da ƙyar take taka ƙafafunta.
Cikin mawuyacin hali takai gaban motar ameerah ta buɗe ta shiga taja aguje tabar harabar hotel ɗin wanda hakan yayi dai dai da sanda ake ta faman ƙwaɗa kiran sallar magariba.
Cikin rawar jiki ya faɗa saman faffaɗan lafiyayyan gadon dake ɗakin hannunshi duk suna zube a ƙasan mararshi yana shafa kwantaccen gashin dayay ma wajan ƙawanya idanunshi lumshe suke bakinshi na fitar da zazzafan huci wanda ya gauraye da zazzafan numfashin dayake ta faman fita da sauri da sauri duk irin uban kiran da Basmah ke mai acikin wayarshi bai sami zarafin ɗauka ba, Sabida yadda jikinshi yake a mace sakamakon waccan yarinyar data so kunno mai cajin batir ɗinshi.
Hancinshi har yanzu yana manne da wani irin sihirtaccen ƙamshin turarenta data bar mai wanda bai taɓa ji ko ganin turare mai kamshi kamar nata ba.
Wata irin lallausar fata gareta wadda take tamkar katifa dan tsabar laushi wanda laushin nata ba'a iya fatar jikinta ya tsaya ba har ma da kyawawan laɓɓanta datai nasarar jefasu cikin bakinshi.
Da wata irin kasala ya miƙe yana mai dafe sirrin girmansa data miƙe take neman agaji, A hankali yake taka ƙafafunshi har ya isa bathroom ruwa mai ɗumi ya haɗa A bathtube nan da nan ya shiga gasa jikinsa da ruwan sabida wani shegen zazzaɓi dake neman kawo mai bara, Kafin ya kammala ya ɗauro alwala ya fito agurguje ya sanya fara ƙal ɗin jallabiya yayi ma kanshi ɓarin haɗaɗɗan turarenshi kana ya shinfiɗa sallaya ya soma gabatar da sallar cike da nutsuwa har ya idar anan zaunan yayi azkar haɗi da karanta suratul baqrah wadda ya ɗauki tsayin lokaci yana karatun bayan ya kammala ya shafa kana ya miƙe domin gabatar da sallar isha'i wanda lokacin daya ɗauka yana karatu shine yakaishi har zuwa isha'i yana idar da sallar isha ya kuma bada nafila raka'a biyu ya jima yana addu'a cikin sujjadarshi ta ƙarshe kafin ya ɗago yayi sallama ya shafe jikinshi da addu'a tashi yayi tare da ninke sallayar gami da tube jallabiyar jikinshi waya ya kira da akawo masa Coffee.
Kana ya ƙarasa gaban gadon ya ciro laptop ɗinshi a chraging ya kunnata ya cigaba da aiki da ita har sanda akai mai knocking ya miƙe tare da raɓewa jikin kofar batare da mai miko mai coffeen ya ganshi ba ya zira hannu ya amsa ya mayar da ƙofar ya rufe.
Adai dai sanda ze koma wajan zamanshi yaga wayarta watse a wajan tsaki yaja tare da tsugunnawa ya ɗauka ya kunnata ya koma mazauninshi still aikin gabanshi ya cigaba dayi akan shari'ar daze gabatar a gobe, Gefe guda yana shan coffe wanda zafinshi ke saukar mai da kuzarin daya rasa a ɗazu
Bai kammala aikin ba se wajan taran dare sannan ya kashe laptop ɗin ya aje cup ɗin coffee ɗin a gefe ya mayar da kanshi saman pillow idanun shi na hasko mai kamannin yarinyar ɗazu........."Ina son ka! kalmar data ke mai yawo a kwanyar kanshi kenan wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce dazata iya furta kalmar so agareshi babu tsoro? watsar da shirmenta yayi tare da ɗaukar waya ya kamo numbern Amminshi duk da tarin kiran basmah daya gani amman seya share a wannan karon jin kewar ammi yake wadda ya jima bai jita ba, Jiki na rawa yake danna mata kira kuma a wannan karon yaci sa'a ta ɗauka cikin cool vioce yake gaisheta kafin tafara masa nasiha cikin tsanani da shauƙin soyayyah irin ta ɗa da mahaifi tsayin lokaci suna magana da ammi har sukai sallama zuciyarshi fes ya miƙe ya ɗauro alwala ya kashe ƙwan ɗakin bayan yayi addu'a ya kwanta ba jimawa bacci yayi gaba dashi sabida akwai tarin gajiya atare dashi.
Allah kaɗai yakai Ummul khairi Gidansu lafiya tana rangaji ta kashe motar tare da daddafawa da ƙyar ta ƙarasa cikin gidan nasu wanda ya koma kamar wata kasuwar mata banda kiɗa babu abin da yake tashi daga tsakar gidan mata ne birjik wasuma daga su se pant da bra suke faman tiƙar rawa cikin sautin wakar data cika gidan.
A hankali take dafa bango tana zubar da hawaye ta ƙarasa ɗakinsu wanda harta kai ga ɗakin babu wanda yasan data shigo ma bare a tanka mata.
BARIKI KENAN GIDAN KAZO NA ZO!
Duhu dumɗin ɗakin babu haske alamun ameerah bata ma ɗakin ahaka ta lallaɓa ta aje mata key ta kuma lallaɓawa ta ɗauki ruwa da dafe bango takai bayin tsakar gida ta kama ruwa haɗi da ɗauro alwala a zaune tayi sallah sabida yadda zazzaɓi da zafin jiki ke damunta ahaka ta zauna ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka! idanunta jajir fuska jajir kamar mai afolo har lokacin isha'i yayi ta tayar anan saman dardumar bacci ya kwasheta wajan ƙarfe goman dare ameerah ta shigo ɗakin tana furta kalmar.
"washh yau fa kayana sunci ubansu! ke ummul yada bacci ga kaza na siyo mana"
Jin shuru yasa ta tsugunna ta tayar da ita wadda har lokacin zazzaɓin bai saketa ba da rarrabe tahau saman gado taja blanket jikinta nata karkarwa wahalallan baccine yayi gaba da ita.
Duk irin kiran da ameerah keyi mata bata iya farkawa ba haka tai ta baccinta wanda bata farka ba se asubahi.
Da ƙyar ta yunƙura tayi sallah wadda da ƙyar ta gabatar da ita haka ta takure a gefen gado tana rawar ɗari.
Ameerah bata farkaba se wajan goman safiya ganin ummul rakuɓe tana ta mayar da numfashi yasa taɗan tsorata tana furta.
"Ke ummul lafiyarki?"
Girgiza kai ta shigayi.
"Bani da lafiya amerah kaini gidan Hajjah seki je gidanmu ki gayama Bamu kice mata bani da lafiya jina ke kamar zan mutu"
Tafaɗa tana mayar da numfashi.
"a,a ummul bara na kaiki hospital"
Girgiza kai tayi wanda hakan yasa ameerah ta gane gida take so don haka da sauri tayo alwala rana gatsal tai sallar safe ta zira katon hijab bayan ta tarairayo ummul jikinta ta ɗauki keyn mota suka fita.
Motsi kaɗan ummul tace"washhh amerah kimin a hankali"
Wanda hakan ya tabba tar da tai muguwar buguwa a ƙugunta.
Da haka suka shiga mota domin nufar inda ta buƙata................
Barrister Aliyu Ali Dikko kuwa se.........
*Ada littafin naira 500 amman yadda wasu ke bina pc suna neman alfarma akan na barshi yadda na saba yasa na barshi a 300 kamar yadda na saba saka farashin ko wani novel nawa idan ina posting sabida haka wannan karon babu wanda zan bawa ta sp ko vip ko inna gama complt, iya normal grp 300 kaɗai zanyi sabida insha Allahu zanyi typing da iya yadda Allah ya horemin na tunani da basirata insha Allahu littafin baze ɗauki lokaci mai tsawo ba zan gama shi, sabida haka duk mai son ya biya kuɗinshi don ayi tafiyar dashi ga hanyar biya nan a ƙasa amman pls bana son katin waya*🙏🏻✍🏻
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218
*Fauzarh's Organic Skin Care*
*INSHA ALLAH YAU ZAMU FARA TRAINING ƊINMU DA MISALIN 8:30pm DUK MAI BUƘATAR SHIGA TAMIN MAGANA NA BATA ACCOUNT NO DA ZATA TURA KUƊINTA.*
_Ina kuke masu buƙatar koyan Sabulai, Creams, Oil, Scrub,?? Ga fa dama ta samu gareku, da kuɗin ki ƙalilan zaki koyi abubuwa da dama, domin yanzu wannan sana'ar tana ɗaya daga cikin abubuwan da kasuwarsu ta ke ci, ke dai maza ki garzayo wajen FAUZARH akan farashi mai kama da kyauta akan dubu ɗaya(1k) kacal za ki koyi abubuwa kamar haka👇_
*_Da farko zanyi bayani akan skin care, yadda za ki san kalar fatarki da rukunin da take. Sannan zan yi bayani akan Menene molato. Aikin molato a jikin fata. Yadda ake awo da muhimmancinsa_*
*YADDA AKE HAƊA SABULAI.*
1- Yadda ake molato body soap.
2- Yadda ake lightening black soap.
3- Yadda ake whitening black soap.
4- Yadda ake Acne/pimple set.
*YADDA AKE HAƊA OIL'S.*
1- Yadda ake carrot oil.
2- Yadda ake coconut oil.
3- Yadda ake molato oil.
4- Yadda ake pink lip balm.
*YADDA AKE HAƊA CREAM'S.*
1- Yadda ake molato body cream.
2- Yadda ake molato face cream.
3- Yadda ake molato scrub.
*BONUS*
Yadda ake haɗa shower gel.
Yadda ake haɗa papaya molato soap.
Sannan zan sanar daku inda zaku samu kayan haɗin duk garin da kuke.
*Domin neman karin bayani a tuntu6eni ta wannan no👉🏼http://wa.me/+2347065012071*
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ 𝐔𝐁𝐄𝐄𝐑𝐀 🔥🔥: *BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
007
Ƙarfe 4:30am ya farka bakinshi ɗauke da addu'ar tashi daga barci ya ziro da santala santalan ƙafafunshi zuwa ƙasa tare da miƙewa tsaye, yana mai yamutsa fuskarshi wadda take nuni da baccin nashi bai ma ishe shiba agurguje ya faɗa bathroom ya haɗa ruwan ɗumi ya watsa ajikinshi tare da ɗauro alwala.
Ya fito gami da shinfiɗa darduma ya soma gabatar da raka'atul fijir seda ya duba time yaga lokacin shiga masjid yayi sannan ya miƙe ya gabatar da asubahi bayan ya idar ya soma rera karatun alkur'ani mai girma wanda inba tsakanin jiya da yau ba ya ɗauki lokaci mai tsayi baiyi karatun kur'ani ba kuma Alhamdulillahi tun jiya daya karanta baqrah yaji daɗin azuciyarshi hakanan yau ma dayake karatun nan baƙaramin daɗi yake jiba.
Seda ya karanta shafi biyu nadaga cikin suratul kahfi sannan ya rufe qur'an appks ɗin dake wayarshi kana ya soma karanta azkarul subhi, Bayan ya kammala yayi salati ga Annabi muhammad (s.a.w)Tare da shafe jikinshi kana ya miƙe.
Gaban mirrow ya tsaya yana shafawa jikinshi cream ƙarfe shidda dai dai ya kammala shirinsa cikin haɗaɗɗun Ash colour suite waɗanda suka amshi kalar fatar jikinshi sukai mai wani irin kyau ɓarin turare yayi ma jikinshi haɗi da ɗaukar wata ƙaramar baƙar jaka wadda takardune masu yawa acikinta.
Wayarshi ya ɗauka tare da manna baƙin glass a saman fuskarshi ya nufi fita daga dakin yana zuba wani irin haɗaɗɗan ƙamshi.
Ƙofar ɗakin yayi ma key da sauri yake tafiya yana dannah layin mutumin dasukai magana dashi ajiya Cikin nutsuwa mutumin ya ɗauka suka soma gaisawa kafin ya sanar masa cewa gashi nan a hanya.
Direct wajan motar shi ya karasa ya buɗe ya shiga tare da bata wuta kai tsaye hanyar kotun da zasu fara shari'a ya wuce.
Tafiya kaɗan ya ƙarasa a bakin kotun suka haɗu da mutumin atare suka ƙarasa ciki inda shi ya wuce wajan alƙali shikuma mutumin ya zauna zaman jiranshi.
Ƙarfe 11:00am aka soma gabatar da shari'a wanda Barrister Aliyu Ali Dikko shiya tsayawa mutumin dake ƙarar Abokinsa daya cinye mai kuɗinshi wanda ya ranta mai waɗanda kuɗin suke da mugun yawa cikin nasara suka soma gabatar da shari'ar wanda mutumin bai musa ba sedai yace aɗan ɗaga mai ƙafa sabida halin rashin da ake fama dashi a ƙasarnan dan haka alƙali yayi rubutu tare da buƙatar kowani ɓangare su sanya hannun yarje jeniyar biyan kuɗin da mutumin ya amince zeyi nan da ƙarshen wata.
Alhamdulillahi Anyi shari'a lafiya angama lafiya don Kuwa komai ya tafi cikin tsanaki bayan an tashi Aliyu sukai musabaha da jama'ar wajan sannan ya hau motarshi yayi gidan kakarshi kamar yadda Yayi ma Ammin shi alƙawarin zuwa....
Banda rawa babu abin da jikin ummul keyi wanda hakan yayi matiƙar bawa ameerah tsoro aranta take ayyanah kodai Ummul tana da wata lalurar ne wadda ita bata san da ita ba Babu abin da take face saurin taje ta sadata da inda ta buƙata saboda gudun kar wata matsala ta afku duk da har zuwa wannan lokacin bata tunanin acikin Ahalin ummul da wanda yasan inda take da zama.
Tafiya ce mai shegen nisa kafin su ƙarasa cikin unguwar Tunga wadda anan gidan mahaifan ummul yake tafiya ameerah take a hankali tana bin yadda ummul ke nuna mata ada idan sunje har suka ƙarasa cikin layin gidan su ummul wanda ya cika da yara ana ta wasan ƙasa wasu kuma na ƴar gala gala alamar yawanci yaran basuje makaranta ba sabida anyi ruwan dare gari duk ya jiƙe.
Tunda motar ta doso layin yaran suka fara ihu! suna bin bayan motar suna shafata kafin ameerah ta sami waje adai dai bakin wani ɗan madaidaicin gida mai ɗauke da farin gate tai parking motar tata.
Dayake baƙin glass motar ameerah kedashi yasa na waje baya ganin na ciki dan haka seda yaran suka gama ihunsu sannan ameerah ta kashe motar tare da fitowa waje.
Itama ummul a hankali ta buɗe nata ɓarin tare da fitowa ta dubi wani ɓaɓurarran gidan ƙasa dayafi ko wani gida lalacewa a layin ta lumshe idanu tare da nufar wannan gidan mai farin gate gami da sanya hannu tana kwankwasawa.
Kamar zata faɗi ameerah tayi saurin tarota jikinta ahaka wata ƴar yarinya da bazata fi shekara goma sha biyar ba tazo ta buɗe musu gate ɗin tare da rabewa ta basu waje suka shiga ƙaramin tsakar gida se kofar falo wadda ɗakuna da kicin da toilet ke ciki wanda alamu sun nuna gidan mai komai acikine.
A ɗan ƙarami falo suka yada zango saman kujera ummul ta kwanta tana kiran.
"Hajjah hajjah hajjata kina ina?"
Muryarta a hankali tana mayar da numfashi.
Da sauri wata fara jajir ɗin tsohuwa wadda zata kai shekaru sittin a duniya ta fito daga cikin ɗakin dake kallonsu bakinta ɗauke da far'a take furta.
"wana keji kamar ummi agidan nawa?"
Tafaɗa tana ƙarasowa zuwa gaban ummul ganin ummu kwance saman kujera yasa wannan tsohuwa wadda ta kira da suna hajjah ta ɗagata da sauri ta ɗora saman cinyarta.
A kiɗime take kallon ameerah tare da cewa.
"Mai ya sami ummi kuma ke yarinya?"
tafaɗa duk hankalinta yana wajan ummul.dake zubar da hawaye.
"Hajja tun jiya take ta zazzaɓi shine yau tace akawota gidan ki"
Ameerah ta faɗa tana mai yaba karamcin tsohuwar.
"To sannu ummi salame zoki kawo mata magani tasha taje ta kwanta daman seda nace karki tafi ki zamanki anan kika kama hanya kika tafi yanzu wa gari ya waya kin bar ahalin ki cikin takaici"
Hajjah ta faɗa tare da amsar ruwan da salame ta miko mata.
Tashi ameerah tayi tare dayi ma hajja sallama ta kama gabanta wanda hajja ita kuma ta kamo ummul jikinta ta bata maganin tasha sannan tace ta kwanta bayan ta kunna mata fanka.
"Yi bacci anjima idan babanku ya fita se a aika akira babar taki, ni bana son ma ki ƙara tafiya ko ina"
Lumshe idanu ummul tayi tana mai jin hajja da tatsuniyarta amman tafiya kam seta koma
"Bara na koma kicin na ƙarasa girki wannan ɗan rigimar ne ze ƙaraso gidan tunda yayi aure shekara biyar yaron nan bai ƙara tako ƙafarshi gidana ba se yau"
Tafaɗa tare da nufar kicin.
Gyara kwanciya ummul tayi ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.....
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ 𝐔𝐁𝐄𝐄𝐑𝐀 🔥🔥: *BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
009
Lumshe kyawawan idanunta tayi tare da dafe saman kirjinta wanda ya tsananta bugawa tamkar zuciyarta zata faɗo Ƙasa.
Sake wara idanun nata tayi akanshi wanda ya wani kauda kai tamkar Bai taɓa ganinta acikin duniyarshi ba.
Kafe shi tayi da lumsassun idanunta tana cigaba da kallon shi tamkar zata lashe shi duk da ɗaure fuskar dayayi tare da cin magani kamar bai taɓa dariya ba, Ita hakan ma dayayi ba ƙaramin ƙara dilmiya zuciyarta cikin tafkin kogon son shi yayi ba.
"Hajja ina kika san shi?"
Fitar amon! sautin muryarta ya bayyana cikin tambayar data ke ma hajja.
"Ke ni bani son kankanba da shegiyar tambayarki kamar ta ƴan jarida tashi tsaye naga ina ke miki ciwo"
Cewar hajja dake ɓallo goron data kunce a gefen haɓar zaninta tana faman garza.
Tura baki tayi gaba cikin shagwabar data kema hajja idan suna tare gami da cewa.
"Nifa hajja bayana da gefen ƙuguna ke faman ciwo amman ina sanya ruwan zafi zanji daɗi"
Tafaɗa still idanunta kafe akan Aliyu wanda yayi kamar bai san da halittar ta a cikin falon ba.
Haushin yadda yayi banza da ita bai nuna yasan da ita wajan ba yasa ta miƙe da ƙarfin dayayi saura agareta tayi hanyar ɗakin hajja.
Sedai ko taku biyu bata kai ba ƙugunta ya riƙe gam da wani irin sauri take ƙoƙarin juyowa sedai yadda Bayanta yay mugun kawo damƙa yasa tai wani irin juyi ta zube bisa jikin Aliyu wanda yayi suman zaune.
Gaba ɗaya baƙon yanayi ya saukar mata ajikinta da sauri take kokarin tashi ya sanya hannu ya matse ƙugun nata yadda babu wanda ze lura da hakan wata irin ƙara ta sanya wadda hajja tai saurin tasowa zuwa gareta.
"Haba Aliko kaiko kamar mai zuciyar mutanan farko zuciya a dake kamar ta rodi kaga yarinya tana ƙarar azaba amman ka saketa ai ka tausaya mata"
Hajja ta sanya hannu ta janyo ummul jikinta da sauri ummul ta mike tana ɗingisawa ta wuce ɗakin hajja hancinta shaƙe da ƙamshin mayen turaren shi.
Tsaki hajja taja mai sauti tare da kokarin bin bayanta.
Shiko ya sanya hannu ya kamo hajja ya zaunar ta gefenshi cikin tattausar murya mai ɗauke da rashin Amo! ya fara magana.
"Haba hajja miye na ɗaukar zafin dan Allah karmuyi rabuwar haka dake please matar, Ita ɗin wacece har zata shiga tsakanin soyayyata dake?"
Ya faɗa yana wani janyo numfashin sa da ƙyar.
Goge ƙwallar dake saukar mata tayi da haɓar zaninta.
"Dole naji babu daɗi idan naga ana nunawa ummi ƙyama na fuskanci tunda ka haɗa idanu da ita kake jefa mata kallon ƙyamata to bari kaji ummi baiwar Allah ce wallahi kaji labarinta sekai kuka fatana dan Allah ku rabu lafiya bana son daga jinina inga wani na nuna mata ƙyamata a sanadin halin data tsinci kanta"
Hajja tai maganar tana mai tashi ta nufi cikin ɗakinta inda ummul ta shiga.
Da kallo Aliyu yabi bayan hajja yana mamakin wannan cakuɗaɗɗiyar magana da hajja tai masa wadda ko fahimtar mai take nufi bai yi ba.
Zaune ta tarar da ummul ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana riskar kuka!
Salati hajja taja tare da zama gefenta.
"Bari salame tazo ta siyo aboniki a shafa maki wancan miskilin baze je ya siyo miki ba sannu ummi ta yaya kika buge?"
Zumɓura baki tayi gaba.
"Nifa hajja ba ciwon bane nagaya miki a ina kika san shi kika hau yimin faɗa bari nayi tafiyata tunda kema ɗin dana kejin sanyi a wajan ki zaki fara hantarata"
Tafaɗa tana kokarin tashi.
Da sauri hajja ta kamota ta zaunar a gefenta.
Tahau share hawayen daya ke fitowa ta cikin idanunta.
"Bana Son inji kina ƙara faɗin zaki tafi ki barni ina fatan wannan zuwan da kikai ya zama shine zaman ki na din din din a wajena dama kinga ni ɗaya ce semu sha zamanmu na tabbata babu wanda zesan kina gidana"
"Shikuma wancan manta shi kikai Aliko ne fa ɗan wajan Ɗiyata Hafsatu dake aure a abuja wanda yake baki alewa idan kina kuka kin tuna shi lokacin dayazo wani ƙarashen karatu nan garin a jami'ar bayero har ya zauna a nan gidan"
Hajja ta faɗa mata cikin sigar murmushi.
Ɗan jimm tayi sannan ta ware idanu kamar yadda hakan ya zama al'ada cikin rayuwarta.
"Lahhhh hajja yaya Baffa daman shine amman ya nuna kamar be sanni ba?"
Tafaɗa tana zubo da wani hawayen.
"Ai baze nuna ba kinsan har yau halin shi na nan na miskilancin koda ma can da yake baki alewar ai wai kukan kine bai so"
Hajja ta faɗi hakan tana dariya.
"Amman ya jima da barin nan tunfa ina yawo ba riga"
Tafaɗa tana kunshe dariya tuno da datai lokacin kuruciya.
"A,a yazo gaf da bikinshi shekara biyar lokacin bakya gida shiyasa baki sani ba,Mace ce ya haɗu da ita shu'uma marar kirki ta karfin tsiya ta rabashi da kowa hatta uwarsa seya jima bai leƙata ba"
Hajja ta faɗa cike da tarin damuwa acikin ranta.
Dum!dum!!dum!!! gaban ummul ya bada sautin hakan cikin rawar murya ta furta.
"Hajja yana da mata kuma harta ma haihu kilan?"
Tafaɗa tana mai kokarin danne tsinin mashin kishin daya taso mata.
"Yana da mata amman bata haihu ba se faman zaga ƙasashe suke mukuma muna nan muna fatan karma ta haihun don irin su matarshi ba'a fatan haɗa zuri'a dasu domin irine na rashin imani! duk wanda ze raba soyayyar ɗa da mahaifi ka duba tsabar rashin imaninshi"
Fakar idanun hajja tai ta goge hawayenta da sauri kuma ta mike tayi cikin bayin dake dakin danne kukan dake neman tona mata asiri tayi tare da wanko fuskarta aranta tana ayyana shikenan yayi mata nisa don ita a duniya tana tsoron kishiya musamman irin matar shi da hajja ta gama faɗin halinta.
A daddafe ta dafo bango ta fito da kallo hajja ta bita kafin ta tashi ta fita minti ɗaya ta kuma dawowa.
"Ummi zo Aliko ya kaiki wajan masu gyara a duba ki dare ake ji"
Tana gama gaya mata hakan ta koma falo wajanshi wanda yaji wannan haɗasun da hajja tai tamkar ta ɗaura mai dala da gwauron dutse ne akan sa dan dai kawai baya son tayi ɓacin rai ne dan haka seya mike tare da daukar keyn mota ya fice.
Ummul kamar wadda aka shuka haka ta tsaya tana auna maganganun hajja kafin ta gyara hijabinta ta bi bayan hajja zuwa falon.
"Ki bishi baya son jira yana waje"
Babu yadda zatai haka tabi umarnin hajja tabi bayanshi seda ta kare fuskarta da hijabi gudun kar wani a yaran gidansu yaganta yaje yakai ma babansu rahoto sannan ta nufi motar gaban motar ta bude ta shiga kusa da shi ta zauna.
Bai ko bari ta karasa rufe kofar ba yaja motar aguje yabar layin a hankali ta dai dai ta zamanta tana mai tsirama hanya idanu...........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ 𝐔𝐁𝐄𝐄𝐑𝐀 🔥🔥: *BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
008
Tuƙi yake cike da wata irin nutsuwa wadda a zahiri haka halittarshi take gaba ɗaya soya ke ya ƙarasa gidan hajja don ba ƙaramar wahala ya kwaso ba,da ƙyar yake tuƙin ga