Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
ya iso wajen a sukwane bisa doki, da zuwa ya fadi gaba Sarki Haidar ya yi 34 gaisuwa, yayin da duk wanda ke wurin ya bishi da idanu, yayin da ya ke sanar wa da Sarki Haidar ccwa, ga rundunar mayaka nan tafe zuwa wannan birni. Ko da rufc bakinsa kuwa, sai suka hango kura daga bayan birnin ta yi sama, suka dinga jiyo ihu da kururuwar mutane. Nan da nan Sarki Haidar ya yi umarni ga mutanensa da su tashi su yi shiri, da duk wacce suka zo za su tare su da ita. Kafin wani lokaci sai ga rundunar mayakan birnin Humar sun wanzu ciki da wajen birnin cikin shirin yaki. A wannan lokaci shi ma kansa Sarki Haidar din da ba shi da isasshiyar lafiya, amma kasancewar jarumi sai ga shi akan dokinsa cikin shirin yaki irin na mazan jiya. A nan fa aka fito sauraron isowar rundunar mayakan nan dake tafe. Can sai ga wani barde a sukwane bisa doki ya doso sansanin mayakan birnin Humar, da zuwa ya ja turjiya ya tsaya, yayin da yake bin mutanen birnin Humar da kallo. Can kuma sai ya fara magana yana mai cewa. "Gare ku masallatan birnin Humar, ku fito mazan ku da matanku ku mika wuya ga rundunar Sarki Haiman kafin mu shayar da ku gidauniyar mutuwa, kada kuyi girman kai ko yunkurin jan daga da rundunar Sarki Haiman, lallai idan ku ka yi haka, to za ku dandani ukuba mai tsanani....." Kafin ya 35 a gama rufe baki, sai jin saukar kibiya ya yi goshinsa, tsinken kibiyar ya 6ula kokon kansa ya fito ta bayan keyarsa, nan take ya fado daga kan dokin yana mataccc. A daidai lokacin ne kuma tawagar rundunar makafirta bisa jagoranci Shugaban runduna, sarkin yakin mayakan Sarki Haiman. Aka ja tunda aka tsaya, kowanne shashe yana nazarin dan'uwansa, shashen Musulmi suna kallo tare da nazarin sashen kafurai, yayin da suma sashen Kafurai suke kallo tare da nazarin sashen Musulmin. Rana ta tafi faduwa, yayin da aka gabza yaki mai tsanani, rayuka suka mutu da dama, ciwuka suka wanzu da dama a jikin mutane, yayin da aka ribace wasu da dama daga cikin mayakan sarki Haiman, wanda a ciki har da shugaban rundunar madugu uban tafiya, Sadauki Jaudaru, kafiri uban makafurta (kirarinsa kenan). Yayin da wasu da dama daga cikin mayakan Sarki Haiman suka juya domin kufutar da rayukansu, suka koma izuwa birnin Baidar domin sanar da Sarki Haiman abin da ke wakana. BABI NA HUDU ayin da iskar nan da ta dauke Sayyar ta bace, ao i hadimin Aljani ne wanda ya wanzue da sihirin Boka Ashfar wanda tun wani lokaci ya wanzu yana kulla kullallan sihirinsa a bisa umarnin makafircin Sarki, Sarki Ukashatu, domin ganin ya wanzar da Sayyar din cikin tashin hankali da kuma kuncin rayuwa, wanda a karshe zai hallaka. Bakin Aljanin nan ya ci gaba da keta hazo da gajimare da Sayyar bin Haidar, yayin da shi kuma а wannan lokaci tuni ya dade da suma a hannun bakin Aljanin. A can kuma cikin turakar tsafin Boka Ashfar, ya na kallon duk abin da ke wanzuwa game da hadimin Aljaninsa ta cikin wata bakar tukunyar tsafinsa wadda aka cika da wani jan ruwa. Yayin da hadimin Aljanin nan ya yi nisa, sai Boka Ashfar ya yi magana cikin wata irin murya mai ban tsoro. "Ya kai Hadimil Ashfar, maza ka ajiye Sayyar bisa tsuburin Jazfar dake kudancin birnin Yaman." Tamkar a gabansa yake, sai kuwa Aljanin nan ya sauka kan wani katon tsuburi dake cikin wani uban daji mai bishiyoyi, ya sauke Sayyar. Ravan va sauke shi, sai Boka Ashfar ya umarce shi da ya tashi ya bar wajen, tashin Aljanin ke da wuya, sai Boka Ashfar ya dauko wata bakar buta ta karfe, ya girgiza ta, sannan ya kira sunan Sayyar sau uku, ya rufe idanu yana wasu sabbatu tare da juya hannuwa yana fifita su kamar yadda tsuntsu yake yi idan ya tashi sama. Bai gushe daga wannan siddabaru nasa 37 ba, sai ga kamannin Sayyar suka juyc suka kuma wani kyakkyawan tsuntsu mai kyawun sura, zuwa can kuma sai tsuntsun ya tashi ya lulluka a sararin samaniya. Boka Ashfar ya kyalkyale da dariya, sannan ya tashi yana mai kokarin fitowa daga dakin tsafinsa. Wata 'yar Sarki tana zaunc a bakin gabar wani ruwa mai gudana cikin wata katuwar gona, tare da Kuyanginta suna shakatawa. Yayin da iska mai dadi ke busawa a cikin safiyar wannan lokaci tare da wani irin yanayi mai sa nishadi da walwala a zukatan al'umma. Jefi-jefi ta kan sa hannu ta na dibar ruwan tana wasa dashi, kallo daya idan ka yi mata zaka fuskanci tana cikin nishadi mai yawa. Kyakkyawa ce a cikin kyawawan mata, Allah ya yi mata kyakkyawar sura ma'abociyar daukar hankali, tana da wushirya a bakinta, wadda idan ta yi murmushi sai ya rudar da wanda ya kamu da begenta. Su kansu kuyanginta dake tare da ita, tana birge su, duk wani motsinta suna kula tare da kiyayewa da ita. Gimbiya Anisa kenan, 'yar Sarki Haiman tare da kuyanginta suke taya ta shakatawa kamar yadda ta saba kullum a cikin babbar gonar da Sarki' Haiman mahaifinta ya sa aka gina mata domin ta dinga shiga tana debe kewa a duk lokacin da ta bukata. Suna nan zaune tare da kuyanginta, suna hirarrakinsu kamar yadda suka saba a duk lokacin da suka wanzu tare da ita a cikin wannan waje, yayin da walwala da annushuwa ke lullube da fuskokinsu a 38 wannan lokaci, musamman ita Gimbiyar Anisa. Can sai kuyangin nata suka lura da ita, hankalinta ba akansu yake ba, balle kuma hirar da suke yi. Don haka baki daya suka juya tare da kai kallonsu in da take kallon. Wani tsuntsu suka gani yana tahowa daga bayansu. Babu wanda ya fauke idonsa daga kan dan tsuntsun har zuwa lokacin da ya sauka kusa da su bisa ciyayin dake bakin ruwan. Gimbiya Anisa ta yi murmushi tare da kura wa tsuntsun idanu, taga tunda take a rayuwarta bata taba ganin kyakkyawan tsuntsu irin wannan ba, haka nan kuma sai ta ji so da kaunar tsuntsun ya shiga ranta, don haka sai ta tashi da kanta ta nufi inda tsuntsun yake da nufin kama shi. Cikin nutsuwa ta sa hannu ta dauke shi tana murmushi, sannan ta dawo inda kuyanginta suke zaune tana cewa. "Na samu abin begena, wanda zai fi komai debe min kewa a rayuwata." Kuyangin nata suka bita da kallo tare da girgiza kai. Gimbiya Anisa ta kura wa tsuntsun idanu tarc da rungume shi a jikinta, sannan ta yi magana tamkar tana yi da mutum. "Ka kwanta bisa jikina sosai, ka zo wajen wadda zata kaunace ka, zata nuna maka kulawa, kuma za ka sa ta farin ciki a zuciyarta dare da rana, daga yau ka zama abin begena, kuma sirrin zuciyata." Kuyangin nata dai bin ta suke da kallo, amına izuwa yanzu abin ya fara daure masu kai, musamman 39 idan suka yi la'akari da irin lafazin da yake fitowa daga bakinta. "Mu gani ranki shi dade." Daya daga cikin kuyangin nata ta bukata tare da mika hannu da nufin ta bata tsuntsun ta gani. Gimbiya Anisa ta girgiza kai. "A'a ki yi hakuri, ba zan ba kowa abin begena ba, domin daga nan sai cikin kejina, wanda zai zama gidansa, amma ba zai je hannun kowa ba.." Yanzu aka fara labarin. Mai karatu ka dakace ni a cikin littafin KAMBUN KARFE Na biyu. Dan'uwanku A Musulunci; NAFI'U SALISU MUSA 08081643197 Kafan daga cikin littafin: RIGAR SAKI "Za ki iya yi min alkawarin ba za ki taba sauraron kowa da nufin soyayya ba, ba za ki mallakawa kowa kanki da soyayyarki ba fa ce ni.?" Cikin muryarta mai ratsa dodon kunne da sanya nutsuwa ga wanda yake saurare, ta amsa mishi da cewa. "Na amince Salim, ba zan kula kowa ba sai kai, ba zan saurari wani da namiji da nufin soyayya ba, sai kai. Kai kadai ne wanda na mallaka wa soyayyata, kai kadai ne a zuciyata, da koda yaushe tunaninka ba ya gushewa daga cikinta....." Sun kulla alkawarin ne a tsakaninsu, cewar kowa ba zai saurari soyayyar waninsu ba, sai dai junansu kawai, duk da cewa ba su taba ganin juna a zahiri ba. NAFIU SALISU 40 08081643197 GARBA MUHAMMAD BOOKSHOP KasnwaoSabon Gai, Kana 08036555794-08069382816 e GBS S BOOKSHOP Tsarin Bango: SALISU JAWOTA GRAPHICS 07090490491 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2