An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KAMBUN
KARFE
NAFI'U SALISU
IBN SALIS
SALIS
KAMBU KARFE - 2
ana gaba suna biye da ita cikin takun
kasaita da nuna akwai mulki, yayin da kuyanginta suke take mata baya. Mutane suna
yin gaisuwa gare ta cikin girmamawa, yayin da
kuma suke bata hanya da gaggawa, duk da cewa ba kan wani abu take tafe ba, balle ace ko suna jin tsoron a bi ta kansu ne a take su, wannan ya
nuna tsananin girmamawar da suke yi a gare ta
ya wuce wasa.
Gimbiya Anisa kenan.
Tana rike da dan kyakkyawan tsuntsunta,
yayin da ta rungume shi a jikinta, kuma
hankalinta ya fi karkata izuwa gare shi. Iskar
dake kadawa a cikin yammacin, yana busa ta
tare da kuyanginta, yayin da hakan ya wanzar
masu da nishadi baki dayansu.
Sayyar ya wanzu cikin dan kyakkyawan kejin da Gimbiya Anisa ta mallaka wajen 'yar'uwarta tun tana da rai, wanda a yanzu ta shafe shekaru da yawa da mutuwa, sakamakon ambaliyar ruwa a kasar da take aure.
Sayyar, kuma wanda a yanzu yake a
matsayin tsuntsu, shi ne abu mafi girman
al'amari da ya jefa so da kauna a cikin zuciyar
Gimbiya Anisa, ta ji tun da take a rayuwarta ba
ta taba son wani abu ba kamar tsuntsun da ta sa
a cikin kejin nata ba. Da farko ta saka kejin ne a
cikin wani dan madaidaicin daki, yayin da take
kula da shi wajen ba shi abinci da abin sha, haka
nan kuma ta ji dadin yadda tsuntsun yake jin
duk abin da take fada, duk da cewa bai kasance
Aku ba. Daga baya sai ta dauke shi tare da kejin
ta maida dakin kwananta, ta rataye shi kusa da
gadonta, kamar yadda ake rataye kwarya akan
ragaya. Ya zamo shi ne abin da ke faranta mata
rai yayin da take bakin ciki, ya zamo shi ne abin
da ke debe mata kewa, ya zamo shi ne abu na
farko wanda idan ta yi tozali da shi take jin
nutsuwa a cikin zuciyarta. So da kaunar da take
yi wa tsuntsun nan, ya sa ta saka mishi suna,
sunan da take ganin ya dace matukar dacewa da
shi.
NURUN KALBI (Hasken zuciya).
6
BABI NA BIYAR
mar yana zaune a bakin - gadon
Abarcinsa, ya yi shiru tare da daga
kanshi sama yana tunanin labarin da Abusamar
Dattijon Makerin nan ma'abocin kira, sannu a
hankali abubuwan da ya sanar da shi suke
wanzuwa cikin kokon zuciyarsa. Yana matukar
son ya mallaki kambun nan na gidan sarauta,
amma ta yaya za a yi ya iya cire wannan takobin
dake jikin bishiyar dabinon can da Marigayi
Sarki Haidar ya soka a jiki, ya kuma tabbatar wa
mutanensa cewar, babu wanda zai iya cire ta sai
dansa Sayyar? Idan haka ne kuwa, to lallai zai
yi wuya ya iya mallakar wannan kambu,
ballantana har ya sa ran zai iya mallakar
Gimbiya Anisa 'yar Sarki Haiman.
Ya yi ajiyar zuciya.
".........Bayan wasu 'yan shekaru da
murkushe dakarun Sarki Haiman da rundunar
Sarki Haidar suka yi, sai rashin lafiya mai
tsananin karfi ta wanzu akan Sarki Haidar, a
yayin da hakan ke faruwa, sai ga rundunar Sarki
Haiman babu zato babu tsammani, suka afka
cikin birnin Sarki Haidar, suka shiga kashe
rayukan Jama'a. Kafin wani lokaci tuni sun
7
hallaka mutane da dama, suka samu damar
dauke Aisamatu suka tafi da ita gaban sarki
Haiman bayan sun saka mata sarka, yayin da
suka baro kasar ana dauki-ba-da-di da mayakan
sarki Haidar.
Duk da cewa sun yi mamayar ba zata,
amma hakan bai hana jama'ar Sarki Haidar yin
nasarar daukar fansa ba. Sai dai tuni sun ci
karfin su, domin a wannan lokaci akwai dakarun
da suke tsaron Sarki Haidar........" A hankali
ya ke tuna irin labarin da Abusamar ya ba shi,
dangane da Sarki Haidar. Amar ya sake jin
ajiyar zuciya a karo na biyu, sannan ya ci gaba
da tunanin labarin da Abusamar din ya ba shi.
".......Dakarun Sarki Haiman suka mamaye kasar
Sarki Haidar, yayin da suka fuskanci sun ci
galaba akan musulmi, sai suka yi aike ga Sarki
Haiman, in da nan da nan ya taho tare da wani
ayarin na rundunar mayaka, suka wańzu cikin
birnin Daulatul Sakaf, in da suka samu Sarki
Haidar rai ya yi halinsa. Nan take suka kama
sauran jama'arsa suka maida su ba yi, wasu daga.
çikin su kuma suka hallaka ta hanyar kisan gillar
da Sarki Haiman ya sa aka yi masu.
8
a
i
1
i
a
Bayan shekara daya da cinye Kasar da yakı.
sai Sarki Haiman ya sa aka rushe birnin baki
daya, aka yi sababbin ginc-gine, ya kuma kafa
masarautarsa a nan, shi ne ya sa wa birnin suna,
Daulatul Sakaf. Daga nan ya ci gaba da
mulkinsa na zalunci, yayin da talakawa suke jin
tsoronsa, haka nan babu wanda yake raga wa
maza da mata. Aisamatu matar Sarki Haidar
kuwa, tana kurkuku a tsare daure da sarka.
Sarki Haiman ya sa wata Bokanyarsa,
wadda ta kasance tsohuwar matsafiya ce, ta yi
masa bincike game da yadda za'a yi a cire
wannan takobi daga jikin itaciyar dabinon nan,
yayin da ta yi masa binciken cikin ilimin
Bokancinta, sai ta shaida masa cewa, lallai sai
ya mallaki wani kambu na bakin karfe. Yayin
da ya ji wannan batu, sai ya tambaye ta.
"Ya ke Amshadatu, a ina wannan kambun
bakin karfe yake cikin fadin duniyar nan.?"
Bokanya Amshadatu, ta girgiza kai sannan
ta yi murmushi. "Shi wannan kambu na bakin
karfe, ya na can karkashin wani bakin dutse,
yamma da kasar Spain, daga nan zuwa can
tafiyar shekara daya ce akan ingarman Doki,
amma ga matashin Aljani kuwa tafiyar sa'a guda
ce,"
Yayin da Sarki Haimana ya ji haka, sai ya
ce, "To na umarce ki, da ki yi gaggawa wajen
saka daya daga cikin hadimanki domin su dauko
wannan kambu."
"Kar ka samu damuwa ya shugabana, lallai
zan cika umarninka, rana ta baka nasara."
Yayin da Bokanya ta yi bankwana da Sarki,
nan da nan ta fita zuwa turakar tsafinta, ta kuma
umarci wani hadimin aljaninta da ya je ya fauko
wannan kambu na bakin karfe.
Washe gari sai ga kambun bakin karfen
nan an kawo wa Sarki, Sarki Haiman ya yi
murmushi tare da kallon kambun, sannan ya
jinjina wa Bokanya Amshadatu.
"Ya kc wannan ma'abociyar sanin ilimin
tsafi, maza bani labarin yadda mutum zai yi
amfani dashi kafin ya samu damar cire wannan
takobi a jikin itaciyar dabinon can."
Bokanya Amshadatu ta kyalkyale da
dariya, sannan ta kalli Sarki Haiman ta na mai
girgiza kai bayan ta dakata da dariyar.
"Wannan al'amari 6oyayye, domin babu
wanda yasan wannan sirri sai Sarki Haidar,
kuma ya riga ya mutu." Ta sanar da shi
Shima yanzu jinjina kai ya yi
"Yanzu ina mafita.?" Ya tambaye ta
"Mafiya daya, sai dai ka bani nan da wani
dan lokacin domin in ci gaba da yin bincike
game da hakan, amma idan ba haka ba, ban san
akwai wata mafita ba tukun, sai abin da
alkalumma suka nuna min."
"Jc ki, na baki lokacin duk da ki ka ga ya
dace da samun mafita." In ji Sarki Haiman
Daga nan suka rabu akan haka.
Amar ya sake yin ajiyar zuciya, domin da
izuwa yanzu ya fahimci al'amarin kambun bakin
karfen nan na da girma, sai dai kuma bai san
abin da Kakansa yake nufi da ya umarce shi da
cewa, yajce gurin Abusamar ya kera masa irin
wannan kambu ya kawo masa shi.
Ya tashi cikin sanyin jiki, sannan ya nufi
wani bangare na dakin nasa, ya bude wani
Katon akwatu na bakin karfe, ya dauko kambun
karfen da Dattijo Abusamar ya kera masa,
sannan ya dauko hoton wancan kambu na sihiri,
11
ya Kare musu kallo gaba daya, yaga komai nasu
iri daya ne. Ya yi wani murmushi na karfin hali,
sannan ya kudurce a zuciyarsa abu daya ne ya
rage masa yanzu, zuwa wajen Kakansa da
kambun.
**
Aisamatu daure da sarka a cikin kurkuku,
yayin da take cikin wani mawuyacin hali na
tsanani, alamun manyanta ya fara bayyana a
gare ta. Babu abin da ya fi damunta, face abu
biyu, na farko rashin maigidanta, sannan na biyu
rashin danta Sayyar, tare da bakin cikin halin da
take ciki a yanzu, na kaskanci da cin mutunci,
cin zarafi da tozartawa.
Kanta a duke tana zubar da hawaye, yayin
da abin duniya ya sha mata kai, ji take yi
mutuwa ta fi mata dadi a wannan lokaci, sai dai
lokaci-lokaci takan yawaita ambaton Allah;
domin ya kawo mata agaji game da halin da ta
kasance.
Takun sawun da ta jiyo a wannan lokaci,
shi ya yi sanadiyar barin tunanin da take yi, ta
natsu tana sauraron tafiyar da ake yi. Wasu
dakaru ne su biyu sanye da wasu jibga-jibgan
12
riguna na gashi, suna rataye da manyan takubba
a kafadunsu, fuskokinsu babu alamar annuri, kai
ka ce wasu ifritai ne.
Dakarun da suke gadin kurkukun, tuni sun
mike domin girmamawa gare su, yayin da suka
iso wurin sai suka yi gaisuwa gare su cikin
girmamawa. Nan suka ja suka tsaya suna kallon
Aisamatu dake daure cikin sarkoki, tare da
mika wa ma su tsaronta wata doguwar takarda.
Yayin da daya daga cikin su ya karanta, jikinsa
na rawa ya umarci dayan da ya bude ya fito da
ita, a sakamakon ganin sakon da ya yi a rubuce
daga Sarki Haiman, cewa a fito da ita za aje a
tsire ta.
"Aisamatu." Cikin tsawa wani ya daka
mata tsawa, yayin da ta dago kanta suka hada
ido, tuni an bude gangamemiyar kofar wadda
aka yi ta da wani murtukeken rodi.
Nan take suka tasa keyarta gaba cikin sarka
hannu da kafa da wuya zuwa in da za'a tsire ta
kamar yadda Sarki Haiman ya yi umarni, wai
rana ce abar bautawar su ta umarci a kashe ta,
idan ba haka ba zata hana masu cikar burinsu
game da takobin Sarki Haidar.
13
Gimbiya Anisa ta shigo cikin dakinta, tana
sanye da rigar alfarma irin ta 'ya'yan Sarakuna
ma'abota tarin dukiya da sarauta, gashin kanta
ya warwatsu bisa kafadarta, fuskarta tana
kyalkyali cikin walwala, kamshin turaran
almiski ya na tashi a jikinta.
Kai tsaye ta nufi in da (Nurul kalbi) ya ke
kwance cikin keji, kasancewar yau ba ta fita da
shi ba, amma yanzu da take kokarin tafiya filin
da za'a tsire Aisamatu, dole ne ta tafi da abin
kaunarta don shima ya ba idonsa abinci.
Gimbiya Anisa ta ja ta tsaya cike da
mamaki, hankalinta ya tashi, mamaki mai
tsanani ya bayyana a gare ta sakamakon ganin
tsuntsun nata ya na kuka. Ta isa gare shi sosai ta
na mai razana da yanayin da tazo ta same shi a
ciki.
"Nurul kalbi me ya faru da kai ne.?" Tа
tambaye shi cike da rudewa
Ya kada fukafukinsa daya, sannan ya yi
wani kuka tare da ce da ita.
"Ya abar kaunata, kukan nan da ki ka same
ni ina yi, ba komai ba ne ya sa nake yinsa, sai
waní babban rashi da kike shirin yi yanzun nan,
14
rashin da idan ki ka yi shi, ba za ki samu kamar
shi ba."
Cikin gaggawa ta ce da shi.
"Maza ka sanar da ni, wanne rashi ne zan
yi.?" Ta kura masa idanu
"Idan ki ka bari aka tsire matar nan da aka
fito yanzu a cikin kurkuku, to lallai za ki rasa ni,
sannan kuma rayuwarki zata shiga cikin wani
hatsari. Nasan idan ba yanzu da zan sanar da ke
wani sirri ba, to ba ki taba sanin cewa ni
garkuwar rayuwarki ba ne...." Kafin ya gama
rufe baki, tuni ta juya da sauri ta nufi hanyar fita
waje.
Wani bakin kato murjeje ma'abocin
manyan kafadu, yana tsaye gaban Aisamatu,
yayin da ita kuma kanta ke duke, an daure ta
jikin wasu manyan itatuwa da ke kafe, yayin da
wani daga gefe yake karanto wasu abubuwa
kamar mai karanto laifin mutumin da aka yi
Kara a kotu. Ya na rufe baki sai kuwa bakin
Katon nan ya daga wani sharbeßan takobi zai
sauke wa Aisamatu kai, nan take sai ji ya yi an
rike takobin da majaujawa, kafin ya ankara sai
ga Gimbiya Anisa bisa Doki ta bayyana a
15
gabansu.
"Ka da ka aikata niyyar ka akanta, domin akwai
sauran shan ruwanta a gaba." Gimbiya Anisa ta
fada a daidai lokacin da ta tsaya da Dokin.
Kowa da ke wurin ya bi ta da kallo cike da
mamaki, nan take ta daure fuska tare da direwa
daga bisa Dokin, ba tare da ta tsaya wani dogon
bayani ba, ta daka masu tsawa.
"Maza ku kwance ta daga nan, ku maida ita
cikin kurkuku." In ji Gimbiya Anisa
Kafin ta sake wata magana, tuni suka
kwance ta suna kokarin juyawa da ita.
16
Gimbiya Anisa ta yi ajiyar zuciya, sannan
ta sa hannu ta tura kofar tare da sa kuba ta kulle,
ta dawo bakin gadonta ta tsaya tare da kai kallonta in da Nurul kalbi yake. Ta sake cire
wannan zoben, sai ga kyakkyawan saurayin nan
ma'abocin kyawun sura ya bayyana kamar dazu.
Kyawun sura da halitta irin na saurayin, ya
mutukar rudar da Gimbiya Anisa, nan take ta ji
wani irin shaukin so da kaunarsa ya sake
mamaye mata gurbin zuciya, ta zaune sosai a
gefen gadon nata tana mai binsa da idanu.
"Ka ba ni labari, mutum ne kai ko Aljan.?"
Ta tambaye shi
"Mutum ne kamar ki." Ya fadi haka kawai
"Sunanka fa.?"
"Sayyar bin Haidar.?" Ya bata amsa
"Ya akai ka samu kanka a wannan
matsayin.?"
"Labari ne mai tsawo." Ya ce da ita
Ta girgiza kai tare da mikewa tsaye ta ja baya cikin taku biyu, sannan ta juya baya tare da rufe idanunta.
Sayyar ya mike tsaye a hankali yana kallon dirinta.
"Anisa." Ya kira sunanta
25
"Nurul kalbi." Ta fada cikin sanyi murya
"Ki juyo gare ni, sannan ki tabbar min da
cewa har yanzu kina kaunata a cikin zuciyarki,
idan ki ka yi haka, zan samar miki 'yanci a cikin
Addini mai girma, kuma mafi daukaka da
daraja, sannan ki samu rabauta a wajen Sarkin
da shi kadai ne abin bauta da gaskiya."
"Anisa, juyo ki fuskanci abin da ki ka daďe
kina kula da shi, ki dade kina tarairayarshi, ki
dade kina begensa, ki wanzu cikin tsantsar so da
kauna, idan har kin bada gaskiya da abin
bautarki." Sayyar na rufe ba ki Anisa ta juyo,
idanunta cike da kwalla. Yayin da suka hada ido
sai hawaye ya fara zubo mata a fuska.
"Me ya sa kike kuka yá a bar begena.?" Ya
tambaye ta
"Hakika a tare da kai akwai al'amari mai
girma, ban taba son wani abu fiye da sonka ba,
ban taba kula da wani abu ba, fiye da kai ba. Kai
kadai ne abin da zuciyata ta fi kusanci da shi."
"Har addininki.?" Ya tambaye ta
"Na tabbatar maka da haka." Ta amsa
Ya girgiza kai.
"To ki gode wa Allah wanda ya saka miki
kaunata a cikin zuciyarki, domin yanzu za ki
26
fahimci ba Allahn da ya halicci sana da kasa
kike yi wa bauta ba, domin kuwa shi kadai ne za
ki fi kusanci da shi fiye da komai ki wanzu cikin
karama. Anisa yanzu ina so ki yi min alkawari
uku, na farko dai ki 6oye sirrina, ki kuma yi min
alkawari za ki kubutar dani da mahaifiyata
Aisamatu, sannan ki amince za ki bau bautar
abin da ku ke bautawa. Idan ki ka yi haka za ki
fahimci rayuwar da ki ka yi a baya, tamkar
rayuwa ce irin ta dabbobi, sai bayan mahaifinki
ya fahimci cewa, mulkin da yake yi ba na shi ba
ne, to sannan za ki fahimci dukkan abin da na
bayyana miki. Yanzu ki san yanda za ki yi ki
fitar da ni daga cikin birnin nan domin cimma
burina."
jiki.
Gimbiya Anisa ta kalle shi cike da mutuwar
"Kin yarda da duk abin da na fada.?" Ya
tambaye ta
"Na amince, amma ta yaya zan iya fitar da
kai daga cikin birnin nan, bayan ina sane da irin
matakan tsaron da suke ciki.?"
"Kar ki damu, ina da mafita."
"Menene mafitar ka.?" Ta tambaye shi
"Matso ki ji in sanar da kc."
27
Ta matso kusa da shi kamar yadda ya
umarce ta, ya fada mata abin da yake ganin shi
ne mafita, ta kalle shi tare da yin wani
murmushin karfin hali, shima ya yi mata
murmushin. Sannan ta bukaci ya sanar da ita
abin da ya haddasa masa zama tsuntsu. Nan take
ya nuna mata bai san komai ba, sai dai ko
mahaifiyarsa.
"To ya kai ka ce min labari ne mai tsawo.?"
Ta tambaye shi
"Don kawai na kawar da maganar, domin
za ta iya hana mu yi wadda ta fita
muhimmanci." Ya sanar da ita.
"Na gamsu." Ta amsa
Mutum dubu biyar da dari hudu da tamanin
ne, suka yo gudun hijira daga birnin Daulatu
Sakaf, da niyyar zuwa birnin Hubar kasar Sarki
Ushaibat tare da karfafa zuciyoyinsu yin imani
da Allah da Manzonsa (S.A.W) wato idan sun
wanzu a Kasar Hubar za su karbi addinin
musulunci, don haka a yanzu da suke tafe wasu
a kasa, wasu a rakumma, wasu a dawakai, wasu
kuma ana fauke dasu bisa dawakai da rakuma,
tsofaffi da marasa lafiya kenan da ba za su iya
tafiya ba. Suna cikin tafiya a cikin sahara, sai ga
rundunar mayaka daga bayansu, Sarki Haiman
ne ya turo a kashe su baki daya. Nan da nan
kura ta turnuke ta yi sama, da suka ga haka sai
suka kasu kashi uku, kashi daya suka tsare
dukiyoyinsu, kashi na biyu suka tsare marasa
lafiya, yayin da kashi na uku suka tsaya domin
su ja daga da rundunar sarki Haiman, domin su
dama sun ringa sun yi niyyar bada gaskiya
izuwa addinin Musulunci, don haka yanzu zasu
tunkari shahada.
Yayin da rundunar mayakan sarki Haiman
suka tunkaro ma'abota' yin hijira, sai wasu daga
cikinsu suka kara saboda ganin yawan rundunar,
domin kuwa duk yawan su rundunar ta linka su,
kuma babu tsofaffi a cikinsu. A yayin da
jagoransu, wanda shi ne ja gaba wajen yin
wannan hijira ya fuskanci halin da wasu suka
shiga na karayar zuciya, sai ya fara kokarin
karfafa masu gwiwa. Nan da nan suka dan samu
natsuwa, to a wannan lokaci ne fa Sayyar ya
bayyana akan,wani Ingarman doki tare da
Gimbiya Anisa, itama tana bayansa, ta yi shiga
irin ta maza sadaukai, babu wanda zai gane ta
29
daga cikin mutanen Sarki Haiman, itama tana
haye kan dokinta. Suna zuwa suka ja linzaman
dawakan nasu suka tsaya, nan take Sayyar ya yi
kabbar domin su fahimci cewa Musulıni ne,
suna jin ya yi kabbar sai suka amsa masa tare da
bin shi da kallo, nan take ya fara magana da
cewa.
"Ya ku ma'abota Imani da Allah Ubangijin
talikai, ku wanzu cikin natsuwa da karfin gwiwa
nasara tana gare ku ma'abota hijira, kada yawan
rundunar makafirta ta tsorata ku, lallai ku sani
cewa yawan nan nasu na kwarjini ne, idan dai
hijirar ku domin Allah da Annabinsa ce, to ku
shirya tarar rundunar ma'abota wanzuwa a gare
ku domin yin shahada."
Duk kowa ya bi shi da kallo cikin rashin
sanin ko wanene shi da yake magana, Anisa се
dai kawai tasan ko shi wanene, amma baya ga
ita ba su san ko wanene ba su.
"Ya ku ma'abota Imani, shin zaku zamo
masu mika wuya ne ga wadanda suke
kaskantattu a wajen ku? To ku yi sani cewa,
Allahn da ku kayo hijira dominsa yana tare da
ku, sai dai idan ba dominsa ku ka yi wannan
30
hijira ba. Da sannu za ku zamo masu rinjaye
akan kafurai."
Nan da nan suka yi sahu-sahu, suka yi
shirin yaki, wasu suka tsugguna a gaba suka
haka kibiyoyinsu, wasu suka tsaya daga baya
rike da masu, wasu suka tsaya a bayan masu
rike da mashin, su kuma suna haye bisa dawakai
rike da takubba. Jagoran rundunar gudun hijirar,
wanda yake dama can Sadauki ne, ya ci gaba da
basu umarnin yadda za su fara afka masu da
kamai, yayin da shi kuma Sayyar tare da
imbiya Anisa suna tare da wasu majiya karfin
adaukai daga cikin mahaya dawakai.
Suna cikin wannan shiri, sai ga rundunar
Sarki Haiman sun iso dab da su, nan take suka
fan yi masu ruwan kibbau, sai dai kaga barade
suna kara suna fadowa daga kan dawakansu, su
kuwa 'yan gudun hijirar sai sakar musu ruwan
kibbau suke yi: Da yake akwai sauran 'yar tazara
tsakaninsu, kafin su cimma su, sun yi masu
6ama da yawa. Ma su harba kibiya suka koma
baya yayin da suka iso gare su, ma su mashi
suka shige su, nan fa wuri ya hargitse, duk in da
ka duba jini ne ke fallatsa kamar feshin ruwa a
lokacin da ake tafka ruwan sama. Kura ta tashi
sama ta fara rufc mayaka, suma su Sayyar suka
shigo aka dinga fafatawa da mazaje, duk in da
Sayyar da Anisa suka dosa, sai dai ka gi
kawunan barade na fadowa kasa, sannan ganga
jiki ta biyo baya.
Yaki ya kai yaki, mazajeisun sha kashi, sur
wanzu cikin gumurzu da dauki-ba-da-dı, yayiı
da dawakai ke tsalle suna faduwa sun
karairayewa, haka nan kukan su ya cika wajen
Karar takubba da sukekeniya da bugayya sur
cika wurin, kura ta turku ta yi sama.
Wani barde da ya lura da Anisa, yadda tak
kashe mutane, sai ya sako dokinsa a sukwane y
tazo da takobinsa tsirara da nufin tsinke mat
kai, Sayyar ya hango shi yayin da suke cikir
fafatawa da wani katon barde, da Sayyar ya y
kokarin rabuwa da shi don kawu mata dauki, sa
kuwa wancan barden ya buge masa takobi ya у
sama, ganin haka sai Sayyar ya yi tsalle ya dir
kasa ya na mai bi takobinsa da kallo yayin da t
yo kasa, tana zuwa ya cafkeeda hannunsa n
dama, sannan ya sake yin tsalleoya haye ka
dokinsa ya zabure shi shima.
Gimbiya Anisa tana ta faman artabu d
wani barde, yayin da wancan barden yn kusant
ta da takobinsa zai sauke kanta, sai takobin
Sayyar ta sauka a gadon bayansa, ta hudo ta
tumbinsa, nan take ya fado tim a kasa kusa da
kafar dokin Anisa, hakan ya yi daidai da lokacin
da barden da suke fafatawa ya yanke ta da
takobinsa a cinyar hannu, zafin yankan ya
shigeta, ta saki nata takobin ya fadi kasa, ya
daga zai kara mata, Sayar ya yi tsalle ya hau
bayan dokin barden ya rike hannayensa tare da
karya su a lokaci daya, barden ya yi wata kara
sannan ya fado kasa, Sayyar ya diro kansa tare
da cake shi da takobi. Nan take ya sungumi
Anisa ya fitar da ita daga cikin sansanin yakin,
ya nufi da ita can in da wasu daga cikin
mutanensu suka boya, ya mika musu ita sannan
ya dawo suka ci gaba da fafatawa.
Can! Sayyar ya dubi wani sadauki ya sauke
masa kai, koda mayakan suka lura da abin da ke
faruwa, sai suka tsorata, ashe shugaban
jagoransu ne aka kashe, kuma babban sadauki a
cikinsu. Nan fa wuri ya fara lafawa, yayin da
wani daga cikin su ya fara kururuwa yana shaida
wa mutane,"An kashe shugaban sadaukan birnin
Daulatul Sakaf," Nan da nan sai kuwa wadanda
suka yi saura suka juya a guje, suka nufi hanyar
33
komawa birnin Daulatul Sakaf. Tuni wasu daga
cikin 'yan gudun hijirar suka rufa masu baya.
** ** **
Sarki Haiman ya yi zarya, ya kara yin
zarya, sai kaiwa da komowa yake yi kamar
mazari, hankalinsa a tashe, ransa a басе.
Abubuwa da dama sun dame shi, na farko babu
'yarsa Gimbiya Anisa, ba aganta ba, sannan an
zo mashi da labarin abin da ya wakana yayin da
ya tura rundunar mayaka don kashe 'yan gudun
hijira. A wannan lokaci ne Sarki Haiman ya tura
ayo masa kiran Bokanya Amshadatu, kafin dan
aiken ya dawo, tun labari ya zo kunnen sarki
Haiman cewa ga rundunar mayaka nan zuwa
birninsa. Nan da nan ya ba da umarni a yi maza
a shirya rundunoni domin rusa duk wasu dakaru
da yawan su ba yawa ne na misali ba, da za su
zo domin jan daga da tasa rundunar. Kafin wani
lokaci rundononin yaki sun haku, birnin
Daulatul Sakaf ya cika makil da mayaka, ta
ko'ina idan ka duba su ne babu masaka tsinke,
nan da nan suka azalzala da jiran isowar
rundunar.
34
Ba a dauki lokaci ba sai ga rundunar su
Sayyar