ta tunkaro, birnin gadan-gadan, nan fa
ran sarki Haiman ya kara baci sosai.
Yayin da Bokanya Amsadatu ta iso, sai
Sarki Haiman ya umarce ta da ta buga masa
kasa domin gano inda 'yarsa Anisa take, nan
take Bokanya Amshadatu ta fito da wasu
alkalumma ta baje akan kasa, sannan ta zana
wani hatimi ta share, ta sake zana wani hatimin
ta sake sharewa. Sannan ta tsaya tana wasu
sambatu, can sai ga wani hayaki ya bayyana a
kusa da su. Can, sai ga hoton Gimbiya Anisa
ana saka mata magani a raunin da aka ji mata.
Nan take Bokanya Amshadatu ta rinka nuna
Sayyar tana fadin "Shi ne, shi ne, ga shi nan, shi
ne...."
"Shi ne wa.?" Sarki Haiman ya daka mata
tsawa
"Sa.........yyar....... yar..yar." Muryarta
na rawa take ambatar sunan.
"Sayyar!?" Sarki Haiman ya tambaya cike
da mamaki
"Shakka babu shi ne, zai kwace maka
mulki idan ba ka dauki mataki ba yanzun nan."
Ta sanar da shi.
35
na
Ο
C
"Maza ki sa aka mashi." Ya umarce ta.
Nan take ta fito da wata buta ta bakin karfe,
ta zazzage wani bakin gawayi a cikinta, sannan
ta kalli rana tana wasu sambatu tare da kiran
sunan wani Hadimin Aljani, kafin wani lokaci
sai ga wani katon aljani ya bayyana, misalta
kamanninsa ba karamin tsoratar da makaranta
zai yi ba.
Nan take ya yi wata girgiza, sai ga kasu
bakaken aljanu suna fitowa daga cikinsa, ya yi
wata hamma iska mai karfi ta fito, yayin da ta
tunkari inda rundunar Musulmin ke fitowa, nan
da nan iskar ta dinga fisge itatuwa tana awon
gaba dasu, gidaje kuwa suka dinga bajewa, kasa
ta dinga tashi tana barin hako kawai.
"Ma za aka wo min Sayyar nan in da nake
yanzu." Bokanya Amshadatu ta bukata
A can kuma yayin da rundunar su Sayyar
din take zuwa, sai suka hango wannan iskar ta
doso su, nan take sai ya karanto wasu addu'o'i
ya karbi ruwa ya kuskure a bakinsa ya furzo, sai
nan take iskar nan ta juya ta dawo baya, yayin
da su Bokanya Amshadatu suka ga haka, sai
hankalinsu ya tashi, nan fa suka fara gudun
k
n
Kra
na
a
K
S
neman tsira, amma kafin wani lokaci tuni iskar
tazo ta yi awon gaba da Bokanya Amshadatu
tare da wasu daga cikin dakarun Sarki Haiman.
Haka su Sayyar suka shigo cikin birnin
suka dinga dauki-ba-da-di tsakaninsu da
rundunar makafirta.
Kwana biyu ana fafatawa tsakanin su, inda
a Rarshe Sayyar ya shiga cikin kurkukun tarc da
wasu dakaru 'yan uwansa cikin wadanda suka yi
gudun hijira, nan ya samu an sakawa
mahaifiyarsa macizai suna kokarin sararta, nan
fa suka dauke kawunan macizan, suka kwance
ta suka fito da ita. Har a wannan lokacin ita
kanta ba ta gane Sayyar danta ba ne, sai da aka
suka fito tsakiyar filin gidan, in da anan wasu
dakarun sarki Haiman suka yi masu kawanya.
Can sai ga Bokanya Amshadatu itama ta faso
gini ta shigo, shima sarki Haiman da wasu
dakaru suka bayyana a wurin. Sarki Haiman ya
kyalkyale da dariya tare da nuna Sayyar yana
mai dakawa wasu dakaru tsawa da yin umarni
gare su, cewa su kama su.
Nan fa suka yo kan shi, Sayyar ya dinga
saransu da takobinsa ba ji ba gani, duk in da ya
kai sera sai kaga an fadi, mutum biyu suka
37
kange mahaifiyarsa, yayin da wasu suka shiga
suna taimaka masa, ita kuwa Anisa wani aljani
aka sa ya damke ta, nan take Sarki ya sa aka je
aka jefa ta a wani daki aka kulle bayan an daure
ta da sarka.
Kafin wani lokaci sai dakarun dake wurin
suka wanzu a kasa, wasu sun mutu wasu suna
mirgineneniya a kasa suna magagin mutuwa.
Bokanya Amshadatu ta yi wata kururuwa,
ta buga kafarta a kasa, ta kira wani suna, yayin
da ta yake baki ta fara sakin wani bakin hayaki,
can sai'ga wani gabjejen bakin basamudan aljani
ya bayyana, ta nuna Sayyar ta ce ya afka masa.
Nan da nan Aljanin nan ya nufi Sayyar da wata
irin guduma narkekeya a hannunsa, ga wani
takobi rike a hannunsa bai fitar da ita daga cikin
gidanta. Ya dauki Sayyar da hannu daya, ya
cilla shi sama, ya fado kasa ya mirgina sau uku,
sarki Haiman ya yi tafi gami da dariyar
mugunta, sannan Sayyar ya yi karfin hali ya
tashi, yayin da aljanin nan ya sake nufo shi, ya
dauko takobinsa ya wurga masa ta cake shi,
amma yaga ko gizau bai yo ba, ya zo ya sake
daga shi ya yi jifa da shi, Sayyar ya fadi gindin
38
dabinon nan in da har yanzu takobın da Sarki
Haidar mahaifinsa ya soke tana nan a jiki.
Aljanin nan ya nufo Sayyar gadan-gadan,
da ya kusanto shi sai ya zare takobinsa da nufin
yana zuwa zai raba Sayyar gida biyu, hankalin
Sayyar ya tashi, ya duba yaga babu wani
makami a kusa da shi, nan da nan sai ya mike ya
isa jikin takobin nan da ke kafe jikin bishiyar
dabino, ya kama zai zaro ta, yana kamawa kuwa
ya fara ja sai ta taho tare da wani haske
matsananci. Hasken yana kaiwa jikin aljanin
nan, sai ya fara kara yana komawa da baya,
ganin haka sai Sayyar ya ci gaba da zaro takobin
hannunsa na kyarma, takobin na jijjiga shi. Nan
fa duk sai aka tsaya ana kallon Sayyar cike da
mamaki. A daidai lokacin ne mutanen gari suka
yo caa! Suka shigo tsakiyar makeken filin gidan.
Ganin abin da ke wakana ne ya sa kowa ya ja ya
tsaya, har lokacin da Sayyar ya zare wannan
takobin a jikin bishiyar dabinon nan, yana zare
ta ya yo kan aljanin nan gadan-gadan, nan take
sai ga aljanin 'nan ya narke ya zama ruwa don
tsananin azaba.
Mutane suka yi kabbara tare da nufo
Sayyar suna murna. Hakan ya y daidai da
lokacin da Gimbiya Anisa ta fito a guje, sarkar
dake jikin ta, ta kwance babu komai, wasu daga
cikin mayakan suka shigo da daurarro wadanda
aka ribace su daga rundunar sarki Haiman.
Nan fa murna ta kama mutane, aka kama
sarki Haiman da sarkoki tare da Bokanya
Amshadatu, da wazirin sarki Haiman, da sauran
wadanda suke tare da shi.
A daidai lokacin ne Amar ya shigo bisa
wani ingarman doki yana haki tare da kura wa
Gimbiya Anisa ido.
Yasan dai ta fi karfinsa, dole kuma ya
hakura da cewa zai same ta.
Ta rogo da gudu ta tsaya gaban Sayyar tare
da kura masa idanu, hakan ya yi daidai da
zaburowar mutane suka daga shi sama ana
murna.
Mulkin zalunci ya karfe a: BIRNIN
DAULATUL-SAKAF, domin Sayyar zai karbi
kujerarsa.
TAMMAТ
Naku: IBN SALIS.. (NAFS!)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels