tashi , ta fita tayi alola, shimfida sallaya tayi , ta fara nafila da kuma raka’a tanıl fakir sukuwa adda habiba da adda deeje harda zulaihat bacci sukeyi dan wani lokacin ma kota tashe su barazu tashi ba saidai sufara mata masifa shiyasa ta daina tashinsu,kullum a makare sukeyin sallah , wajen takawas ko tara , suke tashi suyi sallah , har zulaihat in dan itama a kwai nauyin bacci .
Tana idar da sallah tafiya waje ,ta kwaso buckets 🪣 da zata iba ruwa a rijiya ,ta cika duk randan gida, wanke wanke tayi bayan ta gama tadaura musu koko , dan yau babu wani abun a gidan ida ba kamun kokon ba .
Bayan ta gama ta iba ruwa tayi wanka dukda yunwan da yake cinta , Tana fito daga wanka ta shafa mai ,da powder amma ba sosai ba dan kadan, dan ba lallai mutum yasan ma ta shafa ba ,kwalli ta saka da lip glows ta bude akwanti n, ta dakko a tamfa me kyau nevy blue ,Masha Allah dan yanda kasan dawisu haka take yalki ,hijab ta dauko shima nevy blue,da niqab nata tayi kyau,(ohhh my god 🤗)
Fito wa tayi daga dakin,bakin dakin innah tawuce , sallama tayi har sau uku ba’a amsa ba, kuma tasan sarai taji amsa wane kawai bazata yiba, bata gama tunanin zucin ba Yaji muryan innah , tana surfa mata masifa, ke , dallah matsamun daga bakin kofar daki , ta fada cikin daga murya SULTANA cewa take innah Ina kwana, cikin masifa innah tace , daban kwana ba zaki gannine dan ubanki da fuska da fuska irin ta aljanu , ba zaki daina kallona da wannan yan iskan idanu yawana mage ,SULTANA cikin dan bacin rai ta ce , innah fita Zanayi, kuma baki banı kokon ba ,’’ dan ubanki bazan bayarba,fitsararriyar yarinya kawai ,Watarana sai zaman gidannan ya gagare ki wata Rana indai Ina raye , ta karasa maganan tare da huhura hanci , tana binta da kallan tsana.
Itadai SULTANA,dama batayi tsammanin zata bata abinciba,duk da kuwa ita ta girka,domin ba sabon abu ba ne a wajen ta ,sai taga dama take bata abinci.
Sum sum tanufi hangar waje,tazo fita, abba kuwa ya zo shiga ,dan bayan dawowanshi daga sallah ankira shi wai wani yana sallama dashi a waje,cikin muryanta mai dadi tace,Abba Ina kwana ,banza yayi da ita kaman bai ganta ba ,dan idan ya ciga ba da gannin ta zai iya dauke ta da Mari ma.
Ganin bai kula ta ba , fita tayi daga gidan ,dan wannan bai dame taba,tafiya take yi a hankali cike da nutsuwa ,tayi tayan awa daya da rabi ,kafun ta iso GRA ,dan Dani sa.
———————————————————————-/——//——////🤪
Abuja/Nigeria🇳🇬
Asokoro street
Wani gida ne mai kyau na zamani,falo ne mai gima daya wadatu da kayan more rayuwa.
Babbar macece zaune a kan kujeru na alfarma dake cikin falon ,a shekaru bazata wuce 48 years ba , A duniya idan kaganta zakayi tunanin bazata wuce 38 years ba, gata black beauty ,alamun jindadi da kwanciyan hankali ya Wada ce ta,azkhar ne a hanun ta ,tareda carbi,addu’o’in marai ce take yi.
Wata yarinya ce ta sauko da gudu daga up stairs bazata wuce 15 years ba kyakyawace black beauty,tanada dara daran idanu (brown eyes) kaman madara,tanada jikin girma masha Allah .
Fada wa tayi jikin wannan matar tana cewa , Ammi wai yau yaya alameen zai dawo , tafada tana yatsuna fıska , cikin kulawa Ammi tace eh yau zai dawo,bata fuska tayi,wallahi dama kar ya dawo,dan yana dawowa zai fara takuramun ta fada cikin rashin Jin dadin dawowan sa .
Ammi kuwa tsaya wa kawai tayi tana kallan ta ,,ta rasa meyasa basa jituwa da juna ,saikace ba ciki daya suka fito ba,da fata Ammi tayi da cewa karki damu bazan bari ya miki wani abun ba’’ tab Ammi kenan kina Ina zai mun,mguntar daya sa………….,maganan tane ya makale Jin sautin sallamarsa kaman saukan aradu haka taji,shigo wa yayi hanunsa rike da ludge nashi mai kyau yanaja,kuma tsaf yaji abunda take fada,saurayi kyakyawa farine amma ba tass ba yanada tsayi bacan sosai ba ,gashi bashida jiki sosai,saidai yanada faffadan kirji.
Cike da farin ciki Ammi tace ,lale mutanen Morocco 🇲🇦, cikin sakin fuska da ladabi ya ce ‘’ Ammi Ina wuni ,nasa meku lafiya,lafiya kalau ya hanya,,Alhamdulillah,yace yana mai Jin farin ciki idan yana kusa da maihaifiyarsa.
Cikin dake wata ce yaya alameen,Ina wuni,ka iso lafiya,,cikin basarwa yace lafiya yace lafiya tare da mikewa yace Ammi bari nadan watsa ruwa na fito, a fito lafiya,,yace Ameen ,, dakine mai kyau daya sha (Italian bed) white and brown,sanyi ac ne da kamshin air freshener,yana shiga ya cire kayansa ya daura towel,yashiga toilet 20mins ba ya fito yana tsane jikinshi black three quarter,da t-shirt white yayi kyau ya fito da Kya wunsa na asalin bafulatanin sa, feda turare yayi masu dadi,, fito wa yayi yana tafiya a hankali,cikin falo yashigo .
Bai samu Ammi a falo ba sai shukra da ya gani ,zaune kana kallon Zee world , Kara sowa yayi wajen wajen kujeran ya kira sunan ta, amma bata jiba dan tabada Duk hankalin ta a tv,,bubbuga kujeran yayi fuska a daure yace ‘ke meyasa bakida hankali ne ,,eh ,,ya fada cikin tsawa , cikin sauri tace yaya alameen kayı hakuri banji bane ,kwafa yayi irin na zaki sanine.
Muje kiyi saving Ina ,cikin sauri tace Toh,,dan ita tsoronta karta taba mata lafiyan jikin ta.
Gaba yayi tana binsa a baya tana turo baki gaba,kan dining area ,Jan kujera yayi ya zauna ,,cikin rawan murya ta ce yaya alameen meye za’a saka ma, cikin halin ko in kula yace everything,, pride rice da chicken pepper with zobo mai sanyi,tura masa gaban sa tayi,spoon ya dauka ya fara ci cikin kwanciyan hankali dan abincin ya mishi dadi sosai, juyawa tayi zata tafi,ki zauna idan na gama ki kwashe kwanukan,,Toh tace Taja kujera ta zauna tana jiranshi ya gama cin abincin,,bai wuce 20mins ba ya gama ,,mikewa yayi ya shiga dakinsa dan anfara kiran sallan magrib.
Ita kuma tattare kwanukan tayi tana magana kasa kasa harda mur guda baki,tana gamawa ta wuce dakinta tayi sallan magrib da isha,fito tayi daga daki tawuce dining area anan ta samu,,Ammi da Abu sunacin abinci,,yaya alameen kuwa yana dawowa dakinshi ya wuce ,,kwanciya yayi dan a gajiye yake.
Dan Allah,anayi likes da comment
2024/2025 🔥
Written by amid💞
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
🌎Destiny,Love❤️& Romance 💋
Written by Amid✍️
2024/2025🔥
Bismillah Rahmani Raheem
Book 1
Page 📃 4
Abinci take ci a hankali ,ita kadai ce ta rage a dining table din,dan Ammi da abu sun mata saida safe.
Itama tana gamawa ta tattare wajen ,ta haura dakin ta ,tana zuwa ta cire kayanta ta daura towel ,wanka tayi tafito ,shirya wa tayi ciki riga da wando pink color masu da laushi tayi addu’a ta kwanta.
———————————————————————/——//——////🇳🇬
Gombe state
GRA
Anguwane ta masu hanu da shuni ,gida jene masu kyau a anguwa.
A bakin wani get ta tsaya, dan gidane mai girma ,saidai bacan sosai ba ,cikin gidan akwai up stairs da kuma normal flat guda biyu , daya na boyz quarter ne dan yafi dayan part din girma sosai,Dayan flat din gefen masu aiki ne ,daki biyu ne a ciki.
A hankali take tafiya har ta’isa bakine entrance din dazai sadaka da babban falon gidan, bude wa tayi ta shiga da sallama a bakinta dan lokacin large 8:30 ne , dan da safe take zuwa,dan daura abincin safe.
Bata samu kowa a falon ba,sai dai alamun an gyara falon da n kamshi be ke tashi, Direct kitchen ta wuce ta samu Tana daura musu abincin karyawa dan yau chips with egg source take so tayi.
Cikin kware wa , ta fara fere dankalin ,dan da yawa akeyin abincin gidan ,dasu masu aiki da masu gadi ,dan mai gidan mutum ne mai dattako da kyauta . Tana fere wa take soyawa ,sai fast 10 tagama, dan gidan yan boko ne sai sunyi baccin safe ,dan wani lokacin ma sai sukai 11:00am basu sakko ba , tana gamawa ta zuba a flask masu kyau ta kai dining table ta jera su ,komasa kitchen tayi ta zuba abinci a sauran masu aikin gidan suma.
Diban nata tayi, ta zauna tacı tayi nak ,tace Alhamdulillah,dan rabonta da cin abinci tun jiya a gidanan.
Tana gamawa ,sai lokacin ta farajin hayaniya yan matan gidan ,cikin nutsuwa ta fito daga kitchen din ,dan tazo tayi saving nasu abinci.
Tana zuwa ta samu har mami da daddyn Aneesa suna zaune dan zuwansu Kenan ,yan mata biyu ne da samari biyu , dake zaune a dining table din. Tun daga nesa taga irin kallan da Zainab ta ke biya dashi ,kallo ne irin ta tsana take mata, ta gefen ta kuwa Aneesa ko kallata bata yiba,sai maza biyun da yan na wulla mata kallo irin na yan iskanan,mai suna jabir.
Gaishe dasu mami da daddyn Aneesa ya fara yi , amsa mata daddyn aneesa yayi cikin sakin fuska amma banda mami ciki ciki ta amsa ,sannan ta gaishe da ya mujahid da ya jabir,amsa mata sukayi ,jabir yana wani karshe mata ido daya irin na tantiran yan iskannan ,tukun ta gaishe da zainab da aneesa duk da dai zasu iyayi sa’ani da aneesa .
Cikin kankanin lokaci ta zubawa kowa nishi ta tura mishi gabansa ,suka faraci,ita kuwa kitchen ta koma ta daura abincin rana dan har 12 tayi.
By 2 tagama shima taje ta jera musu a dining ,kafun ta koma kitchen domin daura abincin dare, shima by 4:50 ta gama taje ta jera musu na Daren dan ,tagama aikin ta na yau ,hijab nata ta gyara tareda daura niqab nata,tayi mawa sauran masu aikin saida safe.
Tafiyan awa daya da rabi tayi ,kafun ta isah gidan,dan lokacin har an fara kiraye kirayen sallan magrib,da sallama ta shiga cikin gidan saidai bata tarar da kowa a gidan,sai takalmin innah data gani a bakın kofan dakinta,ajiye abincin da tazo dashi tayi ,wanda na ranan tane ta bari ta ajiye sai ta dawo gida taci, tana shiga dakin nasu ma bata samu kowa ba , fito wa tayi ,tayi alwala ,tayi sallah tukun sai lokacin taji sallaman zulaihat take shigo wa gidan dauke da kwanikan abincin sayarwa tana ganin,SULTANA ta sakar mata murmushi, itama mai da mata da martani tayi ,Masha Allah kunga madarar kyau kuwa dan har beauty points nata sai da suka lotsa,Tabarakallah.
Zulaihat kuwa direct dakin innah taje, SULTANA kuwa daki ta koma dan yau bazai yuwu tayi Shara ko wanke wanke ba ba ,daki ta shiga taci abincin ta ,takoshi ta wanke hanun ta ,ana kiran sallan isah ta , tashi tayi salla ta ,tayi shimfidan ta ,,ta yi addu’a kwanta .
Sai lokacin Adda habiba da adda deeje suka shigo ,tana jiyo yanda suke ta zagin junan su,cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ta .
———————————————————————-/——//——////🥰
USA 🇺🇸
Washe gari 7am ya fito zuwa ,office dan ,an musu kiran gaggawa ne, yasa ya fito, gashi bai gama aikin da ‘’ BOSS LION’’ ya bashi ba ,ji yake yi kaman yayi kuka wallahi dan bayasan abunda zai ha dashi da ‘’BOSS LION’’ .
Yana fitowa ,sojojin suka fara sara mishi ,daga musu hannu kawai yayi,direct wajan da aka parker motocin nasu yaje ,wannan sojan mai suna john Sara masa yayi hade da bude masa matan ,shiga yayi suka fita daga Gidan straight.
Basu dawo ba sai 8pm na dare suka dawo gidan,kuma har lokacin bai samu ya Karasar ba dan shi har ya sadakar sai yayi sai yayi punishment din’’BOSS LION’’ dan ba’a karya mishi doka.
Ruwa kawai ya watsa yabi lafiyan gado,dan kar ya makara zuwa ,dan zuwa karfe biyar (5am) jirgin ‘’BOSS LION “zai saka ,immediately after fajr prayers,jirginsu zai sauka ,shiyasa yake san ya kwanta da wuri dan ya dauko shi akan time ,idan ba haka ba kuwa ,ransa idan yayi dubu Toh zai baci.
Asuba ta gari mutanen”Ashman”✌️
_____________________________________________*✍️
Abuja
Kiran sallan Asuba ne ,ya tashe sa daga baccin gajiyan da ya dauke sa , ban daki yayi alwala ya fito, masallaci ya tafi, bayan an idar da sallah ya dawo gidan.
Dakisa ya wuce,zama yayi ,yai azkhar da karatun alqur’ani mai girma ,lokacin har Safiya ta farayi,kafun ya rufe qur’an ya kwanta ,yana kwanciya kuwa bacci ya dauke shi.
Shukrah kuwa ,Ammi ce ta tashe ta ,tayi sallah Asuba ,bata koma ba dukda kuwa yau Monday akwai school ,amma bata ra’ayi zuwa school yau ,shiyasa bata tashi ta shirya ba ,baccin Tama takoma.
Sai wajen fast 10 tukun ta tashi,daga bacci,a gurguje ta shiga wanka tafito,atampha me design na leaf,pink and purple ,sanan ta daura dankali,daurin Zara Buhari, tayi kyau ,black beauty skin nata dake ta glowing yana shining.
Falo ta fito,at the same time,shima yaya alameen ya shigo falon, Ina ganin shi bansan time din dana ci wani uwar burki ba,dan wallahi kwata kwata na matan da yadawo gidan.
Shikuwa alameen da mamaki yake kallan ta dan yasan dai yau Monday ne,kuma akwai makaranta, ranshi ba karami baci yayi ba dan yasan wannan laifin Ammi ne ,dan ta ta daure mata gindin zama, amma in Fasu san wata ba ,zasu san wata.
Cikin hade Gira yace ,ke shukrah meya hanaki zuwa makaranta “ammm wallahi ya alameen kaina ne yake mun ciwo shiyasa banje ni ba” ke ni sa’an wasanki ne da zaki fadamun wai kanine yake ciwo shiyasa baki je makaranta ba,”marairaicewa tayi tace ya alameen da gaske nake fah.
Gaga sama yaji murya Ammi Tana cewa, wai alameen meyake damunka ne,inadai tace maka bata da lafiya ne,ai zan ce ya kare, ni bansan me yarinyar Nan ta tare maka ba wallahi, ta fada Tana nufah daya daga cikin kujerun falon ta zauna.
Shikuwa alameen dama yasan za’a rina,dan wannan ba sabon Abu bane a wajenta bai san meyasa ba muddin zata yi fada a. Shukrah indai Tana wajen fah,bai isa mata ba.
Cikin warning ‼️ ya kalla shukrah da haryanzu take kalan sa yace wallahi nan gaba muddin ,kika ki zuwa makaranta haka kawai,wallahi ranki inyayi dubu to zai bace, kinjin ko “kanta ta gyada mishi”cikin fada fada yace, Ina miki magana da baki ,zaki wani dagamun kai ,yanda na miki magana da bakai haka zakimun "
Toh tace, insha allahu hakan bazai kara faru ba"good yace
dukansu suka tafi wajan dining cin abinci.
2024/2025🔥
Written by Amid✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
🌎Destiny,Love ❤️🔥& Romance 💋
Written by Amid ✍️
2024/2025🔥
Bismillah Rahmani Raheem
Book 1
Page 📃 5
_____________________________________🌹
USA 🇺🇸
Karfe hudu(4am)ya tashi sallan asuba, alwala ya dauro, kafun ya sauka first floor ,anan ya samu junaid ,uncle İbrahim da uncle tareeq a zaune suna jiranshi ,yana zuwa suka wuce masallacin dake gidan, dansu yau babu wanda yasan yau “BOSS LION “ zai dawo ba.
Suna fitowa daga sallah ,suka shigo cikin gida , cikin sauri “Ashman “ya shiga dakinsa,domin shirya wa ,dan jirginsu ya kusa sauka .
Shaf shaf ya shiga wanka ,bai wuce 10mins ba ya fito dan kar yayi latti,shirya wa yayi cikin kakansa na sojoji ,dan ya farajin karan helicopters 🚁 sunata shawagi, wannan yana nuna musu cewa mai gayya mai aiki ,zai dawo wato “FIELD MARSHAL “ zai dawo kasar .(zakin fama maija da shi sai Allah ).
Fito wa yayi daga daki cikin sassarfa,ya fito main falon , anan ya tarar da junaid dake tsaye yanata zazzare ido alamun ya nuna ya mishi laifi,sauran uncle İbrahim da uncle tareeq suma da suke tsaye dan cikinsu ya dura ruwa .Dan wannan karan helicopters din ,yana nuna fah “FIELD MARSHAL “ nanan ta fe🤪
Bai bi takansu ba ,waje ya wuce ,dan lokacin it already 4:40am ,duk sojojin a shiye suke ,suma cikin kakinsu ,dan suma kana gananin su kasan hankalinsu a tashe yake ,sai dai kawai dake wa irin na sojoji bazaka taba gane waba.
Cikin motocin suka shiga,dan sun iba motoci sukai guda goma sha takwas (18) dan dakko “FIELD MARSHAL “ gudu suke shararawa a hanya,shiyasa suka isah dawuri,dan lokacin time 4:56am , dan sai 5:00 jirginsu “FIELD MARSHAL “ zai sauka.
Fitowa sukayi gaba dayansu,daga cikin motocin , har da “Ash” dake tare da abokin sa farouq,suna tsaye suna magana ,karan saukan jirgi ya karade kunnuwan su,A hankali jirgin ya sauka.
Private jet 🛩️ ce mai shegen kyau da tsada ,a jikin jet din an rubuta , “BOSS LION “a ka rubuta a jikin jet din da manyan harufa masu style,kana ganin jet din kasan ba karamin billions of dollars 💵 aka karshe wajan kera taba, dan ya hadu ne iya haduwa, wai dan ma bamu shiga daga ciki ba.
Bayan yayi landing,baifi da five minute ba ,wasu jiga jiga sojoji ne wa yanda suka amsa sunan su sojoji suka fara dauko wa ,dan sukai su goma sha biyu ,hakanma mai gaiya mai aiki cewa wa yayi shi kai zai je amma Ina ,mutum ne mai muhimmanci d bazasu iya barinsa ya tafi shi kadai ba .
(Bari na leka muku cikin private jet ✈️ din naga meye ne aciki,dan gulma na cina 😂)
Wani saurayi na gani zaune akan kujera masu kyau ,a zaune yake yayi crossing legs nashi ,Baka iya ganin guskan sa dan akwai face marks a fuskan sa da kuma glass no respect,ga shin sa daya sha gyara(black curly hair) ,dan kana ganin yanda gashin yake yalki ,zakasan ba karamin kudi a ke kashewa gashin ba,dan ya sauko har kan fuskan sa,kana ganin sa kaga ingarman namiji , namijin daya amsa sunan sa namiji ,dan wasu matan suna suka tara .
Kansa jingine da jikin kujera,dan idan kagansa zakiyi tunanin bacci yakeyi ,yakai kusan 20mins a haka,kafun ya mike tsaye ,irin mazan nane masu tsayi,dan dogone ba karya dan jikin sa a murmurde yake ,kana ganinsa kasan ya mishi da training,dan wallahi irin wayanan ka kuskura wani Abu ya hadaku Toh sunan ka sorry 😢,
Sanye yake da wane black jeans da t shirt na gucci ,ya daura jacket a jikin Kayan,Kayan sun yi mishi wani shegen kyau,Kyan da idan aka ce kyau Toh ana nufin kyau,dan kayan ya fitar da asalin kyau shi,kana ganinsa kasan bazai wuce ,talatin da biyu (32) ba a duniya.
Tafiya yake yi cikin kasaita,irin na jarumin soja da mututanen da suka jika da hutu,ya zauna a jikin sa Fatan sa sai yalki yake yi ,yanda yake tafiya ma kadai abun kallo ne ,dan tafiya ne irin sojoji masu jini a jika.
Tundaga nesa “ash”da farouq suka hango sa ,su karan kansu sun sani,bakaramin burgesu yake yiba,cikin sanda farouq yabar wajen da “ash”ya koma can gefe ya tsaya.
Sara mishi sojojin suke tayi ,kam zasu yi mishi sujjada tsabar girmamawa,ga yan jarida ma ba’a barsu a baya ba ,dan suma dayawa sukazo,Duk da sunsan ba kulasu zaiyi ba ,hot one shima iya ka cin su dauke sa daga nesa,Duk da har yau acikin 100% baifi 10%ne suka taba ganin fuska sa ba dan koyaushe da face marks a fuskansa.
Ga sojoji ta koina dan ko shugaban kasa albarka dan ba Lallai idan zai samu mutane haka ba .
Kara so wansa kenan wajen motocin,Sara mishi “ash”yayi tare da kame wa , dan nuna ban girma ga yayansa kuma ogansa a wajen aiki.
Yi yayi kaman bai San da halittansa ba awajen,amma sarai yaganshi Jiki da Kai ne kawai.
Direct wajen wata shegiyar mota suka nufa ,mercedes -benz GLE 450 4matic ya nufa , cikin sauri “Ashman “ ya bude masa kofan tare da Sara mishi ya rufe, wuce wa yayi,shima cikin sauri john ya bude masa motan dake bayan na “BOSS LION “ din.
Wani irin gudu suke yi akan hanyan kaman zasu tashi sama,dan har yanzu garin bai gama waye wa ba ,dan bazai wuce 5:45am ba.
_________________________________________________💋
Gombe state
Gabukka
Washe gari Tana tashi sallan Asuba tayi,tan idarwa,tayi Sharada wanke wanke ,kafun ta daura musu dumamen tuwo ,cikin sauri tagama,ta shiga wanka.
Tana fitowa ,ta shiga dakinsu ta shiya cikin material orange color,abunka da farin mutum ta haska kayan,hijab ta dauka ,tasa tukun taje dakin Ina ,Tana tunanin komai zata tarar kuma yau.
Gaishe ta tayi Ina kwana ,wai ke kullum sai an mabaki amsa amma dake ke dakikiya ce kin kasa rike wa .
Ran SULTANA ya baci amma ta shanye dan tasan idan tanına ita zata sha wahala,cikin sanyin murya tace innah abincin “wallahi wannan yariya anyi jara babbiya ,Toh gashi ki dauka kije,Tana dangwarar mata da roban abincin, dauka tayi taje dakinsu tace ,dan ko kwatan koshi bata yi ba ,Tana gamawa ta fito daga gidan .
Tafiyan awa daya da kwata tayi,a hakanma sauri tayi ,Tana zuwa tawuce babban falon gidan, tana bude wa zata shiga ,shikuma zai fita.
Binta yayi da wani mayen kallo irin na tantiran yan iskan nan tare da cewa hey baby yafada yana kokarin Tabata ,saurin kauce wa tayi ,tare da balla masa harara da kyawawan idaonta, cikin masifan da tadade batayi ba tace dallah jabir ka fita a hanyata ,idan kuwa Baka fita a hanya taba zakayi danasani.
Wai Kai kana tunanin kowa dan iska ne irin ka toh wallahi bari kaji Duk iskan cikinka baka kaini ba dan haka ka fita harkanta ,dan nafi karfin ka ,sai gani sai hange tare da mit guda masa baki da harara babu ko dar a zuciyanta .
Shikuwa tsaya wa kawai yayi yana kallanta dan bai taba tunani tanada Baki ba dan kallan shiru shiru yake mata dan bata taba maida mishi da martani ba ,shiyasa yake mata ganin bata da wayo ,Ashe masifaffiya ce, shareware yayi tareda cewa dan halak kafasa ,yabi ta gefenta ya wuce.
A gurguje tayi aikinta dan yau tanaso takoma gida da wuri kafun a kira sallan magrib.
Cikin kankanin lokaci ta gama aikin ta ,dan yau bata hadu dasu aneesa ba da zainab dan sun tafi makaranta .
Zuwa uku da rabi ta gama komai ta shirya wa takama hanyan gidansu.
A kofan gidan su ta samu wani, ta kudirin dan daba, yana tsaye yana jiranta, zuwa tayi zata wuce yayi saurin Shan gaban ta yana ce wa , haba baby kinsan lokacin Dana …..
2024/2025🔥
Written by Amid✍️
💋*_ SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
🌎 destiny,Love ❤️ & Romance 💋
Written by Amid✍️
2024/2025🔥
Bismillah Rahmani Raheem
Book 1
page 📃 6
___________________________________________🌹
A kofan gidansu tasamu wani, ta kudirin dan daba,ya na tsaye