yana jiranta ,zuwa tayi zata wuce yayi daurin Shan gabanta yana cewa haba baby kinsan lokacin dana bata Ina jiranki kuwa gimbiya ta , yanada yake maganan kadai ya’isa ya ,saidawa mutum dan daba ne ,manna mishi tayi ,gimbiya kinsan yanda nake sanki kuwa ,zan iya kashe kowa akanki.
Wuce wa tayi gida tabarshi a wajen ya nata maganan da bashi da Kai bare gindi,da sallama ta shiga gidan ,ranta Duk ba dadi.
Tarasa meyasa innah takeyi mata haka dan Allah,Shikkenan ita bata daga ta kenan,wasu hawaye ne masu zafi suka sauka a kuncin ta ,saurin sharewa tayi ,dan taji muryan innah tana cewa “toh shi wannan din dakike gudu shi zaki aura ko kinaso ko bakya so wannan din dai shi ,a toh,idan zaki sawa kanki ruwan sanyi,tana fada ,ta cikawa zanin ta iska.
Itadai bata kulata ba dan,inta kulata sai abun yazama babba.
______________________________________________😎
USA 🇺🇸
Suna İsa gida , Duk sojojin saida suka fito,suka tsaya suna jiranshi ya fito,yakai kusan 5mins kafun ya fito da kafansa dake sanye cikin booth ,mai daukan hankali,cikin kasaita ya fito daga cikin motan ,abun gonin burgewa.
Kai tsaye main falon gidan ya wuce,anan ya samu su junaid a tsaye alamun jiran shigo wansan sukeyi,ko kallan inda suke baiyi ba a cikin falon.
Wajen lifter yaje,da Kansa ya danna number 4,hawa na karshe kenan,within some seconds kofan lifter yabude.
Fitowa yayi cikin takunsa na ingarman namiji ,wajen wani hadaden kofa yaje,kana ganin wannan kofan kasan dollars tayi kuka ,kofan mai hade de da na’urannane ,da dai kasa password zai bude.
Dan babu mai shiga cikin side nasa sai, junaid da Ashman ,su kadai ne sukasan password na door din, shiga yayi bakinsa dauke da sallama ama iya shi kadai tasan yayi ,falone mai girma daya kawatu da ababen more rayuwa, Dan falon Nan ya nunka falon kasa hadu, main falo kawai girma zai nuna masa.
Shiga yayi , ko Ina a gyare fess fess sai kamshin dake tashi, wajen wani kofa naga sha shiga ,Ashe bed room ne ,bed room ne mai girma daya kawatu da design masu kyau na furniture’s ash and golden colour,ya matu kar kayata dakin, ga wani center table a gefen mai hade da king shape chairs guda biyu da wani L-shape chair shima a gefe, yayi kyau sosai .
Gaban dressing mirror kuwa,perfume ne masu kyau da tsada,shake a gaban dressing mirror,lotions,tissues etc.
Shiga yayi cikin nutsuwa ya fara rage kayan jikinshi,tukun ya daura towel a kugunsa,wata kofa naga ya shiga ,daga gani toilet ne,wani irin jacuzzi ne mai tattare da varb ga wani ,long and beautiful drawer,mai cike da kayan anfanin wanka da soap 🧼 iri da kala,har mutum ya tasa abunda zaiyi dashi ,ta gefen kuma towel hangers ne ,mai dauke da towel white colors almost twelve.
Ruwan wanka ya hada mai zafi dan su koyaushe kasar da sanyi,ga sabulai da abun kamshi iri da kala ,ga kamshi sai tashi yake yi ,da kuma daya zagaye varb in,shiga yayi cikin ruwa ya Kai almost 30 min a cikin ruwan kafun ya fara wanka shap shap,10mins ya kara kafun ya gama Duk abunda zaiyi ,towel ya daura a kumkuminsa Dayan kuma ya na goge curly hair sa.
Fitowa yayi zuwa wajen dressing mirror, wato irin wayanan ko a hanya ka hadu da irinsa to ka canja hanya, dan wani irin murdaden Jiki ne dashi ,daya sha asalin training da daga karfe ,gashi da ffaffadan kirji ga nonuwanan bulbul abunsu,He look dammmn sexy.
Lotions ya sha fada sauran abubuwa , ya dauko hand dryer ya busar da kanshi da sha musu mayuka masu kamshi da tsada ,domin hair sannan ba karamin kudi yake kashe masa ba ,taje wa yayi ya gyara shi sai shining yake yi.
Mike wa yayi,wajen wani kofa ya shiga ,a haka dai babu komai ,gani nayi ya danna wani remote ,take wajen kayan yabude a cikin glass , kayane masu ya wa ga tsada ,danshi company ne suke buga masa kayayakinsa shida ,Ashman,da junaid.
Suits ne kala kala ba kalan da babu daga kan dark color and lights color masu tsadan gaske irin na kece raini ga side na , three quarters , t-shirt,jeans ,vest ,boxers ,p-caps,diamond rings and watches,gold rings and watches,neck tie,shoes,cover shoes silifas,army clothes,face marks…….etc.
Shiyawa yayi cikin three quarter blue with white t-shirt,ya daura a gogon diamond na millions of dollars, silifas ya saka masu lashi,sun karawa fararen yatsun kafan shi kyau ,sai mai muce Tabarakallah Masha Allah .
Fitowa yayi daga dressing room din,cikin room din ya koma ya zauna ,daukan system nashi kiran iPhone, operating nashi cikin kware wa da Birgewa.
Sai lokacin na kare masa kallo ,Masha Allah fari ne tass ,kana ganinsa kaga balaraben mutum,yanada manyan eye bolls (grey color) masu daukan hankali,ga hancinan zuwait kaman pencil,yanada saje daya zagaye dan karamin bakinsa mai shape din heart ❤️ so reddish kaman yasa Jamba ki.
Sai dai fuskansa kaman anyi gobara ,dan a hade take tam,danshi baisan meye dariya ba,ga kwarjini dan wannan a jinin sa yake.
Shigowa dakin yayi bakinsa da sallama ,amsa wa “BOSS LION “ iya labban bakinsa ,idan kana wajan ma zakayi tunanin bai amsa ba,bayan amsa sallaman dayayi ,bai kalla ko inda yake ba ,yiya yi kaman bai San da halittasa ba.
Junaid ne yashigo fiskanshi a sha gwabe hanun shi dauke da coffee ☕️ ,ajiye wa yayi akan bed side drawer yace yaya boss am so sorry 😢 please I will not do its again , please 🙏 tare da kama kunen shi daya yayi kalan tausayi.
Zaka tashi ka fita daga dakinan ne ko,kuwa sai nayi ball da Kai ya fada cikin tsawa jijiyoyin kansa sunyi rudu rudu tsabar bacin rai .
Fashewa da kuka junaid yayi ,ya mike jikin sa na kerma ya fita daga dakin,a bakin kofa ya samu Ashman “zai shiga ,alamun kuma Yaji abunda yake wakana ,fadawa yayi jikin “Ashman din ya saki kuka mai taba zuciya ,bubbuga bayanshi yake yi alamun rarrashi,amma bai bude bakinsa ba,sai da yaji ya fara sakin Ajiyar zuciya,kafun ya sake sa .
Meyasa baka jin magana ne ,janshi yayi suka koma falo ,,amma dai kai ma kasan halin “BOSS LION “ wannan abunda kake ji ba dai dai bane ,kana tunanin bama sanka ne muku hanaka,no,dan kare ka daga shiga fushin ubangiji ne .
Zuwa club ba’abu bane mai kyau ,kasan alkawari ya dauka wa ummie kafun rai yayi halinsa,ta damka amnan mun a hanun sa.
Kokari yakeyi yaga ya cika amanannan, maza tashi kaje ka wanke fuskan ka ,Zanyi mishi maga na idan ya huce ,tashi junaid yayi ya fita daga side din.
Please anayin comment da likes 🙏
2024/2025🔥
Written by Amid✍️
💋*_ SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
🌎Destiny,Love ❤️& Romance 💋
Written by Amid✍️
2024/2025🔥
Bismillah Rahmani Raheem
Paid book ne
Free page 📃 7
Bayan tafiyan junaid,Ashman “ ya mike ya shiga dakin “BOSS LION “ yana zaune a inda junaid ya barshi,coffee yake sha hankali kwance ,amma fuskanan kaman anyi mishi mutuwa,zama yayi a gefensa , kasa magana yayi dan yana Jin shakkan yimasa magana ,dan shima yanada nasa laifin.
Cikin dake wa da aro jarumta irin tasu ta soldiers “yaya “BOSS” Dan Allah kayi hakuri,insha Allah addu’a zamu na mishi ,indai Muna yi masa addu’a Allah zai karba,idan Muna yawan yi fushi dashi ,yana shiga cikin damuwa ,dayake sa yake kara maida weeds or shisha abokin rayuwan sa.
Kamata yayi Muna kwantar masa da hankali dan bashi da kamarmu,please we are so sorry w……………”maganan nasa yatsaya be dalilin wani kallo da “BOSS LION “ ya masa ,ba tare da yayi magana ba ,yanuna masa kofa da ido,dan bai cika yin magana ba ,dan akwai wani SIRRIN DAKE BOYE da ke cikin zuciyansa bayasan ana tuna masa da abunda ya wuce.
Tashi yayi salun alun ya fita daga dakin ,almost 9:30am ,bayan fitan “Ash” da minti goma sai gashi ya dawo da Trey a hanun sa ,mai kyau da dauka hankali golden color ne ,ajiye wa yayi akan center table dake cikin dakin.
Yakai 10mins a zaune akan king chair dake dakin,kafun “BOSS LION “ ya mike ya zauna a dayan king chair ,tare da yin crossing legs nasa,ba tare da yayi magana ba ,Ashman kam wannan abun bai damesa ba ,saving nashi yayi abinci irin nasu nacan,a hankali ya fara cin abincin ,ci yake yi kaman yana yanga, cikin nutsuwa da Jan aji.
Shap shap ya gama cin abincin,tare da mike wa ya shiga toilet dan ya wanke bakin shi ,shikuma Ashman ganin ya shiga toilet sai ya tattare kwanu kan ya fita dasu ,yakuma fesa air freshener masu sanyi dadi.
Fitowan da yayi bai ga Ashman ba ,yasan ya fita,koma wa yayi ya zauna a L-shape chair dake gefen center table din da wasu docoments da system.
Bai fito ba sai karfe daya shima sallan azahar ne ya fito dashi dan kwata kwata baya wasa da sallah komai yake yi zai bari ne yayi sallah.
________________________________________________📚
Abuja
Yau takama Wednesday,tunda ta tashi daga bacci take Jin kwadayin shan ice cream,dan yau cikin farin ciki ta tashi daga bacci.
Wanka tayi ta shirya cikin Riga da wandon makarata tareda wani mini hijab tayi Kyau sosai,daukan school back nata tayi ta wuce falo.
Falo ta sakko bata samu kowa ba ,wuce wa tayi side in Ammi, akan sallaya ta sameta dan azkar take yi,cikin murmushi ta karaso inda Ammi take “Ammi Ina kwana “lafiya kalau autar Ammi ,kin tashi lafiya”lafiya kalau ,kallanta Ammi tayi tace yau kuma autar Ammi mai muka samu mai dadi naga sai murmushi kike yi , darıya Shukrah tayi tare da cewa wallahi yau kwadayin ice cream nake yi” Toh ai sai kije kisamu alameen ki fada masa kinasan san ice cream din zai kaiki ai.
Cikin shagwaba ta turo baki tace “ Ammi amma kinsan halinsa yanzu sai yace bazai kaini ba “karki damu autar Ammi ni zan mishi magana idan ya shigo, cikin Jin dadi shukrah tace thank you best mother in the world,shiya sa nake sanki wallahi” dan dan kwalanta Ammi tayi,tare da cewa tashi ki barmun daki marar kunya kawai ,cikin darıya shukrah tace Ammi ba rashin kunya bace har cikin Raina nake fada,ta karasa magana tare da fita daga dakin tanaji Ammi na ce wa Allah ya kiyaye hanya.
A wajen stairs taga alameen zai wuce dakin Ammi ,cikin Shan kamshi tace yaya alameen good morning “morning ya ce tare da haura wa dakin Ammi .
Ita kuwa yusrah wuce wa dining tayi ,breakfast tayi cikin sauri ta gama ta fita dan driver yana jiranta , shiga tayi motan driver ya ja motan suka wuce school.
A dakin Ammi kuwa yana zuwa yayi knockingna kofan dakin,izinin shiga Ammi ta bashi ,zama yayi a kasa kafun ya fara gaisheta,Ammi Ina kwana kin tashi lafiya, kinsha maganin jiya da daddare,tsaya wa kawai tayi tana ganin sa ,soyayyarsa kullum karuwa take yi a cikin zuciyan ta ,yanda yake kulawa da ita abun ba karamin dadi yake mata ba.
Lafiya kalau”Alhamdulillah,maganina kuma nasha dana ci abincin dare saura na safe, Toh Ammi Allah ya Kara sauki”Ameen ya Allah “Ammi akwai abunda kuke buka tane idan na fita na taho miki dashi,” a’a babu komai Allah yayi maka albarka ameen yace tare da tashi zai fita .
Cikin sauri tace alameen ,komawa yayi ya zauna ,tare da maida hankalinsa Kanta ,Yauwa dama shukrah ce ta tashi da kwadayin shan ice cream “Toh Ammi baga driver ba sai ya kaita su siyo,”baza’a aika drivern ya siyo ba, kai nake so kai nake so ka kaita inda kake zuwa.
Cikin son danne baccin ransa yace Toh Ammi Insha Allah,ya fada tare da mikewa “Toh Allah ya kiyaye ,yayi maka albarka ,Ameen ,tare da fita da ga dakin.
Falo yakoma ko zai sameta ,amma batanan tariga da ta tafi.
___________________________________________🌹
7:45pm
Idar da sallanta kenan taji ana knocking na kofan dakin ,sai kuma taga ya shigo cikin dakin , ganinsa tayi ,sanye yake cikin maroon yad mai tsada anyi mishi dinkin half jampa,dinkin zamani daidai jikin sa.
Cikin takunsa mai dauke da nutsuwa ya isa inda take ,baiyi wata wata ba ya kwade Kanta ,dan har janzu bacin ran bai gama sake shiba.
Wato ni kin rainani harda zuwa wajen Ammi kice mata kina kwadayin ice cream, kuma ni kikeso na siya miki ko ,ya kara sa magana tare da Zare mata ido.
Cikin gunguni tace nifa ,bace wa nayi tace maka kakaini ba , kawai ce mata nayi Ina kwadayin shan ice cream,sai tace bari kazo zata ce maka ka kaini.
Kwafa yayi tare da cewa zaki sanine, wuce kije ki shirya na baki Nan da minti biyu kısa meni a packing space “Toh tace tareda mikewa ,shikuma fita yayi daga dakin.
Wani half Sunnah hijab ta dauka yellow color ta daura akan blue jeans and yellow t-shirt din dake jikin ta ,ta fito cikin sauri ta wuce parking space,anan taga maercese benz 350 maroon color yana kawo wuta, wuce wa tayi tare da bude front site zata shiga , tsawa ya daka mata yace wallahi idan baki koma kin saka kayan arzikiba,jikinki sai ya gaya miki,na baki Nan da one minute ki fito.
Zum buro baki gama tayi ,tare da konawa dan bata San duka.
Komawa tayi ta dauko abaya purple color mai fadin hannu daya sha stones tayi rolling na gyalen tayi kyau sosai, cikin sauri ta wuce packing space,ta bude motan ta shiga ,bai ce mata komai ba har duka Isah hadadden wajan shan ice cream dasu burger 🍔 ,shawarma,pizza,popcorn,drinks ,chocolate,birthday cake,snacks da abubuwa dai kala kala.
Shiga sukayi wajen dan babu hayaniya dan wajene na yayan wane da wane suke zuwa irin wajen.
Mentioning na abubuwan da take so tayi iri su burger ,popcorn,chocolate ,ice cream take so ,kawo mata akayi a wani bag mai dauke da tambarin shop din.
Wuce wa sukayi suka koma cikin mota,kuna motan yayi tare da daukan hanyan gida , bude bakinta tayi tare da cewa yaya alameen Nagode Allah ya saka da alheri , Ameen yace daganan babu Wanda ya sake magana a cikinsu har suka iso gida.
A falo suka tarar da Ammi da Abu zaune suna hira,gaishe da abba yayi da yimishi ya office sannan ya koma dining ya zuba abinci kadan,dan kansa ciwo yake masa,bayan ya gama cikin abincin ya dawo falo anan ya tarar da shukrah sai shagwaba take musu sukuma suna biye mata.
Sai da safe ya musu tareda wuce wa dakinsa dan ya kwanta.
Shukrah kuwa yana ta fiya ta tashi ta kwashe laidodin ta tawuce dasu daki tare da musu sai da safe,dan Ammi ba cin irin abubuwa Nan take yi ba,tana shiga dakinta zama tayi ta bude laidan data shigo dashi ta dakko ice cream in ta saka a fridge,ta fara rage kayan jikin ta ,ta shiga wanka,bayan ta fito ta saka kayan bacci Riga da wando Marasa nauyi milk color.
Dauko ice cream din tayi daga fridge da burger ta ,ta zauna a gefen gadon tana sha ice cream in ta kuma tana cin burgern ta ,dan dadi har lumshe ido take yi.
Bayan ta gama ci ,ta shiga toilet tayi brush, ta koma daki ta kashe wutan dakin ya saura iya bedside lamp ine ya rage tayi addu’a ta kwanta
Asuba tagari
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels