masifanta. Domin kowa yasan madame Victoria Osteen bala'ice ita kanta, shi yasa kowa na gidan ke tsoronta fiye da kowa. Gata ƙaƙƙarfa mace tsananin riƙo da addinin ta ya sanya addininta na christian bata wani babban muƙami gareta a church, da di da ƙari gasu masu shegun kuɗi ne su gaba da baya wannan shi ne ya sake kankarota da sake babban matsayi.
♡
*YASMINE*
Tun da suka ɗauki hanya ta nutse a cikin kujerar motan tare da lafewa luff tana jin yadda bugun zuciyarta ke ta faman kai kawo har zuwa yanzun kuwa, hakan ya sanya bama tasan sun kawo katafaren dogon ginin gidan masu ba har saida driver ɗin ta ya mata magana tare da ɗan bubbuga gilashin motar kana ta firgigit ta dawo daga duniyar data lula. Fitowa tay ta fara tafiya cikin nutsuwar da tafi kama da jin kai da taƙama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankalin me kallonta. Da wata maid service ta haɗu a gaban ƙofar parlour'n shiga gidan tana shanyar kayan data wanke na masu gidan. Shijab ɗin jikinta ta wurga mata saman fuska tare da dogon wandon uniforms ɗin Islamiyyar jikin nata. Kasancewar rigar irin duguwar nan ce har kusan gwiwar ta, Duk inda ta wuce sannu da dawowa ma'aikatan gidan ke mata amma bata kula kowa. Da mahaifinta Ambassador Kabeer Usman ta fara cin karo. Hakan ya sanya a guje tayi kansa tana faɗawa jikinsa tare da fashewa da kuka. "Ohh god waye kuma daga dawowan Ambasa baby zai taɓa min ita?" Fitowan Mahaifiyarta lowyer Khadijah Haroon ne ya sanyata haɗiye maganarta makut tana takurewa jikin mahaifin nata. Cikin muryan No nonsense ba tare data kalli ko inda take ba ta furta. "Oya get out of the here" sum sum ta miƙe tana yin sama se wani tattaro rigan jikinta take. Kai tsaye toilet ta shige tana sakar ma kanta shower, Bata fi 20 minute da shiga ba se gata ta fito ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta.
Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin, sannan tashiga shafe shafen lotion masu sanya fata tayi laushi. Kafin ta feshe jikinta da tarin turarikanta, bayan ta mulke jikinta da Shu'umar humrarta. Cikin clothes na kayanta ta shige, wasu haɗaɗɗun simple ciffon riga da wando taciro tasaka nude, there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka daga kanta ba don wani masifar ƙyaun da kayan suka mata ko nace ta musu. Don kuwa tabbas YASMINE me ƙyau ce, idan nace ƙyau ina nufin maƙura ƙarshe.
Sake fitowa cikin parlour'n tay loƙacin an jima da idar da sallar maghriba. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda Omer da babu jimawa ya zo gidan ɗa ga yayan Hajiya Khadijah Haroon Mahaifiyar yasmine. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance jininta ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya, tana jan fruits table ɗin dake gaban daddy'nta. Tsawa Mafaiyarta da take ƙiranta da Maama t.a buga mata kan cewar bata iya gaida mutane bane? Kana maza tayi hanzarin maida fruits table ɗin data janye daga mahaifin nata. Hannun Ambassador Kabeer ya ɗagama Maama tare da girgiza mata kai alaman ta kyale mishi yarinya haka nan tayi abinda ranta yake so.
"Amma daddy'nta sau nawa zamuyi ta maimaita magana ɗaya kan Ambasajo eheeee? Yasmine fa har yanzu ba yarinyar goye bace gidan wani zata je. Don me ina kallon kusa kurai a cikin rayuwanta tana aikatawa amma da nayi yunƙurin gyarawa kace na dena kona bari? Haba Impossible wllh wannan bame yiyuwa bane bama dole na gyara rayuwar yarinyana da kaina wllh, don duk wata uwa data kasance ta gari ga ƴaƴanta dole zataso ganin ɗan ta cikin kyakykyawar nasaba ba wai a bauɗe irin Ambasajo ba!!!" Daga haka fuuuuu ta bar wurin bayan ta cillama yasmine wani mugun kallon zamu haɗe ne.....
*John*
A..........
_Washhh Hannuna ciwoooo!_
_To ya kuke ganin ko kuke tunanin wasan ze fara?, Nasan wasu zasu fara tunanin...... Ehhhhh ya neeeeee to koma dai miye mu haɗe a page na gaba lol 😄😍🥰 don jin yacce zata kaya_
_Shin shin shinnm...... Kowa yaje yayi tunani ya ƙaraci tunaninsa don duk yacce kuke zata ko tunani to wasan ba haka yake ba lol 😄💃, don nayi ma kaina alƙawarin tabbas sena gindayar daku a wannan karon fiye da MIKIYA, koko TA DABAN, ko kuwa dai DUNIYARMU. koma nace fiye da komai ɗin ma hhhhhh_
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 3&4
Paid book
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION {YOTA}*
_NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA *NIMCY LUV* har abada ƙaunarki ɗaya ce a gareni my Role model me zuciyar lu'ulu'u da Zinare domin duk inda akaje aka zo ke ce AMMEY LAYLERH 💐. Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humy darling princess tawa, my support system, my Role Model I love you_
*Zuciyarki fara Aniyarki fara, kyautatawa Halinkine, Mutunci da karamci duk a tare suke dake,MAMAN IHSAN tawa har gaban abada ke kaunar AMMEY LAYLERH ce, Ina Sonki da yawa da yawa ina matuƙar godiya gareki tare da sake jaddada ƙaunarki gareni*
_Special Thanks to Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗_
ꨄ_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦°♡
*John*
Yana shiga bedroom nashi sarƙar cross ɗin dake wuyansa ya zare, yana ratayeta jikin wani ɗan hangar ƙarami mai kyau dake cike da sarƙoƙi kala-kala a ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban mirror'n yanata faman yamutse fuska. kana a natse ya mike kansa tsaye yana nufar bathroom. Yana shiga babu jimawa aka fara knocking kofar bedroom nashi, amma sai ya sha re yana ci gaba da abinda yake da uzirinsa.
Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin farar ƙafarsa dake nan fara tass ta bayyana, yana ƙarasa fitowa jikinsa sanye da bathrobe sky blue,
Hannunsa ɗaya kuma na rike da karamin towel yana tsane gashin kansa da kallo ɗaya zakai ma gashin ka fahimci yana masifar lasar manyan kudade bana wasa ba, kodan kyau da kyallin da gashin keyi domin yafi karfin a kirashi da suma. Duk abinda yake yi tana nan maƙale a ruhinsa da tunaninsa, Sam beyi tunanin ganin Madame Victoria a bedroom ɗin ba. Bata face nashi yayi tamkar wani yaron goye yana nufar inda take zaune daga bakin bed nashi. Zama yayi gefe da ita tare da jingina kansa da jikinta. Bayansa ta shafa a hankali inda ya waro manyan fararen idanuwansa cike da tsoro, jin ta tabo masa inda waccen babyn robar ta jefeshi. "Ouch Mah!!!" ya sake furtawa da ɗan ƙarfi jin ta sake taɓa masa wurin. Kansa ta dungure masa tana tashi ta ɗebo masa ƙananan kaya black da black ɗin speck. Closet nashi ya shige don baya taba shiryawa gaban Mommah ɗin nashi, duk lokacin data masa kutse irin haka duk kuwa da yanda take sashi gaba. Bai wani jima sosai ba se gashi ya fito cikin black ɗin shigar, inda yamay wani kalan kyau bana wasa ba wanda ya sake fito da ainihin hasken farar fatarsa me kyau da mirjewa. A gaba ta sashi suka fita zuwa entrance dinner na gidan baki ɗaya. Wanda kowa ke hallare a wurin, Mr jef deefer ne ya fara taryan yaron nashi da kayataccen murmushinsa me kyau, kafin X Eeshika itama ta sakar masa nata murmushin wacce take Ƴa ga kanwar Mommah nashi, daga nan se jelly wacce take kanwa a gareshi. Yana zama kujerar kusa da paah ɗin sa X Eeshika ta tsalloka tsilik zuwa kujerar dake kusa dashi, wacce ke pacing nashi. Kwanciya yayi jikin papanshi Mommah ce ta miƙe tana me furta. "Stand up and eat your food" Ta faɗa tana mantawa da gadon bayansa tana ɗagoshi, wata uwar ƙara ya sanya yana riƙo gadon bayan, Se wani haɗa uban zufa yake yana matse kyakykyawar fuskar nan tamkar wani yaron goye, saurin sanya hannunta tayi tana dafe bayan nasa tana furta. "Ohhhh Jesus Sorry boy sorry!" Madame Victoria ta faɗi tana tada shi zaune daidai da tallafin papah'nsa, Sannu mutanen parlourn suka shiga masa x Eashika harda guntuwar kwallarta. Jelly ce tayi saurin ƙara gudun fanka tsabar ɗaurewa karya ƙugu, "Ma'am What wrong with this john?" X Eashika ta tambaya Mommah kai tsaye. Nan madame Victoria ta sanar dasu abinda ya faru, haba nan fa suka shiga babin tsinema Hausa girl dukansu, cikin su kuwa harda masu cin alwashin duk ranar da suka haɗu da yarinyar se sun fasa mata baya itama kamar yanda ta fasama John ɗin su. Jin yanda suke zagin masa pretty ne ya sanya John miƙewa yana me furta.
"Momma I can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping". Ya bata amsa can ƙasan maƙoshinsa. Kuma ya faɗi hakan ne bawai don hakan yake ba, A ahh kawai dai ze basu wuri ne bazai iya zama ana zagar masa love tashi ba. Duk da kallo suka bishi suna son masa magana suna kuma tsoron masan ya sauƙe musu ruwan Bala'insa da ya iya buhu², don shi tamkar fire and Ice haka yake, yanzu za'a kalleshi cikin nishaɗi yanzun kuma za'a kalleshi cikin mugun tsare gida da ɓacin ran da idan ka ganshi a lokacin zama kayi tunanin cewar be taɓa sanin wata aba wai dariya bane. Don haka kowa yayi gim da bakinsa yana tsoron masa magana.
_Great place a wonderful mension_
Mension ne babba da ko a cikin Cristian suke ji dashi, domin kuwa shi ne lamba ɗaya wanda sunansa ya zage baki ɗaya katafanin garin Lagos ɗin harma da kewayenta, sunan POWER kun san me ma'anar sunan yake nufi, kalmar POWER kalmace dake tattarene da karfin iko, Isa, Izza, taƙama. ★ *Mr jef deefer* shi ne ƙatoton arne lamba ɗaya da suke ji dashi. Baya da Imani ko kaɗan, haka Kuma baya da tausayi ko rangwame bare yafiya. Idan kanason ganin murmushi ko dariyarsa to ka tabbatar yana tare da zuciyarsa ne gaba ɗaya wato John. Wani irin mahaukacin So uwa da ubansa suke masa, Wanda samm samm hankali baze Iya ɗauka ba. Mahaifinsa Mr jef deefer Wani irin shimfideden iko yake gudanarwa, sedai samm baya taɓa yarda da maci Amana ko kaɗan. Idan kuwa har ya kama mutum da cin amanarsa yana gindile masa yan yatsu biyu ne, ma'ana babbar yatsar mutum da kuma yar ƙurinsa wannan shi ne hukuncin wanda ya kama da laifin cin amanarsa. A tsarin mension ɗin nasu kuwa. Wani irin katafaren mension ne mai matuƙar kyau da tsaruwa, Wanda ya gama gajiya da haɗuwa iyaka haɗuwa kam gidan nan ya haɗu, kai da ganin ginin gidan kasan masu rayuwa a cikin sa sedai wani babban ƙusa daga gomnati ko dai wani babban ɗan kasuwa ne, gate ɗin gidan kawai abin a tsaya a kalla ne, bangaren uku ne a cikin gidan ga wani dan ma dai dai cin pool a tsakar harabar gidan, daga gefen hagu katafaren parking space ne mai dauke da ƙaton rumfa gefe guda kuma ga wasu fittatun manyan motonci nan babu kalan da babu, tin daga kan su *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll-Royce boat Tail* *land cruiser * Kai ganan dai su motocin babu kalan da babu, su kansu kawai abun kallo ne. daga gefen dama kuma shuke shuken plowers ne in different colors awajen masu matuƙar kyau da ban sha'awa. daga ɗan gefen parking space ɗin kuwa, wani Katafaren wajen hutawa ne dake zagaye da glass. wajen ɗauke yake da wasu ƙayatattun sofa
set ɗaya launin sky blue, a tsaƙiyar kujerun kuma wani haɗaɗɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen, daga gefe guda kuma ga wani irin deep fridge ƙawace da wajen, Wanda suke ɗauke da lemukan sha da barasa, haɗuwa kam gidan ya gama tsaruwa tabbas. Kai tsaye balcony na gidan yayi shigewansa phone náshi tare dashi, Akan wata doguwar Royal Caribbean chier yakai zaune, yana taune gefen lips náshi da tsarin halittarsu yake pink. gaba ɗaya tunaninta ne yake neman fasa kansa,kodan be taɓa jin hakan dangane da kowacce mace bene oho. Amma dai abinda kawai ya sani seya mallaketa kota yayane. Gaba ɗaya lissafinsa cikin lokaci ƙanƙani ya nemi daya kwance, dukkan wani motsi da zayyi ƙamshin turarenta kawai yakeji daya shaƙa yana sake hargitsa tunaninsa, ya sani tabbas shi masoyin ƙamshi ne but a rayuwarsa bai taɓa jin asalin ƙamshin daya taɓa masa ba bayan nashi ƙamshin se yau daya shaƙa nata. Tsaye ya miƙe yana riƙe da ƙugunsa ya fara aikin safa da marwa, yana ma rasa ta ina tunanin wannan Baby'n robar ke kutso masa kai?. Da misalin ƙarfe 9:44 ya lallaɓa ya fito zuwa compound na gidan.
Kai tsaye bayan ya baro ɓangaren sa parking space ɗin dake gidan ya nufa, dake daidai lokacin babu kowa shi ya bashi damar shigewa cikin motar nashi, yana tada ta ya fice a gidan bayan ya ba get man umarnin buɗe gidan. ko lamps ɗin motar bai kunna ba gudun kada a ganshi tamkar wani ɓarowa haka ya saɗaɗa yana ficewa a gidan baki ɗaya. Yana ɗan nesa da gidan nasu ya kunna lamps na motar ya harbata saman titin. Wanda daidai lokacin garin ke haɗe wani irin hadarin da yama sama ado ta hanyar ƙawanyar daya masa da gajimare.
*Ambassadors kabeer house*
Gaba ɗaya mutanen gidan zaune suke cikin wani katafaren parlour na alfarma, Me ɗauke da wasu manya manyan sofa set guda masu numfashi wanda suka kasance masu launin blue da milk, Wanda kalan sukayi wani irin ƙawata parlour'n sosai suka sake fito da asalin kyaun sa, inda yaji komai da ake buƙata na rayuwa, wanda idan nace zan tsaya zayyana muku kyan parlour'n kaɗai ɓata ma juna time,A natse matashiyar yarinyar wacce take fara tas yanayin jikinta kuma kai tsaye na bayyana tsantsar hutu da jin daɗin da suke ciki ta ɗan saci kallar mamy'n nata tare da furta. "Aunty yasmine tana lafiya kuwa Mummy?, Har yanzun bata fito ɗinner ba. Ita da mahaifiyar nata suna sanye cikin shiga iri ɗaya na lace doguwan riga inda ita yarinyar nata a kasance fitet gown ne, ita kuma uwar normal doguwan rigawa esharp. Cakkk kuwa Abbin nasu ya dakata daga sipping coffee ɗin da yake yi, tare da dubar matashiyar yarinyar yana me furta. "Maza Husna je dubomin ko lafiyarta" yay maganan yana dire bowl ɗin dake hannunsa ya zubawa upsairs nata idanu tare da buga wani uban tagumi. Takun takarmin ta da kuma ƙamshin turarenta da baya taɓa ɓuya kawai mahaifin nata ya shaƙa ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya. Har zuwa lokacin data ƙara so cikin tsaƙiyar parlour'n ba a sake ba. "ALLAH sarki Ambasa Baby'n daddy'nta ƙaraso mana",cewar mahaifin nata, wanda ya sata ƙarowa sum sum domin bata mata kashedin mahaifiyar nata ba da tace da ita zasu haɗe. Don duk iskancinta tana tsoron mamy'n nasu. Sum sum take tafiyar har ta kai gaban daddy'n, zaunar da ita yayi gefensa yana tura mata duka kayayyakin dake jere a gabansa. "Eat it ambasajo na" Murmushi ta masa tana gyaɗa kanta wanda babu ko band. "Ina ɗankwalin ki Hau'wa?" Haka ta tsinkayi muryan Mummy nata wacce tayi maganar da ɗan ƙarfi, tura ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi, domin idan da sunan da yasmine ta tsani taji an ƙirata dashi to shi ne Hau'wa. Har ƙara ƙara yasmine ɗin ma amma ita a son samunta kowa ma ya dinga ƙiranta da ambasajo ɗin da mahaifinta ke ƙiranta dashi. "Ba magana na ke miki bane yasmine?" Ta sake wulla mata tambayar a karo na biyu. "Ambasajo ɗin Daddy'n ta maza tashi kije ki samo ko hula ne, Mummy naki bata son a zauna lafiya kinji". Kanta ta ɗaga mishi tana tashi tana tashi,"yawwa that's my girl" babu jimawa kuwa se gata ta dawod da Baby shijjab jikinta. _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ kenan da akafi sani da suna _YASMINE HUTU_ ƙyaƙyƙyawar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu a duniya. Wacce ta kasance ɗiya da farko a wurin mahaifinta Ambassador kabeer Usman Maina, Mahaifinta sananne ne da kowa kusan duka duniyar ta sanshi kasancewar matakin ambassador ɗin daya riƙe.Bayan haka babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin duk wani company'n dake tashe a zagayen Lagos da ketarenta. Yasmine yarinya ce da batajin magana sammm, amma ga wanda be santa ba kai tsaye ze mata kallon nutsatstsiyar yarinya ne, Se dai sammm ba haka take ba. Wanda badan mahaifiyarta dake tsaye a kanta ba da tuni rayuwarta ta jima da taɓarɓarewa, domin kuwa mahaifin shike wuce mata gaba a duk wani rashin ji da kirki nata, Idan mahaifiyarta ta tilasta mata zuwa islamiyya setayi tafiyarta manyan club's ko park. Se ta dedeci loƙacin tashi yayi kana ta nufo gida. kullum zaka kalleta idan zata tafi cikin shigar kayan islamiyya, wanda hakan yasa wasu ke mata kallon kamila kuma natsassiyar mace. gata masifaffiyar gaske ce lamba ɗaya ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu, Musamman ma ga mahaifinta ambasador kabeer maina. Gatan data samu da rayuwar da take a cikin ta seta tashi tamkar renon turai,Inda ta samu zurfafa kanta harta samu wadataccen ilimin boko, sedai na addinin kuwa ko oho amma fa idan ka taɓa ta akan addinin ta bata barin ko ta kwana, wacce zaka ɗauka cewar ita ɗin irin wannan shahararrun yaran nan ce masu haddar Alqur'ani izu sittin a kansu, sedai ko rabin izu bata da. Karatunta kuwa gaba ɗaya a ƙasar ƙetare ta yisa, idan ka cire Nursery school datai a Nigeria kawai. Sam bata son harkar talauci ko haɗa hulɗa da mutanen da suka kasance talakawa, wannan dalilin nema yasa sammm ta tsani islamiyyar da Mahaifiyata ta saka ta. A cewar ta haɗa wurin zama tare da su harma da shaƙar numfashin juna kan iya taɓa ta itama, wai wataran ta zama irinsu kodai ta auri talakan, Wannan dabi'a tata yana taɓa mahaifiyarta kwarai da gaske. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shi ne kasancewa da namiji. Sedai takanyi irin su sking love haka don tace wannan kamm babu laifi, amma fa ba Inji AMMEY LAYLERH ba 🤗 🤣 ato. Inji yasmine lol 😄😍........
"Ambasajo ku matso mu fara dinner, kamar Omer yana nan ma ko?" Yayi maganar da alaman tambaya. Husna ce ta ɗaga kanta ita kuwa yasmine ko motsi batayi ba, duk kuwa da cewar Omer ɗin dan ita yazo.tana ƙoƙarin buɗe kyakykyawan foodplask ɗin dake gabanta, sega Omer ɗin nan ma yana sauƙowa daga saman bene mai ɗan jiki kaɗan haka fari tas da shi. Wanda fuskarsa ke ƙawace da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo, yana da manyan maganai kamar bull ga dogon hanci, wanda kallo ɗaya zaka masa ka kalla irin tsantsar kamar dake tsakanin sa da matar da suke kira da Mummy. A natse ya ƙara sa saukowa daga zuwa downstairs ɗin yana zama. Tare da furta. "Good evening Daddy", "Good evening Omer how was your night?" Cewar Daddy ɗin Mummy na tura masa plate ɗin dake ɗauke da abinci. Husna ce ta fara gaida shi, yayin da yasmine ta sha kunu, domin ita yanzu tunda Mummy nata ta fara sako zancen aure tsakaninta da Yaya Omer ɗin ta dena sakar masa fuska. "Hala yasmine da dukkan alamu bata ga Omer ba ko?" Mummy ta faɗi cikin gatse. Fuskarta ta ɓata ita fa wllh shi yasa sammmm bata son zama kusa da Mummy'n, duk wasu hanyar kusheta seta fito mata dasu, da kuma diagata gaban ko su waye. Ranta a ɓace ba tare data kalle shi ba ta ce dashi. "Ya Omer good evening da "how was your night?" Ya amsata yana ɗan sakar mata murmushin sa me kyau. _I don't like her_ ta faɗi a zuciyarta tana murguɗa masa baki, wanda hakan da tayi ya sanya Omer ɗin kallonta yana waro idanunsa sosai yana kallonta speechless. "Baby yadai? Nafa kina murguɗa min baki" Ya faɗi yana sake waro idanunsa akanta. "Malam wai ina ruwanka da nine ka fiye takura min fa Aha! Kana takura rayuwana."
"Ya takura rahuwar taki yasmine!, Me ya sa ke samm baki da kirki ne idiot kawai" Mummy'n ta ta faɗi a fusace tana miƙewa tayo kanta. Wanda ya sa ta kwasa a mugun guju tana ce dashi zasu haɗu ne. Ta haye samanta tana sauƙe ijiyan zuciya, a gaban mirror taja ta tsaya tare da zare band tare da ribbon ɗin kanta, tana tsurama kanta Ido slowly ta tura hannayen ta cikin gashin kanta, ko me ta tuna kuma se ta wani daki kan nata kaɗan. Tana me furta "Ohhhh ALLAH!!!" A bayyane sakamakon gilmawar kyakykyawar face nashi data gani a cikin zuciyarta. Daidai kuma lokacin ne aka fara yayyafi, kafin a tsuge da ruwan saman sosai, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta ga gauraye ko ina dake cikin garin. A daidai kuma wannan lokacin John ke zaune cikin motarsa yayi Parking nata a wani bakin masjid. Tin yana saka ran za'a dauke ruwan har ya cire. Don kuwa yaga abin bana ƙare bane, se yaji duk zaman motar ya gama gundirarsa. Don haka a natse a kuma wani irin Hankali ya fito daga cikin motar. Wata brander ya hango babu kowa a wurin, se yaji kamar hankalinsa ya ɗan nutsu da daya zauna a wurin. Umbrella ɗin dake bayan motar ya miƙa hannunsa yana ɗauka, kai tsaye yana yin wajen....
*Around 5:00pm*
♡
Ahankali slowly ya shiga buɗe blue eyes nashi wanda suke ɗauke da barci, kai da ganin idon nasa zaka san cewar idon nasa barcin be gama ishar shi ba, yanayin seya sanya idon nasa ya ƙara kyau dan yanayin se yayi yanayi na daba, wani kalan saurin miƙewa a zabure yayi tuno da wani kalan hargitsetstsen mafarkin da yayi akanta. Wani kalan duka yaji ƙirjin sa ya masa lokaci guda, wadda yasa yaji barcin ya watstsake masa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar makeken gadon nasa yana dafe da saitin faffaɗar kirjin sa, "What happiens?, Meke shirin faruwa da rayuwana? " dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa zuwa ƙasan bed ɗin kana ya miƙe yana nufar toilet. Wanka yayo yana fitowa jikin sa na ɗigar ruwa ya shirya kansa cikin wani haɗaɗen jeans mai kyau da tsada launin baki da high neck sleeve shirt launin ash, hakan ya bayyanar da kakkafar suran ƙirjin sa, faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaɗar kirjin nasa ta kara buɗe wa sosai, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su se hular pcap ɗin daya sanya, bayan ya ɗaure dark black curly hair nashi inda gashin ya sakko harta ƙasar ƙeyarsa. Kai tsaye yana fitowa zuwa garden na shi, yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, fuskar nan a ɗaure take tamau don mafarkin da yayi sosai ya sake taɓa zuciyar sa,