Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KAMBUN KARFE NAFI'U SALISU IBN SALIS NAHIYAR SAIFANA ska ma'abociyar sanyi mai dan ratsawa cikin Ijiki na kadawa a hankali, gabas, yamma, kudu, arewa, rassan dogayen bishiyoyi na rangaji gwanin ban sha'awa, kunnuwan su na fado zuwa bisa shimfidaddiyar kasar da Ubangijin sammai da kassai ya shimfida a doron duniya, yayin da kukan tsuntsaye da na wasu daga cikin namun daji ke wanzuwa a daidai lokacin. Nahiyar na da fadin gaske, dauke take da duwarwatsu da tsaunika ma'abota girma, akwai bishiyoyi masu tsawo da kauri, sannan akwai koramu ma'abota gudanar da ruwa a cikinsu, wanda hakan na daya daga cikin abin da ya sa wannan nahiya ke da sanyi wuri. Kwal!Kwal!!Kwal!!! Sautin bugun karfe ke bayyana daga gindin wani dogon tsauni dake cikin wannan nahiya, ga duk wanda ya saurara da kyau ya ji karar dukan dake bayyana, zai fahimci ana dukan karfe da karfe nc daga can in da sautin karar ke fitowa. Daga kudu da wannan dogon tsauni in da karar dukan karfe ke fitowa, sai ga wani mahayin Doki ya fito haye kan wani bakin Dokinsa ma'abocin karfin kafadu. Wanda ke kan dokin, saurayi ne mai cikar zatin halitta, ma'abocin kwarji. Iskar dake kadawa tana shawagi a'sararin duniya a wannan lokaci, ta na 5 kada gashin kanshi ma'abocin yalwataccen baki mai ban sha'awa. Ya na sanyc da wata rigar gashi, akwai wani dogon takobi a jikinsa, sannan ga wata garkuwa a bayansa ya goya ta, a kafadar haggunsa kuma kwari da baka ne a rataye, kai kace wani mafara uci ne yayin da ya fito farauta cikin dokar daji. Idan ka yi masa kallon natsuwa, za ka fahimci akwai jarumtaka a tare da shi, haka nan idan ka kalli kirar jikinsa, za ka fahimci jan gwarzon saurayi ne. Dokinsa kuwa Ingarma ne. A hankali ya doso in da karar dukan wannan karfe ke bayyana. Yayin da ya kusanto wannan tsauni, sai ya hango Dattijon shi da matarsa, da ya sake matsiwa sosai sai ya ga matar na juya irin karfen nan na zuga wutar makera, can gefe guda kuma tartsatsin wuta ne ke tashi, shi kuma wannan Dattijon yana dukan wani karfe dake kan wani katon karfe da wata katuwar gudumar karfe dake hannun damarsa. Da matashin saurayin nan ya sakc yin duba can gefe guda, sai ya hango wani karamin yaro zaune ya na wasa, Shekarun yaron ba su wuce uku zuwa hudu ba. A wuyan yaron akwai wata azurfa da aka daura masa mai haske da daukar idanu. Dattijon nan ya waiwaya wajen matarsa mai yi masa zugar wutar makerar lokacin da ya ji ta daina juya abin zugar wutar. Ga mamakinsa sai ya ga tana kallon wani waje daban, cikin mamaki da yanayin da ya ganta, ya tambayc ta. "Aisamatu me ki ke kallo ne haka.?" Maimakon ta amsa masa tambayar da ya yi ma ta, sai ta nuna mashi in da take kallo da bakinta. Dattijon ya waiga a hankali domin ganewa idanunshi abin da ya dauke wa Aisamatu hankali daga barin zugar wutar makerar. A nan ya yi ido hudu da matashin saurayin dake kan doki, har ya iso inda suke tsattsaye ba dauke idanunsa daga gare shi ba. Dattijon nan bai yi magana ba, har sai bayan da matashin ya sauka daga kan dokin nasa, yayin da ya nufo wurinsa cikin natsuwa tare da sakin fuska cikin fara'a. "Barka da zuwa ya kai wannan ma'abocin kyawun halitta." In ji wannan Dattijon Kafin Dattijon ya gama rufe bakinsa, matashin saurayin ya iso gare su yana murmushi tare da amsa sannu da zuwan da Dattijon ya yi masa. Dattijon ya aje kayan kirar dake hannunsa, sannan ya yi wa matashin nan jagora zuwa cikin tsaunin nan in da a nan gidansa yake. Bayan sun kadaice a cikin wani kogo wanda fadinsa ya kai girman dakin kwanciya. Saurayin nan ya gabatar da kansa ga Dattijon nan, bayan ya bukaci hakan. 7 "Sunana Amar bin Zubaid, na samu labarinka a wajen Kakana Sarkin bokayc, yayin da na ziyarce shi da wata bukata tawa. Wannan bukata tawa kuwa ita ce, ya kai wannan Dattijo ma'abocin sanin sirrin kira, ban wanzu gare ka ba face dan wata babbar bukatata, kuma karama a wajenka. Na kasance daya daga cikin mutanen da suke son mallakar Gimbiya Anisa 'yar Sarki Haiman wadda mahaifinta ya yi alkawarin zai aurar da ita ga duk wanda ya sanar da shi yanda za ayi amfani da sihirtaccen kambun nan na bakin karfe wanda ya sa aka dauko masa a karkashin dutse, dake ajiye a gidan sarautar kasar Sarki Haiman din, DaulatulSakaf, don haka ina so a bisa basira da kware irin wadda Allah ya yi maka, ka kera min irin wannan kambu ya kasance kamarsa da wancan komai iri guda, don haka da na je wurin Kakana ya buga min alkalumma, ya sanar da ni cewa kai kadai ne wanda zaka iya kera min irin wannan kambu a duk makeran duniya ba ki daya, idan ka yi haka, zan mallaka maka dukiya mai tarin yawa, wadda kai kanka sai ka yi mamaki da ita." Lokacin da Amar bin Zubaid ya kai aya a zancen nasa, sai Dattijon nan mai suna Abusamar ya dube shi sosai yana mai cewa. "Lallai Amar ka zo gare ni da al'amari mai girma, a rayuwata kai ne mutum na farko da ka taba zuwa garc ni da abin da na ji shi kamar a mafarki. Anya kuwa kai kana da labarin Kambun nan na gidan. sarauta? Idan kuwa haka ne, to lallai rayuwarka na fuskantar wahala da kunci idan ka ce zaka nemi sanin yadda ake amfani da wannan kambu, domin karshe ma dai zaka iya rasa rayuwarka gaba daya, idan har ka ce sai ka binciko domin ba kai ba ma dan Adam, ko matashin Aljanin Kakana Huzaid ya gagare shi." Shi ma Dattijon Abu-samar da yazo nan a zancensa, sai ya saurara ya na kallon kofar kogon da suke ciki. Matarsa Aisamatu ta shigo dauke da wani gora na jar fata, ta aje kusa da Amar da ya zo wajen maigidanta. Amar ya juyo suka fuskanci juna shi da Aisamatu, ya yi gaisuwa cikin girmamawa a gare ta, ya na mai farin cikin kawo masa wannan ruwa da ta yi. Ba tare da ta tsaya wajensu ba, ta fito daga kogon wanda za'a iya cewa daki ne guda. Abu-Samar ya shafi gemansa da hannunsa na haggu, sannan ya kalli Amar ya na mai sauraran abin da zai sake fitowa daga bakinsa. Amar ya ce "Ya kai Abu-Samar, ka yi sani cewa, mu mun kasance ma'abota tarin dukiya, kuma jinin sarauta, don haka idan har zaka iya kera min irin wannan kambu, to lallai zan mallaka maka dukiya mai tari yawa, bayan haka za ka iya fadin duk abin da ka ke so, na rantse da rana ma'abociyar haske, sai na mallaka maka shi, in dai har bai f Karfina ba." A lokacin da Dattijo Abu-Samar ya ji wannan batu, sai ya yi murmushi ya sake shafar gemunsa, sannan уа сс. "Na ji abin da ka fada ya Amar, amma idan har haka ne, to ina bukatar yin nazari akan wannan al'amari, don zai iya kasancewa nima wani tashin hankali ya shafe ni a sakamakon haka, saboda haka ka tafi izuwa saurare na har tsawon kwana bakwai, sannan ka dawo." Amar ya ji dadi tare da farin ciki sannan ya kawo zinare saba'in masu nauyi ya ba shi, kafin daga nan ya yi masa sallama tare da godiya a gare shi ya tafi. Dattijo Abu-Samar, ya kasance mutum ne mai shekaru da dama a duniya, kuma ya kasance mutum mai sha'awar zaman ciki dokar daji shi kadai, don haka ne ma ya kasance cikin daji tare da iyalinsa. Sana'arsa ta kira kuwa, ya gajcti ne a wajen Kakansa da har yanzu yana raye, sai dai kuma tsufansa ya yi nisa sosai. Abu-Samar ya kware to fuskar iya kira, domin a wannan lokacin masana bincike sun gudanar da bincike akansa, sum kuma gune babu wani mutum da ya ke yin kira wanda ya 10 kai shi kwarewa, domin lokuta da dama ya kan kera wasu abubuwan ban mamaki, haka nan idan ka zo ka ce ya kera maka takobi irin na Sarki wane, ko sarauniya wance, kambun sarauta ko zoben sarauta da dai sauransu, to zai yi maka irin sa. Yana da wani kundi wanda a cikinsa ya ke dauke da rubutattun sunayen abubuwa da suka shafi kayan sarauta na sarakuna, haka nan kuma duk wani takobi, zobe, kambu, da wani mai mulki ya mallaka na sihiri ko kuma mai kudi na ban mamaki, to akwai sunayensu da tarihinsu a rubuce cikin wannan kudi. Abu-Samar da matarsa Aisamatu, basu taba haihuwa ba tunda suke a rayuwarsu, don haka sai suka dauko dan kaninsa domin su rene shi, wanda a yanzu yake wajensu. BAYAN SATI GUDA Da kwanaki bakwai suka cika, a cikin kwana na takwasa, sai ga Amar ya dawo izuwa ga AbuSamar kamar yadda ya yi masa umarnin cewa bayan kwanakin bakwai ya dawo domin jin in da aka kwana game da bukatarsa. A wannan lokaci sai Abu-Samar ya fara ba Amar labarin. BABI NA DAYA A wani lokaci, a wani zamani, shekaru aruaru da suka shude (wuce), a cikin Kasashen Larabawa. An yi wani sadauki ma'abocin nauyin kafadu, kuma ma'abocin karfin damtse da kwarcwa wajen iya yaki. Babban kafiri ne amma daga baya ya yi imani da Allah (daya) ta dalilin wasu isharori da suka wanzu gare shi na ban mamaki da al'ajabi, don haka sai ya shiga Musulunci tare da wasu daga cikin mutane da ya ke tare da su. Kafin wannan lokaci, wannan Sadauki mai suna Haidar sai da ya yaki rundunar sarakuna da sarakai daban-daban, a bisa jagorancin mahaifinsa wazirin Sarki Lamrud da ke mulkar birninsu, a ciki har da wani babban Sarki wanda ya so karbar addinin Musulunci, sai dai kafin wannan lokaci Haidar ya shirya rundunar makafirta suka yaki wancan sarkin shi da jama'arsa. An yi kiyasin cewa, a wancan lokacin duk wani Sadauki ba ya nuna shi sadauki ne, matukar Haidar ya na nan, yanzu ya karar masa da numfashi. Takobin Haidar, shi ne takobin da, idan ya kai sara ko da bai samu wanda zai sara da takobin ba, to iskan takobin kadai sai ya ji wa mutum rauni. Haka nan idan kuma ya samu mutum to lallai sai dai gawarsa. Aljannu kuwa konewa suke idan takobin 12 ya taba jikinsu. Hatta karfe idan ya sare shi da shi, to sai ya lalace. Bayan Haidar ya karbi Addinin Musulunci, sai nan da nan labari ya iskc Sarakuna daban-daban, wanda mafiya yawa daga cikinsu kafirai ne, don haka sai bakin ciki ya kama su, takaici ya shiga addabarsu, su kuwa Sarakunan masallata, sai farin ciki ya wanzu a zukatansu, murna da farin cikin wannan al'amari ya sa su cikin walwala da nishadi, fargaba da yawan damuwar zaluncin da Haidar yake a da, ya gushe daga zukantansu. Har ma sai da aka samu wani Sarki daga cikin Sarakunan Musulmi ya ba shi aurcn diyarsa kyauta. A wannan lokaci nc, Sarakunan kafirai suka dinga aikawa da sauran makwabtansu labarin Musuluntar Sadauki Haidar, wannan kuma shi ne abin da ya zama fargaba a zukatan Sarakunan kafirai, mazansu da matansu. Don haka tun ba aje ko'ina ba, sai suka fara shawarwarin yadda zasu Gullo wa lamarin, in da a karshe suka yanke shawarar shirye-shiryen makircc-makircen yadda za su hallakar da Sadauki Haidar. ** Sarki Ukashatu, wani makafirci, kuma daya daga cikin manyan sarakuna a wancan lokacin, yana daya daga cikin sarakunan kafiran da suka sha 13 alwashin ganin bayan Sadauki Haidar, don haka sai ya jefa gaba da kiyayya mai tsanani tsakaninsa da mutanensa maza da mata, kowa a garin ya zama mai kyama da kin Sadauki Haidar, sabanin baya kafin musuluntarsa da duk wani kafiri yana sonshi, musamman ma ta fuskar kisan gillar da yakc yi wa Musulmi, duk da cewa akwai wasu da yawa da bautar su ba daya ba ce da ta Haidar. Akwai masu bautar wuta, kogo, gumaka, rana, taurari da wata, darc, dutsc, dabba, da sauransu. Wata rana Sarki Ukashatu, ya bukaci ganin bokansa wanda yake sanar da shi al'amuran yau da kullum ta fuskar sihiri, ya wanzu tare da shi, sai ya ce da shi. "Ya kai wannan Boka ma'abocin sanin kafar sihiri, ina so ka wanzu cikin ilimin bokancinka, ka kuma tabbatar ka samar da wani sharri wanda zai zamo sanadiyar mutuwar Amirul Jihad (kamar yadda wasu da yawa suke kiransa) Haidar kenan, "Ya kasancc ba zai yi wani yawancin kwana ba, sannan kada ka bari jininsa (da ko dan uwa) daga ahlinsa ya wanzu cikin rayuwa mai dadi a doron kasa, facc ka wanzar da shi cikin kunci da wahala. Wannan shi ne babbar bukatata." Da kammala wannan magana, sai bokan nan ya yi murmushi, sannan ya tabbatar masa da cewa, wannan an yi an gama. 14 Tun daga lokacin da Sarki Ukashatu suka rabu da Boka Ashfar, bayan da ya koma gida, a cikin wannan yini ya fara kullc-kullin abubuwan sharri da makirci ta hanyar siddabaru da sihiri wanda zai cutar da Sadauki Haidar, bisa cika umarnin Sarki Ukashatu. BAYAN WASU SHEKARU Sai ga takarda daga wani babban sarki, shi kuma wannan Sarki ya kasance mai bautar gumaka shi da jama'arsa. Yayin da wannan takarda ta iso ga Haidar, sai ya ga tana dauke da neman gayyatarsa zuwa walima a kasar wannan Sarki, wanda ake kira da suna Sarki Ushaibat. Haidar ya yi farin ciki da ganin wannan takarda, sannan ya amsa a rubuce cewa, zai ziyarci kasar Sarki Ushaibat (wato kasar da yake mulki Hubar). Yayin da wannan takarda da Haidar ya sa aka rubuta ta amsa gayyatar da aka yi masa ta riski Sarki Ushaibat, sai murna da farin ciki suka wanzu cikin zuciyarsa, ya kuma aikawa sauran sarakunan makafirta cewa, ga abin da ya shirya na son hallaka Sadauki Haidar, kuma shigaban sadaukai. Ya shirya tuggu da makirci domin hallakar da Sadauki Haidar, wanda wannan ya faru ne saboda ganin jarum taka irin tasa idan ya shirya jakar wanda ya yi niyya to fa 15 lallai sai ya cimma burinsa, to suna tsoron ya zama sarki. Bayan haka, al'umma da dama sun shiga addinin Musulunci ta dalilin şhiriyar Haidar izuwa bautar Allah Ta'ala, don haka yana da jama'a sosaí, kuma ya bi gari-gari yana wa'azantar da mutane daga barin bautar wanin Allah (Shirka), da su dawo izuwa babban rabo, (Addinin Islam). Sannan da yawa daga cikin mutanensa su ma, sun kasance sadaukai masu nauyin kafadu, idan suka sara ko suka ko harbin kibiya da sauransu to lallai sai mutum ya dandani ukuba, imma ba sauran shan ruwan mutum a gaba, sai ya mutu. ** Al'amari ya gabato, dangane da amsar gayyatar da Sadauki Haidar zai yi a birnin Hubar (wato birnin Sarki Ushaibat), don haka sai Haidar ya fara zikiri ga Ubangiji (Madaukakin Sarki) akan neman nasarar wannan tafiya cikin sa'a da neman a kammalá komai lafiya ya dawo tare da Jama'arsa lafiya. Haka ya wanzu yana addu'o'i a turakarsa, bai gushe ba har sai da ya kwana goma sha biyar, a rana ta goma sha shida ne, bayan ya wanzu yana zikirin Allah, kamar yadda ya saba, sai wani nannauyan bacci da bai taba jin irinshi ba ya wanzu garc shi. 16 rijiyoyin nan, sannan wasu mayaka daga cikin sadaukai su ja tunda a kowacce kuskurwa, .da zarar Haidar ya afka cikin rijiya, sai su bi sauran mutanen da yake tare da su da sara, yayin da za su yi kokarin komawa baya idan sun fahimci haka Nan da nan Baraden Sarki Ushaibat suka bazama ko'ina a cikin birnin Hubar, wasu, akan Dawakai, wasu kuma a kafa, wasu dauke da garkuwa da makamai majiya karfi akan dawakai suka samu wurin labewa, kai ka ce dama can an aiko masu ne da shirin gwabza yaki Shiru, babu motsin wani abu mai giftawa, a cikin birnin sai dai iska kawai ma'abociyar wanzuwa a sararin duniya. Birnin Hubar ya yi shiru tamkar babu wani bil-Adama a cikinsa! Da adadin sa'a guda ta cika, sai ga kura ta turnuke ta yi sama daga can wajen gari, wannan alama ce ta cewa Haidar da mutanensa sun iso birnin Hubar. Nan da nan labari ya isa kunncn Sarki Ushaiba, ya yi dariyar mugunta sannanya tashi yayo hawa da wasu daga cikin mutancnsa domin ya zo ya ganewa idanunshi abin da zai wakana. A gefen damansa, wazirinsa ne sai kuma haggunshis Bokayc hudun da suka yi wa rijiyoyin shiri ne cikin wata shiga, kai ka cc Iblisai ne, don Isananin muni, sai kuma babban sadaukin Sarki Ushaibat da wasu masu bin bayansa a tsaye su ma daga dama kusa da 25 daya. Nan take Haidar ya yi kabbarar shi ma kafin ya rufe baki sai ya nuna saitin wadannan rijiyoyi da takobinsa, nan take sai wani haske gami da iska mai karfi suka bayyana a wurin, nan da nan sia ga kasa tana tsagewa mutanen Sarki Ushaibat suna afkawa ciki. Ganin wannan abu sai hankalin Sarki da duk wanda ke wajen ya tashi, nan take ya juya shi da wasu da dama daga cikin mutanensa da nufin komawa cikin birnin. Kafin su ankara tuni rijiyoyin nan masu bakunan sihiri sun cika da mutanen Sarki Ushaibat, ihunsu da karaji kawia ake ji. Zuwa can kuma sai wurin ya zama ya shafc, nan da nan Haidar ya kalli jama'arsa tare da basu umarnin su biyo bayansa. Yayin da suka shiga tsakiyar birnin Hubar, sai Haidar ya sakc rikontakobinsa ma'abociyar kaifi da kyalkyali kamar madubia cikin rana, ya daga murya yayin da sautin maganar ke fita da karfi har ya na amsa kuwwa cikin birnin Hubar, ya na mai cewa. "Kaiconku makafirta, kaiconku, ashc ba ku zamo masu cika alkawari ba sai ku kasance masharranta ga bayin Allah? Hakika da kunsan abin da ba ku sani ba, da ba ku kasance masu shirya tuggu da makirci ga bakin ku ba.Toina mai tabbatar wa a gare ku, ba za ku zamo masu rinjayc a gare mu ba, da sannu Ubangijinmu (Allah) zai kubutar damu daga bakin tarkonku na makirci. 27 Haidar ya daga kai sosai ya kalli kowa, tun daga kan Dakarun Sarki har zuwa kan Sarki Ushaibat da wazirinsa, ya girgiza kai, sannan ya fara da cewa. "Kaiconku makafirta, lallai kun yi kuskure game da abin da ku ka kasance kuna aikatawa a gare mu na yaudara, to ku yi sani cewa, Ubangijinmu (Allah Ta'ala) shi ne wanda zai karre mu da kariyarsa daga duk wani makirci naku Ba mu zo gare ku da nufin yaki ba face mun zo ne bisa amsa gayyatar ku, wanda ku ka yi haka domin cutar dani daga zaluncinku, to tunda ba yaki ya wanzar damu a birninku ba, kuma babu alkawarin yakin a tsakaninmu, to lallai mu masu kiyayewa ne a bisa zaman lumana. Amma da sannu zan wanzu a wannan birni naku, ba zamu juya baya gare ku ba, face kun zama kararru a cikin wannan birni naku, idan har kuwa muka juya baya gare ku, to sai dai idan har kun kasance masu yin mubaya'a a gare mu tare da yin Imani da Allah da kuma Manzonsa (S.A.W)." Haidar na kammala wannan jawabi nasa, ya juya wajen jama'arsa ya kuma yi umarni a gare su a wannan lokaci da su juya domin komawa garinsu, kafin kiftawar idanu, sai duk kowa ya juya kan Dokinsa da nufin komawa. 30 "Haidar." Muryar Sarki Ushaibat ta yi kiran sunan Sadauki Haidar, shi kadai ya tsaya bisa dokinsa tare da juyowa, suka hada ido da Sarki Ushaibat durkushe da guiwowinsa bisa kasa ya na mai cewa. "Ka yafe ni ya kai wannan Sadauki ma'abocin kadaita Ubangijinka mai girma. Ma za ka sanar da ni kalmar Shahada, lallai na yi alkawari a gare ka zan ba da gaskiya da Ubangijinka da kuma Ma'aiki (S.A.W)." Da jin haka, sai nan da nan Haidar ya yi wa mutanensa umarni da su dakata, Haidar ya iso ga Sarki Ushaibat yana mai farin ciki, nan take ya sanar da shi kalmar shahada, ya fada tare da nanatawa har sau uku, wanda hakan yasa sauran jama'ar Sarki da dama suka mika wuya su ma. Wannan shi ne abin da ya faru na dangane da makircin Sarki Ushaibat ga Haidar. Maimakon makircinsa ya kama Sadauki Haidar sai hakan ya zama sanadin Imaninsa da Allah Makadaici tare da jama'arsa. Don haka Haidar da jama'arsa suka dawo cikin birnin Hubar aka sha shagali har na tsawon kwana bakwai, sannan daga baya Haidar da mutanenshi suka yi wa Sarki Ushaibat da jama'arsa sallama suka bar birnin. 31 BABI NA UKU H aidar ya zama Sarki a garin su, yayin da mutanensa suke girmama shi, suke ganin darajarsa da kuma kimarsa, sai dai duk da cewa yanzu ya zama sarki ya na kan gadon sarauta, babban abin da ke damunsa bai wuce na rashin sanin in da dansa yake ba. Idan dai mai karatu bai manta ba, tun lokacin da Haidar ya daura wa dansa Sayyar zoben nan a wuya, iska ta dauke shi ta tashi sama dashi, har zuwa yanzu rabonsa da shi kenan. To me ya faru da shi bayan rabuwarsu.? Duk da cewa Haidar ya na kan karagar mulki yanzu, to amma abin da yake tunani shi ne, idan ya mutu wanene zai gaje shi? Ya san dai babu wanda ya fi cancanta da ya maye gurbinsa bayan ya kwanta dama tamkar dansa na cikinsa da ya haifa, sai dai kuma ga yadda ta kasace a gare shi. Mahaifiyar Sayyar Aisamatu kuwa, wannan al'amari ya jefa ta cikin tsananin bakin ciki, musamman ganin cewa Sayyar shi kadai ne dan da Allah ya basu, ba su kuma sake haihuwar wani dan bayan shi. To amma a duk lokacin da ta yi Sallah, tana rokon Allah da ya bayyana mata yaron nata 32 kafin lokacin da zata koma zuwa ga Mahaliccinmu Allah. Haidar ya samu shekaru da dama yana mulki, yayin da mutane suke jin dadin mulkinsa, domin ya kasance mai yin adalci a tsakanin jama'arsa, tare da kiyayewa da kare hakkokinsu mazansu da matansu. Kwanci tashi, wata rana aka wayi gari Sarki Haidar ya kwanta rashin lafiya, don haka sai wazirinsa ne ke tafiyar da harkokin mulkin kasar. Ana cikin wannan ne, rannan sai Sarki Haidar ya fito zuwa tsakar birninsa, inda wani matashin dabino ya ke dashe, wanda bai fara yin 'ya'ya ba. Anan aka yi sallar Azahar a wannan rana, bayan da aka idar da sallar, sai Sarki Haidar ya tashi cikin karfin hali yana yi wa mutanensa nasihohi kamar yadda ya saba, in da daga bisa ni ya sa wazirinsa ya miko masa takobinsa. Ya karba ya cire ta daga cikin gidanta, sannan ya ambaci sunayen Allah tsarkaka, ya yi kalmar shahada sannan ya soka takobin a jikin bishiyar dabinon nan. Duk mutanensa suka bishi da kallo cikin mamaki tare da al'ajabin abin da ya yi. A lokacin da takobin ta shiga jikin dabinon, sai da rassan bishiyar suka yi girgiza, sannan abin da ya fi ba kowa da ke wajen mamaki, yadda rabin takobin ya shige jikin bishiyar dabino. 33 Sarki Haidar ya juyo ya kalle su daya bayan daya yana mai yin murmushi, sannan ya shafi gemunsa ya na mai cewa. "Ya kuma mutancna, hakika nasan zaku so jin dalilin da yasa na yi haka." Ya fan dakata Duk suka kada kai kamar kadangaru. Sarki Haidar ya ci gaba "Dalilina na yin haka kuwa shi ne, domin na bar maku wasiyya da cewa, babu wani mutum da ya isa ya cire wannan takobin daga jikin bishiyar dabinon nan, face dana Sayyar, shi kaďai nc zai cire wannan takobi daga jikin wannan bishiyar dabino, ko da bayan raina, idan aka samu wanda ya yi haka, to kuwa shi ne dan Sayyar: Amma idan ba shi ba, to babu wanda ya isa ya cire wannan takobi daga jikin wannan bishiyar dabino." Yayin da mutanensa suka ji wannan batu, duk sai suka cika da mamaki da kuma al'ajabi, don haka sai kuma suka ji dadi domin sun samu hanyar da za su gane Sayyar dan sarkinsu a duk lokacin da hakan ta faru. Sarki Haidar ya sake cewa. "Sannan wasiyya ta biyu da zan bar muku ita ce........" A daidai wannan lokaci ne wani mutu daya daga cikin mutanen garin,

Chapter 1 of 2