammi ta taso tazo wajen gaban tazauna Marwan yazauna yana bude locket saiya ciro zanen da Amirah tayi daya linke yamikama Ammi yace  Ameenah tai zanen nan ahankali Ammi tasa hannu ta karba saita shiga warwarewa batamasan Amirah tai zane ba Ammi ta zana tsafa akasa ga Daddy yana kaimata punches da duka dasauri Ammi tarufe zanen takalli Marwan dake kallonta tace  Dr Amirah tai zanen nan? Bata taba zane a agida ba banmasan ta iya Zane hakaba ahankali Marwan yace  kids like her nada talents da dama da bazama kasani ba sai randa zasuyi zakaita mamaki, and yara irinsu nada wani irin memory da basa mance abu, she might not be verbal but she has many ways na communicating abu example this drawing datayi Marwan yayi shiru sai chan yace  I know this is your private life and baikamata nasani ba, but did you know what this means for yara irin su Amirah the day dasuka fara samun takardan zane su zana abin nan sai Marwan ya karbi paper ya warware yakalallo Ammi yace  it means this is matsalan dake damun Ameenah! I believe I can help Ameenah get better but I can t do it without your help dole saikin taka rawan gani a nema mata lafiya, please answer me sincerely yayi shiru kafin kai tsaye Marwan yace  idan mijinki na dukanki agaban Ameenah yakeyi?! Sauka tambayan yayi a kunnen Ammi kaman saukan aradu, bawai tambayan yana dukanta ko ba a dukanta yayi ba no kai tsaye yamata tambayan cus he s sure anayi ne sai Ammi takasa magana, ahankali Marwan yace  I am sorry I know my question might be somehow on your ear, amman condition din Amirah shine wannan, akwai cases na children dasukai withnessing domestic abuse, ana dukan iyayensu agabansu dayasa suka shiga depression, wasu suka sami ciwon hauka etc Marwan yace  I read history nata she was okay as kid but around 6/7yrs kika dawo da ita hospital dinnan akan she hardly talks, ko a school batason mutane, she s so clingy towards you batason ta barki even for a second, that means alokacin brain dinta yafara wayau tafara understanding someone is hurting her mother or her mother is always sad ko abu makamancin haka am I right? Lumshe idanu Ammi tayi hawaye na fitowa saitasa hannu ta sharce ahankali tace  Dr are you saying nine sanadin da Amirah take haka? Ahankali Marwan yace  not entirely but kin dauki 70% na dalilin dayasa she s like that Tashi Marwan yayi saiya wuce wani drawer saiya dauko wasu abubuwa kaman roba kaman ceramic amman all of them brain ne guda biyu yace  can you touch this hannu Ammi tasa ta taba na farkon Marwan yace  what did you feel? Tace  karfi yanuna mata dayan alamun ta taba ta taba tace  taushi wannan Marwan yace  good I want you to picture brain na Amirah as mai taushin nan Ahankali yace  yawanci a matsalan kwakwalwa duk wanda zakiga yakeda tabun hankali kokuma wani matsala na kwakwalba abu daya zuwa biyu ko uku ne, na farko akwai heredity inhar a danginka kunada mai ciwon hauka so likely a lineage naki ko family naku akwai Wanda zai dauka, sai nabiyu family, family plays a big role good or bad a ciwon hauka now this is inda Ameenah tashigo, don t forget nace ki dauki brain na Amirah as soft one dinnan, Allah yana halittan"

"mutane with different features, akwai mutane masu taurin rai, taurin zuciya karfin hali da sauransu,"

"akwai mutane masu sanyi zuciya, hakuri, peaceful marasa damuwa, Example now Amirah and Maryam"

"are siblings amman Maryam looks tough a inda Amirah take, Amirah is a child dakika haifa that s so soft consider her an egg, she s so dalicate abu kadan zai iya tada mata da hankali sabida haka Allah ya yota, that girl loves you more than anything and all of a sudden tana yar karaman nan maybe she witnessed kullum mahaifinta ke dukanki her little delicate brain couldn t take it and boom Marwan yadauki brain din ya wurga a kasa saiya fashe ga abubuwan brain din sun tarwatse Ammi takalli abin Marwan yace  this is brain na Amirah, her brain doesn t function well sabida she s traumatize with abinda take gani a g1da saisa she doesn t act normal, ganin mahaifinta triggers her anxiety, she s always clingy towards you cus she feels that s her own way of protecting you idan tana jikinki nobody can hurt you babu wanda zai taba mata Mama, she s scared, afraid of mutane she feels kaman za a daketa they might hurt her yanda ake miki, gani mutane da yawa na daga mata hankali, she s constantly not at peace, she s always sensing danger around duk inda take, hallucinating it, she s never at peace saisa bacci kemata wahala koda yaushe she s thinking or imagining you might be in danger, she s sad from abubuwan dataga ana miki saisa she grew up not to know yanda ake smiling ko wani abu her face is always straight da sauransu, low speech tone, her voice is always low, she hardly talk, very attach to you dake kadai take yarda aduniya, all this are signs na Schizophrenia spectrum disorder, wanda particularly trauma during childhood, can disrupt healthy brain development and trigger symptoms na schizophrenia, that s why kike ganinta she s not a normal girl as she should be kaman sauran yara yammata of her age duk yanda Ammi taso ta daure takasa tafashe da kuka sosai gaban Marwan, wlh da gaske ne ilimi ba karya bane, bata taba sanin cewa yaro yataso yana ganin fadan iyaye, dambe ko ana dukan mahaifansa yakansa yasami trauma dahar kwakwalwansa zata buga ba sai yau, brain na kowa daban akwai wanda baida karfin zuciya da abu kadan koda tsoro ne zaisa kansa ya tarwatse, Ammi tabasa tausayi saiya sauke kansa kasa yayi shiru, Ammi takama bakin hijabinta ta share fuskanta tace  bantaba sanin i could be the reason why diyata is like this ba sai yau Doctor and it breaks my heart so so much Ya Allah! Ninaja y ata is like this Ammi ta share hawaye, da kyar tai shiru muryanta yayi rauni sosai tace  Doctor Marwan can she be fine? Ana warkewa ? Ajiyan zuciya Marwan yasauke yace  lemme answer you as a Muslim cewa duk cuta nada magani banda mutuwa da tsufa so yes, as a Doctor kuma idan mutum yakamu da schizophrenia ba a warkewa amman ana warkewa ahankali yace  what I mean by ba a warkewa shine inhar zata koma tacigaba da ganin mai dukan ki ko ana dukanki still you are in pain or you are sad she will always be coming back to square one, she will not be fine, ana warkewa idan har an kiyaye duk wani abu dazai dinga triggering anxiety nata, if you re the problem you need to be in a space with her dazata tabbatar cewa you are 100% safe and happy hakan zaisa she will be relax and calm tafara sakewa, then in my side as the Doctor I will take my part na giving her therapy, teaching her how to manage her anxiety, how to overcome her fears dasauransu, your daughter have high chance of getting better she s still young she s just 20, zata warke and act like any other kids kawai yawan magana hira da sauransu sune ahankali ahankali zatazo ta saba da yi Ammi tai shiru sai chan tace  it s all my fault and kome zanyi zanyi dannaga Amirah tasami lafiya, akwai bukatan ta zauna a asibiti? Gyadamata kai yayi yace  yes I want to monitor her for 21days that s 3weeks and see progress chat nata, in those days inaso ki dinga zuwa ganinta after every 3-5days, before yanzu kitafi talk to her and kigayamata kinaso tanemi lafiya taji sauki, what I mean is for the first time I want you kiyi magana da Amirah kaman kina magana da an adult not yarinyaShe understands things sama da yanda kike tunani, just talk to her, and pray for your"

"daughter s health addu an mahaifiya babban abune, pray for her to be strong minded, tazama yarinya"

"that can live and depend on kanta even without you being there, just pray hard kibarma Allah komi "

"Ammi tadade tana kallon Marwan dake magana gabaki dayan rayuwanta bata taba ganin matashi ko likita mai hikima daya bata lokaci yamata bayan1n rashin lafiyan Amirah, sannan yakaranci Amirah yagano matsalan Amirah like this doctor right here for the past almost 20yrs kenan, kawai saitaji Marwan yashiga zuciyanta sosai, ahankali tace  nagode Marwan nagode kwarai, Allah yamaka albarka gyadamata kai saiya mike yace  go and meet her wucewa tayi yayi Ammi ta mike tana bin Marwan da"

kallo yabude kofa ya tsaya Ammi tazo tawuce sannan shima yafita yakai Ammi dakin.

WHAT DO YOU GUYS KNOW ABOUT CHILDHOOD TRAUMA???

"ITS VERY BAD YARA KANANA SUNA GAN0N IYAYENSU NA DAMBE KO FADA, PLEASE PARENTS TAKE NOTE"

AND NEVER TRAUMATIZE ABINDA KIKA HAIFA!!!

EPISODE

Budema Ammi kofan dakin dasuke ciki yayi yahada idanu da Amirah datai lamo ta kwanta ajikin Miemie

"kaman itace kanwar Miemie, Miemie kuma itace yayan, Miemie na playing game da wayanta na candy crush Amirah na kallo, kana ganinsu kaga siblings dakeson juna dakeda hadin kai, inhar babu Ammi to tasan Miemie, idan kuma akwai Ammi, Amminta kadai tasani, hada idanu dasukayi yasa Marwan yadauke kai yawuce yana rufo musu kofa Ammi ta shigo dakin, ahankali Amirah tacire idanunta daga kofan ganin Ammi ta tashi daga jikin Miemie Ammi tazo ta zauna zata shiga jikinta sai Ammi tace  tsaya tsaya Amirah, magana zanyi daku dukanku especially ke Amirah Amirah ta kalli Ammi asanyaye, Ammi tadan sauke ijiyan zuciya maganan namata nauyi sosai abaki amman ta tattaro duka natsuwanta tace  hospital ba shine wajen daya kamata nayi irin maganan nan daku ba amman dole anan zanyi ta da ku cus is very important Ammi tasakeyin shiru, saitace tana kallon duka yaran tace  Amirah bata gama cika shekara daya aduniya ba mahaifinta yarasu ta sanadiyyan hatsari dayayi! Ammi tai shiru saita kalli Amirah tace  Babanki was hardworking and he s doing very well, baiyi makaranta kaman Yayansa Baban ki Miemie ba dan Babanki dan boko ne, sannan shine kannin Babanki, trailer yake tukawa yana zuwa su lagos da sauransu ahaka Allah yabudamai yasai nasa trailer yafara tafiya da ita kafin yarasu yanada trailer guda uku tasa ta kansa, gidan mu dinnan nasa ne, da motoci biyu wanda an saida Babanki Miemie yasai sabo da kudaden, da sauran kudin gadon ki duk yana wajensa Ammi tai shiru saita sauke ijiyan zuciya tace  bayan Babanki ya rasuwa tun kafin nagama takama Babanki Miemie yaje yasami Umma ta"

"kafin tarasu kan zai aureni sabida ke marainiya, menene, menene, Umma ta yarda da hujojin daya bayar"

"dudda raina bai soba amman da Umma tamin bayani nima naga gaskiyan ta, mace ce diyata, bakowani"

"namiji zai yarda najemai da yarinya ba, sabida ke na yarda na auresa badan ina sonsa ba ko wani abu kawai Umma tadage sabida tagansa babba yanada hankali, ga ilimi zaiyi kasuwanci da gadonki kudin hayayyafa duba da iliminsa menene menene itada yayana dai saida sukasa nai auren, tunda nai auren banjin dadi, gashi immediately saina sami cikin ki Miemie, saisa dake da ita shekara dayane banbancin ku Ammi tai shiru duk tana kallon yaran dake kallonta tadan fuzar da ijiyan zuciya tace  cin mutuncin yau, daban na gobe daban Amman ina hakuri na daure ganin Allah yariga yabani yara mata da kansu yake daya to ya zanyi idan ban hakura na zauna ba? Natafi wazai kulamin da ku Maman Baby ko ganinku bata kaunar yi, banda komi, gadon duka ya amshe yana hannunsa, nasan kun riga kun sani mahaifinku mutum ne mai saurin kai hannu, so yakan dokeni tai maganan tana kallon Amirah dake kallonta batako kyafta idanu, saita kalli Miemie ahankali tace  nasha tunani da dama but among reason dake hanani daukan mataki harda ke Miemie, nakanyi tunani idan nabar gidansa aurenki fa? Nine mahaifiyanki I need to stand akanki na shirya ki na koyarda ke zaman gidan miji, yaya kenan? Ammi tai shiruu tace  as yarana banda abokan shawara ayanzu sai ku, ko yayana ban sanar da shi abin nan dazan fada muku yanzu ba sabida bazai barni ba, kunakeso na sanar sabida kune hakkin ku ke kaina Ammi tai shiru kafin ahankali tace  inaso na rabu da Babanku auren mu yakare gabaki daya kun yarda? Duk sukai shiru suna kallonta, Miemie ce ta iya breaking silent din tace  Ammi kika rabu da Daddy yazakiyi? Ina zamuje? Yaya baida kudi balle muje gidansa, I m sure Daddy bazai taba baki gadon Amirah ba har gidan ma dudda gidan Amirah ne ina zamu? Murmushi Ammi tayi tace  banson gadon yarike, gadon nata ma duka yarike, akwai wani fili da Baban Amirah yabani tun yanada rai, Yaya naba alokacin ya ijiyemin takardun suna wajensa zan sa adaga filin asa akasuwa konawa na samu zansai karamin gida haka abarayin unguwan su Yayana, sai na miki siyayyan kayan daki dan nasan narabu dashi zai iya cewa bazai siya miki komiba, na rike na neman maganin da asibitin Amirah, sai na ja jari nakama wata sana a sabida na iya kula da Amirah in sha Allah, kun yarda? Ahankali Miemie tace  na yarda Ammi, Ammi you re a good woman, Daddy baya sonki at all, babu amfanin zama da wnada bai sonka, sabida mu baikamata kiyita cutuwa ba, I know halin dana shiga rannan dakika sume akasa, I m with you and I pray Allah yasaka miki da abu mafi alkhairi, sannan Allah yabiyaki hakurin dakikayi all this years sanadiyan mu Ammi ta lumshe idanu tace  Ameen Ameen, thank you Maryama na saita kalli Amirah tace  kin yarda na rabu da Daddynku Ameenatu? Bazai kara tabani ba, he will not have power over me, zamubar gidansa and live far away kinason haka ? Gyadama Ammi kai tayi alamun eh, murya chan kasa yar karama kaman mai tsoron magana tace  I don t like him murmushi Ammi tayi saita kama hannunta tarike tace  kinsan menakeso kimin yanzu Ameenatu na? Girgixakai Amirah tayi alamun a a, Ammi tace  I want you to stay here kiji sauki completely, Dr Marwan is a good Dr, inaso ki sami lafiya Amirah, kizama daidai dakowace diya mace sa an ki, kafin nan nikuma da Miemie munsai sabon gida, mu koma sabon gida, Daddy ki will never touch me again, nor beat me, or make me sad, we will always be happy, sannan muyi aure da bikin Miemie, zan zo jibi, upper jibi sainazo na daukeki mukoma sabon gidan mu just me and you da Miemie ko kinason haka ko? Tadade tana kallon Ammi saita gyadama Ammi kai alamun eh, Ammi tace  kidinga bude baki kina magana, biggest buri na aduniya is naga kin warke, inhar kin warke I will be very happy babu abinda zai kara damuwa, kinason Ammin ki ta kasance cikin farin ciki? Gyadama Ammi kai tayi alamun eh, Ammi tace  naganki kin warke shine zaisa naji farin ciki, promise me you will be fine daga yanzu tunda ba Daddy ? Ahankali ta gyadama Ammi kai tace  I promise murmushi sosai Ammi"

tayi tace  toh bari nakama gashin nan ahankali zan miki kinji gyadama Ammi kai tayi Ammi ta kwantar

"da ita akan cinyanta tafara mata manya manyan kalaba, gashinta tsantsi, wuraren 12 Ammi tagama saita"

"maida mata hulan goshinta yadan fito tayi kyau, Ammi tace  muje toh Ammi na rike da hannunta suka fito daga dakin daidai Saleem na saukowa daga sama ward nasu, he s feeling very sick today, sai amai yake gawani kalan tunanin Amirah daya addabesa, baisan yarinya ba, baimasan sunanta ba amman ko kulle idanu yayi ita yake gani wlh, ganinta tareda wata mata dayana gani yasan mahaifiyanta ne saida gabansa yafadi, gawata yarinya da kusan kansu daya da Amirah, she look a bit older or bigger than"

Amirah ma.

"Knocking yaga Matar tayi suka tsaya, muryan Marwan sukaji a nutse daga ciki yace  come in bude kofa"

Ammi tayi ta shiga kaman Amirah taji ajikinta ana kallonta dan dago idanunta tayi karaf tahada idanu da Saleem daya tsaya chak yana kallonta dasauri tadauke kai kirjinta na bugawa sosai itada Miemie na shiga

cikin office din.

"Marwan na magana dawani male patients ne, daidai sun gama su Ammi suka zauna patient din yafita,"

"Ammi takalli Marwan tace  Dr zamu tafi Amirah zata zauna anan kuma tayi alkawari zata dinga shan magani dan ta tsani magani, sannan zata dinga jin magana, bazatai komi dabe dace ba ko Ameenatutu nah ? Gyadama Ammi kai tayi tai lamo jikin Ammi kaman marainiya, Ahankali Marwan yace  that s okay Ammi tace  akwai wani kudin da za a biyane? Cikeda girmamawa yace  no babu Ammi tace  to shikenan bari muje, tashi muje Miemie mikewa dukansu sukayi harda Amirah dasaurinta Ammi zatai magana , calmly Marwan yace  sit down Ameenah komawa Amirah tayi ta zauna amman tai tsuru tana kallon Ammi da Miemie dake tsaye, Ammi saita bude jakanta tabata wata yar leda dake cikeda snacks harda cincin tace  kiyita ci kinji zanzo jibi i promise kinji yarinya na gyadama Ammi kai tayi jikinta duk yayi sanyi sai Ammi kawai tajuya dasauri tafice cus wani abu yazo mata wuya kaman tai kuka dasauri"

Saleem yaboye awani lungu ganin mahaifiyar yarinyar tafito tana tafiya dasauri.

Daidai Miemie dake waigowa tana kallon Amirah idanunta yacika da hawaye zata fita itama Marwan

"yace  Maryam dasauri Miemie tajuyo bakinta nadan rawa tace  na am

Please Login or Register in order to submit comment